Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har bedroom nashi ta wuce riƙe da hannunshi suna shiga ta faɗa jikinshi.
Wani irin rumtse idanunshi yayi da azaban ƙarfi tare da ruggumeta tsam a j...!






Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 zaku turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276.
Bana son VTU in kinyima ni ba ruwana. In ya kama dole ma baki da damar tura kuɗin ta Account ɗina to katin mtn zaki saya ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsapp 09097853276.



Gareku *Murmushi group* ngd da halaccin ku, zumuncin kenan.






By
*GARKUWAR FULANI*
[3/16, 9:48 PM] +234 806 559 0880: A jikinshi, ya matseta da ƙarfi, sabida tsananin fushin da yake ciki da tafasar da zuciyarsa keyi, ji yakeyi tamkar ya matseta ya medata cikin jikinshi kanta ya danni zuciyarsa ko zaiji sassaucin.
Ƙuna da ƙuncin da kalaman da Gimbiya Saudatu ke jifarshi dashi da mahaifiyasa dasu.
Haƙiƙa ita kaɗaice mutun da ta samu nasarar gano abinda ke ta'azzara fushinsa har ya kasa control ɗin kanshi ta tunzurashi.

Wani irin wahaltaccen numfashi Aysha ta fesar a hankali sabida jin wani fitinenne rugguma da yayi mata tamkar zai gamesu ya cure jikinsu wuri ɗaya.
Gaba ɗaya jikinshi rawa da kerma yakeyi tamkar mazari.
Cikin fizgo numfashin ta kwantar da kanta bisa ƙirjinshi dai-dai kan ƙahon zuciyarsa,
Kana tasa hannun ta saƙalo wuyanshi, ta ware yatsunta manya tana yin sama da ƙasa dasu a kan tattausan sajensa
Cikin sanyi tare da muryar kwantar da hankali tace.
"Indai har ikon Allah kan iya yaye duhun dare da hasken rana ya meye gurbindun.
To tabbas yaye baƙin ciki i zuwa farin ciki a zuciyar bawansa al'amarine mai sauƙin gaske.
Abin sani kawai shine su mumanai girman jarrabawa ko ƙalubalen rayuwa baya sasu fidda tsammanin samun rahamar ubangijin taliƙai."
Murza kanta ta kumayi bisa ƙirjinsa sabida tanajin wuya da zafin ruggumar da ya mata cike da fushi.
Cikin sassanyan murya tace.
"A shawarce kayi ƙoƙarin jagorantar zuciyarka, kayi baya da lamuran kowa ka ruggumi naka.
Sabida kana zagaye da Magauta makusanta yau da gobe ita ce zata ganar da kai abubuwa da yawa, ka fuskanci magautanka ka dena dukan dungu."
Mutsu-mutsu ta farayi a jikinshi sabida kalamanta na ratsashi kuma suna sashi zafafa ruggumar da yayi mata. Koda yake hakan baya rasa nasaba da hautsunewar kwanyarsa a kan kalamanta.
Cikin ɗan buɗa murya taci gaba da cewa.
"Kafin ka yarda da mutane to ka rinƙa morar Kekkyawar ƙwaƙwalwarka mai tarin basira da nazartarsu, ka dena yarda da mutun a bisa fuskarshi ta zahiriya.
Kafin ka buɗe musu zuciyarka ba basu kekkyawan mazauni na mutane masu amana.
Da yawan mutane dake da kaifin basira da iya tsara zance, har su sanyaya zuciyar mutun su sa mishi yardarsu a ransa.
Da idan zaka shiga zukatansu zaka samu dafin guban dake zuƙatansu yafi na baƙin kumurci.
Yah Sheykh kada ka damu da sauyin ɗan Adam tunda dama shi halittace mai rauni kan rikon amana da halaccin.
Har kullum ka jingina da kanka, duk wanda ya nuna zai zamto tsanine a gareka, koma yake ganin shine tsaninka, nuna mishi tun kafin zuwasa gareka.
A tsaye kake da ƙafafunka.
Ta hakane zai san ƙaucewarsa bata nufin faɗuwarka."
Ɗan tsagaitawa tayi ta ɗago kanta, ta kalleshi sabida jin yadda tattausan gemunshi ke shafa goshinta.
Lip ɗinshi na ƙasa ya taune tare da girgiza gemun.
Ya kuma rumtse idanunshi sai dai yanzu ya ɗan fara sassauta ruggumar da yayi mata.
A hankali taci gaba da cewa.
"Gimbiya Saudatu fa, ba belbela bace, Yah Sheykh ka nazarci kalamai na, ita bushiyace ko ince kunkuru.
Zanfi son ka ɗauki zancenta dana mai taɓun hankali a ma'auni ɗaya.
Ni dai ban san menene tsakaninku ba, sabida bani da damar sanin komai naka, da ace na sani da ni zanji da ita, sai dai batun gsky ka dena yankewa littafi hukunci a bisa bongon bayanshi, ka buɗe littafi ka nazarceshi shafi zuwa shafi kafin ka yanke wa littafin hukunci".
A hankali ya buɗe idanunshi.
Ya zuba matasu, tabbas yaji wani abu ya ɗarsun masa a zuciya, da zai samu yanzu duk suturan jikinta zai kekketashi ko zaiji sassaucin abinda yakeji.
A hankali ya saketa.
Kana ya zauna a bakin gado,
Kanshi ya dafe da hannunsa duka biyu.
Still har yanzu jikinshi kerma yakeyi.

Ita kuwa Aysha juyawa tayi da sauri ta nufi falon, da nufin ta ɗauko mishi ruwan sanyi yasha ko zaiji sassaucin abinda yakeji a ransa.

Ba ruwa Fridge ɗin nasa.
Hakane yasa kai tsaye ta wuce babban falon.


A can falon kuwa Affan da Jamil, sai dariya sukeyi ganin yadda har yanzu Gimbiya Saudatu taketa lalube a inda ta faɗi kasa dirsham.
Tuni fuskarta ta haye ta kumbura tayi sintim.
Hakama bakinta.
A hankali ta fara bude idanunta, sai ta kuma rufesu.
Ummi ce tayi murmushi mai cike da jin daɗin marukan da Sheykh ya yayyarfa mata.
Cikin dakiya ta kalli hadiman Gimbiya Saudatu dake gefe suna murmushi suma tace.
"Ku matso kuyi mata jagora".
Da sauri Gimbiya Saudatu ta gyara zamanta tare da buɗe jajayen idanun nata, cikin masifewar murya tace.
"Ke tafi daga nan Jakadiya mara galihu".

Da sauri suka juyo suka kalli inda Aysha ke tsaye wacce ta nuna Gimbiya Saudatu hanyar fita tare da cewa.
"Ki ɓace min daga nan, sabida mijina bazai juri jin ihun haukanki ba".
Wani mugun kallo ta watsawa Aysha da jajayen idanunta kana tace.
"To fitsarerriyar ƙauye, mai gaggawar tsiri da cewa miji Baba, waya kasa dake bare ki zari babban kashi".
Jalal ne ya ƙaraso cikin falon, sabida yana son yaga matakin da Aysha zata ɗauka tunda ta iya fesa Hajia Mamansu ma rashin kunya.
Ummi, Jamil, Affan, suma gyara zama sukayi.
Ya Jafar da yanzu ya shigo ma gefen Jalal ya zaune.

Ita kuwa Aysha cikin isa da ƙasaita ta iso gaban Gimbiya Saudatu kujerar dake gabantan ta zauna a kai wacce kujerar zaman Sheykh ne. Kai ta jinjina tare da cewa.
"Ƙauye tushen kowa! Duk wanda bashi da ƙauye to bashi da asali kenan, shin baki san cewa da ƙauye akanyi birni ba.
Shin ke kinma san me ƙalmar ƙauye take nufi kuwa?".
Ƙafarta ɗaya ta ɗaura kan ɗaya, kana taci gaba da cewa.
"Da fari Makka itace babban birni sabida Annabi Sallallahu alaihi Wasallama yana cikinta.
Da yayi hijira ya koma madina kuwa sa madina ta zama babban birni mai cike da salama sabida addinin da kanshi ya koma can.
In kin gane me ƙalmar ƙauye take nufi garin da babu addini ba ilimi garinda kafurai suke, shine ƙauye, domin duk inda hasken addini yake da ilimin da masana ilimin to sun zarta ace musu ƙauyawa, domin kalmar ƙauyawa tana nufin jahilai, niko nan da kike ganina gidanmu tushene na tsanƙaya yara da dattawa.
Dan haka janye kalmarki ta fitsarerriyar ƙauye, gorinki bai samu muhalliba."
Tsaki taja tare da cewa.
"Baki san cewa kunne ya girmi kaka ba ko? To inma baki saniba Ni nan Aysha ina sane da labarin ƙuruciyarki da rashin kunyar da fitsarar da kikayi da taraddadin da kika sawa iyayenki na alamun lalacewa, dan haka kece fitsarerriyar. Kana kuma in kin mance in tuna miki ƙauyenmu ya zarta asalin naku ƙauyen girma da daraja ko dai kin mance inane asalin ƙauyenku.
In kin mance in tuna miki, ita kanta masarautar Joɗa kafin a auroki cikinta zata amsa kiran suna ƙauyen da hausawan ke nufi.
Yau da gobe shike sauya komi da kowa.
Ni nan da kike gani da mgnarki data ɗaurerre a turu basu da maraba."
Cikin masifa Gimbiya Saudatu tace.
"Sai dai in kece mahaukaciyar".
Dariya tayi tare da cewa.
"A a akan bola nake".
Miƙewa tsaye Gimbiya Saudatu tayi tare da fara gyara al'kyabbar jikinta, tare da cewa.
"Zanyi mgninku zaku gane kurenku".
Taɓe baki Aysha tayi.
Ita kuwa juyawa tayi ta, fice hadimanta na biye da ita a baya.
Dariya sosai Ya Jafar yayi wacce saida ta basu mamaki.

Sheykh kuwa da tun ɗazu ya fito bayan yayi al'wala ganin azahar tayi,
Tsayuwa yayi yana jin yadda Aysha keyi da Gimbiya Saudatu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu ganinshi ne yasa ta miƙe maza ta fice.
Miƙewa Aysha tayi da sauri jin muryar sa yana cewa.
"Ku tashi kuje kuyi al'wala lokacin salla yayi".
Juyowa tayi ta zuba mishi ido.
Tabbas daga jin muryarsa da yanayin fuskarsa zai iya nunawa mutun cewa har yanzu a zuciye yake.

Kallonta yayi a fizge kana yaja idonshi yayi gaba su Affan na biye dashi a baya.


Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Dai-dai kenan yau dai Sheykh ya sawa Gimbiya Saudatu tsoron zuwa nan ta baje kolin rashin kunyar ta."
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"Uhummm Ummi an dukan tenki akefa aka bar jaki a ɗaure"

Cikin sauri Ummi tace.
"Kamar yaya?".
Kai ta jinjina kana tace.
"Muje muyi salla, Ummi".
To tace tana mai son nazartan kalaman Aysha.

Bayan sunyi salla ne suka fito falon.

Suna zama Sheykh Jabeer ya shigo.
Affan, Jalal, Jamil, Ya Jafar. Na biye dashi a baya.
Su duk Dinning table suka nufa.
Ummi na biye dasu a baya.

Abinci ta fara zuzzuba musu.
Shi kuwa Sheykh tuni ya wuce Side ɗinsa.

Ita kuwa Aysha waya takeyi da Aminiyarta Rafi'a.
Gyara zamanta tayi tare da cewa.
"Rafi'a naji kamar an nememu a makaranta ko?".
Ɗan gajeren tsaki Rafi'a taja tare da cewa.
"Haka dai akayi ta cewa, to amman zancen Babu tushe, ance ƙaryane, gwamnatin ma bata nemi malaman ta zauna dasu ba."
Ɗan murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah aini wannan yajin aikin da aka shiga yamin rana, kinga da wannan tsarkafeffen auren da aka liƙamin da ya sani a tsaka ba fita.
To amman yanzu kinga duk muna a tare, zan kuma dage inyiwa Umaymah batun karatun nawa, kafin a nememu, in tayiwa Yah Sheykh mgna dai nasan zai barni."
Tsaki Rafi'a ta kumayi tare da cewa.
"Hegiya Aysha wato ke murna kikayi".
Dariya tai kana tace.
"Sosai ma kuwa". Kauda zancen Rafi'a tayi da cewa.
"Yauwa su Ummey sun dawo kuwa? Ɗan na kwana biyu banyi mgn da suba."
Jingina kanta tayi da jikin kujera kana ta fesar da numfashi a hankali tace.
"Uhummm basu dawoba, Rafi'a bani da kowa nawa a kusa dani, tunda nazo gidan nan ban sake ganin Ummey naba gwara Bappa na da Ya Al'ameen sunzo da bani da lfy, ina kewar Junainah, ina kewarsu Yah Giɗi in na tunosu hankalina na tashi ina masifar kewa da son ganin Dedde na".
Cikin tausayawa Rafi'a tace.
"Ba komai Aysha kiyi ta musu addu'a in sha Allah zasu baiyana kuma Allah zai karesu.
Su Ummey kuwa kwanaki da mukayi mgna da Junnu tace min wai sun kusa dawowa".
Cikin sanyi tace.
"Wasa sukewa Junnu, sabida ta matsa wai ita zata zo wurina kuma ita ko a gidansu Junaidu zata zauna".
Dariya Rafi'a tayi tare da cewa.
"Uhmm su Junainah manya wato ita fa da gaske har ranta take son Junaidun fa".
"Sosai ma kuwa".
Aysha ta faɗa tana kallon Ummi dasu Affan da suka miƙe tsaye alamun sun gama cin abinci.
"Yauwa ga Umma wai tayi kewarki kwana biyu baku gaisaba".
Rafi'a ta faɗa tana miƙawa Ummanta wayar.
Amsa Umma tayi tare da cewa.
"Aysha ya gida ya kwana biyu".
Cikin jin daɗi tace.
"Lfy lau Alhamdulillah Umma yasu Jamila".
"Lfy lau suna gaidaki".
Tace.
Kana ta miƙawa Rafi'a wayar tare da cewa.
"Tashi kije kinyi baƙo".
To tace kana ta katse kiran sannan ta fita.

Ita kuwa Aysha juyowa tayi ta kalli Ummi dake miƙa mata wayarta tare da cewa.
"Amshi Umaymah ke son mgna da Sheykh ta kira wayarsa baya ɗagawa ke kuma ta kiraki taji kina waya."
Amsa tayi da sauri kana ta kara a kunne tare da cewa.
"Assalamu alaikum, Umaymah ina wuni".
Umaymah dake kwance kan gado Mamma na gefenta,
Murmushi tayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah Aysha, ya gajiyar hanya?".

"Alhamdulillah Umaymah inasu Hibba da Safiyyah".

"Suna lfy, suna can Side ɗin Jannart".

Ayyah tace, ita kuwa Umaymah gyara kwanciyarta tayi tare da cewa.
"Yauwa Aysha Kaiwa Jazlaan waya".
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
"To Umaymah bari in Kai mishi".
Corridor'n ta shige, tana tafiya tana gaisawa da Mamma data amshi wayar.
A hankali ta kutsa kanta cikin falon shiru, babu kowa sai hasken wuta daya karaɗe falon.

Ƙofar bedroom ta nufa, tare da kallon wayar da taji kiran ya katse.
A hankali tasa hannun ta tura ƙofar Bedroom ɗin tare da sallama a saman lips ɗin ta.

A hankali ta meda ƙofar ta rufe,
kana ta ɗan tsaya tana kallon yadda ya kunna wutan ɗakin gaba ɗaya hasken ya cika ko ina.
Can ta hangoshi konce bisa gadonshi,
ya kwanta a kife, kana babu riga ko singilet babu a jikinshi.
Dagashi sai gajeren wondon, wanda yazo mishi har guiwarsa.
Roban ya zagaye ƙugunshi ya manne gam.

A hankali ta fara yin taku, tana matsowa, kusa da gadon.
Shiru ta ganshi kwance lib.
Ya kwantar da kanshi bisa pillow'nshi yana kallon gefe jikin gini.

Cikin nitsuwa ta ƙaraso gabanshi, ido ta zurawa Kekkyawar farar fatar bayanshi, da take tamkar ta Balarabe.
Sumar ƙeyanshi ta kalla, ido ta lumshe tare da ɗan sunkuyowa, bakinta ya kusanta da kunnenshi, a hankali ta buɗe baki tare da cewa.
"Yah Sheykh!".
Idonshi ya kuma lumshe da kyau, jin sautin zazzaƙar muryarta cikin kunnensa.
Tun shigowarta idonsa biyu, dan ya gaza samun bacci, yaso ace ya sauyawa Gimbiya Saudatu kamanni ta yadda har abada bazata sake tsayuwa a gabanshi ta ƙalubalanci ƙaddarar mahaifiyarshi ta kalmar sakaiyar zunibinta ne ba.

Ƙara manna kanshi da pillow'nshi yayi, jin alamun ta hau kan gadon.
Ita kuwa Aysha a hankali ta rarrafo ta matso gareshi.
Sunkuyowa tayi ta leƙa fuskarsa,
tare da kiranshi.
"Yah Sheykh".
Shiru bai motsaba bai kuma amsaba, kana bai buɗe idanunshi ba.

Idonta ta lumshe tare da buɗesu a hankali.
Fatar bayansa ta zubawa idanun, zuwa ƙeyarshi da sajenshi.
A hankali tasa tafin hannunta kan kafaɗarsa ta ɗan taɓa a hankali tare da kuma kiranshi.
Still bai kulaba, yana dai jin yadda take taɓa kafaɗarsa, tana ɗan jujjuyasa, bai kulaba sabida jin yadda taketa ƙara matsoshi.
Ita kuwa Aysha kwarmin bayanshi ta kalla, sai kuma ta ɗan ronƙofo kansa,
Dai-dai lokacin kiran Umaymah ya kuma shiga.
Da sauri ta amsa kiran wai sabida kada ya tashi daga baccin.
"Umaymah nazo kuma yana bacci".
Ta faɗa a hankali.
"Okay to ba matsala barshi in ya tashi zamuyi mgna".
Umaymah ta faɗi tare da katse kiran.
Wayar ta ajiye gefen kansa,
Cikin lumshe idonta, tasa yatsarta dai-dai bisa ƙugunsa, cikin tsakiyar kormin bayansa, a hankali ta fara yin sama da yatsar, tana jin taushin fatarsa.
Shiru yayi tamkar bashi da rai a jikinsa, sabida wani irin masifeffen abu da yaji yana bin duk ta inda hudan gashin jikinsa yake, yana bin jininshi da jijiyoyin jikinsa.
Yana aika saƙo zuwa ƙwaƙwalwarsa.
Numfasa ne ya fara sauya fitarsa. Amman ita bata ganeba.

Saima sa doguwar yatsarta ta tsakiya da tayi ta haɗa da manuniyarta tana yimishi tafiyar tsutsa a tsakiyar banshi.
Yar-yar haka tsikar jikinsa ta zuba tare da mimmiƙe".
Ɗaya hannun tasa bisa ƙeyarshi, yatsunta ta cusa cikin ƙeyar tasa, tana yamutsawa.

So take ya juyo rigingine sabida, wannan zanen macijiyar take son ganin ya yake a jikinsa a yanzu.

Wani irin fitinenne numfarfashi ya fesar a sanyaye tare da mirginowa ya juyo rigingine sabida bazai iya jure abinda takeyi mishiba.
Wani irin tsalle tayi ta diro ƙasa, lokacin da ya juyo rigingine ya kwanta, tsuma jikinta ya fara sabida, yadda taga Sheykh ɗinsa tayi wani irin kumbura ta taso tayi sama tamkar zata faso boxes ɗin shi ta fito woje.
Da sauri ta juya da gudu ta nufi ƙofar fita, sabida ganin yadda abun ya miƙe fiye da yadda ya miƙe na farin.

Juya kwayar idanunsa yayi tare da binta da ido.
Ganin ta fice a guje.

Uhummm yace a bayyane kana cikin zuciyarsa kuma yace.
"Zakiyi bayani ne yarinya".

Juyawa yayi ya kifu rub da ciki.
Daƙiƙu biyu tsakani, ya kuma juyowa rigingine tare da jan dogon tsaki.
gefen damansa ya kuma juyowa amman ina duk yadda yayi babu damar kwanciya domin, ya rigada nitsiwarsa ta bar jikinshi.
Ta gama hautsuna mishi lissafi.
Ta birkitashi, ta tsokano mishi bananarsa ta hanashi salama.

Da sauri ya miƙe tsaye, bathroom ya shiga.
Yana shiga kuwa ya sakarwa kansa ruwan sanyi wai ko zaiyi ƙasa da fitinenneyar sha'awar data yunƙuro mishi, uwa zata kaishi ƙiyama.
Madadin ta kwanta sai ƙara ƙarfi da miƙewa da cika takeyi.
"Shehhhhyyt".
Ya faɗa cikin hautsunewar kwanyarsa.
A hankali ya fito, kana ya sauya boxes ɗin.
Sannan ya fito.
Komawa yayi ya kwanta amman ina abunfa yama wuce zatonsa.

Haka ya rinƙa juye-juye bisa gadon.
Kamar zaiyi hauka, to abin ya haɗe masa da yawa ga fushin da bai husheba, muddin ba ya samu ya kekketa wani abunba.
Sabida shi in ya fusata koda abincine in zaici zakaga yana taunarshi da ƙarfi kamar dai yana hucewa a kansa.

To yau kuma ga fushi ga Sha'awar data addadabeshi wacce yasan Aysha ce ta tsokano mishi ita.
Gashi kuma in a fushi yake duk abinda zai yaken mishi da ƙarfi, hakane ya ta'azzara bukatarsan.

Aysha kuwa tana fita kai tsaye ta wuce.
Ɗakin Ummi sabida ta samu ba kowa a falon alamun su Affan duk kowa ya tafi uzurin gabansa Jalal wurin aikinsa ya wuce, hakama Jamil.

Kwance ta samu Ummi a bisa gado tana bacci.
A ƙasa ta kwanta, bisa carpet,
Tana zazzare idanunta sabida gani take in ta shiga ɗakinta kamar zai biyota,
sabida sosai ya firgitata da jarumtarsa.
numfashi take fiddawa a hankali tare da lumshe idonta.

Duk da bai taɓa nuna zaiyi wani abu da itaba.
Taji tana tsoronshi yau, ko dan ganin fusatarsa da fushin da yake cikine. Oho.
Ta faɗa a hankali.
A haka dai itama bacci yayi gaba da ita.

Shi kuwa Sheykh Jabeer karo na forko a rayuwarsa da sha'awar ta gigitashi ta sashi, fita haiyacinsa.
Yayi wonka kusan sau huɗu tsakanin azahar da la'asar, sabida masifar da yakeji.

Ƙishin da yakeji yasashi fitowa falonshi, Dinning area ya nufa.
Fridge ya buɗe, babu ruwa ko ɗaya, sai madarar ruwa ta goggoni,
Ɗaya ya ɗauka, mai sanyi kana yazo gaba show glass ɗin da cups da sauran ababen buƙatarsa suke ciki,
Ya buɗe.
Bula gongonin yayi yasa a cup kana ya ɗauki ɗan galan ɗin zuba dake wurin, ya cika cup ɗin.
Spoon ya ɗauka ya jujjuya, kana ya zauna bisa Dinning chair.
Kafa kanshi yayi ya shanye shi tas.
Sannan ya miƙe ya koma bedroom.
Bathroom ya wuce.
Al'wala yayi bayan ya kuma watsa ruwan.

Yana fitowa ya buɗe drower'rsa wani sabon boxes da yasan zai matseshi ya zaro, ya saka kana yasa wani gajeren wondon a kai sabida su danne mishi Sheykh ɗinsa dake son nunawa duniya a yunwace take.
Farar jallabiya ya zura, kana ya ɗauko al'kyabba irin mai shara-sharan nan ita kuma Sky blue ya saka, sannan yasa hiramin ya fesa turare.
Kana ya fito.

Shiru falon ba kowa, haka yasa ya fice. Da ɗan sauri sabida lokacin yayi.

Kiran salla ne ya tada Ummi daga baccin da ta ɗan yin.

Da mamaki take kallon Aysha dake kwance itama tana baccin.
Sauƙowa tayi ta tsaya kana ta gyara ɗaurin zaninta sannan, ta sunkuyo kan Aysha ta tasheta daga baccin.
Da sauri ta tashi zaune tana waige-waige.
"Tashi kije kiyi salla lokaci yayi".
Ummi ta faɗa tana shiga bathroom.
To tace tare da miƙewa ta nufi ɗakinta.


Bayan sun idar da salla ne, suka fito a tare.
Kitchen Suka nufa.
A nan suka samu Sara tana jajjaga kayan miya.

Ummi kuwa tukunyar data ɗaura tun kafin taje tayi bacci ta buɗe, bul-bul haka yake bararraka a hankali sabida ta rage wutan sosai yadda ko zata kai magriba ruwan bazai kare ba.
Ƙara wutan tayi, tare dasa ludeye ta ɗan motsa ƴan ƙananan mulmulen tunkusa, wanda suketa bararraka da jan nama mai kyau da tantaƙwashi, sai ƙamshi yakeyi tuni saman ruwan ya cika da mai naman kab ya diddige ya marmashe.

Juyowa tayi ta kalli Aysha tare da cewa.
"Me zaki dafawa Sheykh?".
Matso tayi kusa da ita tare da cewa.
"Ba miyar kase za'ayi ba, ai yanaci".
Kai Ummi ta gyaɗa tare da cewa.
"Eh yanaci kam, bare an kwana biyu ba'ayi ba.
Yanzu ɗebo nama mai ɗan yawa ki haɗa kifi kizo.
Ki saka.
Ke kuma Sara gyara min ganyen yakuwar nan."

To sukace baki ɗayansu.
Sara ta fara gyara yakuwar.

Ita kuwa Aysha naman tukunyar dake gabanta ta buɗe wanda sulallen naman ke ciki.
Juyewa tayi cikin tukunyar miyar, kana ta juya ya shiga Store bandan kifi ta ɗebo manya masu kyau.
Ruwan ɗumi ta zuba a ciki ta wonke ta gyarasu fes.
Kana tasa a cikin tukunyar.

Ummi kuwa tukunyar tuwo ta ɗaura.

A masallacin Masarautar Joɗa kuwa, ana idar da sallan la'asar duk, aka fara fitowa.
Affan shi cikin gari ya wuce wurin aminansa Yusuf da Aryan.

Jalal kuwa amsa kiran uban gidansu ya tafi.
Jamil da Ya Jafar ne suka dawo gida.
Suma Side ɗin su Jamil ɗin suka wuce.

Ƴan tsirarun mutane ne suka rage a masallacin wanda Sheykh yana cikinsu.

Mafiya yawa karatun al'ƙur'ani mai girma sukeyi.
Wasu kuma tasbihi sukeyi wasu kuma a kwance suke suna sauraron sautin murya.
Sheykh dake Karatun Alqur'ani cikin sassanyan murya.

Biyar dai-dai Sheykh ya fito cikin masallacin da sauran mutane.
Sabida wani irin duhu da ya fara yiwa illahirin garin Ɓadamaya ƙawanya.
Bisa alamu wani babban hadarine ke ketowa tun daga ƙasa.

Dimmmmmmm haka garin yayi, koda tsuntsaye baka ganin suna shawagi.

Gaba ɗaya kowa hanyar gidansa ya nufa.

Cikin nitsuwa bakinshi ɗauke da tasbihi yake tafiya.
A Lamiɗo da Galadima suna gabanshi.

A haka ya isa farfajiyar Side ɗinsa.

Ya kai hannu zai tura ƙofar kenan yaga an buɗe.
Gefe ya ɗan koma yana jiran mai fitowa.
Sara ce ta fito riƙe da kuloli a hannunta da alamun sun gama girki kenan.

Da sauri ta wuce saboda ganin hadarin.
Batama lura dashi ba.

A nitse ya shiga falon da sallama a bakinshi.
Ummi ce ta amsa tare da juyowa ta kalleshi.
Windows ya fara rurrufewa yana gyara labulayen.
"Hadari ne a garin namu ko?".
Ummi ta tambaya tana kallonshi.
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Mai ƙarfi ma kuwa Ummi, ku rurrufe windows ɗin falon can da ɗakunan ku.
"To". Ummi tace tare da miƙewa ta nufi falon.
Gefen Aysha ya ɗan ratsa ya nufi kitchen.

Zagayawa baya yayi, ya dudduba ko ina kana ya dawo.
A inda ya barta a nan ya sameta.

Tana ta danna waya.
"Nace kije ki rufe windows ɗinki ko".
Ɗan juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"A rufe suke".

Kanshi ya gyaɗa kana ya wuce ya barta a wurin.

Lib-lib haka gari ya ƙara ɗibkewa da duhu.
In dai wuri babu hasken ƙwan wuta to ko tafin hannunka bazaka gani ba.
Da sauri ta nufi ɗakin Ummi.

A zaune ta samu Ummi tana gyara carbinta daya tsinke.
Gefe ta zauna ta fara tayata.

Shi ko Sheykh Windows ɗinsa ya rurrufe,
tare da kashe komai na wuta dake falonshi da Dinning area,
hasken wayarshi ya kunna kana ya wuce bedroom.

Wutan ya ɗan kunna guda ɗaya hasken yayi dai-dai misali.

Umaymah ya kira bayan sun gama mgna ya katse kiran.
Sai ya zauna bakin gadonshi tare da jawo system ɗinsa.
Gaba ɗaya hankalinsa ya meda kanta, shiyasa baima san lokacin ya tafi ba.

Shida dai-dai, hadarin ya gama haɗa gangaminsa tako ina gabas da yamma kudu da arewa da tsakiyar sararin samaniya yayi baƙiƙƙirin

Sai wani irin walƙiya mai masifar haske da akeyi tako wani sashin.

Wani walƙiyane da a haska yazo tare da wani razanenne tsawa mai firgitarwa ne yasa Aysha wani irin zabura ta takure kanta cikin cinyoyinta tare da cewa.
Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Itama Ummi abinda ta maimaita kenan sabida ta razana matuƙa.

Sheykh kuwa hannunshi yasa ya rufe system ɗinsa tare da cewa.
"Subhanallazee yusabbihu ra'adu bi hamdihi wal Mala'ikatu min khifateeh".
Ya maimaita sau uku. Wani irin kumshe idonsa yayi lokacin aka kece da ruwa tamkar da bakin kwarya.
"Allahumma saiyiban nafi'an".
Ya kuma fara mai-maita wa.

Aysha kuwa da sauran matsorata irinta ajiyan zuciya ta sauƙe, tare da cewa.
"Kai ya Allah kasa mucika da imani, wlh Ummi ina tsoron walƙiya da tsawa a rayuwata, ina son yanayin damuna amman ina tsoronshi".

Jingina kai da jikin gado Ummi tayi tare da cewa.
"Tsawa abin tsorone ƴar nan. Nima kaina naji tsoron".
Kai ta gyaɗa jinjina tare da cewa.
"Tab Ummi kema kina tsoro".
Sosai ma kuwa tace. Dariya suka sa.

Ruwane fa ake tsulawa da iya ƙarfin shi.
Miƙewa Sheykh yayi tare da kallon time a wayarshi.
Shida har ta wuce.
Gab ake da kiran sallan magriba.
Gashi kuwa ruwa aketa fesawa babu kama hannun yaro.
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"Da ban dawo bama sai nayi salla a masallaci".

Bathroom ya wuce. Al'wala yayi kana ya fito.

Turare ya fesa, a jikinshi kamar yadda yakeyi koda yaushe.

Falonshi ya fito, dai-dai lokacin aka kuma danna wata tsawar da ta kece da ruwa mai ƙarfi.

"Ya ilahi". Yace lokacin da ya fito babban falon, shiru ba kowa sai hasken wuta.
Sanyin dake ratsa jikinshi ne yake sashi cikin wata fitinar kuma.

Baka iya jin sautin komai sai na ruwan shuuuhhhh.

Ƙofar falon ya nufa, a hankali ya buɗe.
Jingina kanshi yayi da jikin ƙofar yana kallon ikon rabbil samawati.
Ruwane tako ina yake kwaranya.
Ƙasa tasha ruwa ta ƙoshi.
Tabbas in matsoraci zai gani zaiyi zaton ƙasar ma tsastsafo da ruwa takeyi.

Magadanan ruwan duk sun cika tambul.

Dole ya maida ƙofar ya rufe, sabida.
Ruwan yayi yawanda in ya shiga kafin ya isa masallacin zai iya cutar dashi Allah ya sani baya son yayi salla

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment