Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Aunty Ayshan Hamma Jabeer tazo".
Tayi mgnar da alamun tasan Aysha a hoto.

Murmushi tayi tare da sa mata bakin gorar ruwan a baki.
Cikin mussuke ido ta buɗe baki ta fara shan ruwan.
Aunty Rahma kuwa, kallon Aysha take cike da ƙauna.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Aysha cikin yanayin da bazaka gane manufarshi ba tace.
"Sannuku da zuwa yau kam gaki a masarautarmu tushenmu, gaki ga Sitti kakarmu data haifi babana ta kuma haifi Mamansu Sheykh da Ya Jafar dasu Jamil jininmu ɗaya".
Ta ƙareshe mgnar cikin nuna kusanci da dangatakar dasu Sheykh na jinine.
Kai Aysha ta ɗan juyo ta kalleta,
murmushin gefen baki tayi,
dan ta gane manufar Aunty Juwairiyya tana nuna mata cewa su jini ɗaya ne, itace bare a tsakaninsu.
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh yau kam gani ga Sitti ga Aunty Rahma".
Ta ƙareshe mgnar tana wata mgnar a zuciyarta.
"Uhumm Aunty Juwairiyya kenan, ai dama saida ɗan gari akanci gari da yaƙi, kina matsayin yar uwarsu kuma kike cutar dasu, in da zasu sani da bazasu aminta da keba".
Muryar Ishma ce ta katse mata mgnar zuci da takeyi.
"Aunty Aysha ina Hamma Jabeer".
Kanta ta ɗan shafa tare da cewa.
"Yana Tsinako".
Da sauri tace.
"To shi bazai zo bane?".
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
"Zai zo".
"Yaushe?". Ta kuma tambayarta a gajarce.
murmushi ta ɗan yi tare da cewa.
"In Sha Allah gobe zasu zo".
Allah ya kaimu ta tafaɗa tana wasa da jelan gashin Aysha dake bisa kafaɗarta.


Aunty Rahma ce ta ɗan harareta tare da cewa.
"Maza tashi a jikinta ki barta ta huta".
da sauri ta ɗan zame ta sauƙa ita kuwa.
Aysha kai ta ɗan karya tare da cewa.
"Aunty Rahma barta".
Safiyya ce tace.
"Ahyya baki san Ishma bane da shegen surutu da son jiki".
dariya sukayi ganin yadda Ishma ta zumbura baki.
Sitti ce ta miƙe tsaye tare da kallon jikokin nata da yar autar tata, tace.
"Toh maza ku tashi muyi sallan azahar, in mun idar ku isa wurin Jadda ku gaisa."
Kusan a tare suka mimmiƙe, Aunty Rahma ce ta kamo hannun Ishma tare da cewa.
"Jadda ya fita, ai ɗazu ya kirani yace in masa abincin dare, wai ya ɗan fita zai kai dare kafin ya dawo".
Dariya Sitti tayi tare da cewa.
"Uhumm kai Jadda wato ki masa abincin dare. In kun koma kuwa naga wa zai ce ta dafa mishi".
Safiyya ce tace.
"Oh zai ci girgikin yar autarsa".
Ita dai Ramatu murmushi tayi tare da cewa.
Aysha Juwairiyya Jazrah Safiyya mu tafi ɗakina".
To sukace kana suka bita a baya.
Har zasu fitane Sitti tace.
"A a Aysha dawo nan, ke kam baƙuwa tace ga masauƙinki".
Murmushi Aysha tayi kana ta juyo ta dawo sabida tafi gamsuwa da zama kusa da Sitti akan a tsakiyar Juwairiyya da Jazrah dake mata wani irin mayataccen kallo.


Haka dai sukayi sallan azahar,
kana suka fara shirin kamu.
Wanda tuni ango Haroon da tawagar abokanshi sun iso.

Anayin Sallan la'asar suka fara.

Sai gab da magriba suka tashi.
Ranar kusan kwanan zaunen sukayi anata hirar yan uwantaka.
Yayinda Aysha bata gajiya da jin muryar Aunty Ramatu da kallon fuskarta da fuskar Ishma.

Basu samu sun isa wurin Jadda ba.
Sun bari a akan sai gobe da safe in Allah ya kai rai.


A can Tsinako kuwa, gaba ɗaya al'ummar masarautar Tsinako da baƙi abokan Abbansu Haroon dana kakansu Sarki.
Da kuma baƙi na nesa dana kusa duk an kwana cikin shirin, tafiya ɗaurin auren.
Masu tafiya a jirgi ƙarfe tara jirginsu zai tashi.
Masu tafiya a motoci kuma sammako zasuyi.
Sabida sha ɗaya na safe za'a ɗaura auren.



Haka kuwa akayi washe gari da safe masarautar Jalaluddin, ta fara amsar baƙi tako wani saƙo na ƙasar Nigeria.


Fadar masarautar dama farfajiyar ta cika tayi tab da baƙi da ƴan gari, tako ina halarta mutane keyi.

Karfe sha ɗaya dai-dai na safe taron al'ummar musulmi suka shaida ɗaurin auren Haroon da Jannart.

Bayan an ɗan wawwatse mutane duk sun kama hanyar komawa inda suka fito.
Sai Abokan ango da zasu ɗauki ƙawayen Amarya da wasu yan uwa.
Dan amarya dasu Aunty Juwairiyya da Jazrah da Aunty Rahma Ishma da ƙannen mamansu Jannart duk sun tafi a jirgi, da ango.
Safiyyah da Aysha da Azeema da Hibba ne kaɗai suka rage.
Dan Safiyyah ce ta hana Aysha tafiya dasu Auntyr Rahma tace, ita tare zasu tafi.
Haka kuma Sitti ma tace haka yasa koda suke ribibin tafiya ita tana bacci a ɗakin Sitti bisa gadon mulkinta, dan kwanan da sukayi ba bacci yasa duk suna cike da bacci.

Ibrahim da Sheykh kuwa sune suka tsaya da wasu abokan Haroon biyu, sai sunga duk mai buƙatar zuwa ta tafi.


Ƙarfe sha biyu dai-dai Sheykh Jabeer da Ibrahim da Munnir da Mansur abokan Haroon Suka shigo babban falon Sitti.

A nan suka samu Jalal da ya Jafar da Ammar ƙanin Aunty Juwairiyya da Ibrahim wanda shine yayan Jannart.

Sai kuma Goggo Mairo ƙanwar Jadda da kuma sauran yaran Jadda wanda kishiyoyin Sitti suka haifa.

Safiyyah na ganin shigowarsu ta miƙe ta nufi Dinning area fridge ta buɗe ta haɗo musu ya'yan itatuwa masu sanyi, ta gyara kana ta kawo musu.

Bayan sun gaggaisa ne,
Ibrahim ya ɗan kalleta tare da cewa.
"Kun gama shiryawa ko?".
Kai ta gyaɗa mishi al'amar eh.
Sai ta kuma kalli Sheykh dake miƙawa Ya Jafar nonon inabi yana kuma ce mata.
"Sitti fa?".
jujjuya kai tayi cikin falon ta kalli gabas da yamma kudu da arewa.
Gane wai neman inda Sitti takene yasa Goggo Mairo cewa.
"Bata nan ai ta fita".
ɗan miƙewa tsaye tayi tare da cewa.
"Ikon Allah kuma fa da muna nan tare da ita. To ina tayi".
Aunty Salima wacce take itace Babba a yaran Jadda ne tace.
"Nima fa ita nake jira".
Jalal ne ya ɗan kurɓi ruwan sanyi tare da cewa.
"To ko tayi ciki ne".

"Ba mamaki". Goggo Mairo tace.

Cikin nitsuwa Sheykh ya miƙe tsaye, kekyawar al'kyabbar jikinshi ya ɗan buɗa tare da gyara zamanta jikinshi.
Corridor'n da zai sadashi da special Side ɗin Sitti ya nufa, a nitse.

A can bedroom ɗin Sitti kuwa.
Aysha ce tsaye gaban dreesing mirror bayan ta gama ado da kolliyar ta.
Wani dandatsetsen Shadda lace ne mai masifar kyau da taushi tare da sheƙi ne a jikinta, ɗinkin Doguwar rigace.
Ta zauna ɗas a jikinta gwanin burgewa da ban sha'awa.

Kalan kayan sun taimaka kwarai wurin burgewa, dark red wine mai masifar kyau, sai ratsin zare Royal blue mai azabar kyau da sheƙi da aka zubashi suffar zanen ɗawisu.

Turare ta feshe jikinta dashi,
kana ta maida kolbar sannan ta dawo gaban dreesing mirror kujerar ta jawo ta zauna.
Kasan cewar dreesing mirror babbane mai tudu hakama kujerar.
hannu tasa ta fara tsaɓule ribon ɗin da ta tubke himilin gashinta dashi.


A nitse ya iso bakin ƙofar Bedroom ɗin Sitti.
hannunshi yasa ya tura ƙofar,
ɗan wani guntun tsaki yaja tare da sa guiwar yatsunshi biyu ya ɗan ƙonƙosa kofar sau uku.
Kana ya ɗan tsaya gefe.

A hankali ta juyo kanta ta ɗan kalli bakin ƙofar,
har kamar bazata tashi ba.
Sai kuma ta tuna ta rufe ƙofar lokacin da Safiyya ta shigo ta tasheta kan ta tashi ta shirya su tafi.
To da zata shiga wonka ne ta rufe ƙofar dan tana jin kunya kada ta fito tana shiryawa wasu su shigo su sameta.

A hankali ta miƙa tare da juyawa ta nufi ƙofar tana ƙoƙarin warware ɗan kwalinta.

Isowarta bakin ƙofar yayi dai-dai da lokacin ɗaya kuma ɗan buga ƙofar.
Hakan yasa bata gama warware ɗan kwalinba tasa hannu ta buɗe ƙofar dan a zatonta Sitti ce ko Safiyyah.

Tana buɗe ƙofar sai ta ɗan koma da baya, haka yasa bata ganshi ba.
Bai ganta ba.

Kutsa kanshi yayi cikin ɗakin tare da sallama a bakinshi.
kana yasa hannunshi ya maida ƙofar.
Kasan cewar dreesing mirror yana fuskantar ƙofar shigowan ne, yasa. Mutun zai iya ganin abinda ke bayansa muddin yana kallon cikin madubin.

Kanshi a sunkuye da alamu wayarshi yake ɗan lallatsawa.

Haka yasa hankalinshi baya kan madubi.

Ita kuwa Aysha, wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe a hankali jin daddaɗan ƙamshin turaren jikinshi.

A hankali ta zubawa bayanshi idanu tun daga kan dudduniyar farar kekyawar ƙafarshi, har zuwa kan tattausan suman dake kwance lib a ƙeyanshi.
Kasan cewar da yasa hiramin yau yayi irin siririn sakun nanne ya tattare gefe da gefen hiramin.

Taku uku yayi ana huɗu ya tsaya cak, ba tare da ya ɗago kanshi ba ko ya juyoba, yace.
"Wannan kallon fa?".
Cikin tsananin mamaki da tsoron al'amarin Sheykh tayi saurin yin ƙasa da kanta.

Shi kuwa Sheykh a hankali ya ɗago kanshi, ya dire idanunshi kan faffaɗan mafubin daya hasko mishi ita ras a ciki.

Shigarta surarta yanayin tsayuwarta da yadda take wasa da yatsun hannunta da kuma sumanta dake zube a kafaɗunta sunyi masifar jirkita mishi jiki da jini da kwanya.

Tabbas jikinshi ne ya sanar mishi ana kallonshi.
Shiyasa yace.
"Wannan kallon fa?".
A zatonshi ma Aunty Rahma ce, ko Sitti dan yasan sun iya tsura mishi ido duk da sun san baya son kallo a rayuwarsa.

Ita kuwa Aysha, Koda tayi ƙasa da kanta digadigin sawunshi ta zubawa ido.

Shi kuwa Sheykh a hankali yaja wani nannauyan numfashi ya sauƙe a hankali.

A hankali ya ɗan juyo fuskarshi ya haɗe tare da cewa.
"Ke da izinin waye kika baro Tsinako kika zo nan?".

A hankali ta ɗan ɗago kanta, kana ta ɗan turo baki,
sannan ta gyara tsuyawarta, tare da cewa.
"Cemin akayi in zo".
Ta ƙareshe mgnar da yin taku biyu zuwa na uku da nufin zata koma gaban dreesing mirror ta ƙarisa shirinta.

Tana isowa gab dashi, da nufin zata wuce da sauri ta rumtse idanunta.
jin ya...




Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k a mako biyi huɗu ake gama Part one da two. Normal group Kuma 300 a mako takwas za'a gama Part one da two. Idan kina buƙatar special Group kimin TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta wannan number da nakeyin whatsApp da ita 09097853276. In kuma Normal group kikeso na ɗari ukun, shima kiyi min TRANSFER ta ASUSUNA na Jaiz din in baki da halin turowa ta banki to ki sayi katin Mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ki turo min ta WhatsApp 09097853276. BANA SON VTU KADA KIYI MIN TRANSFER'N DIN KATI BANA SO.


By
*GARKUWAR FULANI*
Yasa ƙafarshi ya ɗan taɗe mata ƙafa.
Da sauri ta rumtse idanunta tare dasa hannunta ta kamo nashi ta riƙe gam.
Haka yasa bata ida faɗuwar da ta kusa yiba.

Shi kuwa Sheykh fuskarshi ya tsuke tare da sa hannunshi ɗaya ya ɓamɓare hannunta dake ƙamƙame da nashi, kana ya ɗan ture ta.
Da sauri ta kuma riƙo hannunshi jin tayi gefe zata faɗi.
Wani irin ɗan ihun tsoro tasa, jin ta tafi shi kuma ya biyota,
da sauri ta rumtse idanunta jira kawai takeyi taji kanta ya raɗu da ƙasa, sabida tsoro yasa tama mance ta gefen gado take.
Jin ta faɗa kan tattausan katifar gadon Sittine yasa tayi wani irin dogon ajiyan zuciya.
Sai kuma ta buɗe idonta da sauri jin ya faɗo jikinta.
Da sauri ta kuma maida idon ta rufe ganin yadda sukeda kusanci.
Fuskarshi na kan fuskarta, hancinshi na gogan mata gemunshi na bisa haɓarta, goshinsa na kan nata, hakan yasa data buɗe idon nata sukayi kiciɓis da nashi idanun masu kwarjini.
Cikin jan numfashin tace.
"Wayyo Allah na nauyi ƙirjina zai fashe,
Babba da kai zaka fasamin ƙirji".
Ido ya zubawa lips ɗinta yana ganin yadda take motsasu, sai sheƙi sukeyi.
Haka nan yaji yana kusanto da bakinshi ga nata,
da sauri kuma ya maida kanshi tsakankanin wuyanta da kafaɗarta, ya cusa hancinshi cikin tattausan suman kanta da ya baje a kafaɗun nata,
wani irin sassanyan numfashi ya zuƙa tare da ƙamshin gashin kanta da jikinta,
wani irin Yar-yar yaji tsikar jikinshi na zubawa suna miƙewa tsaye.
hannunshi ya cusa tsakanin bayanta da katifar, ya ruggumeta gam-gam a jikinshi.

Shiru tayi tana jin yadda yaketa sunsunar wuyanta yana ƙara matseta tare dasa harshensa yana ɗan lasar fatan wuyan nata.
Tattausan sajenshi na gogar haɓarta, haka yasa tsikar jikinta zubawa.

A hankali ta buɗe idonta ta zubasu kan sajen nashi dake kwance lib-lib tamkar ciyawar dake samun yabanyar safe da yamma.
sai sheƙi yakeyi da ƙamshi,
da sauri ta ɗan maƙe kafaɗarta jin yadda ya manna hancinsa da bakinshi ya manna mata wani irin sihirtaccen kiss mai masifar ratsa jiki da zuciya.
Sosai take jin nauyinshi sabida duk jikinshi ya sake gaba ɗaya nauyinshi ya sakarmata.
Haka yasa tasa tattausan tafin hannunta ta tallabe gefe da gefen fuskarshi cikin jan numfashin tace.
"Ƙirjina kayi nauyi na tuba sauƙa".

Ƙara matseta yayi a jikinshi kana ya maida bakinshi cikin kunnenta cikin dafeffiyar murya yace.
"Waya ce ki jawoni jikin naki?
Kuma da izinin waya kika baro Tsinako kika zo nan?".
Cikin fidda nishi tace.
"Ni ba jawoka nayiba na riƙeka ne dan kar in faɗi.
Zuwa nan kuma ai Umaymah ce tace inzo".
ƙara manna ƙirjinshi da nata yayi sannan yace.
"Na'am wato Umaymah ce Allah yace kada ki fita in ba izinin ta?".
Cikin cinna ɗan bakinta sama tace.
"To ba Mamanka bace".
kanshi ya maido ya haɗe fuskarshi da tata, on expected taji yasa bakinshi kan nata.
Lips ɗin ta na ƙasa ya kama da fararen haƙoranshi na gaba ya ɗan ciza ka ɗan.
da sauri tayi zillo tare da buɗe bakinta zatayi ihu, hakan ya bashi damar lalumar tattausan harshenta yayi mata wani irin masifeffen tsotsa mai gigitarwa.

Ta kasa gane a zahirine ko a mafarki, wani irin kiss yake mata mai masifar ratsa jiki da zuciya.
Tana gaza nazari ko tunanin gane Sheykh wanne iriyar halittace shi a cikin halittun bani Adam komai nashi special ne.
Duk da babu wani ɗan adam daya taɓa sumbatarta tanada tabbacin ba ko wani namiji ya iya irin wannan zazzafan sumbatar Ustazan nan ba.

A hankali tasa tafin hannunta bisa wuyanshi yatsunta ta cusa cikin sumar ƙeyarshi mai sulɓi.
Shi kuwa Sheykh wani irin kanainaye harshenta yayi da nashi ya naɗe nata cikin nashi.

A hankali ya fara zaro nashi cikin nata, wanda haka yasa taji wani abu na mata.
Zir, zir, zir a cikin dukkan sasan jikinta, cikin baƙon yanayin daya cusata tayi wani irin juya harshenta cikin bakinshi ta lalumo harshenshi ta riƙe ƙam ta fara mishi wani irin shan tom-tom har tana bada wani sautin Douh.

Wani irin tsuma da karkarwa jikinshi ya farayi tamkar mazari, hannunshi ɗaya ya zaro ya tallabo kanta da kyau.

Dai-dai lokacin kuma Sitti ta fito daga falon Jadda tazo falonta, nan ta samu su Goggo Mairo duk sun tafi sai Ibrahim da Safiyyah da ƙannen iyayensu.
So bayan sun gaisa da Ibrahim ne take tambayar.
"Ibrahima ina Jazlaan ban ganshi ba tunda kukazo, bai shigoba, ga can jadda ma yace kuje yana nemanku".
Shi dai Ibrahim murmushi kawai yayi yaci gaba da wasa da yaronshi.
Safiyyah ce tace.
"Yana bedroom ɗinki tun ɗazu ma shi muke jira duk kowa ya tafi saura mu.
Su Azeema ma sun tafi da abokan Ya Haroon".
Da sauri ta miƙe ta nufi special Side ɗinta kai saye bakin ƙofar Bedroom ɗinta ta nufa.

Tana isa tasa hannu tana ƙoƙarin buɗewa tare da cewa.
"Jazlaan! Jazlaan!! Jazlaan!!!".
Kamar a wata duniya ko cikin mafarki haka yake jiyo muryar Sitti.
cikin sauyawar tsari ya fara ƙoƙarin janye harshenshi daga gareta, amman ina ta riƙe gam. Cikin sauri ya buɗe idonshi ya zubasu kan fuskarta,
wani irin sanyi yaji yana ratsa zuciyarshi.
Jin motsin turo ƙofarne ya sashi yunƙurawa da ƙarfi ya janye harshenshi tare da janye jikinshi ya miƙe tsaye cikin tsananin kunyar kada Sitti ta shigo ta sameshi a wannan yanayin.
Al'kyabbar ajikinshi ya fara bazawa yana buɗata yana gyarawa.
Ita kuwa Aysha jin yadda ya zare harshenshi da yadda ya miƙene yasata dawowa cikin haiyacinta daga gigitar da ya sakata.
Jiki na rawa ta mike zaune tare dasa tafin hannunta tana goge damshin bakinta cikin tarin azabebiyar kunyarsa.

Sitti kuwa tana shigowa ganinshi tsaye yana murmushi yasata isowa gareshi ruggumeshi tayi cikin tsananin jin daɗi tace.
"Masha Allah. Marhababika ya Habibi, ana Uhubbuk".
Murmushi yayi tare da janye jikinshi gareta kana yace.
"Ana uh hibbuki hubban azeem ya Sitti".
Hannunta tasa ta shafa kansa fuska cike da annurin ganin jika mafi soyuwa a gareta tace.
"Jazlaan me zan kawo maka? me zakaci? me kake da buƙata?".
Murmushi ya kumayi kana ya zauna bisa kujerar sarautar dage gefenshi tare da cewa.
"Sitti na samu komai".
Sai kuma ya ɗan kalli Aysha ta wutsiyar idonshi.
Har yanzu jikinta na tsuma.
Safiyyah ce ta shigo da sallama tare da cewa.
"Ya Sheykh mu tafi darefa nayi".
Kai ya gyaɗa mata alamar to.
Ita kuwa juyowa tayi ta kalli Aysha tare da cewa.
"Kin gama shiryawa ko".
Itama kai ta gyaɗa mata.
har ta buɗi baki zata kuma yin mgna sai tayi shiru jin Sitti na cewa.
"Yauwa to kuzo taso muje Jadda na son ganinku mu tafi ko".
Ta faɗa tana miƙewa tsaye.
Safiyyah ce ta fara binta a baya kana Sheykh.
Har sunje bakin ƙofar fita ya ɗan juyo ya kalleta a fakaice.
Mayafinta take yafawa tare da biyo bayansu.
A falon suka samu Ibrahim, nan ya miƙe yabi bayansu.

Kai tsaye Side ɗin Jadda suka nufa.

Shi kaɗai yake zaune a falon nashi dan ya bar fada yace zai gana da jikokinsa.

Cikin murmushi mai cike da kamala da dattaku, yake kallonsu tare da cewa.
"Lale marhabin da jikokin Sitti da Jadda."
Ya ƙare mgnar yana miƙawa Sheykh da Ibrahim hannunshi, Sheykh ne ya riƙe hannunshi na dama kana Ibrahim ya riƙe na hagu suka zauna suka sashi a tsakiya.
Safiyyah ce ta matso gefen mijinta ta zauna.
Ita kuwa Aysha a hankali ta rusuna zata zauna a gefe, da sauri Sitti tasa hannunta ta kamo nata tare da cewa.
"Matso nan kusa zauna kusa da mijinki shine farin cikinmu.
Yau gamu Allah ya nuna mana matar Sheykh."
Ta ƙare mgnar tana ajiyeta kusa da Sheykh har jikinsu na gogar na juna.

Murmushi mai cike da so da tsammani da zato Jadda yayi tare da cewa.
"Amaryar Sheykh jikar Sitti da Jadda".
Cikin murmushin tace.
"Allah rene Jadda Allah nɓeddu sabbugo".
Wani irin murmushi mai cike da masha hurin daɗi Jadda da Sitti sukayi tare da haɗa baki wurin cewa.
"Amin Amin, tare dake da mijinki".
Cikin tura baki Safiyyah tace.
"Ikon Allah wato banda mu".
Da sauri Sitti tace.
"Wa lakum".
murmushi sukayi dukansu, kana Jadda yasa tafin hannunshi bisa tsakiyar kan Sheykh da Ibrahim tare da cewa.
"Wannan kawuna biyu duk masu ɗaukan rawanin girmane, hakama na ukunku Haroona shima akwai nauyin rawanin bisa kansa.
Ibrahim da Haroon bani da fargaba a kanku.
Amman shi Muhammad Jabeer akwai ruɗu a al'amarinsa akwai firgitarwa, yana tsakiyar Magauta.
Sun kuma rigayemu sanin rawani na bisa kanshi.
Shiyasa sukeyi mishi zagon ƙasa tun yana ƙaramin yaro."
Shiru sukayi dukansu suna jin zantu kanshi, shi kuwa ɗan tsagaitawa yayi kana ya kalli Aysha yafi tota yayi da hannu alamun ta ƙara matsoshi.
A hankali ta rarrafa ta matsoshi, kanta ya dafa kana yace.
"Wata rana kina iya zama a matsayin da Gimbiya Aminatu take a yau.
Ban saniba ko kafin lokacin ina raye, ko na amsa kiran Ubangiji na.
Ga Muhammad Jabeer mijinki ne, kuma uban ƴaƴan kine, in sha Allah, sannan GARKUWArki. Dan Allah Aysha na baki amanarsa ki zame mishi GARKUWA ki kula da damuwarsa tun kan ta riskeshi.
Yanada nauyi a cikin zuciyarshi mafataucine a faɗin duniya yana neman wani abu nasa mafi, ƙololuwar daraja ga ɗan adam daya ɓace matsa tsowon shekaru masu yawa, a hasashen da akayi mana zaki iya haska mishi hanyar da zaibi ya ganoshi".
Kai kawai take gyaɗa Dattijan tanajin hawaye na cika mata ido.
Da kalmarshi ta ko yana raye ko ya amsa kiran Ubangiji.
Shi kuwa Sheykh lokaci ɗaya yanayin fuskarshi ta sauya cikin muryar dake nuna dafin zafi da tiririn da ke cikin zuciyarsa yace.
"Uhummm Jadda taimakon Ubangiji na mahaliccina masanin zahiri da baɗini kawai nake nema, shi zai haskamin hanya in riski haskena.
Zanyi ta roƙonshi kuma da fatan ya baku aron rai da lfy har sanda burinmu zai cika.
Ina addu'o'in Allah ya bawa magautanmu lfy da rai har zuwa lokacin da gsky zatayi halinta".
Tuni Safiyyah da Sitti sun fara sakin Shessheƙan kuka.
Wanda sam Aysha ta gaza gane dalilinsa kalaman Jadda da Sheykh kuwa sunyi mata ɗaurin talala a ƙoƙolwarta, ta gaza gane bakin zaren haka yasa ta tattare yawun bakinta cikin kukan da taji yana son kubce mata tace.
"In sha Allah Jadda zan kula da amanarka iyakar iyawata.
Zan kuma tayashi da addu'a koda bana yankin da yake.
Tabbas watan-wata-rana gsky zatayi halinta".
Sai ta kuma kalli Sitti da Safiyyah tare da cewa.
"Sitti kiyi haƙuri du ban san zafin me kikeji a zuciyarki ba, amman kukanki yamin kama da kukan uwar data rasa ɗanta, kiyi haƙuri".
Da sauri Sheykh ya miƙe ya fita, hakama Ibrahim.

Safiyyah kuwa hawayenta ta share kana ta kamo hannun Aysha tace.
"Jadda mu zamu tafi kada dare yayi mana".
A hankali Yace.
"Bazaku tsaya kuyi sallan la'asar ba".
Sitti ce tace.
"Sai dai suyi a hanya naga yadda Sheykh ya fita bazai dawo cikiba".
Kai ya jinjina kana yace.
"To Allah ya kaiku lfy ya tsare hanya.
Aysha Allah yayiwa aurenku al'barka".
Kusan a tare sukace Amin.
Kana suka miƙe suka fita.
Shi kuwa Jadda ya kira Sarkin dogarai ya bashi umarnin a haɗa motar dogarai hudu suyiwa jikokinsa rakiya.

Biyu a gaba biyu a baya tasu Sheykh a tsakiya.

Wacce Sheykh da Aysha suna baya.
Ibrahim da Safiyyah suna gaba, Ibrahim ke jan motar.

A haka suka bar masarautar Jalaluddin suka nufi jihar Tsinako.


Tafiyar mai yar tazara ce.

Shiru cikin motar Ba maiyin mgn, Sai sautin Radio da suka kunna.

Jingine yake da kujerar yayi shiru, idonshi a lumshe sai lips ɗin shi da yake motsawa alamun yana tasbihi kamar ko yaushe.

Ita kuwa Aysha sosai ta faɗa duniyar nazari.

Ibrahim kuwa ya maida hankali kan tuƙin.

Safiyyah kuwa bacci nema ya saceta a motar.

A ƙalla tafiyar awa ɗaya sukayi, kana suka fita jiharsu Jadda suka fara tafiya cikin dajin jiharsu Haroon.



A hankali ya buɗe idonshi.
Jin Ibrahim na cewa.
"Tab lallai Abban Haroon da Sarki Ahmadu suna ji da wannan walimar da za'ayi.
Kajifa duk gidajen rediyon Tsinako, gaiyatar walimar akeyi ba ƙaƙƙautawa kaji ko zasu sakeyi."

Meda kunnuwansu sukayi kan abinda ake faɗin.
"A madadin iyalan mai girma sarki Ahmadu suna farin cikin gaiyatar walimar auren. jikokinkin mai Martaba Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗo da matarsa Aysha Aliyu Garkuwa.
Da kuma Haroon Abubakar Ahmadu. Da amaryarsa.
Jannart Umar Jalaluddin
Za'ayi walimar ne a wurin babban filin taron al'ummar musulmi na Tsinako, ana gaiyatar ɗaukacin al'ummar musulmai wurin walimar wanda za'ayi yau misalin ƙarfe takwas na dare zuwa goma da izinin ubangiji, in da sanan malamin nan Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda shima angone kuma shi zaiyi nasiha ga mauratan.
Saƙon gayyata daga Mai martaba Sarkin Ahmadu. Allah ya bada ikon zuwa Amin...".

Gajeren tsaki Sheykh ya ɗan ja tare da cewa.
"Kai tsoffin nan fa sunada matsala, ji wani dogon sharhi iya sunayemmu ya ishi a gunduri mai sauraro".

Murmushi Ibrahim yayi tare da cewa.
"Kuma wlh tallatar tayi armashi."
"Sosai ma kuwa". Safiyyah tace, cikin jin daɗi.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
"Tsaya nan garin muyi salla la'asar tana gab da wucewa".
To Ibrahim yace, kana sukaci ga da tafiya.
Tafiya kaɗan sukayi suka isa.
Wani masallaci mai kyau wanda dama dan matafiya akayishi.
Gefen mata da ban gefen maza da ban.

Bayan duk sunyi parking ne fadawan, suka fara fitowa.
Da sauri sukazo suka buɗe musu mota.
Ibrahim ne ya fara fita kana Safiyyah.
Juyowa yayi ya ɗan kalleta ganin ta gyara zamanta ta kishin giɗa tare da lumshe idanunta.
fuska ya ɗan yamutsa kana yace.
"Fitowa zakiyi muje muyi salla. Ba gyara zama zakiyi ba."
Shiru batayi mgna ba, haka yasashi haɗe fuska ya kuma maimaita mgnar.
Fuska ta kwaɓe tare da cewa.
"Ni nayi".
Idonshi ya zubawa fuskarta na daƙiƙu biyar.
Uhummm yace kana ya sa ƙafarshi ya fita.

Bayan sunyi sallan ne kana suka dawo sukaci gaba da tafiya.


Ƙarfe biyar dai-dai suna cikin masarautarsu Haroon.

Suna shiga fadawan suka wuce masauƙinsu dan sai gobe zasu koma.
Su kuwa Sheykh da Ibrahim Side ɗin Abban Haroon Suka nufa sabida kiransu da yayi a woya.

Aysha da Safiyyah kuwa Side ɗin Umaymah suka wuce.
Suna Shiga Hibba tace.
"O oyoyo My Aunty's Umaymah gasu Aunty Aysha sun iso".
Da sauri Umaymah da Aunty Hafsat da Rahma suka fito.
Cikin kula Umaymah tace.
"Allah sarki Ɗiyata sukayi muku wayo suka dawo a jirgi ku suka barku da gajiyar mota ko".
Murmushi tayi tare da sunkuyar da kai tace.
"Ina wuni Umaymah Aunty Hafsat barka da yamma".
Murmushi sukayi suka amsa cike da kulawa.
Aunty Rahma ce tace.
"Yaseen kuwa Umaymah ba wayo mukayi musuba Ibrahim ne yace mu barsu zasu dawo tare tun randa mukaje hutasa bayi shirin dawowa dasu a jirgiba".
Ta ƙare mgnar tana kallon Aunty Juwairiyya da Jazrah da suka shigo yanzu.
"A Safiyyah sai yanzu kuka iso".
Jazrah ta faɗa tana ƙin kallon inda Aysha take.

"Eh ba kun musu wayo ba".
Aunty Hafsat ta faɗa.

Murmushi suka ɗan yi.
Cikin kula Umaymah tace.
"To Safiyyah yanzu dai kuje ku ɗan huta, kafin ku fara shirin zuwa walimar."
To tace kana suka nufi ɗakin Hibba dan yau Side ɗin Umaymah cike yake maƙil da taron al'ummar Annabi.

Suna shiga Aysha ta wuce Bathroom da hand bang nata a hannunta.
Meda ƙofar tayi ta rufe

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment