Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta suma amman wannan Shegen yaron duk abinda nayi a kanshi ko matarsa yanzu dama yar tashi abun baya tasiri.
Sannan babban tashin hankali na, shima Sarkin al'adun suna bai dawoba.
Kuma wayarshi na shiga baya ɗagawa, tsorona kada dai sun ganeshi".
Cikin sauya muryarsa ih zuwa muryar Jahan yace.
"A a ba dai kamashi ba kam, sai dai ko in yana jin tsoron amsa kiran nakine sabida kada kiyi mishi faɗa tunda ƴar bata rasuba kada kice bai iya aikinsa bane a ganina fa shine yasa baya amsa kiran naki".
Cikin tashin hankali tace.
"Ni babbar matsala ma yau tunda gari ya waye hankalina yake a tashi zuciyata na tsinkewa gaba ɗaya tsoro ya rufeni ji nakeyi wani mugun abu yana tunkaro rayuwata, naje gidan boka kuma ya koroni shima sai tsalle yakeyi yana kaɗe jikinsa
Wai komai na gab da dawo mana".
Murmushi mai cike da jin daɗi yayi a ransa yake zaton ko shiryace zata zo mata, haka yasa yace.
"Sai gobe zanzo muyi mgn in kaiki gidan wani sabon boka".
Da sauri tace.
"To".

Daga nan ya katse kiran.
Kana ya miƙe ya fito falo, a hankali ya kalli Jalal da Hibba tare da cewa.
"Jamil fa".
"Yana Part ɗin mu".
Jalal ya bashi amsa".
To yace kana ya juyo ya kalli Yah Jafar da yanzu ya shigo kenan.
A hankali ya tsaya gaban Sheykh.
A hankali suka lumshe idonsu a tare, da sauri Sheykh da Jalal da Hibba suka matso kusa dashi sosai jin yana cewa.
"Jabeer zuciyata na tsinkewa tun jiya sai inji kamar wani abu zai faru".
Cike da mamaki Jalal yace.
"Wlh nima tun jiya zuciyata ke tsinke kirjina yaita bugawa".
Wani irin rumtse ido Sheykh yayi tare da cewa.
"Nima abinda naketa fama dashi kenan tun jiya, to da Aisha ta suma sai nai zaton ko abinne ke samin tsinkewar zuciya.
To kuwa still abin bai bariba saima ƙaruwar da yakeyi yana tsananta".
Cikin sanyi Hibba tace.
"To kuyi ta addu'a hakama Umaymah da Mamma da Aunty Rahma sukace suna ji".
Kai suka gyaɗa gaba ɗaya.
Hannun Yah Jafar ɗin Sheykh yaja suka nufi Part ɗin su Jamil.

Su kuwa su Jalal zama sukayi suna kallon Ishma da Junainah daketa sabgoginsu.

A hankali Sheykh ya zauna tare da kallon Jamil dake zaune tsakiyarsu Giɗi a hankali yace.
"Ka barsu su huta mana".
Cikin sanyi Jamil yace.
"Allah ko Hamma Jabeer ina so in tafi wurin Khadijah ma sai inji zuciyata na tsinkewa kamar dai zan samu wani abu".
Cikin kula Sheykh yace.
"Uhmm duk haka mukeyi kaita mai-maita innalillahi wa innailaihi rajiun".
To yace.
Shi kuwa Sheykh nitse ya kalli Gaini da zai kai sa'an Affan.
Cikin kula yace.
"Sannunku da hanya".
A tare sukace sannu.

Jamil ne ya ɗan kallesu tare da cewa.
"Shine babban yayanmu Sheykh da yasa aka fito daku".
Da sauri suka ɗan gyara zama suka matsoshi tare da cewa.
"Allah sarki bawan Allah mun gode Matuƙa Allah ya saka da al'khairi ya kula da ahlinka fiye da yadda ka kula damu".
Cikin jin daɗi yace.
"Amin ya rabbil izzati, amman kuma duk haka ya farune sanadin Sulaiman da aka rufeshi tare daku".
Cikin gamsuwa sakace.
"Ayyah".
Sai kuma Giɗi ya ɗan share hawayen da suka zubo mishi tare da cewa.
"Ayyah bawan Allah yaushe zamu koma Rugar Bani muga Bappa da Inna da Ummey da Shatu da Junnu".
Cikin gamsuwa da tausayinsu Sheykh yace.
"In sha Allah nan kusa amman nafi son sai naga kunyi aski kun ƙara hutawa, gobe zuwa jibi da kaina zan medaku".
Cikin wani irin masifeffen jin daɗi sukace.
"Allah ya kaimu".
"Amin Amin". Yace kana ya musu sai da safe.

Daga nan wurin Abbanshi da Lamiɗo da Galadima yaje suka ɗan yi wata mgnar kana ya dawo.

Ranar dai haka suka kwana gaba dayansu babu wanda yayi isasshen bacci sabida masifar bugawa da ƙirazansu keyi.


A can Rugar Bani kuwa.
Ko abincin dare Ummey bata iya ciba.
Haka nan sai taji zuciyarta na tsinkewa yana bugawa.
Tun abun bai damunta har ta gayawa Bappa, so ya bata ƙarfin guiwa da yin addu'a.


*Ba'ana*
Zaune yake gaban yaransa cikin rauni da yanayin damuwa yace.
"Nanda wata uku masu zuwa zan koma ƙasar Nigeria zanyi yaƙin neman Shatu koda zan rasa rainane, zan koma gareta.
Zan gaya mata ko mutuwa nayi sonta ne ajali na".
Cikin bashi ƙarfin guiwa ɗaya daga cikinsu yace.
"Zama kayi nasara".
A hankali yace.
"Babu tabbas, domin tunda na rasa Shatu nakega nayi rashin babbar nasara".
Sai kuma ya miƙe ya shiga cikin ƴar ƙaramar bukkarsa.

Murmushi Baron yayi tare da katse kiran da yayi Sheykh yana jin duk bayanan Ba'ana.
Dan shi Baroon yanzu ya zama ɗan aikin Sheykh dan tun zuwansa lokacin ciwon hannun Shatu.
Da fari har yasa a kirasa daga baya yasa aka dawo dashi.
Ya biyashi kuɗi masu tarin yawa, yayi mishi duk bayanin ɗaya nema, kana yasashi ya koma wurin Ba'ana kuma ya naɗo mishi rahoto da duk wani motsin Ba'ana yana turo mishi.
Alhamdulillah kuma yanzu duk shirin kama Ba'ana yakeyi.

Washe gari ranar asabar yau babu aiki.
Da misalin ƙarfe goma na safe jirginsu Abboi ya sauƙa cikin birnin Ɓadamaya.

Kai tsaye Salmanu yayi musu jagora zuwa Rugar Bani dan a take suna sauƙa wasu tsala-tsalan motoci guda biyar suka iso wanda dama su tun jiya suka iso.
A ƙasan plate number motocin akwai tambarin hatimin kan shanu a ƙasa ansa Abboi, irin tambarin dake jikin jiragen Abboi kenan.

Suna zuwa kuwa babu ɓata lokacin suka isa har cikin gida.
Inda nan Arɗo Bani da kanshi da sauran dattawan sukazo.
Bayan sun gaggaisane Abboi ya ɗan yi gyaran murya tare da cewa.
"Toh Alhamdulillah lallai komai yayi forko to tabbas yana da ƙarshe, to bayan bincike da bin diddigi dai mun gama fahimtar inane asalin wannan baiwar Allah'n kuma munada yaƙinin daga masararutar Joɗa ta fito.
To yau dai kam ranar data kamata mu shiga da ita ciki da yardar ubangiji tazo.
Kamar yadda muka tsara, yanzu zamu tafi".
Cikin tsananin jin daɗi da kuma fargabar ko ya al'amarin zai kasance Bappa yace.
"Alhamdulillah mu duk a shirye muke, fatanmu Allah yasa ina munje ta tuna baya, ta tuno ita wacece".
Da sauri Arɗo Bani yace.
"In Sha Allah ma zata tuna Malam Babayo".
"Allah yasa haka".
Al'ameen ya faɗa.
Amin Amin sukace kana duk suka miƙe suka fito.

Kana Bappa yazo yacewa Ummey da Dedde su fito.
Nan suka mara musu baya.

Mota ɗaya Bappa da Abboi da Arɗo Bani suka shiga.
Ummey da Dadde da Al'ameen kuwa suma mota ɗaya suka shiga.
Sauran kuma ƴan tsaronsu ne a ciki sai motar Yah Salmanu da Hafsi ƙanwar Shatu a haka suka fito daga Rugar Bani suka nufi Masarautar Joɗa.

A hankali Ummey ta jingine kanta da jikin kujera tare da dafe ƙahon zuciyarta a hankali ta furta innalillahi wa innailaihi rajiun".
Sabida tsananin tsinkewar da zuciyarta keyi Dedde kuwa hankalinta naga makiyayan dake zirya.


A nan cikin birnin Ɓadamaya a tsakiyar Masarautar Joɗa kuwa.

Gaba ɗaya su Umaymah suna falon Shatu.
Aunty Rahma ce da su Sara a kitchin, Aunty Juwairiyya tana part ɗinta da Hibba.

Junainah da Ishma kuwa suna kitchen tare da Aunty Rahma.
Kowa sabgar gabansa keyi.
A hankali Shatu ta miƙe ta nufi ƙofar falon Sheykh da sallama a bakinta.

Shiru ba kowa a falon tray'n breakfast ɗinshi shida Haroon ta ajiye bisa Dinning table.
Ganin ba kowane yasa ta turo kanta cikin bedroom ɗin.

Shiru ba kowa a hankali ta ƙara so ciki tana cewa.
"Salam Yah Sheykh". Ƙofar bathroom ta matso a hankali ta tura ba kowa a ciki komai yana kimtse tsab-tsab.
"Toh ina yaje kuma yau Lahadi kuma ai babu inda zaije".
Shiru tayi tare da juyowa ta matso tsakiyar ɗakin jujjuya kanta tayi ba mutun ba alaman mutun a ɗaki.
Har ta juya zata fita, sai kuma tayi sauri ta juyo tazo bakin gadonshi, abun data hanƙo ƙasan pillow'nshi ne yasa ta sunkuyowa da sauri hannunta tasa ta zaronshi.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Ta faɗa jiki na rawa tare da sakin fuskar robar da Sheykh ake amfani da ita a matsayin Jahan.
Da sauri ta juyo da nufin zata fita, sabida tsoron daya rufeta.
Sai kuma tayi sauri taja da baya tare da zare idanunta dai-dai lokacin da ta iso jikin marfin wodurob ɗin sa
Wanda yayi dai-dai da lokacin da Sheykh ya turo marfi ya fito.
A gigice take jujjuya kai tare da zaro ido.
Sai kuma ta juya da sauri ta kalli fuskarnar da ƙarfi ta buɗe baki tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun Yah Sheykh".
Da sauri yasa hannunshi ya kamo nata ya fizgota jikinshi cikin haɗe fuskarsu wuri ɗaya yace.
"Na'am Aysha please kada kiyi ihu tsaya nitsu nine Muhammad Jabeer Yah Sheykh mijinki Abu Afreen".
Cikin yanayi kaɗuwa tace.
"Yah Sheykh kai mutum ne ko al'jan".
Da sauri ya kamo hannunta suka iso gaba durowar.
Buɗe ƙofar yayi, kana a hankali yasa hannunshin ya ture, al'kyabbas ɗin shi dake jere a hanga a saƙale, sai ga wani ƙofa mai kamar glass.
A hankali yace.
"Aysha nitsu ki jini kinji ko".
Cikin sauƙe numfashi tace.
"Toh".
Kanshi ya gyaɗa kana a hankali yace.
"Kinga wannan wurin ko?".
Da sauri tace.
"Eh naga kamar ƙofa ne".
Jawota yayi suka ɗan matso hannunshi yasa ya tura ƙofar da sauri tace.
"Lahh".
Sabida ganin wata ƴar siririyar hanya mai tsawo.
A hankali yace.
"Ni mutum ne Aish yanayin tsarin masararutar Joɗa ne yasa dole nake amfani da wasu ababen.
Kinga wanan hanyar har cikin bedroom ɗin Lamiɗo da Abba na duk akwai su.
Muna haɗuwa dasu a ɗakin Lamiɗo lokuta da dama.
In kina so anjima zan nuna miki, dan yanzu Lamiɗo ya rufe ƙofarsa ne da yanzu zamuje".
Da sauri tace.
"Me kukeyi a ɓoyen".
Jawo ƙofar yayi ya rufe kana a hankali yace.
"Ina wani aikine Aish Kuma aikin sirrine, tsawon shekaru inayi babu wanda ya sani sai Lamiɗo da Abba na da Umaymah sai yau kuma da kika zama ta uku".
Ya ƙarashe mgnar yana jawota suka zauna bakin gado.
A hankali ta sauƙe numfashi ido ta zuba mishi a hankali tace.
"Kai SS ne ko Yah Sheykh?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ba'a faɗa kiyi shiru kada wani yaji kinji ko sirri ne Boɗɗo na".
Murmushi mai cike da jijjina tayi mishi.
Shi kuwa ruggume ta yayi ya koma baya ya kwanta.

Dai-dai lokacin kuwa motar Salmanu dake gaban motocin su Abboi ta kusa kai cikin matsarautar Joɗa bayan an wangale musu gate.

Wani irin rumtse ido da ƙarfi Ummey tayi tare dasa kanta bisa guiwowinta sabida wani irin masifeffen tsarawa da kanta yayi da azaban ƙarfi.

Kai tsaye bakin part ɗin su Sheykh Salmanu ya nufa dasu sai dai Motar Abboi da sauran duk a can baya bakin fada suka tsaya inda Bappa ya nuna musu.

Yadda suke ƙara kusanto Part ɗin su haka sarawa da bugun zuciyar da Ummey keyi yake ƙaruwa.

A can cikin falon Shatu ma, da sauri Umaymah da Mamma Suka kalli juna sabida masifar bugawa da ƙirazansu sukayi.

Sheykh kuwa da ƙarfi ya ruggume Shatu sabida ji yayi tamkar zuciyarsa zata faso ƙirjinsa ta fito woje.
Jalal da ke Part ɗin Yah Jafar da sauri ya rumtse idanunshi shida Yah Jafar ɗin.

Hakama Jamil dake tare dasu Gaini.

A hankali motocin sukayi parking.
Ummey kuwa wani irin ƙara rumtse idanunta tayi da masifan karfi.
Dedde kuwa a hankali ta buɗe ƙofar.
Ta sako ƙafarsa cikin shigarta ta al'farma.

Shi kuwa Al'ameen da sauri ya zagayo ya buɗe wa Ummey kofar tare da cewa.
"Ummey mun iso bismillah".
Cikin tsananin danne sarawar da kanta keyi ta ɗago jajayen idanunta a hankali ta zuro ƙafafuwan woje.

Ras ras Din dab din dab haka zuciyarta ta bada wasu tagwayen bugu.
Da sauri tasa hannunta ta dafe ƙirjinta.
Dedde kuwa a hankali ta zagayo inda take.
Shi kuwa Al'ameen a hankali yace.
"Bismillah ku shiga ga ƙofar".
A hankali Dedde tace to kana ta nufi ƙofar.
Ita kuwa Ummey cikin rawan jiki ta ɗaga ƙafarta ta dama ta ɗaura kan barandar tare da ƙara dafe ƙirjinta da rumtse idanunta sabida jujjuyawan da kanta ya fara.
Shi kuwa Al'ameeen bayansu yabi.

Shi kuwa Salmanu a hankali ya kalli Hafsi ƙanwar Shatu dake bin Khadijah.
Cikin yin ƙasa da murya yace.
"Ko in ɗagaki ne in kaiki".
Cikin jin kunya tace.
"A a Yah Salmanu zan shiga da ƙafata".

Su Bappa kuwa Sarkin ƙofa ne yayi musu iso zuwa cikin fada.

A hankali Dedde ta kai hannunta ta kama handil ɗin ƙofar falon ta murɗa tare da turawa kana tasa ƙafarta ta dama ciki bakinta ɗauke da sallama.

Aunty Rahma dake fitowa daga kitchen Junainah na biye da ita da sauri ta ɗan juyo ta kalli Dedde tare da cewa.
"Wa alaikassalam".
Ta ƙarashe amsa sallamar tana matsowa dan ganin wani irin fitinenne kama da Dedde keyi da Shatu.

Da sauri ta juyo bayanta jin Junainah na cewa.
"Lah Oyoyo Dedde".

Dai-dai lokacin kuma Ummey ta ƙarasa shigowa ciki wanda hakan yayi dai-dai da bugawar da kanta yayi wanda saida tayi sauri sa hannunta duka y ta damƙe kanta da masifan karfi tare da cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun".
Da ƙarfi wanda haka yasa Dedde juyowa ta fuskanceta sanadin juyawar da Dedde tayi kuma ya bawa Aunty Rahma da Junainah damar ganin fuskar Ummey da kyau.
Wani irin sauri Junainah tayi ta nufi inda suke ganin yadda gaba ɗaya jikin Ummeynta yake karkarwa da tsuma.

Aunty Rahma kuwa cikin wani irin tsananin firgita da kaɗuwa ta zazzaro idanunta waje har kamar zasu faɗo.
Wani irin taku mai cike da firgici tayi tana matsowa gaban Ummey dake jujjuyawa tana mai-mai-ta.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahiwani'imanwakil".
Wani irin matsowa kusa da ita Aunty Rahma tayi tare da buɗe baki da ƙarfi tace.
"La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallama. Aunty Mamey!."
Ta ƙarashe kiran da azaban ƙarfi da rakaɗi.
Ummey kuwa.
Kiranta da Aunty Rahma tayi yasata ƙara gigicewa.
Karkar haka jikinta ke rawa.
Cikin wani irin gigitaccen murya Aunty Rahma ta fara rabkawa ahlinta kira.
"Umaymah! Mamma Jazlaan ga Aunty Mamey ta dawo da izinin ubangiji Jazlaan, Jafar, Jalal, Jamil, Umaymah. Kuzo ga Aunty Mamey...".
Wani irin azabebben zabura...!





Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k ne kacal zaki turo ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Normal group Kuma 300 zaki turo ta asusuna ɗin sai kuyi screenshort na Debit Alert din ku turo min ta whatsApp 09097853276.




By
*GARKUWAR FULANI*
[4/2, 7:40 AM] +234 806 559 0880: Cikin tarin kaɗuwa Umaymah, Mamma, Ummi, suka kalli juna tare da yunƙura suka tashi a tare.
Sabida jin kalmar da Aunty Rahma ke mai-maita wa, da tsananin ƙarfi da karaɗi.
A guje suka nufo falon sabida jin yadda take ƙara auna musu kira babu ƙaƙƙautawa.

Jalal da Yah Jafar da Aunty Juwairiyya dake Part ɗin su kuwa, suma da ƙarfi suku mimmiƙe tsaye, tare da juyowa suka nufo Part ɗin Sheykhhhh.

Dedde kuwa da sauri ta matso kusa da Ummey da nufin sa hannunta ta tallabeta, cike da al'hini al'amarin.

Junainah kuwa da gudu ta iso gareta tare da da faɗa wa jikinta ta ruggume sawunta tare da sakin kuka da ƙarfi sabida ganin yadda gaba ɗaya jikinta ke karkarwar.

Sheykh kuwa da Shatu kafin kiran Aunty Rahma tayi mgnarta ta forko ruggume da ita yayi da kyau tare da cewa.
"Uhmmm kin san ko wanni sirri nawa, har na aikina da yake sirri amman ni kin gaza fitowa fili ki nuna min waye Bappa a wurinki waye Abboi a gareki".
Hannun tasa ta ɗan shafa sajenshi ta buɗe baki da nufin yin mgn kenan suka tsinkayo. Muryar Aunty Rahma.

Wani irin tsinkewa da bugawa zuciyar Sheykh tayi da masifar ƙarfi wanda hakan ya haddasa wata iriyar fitinenneyar karkarwar zuciya da jiki, da ƙarfi ya sake rumtse idanunshi tare da sa yatsunshi cikin kunnuwanshi ya jijjiga sabida jin abin yakeyi kamar gizo.

Junainah kuwa wani irin masifeffen kuka tasa mai cike da rauni tare da yayyarfa hannunta murya a hargitse tace.
"Wayyo Adda Shatu! Adda Shatu zo kiga Ummeyn mu bata da lfy Adda Shatuuuu".
Tayi kiran da masifan ƙarfin.
Ganin yadda Ummeyn ta tureta tare da jujjuyawa a tsakiyar falon kamar irin wacce hajijiya ke juyawa haka take tafiya tangal-tangal.

Wani irin zabura Shatu tayi wanda yayi dai-dai da lokacin da Mamma da Umaymah da Ummi da suka fito yanzu suka haɗa baki wurin cewa.
"La ha ila ha illahu Muhammadu Rasulullahi Sallallahu alaihi Wasallam".
Sai kuma gaba ɗaya jikinsu ya saki wani irin masifeffen karkarwa da sakewa ya rufesu.
Suka kasa koda ɗaga sawunsu bare su matsa inda suke.
Sabida tsananin kaɗuwa.

Ita kuwa Shatu tsalle ɗaya tayi ana biyu sai gata a bakin ƙofar Bedroom ɗinsa.
Cikin gigita shima ya yunƙuro da ƙarfi ya mara mata baya, sabida yadda yake jiyo falon a hargitse.

Gudu ya farayi ganin yadda Shatu ta fice a guje sabida ihun Junainah da take jiyowa.


Da sauri Yah Al'ameen ya sako kansa cikin falon jin muryar Junainah da abinda take cewa.

Yah Jafar da Jalal da Aunty Juwairiyya na biye
dashi a baya.

Cikin matsanancin tashin hankali Shatu ke kallon Ummey dake tsaye acikin tsakiyar falon, tana me riƙe da kanta dake juya mata sosai, ko mai bibbiyu take ganinsa, hakan yasa numfashinta soma ƙoƙarin ɗaukewa, take kuma idanunta suka rufe rub, hakan yasa ta-ta-fi luuu zata faɗi.

Da wani irin sauri mai haɗe da gudu Shatu da hankalinta yakai ƙololuwa wajen tashi ta ƙarasa wajen da Ummeynta ke tsaye, hakanne kuma yasa Ummeyn ta faɗa jikinta.

Hannayenta duka biyu tasa ta rungume Ummeyn tare da fara jinjigata cikin kiɗima da gigita, cikin muryar kukan da yazo mata lokaci ɗaya ta shiga faɗin.

“Innalillahi Wa’inna ilahirraju’un.
Ummeyna Ummeyna maiya sameki? Ummey ki tashi dan Allah, ki buɗe idanunki!!!”.
Ta ƙare maganar nata cikin matsanancin kuka, tare kuma da sanya hannayenta ta shiga girgiza Ummeyn da ƙarfi.

Sheykh kuwa dake tsaye ganin fuskar matar da Shatu’n nasa ke kira da sunan Ummey ne yasa shi, jin wani irin abu ya daki zuciyarsa da ƙarfi, wanda hakan yasanya shi jin ƙafafunsa sunyi masa nauyi, lokaci ɗaya kuma wani irin rauni ya cika zuciyarsa, wanda har hakan yasa yaji wasu irin ƙwalla masu ƙuna suka bayyana acikin idanunsa.

Ahankali ya ɗan soma taka ƙafafunsa tare da ƙarasawa wajen da Shatu da kuma Ummey'n suke.

Durƙusa guiwowinsa yayi aƙasa a dai-dai lokacin daya iso wajen da suke, cikin wani irin yanayin dake fusgansa, ya shiga ambaton sunan Allah, a dai-dai lokacin daya sanya duka hannayensa biyu ya rungumo Shatu da kuma Ummey’n jikinsa.

Cikin wata irin sassanyar muryarsa wanda amo da kuma sautinta baya bayyana ya shiga faɗin.
“Subahanallah!. Alhamdulillah!! Hasbunallahu wani’imal wakil, innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, la haula wala k’uwwata illa billahil aliyil azim!!”
Sune tasbihan da yaketa mai-mai-tawa
Shatu dake kuka kuwa jin ya sakasu ajikinsa ne, yasa ta ɗago jajayen idanunta dake tsiyayar da hawaye, cikin matsanancin damuwa da kuma ruɗewa haɗi da tashin hankalin da ta samu kanta aciki tace.

“Hamma Jabeer Ummeyna bata numfashi.
Dan Allah kace ta-tashi, kace ta buɗe idanunta, banason wani abu ya samu Ummey na, ka taimakamin, wayyo Dedde na Umaymah kuzo Ummeyna ...”

Kasa ƙarasa maganar nata tayi, saboda sosai kuka yaci ƙarfinta, sai-dai kuma amma duk da haka bata daina jijjiga Ummeyn nata ba.

Su Yah Jafar Jalal Ummi Mamma Aunty Juwairiyya Aunty Rahma Khadiya Aunty Amina Ishma, Hafsi Yah Al'ameen kuwa gaba ɗayansu zobe sukayi musu, cike da tarin al'ajabi al'hini kaɗuwa da tarin farin ciki.

Junainah kuwa da ta ƙara ruɗewa saboda ganin kukan da Shatu keyi, ƙarasowa jikin Shatu’n tayi ta raɓa jikinta, cikin muryar kuka take cewa.
“Adda Shatu Ummeynmu.
Adda Shatu Ummyen kice ta tashu mukaita asibiti kada wani abu ya sameta!”.

Sauran jama'ar kuwa.
Kowannensu fuskarsa ɗauke da hawaye suka ƙaraso garisu sosai kusa dasu Shatu, Sheykh, da Ummey’n suke.

Sautin kukan Aunty Rahma ne mai nuna tsantsar farin ciki da na Umaymah da Mamma ne suka fito fili, a dai-dai lokacin da sukayiwa Ummey’n zobe, Kowannensu kuka yake, sai-dai kallo daya zakayiwa kukan nasu ka fahimci cewar ba kukan baƙin ciki bane kukane na tsantsar farin cikin da yiwa Allah godiya, domin kuwa acikin muryar kukan nasu suke ambaton sunan Allah, suna me faɗin.

“Alhamdulillah! Alhamdulillah ya Allah!! Alhamdulillahil lazi bi ni’imati hi ala tatimussalihat!!!”

Umaymah kuwa da matsanancin farin cikin mara misaltuwa da take jin kanta aciki ya kasa ɓuya, durƙushewa tayi bisa guiwowinta tare da kifa goshinta aƙasa tayi Soujjadar nuna, matsanancin godia ga Allah daya dawo mata da ƴar uwarta.

Ummey kuwa wani irin Numfarfashi taja sai gata a sume.

Dai-dai lokacin kuma Jamil da jiyo hayaniyarsu ya sashi tahowa a guje, ganinsu cike a falon kowa fuska cike da hawaye kuma sai kalmar Alhamdulillah suke maimaitawa.
Duk sun kasa bin ta kan kalaman Shatu.
Ganin Jamil ne yasata mgn cikin rauni tace.
"Jamil dan Allah taimaka min Ummey na ta suma".
Jin hakane yasa ba tare da ya iso inda sukeba ya nufi kitchen da sauri mai kama da gudu ruwa ya ɗebo kana ya dawo.
Yana isowa gab dasu, ya zaro idonsa baki ɗaya murya can sama yace.
"Mammeyyyyy".
Sai ga ruwan ya kwaɓe a hannunshi shima ya faɗi bisa jikin Yah Jafar a sume.

Gaba ɗaya sun gaza cewa komai sai ambaton Allah.
Da gudu Affan da tun jiya daya dawo dasu Giɗi bai gana da Hamman nasu ba sai yanzu ya nufo Part ɗin.
Jin ƙaran muryar Jamil ne ya sashi shigowa falon da sauri yana cewa.
"Me haka Jamil lfyarka kuwa?".
Turus yayi a bakin ƙofar ganin duk suna cike a falon sun taru wuri ɗaya kowa da irin addu'ar da yakeyi.
Cikin tsaro da fargabar kardai wani abune ya samesu ya nufosu.

Cikin kaɗuwa yace.
"Mamey". Ya kira sunanta da ƙarfi lokacin da idanunshi suka sauƙa bisa fuskar Ummey.
Jiki na rawa ya juyo ya kalli Sheykh dake mgn cikin rawan murya da rauni yake cewa.
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Yah Allah na gode maka bisa wannan rahama da kaimin ko yau ka ɗauki raina burina ya cika, yau gani ga Mameyna a cikin masarautar Joɗa a suffar mutun bani Adam ba tsuntsuwar Boleru ba".
Wani irin kuka ne mai rauni ya kwabce mishi.

Yah Jafar ma kuka yakeyi tare da cewa.
"Alhamdulillah al'ƙadarin Magauta ya karye".
Ummi kuwa da rarrafe ta rusuna gaban Ummey tare dayin ƙasa da kanta cikin rauni tace.
"Barka da dawowa Adalar Uwar gijiyata".
Umaymah kuwa da sauri ta jawo wayar da ta gani kusa da ita.
Saida ta danna sai taga ashema wayar Hibba ce da ta bawa Junainah nayi Game.
Jadda ta dannawa kira.
Yana ɗagawa tace.
"Assalamu alaikum Alhamdulillah Allahu Akbar Jadda! Jadda!! Jadda!!!".
Cike da kaɗuwa Jadda dake kishinƙiɗe ya miƙe zaune tare da kallon Sitti dake yanka mishi lemu wanda tana iya jiyo abinda Umaymah ke faɗa sabida yadda take mgn da ƙarfi.
Wani irin dogon numfashi suka sauƙe a tare jin Umaymah na cewa.
"Alhamdulillah Jadda Aunty Mamey ta dawo Jadda zatonmu da tsammanin mu ya zama gsky Aunty Mameyna ta dawo gata gabanbu Jadda kace Alhamdulillah".
A tare Jadda da Sitti suka fara maimaita kalmar hamdala.

Affan kuwa cikin wani irin sauri ya juya a guje tamkar ƙaramin yaro ya nufi Part ɗin Abbansu.
Yana shiga da gudu yana mai cewa.
"Abba Abbanmu Abbana Mamey Mamey".
Da sauri Gimbiya Samira amaryar Abban ta fito tare da cewa.
"Affan lfy kuwa Abbanku yana fada".
Ai bai kuma bin ta kanta ba ya fito.
Kiciɓis yayi da Hajia Mama tana cewa.
"Kai lfy kuwa kake gudu kamar yaro?".
Ba tare da ya tsaya ba yace.
"Abba nake nema ina yaje Mamye."
Daga nan ya nufi fada.

Ita kuwa Hajia Mama cikin wani irin masifeffen tsinkewar zuciya da fargaban jin sunan da bata ko son jin an kira ta juya ta nufi ɗakinta.

A can fada kuwa bayan sarkin ƙofa yayiwa su Bappa iso cikin ƙaton falon.
Abboi na gaba Bappa da Arɗo Bani da Alhaji Haro suna biye dashi a baya kana sai masu tsaronshi da suka tsaya can bakin ƙofar shiga sabida dakatar dasu da yayi.

Suna shigowa Lamiɗo dake fuskantar Kofar shiga fuska cike da annuri da haiba yace.
"A a a Masha Allah lalle marhabin da Alhaji Abbo lale da zuwa masarautar Joɗa Fulle bandu fullo".
Da sauri Wambai, Dirankadi, Ɗan isa, Ɗan buram, Sarkin fada, Ɗan kade, Galadima Ɗan maliki Chiroma Durbi Ma'aji. Duk suka miƙe tsaye cikin tsananin sakin fuska da alamun sanayya na mutuntaka suka kalli Abboi tare da haɗa baki wurin cewa.
"Marhababika da zuwa masarautar Joɗa".
Sai kuma ɗan zagi ya fara baza rigarsa tare da cewa.
"Sarki ya gaisheka. Sarki yace ayi maka sannu da zuwa fullo Nbandu fullo manyan fada na farin ciki da zuwa ka".
Wani irin murmushi Abboi yakeyi mai cike da kamala ya nufi gaban Lamiɗo.
Har kusa dashi ya isa kana ya rusuna, yayinda Bappa da sauran ke biye dashi a baya.
A hankali ya sunkuyar da kanshi tare da ture hularshi yayi baya da ita.
Cikin alamun shaƙuwa Lamiɗo yasa hannunsa tsakiyar kansa tare da cewa.
"Allah yayi muku al'barka".
Murmushi Abboi yayi tare da cewa.
"Amin ya Allah Baba".
Sabida Lamiɗo yasan Abboi a matsayin ɗansa yake zuwa gareshi yana jin daɗin abokin mahaifin nashi ya sanya mishi albarka".

A hankali ya koma ya zauna ya tanƙwashe sawunshi

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment