Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Badamasi, Nasiru, basiru.
Dr Aliyu ne, ke gefen daman Habibullah, bisa alamu duk mgna yakeyi mishi a kan lfyarsa.
Bappa Nasiru, wanda shine, yake bin Habibullah a girma sai dai uwarsu ba ɗaya ba, gyara zama yayi tare da jan dogon tsakin da yasa duk suka meda idonsu kanshi.
Cikin kula Habibullah yace.
"Lfy dai Nasiru?."
Wani irin kallo mara daɗin gani ya watsa mishi tare da cewa.
"Yes lfy lau, sai dai mu nan duk muna da aiki, ba zauna gari banza, irinka bane, kowa yanada hidimar yi gashi har yanzu,
Lamiɗo bai fitoba".
Murmushi yayi ba tare da yaji ciwon abinda ya gaya mishibs, a hankali yace.
"To Nasiru, ai duk saurinka kayi haƙuri dai ya fito, kaga lfyarsa yaga taka, tunda shi bai gajiya da bincikar lfyarmuba, ai muku wa bazamu gazaba.
Domin abune mai wucewa".
Wani irin kallo mai cike da tsana da tsoggoma ya mishi tare da kauda kanshi.
Basiru ne yayi dariya alamar jin daɗin kallon da ɗan uwanshi yayiwa Babban yayansu da suke ƴan uba.
shi kuwa Habibullah Abbansu Sheykh, kauda kai yayi kar bai ganiba.

Kusan a tare suka miƙe gaba ɗayansu,
tare da haɗa baki wurin cewa.
"Barka da fitowa, Mai alfarma Lamiɗon Joɗa."
Murmushi yayi tare da kallon ƴaƴan nashi ɗaya bayan ɗaya, a hankali ya ƙarasa fitowa, hannunshi sarƙafe da hannun Jabeer.
Wanda baiyanarsa yasa, gaba ɗaya suka zazzaro ido. Cikin tarin mamaki, al'ajabi, firgici, kaɗuwa, gamida tsayawar idanunsu kan ɗan babban yayan nasu, cikin wani irin daskarewa, suka juyo suka fuskaci, junansu wannan ya kalli Wannan wannan ya kalli wancan.
Murya a daburce, Nasiru ya nuna Jabeer dake tsaye, cikin wani masifeffen al'kyabbar mai masifar kyau da zadan gaske, cikin ƙafewan yawun baki yace.
"Ka gafarceni Lamiɗo, me idonuna ke gani, daga ina ka fito da Jabeer? Me kayi dashi? Meye ma'anar hakan? Mu duk ƴaƴan ka bamu kai ka shiga damu ba sai shi?".
Cikin tsare fuska irin ta manyan sarakai dattawan,
ya zubawa, Nasiru idanu, wanda dole tasa ya hadiye rahowar maganar tasa.
Habibullah kuwa, wani irin rawa da karkarwa jikinsa ya fara.
Wani masifeffen tsoro da fargabane ya rufeshi akan ɗan nashi, koda dai baya jinsu a ranshi kamar sauran ƴaƴanshi, hakan bai hanashi tsoro da fargabar abinda zai cutar dasuba. Barrister Kamal kuwa.
Wata irinyar madifeffiyar zuface ta keto mishi daga saman kanshi har tsakiyar tafin sawunshi.
Lokaci ɗaya yaji wani irin abu ya saki ƙahon zuciyarshi,
Maƙoƙoronshi ya bushe ƙamas,
duhun daya rufe mishi idone yasashi komawa zaune.
Dr Aliyu kuwa, wani irin murmushi yakeyi yana kallon ɗan babban wansun.
Shi kuwa Lamiɗo hannun Jabeer ya kuma ja, wanda yake motsa laɓɓansa a hankali yana tasbihi kamar yadda ya saba.
Zama yayi kujerarsa ta musamman, kana Jabeer kuwa ya zauna gabanshi.
Cikin tattaro yawun baki Barrister Kamal yace.
"Barka da safiya. Sarkin Joɗo.
Sai ya kuma danne tarin baƙin cikinsa yayi mishi rumfa da fuskarsa ta zahiri kana ya kalli Jabeer da ya ɗan sunkuyar da kanshi tare da gaidashi.
Cikin dakiya yace.
"Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Joɗa.
Yaushe a gari".
Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa.
"Daren jiya".
Nasiru ne ya katsesu da cewa.
"Lamiɗo, ɗakin sarautar sarakunan Joɗa kuma ya zama kowa zai iya shigane?".
Bai kulashi ba, har saida suka gaisa gaba ɗayansu, kana, ya fuskancesu, duka cikin hikima da, kaifin basira yace.
"Rigar sarautarsu ta GARKUWAN FULANI, na bashi.
Sabida akwai tafiyar gaggawa da zamuyi zuwa, Rugar Bani, da ƙaɓilun wurin suka far musu da kisa."
Kai suka gyaɗa alamun gamsuwa, kana duk, ya sallamesu.

Duk suka fita kowa da abinda ke cikin ransa, da zuciyarsa.


Bayan fitansu ne ya kalli Jabeer cikin, tarin kula yace.
"Kaje ka shirya kazo mu tafi".
Kanshi ya kuma rusunarwa cikin ladab yace.
"Allah saine, mu bari sai bayan sallan, jumma'a ina munyi jam'i anan, mu tafi gudun kada muje bamu dawoba kafin lokacin sallan."
Gyara zamanshi yayi tare da gyaɗa kai kana yace.
"Haƙƙun kayi, gsky to mu bari sai an sauƙo mutafi, in yaso muyi sallan la'asar a can."
Da Wannan shawarar suka bari sai bayan sallan, azahar ɗin su tafi.
Sun daɗe suna tattaunawa kafin, ya sallameshi ya tafi, shi kuma ya nufi fada.


A falonshi kuwa, yana shigowa duk suka zuba mishi ido, da mamaki cikin zaƙuwa Jamil yace.
"Hamma Jabeer wai ta ina kabi ka fitane? Duk bamuga fitankaba".
Kanshi ya mirgina, alamun gajiya, kana a fakaice ya kallesu baki ɗayansu, tare da cewa.
"Sama".
Murmushi sukayi baki ɗayansu, sabida fahimtar amsar daya basu, na nuni basuga sanda ya fita bane.

Bisa wata tattausar doguwar kujera ya zauna.
Kana ya fuskanci ƙannen nashi da kyau.
Jalal ne ya ɗan sunkuyar da kanshi, ganin yadda Hammanshi ya zuba mishi ido, Jamil kuwa, kanshi ya ɗan rausayar tare da katse wayar da yakeyi, ya fuskanci ɗan uwan nasu,
Cikin yin fiki-fiki da idanu yace.
"Barka da safiya Hamma Jabeer, ya hanya?".
Alhamdulillah, yace mushi a taƙaice, kana ya ɗan gyara, hiramin dake bisa kafaɗunshi.
Jalal ne ya ɗanyi baya tare da lumshe idonshi cikin saisaita muryar da indai da Hammanshi zaiyi mgna to sai ya nitsu ya gyarata,
Domin yakanji yanada rauni duk sanda yake gaban Hammanshi, yana ji tamkar a gaban mahaifinshi yake.
Cikin sanyi yace.
"Ina kwana? Hamma Jabeer, ka dawo lfy t
yasu Sitti?".
Ido ya ɗan kauda kana yace .
"Alhamdulillah, Jalal ya jikin Ya Jafar?".
Kanshi ya ɗan jujjuya kana a hankali yace.
"Kalmace dai ta musulmi, koda cuta babu sauƙi ya zame mana ɗa'a muce, da sauƙin, amman a zahirin gsky ciwon Ya Jafar babu sauƙin, komai yaci tura, abubuwan sun yawaita".
Ya ƙarishe mgnar tamkar zaiyi kuka,
ganin hakane yasa Jabeer ɗan kauda kanshi, Allah yasani, baya son ganin ƙunci ko baƙinci ko wata damu a fuskarsu, sabida ya ɗauka cewa Allah ya barshi da rai da lfy ne a tsakiyarsu, su da akewa kallon marasa lfy ya zame musu Garkuwa. A hankali ya miƙe cikin kula ya kallesu, murya a ɗan macce yace.
"Kuzu kuci abinci".
To sukace baki ɗayansu, kana duk suka nufi, dinning table ɗin.
Wanda yake cike da abinci kala-kala.
Juwairiyya ce ta sakawa kowa abinda yake buƙatar ci,
Shi kuwa Sheykh sai jujjuya mata kai yayi alamar babu abinda zaici.
Ya dai zauna yana kallonsu,
Ummi kuwa, tana gefenshi.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli Haroon dake shan tea kuma still wayarshi na kunne yana, mgna da Jannart,
ɗan gajeren tsaki Jabeer ya ja, jin Haroon na cewa.
"Ina yin breakfast ne, ke me kikeyi? Bacci? Ko kwaliya? Ko kallo?".
hannunshi yasa ya zare wayar kana ya katse kiran tare da mishi nuni yaci abinci kafin ya tsaya yin waya.
Cikin haɗe fuska Haroon yace.
"Ka ganka ko? Ni shiyasa har tsoron zama kusa da kai nakeyi, sabida tsarabe-tsarabenka nada yawa, yanzu zaka fara jawowa mutum aya da hadisai, kana wani, abu kaza ba laduban kaza bane, in an jika kayi doguwar mgn to an sosa maka wuri biyu, ko ayar Allah, ko wannan mulkin da kake cewa an liƙa maka jaraba".
Jamil ne yayi ƴar dariya tare da cewa.
"Mulkin nema jaraba a wurin shi ko? Gacan wasu na neman, zaunece sabida Garkuwan da aka bashi".
Jalal ne ya ɗan tsuke fuskarsa tare da cewa.
"Ni kaina Wannan GARKUWAN bai wani burgeniba, sabida baya cikin, masu iya gadar mulki, sabida shi ai ba jikan sarki ta wurin ƴa mace bane, jikanshi nefa ta wurin ɗa namiji ta yaya zai bashi Garkuwa?".
Ummi ce taja wani dogon ajiyan zuciya tare da cewa.
"Uhummm ta yaro kyau take bata ƙarko, to kai Jalaluddin, yanzu Jafar da aka bashi Galadima, wani hali yake ciki? Tun randa aka naɗa masa sarautar me mutane suke kallon ya zama? Dukfa duniya kallon majanun akeyiwa Jafar".
Juwairiyya ce ta ɗan rumtse idonta tare da cewa.
"Ni banyi fataba, banso a sake bawa Kowa wani mulkin da nasan baza'a barku lfy ba, shi Lamiɗo, meyasa ko ƴaƴan nashi babu wanda ya bawa mulkin komai?".
Da sauri Ummi tace.
"Sabida muddin yace zai basu sarautu, to wasu zasu hallaka wasu".
Cikin daƙilewa Jalal yace.
"Ok shine sai ya zaɓi ƴan ɗakinmu a matakan zakarorin gwajin dafi? Ya bawa Ya Jafar Galadima, yaga yadda aka medashi dare ɗaya, da rashi da bazamu samu madadinshiba a duniya, an cire hankalin mahaifinmu a kanmu, sannan ya kuma bawa Hamma Jabeer wani mulkin, salon a sabautashi kenan, nest target nasu kuna, wato a kanshi ne?".
Shiru sukayi jin Jabeer na cewa.
"Azzannu zambu walau kana haƙƙun, na haneku da irin waɗanan zantukan, babu wanda ya isa, ya cutar da wani sai Allah, domin shine mai rayawa, kuma mai kashewa, mai badawa, mai hanawa, mai cuta mai waraka. Ummi har kema, ya zakiyi ki zauna kina gaya musu hakan, to waye zai cutar damu, acikin ahlinmu, daga ƙannen mahaifinmu fa, sai ƙannen kakanmu, sai matasansu da jikokinsu, sai kuma ƴan uwanmu, dan Allah ku bar munanawa mutane zato."
Juwairiyya ce ta ɗan girgiza kai.
Shi kuwa Jabeer, cikin bada umarni yace.
"Juwairiyya jeki duba Ya Jafar, nasan zuwa yanzu ya tashi daga baccin."
To tace, kana ta miƙe ta nufi tsakiyar falon. da sauri ta tsaya tare da ɗan raɓawa gefe, sabida ganin Gimbiya Saudatu, na tsakiyar falon.
Da sauri ta ɗan rusuna tare da cewa,
"Barka da fitowa Gimbiya Saudatu".
Zama tayi bisa kujerar da Jabeer ke zama, ɗaura kafarta tayi ɗaya kan ɗaya.
Hadimanta, biyu ne suka zauna gefe da gefenta.
Fuskarta babu wata alamar annuri, sai tsantsar tijara, cikin isa da ƙasaita tace.
"Kai Jabeer!."
Ido Jakadiyarsu ta zazzaro cikin firgici da tsoro ta kalli Jabeer da a take fuskarshi ta sauya launi,
cikin rawan jiki da tsoro tayi ƙasa da murya tare da cewa.
"Jabeer ka amsa, Gimbiya Saudatu ce, da kanta."
Jalal ne da Jamil suka kalli juna, kana suka maida idonsu, kan Hamman nasu, da ya lumshe idonshi ya koma ya jingina tamkar badashi akeyi ba, kamar daga sama suka jiyo muryar Gimbiya Saudatu tana ratsa kunnuwansu.
"Kai Jabeer, ka fito kazo nan, ina nemanka".
Still bai buɗe idanunshi bama, bare ya amsa ko yunƙurin tashi,
sai dai laɓɓan bakinshi da suke motsawa yana maimaita sunan Allah a zuciyarshi da harshenshi.

Zuwa yanzu Gimbiya Saudatu tayi masifar kufula, cikin wani irin mugun kallo ta kalli Juwairiyya da jikinta ke baiyana tashin hankali ta, cikin isa da ƙasaita tace.
"Ke maza wuce, kije tun wancan karen larabawan da suka turo ahlin masarautun Fulɓe, dan samun damar maida masarautun a hannunsu, kice mishi yazo dan kan uwarshi".
Da ƙarfi Jabeer ya rumtse idanunshi, wani irin bugawa zuciyarshi ta farayi a saba'in.
Ita kuwa Juwairiyya kasa motsawa tayi daga inda take tsayen.
Ummi kuwa cikin firgici, ta kalli Jalal daya miƙe tsaye tamkar wanda aka tsabura.
Jiki na rawa ya ture kujerarshi, zaiyi baya ya fita ya nufi inda taken.
da sauri ya juyo cikin tarin zafin rai jin an riƙe mishi, hannunshi.
ganin Hamma Jabeer ɗinsune ya damƙi hannunshi ne ya sashi, taune lips ɗinshi da masifan karfi.
Jamil kuwa ido ya zubawa Hamman nasu yana ganin yadda jikinshi ke karkarwa, kowa ya sani duk duniya babu abinda yake saurin harzuƙa Sheykh sama da a zagar mishi iyaye Especially uwa! Haroon kuwa zuru yayi da idanu yana kallon ikon Allah.

Ummi kuwa cikin rawan murya da tsoro da firgici ta kallesu murya na rawa, tace.
"Dan Allah Jabeer, kaje, tashi muje ka amsa kiranta dan Allah badon niba, dan darajar Manzon Allah".
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin zubewa kan guiwowinta,
Jin kalaman da tayi mishi da gane nufinta na rusuna mushine ya sashi saurin miƙewa tsaye.
da sauri suma duk suka miƙe tsaye.
Gyara kekyawar al'kyabbar jikinshi yayi wacce take ta limamaice bawai ta sarautaba, jam hiraminshi yayi ya rufe sajenshi da kyau ya rage iya shatin fuskarshi dan yasan dole tazo da hadimanta mata.
Jalal ne ya tsaya gefen damanshi, kana Jamil a gefen hagunshi, Haroon kuwa na bayanshi, Jakadiyarsu kuwa tana gaba tanayi musu jagora.
A haka suka fara taki kan stpes ɗin sauƙowa daga kan dinning area ɗin, wani irin taku sukeyi mai cike da ƙasaita da kwarjini. Yana tsakiyarsu tamkar sarki da fadawanshi.
A haka suka nufo tsakiyar babban falon da ya kai wasu faluka huɗu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu, wani irin hushi da numfarfashi takeyi tamkar wacce tayi gudun fanfalaƙi,
cikin izaya da isa, take zaune bisa mazauninshi.
Tare da cewa.
"Ina karen Larabawan yakene, Dan kan uwark?".
Bata ƙarishe mgnar tataba, sabida ganinsu sun nufota gadan-gadan, wani irin kwarjini yayi mata,
wanda yasa ta haɗiye ragowar mgnar tata,
shi kuwa Sheykh Jabeer, cikin wani irin taku naƙasaita suka karaso tsakiyar falon.
Ido ta zuba musu kana cikin tijara tace.
"Me zaka zo ka tsaya min a ka, ka zauna inada mgna da kai".
Cikin wata iriyar dakekkiyar murya mai cike da ƙasaita yace.
"Ai ba sai kince na zaunaba, dama dole in zauna, tunda ni ba bawanki bane, bazan tsaya a kankiba, sabida Ni ba dogari bane".
Ido ta zazzaro woje alamun tarin mamaki, ajiyan zuciya ta sauke a ranta tace.
"Ehe mai jajayen kunnuwa, uwarka zanci".
Shi kuwa Jabeer, wani irin taku yayi mai cike da izza, bisa kujerar dake fuskantar wacce take zaune a kai ya zauna, da sauri ta tsareshi da ido tare da cewa.
"Kai ina sama kana sama, haka aka koya maka irin tasu tarbiyar ta larabawan kenan".
Ƙafarshi ɗaya ya ɗaura ya ɗaurs kan ɗaya, kana ya gyara zamanshi da kyau,
cikin muryar ƙasaita yace.
"Ki dena yimin ihu a kai, nan ba fadar masarautar waɗancan surutattun bane, nan fadace mai daraja masarautar Joɗa ce, kiyi hattara da lafuzanki, na baki mituna biyar daga cikin wunin yau gaya min damuwarki in baki mgninta".
Jakadiya dai gaba ɗaya jikinta rawa yakeyi.
Haroon kuwa, bayan kujerar da Jabeer ke zaune ya tsaya,
Jalal kuma yana gefenshi hakama Jamil.
Juwairiyya kuwa, tana inda take tun ɗazu.

Wani irin mugun kallo ta watsa musu, kana cikin zafi da azalzalar zuciya da jin tarin tsanarsu ta gyara zama tare da cewa.
"Naji yau an ganka ka fito ɗakin sirri na masarautar Joɗa kaida mai martaba Lamiɗo, me hakan yake nufi?".
Ba tare da ta gama rufe bakintaba yace mata.
"Ina ɗakin sirrin masarautar Joɗa akace miki na fito, ba ɗakin sirrin masarautar kuba na fito?".
Cikin kufula tace.
"Itama ɗin wannan masarautar ai tamuce, tunda ƴaƴanane manyan jikokin sarkin Nuruddeen, kuma babansune Galadima, shine kuka kasheshi, aka bawa wancan majanunin yayan naki mulkin Galadiman, to yanzuma kuma ɗan tsurfa da tsiri uwar me kukayi a cikin ɗakin sirrin? Me ya gaya maka? Me kuke shiryawa?".
Still harshenta ma bai gama komawa zaune ba ya jefa mata amsa.
"Ɗakin sirri mgnar sirri, tunda shi jakin daya kai miki rahoton, bai sanar miki me muka tattaunaba, Ni sai in miki jagora zuwa wurin Lamiɗo ki samu ki ganshi yanzu sai ki tambayeshi me yace min me mukayi, tunda kinsan in bani nai miki isoba sai ki kai sati nan gaba baki samu damar ganinshi ba".
Ya ƙarishe mgnar yana tsareta da fitinennun idanunshi wanda babu tsoro a cikinsu.
Cikin kufula tace.
"Ba girin-girin ba tayi mai, ta yaro kyau take bata ƙarko".
Amsa ya kuma bata.
"Surkin nakine yaron? Mutumin daya haifa miki miji, kika aura har kika haifi yayan da kike son su gajeshi, shine yaron? To asheko masarautar duk yarace, ke mulkarta, tunda nasan ko tsohonki bai kai, Lamiɗo ba".
Ohoho ina wuta ta faɗa ciki, cikin kausasa murya tace.
"Ina mai umurtarka da kada ka kuskura ka amshi wani mulkin daya wuce Garkuwa".
Cikin taɓe fuska yace.
"Anƙi bin umarnin naki".
Wani irin Murmushi mai baiyana jin daɗi da tarin Mamaki Haroon da Jamil sukayi.
Jalal da kanshi yau Hamma Jabeer ɗinsu ya shayar dashi tarin mamaki, ashe shi nashi ƙarfin halin da ake gani wasane, ga Jarumin da jarumtarsa ta girgiza, zuciyar Jalal. Dan harga Allah shi dai ya sani bazai taɓa iya yiwa Gimbiya Saudatu abinda Haammanshi keyi mata yanzuba, ashe dama haka yake, da kafiya da bada amsa tun kafin ta huta. Muryar Gimbiya Saudatu ce ta kuma katse mishi tunani.
"Yanzu bakinka ke iya furta ka haka,, yaro zakaci kan uwark".. da sauri ta zaro mishi ido jin yace mata.
"Kul kada ki ƙarasa, in kuwa kikayi gangancin ƙarasawa, zan". Katseshi tayi da cewa.
"Zakayi me? Gaya min isshe ɗan fitsara me zakayi".
Jalal ne ya amshi zancen da cewa.
"Zan datse miki harshe, kika kuma zagar mana uwa".
Cikin tsananin tsana ta watsawa Jalal harara tare da cewa.
"Zaka aikata! Babu musu! Menene ɗan giya bazai iya yiba, menene, ɗan iska ɗan daba bazaiyiba, banza ɗan sara suka, gwada datse min harshen ka gani, in akwai wanda zai rage da harshe a zuriyar uwarku".
Jabeer ne ya ɗan taune leɓenshi tare da kaɗa mata yatsa kana yace.
"Kulfa, ki raba kanki da zagin mace mai daraja".
Cikin isa da ƙasaita tayi wani irin dariya, kana ta miƙe tsaye, gabansu ta ɗan matso kana cikin izaya tace.
"Eh daraja ko? Uhummm lallai kam, aifa sai dai mace mai daraja."
Sai kuma ta ɗan ja da baya kana tace.
"Mace mai daraja ko mai zunubi, ai dai kun fara ganin sakayyar Allah tun a duniya, waya san metayiwa ubangiji, y...."
Juwairiyya ce, tasaki wani irin ƙara da yasa duk sukayi shiru.
Ita kuwa ta faɗi kasa a sume alamun makaranta sun dawo.
Ganin haka yasa Jakadiyarsu tayi kanta da gudu.
Ita kuwa Gimbiya Saudatu murmushin jin daɗi tayi tare da cewa.
"Haka dai. Duk a haka zaku ƙare, mulki kuwa sai dai ku ga anayi, GARKUWAN da aka bakanma, zakaga me zai sameka dashi".
Tana faɗin haka ta juya ta nufi hanyar fita Hadimanta na biye da ita a baya.
Shi kuwa Sheykh Jabeer murya ya ɗan ɗaga a hankali yadda zata iya jinshi yace.
"Babu abinda zai sameni face dama Allah ya ƙaddara zai sameni, domin baki isa ki cutar daniba".
Cikin harshen fillanci tace.
"A laran ai, zaka gani ai".
Bai kulataba.
Ita kuma fita tayi.

Jalal da Jamil kuwa, zama sukayi gefenshi, suna mai bin kofar fita da ido.
Haroon kuwa cikin rudu da ɗaure war kai yake mgnar zuci.
shin wai wannan wacce iriyar fitinenneyar masarautace, mai cike da tsarƙaƙiya, yanzuma dama a irin wannan yanayin Jabeer ke rayuwa da ƙannenshi da yayanshi da mahaifanshi.
To meyasa, bazasu bar musu masarautarba, tunda shi Jabeer bama son wannan mulke-mulken yakeba.
Sassanyan zazzaƙar Muryar Sheykh Jabeer ne ta katse mushi nazari, jin yana rere karatun Alqur'ani cikin nitsuwa yake, karanta fatiha.
Bayan ya kai ƙarshenta ya kuma yi bisimilla, ya fara Suratul Baqra, wanda yakeyi da ɗan ƙarfi, tare da fuskantar inda Juwairiyya ke kwance,
Yanayin karatun cike da taƙawa da kekyawan tajwid, shiyasa in ya fidda wani harafin kamarsu Khah sai kaji har ƙasan wurin yana amsa amon sautin."
A hankali Juwairiyya ta fara buɗe idanunta, tana mai bin karatun da takejin,
Cikin sauƙe ajiyan zuciya Jakadiyarsu tace.
"Alhamdulillah Jabeer ta farfaɗo".
Ta faɗi hakane sabida tasan duk sansa Juwairiyya ta faɗin in dai zai mata Rugyag rufe idonshi yakeyi.
Jin Jakadiyarsu tace ta farfaɗo ne, tasashi, yin hamandala tare da cewa, Jakadiyarsu ta meda Juwairiyya Side ɗin ta, kana ya kalli Jalal tare da cewa.
"Jalaluddin kaje, ka kula da Ya Jafar, ka bashi abinci kana ka shirya shi, shirin zuwa sallan jumma'a kaima kaje ka shirya."
To sukace kana duk suka fita. har sunje bakin ƙofar fira yace.
"Jalaluddin kasa kayan mutunci".
Cikin sanyi yace.
"To". Sannan suka fita.
Kanshi ya ɗan juya ya kalli, Jamil, tare da cewa.
"Ka gyara mana bedroom."
Yana jin haka ya miƙe ya nufi bedroom ɗin.
Shi kuwa Haroon ido ya zuwa Jabeer, sabida gaba ɗaya muryarshi ta tabbatar musu, yana cikin tsananin ɓacin rai, kai Haroon ya jinjina ganin Jabeer yasa hannu ya janye hiramin dake kanshi, ya taune lips ɗinshi, kana ya rufe idanunshi, cikin ƙarfi yasa hannunshi ya fara jan bakin hiramin , da yake sabo fil janshi yakeyi alamun zai yagashi.
Shiru Haroon yayi baiyi yunƙurin hanashi ba, domin dama yasan za'a rina, sabida shi Jabeer wannan itace babbar alamar tsananin ɓacin ransa, muddin fushinsa ya hauhawa to, yakan yayyaga abu da karfi.
Fass haka Haroon yaji sautin, yagewar sabon hiramin nan.
Shi kuwa Jabeer idonshi ya ƙara rumtsewa yanayi mai ci gaba da fatattaka hiramin.
Murmushi Haroon yayi cikin tare da fara ɗaukar shi video.
Yanayi dan tsokana.

A can sashin Hajia Mama kuwa, ganin shiru-shiru Jabeer bai shigo bane, kamar yadda ya saba in yayi tafiya ya dawo yakan,
Batul kuwa, ta gaza zaune ta gaza tsaye, ta ƙenƙesa ado da kwalliya tamkar mai zuwa gasar kyau.
A karo na barka tai ta kalli Hajia Mama, cikin zaƙuwa tace.
"Yakura, muje, side ɗinshin mana, mu duba lfy kuwa har yanzu bai shigoba."
Ajiyar zuciya Hajia Mama ta sauke, tare da miƙewa tace.
"Muje Batul ni kaina, na banyi zaton zai kai iwar haka bai shigoba, dole akwai abunda ya tsareshi".
Da haka suka fito, suka nufi sashin Jabeer ɗin.

Kasan cewarta matsayin uwa, yasa sam bata da hijabi da sashin, haka yasa, sarkin ƙofar na ganinta suka rusuna tare dayi mata kirari kana ta wuce.

A falon suka samesu, zaune.
Haroon ya tasashi gaba da kallo da wayarshi, shi kuwa Jabeer, idonshi a rumtse, bakinshi na motsawa a hankali, yana maimaita, tasbihen daya zame mishi abokan rayuwa.
Kana hannunshi nata yage sabon hiraminshi.
Haroon ne ya amsawa Mama sallamarta, tare da cewa.
"Barka da fitowa Hajia Mama".
Da sauri ta ƙarasa gabansu, kujerar dake kusa dasu ta zauna,
cikin tarin kula tace.
"Haroon da kai ake tafe kenan? Ya yar uwata, yaushe ka dawo?".
"Haroon lfy kuwa me akayiwa Jabeer? Waya taɓa minshi? Waya taɓo ɗan lelen Umaymah'nshi Da Sitti'nshi?".
Cikin lumshe ido Haroon yace.
"To Hajia Mama wacce tamɓaya ɗaya zan amsa miki, ta ƴar uwarki ko ta ɗan rigimarku, mutun in yayi fushi sai yayi ta yage-yage, wannan in ya samu dama in yayi fushi ya samu ya damƙi ƴar mutane a hannunshi tabbas zai yageta, dan ko namiji da kyar zai iya ƙwatar kanshi".
Murmushi mai cike da kulawa tayiwa Haroon kana,
ta kalli Batul da zauna gefenta, ta zubawa Jabeer idonu tamkar zata cinyeshi ɗanye,
wani irin sonshi da ƙaunarshi takeji, jiki da zuciyarta,
Kekyawan sumar kanshi ta zuwa, idanu a hankali ta dawo da idon kam tattausan sajen da yayi fuskarshi ƙawanya, har kan gashin gemunshi da ya kai kamu ɗaya, yayi baƙi sitib dashi ya konta lib sai sheƙi yakeyi, jajayen laɓɓan bakinsa, da suke motsawa ne ta zubawa kwayar idanunta.

Shi kuwa Sheykh Jabeer, sanadin tasbihin da yakeyi ne, yaji zuciyarshi tayi fes,
fushin da yakeji duk ya kau. A hankali yakejin tsikar jikinshi na amsa sautin yam-yam tana sanar mishi ana kallonshi.
Yunƙurowa yayi ya tashi zaune, kana a hankali ya fara buɗe idanunshi.
Da sauri ya kauda ƙwayar idanunshi sabida ganin kwayar idanun Batul cikin nasa,
Hajia Mama kuwa, cikin sanyi tace.
"Innallaha ma'assabirin".
Idonshi ya kuma lumshewa, wannan abu shike ƙara sashi jin ƙarfin guiwar zama cikin masarautarsun. Sabida yayi dace, da uwar da take ƙara bashi tarbiyar da yasan itace dai-dai tana danne dukkan baƙin cikinta, domin ta sama mishi nitsuwa. Duk da kasancewar shi malami.
Tana ƙara nusar dashi.
A hankali yace.
"Barka da safiya Mama".
Murmushi tayi kana tace.
"Barka dai, Muhammad Jabeer. Garkuwa mai nagarta,
Yau na tashi da tsantsar farin ciki , tunda maji muryarka da asuba, meya ɓata maka rai daga dawowa?".
Cikin sanyi yace.
"Babu komai Mama, Sheykh Abdulkareem, da ahlinshin duk sun gaisheki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Tsoho mai ran ƙarfe, kakanmu bawan Allah, yana lfy ko?".
"Alhamdulillah". Yace mata, yana mai sa hannu ya ɗauki hular da Jamil ya ajiye a kusa dashi ya ɗaura a kanshi, sabida wani irin kallo da yaga Batul nayiwa suman kanshi.
Ita kuwa Batul ido ta ɗan lumshe, ganin yadda ya tamƙe fuskarshi ya watsawa gefen da take kallon, ƙasaita.
A hankali ta buɗe idonta kana ta sauƙesu kan sajenshi,
Wani gajeren tsaki yaja,
tare da kauda fuskarshi.
Ita kuwa Butul mgnar zuciya takeyi.
"Masha Allah, Ya Jabeer, komai kayi kyau kakeyi, ya Allah ka tabbatarmin da mafarkina mana, wannan kekkyawan bawa naka ya zamo mijina, domin shine mijin daya dace dani, mijin kece raini da nunawa sa'a, Uhumm jin kai da ƙasaita ba, kayi naka, kafin ka shigo hannuna, in sha Allah, sai na zama sarauniya ka zama bawana."
A hankali tace.
"Ya Jabeer ina kwana".
Shiru yayi kamar bai jitaba,
Allah ya sani ya tsani kallo a rayuwarsa ta duniya, baya kuma son mace, da rashin kamun kai.
Hajia Mama kuwa ganin yadda ya takurene yayi kici-kici da fuska, yasa ta ɗan, kalleshi tare da cewa.
"Jabeer Batul ke gaidaka, itama jiya tazo".
Kanshi ya ɗan rusunar tare da miƙewa tsaye, cikin sanyi yace.
"Masha Allah".
Daga nan ya ɗanyi taku biyu zuwa uku, kana yace.
"Mama barin inje inyi shirin jumma'a".
Murmushi tayi tare da cewa to. Dan ta fahimci zillewa yakeyi.

Daga nan shi dai yayi, ciki.
Su kuma suka, fita.

Haroon kuwa Data ya kunna,
Umaymah ya turawa video ɗin da yayiwa Jabeer da yana cikin fushin.


A can Rugar Bani kuwa, yau tun safe, su Shatu suka baro asibitin, sabida, matasan mayaƙan cikin garin Shikan ɗin sai kai komo sukeyi, cikin asibitin. kana sai zuwa sukeyi maja'iunsu, suna mitin.
Bisa dukkan alamu, sunada wata manufa, ganin hakane, yasa likitoci musulmai, suka bada shawarar a kwashi marasa lfyar a medasu cikin asibitin babban birnin Ɓadamaya, sabida su nan babban likitansu ya hanasu duba kowa.

Da wannan shawarar ne, aka kwashi duk marasa lfyan da taimakon yan agaji aka shiga dasu cikin Adamawa.
Dan an fara rade-raɗin wai fulanin Rugar Bani sunce zasu ɗauki fansa, to shisa ƙabilar ɓachama suma suketa guzurutsoma, har ta

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment