Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gangara, gefe kaɗan ya wonkeshi a bakin ruwan wutsiyar Kogin da yayiwa Rugar tasu ƙawanya.
Ya tahowa tana kallonshi.

Koda ya iso miƙa mata yayi,
kana ya ɗauki kondon, ganin still tanata kallonshi ne ya sashi cewa.
"Ya dai?".
Kai ta kauda tare da fara tsinkar ƴaƴan inabin tana afawa a baki tana taunawa,
Murmushi ya kumayi ganin yadda ta lumshe idonta.
A hankali tace.
"Ya Junaidu kayi kyau sosai yau, har kamar ka fini kyau".
Dariya ya ɗanyi kana yace.
"Yo dama ai na fiki kyau".
Maƙe kafaɗa tayi tare da cewa.
"Uhum a a kam".
A haka dai suna tafe suna hira.

Can cikin gida kuwa, Ummiy ce zaune bisa kujera ƴar tsuguno da buta a gabanta, alamun al'walan sallan walaha, zatayi.
Inna kuwa, da wasu maƙotansu uku Biba, Hari, da Innawuro. suna zaune bisa taburma a tsakar gidan. Suna amsar gaisuwa.

Can cikin garin kuwa su Alhamdulillah Manu dasu Siddine da dai sauran dattawan garin ne zaune a fada.
Sai yara daketa kai komo.

Da sauri su Siddi suka miƙe tsaye ganin, matasan mayaƙan ƙabilar ɓachama, sunata shigowa garin tako ina gabas da yamma kudu da Arewa, bisa dukkan alamu zobe sukayiwa garin
Kana ga zurma-zurman makamai masu tsawo tamkar raƙumai. Sai sheƙi sukeyi.

Cikin ɗaga murya, Alhaji Manu yace.
"Kai lfy? me haka?".
Ganin sun nufosu gadan-gadan ne yasa, suka miƙe gaba ɗayansu, kowa ya fara, neman makari, to amman ina, basu da zato ko sanin za'a far musu, shiyasa basu da shirin komai na kare kai.
Ɗaya daga cikin sune, yace.
"Mu gudu kashemu sukeda shirin yi ba tare da laifin komaiba".
Siddine ya kuma ɗaga murya tare da cewa.
"To in mun gudu matanmu da yaranmu fa".
Ihun da sukajiyo tako wani sashi na garinne ya tambatar musu, ana karkashe su.
Gudu suka farayi kowa ya nufi hanyar gidanshi dan ɗaukar matakan kare kai.
Sai dai ina basu da hanya duk inda suka ɓullo sai sunci karo da, mayaƙan.

Lokaci ɗaya garin ya ruɗe ya birkice kota ina sai ife-ife da gudun ceton rai da makiyayan Rugar Kikan keyi.

Wani irin sauti mai baiyana azabar fitan rai Alhaji Manu yayi, lokacin da wani kafurin ya caka mushi sitaka a ƙahon zuciyarshi.
Siddine ne ya juyo da azaban razani, amman sai shima ya saki wani sauti mai gigitarwa jin azaban sara da sukan da akeyi mishi.
Garifa ya kacame,
Hadi ne babban ɗa ga Alhaji Haro mahaifinsu Junaidun Junainah, ya nufi cikin gidansu da azama,
Yana cike da fargaba, da tashin hankali domin wasu irin ihu da yake jiyowa a cikin gidan nasu.
Yana kusa kai ya samu, makasan suna cike a gidan.
Suna ta'addanci, sun kashe kowa na gidan.
Ganin haka ya juyo yana juyowa. Yayi kiciɓis da abokinshi Sale, yana tafe jini na zuba an farka mishi ciki.
Cikin magagin mutuwa yake cewa.
"Hadi sun kashe kowa na garin nan sai wanda baya nan.
Hadi na kira Hukumar yan sanda ta nan cikin Numan na shaida musu, amman kafuran nan maƙiya Allah da Manzonsa sai cewa sukayi,
A kashe mu mana, ai an rage musu aikine.
Na kira su Arɗo Bani, suna ɗagawa katin wayata ya ƙare.
Hadi sun kashe kowa na gidanmu.
Taroshi Hadi yayi suka faɗa nan suna kuka mai cike da taraddadin rabuwa.
Cikin ƙarfin hali Sale ya ture Hadi tare da cewa.
"Ka gudu Hadi ku gudu, Ni nasan bazan rayuba.
Ka gudu.
Sun kashe min Kowa har jariren tagwayen da aka haifa min shekaran jiya, sun kashesu.

Cikin kuka Hadi yace.
"Bazan iya guduba Sale su kasheni kawai, ina zanje bayan sunyiwa garin zobe.
Da ƙarfi Hadi ya abka jikin Sale Jin ansa gatari an sari kafaɗarsa ta dama,
Juyowar da zaiyi kuma aka tsira mishi mashi a ƙirji.
Nan take ya cika, hakama Sale.

Cikin gidansu Shatu kuwa.
Ummiy ta sallame sallan kenan, taji.
Inna dasu Innawuro suna kurma ihu da salati.
Yunƙurawa tayi da azama jiki na rawa ta nufo woje.
Fitowanta yayi dai-dai da lokacin da aka sare kan Innawuro, wanda kan yayi tsalle ya faɗo kanta, kana ya gangara ya faɗa gabanta.
Wani irin ihu mai cike da karaji gauraye da salati ta kurma lokacin da taga an burmawa Inna mashi a ciki.
Ihunta da salatinta ya jawo hankalin su, sukayo kanta.
Sai dai kafin su isoma ta yanki jiki ta faɗi babu numfarfashi tamkar matacciya.

Koda suka iso, dariya suka kece da ita cikin rashin imani ɗayansu yasa ƙafa, ya taka ruwan cikinta, tare da cewa.
"Shegun FULANI ku mutu, mu huta, da ganinku a garinmu, gonakinku da dabobbin ku duk sun zama namu.
Mu ɗauke yaranku mata mu maidasu karuwanmu, muyi musu ciki su haihu mu bawa dodo.
Muji daɗi dasu.

Ganin kamar ta mutune yasa suka tattakata suka wuce suka fita daga gidan.

Junainah kuwa da Junaidun, suna gab da shigowa garin suka fara jiyo ihun mutanen garin.
Cikin azaban firgici Junaidu ya wurgar da kondon ƴaƴan itatuwan dake hannunshi,
da gudu yabi bayan Junainah data ruga a guje sabida hango, anata kashe mutane a gabansu.
Cikin kuka da tarin kiɗima da fita haiyacinta take cewa.
"Wayyo Ummiy Wayyo Inna Wayyo Bappa, zasu kashemu.
Wayyoooooooo Adda Shatu zasu kashemu".
Riƙo hannunta yayi da ƙarfi cikin rawan jiki da murya yace.
"Junainah bazasu kashekiba, zan kareki da izinin ubangiji, zaki rayu, Shatu bazata rasa kowa duniya ba.
Junainah zan zame miki Garkuwa zan fanshi ranki da nawa ran.
Ki zama tamkar yar tsira, Shatu ta zama tamkar yar jarida, ta rubutawa mutanen duniya su karanta, kisan gillan da akeyiwa Fulani mazauna daji.
Da ƙarfi yasa hannu ya zaro wukar dake ƙugunshi wanda da ita ya yayyanki nonunan ayaba dasu inabi.
Wayarshi ya kuma zarowa
Ya Salmanu ya kira,
Salmanu kuma dake, kwance a gadon asibitin nan Genaral Hospital Numan.
Wanda bai workeba tun dukan shaɗi da ba'ana ya mishi.
A hankali yasa hannunshin ya amsa kiran wayarshi ganin Junaidu ke kiranshi.
Cikin kiɗima da firgici Junaidu yace.
"Ya Salmanu, mayaƙan ƙabilar ɓachama sun shigo Rugar mu, sunata kashemu, mazanmu da matanmu.
Ya Salmanu Junainah ina son ta tsira, ko dan ran Junainah ka kira mana hukumar yan sandan cikin Adamawa, ina son su iso su ceci Junainah kada Shatu ta rasa kowa a duniya.
Ban saniba ko zan gazawa bawa Junainah tsaro".
Gaba ɗaya jikin Salmanu rawa da tsuma yakeyi, katse kiran yayi da sauri ya kira.
"A.S.P Kabiru Nasir. Wanda yake, Hetkotan Adamawa.
Koda ya mishi jawabin abinda ke faruwa, a take. A.S.P ya kira.
S.P Daniyel dake Numan ya bashi doka da oda maza-maza su bawa fulanin Rugar Kikan tsaro gaggawa, shima yana nan tafe da rundunar sa. Ya bashi umarni mai ƙarfi ya ƙara da cewa, muddin yazo ya samu ba dai-dai ba ta ɓanƙaren tsaro, to akan aikinshi.

Wannan abun na umarni daga samane, yasa mugun kafurin nan. Firgita gudun rasa aikinsa, da tonuwar asirinsu da gudun kada a cireshi asa musulmi a kujerarsa, yasa cikin gaggawa ya haɗa kan rundunar sa ya nufi.
Cikin Rugar Kikan.

Junainah kuwa wani irin karkarwa takeyi wanda, tuni fitsari ke tsiyaya yana bin sawunta.
Wani irin ihu tayi, ganin wani kafurin ya kaiwa Junaidun sara a bayanshi.
Wani irin juyi Junaidun yayi ya farma kafurin da da wuƙarsa dan kare kansa da Junainah.
Duk da su biyar suka zagayesu, basuyi nasara a kanshiba, yana kare kanshi da Junainah, har saida suka tsira daga waɗannan.
Sai kuma wasu, mutun takwas suka cimmusu.
Da ƙarfi suka banƙaren Junaidun, suka fara kiciniyar zare Junainah da ya ruggumeta da azaban ƙarfi da yayi.
Wani irin ihu yasa jin an caka mishi.
Wuka a gadon baya.
Still bai saketaba, sai yaƙin kareta da ya farayi, da iya ƙarfinshi.
Ita kuwa Junainah ganin an caka mishi wuƙane yasa ta sume.
Dai-dai lokacin kuma rundunar yan sandan suka iso.

Kamar bazasu guduba, dan sun san da bakin hukumar sukeyin aikin, to sai dai ganin musulman cikin yan sandan suna sakin harbine yasa.
Suka ari ta kare.


Daga nan suka rinƙa gudu sunayiwa yan uwansu fito alamun su gudu.
Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gudu.

Su kuwa yan sandan, suka shiga cikin Rugar Kikan ɗin.
Hankalin musulman cikinsu yayi masifar tashi ganin irin kisan gillar da akayiwa bayin Allah'n nan, kisa na rashin imani.
Nan take suka kira motocin asibiti.
Suka rinƙa jidon masu sauran rai suna sawa a motar ambulance suna kai cikin Genaral Hospital Numan.
Kana suna harhaɗa gawakin kuma a tsakiyar garin.
Cikin mintuna talatin rundunar A.S.P ta iso.
Tare da yan jaridu.


Su Bappa kuwa. Koda suka gama tattaunawa da Maimartaba, sai ya umarci Waziri daya hanasu tafiya a bisa adalcinsa.
Yace su tsaya suci abincin rana, kana suyi sallan azahar kafin su tafi.
To haka yasa suka zauna.
Waziri yasa akayi musu duk ihsanin da Maimartaba ya bada umarnin ayi musu.
Sukaci abinci sukasha, Sannan sukayi sallan azahar.
Daga nan aka sallesu suka tafi.

Tuni cikin gari kuwa gidajen rediyo sun ɗauka, batun faɗan FULANI makiyaya da Ɓachamawa manoma, wanda akaso a juya rahoton da cewa makiyayan ne sukayiwa manomanne ɓarna.



Bayan. Tafiyan su Bappa da kamar 30 minutes ne. Labari abinda ya faru ya riski Maimartaba.
Nan take yasa Waziri da Galadima da hadimai mutun ashirin suka nufi cikin Numan dan suje su tabbar da abinda akace ɗin.

Su Bappa kuwa, sam basuji lbrinba saida suka isa cikin Numan.
Ganin garin a hargitse ne yasa Arɗo Bani ya kalli Bappa da Alhaji Haro da suke gefenshi cikin mmki yace.
"Lafiya kuwa? Meke faruwane a garin nan?".
Cikin kaɗuwa suka haɗa baki wurin cewa.
"Allahu alamu".
Drivern nasune, ya kallesu a tsorace yace.
"Anya kuwa yau ba faɗa akeyiba a garin nan ba".

"Kai ba lfy ba kam!".
Cewar Alhaji Umaru
Shi kuwa Drivern, bakin titi ya ɗan gangara ya tsaya, ya tambayi wasu yan agaji daketa.
Shiga cikin wani babban Pharmacy da alamun magunguna suke saya,
koda suka mishi bayanin abinda ya faru.
Jiki na rawa yazo ya sanarwa su Arɗo Bani.
Lokaci ɗaya hankalinsu. Yayi masifar tashi.
Nan sukace ya wuce dasu.
Asibitin.

Koda sukaje hanasu shiga akayi.
Hakane yasa, sukace to ya wuce dasu Rugarsu.
Suga ko canma akwai uban da zai hanasu zuwa.

Nan ya nufi cikin Rugar tasu dasu.

Su Wazirima tuni, sun iso.

A can cikin masarautar kuwa,
Sosai hankalin Maimartaba ya tashi.


A can ƙasa mai tsarki kuwa.

Sitti ce tsaye gefen Sheykh lokacin da yake mgna da kakanshi.
Zama tayi gefenshi, tare da tsareshi da ido.
Baibi ta kantaba, ya ci gaba da sarrafa wayarshi.
Wata number, ya dannawa kira kana ya kara wayar a kunne, jim kaɗan aka amsa kiran.
Bayan sun gaisane, ya ɗan gyara zamanshi tare da ɗan kallon Sitti ta gefen ido
Cikin harshen fillanci yace.
"A haɗa min zama da Ƙungiyar TABITAL POOLAKU".
Sai kuma ya ɗan shaƙi sanyi da ƙamshin ɗauki ido ya lumshe cikin kamala da nitsuwa yaci gaba da cewa.
"A kira min Ƙungiyar MIYETTI ALLAH, da gaggawa, ina da zama dasu.
Ranar Jumma'a in sha Allah".
Hannun damanshi yasa yana shafa sajenshi, tare da sauraron mgmar da. Arɗon Arɗaɓe keyi.
"Ranar jumma'a kuma? Ka dawone?".
A takaice yace.
"Zan dawo!".
Cikin gamsuwa da mgnarshi sanin in yace eh, eh ɗince in kuma yace a a, tofa a ance.
Muddin kuma yace zaiyi abu to da izinin ubangiji sai yayi shi.
Cikin jin daɗi adalci da kulawarshi ga shugabanci da aka bashi yace.
"To Allah ya dawo da kai lfy".
Yatsun ƙafarshi ya sunkuyar saida suka ɗan bada sautin ƙaras, kana yace.
"Amin ya rabbil izzati".
Daga nan ya katse kiran.

Kamar bata wurin haka ya jawo System ɗinshi ya fara daddannata.
Kamar babu kowa kusa dashi haka yaci gaba da aikinshi.
A system, ita kuwa Sitti ido ta zuba mishi.
Tana kallon yatsun hannunshi da yaketa sassarfa, tamkar shiya haaliccin na'ura.

Yanajin idanunta na yawo a sasan jikinshi, hakan yasa, ya ɗan juya kwayar idanunshi, ya ɗan kalleta ta wutsiyar idonshi, murya can ƙasa yace.
"Sitti wannan kallonfa, kin san bana son kallo kam ko?".
Ajiyar zuciya ta ajiye, kana ta ɗan janye Hiramin kanshi, da sauri yasa hannunshin ya kame hiramin cikin kwaɓe fuska yace.
"Sitti ya haka, kinsan Haroon ba kan gadone dashiba, yanzu zai iya shigowa da yaran nan".
Ido ta ɗan rufe kana tace.
"To su yaran mayune, ko yaushe kana rufe da Al'kyebba da hirami, kasha iska mana, ko nauyi basa makane?".
Kanshi ya ɗan juya kana a hankali yaci gaba da aikinshi tare da cewa.
"Suturce jiki shine, zaiyiwa ɗan adam nauyi, Sitti, sannan ya za'ayi in bari ko wani Tom and Jerry su kallarmin suman kai, ai shi hula da hirami kamar ɗan kwaline wa mace".
Sai ya kuma ɗan juyowa ya kalleta tare da cewa.
"Yauwa Sitti, bana son ana sawa Jazrah tana samin abinci, bana so, sai a turrota tazo taita kare min kallo".
Fuskarta ta haɗe kana tace.
"To yayi kyau, kawai in baka sonta, ka fito fili ka faɗa mana".
Kauda mgnar yayi tare da cewa.
Ki shirya in sha Allah zuwa ran jumma'a ina son in kasance cikin ƙasata ta haihuwa a jiharmu a kuma masarautarmu".
Haroon da yanzu ya shigone ya ɗan kalli ɗan uwan nashi, cikin mmki yace.
"Sheykh kawai dan ana mgnar baka matar aure shine kake shirin guduwa zaka bar ƙasar ba?".
Bai kalli Haroon ba kuma baice, komai ba, sai rufe system ɗinshi yayi kana ya miƙe a hankali,
gaban drower'n gadon ya nufa,
buɗewa yayi, wasu E Passport guda biyu ya ɗauko,
Kana ya dawo gaban Haroon.
Hannun shi ya kamo ya danƙa mishi su, kana yace.
"Gasu, ina son zamu bar ƙasar nan ranar al'hamis."
Da sauri Sitti tace.
"Kaida waye zaku tafi".
Ba tare daya kalletaba yace.
"Da ke".
Kai ta kuma juyawa tace.
"A a kam ka koma kai ɗaya, ni ban gaji da ganin ahlinaba".
aKanshi ya kaɗa tare da cewa.
"Zafa ki koma, don bazan barki a kasar nanba, kiyi ta haɗa min tarko, dole tare zamu tafi, inada zama mai mahimmanci, dole inje inji da matsalar al'ummar da aka naɗani GARKUWANSU, tunda ke kika sa na amince da wannan naɗin, ina zamana lfya, wani mulki ko sarauta basa jadawalin rayuwata, keda waɗancan tsofoffin sarakunan kuka likamin wai GARKUWAN FULANI,
To sun samu matsala kuma dole inje in bincika".
Shiru kawai Sitti tayi ganin karfin hali ziraran miraran.
Zuwa yanzu ta dena mmkin, cewa akan abu biyu Sheykh ke iya doguwar mgna, akan Alqur'ani, wanda shine zaka samu zai iya wuni a zaune yana tabsiri ba gajiya ba yunwa bare ƙishi ko bacci.
Sai kuma akan wannan sarautar GARKUWAN FULANI da aka bashi shekarun biyar baya, wanda harga Allah baison wannan Sarautar ko kaɗan sai dai dole da akayi mishi, da fushin da Abbunsu ya nuna a kan haka.
Shiyasa duk sanda zaiyi ƙorafi yakan iya jera mgna biyar zuwa bakwai, wanda sam shi tsarin rayuwarsu ba mai doguwar mgna bace.

Kai takaɗa jin yana cewa.
"Ku ɗan bani wuri".
Basuyi mgna ba suka fita, a tare, domin sun san Sheykh Jabeer mutunne mai tarin tsananin al'kuyya da killace jikinsa, shi kanshi yana kunyar kanshi a rayuwarshi ta duniya shi bai taɓa yin tsirara a kan kanshi wai yaga surar jikinshi ba, Allah yasani yana masifar jin kunyan kanshi.
Haka yasa koda wonka zaiyi, baya yin tsirara,
yanada wasu tausasan gajerun towel wanda duk rintsi dasu yakeyin wonka a jikinshi.


Suna fita falo, Haroon ya tsaya yana kallon Jazrah, dake konce bisa kujera ta kife kanta a cinyar Jannart tana kuka mai sanyin sauti.
Kai Sitti ta juya ta nufi ɗakinta,
Allah ya sani Jazrah na son Sheykh, shi kuwa bai nuna ya tsaneta ba, amman dai ya nuna zahirin bazaiyi aureba.

Haroon da Jannart ne suka zauna suna bata baki.
Saida ta nitsune suka fita tare.

Shi kuwa Sheykh suna fita, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe.
Kana ya dawo bakin gado.
A hankali ya zare tattausan al'kyabbar jikinshi, fararen kayan dake jikinsa suka baiyana.
A hankali ya zare rigar ya ajiyeta gefe.
Zariyan wonɗon ya kunce, tare da zama, ya saɓule tare da matsawa gefe.
Ya rage dagashi sai fararen boxes da vest.
Juyawa yayi yana taku mai cike da nitsuwa,
ya shiga bathroom ɗin.
Yana shiga ya maida ƙofar ya rufe,
kana ya rage hasken ciki.

Sannan ya cire ƙananan suturun dake jikinshi tare da ɗaura towel ɗin, a ƙuginshi zuwa kan cinyoyinshi masu yelwar gargasa mai taushi da tsulɓi da sheƙi tana,konce lib-lib a farar fatar jikinshi.
A haka ya fara, wonkan, bayan yayi Brosh a hankali yake bin jikinshi da sabulun mai ɗan karen ƙamshi, yanayi ya cuccuɗa jikinshin.
a hankali ya iso kan ƙugunshin, cikin sabo da iya ɗabi'ar tasa, ya cusa hannunshi ta cikin ɗaurin towel ɗin, ya rinƙa cuccuɗa jikinshin da murza mishi daddaɗan sabulun ya murje ko wani lungu da saƙo na sasan jikinshi ba tare da idanunshi ma, sunga tsiraicinsaba.

A ƙalla yayi sawon daƙiƙu ashirin a bathroom ɗin kafin, ya fito,
yana ɗaure da wani babban towel mai ɗan karen kyau da taushi bayan ya matse wancan ya shanya.

Yana saƙo ƙafarshi cikin bedroom ɗin ya...!






Solo-salo-salon GARKUWA na dabanne!


By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 13

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🌈🦚🤴🏻💘


FREE PAGE

Littafin GARKUWA na kuɗine, Special Group 1k Normal 300, in kina buƙatar karanta lbrin GARKUWA turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276. Gareku mutanen Special Group turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number 09097853276.



*Dan Allah da Manzonsa da darajar iyayenki, in kin san zaki sayi littafinane dan ki fitar dashi, na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar iyayenki kada ki saya bana son kuɗinki, ki riƙe kudinki ki barni in riƙe littafina. Dan Allah nace badon niba.*



Yaji anata bubbuga mishi ƙofar ɗakin,
bai kulaba, yazo a zauna bisa kujerar dreesing mirror, a hankali yake tsane ruwan jikinshi, bayan ya gama ɗan tsane ruwanne ya busar da tattausan sumar kanshi, ta hanyar na'urar busar da gashi.
Mai ya ɗan shafa, kana ya gyara gashin da kyau, sannan ya miƙe yaje gaban.
Drower'n, a nitse ya buɗe, wasu datsatstsun kaya riga da wondo na yadin Lamud, yadin Sky blue ne mai masifar kyau. Sai kuma ya zaro wata farar al'kyabbar fara ƙal. Da farin hirami.

Rufe wannan gefen yayi, kana ya buɗe ɗaya gefen.
Ƙananan kayan ne a ciki kamarsu Jallabiya da boxes vest dasu zagayen baƙin abin da yake ɗaurawa kam hiraminshi.
Suma duk mafi akasari su fararene.
A bakin gadon ya ajiyesu.
Kana ya fara kimtsawa.

Bayan ya gama shirinsa ya fito ras cikin kalar sky blue and white sai Black half cover da kuma baƙin zagayen saman hiramin.
Ya fito ras tamkar dai yadda zuriyar mahaifiyarshi da suke tsatson limamen Harami suke fita.
Ko yaya ka ganshi dole kace shi balarabene, sabida komai nashi irin nasune. Kyau, fari, gashi, ilimin addini, nitsuwa, imani, da kuma irin shigarsu, da shima ya rainu da hakan tunda a cikinsu ya girma.

Wani turaren Oud Kareem ya feshe jikinshi dashi.
Lumshe ido yayi sabida shida kanshi ya shaida ƙamshin wannan turaren nashi iyakane.

A hankali ya nufi ƙofar fita yana tafe yana tasbihi.
"Astagafirullaha wa'atubu ilaik.
Astagafirullaha zunuba jami'an. Subahanallahi Wal'hamdulillah wa la'ilahaillahu Allahu Akbar."
Da wuya ka iya jin abinda yake faɗin, sai dai ina ka lura da motsawan jajayen laɓɓansa, masu kama da jajayen kunnen fire masu taushi zaka fahimci tasbihi yakeyi.

Ba kowa a wurin sabida haka ya nufi falo a nitse,
A falon ya samu Sitti bisa dukkan alamu, shirin tafiya harami tayi.
Tana ganinshi ta miƙe tare da cewa.
"Muje ko". Kai ya gyaɗa mata, kana ya ɗan kalleta bayan ya ɗan tsagaita tasbihin bakinshi yace.
"Zan shiga wurin Sheykh Abdulkareem".
Cikin kula tace.
"Muje sai mun dawo mana".
Kanshi ya jujjuya mata kana yace.
"Zan sanar dashi batun komawarmu".
Gyara matafinta tayi tare da cewa.
"Na sani ai, muje sai mun dawo".
Fuskarshi ya ɗan haɗe tare da cewa.
"Ni a harami zan kwana".
Ganin ya kafe tasan fa duk yadda tayi, hakan zaiyi,
binshi kawai tayi,
suna shiga suka samu kamilin dottijon nan, bisa tsakiyar yaranshi, da alamun suma ɗin anjima zasu taho masallacin.
Yana hanƙoshi ya miƙa mishi, hannunshi na dama, da sauri ya isa gareshi, ya kama hannunshi tare da rusunawa, ɗaura hannun yayi bisa tsakiyar kanshi, sannan yayi shiru yanajin yadda dottijon ke zuba mishi addu'o'in.
Yayinda kamilan yaranshi ke amsawa da.
"Ahmeehn! Ahmeehnn!! Ahmeehnn!!!."
Bayan ya gama mishi addu'o'in ne, ya juyo ya gaida kakanun nashi, baki ɗayansu.
Kana ya shaida musu tafiyarsu data taso cikin gaggawa ya kuma sanar musu dalilin tafiyan.
Sun gamsu da hakan, kasan cewar sun ɗan ɓata lokaci a nanne yasa. Tare suka tafi masallacin baki ɗayansu.

Haroon kuwa cikin kwana biyu ya gama musu komai na tafiyarsu, gida dan shima dama yana son tafiya gida shida Jannart ɗinshi duka.



A cikin makarantar su Aysha kuwa.
Sam bata samu lbrin abinda ya faru a rugarsuba.

Sai da yamma, nanma Rafi'a ce, dake riƙe da wayarta tana chatting.
A nan ne ta gani a kafafen yaɗa labarai cewa.
Anyi faɗa a tsakanin MAKIYAYA da manoman, a garin Kikan dake gaɓar kokin Namun.
Koda ta sanarwar Aysha.
Taga tashin hankali ya wuce zatonta,
hakane yasa ta bita suka tafi tare.

Su Bappa kuwa bayan sun nufi, rugar tasune, sukaci karo da motar police officers, da kuma Ambulance ɗin, daya ɗebo su Ummiy dasu Junaidun da Junainah, kana. Da wasu wadanda ake ganin kamar sunada ɗan sauran numfarfashi.

Da sauri C.P Daniyel yasa, drevernsu Arɗo Bani, ya juya dasu, dan suka nufi cikin Genaral Hospital Numan ɗin, sabida yasan in sukaje suka, ga irin kisan gillar da ƙabilun nan sukayiwa yan uwansu, tashin hankali zaiyi yawa ya kuma san A.S.P Kabir da rundunarsa na, can, to zasuyi mishi bayanin da zaisa ya iya korarshi a aikinshi.
Shiyasa ya jasu suka koma, cikin asibitin.
A cewarsa su kula da mutanen su, saura kuma, kuma, akwai hukuma na, kula dasu a can.

To wannan dalilin ne, yasa suka koma cikin asibitin,

Hakane yayi sanadin da koda Waziri da Matawalle da rundunar Hadiman da Sarki ya aiko,
Suka zo, basu ga su Arɗo ba a cikin Rugar, kana kusan wuni sukayi a nan dan sai yamma, suka juya suka koma masarautarsu.

Ita kuwa Aysha, suna zuwa, kai tsaye cikin asibitin suka nufa, dan tayi waya da Bappa.

Koda suka iso, sosai hankalin ta ya tsananta gaba hankalinta ya tashi, ganin gaba ɗaya asibitin a cike yake da mutane su,
sai dai ta ɗan samu nitsuwa kaɗan ganin Ummiy da Junainah sun farfaɗo,
sai dai duk basa mgna sunyi zurui dasu hakama sauran waɗanda suka samu suka farfaɗo ɗin.

Koda ta tambayi Bappa inasu ya Giɗi sai cemata yayi suna gida, ya ɗaura da cemata.
"Yauwa Shatu ku zauna nan, ku kula da marasa lfyan, bari mu kuma mu ƙarasa can Rugar tamu, mu duba meke faruwa a gidan".
Hannu tasa ta share hawayenta dake shatata daga cikin kumburarrun idanunta cikin disashewar muryar da kuka yasa ta dishe tace.
"To Bappa kuje, zamu kuladasu, ga can Ya Salmanu ma, ya turo mana abokanshi, ga kuma ƴan agaji, zamu zauna dasu".
Cikin tarin ƙuna da tafasar zuciya, Alhaji Haro, ya gyara gariyarsa tare da cewa.
"Mu tafi".
Arɗo Bani ne ya miƙe tsaye tare da yin gaba kana duk suka bishi a baya suka fita suka tafi.

A hankali Rafi'a tasa hannu ta tallabi Aysha daketa kuka mai sosa zuciya, kuka mai cike da rauni da taraddadi.
Zama sukayi cikin tausayawa Rafi'a tace.
"Ki dena kuka Aysha, in sha Allah babu komai."
Murya na rawa hawaye na kwaranya ta buɗe manyan idanunta da suka rine sukayi jazir da kuka da tashin hankali, cikin rauni tace.
"Rafi'a babu komai kuma?, ko dai komai ya faru, kalli fa halin da yan uwana da maƙotanmu suke ciki, kinjifa ance an kashe mutun kusan 40, kuma kin san gidajen rediyo suna ragewa nema wasu lokutan sabida kada, hankali mutanen duniya ya tashi.
Rafi'a banga Yayuna ba, ko ɗaya ban ganiba, banga Inna ba, kalli Junaidu, kalli can Ya Mati yayansu Ya Salmanu. Kowa baya cikin haiyacinsa,
Ummiy ta zama kamar kurma meta gani ya gigitata haka, kalli yadda Junainah keta fizge-fizge alamun taga mugun abun daya firgitane ya ɗimautata.
Rafi'a ga tozarci da cin fuskar da akeyi mana, kallifa babu likitan da yazo ya kula mutanenmu, an barsu ciwukansu nata tsami,
sai Nurses keta, hararanmu.
Rafi'a ya zanyi in banyi kukaba, ina zansa raina, Ina Yah Giɗi, ina Yah Gaini, Ina Yah Seyo? Rafi'a sun kasarani sun rabani da yan uwana."
Kife kanta tayi jikin gadon da Ummiy ke kwance a kai, cikin murya mai cike da rauni tace.
"Ummiy kiyi min mgna mana, Ummiy na inasu Ya Giɗi na ina Ya Gaini, ina Ya Lado, ina ya Seyo,

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment