Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mutumi nane yakan tsaya a nan in zai shiga gari, kuma yanada ɗan karen surutu da fara'a shiyasa na sansu, akwai randa yana tsaye a nan yaga Jalal ɗin ya wuce a guje shine yayi dariya yace.
"Hege mai komaɗeɗɗiyar fuska bosawa Sheykh ne ke nemanshi shine yake gudu kamar zai tashi sama".
to nan ya ɗan bani labarinshi. Kuma Sheykh ɗin da kanshi akwai shekarar da yayi azumi a garin nan yakan sayi kaya wurina, wani lokacin
Shiru sukayi tare da zubawa motocin idanu.
ganin sunata gilmawa, saida suka wuce gaba ɗayansu.
Sannan sauran al'ummar gari suka fara biyo bayansu.
Mafi akasari ababen hawan dama mutanen dake tafiya a ƙafa kab masallacin Masarautar Joɗa ba fadan jihar suka nufa wanda tuni Sheykh ya isa har yanata gabatar da Hudubar jummar sa mai taken, mu tsaida salla a lokacin ta.

A can cikin masallacin Masarautar Joɗa kuwa tuni al'ummar Annabi sun cika sunyi maƙil tako wacce kusurwa jama'a ne saffan-saffan suke shigowa,
yayinda cikin masallaci yayi maƙil har harabar masallacin ma ya cika tab da muminai salihan bayin Allah.

Kusan a guje wasu ke shigowa sabida lokaci na gab da ƙure musu domin bisa dukkan alamu an kusa ƙare Huɗubar.

Duk da tarin mutane manya da yara, amman sabida ladabi irin na addinin musulunci addinin mafi karamci da tsari, shiyasa baka jin motsi ko sautin kowa.
Sai wata iriyar zazzaƙar murya mai tsanani daɗin ji da sauraro da iya sarrafa harshe, cikin nitsuwa da iya laffazi muryar Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ke tashi yayinda yake ratsa zuciya da jiki da Kunnuwan dukkan muminin dake sashin da sautin muryarsa ke kaiwa.

A can cikin masallacin yake a fili na musamman wurin da aka ware domin Limami,
Yana tsayene bisa sawunshi ya fuskanci tarin bani Adam dake cike maƙil a wurin.

Kekyawan matashine mai tarin kwarjinin da haiba mai firgita magautanshi,
Sanye yake cikin shiga ta al'farma shigar dake nuna nasabarsa ta wanne sashi,
Wani datsetstsen yadin Getzner ne fari ƙal-ƙal wanda yasa riga da wondo,
Kana sai wata hamshaƙiyar al'kebba dake nuni da nasabarsa mai tarin ilimin addini da kuma alaƙantuwa da jinin sarauta,
Wani irin rawani ne ke murze a kanshi wanda jelanshi ke kwance a gadon bayanshi.

Farar fuskarsa dake zagaye da tattausan saje baƙi ƙirin mai fitinenne sheƙi da ɗaukar ido,
Ne yayi matuƙar kara mishi ƙwarjini sai tsabtataccen gemunshi da bazai gaza kamu ɗaya ba.

Cikin rahama da nimar da ubangiji yayiwa laraba ta baiwar iya sarrafa harshe da tausasan laffuza, yake gabatar da Hudubar jummar da yakeyi.
Wanda yana bayayi ne da jan hankali kan girma da darajar salla da tsaida ita a kan lokacin ta.

Shiru mutane nen ya ƙara tsananta ne a lokacin daya fara tsorotarwa a kan illloli da masifun dake bibiyar mai wasa da salla.

Shiru masallacin da farfajiyar sukayi baki ɗayanshi sai sautin A/C da kuma sauƙar numfarfashi mutane da shessheƙan kukan da wasu salihan bayin Allah sukeyi sabida yadda wa'azin ke ratsa jiki da zuciyar mai imani.

A hankali yasa hannunshin ya gyara zaman al'kebbar jikinshi tare da gyara abin sautin maganar dake saƙale a wuyan al'kyabbar jikinshi.
A hankali ya lumshe idanunshi kana yayi ƙasa da kanshi cikin yanayin nitsuwarsa ya buɗe jajayen laɓɓansa cikin zazzaƙan sautin muryarsa yaci gaba da cewa.
"Ya ƴan uwana musulmai muji tsoron Allah mu tsaida salla, domin itace forkon, abin bincika a cikin aiyukanmu.
Kada muyi wasa da salla a cikin dukkan halin da muke ciki.
Domin hukuncin mai wasa da salla hukuncine mai girgiza zuciyar dukkan mai mutuwa".
Kanshi ya ƙara rusunarwa sabida tarin manyan mutane daddatawa dake gabanshi waɗanda da yawa sunyi jika dashi wasu kuwa sun haifeshi, cikin tausasa lafazi yaci gaba da cewa.
"Hukumcin mai wasa da salla lokuta biyar ɗin nan.
Duk mai wasa da salla, za'a ɗebe al'barka a rayuwarsa.
Ƴa yan uwana mene amfanin rayuwar da babu al'barkan Allah a cikinta, babu.
Kana duk mai wasa da salla za'a ɗauke kamala ta mutanen kirki a fuskarsa, ya zamana baka da kamala da daraja a idanun al'ummar duniya.
Sannan muddin baka tsaida sallaba dukkan wani aikin da zaka aikata Allah bazai baka ladaba.
Kana dukkan addu'o'in da zakayi baza'a ɗaukakasu zuwa samaba.
Kana bazaka kasance daga cikin addu'o'ina salihan bayiba matuƙar kana wasa da salla".
Sassauta muryarsa yayi cikin yanayinshi na tarin kamala ya ɗan nago kanshi wanda dai-dai lokacin kuma ya hango ƙaninsa Jalal yana shigowa cikin harabar masallacin.
Kanshi ya kauda kana yaci gaba da cewa.
"Akwai uƙuba uku lokacin mutuwar dukkan mai wasa da salla.
Na ɗaya duk mai wasa da sallah zai mutu a matsayin matsiyaci gafalelle.
Na biyu
Zai mutu yana jin yunwa.
Kana na uku
Dukkan mai wasa da salla zai mutu yana tsananin jin ƙishi.
Ƙishinda koda za'a bashi ruwan ƙoraman duniyar nan baki ɗaya bazai gusar masa da wannan ƙishinba.
Kana duk mai wasa da salla akwai uƙuba uku dake jiransa a ƙabarinsa.
Za'a ƙuntata masa ƙabarinsa ya tsuƙe ya matse har sai ta kai matsayin da haƙarƙarinsa na dama ya haɗe dana hagu.
sannan kuma. Za'a saka masa garwashin wuta a cikin ƙabarinsa yayi ta juyawa a cikinsa ba dare ba rana.
Na uku. Za'a saka masa wata macijiya mai suna Shuja ul Qara,u wacce ta kasance ne ɗaya daga cikin macizan wuta.
Ida nunta na wutane. Farshenta kuma na baƙin ƙarfene.
Tsawon ko wani farcenta ɗaya tsawon tafiyar wuni ɗaya ne.
Zatayiwa mamaci magana, da muryarta mai tsawa da amo mai firgitarwa, zatacewa mamaci mai wasa da salla yayin rayuwarsa cewa.
(Ubangijina ya umarceni inyi ta saranka tun lokacin sallan asuba har zuwa azahar, daga azahar har suwa la'asar daga la'asar har zuwa magriba daga mangriba har zuwa isha'i daga sallan isha'i har zuwa wayen gari asuba.
Duk sara ɗaya da zaiyima mai wasa da salla har ya mutu bai canzaba zai nitse cikin ƙasa anayi mishi azaba, bazai gusheba anai mishi azaba har tashin al'ƙiyama.
Allah ya tsaremu.
Uƙuba uku lokacin fitowarsa daga ƙabarinsa itace.
Na ɗaya hisabi mai tsanani.
Na biyu. Fushin Ubangiji.
Na uku. Shiga wuta. Allah ya tsaremu ya bamu ikon kiyaye salla da tsaidashi a kan lokacinsa, yaku taron matasa kune shagala tafi auranku, mu dage mu tsare salla duk rintsi".
Ya ƙarishe maganar cikin rauni da kushu'i.

Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi la'asar musamman matasa masu wasa da salla,
Jin ya juya yayi gyaran murya ne.
Yasa gaba ɗaya kowa ya mike ya fuskanci gabas masamar lada.

Cikin nitsuwa da tattausan harshe yake rare karatun al'ƙur'ani mai girma.
Lokacin da yake limancin sallan jumma'ar da a ƙalla yana samu halartan mutun sama da Dubu biyu.

Bayan anyi salla raka'a biyu kamar yadda yazo a nafsi, akayi addu'a aka shafa kana, mutane suka fara firfita daki-daki.

Bayan 30 minute shal cikin masallacin.
Dan gaba ɗaya kowa ya nufi wurin lamuran yau da kullum ɗinshi sai mutanen da ba'a rasaba wanda su sai dare zasu bar cikin masallacin.


Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa, ne tafe a hankali cikin irin takunsu na sarakai,
Yayinda Jikinsa mafi soyuwa a garesa ke gefen damanshi,
fadawane ke biye dasu a baya, sun zagayesu,
Sai kuma bayansu can kuma Ayarin fadawan Jalal da Jamil ne wanda suke tagwaye ƙannen Sheykh Jabeer.
shi kuwa Malam Jabeer taku yakeyi a hankali cikin rashin nuna ɗagawa a kan doron ƙasa, tafiyar yake tamkar yana tausayawa ƙasar yayinda mutane kuwa ke kallon hakan a matsayin ƙasaitace da jinin sarauta dake yawo a sasan jikinshi.

Suna tafene a tare yayinda bakin Sheykh Jabeer ke motsawa a hankali hankali, wanda sai ka lura kake gane, tasbihi yakeyi a zuciyarshi wanda hakan ya zame mishi abin ci da sha a rayuwarshi.
"Astagafirullaha wa'atubu ilaik, Astagafirullaha! Astagafirullaha!! Subahanallahi! Walhamdilillah wa lailaha'illalahu Allaahu akbar. Astagafirullaha".
Waɗannan sune kalamen da basa rabuwa da bakinsa, dama wasu masu tarin yawa.

Ta ƙofar dake shiga masarautar daga jikin masallacin sukabi.

Masarautar Joɗa babbar masarautace mai tarin girma tarihi.

Ginin Masarautar ginine mai masifar kyau da ɗaukan hankali.

Kana shiga daga asalin babban gate ɗin fadar, zaka samu wata shimfiɗeɗɗiyar hanya mai girma irin mai guda biyun nan, gefe da gefen hanyar duk wasu irin dogin fulawowi na mijin kwanda ne masu tsawo da kyan gani,
sai kuma tsakanin titunan, shima jerin dogayen bishiyoyin ne.

Tafiya mai ɗan tsawo, zakayi kafin, ka isa wani babban Round about mai masifar kyau, wanda cikinsa ke ɗauke da babban kwarya a ƙasa, sai kuma ƙananan kware, guda uku, sai kuma ginin mutum-mutumi na kekyawar saniya fara mai ɗigo-ɗigon baƙi, wanda mace ke tsugune a gefe kamar tana tatsan nono sai kuma ɗan saurayi matashi na riƙe da sanda ya coge da ƙafa ɗaya.

Sai kuma korayen ciyawi masu masifar kyau da sanyi wanda akayi alamun manomi na ciki.

Daga nan ne hanyoyin cikin masarautar suka rabu huɗu, ɗaya yayi gefen dama ɗaya yayi gefen hagu ɗaya yayi gabas ɗaya yayi yamma wanda ta nanne ake shigowa.

In ka miƙe ta yamma daret itace titin da zai sadaka da asalin sashin Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa wanda nan sashin matanshi da hadimanshi yake da sashinshi dama faɗar duk nan take.
In kayi gefen dama kuwa wasu irin tsala-tsalan gine gine-gine masu tsananin kyau da ɗaukar hankalin wanda suna nan part-part ne masu girma da tsaruwa, an ƙawata tsakiyarsu da wani sassanyan Garden mai girman gaske.

Inda part ɗin sun kai goma, mafi kusa da sashin mai martaba sarkin Nuruddeen Aliyu Bubayero, shine sashin GARKUWAN FULANI, wato Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Sai kuma na gefen daman Sheykh Jabeer shi kuma na Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero ne, da matarsa Juwairiyya.
Sai na gefen hagunshi kuma na Jalal, ne na kusa da Jalal da kuma na Jamil ne sai dai Jamil yafi zama a sashin Jalal duk da korarshi da yakeyi wasu lokutan kuma lokacin kuma yana sashin Sheykh.
Sai sashin baya kuma sashin Affan.

Daga gefen hagun Masarautar kuwa wasu tamfatsa-tamfatsan plat ne masu girma har guda huɗu, sai kuma wani babban bene dake tsakiyarsu mai tarin girma wanda nanne sashin babban ɗan sarki Habibullah da matanshi.

Sai ta gefenshi can kuma wasu manyan part- part ne kimanin guda biyar wanda duk ƙanne shi ne da iyalansu da ƙananan yaransu a ciki.
Yayinda duk manyan yaransu kuwa kowa nada part ɗin shi a gefen da part ɗin Sheykh yake a ƙalla dai Part ɗin cikin masarautar Joɗa sun kai hamsin da biyar.

Can wurin mashigar kuma wasu ƴan saffan-saffan part-part ne wanda bisa dukkan alamu duka na bayine da hadimai da matansu.

Tsayuwa fasalta cikin ko wanne sashi na masarautar bazai yiwuba, sai a hankali.

Sai dai ko wanne part yanada Garden mai ɗan girma, wannane yasa gaba ɗaya masarautar ke zagaye da korayen fulawowi da bishiyoyi masu kyau.
Fentin masarautar gaba ɗaya iri ɗaya ne, Sky blue and white, mai ɗan karen kyau, a mahaɗar sashukan kuwa wani irin tamfatsetsen sweeminpool mai girma wanda ruwansa ke sky blue.
Can bayan sashin Mai martaba da Sheykh kuwa wani ƙaton filine mai cike da dawakai, da sashin mai rainonsu, gefe ɗaya kuma raƙuma da shanaye ne da makiyaya su, kana ga tumaki, a gefen Sheykh Jabeer ne kuwa akayi wani ɗan madai-daicin gidan zu ta bayan ɗakunan shi wanda yake da tarin tsuntsaye kamarsu, Ɗawisu, jimina, mikiya, agwagin ruwa, tolo-tolo, tattabaru, kana sai Aku. Da sauran tsuntsaye carki, kurciya, hasbiya, caccagi da-dai sauransu, shiyasa sashinsa ya kasance namusamman, don Garden Park ɗin ciki yafi na sauran part ɗin duka girma da kyau, sabida shine asalin Garden ɗin tarihin masarautar Joɗa.
Daga nan mashigar masarautar kuwa akwai wani babban filin sukuwa mai girma.

Daga masallacin Masarautar kuwa akwai miƙeƙƙiyar hanya har cikin masarautar wanda za'a iso gab da fada sannan kowa zai samu hanyar sashinsa.

A tsakiyar cikin masarautar ma kuwa akwai wani masallaci mai girma.

Wannan kenan sai a hankali zaku san mutanen masarautar da sunayensu halayensu dama nasabarsa da danƙantarsu da manufarsu.

A hankali Sarki Nuruddeen da Sheykh Jabeer suke takawa.
Suna shiga cikin gidan waɗannan fadawan suka tsaya a bakin Gate ɗin.

Kana wanda suka samu a wurin suka miƙe da azama wani dogon carpet mai azabar kyau da taushi, ɗaya daga cikin fadawan ya zo ya ajiye gabansu kana ya rinƙa yin baya-baya yana worwore musu carpet ɗin.
A hankali Sarki Nuruddeen Bubayero Joɗa yasa hannunshi ya kamo hannun kekyawan matashin jikan nashi da kab cikin jikokinshi ya fita da ban, hannunshi yake murzawa cikin nasa hannun a hankali a hankali.
kana suna tafiya a hankali, cikin takun sarauta,
Gefen mai martaba Nuruddee bayine da dogarai a ƙallah sun kai Ashirin da biyar, gefen Sheyk Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kuwa,
Ƴan saffan-saffan fadawane da basu kaishi shekaruba, a ƙalla sun kai goma.
Wanda wannan tsarinsa ne yace bazai iya ganin sa'an mahaifinshi ba ko sa'an Ya Jafar ɗinshi ba suna mishi bauta Babban Yayansu Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero suke kira Yah Jafar.
Kanshi ya ɗan murza ya juya a hankali da gefen ido ya kalli Kakan nashi dake magana cikin yin ƙasa da murya dan ko sarkin dogaren dake gefenshi baiji me yake cewa ba.
"Sheykh yaushe ne tafiyar taku?".
Siraran kyawan Idonshi ya lumshi a hankali ya kuma buɗesu tare da rausayar da kanshi.
Maimartaba bai damu da jiran amsar tasaba yaci gaba da cewa.
"Munyi Magana da Aminina Sarki Jalaluddin yace min Kakarka UmmuKulsum tace tafiyar taku ta ƙara toko?".
Shiru ya ɗanyi har saida sukayi taku uku zuwa biyar kana ya gyaɗa mishi kanshi kai a hankali irin gyaɗa kai na kamala".
Dai-dai lokacin kuma suka iso dab ƙofar mashigar sashin Maimartaba, wanda dama duk ran jumma'a daga shabiyu yake tashi zaman fada,
sanin hutawa yake a irin wannan lokacin ne ya sashi ɗan sake hannun Sheykh Jabeer tare da cewa.
"Sirranta komai a rai yanada wuya, amman kai baya maka wuya, ya zama kamar jininki, akwai tauraro na musamman a goshinka, wanda nake fatan watan wata rana ya haska zuƙatan ahlinka dama talakawan da zaka mulka".

Jin kakan nashi ya sake hannunshi da kalaman da yake jero mishine yasa ya ɗan kalleshi a hankali ya kuma sunkuyar da kanshi.
Sai ya kuma ɗan kalli Sarkin tare dayin mgna.
"Mulki yana da nauyi mai girmi Ni kuwa baya cikin tsarin jadawalin ababen buƙata ko sha'awa a rayuwata,".
Murmushi Lamiɗo yayi tare da cewa.
"Ba sai lallai abinda mutun keso ke samu ba, bakuma dole ka rasa abinda baka soba".
Ganin kakan nashi yaci gaba da tafiya ne yasa shima ya yaci gaba da tafiya.

Inda fadawanshi ke biye dashi a baya.

Yayinda fadawan Maimartaba kuwa suka tsaya a bakin sashin sa.

Sunyi tafiya mai nisa kaɗan kafin suka ratso ta gaban sashinsu mai azabar girma da kyau sashine mai ɗauke da part-part masu tarin yawa da girma wanda tsakanin ko wannensu da ƴar tazara sosaima.

A hankali ya ɗago hannunshi daga cikin babbar rigarsa da zazzafar al'kebbarsa ta rufe,
ɗan ɗaga musu hannunshi yayi alamun su tsaya daga nan.
Cikin abinda bai gaza 18 second ba duk suka rusuna ba tare da sun ƙara koda taku ɗaɗɗaya ba, kusan a tare suke cewa.
"Takarwarka lafiya ɗan Baban yaya Habibullah jikin Sarki Nuruddeen, jika ga sarki musulmai Jalaluddin".
A hankali ya kuma ɗaga musu hannunshi alamun ya isa haka, dan shi dai Allah ya sani har ranshi baya jin daɗi da son wannan kirare-kiraren dan yayi imani da Allah zasu iya sawa ɗan adam ɗagawa da jin kanshi shi wani abune, zasu iya sa mutun yaji kansa a matsayin wani sarki mai iko bayan kuma babu wani Sarki sai Allah.

Yana tsoron ɗagawa ta samu mazauni a zuciyarshi, sam baya son wannan kirare-kiraren na zamanin jahiliyya ina dalili kana mutum ɗan Adam mai daraja azo ana wani ce maka toron giwa ko tozon raƙumi ko dokin ƙarfe yaya Allah ya karramaka yayika ɗan Adam ka bari na ƙasa da kai suna suffantaka da dabbobi.
A hankali yace.
"Ya isa, duk kuje kowa yayi uzurin gabansa in inada buƙatar ku zan nemeku".
Shiru sukayi tare da baje manyan rigunansu suka zauna a inda ya dakatar da suɗin.
Kana sukace.
"An gama".
Shi kuwa a hankali yake taku cikin shigarsa da tafi kama data limamen harami.

A hankali yake taku, har ya iso bakin ƙofar shiga side ɗinsa inda a nan dogari mai tsare mashigar sashinsa sarkin ƙofarsa ke tsaye.
Tuni Sarkin ƙofa ya miƙe yasa hannu zai buɗe mishi ƙofar kenan sai ya kuma ɗan rusunar da kanshi,
Ganin Jamil ya rigashi kai hannunshi ya buɗe ƙofar cikin salonsa na raha ya nunawa Hamman nashi ƙofar tare da cewa.
"Sheykh Dr Malam Hamma Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa GARKUWA barka da yamma".
Kanshi ya kauda daga kallon ƙanni nashi, sannan ya kutsa kai ciki,
da sauri shima Jamil ya mara mishi baya,
Cikin wani haɗeɗɗen corridor mai fitinenne ƙamshi da azabebben sanyi suke tafiya a hankali.

Tafiya kaɗan sukayi sai gasu cikin wani tamfatsen falo na al'farma da more rayuwa,
ɗaya daga cikin lumtsuma-lumtsuman kujerun kilisai na manyan sarakunan dake falon ya zauna a hankali.

Ido ya ɗago ya watsa ƙanin nashi su, cikin sauri Jamil yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
"Na tuba Hamma kayi magana ina tsoron hukunci da idanunka gwara kamin duka kon ka haɗani da wannan saggamemen na bakin ƙofar kan nan ya dakani kawai in huta".
Kanshi ya kawar Cikin harshen larabci yace.
"Ban gankaba a masallaci".
Da sauri ya durƙuso gaban Hamman nashi cikin yin wuƙi-wuƙi da idanu cikin sanyi yace.
"Ana Aspet ya Akhi, a matsallacin ƙofar gidansu, Khadija nai sallan jumma'ar".
Kanshi ya gyaɗa kana ya kauda kanshi ya fuskanci wani katon majigi dake liƙe a jikin ginin yana fuskarta kujerar da yake zaune a kai.
Majigine dake ɗauke da full Qura'an, a hankali yake karatun cikin sassanyan murya.
Ganin hakane yasa Jamil ɗan rusuna duk da yasan ba amsa zai samuba cikin sanyi yace.
"Hajia Mama tana son ganinka".
Kanshi kawai ya gyaɗa yaci gaba da karatun shi.
Ganin hakan yasa Jamil ya juya ya fita. Shikuwa Sheykh yaci gaba da karatunshi, kusan awa ɗaya kana ya shiga Bedroom.

Shine bai fitoba sai lokacin da sallan la'asar ta gabato, jin an kira sallane, yasa ya shiga ya sabunta al'wala kana ya fito ba kowa a wurin sun watse kemar yadda ya umsrcesu.
Sai can bakin mafita ya samu mutun huɗu, yana tafe fadawanshi na biye dashi wanda suma sunyi al'walan.

Jamil kuwa daga sashin Hajia Mama ya fito da nufin zaije side ɗinsu yayi al'wala.

A harabar gidan yayi kiciɓis da abokin tagwaicinsa wato Jalal, cikin sanyi ya kalli yadda Jalal ke zagaye da fadawa yana tafiya da yanayinsa da muddin zaka yanke mishi hukunci da ganin zahiri zakace cikekken ɗan iskane, sai dai a baɗinin ba haka abin yakeba.

Kekyawa ne shima dan shi yana ɗibin kamanni da Hamma Jabeer ɗin nasu sosai saɓanin Jamil da yafi kama da Babban yayansu, Barrister Jafar Habibullah Nuruddeen Bubayero.

Tafiya yake cikin shigar tsamari zamani, wondon a saɓule har kana iya hango boxes ɗinshi, kana ga wani irin kafirin aski da yayi mai ɗaukar hankali.
sam a rayuwarsa shi baya ta'ammali da manyan kaya,
Baya tsoro ko shayin ko shakkar kowa a duniya sai Hammansun kaɗai.
tafe yake bayinshi na biye dashi a baya, da wasu kolabe a hannunsu, cikin tsare fuska Jamil yace.
"Kai ku tsaya, kolaben menene wannan a hannunku?".
Juyowa yayi a zafafe cikin halin faɗa yace.
"Kwalaben Giyane ko kanada maganne Akukkuturu?."
Da azaban ƙarfi da tsoro Jamil ya zazzaro ido cikin ɗaga murya yace.
"Kwala ben giya a gidannan Jalal kasan abinda kake cewa kuwa? Kwalaben giya a Masarautar Joɗa".
Ya juyo da masifa kenan yayi arba da Hamman nasu,
shiru yayi tare da yin ƙasa da kanshi, jiki a mace.

Shi kuwa Sheykh Jabeer idanu ya zuba mishi na wasu yan daƙiƙu kana ya juya ya nufi hanyar da zata sadashi da ƙofar tafiya masallacin Masarautar tasu ba tare fitar nan bisa dressing mirror suka ajiyesu kana suka juya suka fita.

Shi kuwa al'wala yayi ya nufi masallacin.


Ƙarfe tara dai-dai na dare. Sheykh Jabeer, ne zaune a bisa wani tattausan carpet mai azabar taushi,
Wata Hamshaƙiyar Gimbiyace mai cikan iko da muƙami, mulki, iko, cikin wani irin kallo mai cike da kulawa tasa hannu ta ɗauki ɗaya daga cikin nonon inabi dake cikin wani kekyawan tray dake gabanta miƙa mishi tayi tare da cewa
"Jabeer Yaushene tafiyar taku?."
Tankwashe kanshi yayi bisa kafaɗunshi kana a hankali ya ɗan kalleta tare da motsa laɓɓanshi a hankali yace.
"jibi".
ya faɗi mgnar a gajarce, gyara kishingiɗarta tayi bisa kilisan tum-tum dake gefenta,
Cikin kulawa tace.
"Da Umaymah zakuje ne?".
Kanshi ya jujjuya mata alamun a a.
Kanta ta rausayar cikin ƙasaita tace.
"Naga kamar bacci kakeji Saida safe".
Kanshi ya gyaɗa kana cikin girmamawa yace.
"Allah ya bamu al'khairi".
Amin tace, shi kuwa daga nan ya fita ya tafi.

Koda ya koma sashinsa. A falo bakin ƙofar ya samu Jakadiya, tana ganinshi ta ɗan rusuna duk da tasan yana hanata hakan a hankali tace.
"Akarmakallahu, Umaymah ce take biɗar mgna da kai, ta kirayi layinka ba'a ɗagawa, shine tace in kawo maka wayar".
Kanshi ya ɗan sunkiyar a hankali yace.
"Ummi kice mata tayi hakuri saida safe".
Cikin mamaki jakadiya tace.
"Lafiya dai ko Sheykh?".
Kanshi ya gyaɗa mata alamar eh lfy.
"To ba laifi zan gaya mata".
Daga nan ta juya ta koma sashinta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, daga bakin ƙofa ya dakatar da bayinshi.
Kana cikin nitsuwa ya kallesu tare da cewa.
"Sarkin ƙofar ka janye bayin dake bina da bin Jalal da Jamil, kaima ka koma can sashunku, ba'a buƙatar bibikon nan, in inada buƙatar ku Ummi zata sanar muku."
Ciki girmamawa sukace.
"To Sheykh". daga nan ya juya ya nufi ciki.
Su kuma suka juya.

Koda ya shiga ɗakinshi kai tsaye bathroom ya wuce wonka yayi tare da al'wala a cikin bathroom nashi da yafi makoncin wani kyau.
Komai na bathroom ɗin glass ne mai ruwan garai-garai, bathroom ɗin katone, mai ɗauko da babban drower'n glass wanda yake cike da ƙananun kayan sirrin jikinshi kamarsu vets boxes and pants kana towels da rigunan wonka da jalabiyoyinshi masu masifar kyau da tsada da taushi da yawa, sai kuma 3 qtr da kuma turaruka dasu brosh da su makilin da dai sauran kayan buƙata na aske pravet part. Ko ina na kusurwan ban ɗakin da madubai.

Bayan ya fitone, yayi shirin baccinsa cikin wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da tsada,
A bakin gadonshi na sarakuna ya zauna,
idonshi ya zubawa woyoyinshi dake kan bedside drower' Woyoyin sun kai biyar,
a hankali yasa hannunshin ya ɗauki ɗaya daga cikinsu data kawo haske, alamun ana kiranshi,
Karawa yayi a kunnenshi tare da yin shiru.
A can ɗaya sashin kuma kekyawar tsohuwar balarabiyace keta mishi faɗan ina ya shiga tana kiranshi bai amsawa.
A hankali ya lumshe idanunshi tare da mirginawa ya konta tattausan gadonsa da shimfiɗar sa, wanda Jamil ke gyara mishi a koda yaushe, cikin harshen larabci yace.
"Sitti raja'an!".
shiru sukayi baki ɗayansu, can kuma sai yaci gaba da magana cikin larabcin,
sawon 32 second yana maga kafin ya katse kiran,
kana yayi laduban konciya bacci ya konta.


Washe gari da safe da misalin karfe sha ɗaya na rana.
Dawawonshi kenan daga fada,
Yana shiga falonshi asalin falon dake gab da makoncinsa kiran Umaymah na shiga wayarsa.
Ganin video call ne ya sashi, amsa kiran kana ya ajiye wayar kan Glass Stull dake gaban kujerar da yake zaune.

Fuskar wata kekyawar Matace ya bayyana a fuskar wayar tashi, cikin sanyi ta zuba mishi idanu ganin yadda ya tonƙoshe wuyanshi bisa kafaɗunshi a hankali tace.
"Jazlaan". Kanshi ya ɗan mirgina cikin wani yanayi ya jujjuya mata kai a hankali yace.
"Jazlaan, Umaymah sai yaushe zan zama Jazlaan? Sai yaushe, Jazlaan zai wadaci rayuwarmu?".
Murmushi mai ciwo a zuciya tayi tare da cewa.
"In sha Allah nan kusa".
A hankali ya lumshe idanunshi cikin sanyi yace.
"Umaymah, kizo kafin mu tafi, ina so mu haɗu".
Cikin tarin kulawa da tsananin ƙauna tace.
"Menene matsalarka?".
A hankali yace.
"Ya Jafar...!




Littafin na kuɗine.





By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 4

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘




*GAREKU MUTANEN NIGER, +22799460151 kuyi haƙuri an samu akasin number da nada bada, wayarta ta lalace. Yanzu ga number da zakuyiwa mgn +22799460151 300 ko 1k idan kun turata mata, saita turo min number ki/ka sai in saki/ka a group ɗin da kika biyawa🤝🏻. Gareku mutanen ƙasata ga number ta 09097853278, turo katin mtn na ɗari uku kacal, ko kimin TRANSFER ɗin darinki uku ko 1k ɗan samun SP Group. In kin biya sai kiyi screenshort ki turo min shaidar biyan kuɗin littafin GARKUWA ta wannan number dai 09097853276*




Cikin nitsuwar da ya kasance halittarsa, ya ɗan ranƙwafar da kai yayinda fuskarshi ta ɗan sauya yanayi murya

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment