Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki".
Cikin sanyi tace.
"To jiki kam dai babu daɗi.
Sai dai godiyar Allah".
Cikin sanyi tace.
"Dukkan tsanani yana tare da sauƙin.
Ya iyayenta sunji ko?".
Kai ta gyaɗa alamun eh.
Juwairiyya ce taje falon ta kawo mata ruwa da abinci.
A hankali tace.
"Juwairiyya ajiye abin cinnan bazai ciwuba".

Dai-dai lokacin Hajia Mama ta shigo da Affan yana cikin kiɗima.

Ganin Umaymah ne yasa suka zaune kusa da ita tare da cewa.
"Ya jikin nata".

"Alhamdulillah ta samu tayi bacci."
Umaymah ta basu amsa.
Cikin kula Hajia Mama tace.
"Sannunki da zuwa, ya hanya".
Yauwa sannu Alhamdulillah tace.
Hibba ce ta dawo tacewa Umaymah kafin ta fitama ya tafi.
To kawai tace.


Daga nan suka zauna suna al'hinin abin.

Har azahar tayi nan suka watse kowa taje tayi salla.
Ita Umaymah a ɗakin Aysha tayi salla.

Bayan sunyi sallan ne Ummi ta kawo musu abinci suka ɗan ci.

A nan suka zauna Ummi da Umaymah a ɗakin Aysha.
Juwairiyya kuma taja Hibba suka tafi dan yin girkin dare.

Haka suka zauna har la'asar bata tashiba.

Sheykh kuwa sai ƙarfe biyar na yamma ya dawo gida daga asibitinshi.

Nasa falone ya wuce Side ɗinsa kai tsaye.


Biyar da miti bakwai dai-dai ta farka daga nannauyan baccin azabar.
Da sauri Umaymah tayi kanta.
Ganin tana ƙoƙarin tashine yasa Umaymah taimaka mata.
Cikin disashewar muryar tace.
"Lah Umaymah yaushe kikazo? Sannu da zuwa".
Cikin tausaya mata tace.
"Sannu Aysha ai ke za'a cewa sannu. Ya jikin naki".
Cikin sanyi tace Alhamdulillah".

Sai kuma ta zuro ƙafafuwan ƙasa tare da cewa.
"Umaymah zanyi salla zanyi wonka".
To tace da sauri kana ta juya zata shiga bathroom ɗin.
Da sauri Ummi tace bari in haɗa mata ruwan wonka."

Umaymah kuwa kamota tayi ta tsayar da ita.
Dai-dai lokacin Ummi ta fito hannun ta zubawa ido cikin sanyi tace.
"Ya naga kamar hannun ya ƙara kumɓura ne?".
Kallon hannun sukayi a tare.
Cikin sanyi tace.
"Eh kamar ya ƙara kumɓura".
Umaymah ce ta ɗan kalli hannun kana tace.
"Je kiyi wonka ki fito kizo kiyi salla kici abinci, in baki mgnin da nazo miki dashi."

To tace kana ta nufi Bathroom ɗin tana cewa.
"Bana iya gogo sosa a jikina sai sabulu kawai.
Shiyasa nakeji kamar ba wonka nakeyi ba".
Cikin tausayawa Ummi tace.
"Allah sarki in kin samu lfy dai shike nan".

A haka ta shiga bathroom ɗin yau ko sabulun bata iya gogashi da kyauba.

Ita kuma Ummi kaya ta fito mata dashi kamar kullum.

Ita kuwa Umaymah Dinning area taje.
Ta ɗauko Foodflaks ɗin da plate ta dawo nan.

A hankali ta fito bathroom ɗin.

Cikin ɗaga hannun sama ta kalli rigar da aka fito mata dashi a hankali tace.
"Ummi bazan iya sashi ba, matsastsene a bani mai faɗi".

To Ummi tace ta sauya mata wani.
Mai faɗin ita kuwa dogon wondon dake kan gado ta ɗauka ta koma bathroom ta saka da kyar sannan ta fito.

Koda Ummi ta bata rigar sai ta gaza sata.
Ido cike da hawaye tace.
"Ummi samun hannun rigar a hannu mai ciwon a hankali kada ya taɓa shi, sai kin buɗashi da hannu biyu.
Cikin sanyi Umaymah tace.
"Bakisa bra ɗinba".

Kanta ta sunkuyar tare da cewa.
"Bazan iyaba".
Shiru Umaymah tayi tana tunanin dole jinyar hannu sai da mataimaki.
Ita da Ummi kuma surkaine Hibba ƙaramace.
Shiru dai tayi tana nazari.
Bayan Ummi ta taimaka mata tasa rigar ne.
Ta saka hijabi tayi sallan a daddafe da taimakon lafiyayyan hannun.
Tana idarwa Umaymah tasa mata abinci a plate kasan cewar tuwone da miyar ganye da ɗan tsami.
Sai ya zama gaba ɗaya a kaikaice take sa spoon ɗin da niyar gutsuro tuwon.
Kuma taji tana son cin miyar.
Da kyar ta gutsuro gaya ta ɗan ɗebi miya ta ɗaya zata kaishi bakinta kenan ya faɗi a jikinta.

A hankali ta kallesu cikin sanyi tace.
"Umaymah a bani tea kawai bazan iya cin wannan ba, zai tazubewa."

Da sauri Ummi ta gyara zama tare da cewa.
"To matso in baki".
Ɗan gajeren murmushi tayi cikin jin kunya tace.
"A a bari in sake gwadawa to".

Dai-dai lokacin Sheykh da Umaymah ta kirashi a waya ya shigo yanata buɗe al'kyabbar jikinshi gudun kada a iya ganin tudun abinda yake ɓoyewa.

A bakin ƙofar ya tsaya tare da yin sallama.
Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace.
"Shigo".

A hankali ya tura ƙofar ya shigo.
Tunda tazo gidan tsawon watanni biyu kenan yanzu bai taɓa tako ƙafarsa nan ba sai yanzu.

Ta gefen ido ya kalleta ta sake ɗaukan loma a karo na uku kafin ta kaishi bakinta ya ɓare.
Ture plate ɗin tayi tare da cewa.
"Bana iya cin abu da hagu gwara tea zan iya kafa kofin insha wani wani ya ɗan zube".
Ta ƙarishe mgnar tana shere hawayen da suka zuba mata.

A hankali Ummi taja flaks ta fara haɗa mata tea.
Umaymah kuwa.
Gefenta kan Bedside drower'n ta nuna mishi tare da cewa.
"Zauna".
fuska ya ɗan kauda kana ya zauna.
A hankali tace.
"Me zamuyi kan hannun yarinyar nanne?".
Cikin jin haushi yace.
"Sai abinda su Lamiɗo sukace ai.
Ni Ko nayi mgna sai sun musamin ya rigada sun maidani kamar sa'ansu, bani da ancin mgn kan komai nawa sai yadda suka tsara min in naƙi bin unarninsu keda Abba kuyi faɗa, to ya zanyi?".
Murmushi Ummi tayi ganin yadda yayi mgnar a tsare kamar shine babba a kansu ba suba wai sun ɗauke shi sa'ansu.
Ita kuwa Umaymah cikin sanyi tace.
"Kaga bata iya ko cin abinci tana bukatar kulawa ta musamman.
Wonka ma wuya yake bata haka al'wala ko kaya sai an saka mata".
A hankali yace.
"Toh lallai kam Allah ya baku ladan jinya".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Amin". A ranta kuma tace.
"Zanyi mgninka".

Ganin tayi shiru ne ya sashi miƙewa tare da cewa.
"Allah ya sauwaƙa kana ya fita."
Yana mai jin zafin katsalandar dasu Lamiɗo ke mishi a kan lamuran rayuwarshi, komai nashi sai sun saka mishi baki. Yace kar asa mgnin amman dan rainin wayo sunce dole sai an saka.

Su Umaymah kuwa nan suka zauna har akayi sallan magriba.
Su Jalal Jamil Affan sukazo suka ci abinci aka ɗanyi hira dasu.

Har zuwa ƙarfe goma na dare hannun shiru ba ciwon sosai.

Haka kowa ya shiga yana cemata saida safe Allah ƙara sauƙin.
Umaymah tace Ummi ta tafi da Hibba ɗakinta ita zasu kwana tare.

Haka kuwa akayi, har sun fara bacci.

Habawa sha ɗaya dai-dai,
Ciwo yace salamu alaikum.
Tashin hankali iya tashin hankali Umaymah ta ganshi a ranan.
Domin har gabanin asuba basu rintsaba kamar dai yadda ta kwana jiya da Ummi abinma har yafi haka yau.
Sau biyar Umaymah na kiran layukanshi duka basa shiga.
Kuma Aysha guduwa kawai take nufa.
Haka yasa dole tai ta riƙe ta.

Asuba na ƙaratowa tayi bacci kamar na jiya.

Sai da akayi sallan Umaymah ta tada ita.
Tayi salla lfy tasha tea.
ta koma bacci rana na fitowa ciwo ya dawo.

Gaba ɗayansu sun gigice sun tsorita da lamarin Umaymah ta tura Ummi taje ta gayawa Lamiɗo yazo yaga yadda take.

Hibba kuwa da Saratu sun kasa yin aikin da aka sasu sai kuka.

Hannun kuma yau yayi biyun na jiya.
Idanunta sun kaɗa sunyi jazir.
tana zaune kan kujera Umaymah na tsaye gefenta gudun kadda ta arce.
Ta ɗaura hannun a kai tana kuka iya kuka, kukan azaba haɗe da salati.
A haka Sheykh ya shigo ya samesu.
Cikin takaici Umaymah ta juya ta nufi falon Ayshan tana kallonshi tana cewa.
"Gata ka barta kada ka kula da jinyarta da haƙƙinta ne Allah ya rataya a kan wuyanka ai ka fini sani.
Ka sani kana take sani".
Ta ƙarishe mgnar tana zubda hawaye sabida duk wanda yaji kukan da Aysha keyi yasan na wahala ne.

Ita kuwa Aysha da sauri ta miƙe ta kife kanta jikin gini tana mai ci gaba da kuka.
Jamil, Jalal, Affan, sunata yi mata sannu.


A hankali yabi bayan Umaymah da kallo tabbas ranta yayi matuƙar ɓaci, ga tashin hankali ga rashin bacci.

A hankali ya isa inda take.
Hannunshi yasa ya kamo nata. Da sauri ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi, cikin zubda zafafan hawaye tare da cewa.
"Yah Sheykh zafi, hannuna zai tsinke."
Wani irin masifeffen rauni da tausayinta ne yaji sun rufeshi, kanshi ya juya cikin sanyi, yaja hannuntan.
Suka nufi ɗakishi.
Ita dai binshi a baya takeyi tana tafiya kamar a sama takejin kanta.
Kai tsaye har bedroom ya wuce da ita.
Kan gadonshi ya ajiyeta yanajin kukanta na hawa kanshi.

Bakin gadon ya zauna ya bata baya tare da cewa.
"Ki kwanta kiyi addu'a zakiji sauƙi."

Ba jinshi takeyi ba bare ta gane abinda yake nufi.
Da sauri ta yunƙura zata sauƙa.
Juyowa yayi ya kamata ya ajiyeta kusa dashi kana ya juyo suna fuskantar juna.

Cikin kuka ta faɗa jikinshi tana cewa.
"Umaymah hannu zai tsinke.
Zafi zai kasheni".
A hankali ya ruggumeta tare dasa hannunshi ya kamo hannun dake ciwon.
Da sauri tayi tsalle zata zille hakan ne yasa ya ƙara ruggumeta gama ya haɗa jikinsu wuri ɗaya.
cikin sanyi ya fara mata karatu a kunne yana hura mata iskar bakinshi kan hannun

Ajiyan zuciya mai ƙarfi da numfarfashi ta fara sauƙewa da ƙarfi-ƙarfi.

Umaymah kuwa jin shirune yasa, ta nufo Side ɗinsa.
Ganin baya falone.
Tace.
"To ina suke ina ya kaita?".
Ta ƙarishe mgnar tana tura ƙofar Bedroom.

Tana tura ƙofar sai kuma tayi sauri taja da baya sabida hangosu da tayi yana konce lib yayi rigingine ya ɗan jingina da allon kan gadon.
Kana ita kuma ya kontar da ita kan jikinshi, ya ɗaura kanta bisa ƙirjinshi hannunshi na kan...!












Jinyar Sheykh ta musamman ce. To ya zata kaya ne in ɗan gidan ba'ana yazo. Hege Sarkin baka wa yakewa aikin.



By

*GARKUWAR FULANI*
Cikin tsuke fuskarsa da muryar dake nuna zafin abinda ke zuciyarshi yace.
"Ummi in ya fito kiyi mishi jagora zuwa wurin sarkin ƙofa ki nunashi kada a sake barin yazo ko kusa da katangar masarautar Joɗa ne, a korashi ya bar jihar Ɓadamaya."

Da sauri Ummi tace. "Toh".
Kana tayi gaba tare da cewa.
"Mu tafi".
Da sauri Barun yabi bayanta.

A can falon Sheykh kuwa komawa yayi ya zauna gaban Bappa cikin sanyi yace.
"Bappa kayi haƙuri, ka gafarceni, bisa korarshi da nayi.
Wannan sunada manufar data kawoshi, ni zan ji da ciwon hannunta, in sha Allah zata samu lfy. Ka kwantar da hankalinka."

Ido Aysha ta zuba mishi cike da mamakin ta ina ta yaya ya gane meke tafe da Barun har ya gane sunada wata manufa, ta yaya ya gano kuramen bakin da Barun ya karanta mata, ta yaya yayi musu wasali har ya basu cikekkiyar jimla ya karancesu da fassararsu, meya sani a kanta.

Hakama Bappan kallon Mamaki yakeyi mishi amman sai ya gyara zamanshi tare da cewa.
"Ba komai Muhammad Allah ya bamu sa'a ya kuma bata lfy".

Amin Amin yace shida Umaymah.

Al'amin ne ya ɗan gyara zama tare da cewa.
"To Allah yasa a dace. Amman ko za'a gwada asibiti ne?."
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Kada ka damu, in sha Allah ba damuwa".
Kai ya ɗan gyaɗa cikin gamsuwa.
A hankali Umaymah ta miƙe ta fita.

Shi kuwa Sheykh Aysha ya kalla tare da cewa.
"Tashi ki barsu suci abinci mana".
Da sauri Bappa da Al'amin sukayi mgna kusan a tare sukace.
"Alhamdulillah mun ƙoshi".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Al'ameen da kyau kana a hankali yace.
"Ba'a zuwa masarautar Joɗa a fita ba'aci komaiba".
Murmushi mai cike da gamsuwa Bappa yayi kana yace.
"Eh Alhamdulillah munci a wurin Lamiɗo ai".
Kanshi ya gyaɗa cikin gamsuwa da hakan yace.
"Toh Bappa".
Cikin sanyi ita kuma Aysha tace.
"Ya Al'amin bani zanci".
Murmushi Al'amin yayi kana ya jawo Foodflaks ɗin,
a plate ya zuba mata Couscous da biyar hanta.
gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau itama gyara zamanta tayi.
Bappa kuwa Murmushi yayi yana kallonsu.

Shi kuwa Sheykh ido ya zuba musu zaiga dai iya gudun ruwansu duk da zuciyarshi ta gama gano mishi nasabarsu.

Shi kuwa Al'ameen. A hankali yasa spoon ya ɗan ɗibo, kana ya nufi bakinta da spoon ɗin tare da cewa.
"Ha, buɗe bakin".

To tace kana ta buɗe bakin ya saka mata.
lumshe idonta tayi tare da tauna abincin dan ya mata daɗi.
Sake dibowa yayi ya bata, still ta buɗe baki yasa mata.

Cire kanshi yayi a kansu, ya maida dubanshi kan Bappa dake mishi mgna.
Umaymah da Ummi ne suka shigo a tare ita Ummi cewa.
Sheykh tayi an fidda Barun.

Ita kuwa Umaymah ƙwaryar fura da nono ta kawo musu.

Murmushi sukayi ganin yadda Aysha ta zage tana cin abinci.
Shi kuwa Al'amin ya dage yana bata.
"Ya Al'amin zan sha ruwa".
Tace mishi tana taunar sokar naman da yasa mata a baki.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli Umaymah tare da cewa.
"Allah rene a sammin ruwa in bata".

To Umaymah tace ta miƙo mishi ruwa.
Tana kallon kamanninshi da Aysha ba sai an gaya maka cewar ɗan uwanta jininta bane.
Bata ruwan yayi har baki.
Tasha sosai.
Kana ya kalleta tare da cewa.
"In ƙara miki abincin ne?".
Kai ta gyaɗa mishi.
murmushi yayi tare da cewa.
"Bubbuga rumbun Abboi".
Murmushi tayi itama tana mai share hawayen da suka silalo mata.
Ƙara mata yayi tare da ci gaba da bata.
Sosai kuwa taci tayi haniƙan.
Sheykh kuwa da wutsiyar idonshi yake kallon dukkan motsinsu.
Bayan tayi gyatsa ne, Ummi ta matsar da kwanukan.
Babu yadda Sheykh da Umaymah basuyiba, amman Al'amin da Bappa sunƙi suci abinci.

Kiran sallan azahar ne,
Yasa duk suka miƙe.

Cikin sanyi Al'amin ya kalli ogogon hannunshi da yaketa sheƙi yace.
"Bappa muyi salla mu tafi kada lokacin ya ƙure mana".
Cikin kula Umaymah tace.
"Ba kwana zamuyi ba".
Murmushi Bappa yayi tare da cewa.
"A'a zamu koma tunda jiki da sauƙin gata taci ta ƙoshi tana hira."
A hankali Ummi tace.
"Eh ai dama haka takeyi, anjima kuma in ciwon ya tashi zakace kamar zata shiɗe, sai an mata tofi take ɗan samun sauƙin".
Murmushi Al'amin yayi tare da kallon Sheykh cikin nitsuwa da gogewar cikar wayewar dake nuni ba makiyayin daji bane yace.
"Sheykh ka samu sabuwar wayar hannu, kenan tunda sai kayi tofi akejin sauki.
Dan Allah duk inda kake ta kasance a nan a ƙara kulan mana da Boɗɗin Abbai".
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"In Sha Allah".
Cikin karrama Sheykh ya nuna musu wata ƙofar dake gefen ɗakinshi yace.
"Ga wuri kuyi al'wala mu tafi masallacin".
kai Al'amin ya gyaɗa kana yace.
"Bappa je kayi al'wala kazo mu tafi.
Cikin nitsuwa Bappa yace da al'wala ta".
Shima Al'amin gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"Nima inada al'wala".

Cikin gamsuwa Sheykh yace.
"To bisimilla muje nima da al'wala".
To sukace kana duk suka nufi babban falon.

Suna isa tsakiyar falon. Al'amin ya ɗan tsaya tare da cewa.
"Parvina zo".
Da sauri ta ƙaraso gabanshi.
Shiru sukayi jin Al'amin ya juya harshe zuwa wani Yaren ba larabciba ba Turanciba ba hausaba ba fillanciba.

Mgna yakeyi riƙe da hannunta.
Ita kuwa Aysha kai taketa gyaɗa mishi ido cike da kwalla.
Hannunshi yasa ya share mata hawayen kana yasa hannunshi ya shafa kanta tare da juyawa ya fita.
Ita kuwa Aysha cikin sanyi tace.
"Bappa dan Allah a kawo min Junainah".
Kanshi ya gyaɗa kana shima ya fita.
Binsu a baya Sheykh yayi.

Ita kuwa hannunta mai lfyar tasa ta share siraran hawayen da suka zubo mata.
Kana ta juya ta nufi ɗakinta.
Ummi da Umaymah kuwa kallon juna sukayi suma suka wuce ɗakin su.

Bayan an idar da sallan ne, Sheykh da kanshi ya ɗauki su Bappa ya kaisu tasha kamar yadda sukace.

Bayan ya kaisune. Yayi musu fatan isa lfy ne, yaja motarsa kamar ya tafi.
Ya koma can baya ya ajiye motar kana ya kira Ado drevernshi da yake cikin but ya fito.
Sannan yace.
"Bisu".

Da sauri Ado yabi bayansu.

Shi kuma yayi gida.

A hankali Ado yake binsu.
Ga mamakinshi sai yaga sun tari taxi sun shiga.
Shima taxi ya tsaida ya shiga,
tare da cewa.
"Bisu duk inda suka nufa."

To yace, kana yabi bayansu kai tsaye international airport Ɓadamaya suka shiga.
Suna shiga.

Kuwa suka fito. Suka biya mai taxi ɗin da kuɗin ma da bana ƙasar Nigeria bane kuɗin ƙasar Cameroon ne.
Cikin sanyi Al'amin yace.
"Yi haƙuri bamu da canji ne, kaje wurin yan canji za'a canza maka su zuwa Naira".
Cikin jin daɗi mai taxi ɗin ya tafi.

Shima Ado ya sallami nasa mai taxi ɗin.

Kana yabi bayansu tafiya kaɗan sukayi yaga wasu mutane a ƙalla su shida, sunbi bayansu duk suna cikin shigar sut.

Al'amin dake gefen Bappa ne ya miƙo wa ɗaya na kusa dashi hannu.
Wayar iPhone ƙirar wannan shekarar ya miƙa mishi.
Sai kuma system ɗinshi.
Daga nan kan tsaye sukaje suka shiga jirgi.
Dole Ado ya rakasu da ido.

Su kuma jirgi ya ɗaga dasu.

Tun kafin Ado ya koma gida ya kira Sheykh ya labarta mishi.
Murmushi Yayi jin abinda Ado yace mishi. Kai ya jinjina tare da danna wasu ababe a wayarsa.
" ?+? ".
Murmushi yayi kana ya jefa woyar a al'jihunsa.

Bai shiga gidaba sai bayan sallan isha'i.

Yana shiga kuwa ya samu su Ummi a falo.
Aysha da hannunta ya ɗan fara zogin.
ta bishi da ido.
ganin kamar bazata tashi bane yasa.
"Umaymah cewa tashi kije ya miki tofin."

To tace kana ta miƙe, ta nufi Side ɗin nashi.
Babu kowa a falon sai dai ta hango shigarsa ɗakin.
A hankali tabi bayanshi tura ƙofar Bedroom tayi tare da sallama.
Kana ta kutsa kai cikin ɗakin.
A hankali ta isa tsakiyar ɗakin babu kowa.
cikin sanyi tace.
"Ina jiranka dan Allah kamin tofin".
Shiru taji ba mgna ba kuma motsin komai a ɗakin.

Cikin sanyi ta ɗan fara hurawa hannunta iskan bakinta.
Tana kallon ƙofar Bathroom ɗin.

A hankali kuma ta miƙe tana cewa.
"Shyyyuuu hahjjyyyyyyyt".
Sai kuma ta matso bakin ƙofar Bathroom ɗin da niyar ta bubbuga ƙofar.
Tana sa hannu bisa ƙofar ta buɗu.
Da sauri ta ɗan ja da baya.
A hankali tace.
"Yi haƙuri bansan a buɗe yakeba".
Still ba mgn kuma ba motsin ruwa.
Hakane yasa ta ɗan leƙa.
Ganin ba kowane a ciki ta kutsa kai ciki tare da cewa.
"To ina kake ina ka shiga".
Shiru wayam ba kowa, komai na bathroom ɗin yana nan fes-fes a kimtse.
Da sauri ta fito bedroom ɗin.
Waige-waige tayi ba kowa.
Haka yasa ta fito falon da sauri tana cewa.
"Umaymah ban ganshi bafa, kuma na hangoshi yana shiga ɗakin.
Na shiga kuma ban ganshiba."
Ummi ce ta amshi zance da cewa.
"Ko ya shiga wonka ne".
Da sauri tace.
"A a baya cikin bathroom".
Umaymah ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Ki duba Dinning area ko yana can".
Da sauri ta juya tana cewa.
"Ɗakin fa ya shiga, kuma ban ganshi ba."

Ummi ce tace.
"To kije dai ki ƙara dubawa".

Dube-duben tayi a falon kana ta koma cikin bedroom ɗin wayam fa

A hankali ta ƙarewa wodurob ɗin shi kallo, buɗesu tayi duka, tana cike da mamakin to ina ya shiga, dan tabbas taga shigarsa ya kuma za'ayi baya ciki to ina ya shiga?.
A haka duk ta bubbuɗe durowowin babushi babu alamarshi.

Falon ta sake fitowa tana mai jin zohin hannun yana tsananta.

Ɗaura hannun tayi a kanta tana jin idonta na kawo ruwa.

Umaymah ce ta shigo.
Ƙofar shiga cikin Garden ɗin su ta duba.
A rufe take babu alamun an taɓata ma.

Ƙofar ɗaya ɗakin ta nufa zata buɗe.
"Aysha tace.
"Allah ko Umaymah bai shiga nanba ɗauki shi ya shiga.
Kuma na duba baya ciki tako ina kuma banga fitanshi ba."

"Ikon Allah to ina ya shiga?".
Umaymah ta faɗa tana.
Shiga ɗakin. Jim kaɗan ta fito.
A gefe ta tsaya tana mamaki tabbas dai sunga ya wuce.

Da sauri suka miƙe ganin ya buɗe ƙofar ɗakinshi ya leƙo yana cewa.
"Umaymah lfy kuwa? Naji kunata salati".
Da sauri tace.
"Kai muke nema bamu ganka ba, ina ka shiga Aysha tace baka cikin ɗakin."
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta tare da cewa.
"Uhumm to dama ya za'ayi ta ganni tanata kuka ta gigita kanta ba dole ta makanceba".
Cikin gamsuwa da hakan dan Umaymah ta yarda wata ƙil ciwone ya gigita Aysha shiyasa Bata ganshi ba.

Ita kuwa Aysha cikin zafin tace.
"Wlh Umaymah ba ciwo bane na duba ko ina ban ganshi ba".
Kai Umaymah ta gyaɗa kana tace.
"To kije ya miƙi tofin".
Miƙewa tayi ta nufi cikin ɗakin.

Ita kuma Umaymah ta koma falon.

Raɓawa gefe tayi ta shigo.
Shi kuwa maida ƙofar yayi tare da cewa.
"Zo nan".
Matsowa tayi ya fara yi mata tofin
tana jingine da ƙofar yanayi yana hura mata iska.
A hankali ta fara lumshe ido,
ganin zatayi bacci ne yace.
"To jeki".
Har zata fita sa kuma ya ɗan sha gabanta ido ya zuba mata kana a hankali yace.
"Ke komai kika gani sai kinyi mgn ne?".
Kai ya jujjuya alamun a a.
Gashin girarta ya zubawa ido tare da cewa.
"Bubbuga Rumbun Abboi".
Baki ta ɗan tura tare da cewa.
"Ni dai ba bubbuga Rumbun bace".
Matsota ya farayi ganin hakane ta ɗan ja da baya ta jingina da ƙofar, kusa da ita ya kuma matsowa kana a hankali yace.
"To ke meyece in ba bubbuga Rumbun ba, ko kunya babu kin zauna gaban wanda ba mijinkiba, yana baki abinci har baki".
Gashin tattausan gemshi ta ɗan kalla tare da cewa.
"To nida Yayana ɗan uwana, tunda mai bani Allah ya kawoshi ai sai ya bani kada yunwa ta kasheni".
Murmushi mai sanyi yayi sabida tambaya ɗaya ya mata cikin amsa tambaya ɗayan kuma ta amsa mishi tarin tambayoyinshi. iskar bakinshi ya ɗan hura mata tare da cewa.
"Kince in baki ban baki bane?".
Da sauri tace.
"Toh sai nace ne?".
Ƙara matsowa kusa da ita yayi tare da ɗada mata girarshi ɗaya a hankali yace.
"Na'am sai kin ce mana shima ai ce masa kikayi ya bakin".
Mutsu-mutsu ta farayi jin ƙirjjinshi na danne nata a hankali tace.
"Toh ai shi ɗan uwanane".
Ba zato yaji mgnar ta subce mishi.
"Toh ai Ni kuma mijinki ne".
Sai kuma yayi sauri ya matsa, tare da juya mata baya.
Ita kuwa sumar ƙeyarshi ta zuba ido kana a hankali ta juya.
Cikin lumshe ido ta fita.

Shi kuwa Sheykh wata iriyar sassayar ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi.
Kana ys cire kayan jikinshi.
Sannan ya shiga wonka.
Bayan ya fitone yayi shirin baccinsa.
Kana ya kwanta.

Ita kuwa Aysha tana shiga ɗakinta ta kwanta sai bacci.

Umaymah kuwa na ɗakin Ummi suna tattauna wata mahimmiyae mgna,
sai ƙarfe sha biyu ta shigo.
Tayi mamakin ganin Aysha konce tana baccin.
A hankali tace, uhum tana tashi zan kai maka ita tunda ka iya kora masu maganin ka kora sarkin bakan masarautar Joɗa kana ka kora wanda iyayenta suka zo dashi.

Daga nan taje tayi al'wala tazo ta kwanta.

A can wani yankin kuma.
Sarkin baka ne da Ɗalhatu mai sa tayis ne,
zaune su, suna musu bayanin duk abinda ya faru.
Dariya tayi mai cike da jin daɗi tace.
"Uhumm ai zanyi maganin ƴan iska watan cin uwarsune ya kama.
Wannan shegen yaro Jabeer Allah ya sani bana ko son ganin fuskarshi.
Duk sanda na ganshi sai inji zuciyata ta tsinke hankalina ya tashi.
Ɗaya dake gefenta ne, yace.
"Aini da inada dama da a daran nan zan kashe shegu gaba ɗayansu."
Kai ta juya tare da cewa.
"Uhum baka san rashin kunya da tijara da magangun da wannan matar tashi mai kama da aljana tayi minba ne.
Shiyasa dole in taka mata birki zanci uwarta zata gane bata da wayo."
Daya na gefenta ne yace.
"Uhummm ni wlh da zan samu wutan zan bunkawa shegu duk su babbake".
Nan dai sukaci gaba da yiwa Ahlin Sheykh tanadin mugunta.

A can cikin dajin kuwa zaune yake gaban bokanshi shi.
Cikin hatsala yace.
"Kace min abubuwa suna gabda nasara amman akwai tsaiko menene tsaikon gaya min shi in kaudashi".
Dariya bokan yayi tare da zazzare idanu kana yace.
"To ka dai san babban abunda ya hanamu nasara kan yaron nan, shine addu'o'in da yakeyi da yawan zama da al'wala da karatun al'ƙur'ani.
To yanzu kuma na gano wannan matar tashi da aka aura mishi idonta a buɗe suke.
"Akwai makaran gado, wanda sukeda ƙarfin iko, ko jiya wata cikinsu tazo tajamin kunnen kada in kuskura in cutar da ita.
Sannan kuma akwai saurayi ta da ya raineta ya shirya mata jiki, kana tana iya gane sihiri a wuri duk ƙanƙantarshi.
To in dai ba rabashi mukayi da itaba ko a kasheta ba tsira zamuyi ba.
Kuma tana iya tona asirin kowa".
Cikin tashin hankali yace.
"Uhumm zata kuwa bar Masarautar Joɗa nan kusa.
In kuwa ta nuna taurin kai tabbas zata bar duniyar nanda bada jimawa ba, bazan bar duk wani abun da zai shiga tsakanina da sarautar masarautar Joɗa ba".
Daga nan sukaci gaba da tattaunawarsu.


Barun kuwa ana korashi ya nufi ƙasar Cameroon, Ba'ana bai iya jiranshi ba, tahowa yayi suka haɗu ya gaya mishi duk yadda sukayi da Sheykh.
Nan suka sake komawa cikin Rugar tasu can inda ya samu sabon uban gida.
Yanaji kamar ya mutu dan baƙin ciki.
Nan yaci gaba da shirya yaƙan Sheykh.

A nan kuwa ɗakin Aysha.
Ƙarfe ɗaya da rabi Aysha ta farka da salati a bakinta.
Cikin sauri ta buɗe idonta.
Tare da miƙewa a hankali ta nufi falon.
Domin taji zogin na dawowa.
Tazo falon kenan ta hango mutun da irin shigar ranan cikin tsoro tace.
"Waye ne kai me kakeyi mana a nan?".
Juyowa yayi ya kalleta cikin isa ya fara takowa zuwa gabanta.
Da sauri ta fara jan baya-baya tana cewa.
"Me hakan? Me kake nema damu?".
Cikin Tsuke fuskarsa yace.
"Me na samu dai. Ai Jahan tun kafin ya nemi abu yake samun abun a hannunshi".
Da ƙarfi ta buɗe bakinta zata zurma ihu.
Taku biyu yayi ana uku ya isota.
Tafin hannunshi yasa ya rufe mata baki tare da cewa.
"Kada ki razana wancan mataccen mijin naki".
Wani irin zazzaro ido tayi tare da jujjuyasu cikin alamun firgici da tsoro da kiɗima.
Kanshi ya jujjuya mata tare da cewa.
"Kada kisa zuciyarki ta buga a banza dan nace wancan mataccen mijin naki.
Ban kasheshi ba, amman dai ke a wurinki dashi da mace yar uwarki ba sauyi".
Hannunta mai lfyar ta fara kiciniyar ɗagawa zata ture hannunshi da ya ɗaura kan bakinta, ya rufe, ya haɗa kanta kuma da

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment