Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta gefen hagunshi,
suka ɓullo farfajiyar wani babban part,
Jakadiyarsu na gaba suna biye da ita a baya, Umaymah na biye dasu.
A hankali suke taku cikin ƙasaita hadimai da fadawa na mara musu baya.
Suna shiga ciki, suka samuwa wata dattijuwar tsohuwa mai tarin shekaru.
Cikin murmushin da muryar tsufa tace.
"Malamai magada annabawa, lallai yau inada babban baƙo da babbar baƙuwa."
A hankali suke tafiya har zuwa gabanta, inda take zaune bisa tattausan carpet hadimanta na kewaye da ita.
wanda biyu daga cikinsu, suka tashi da sauri suka kawo ababen motsa baki suka jera a gabansu.

Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya kalli tsohuwar da take matar ga Galadima.
Cikin kula yace.
"Barka da safiya Innano". Cike da kula tace.
"Barka dai Malam Muhammad, mun samu ƙaruwa ko".
Kanshi ya gyaɗa mata a hankali haka yasa duk basu ganiba sai ita da yake gabanta.
"Cikin muryar tsufa tace.
"Allah ya sanya al'khairi. Ya baku zaman lafiya. Yasa matarkace iya rai da mutuwa. Ya azurtaku da zuriya ɗayyiba."
Da Sauri Umaymah ta amsa da Amin Amin hakama sauran baki ɗayansu.
Ita kuwa Shatu, cikin saisaita nitsuwarta ta ɗan kalli tsohuwar tare da cewa.
"Ina kwana".
Murmushi tayi tare da kai hannunta ta kamo hannun Shatu, tafin hannunta ta buɗe ta zuba musu ido, na yan wasu ɗakiƙu kana tace.
"Lafiya lau, ya baƙu ta?".
A hankali tace.
"Alhamdulillah". Jakadiyarsu ce ta ɗan rusuna tare da cewa.
"Mun barki lfy".
Kai ta gyaɗa kana tayiwa hadimanta umarni su miƙo kyautar da take gadon masarautarsun ce farin gyale ne mai kyau da taushi.
Umaymah ce ta amsa ta miƙa hadiman dake bayanta.

Kana suka miƙe suka fita.

Daga nan sashin wani sashin na kusa dashi suka shiga.
Wanda yake sashin ƙannen Lamiɗo ne.
Saida suka gama da sashukan manyan masarautar.
Kana suka nufi sashin Hajia Mama.
Tuni tasan da zuwansu.
haka yasa ta kimtsa ta tsara komai na tarban surkar tata.
A matsayinta na uwar ango.
Har can cikin bedroom Ummi ta wuce, su kuma suna biye da ita a baya.
Suna shiga suka sameta, zaune bisa kilishi,
Batool na gefenta, wacce son ganin amaryar ne, ya hanata tafiya.
Hadimanta kuma na zagaye da ita.
Suna shigowa ta tashi zaune daga kishingiɗar da tayi.
Cikin tsananin baiyana farin cikin ta, ta nunawa Jabeer kusa da ita.
a hankali suka iso suka zauna gabanta.
Umaymah kuwa gefenta ta zauna.
Ummi ko na bayansu hadiman kuma suna can falo.
Hannunta tasa ta kamo hannun Jabeer.
Cikin fara'a tace.
"Alhamdulillah Muhammad Jabeer, Allah ya sanya al'khairi ya baku zaman lfy".
To shifa suna ɗaure mishi kai, da tarin addu'o'insu na al'khairi, shi dai ba sonta yakeba ba kuma zama da ita zaiba,
to me zai wahal dashi da zaice Amin Amin.

Umaymah da Jakadiyarsu ne suka amsa da Amin Amin kamar dai yadda sukayi a sauran wuraren.

Batool ce ta kalli Shatu cikin isa tace.
"Amarya ki ɗago kanki mana kinga gaban uwar mijine kike".
Duk da taji mgnar Batool sai tayi kamar batajiba,
Abubuwan ci da sha dake gabansu ne,
Hajia Mama ta jawo wani ɗan ƙaramin tray da cups biyu ke kanshi.
Gyara zama tayi da kyau, tana murmushi ta kalli Shatu dake mgna a hankali.
"Ina kwana Mama".
Cikin kula tace.
"Lfy lau ɗiyata ya baƙun ta".
Alhamdulillah tace, tare da tsurawa madara da zumar da Hajia Mama ta zuba musu cikin kofu nan ido.
a hankali ta ɗan muskuta kaɗan tayi baya, tare da ƙara yin ƙasa da kanta.
ita kuwa Hajia Mama, kofin ta ɗauka ta miƙa mata.
Tare da cewa.
"Gashi ɗiyata amshi kisha."
Cikin sanyi murya can ƙasa ta girgiza kanta tare da cewa.
"Alhamdulillah".
cikin nuna kulawa da so Hajia Mama ta ƙara miƙo mata kofin tare da cewa.
"A a ɗiyata, amshi kisha, wannan al'adace ta masarautar Joɗa, dole in marabceki dashi."
Kai ta kuma girgiza alamun ya isheta.
da sauri Umaymah ta matso kusa da ita tare da cewa.
"A a Shatu amshi kisha kinji ko?".
Cike da mamaki ta ɗan kalli Umaymah ta gefen idonta.
jin Umaymah na ƙoƙarin matso da kofin kusa da itane yasa tayi mgna cikin ɗan ɗaga murya tace.
"Bana shan madarar".
wani irin kallo mai cike da damuwa Hajia Mama tayi mata tare da cewa.
"Subahanallahi, bakya sha, kuma, amai yake sakine? Ƙa'idane da dole kishi".
Ta ƙarishe mgnar cikin damuwa.
Ita dai Shatu shiru tayi idonta na bisa kofunan madarar.
Ummi ce ta matsota tare da cewa.
"Shatu amshi kisha koda kurɓa ɗaya ne".
Cikin rawan murya tace.
"Bana sha".
Jin alamun rawan murya irinta an takura mutum ne, yasa duk sukayi cirko-cirko suna kallon Madarar.
Zuwa can Hajja Mama ta sauƙe wani bahagon ajiyan zuciya, kana ta ɗauki ɗaya kofin ta miƙa Jabeer tare da cewa.
"To gashi kai kam kasha naka".
Zamanshi ya ɗan gyara tare dasa hannun damansa ya amshi kofin.
Wani irin zaro ido Shatu tayi.
Kallon kofin takeyi tamkar zata maida kwayar idanunta cikin kofin.
duk jikinta tsuma yakeyi, wani irin masifeffen bugawa ƙirjinta yakeyi da ƙarfi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer zaune yake riƙe da kofin, ya fuskanci Hajia Mama da kyau.
Ita kuwa Hajia Mama hannunta tasa ta kamo ɗaya hannun Jabeer da baya riƙe da kofin.
Kana ta miƙowa Shatu hannun alamun ta miƙo mata hannunta.
Ƙara runsunar da kanta tayi tamkar bata gane me take nufiba.
Cikin murmushin Hajia Mama tace.
"Kawo hannunki ko ɗiyata".
A hankali ta ƙara maida hannunta baya,
dai-dai lokacin kuma Jabeer ya ɗago kofin ya kai saitin bakinshi da niyar zai sha.
cikin hikima ta muskuta ta ƙara matsowa jikinshi da sauri ta ɗago hannunta kamar zata miƙawa Hajia Mama hannun.
sai kuma ta ɗan kaikaice, ta buge c...!




Ƙaƙa tsara ƙaƙa




By
*GARKUWAR FULANI*
Ta bugi kofin madarar, ba zato ba tsammani, Jabeer yaji kofin ya tsumbce mishi.
ya faɗi gefenshi.
Tass ya fashe madarar ta kwaranye a ƙasa.
Cikin sauri da tsuƙe fuskarshi ya juyo ya kalleta.
Itama ɗin shi take kallo.
Ido cikin ido sukayi da ita a karo na forko a rayuwarsa duk da yasan sun taɓa haɗuwa.
Kallon kwaɗayye mai irin bakin Junainah, tayi mishi.
Sai kuma ta janye ƙwayar idanunta cikin nashi da sauri.
Sabida wani irin kallon da taga yanayi manata.

Umaymah da Ummi kuwa, kallon junansu sukayi, cikin yanayin son gane ya akayi kofin ya faɗi dan basuga sanda ta ta ɗan buge mishi hannunta.

Hajia Mama kuwa cikin tashin hankali da kiɗima ta kalli Umaymah tare da cewa.
"Akwai matsala, ita batasha, shi nashi ya kwaɓe."
Sai kuma ta maida dubanta ga Shatu cikin alamun damuwa tace kawo hannunki na dama."
Still maida hannun nata tayi baya, ba tare da tace komaiba.
Ummi ce ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
"Miƙa mata hannunki ku gaisa".
Murya can ƙasa tace.
"Yana ciwo". Ta ƙarishe mgnar da jin haushin kanta da ƙaryar da suka satayi.

Batool ce ta kalleta sama da ƙasa kana cikin gyatsine tace.
"Umaymah ai wannan ba irin matar Sheykh bac."
Sai kuma ta haɗiye ragowar mgnar dan ganin wani irin kallon daya watsa mata na alamun.
Ki kama kanki da kiran sunana a bakinki.

Wani dogon ajiyan zuciya Hajia Mama ta sauƙe cikin fargaba tace.
"Tashi Kuje ku gaida sauran. Allah yayi muku al'barka ya baku zaman lafiya.
In sha Allah babu komai".
Kamar jira Shatu takeyi a basu izinin tashi tayi fit ta miƙe.

Da tarin mamaki Umaymah da Ummi suka miƙe, dan abubuwan da suka faru da yanayin Shatu, ya tsaya musu a rai.
Shima Sheykh Jabeer miƙewa,
yayi kana suka jere suka fita.
Sai dai Shatu na ɗan sassarfa.

Cike da mamakin wannan abun suka nufi Side ɗin Gimbiya Saudatu.

A falonta suka sameta tana hakimce bisa kujerar ikonta,
ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tana karkaɗa ƙafar cike da izza.

Ummi na gabansu suna bayanta Umaymah na bayansu.
Cikin rusunar da kai Jakadiyarsu ta durƙusa gefenta tare da cewa.
"Barka da safiya Gimbiya Saudatu, ga Sheykh Jabeer ya kawo miki da amaryarsa!".
Cike da izza ta ɗan kallesu sama da ƙasa, kana ta nuna musu gabanta.
Alamun su zauna, cikin sanyi Shatu ta rusuna tare da sunkuyar da kai ta zauna gabanta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer wani irin kallo yayi mata, mai cike da ma'anoni,
gefen ta ya kalla inda wata kujerar ke kusa da tata komansu iri ɗaya.
Taku yayi cike da ƙasaita ya isa gaban kujerar, kana ya juyo ya zauna kan kujerar.
Hakan yasa ya fuskanci Shatu da Umaymah.
zaman ƙasaita da isa yayi.
wani mugun kallo take binshi dashi har ya zauna.
Ita kuwa Shatu kanta a duƙe tana murzam ƴan yatsunta.

Umaymah ce ta ɗan taho zata zauna kusa da ita, a hankali ya jujjuyawa Umaymah kai, alamun. A a kada ta zauna a ƙasa.
gane manufarsa ne, yasa ta zauna bisa kujera.

Shiru kakejin falon, sai takun sawun hadimanta dake kawo ababen motsa baki, suna ajiyewa gaban Shatu.

Suna gama jerawa suka koma can gefen.

Jin shiru-shirun yayi yawane yasa Shatu ɗan ɗago kwayar idanunta, ta kallesu.
A ranta take mgnar zuci.
"Ikon Allah, ohoho ni Shatu wannan wanne irin bahagon gidane, mai cike da sarƙaƙiya da tubkar baƙin zare,
To ko dai ita wannan ɗin kurmace."
Muryar Gimbiya Saudatu ce ta ƙatse mata tunani ta,
cikin isa da izza ta kalli Sheykh Jabeer, kana ta juyo ta kalli Shatu, murya a daƙike tace.
"Bakiyi sa'an mijiba, yarinya duk da gashi kamar kinada nitsuwa".
Ido Shatu ta jujjuya cikin hular al'kyabbar jikinta.
Shi kuwa Sheykh Jabeer, ko ta kan mgnar ta bai biba,
sabida ai dama ya tsammaci, hakan
kai ta juyo ta kalli Umaymah cikin ɗagawa tace.
"A buɗe min fuskar amaryar in ganta da kyau, inga wanne irin idone da ita".
Bata rufe bakintaba taji yana cewa.
"Baza'a buɗe ba!."
Murmushi Umaymah tayi sabida tsamar Sheykh Jabeer da Gimbiya Saudatu wani lokacin yadda kasan shi ubanta ne, haka yake mata mgna da yanke hukunci kai tsaye a karan kanta ma bare akan abinda ya shafeshi.
ita kuwa Shatu a hankali take juya ƙwayar idanunta, tana kallon sawun Gimbiya Saudatu.
cikin al'kyabbar ta ɗan juya idonta da kyau ta maidasu, kan kyawawan fararen sawun Sheykh, wanda suke tamkar ka taɓa jini yayi yo tsalle ya fito, sabida taushi da laushin fatar
Wanda duk mutun mai zama da al'wala da yawan karatun al'ƙur'ani tafin hannunshi da ƙafarshi sukanyi wani kala mai masifar kyau da ɗaukar hankali koda baƙin mutun ne sai fatar hannunshi dana ƙafarshi sunyi kyau na musamman, hakama kuma fatar jikinshi wannan shine baiyanennen darajar zama da al'wala da yawan ambaton Allah kenan.

Da ƙarfi ta rumtse idanunta tare da buɗe su.
kan babbar yatsar kafarshi ta zubawa ido, sosai da sosai.
wani ɗan zane baƙi mai suffar tafiyar maciji ta gani.
sai dai bata samu ganinshi ras yadda take soba, shiyasa taketa zare ido,
shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya ɗan turo ƙafar damanshi gaba.
Dan ya gyara zaman ɗayan a kanta.
Hakanne ya bawa Shatu damar zubawa yatsun nashi ido, suna nan zara-zara alamun mutum ne mai matsakaici tsawo.
Ras zanen bindin maciciyar nan yake kan babbar yatsarshi.
har zuwa bisa rumfar ƙafar kamar zanen dayis,
cikin tarin mamaki da al'ajabi take bin zanen da idanunta.
har inda igiyar takalminshi ya tsare zanen.
Wani irin sassanyan numfashi ta sauƙe a hankali.
sabida rashin ganin ƙarshen wannan zanen, da kuma inda ya nufa, da kuma ganin ya saman zanen yake.
Hankalinta kab ya tafi ga zanen shiyasa bata jin ta ƙaddamar da Gimbiya Saudatu ke zubawa ba.
Muryar ta taji da ɗan ƙarfi tana cewa.
"Bata da sunane? Ke me sunanki".
Ta ɗago kai da nufin yin mgna kenan sai kuma tayi shiru.
jin Umaymah na cewa.
"Sai kisa mata naki sunan, ba sai kiji namu ba".
A gyatsine ta kalli Umaymah kana, ta ɗan matso bakin kujerar,
hannu tasa ta ɗauki tupa cikin jerin ƴaƴan itatuwan da aka jera a gaban Shatu.
miƙa wa Shatu tayi tare da cewa.
"Kici kada ki tafi bakici komaiba,".
A hankali tace.
"Alhamdulillah!". Cikin sauri Gimbiya Saudatu tace.
"A ni ba'a zuwa sashina a tafi ba abinda akaci".
Hannu ta miƙa ta amshi tupan kana ta riƙe shi.
Shi kuwa Sheykh Jabeer miƙewa tsaye yayi alamun tafiya hakane yasa.
Suma suka miƙa suka fita.


Daga nan kai tsaye Side ɗin.
Baba Nasiru suka nufa.
A falo suka samu matarshi da yaranshi dama shi kanshi.
Bayan sun zaunane.
ya kallesu sama da ƙasa yace.
"Dama baku zauna ba, a hakama na ganku.
ba sai kun zauna ba".
Cikin sanyi ƴarshi Jamila ta ɗanyi ƙasa da murya tare da cewa.
"Ayyah Baba ka barsu mu gaisa".
Haɗe fuskarshi yayi sabida yasan irin masifeffen son da Jamila keyiwa Jabeer lokuta da dama, takanyi ta kuka in taji abubuwan da mahaifinta yakeyi mishi.
shi kuwa Sheykh Jabeer tuni ya zauna ya harɗe ƙafa,
Jamila kuwa cikin nitsuwa ta gaidasu kana.
Ta kawo musu abin sha,
Ummanta ku ko kallo Bata ishesuba yadda itama bata lallesu ba.

Haka dai suka fita suka tafi.
gidan Baba Basiru kuwa suna shiga ya tashi ya bar musu wojen.

Daga nan suka shiga gidan Barrister Kamal
Baba Kamal kenan.

Yana ganinsu ya tashi ya ruggume Sheykh tare da cewa.
"Masha Allah, Alhamdulillah yau dai Allah ya nuna min ɗana da matarsa".
Zama sukayi bayan sun gaisane yayi musu addu'o'in al'khairi.
Daga gidanshi gidan Dr Aliyu sukaje,
wanda yake mutun mai mutunci da kamar Barrister Kamal.
Sosai suka jima a sashinsa,
yayi musu addu'o'in da sanya al'khairi da al'barka.

Daga nan kuma sai Sashin Mom tsakar gidan Abbanshi.
Maman Imran, ba yabo ba fallasa ta amsa musu.
Daga nan wurin Amryar Abbansu sukaje, wanda suka sameshi a can.

Daga nan sukaje gidan Ya Hashim da sauran ƴan bappanunsu.
Gida na ƙarshe dai gidan Aunty Juwairiyya ne, can suka samu Hibba da Ya Jafar.
Bayan sun gaisane,
Umaymah ta ɗan matso kusa da ita cikin sauƙe numfashin gajiya tace.
"Ɗago kanki Shatu kinga nan ƙofar Aunty Juwairiyya ce, ga mijinta shine babban yayan Jabeer, kuma yanada matsalar ƙwoƙolwa.
Yanzu daga nan Side ɗinkin zamu wuce, wanda yana nan kusa da nasun. Sai gefen nakun kuma nasu Jalal ne."
A hankali ta ɗago kanta ta kalli Ya Jafar, yana riƙe da hannun Jabeer yana karatun shi a hankali.
Cikin sanyi tace.
"Ina kwana yaya!".
Kafaɗarta Umaymah ta dafa tare da cewa.
"Baya mgnar komai a duniya inba karatuba, sai dai yanajin komai kuma yana gane komai in an gaya mishi amman fa baya mgna kam in ba karatuba."
Cikin tsananin rauni da tausayawa,
idonta cike da ƙwalla tace.
"Allah sarki, Allah ya bashi lfy".
Karon forko kenan tunda suko fito dashi taji ya amsa addu'a duk da tarin addu'o'in da akayi ta musu sai yanzu taji yace.
"Amin ya Allah". Hakama Umaymah da Jakadiyarsu da Hibba sai dai duk ya riga su amsawa.
A hankali take ɗan satan kallonshi a fakaice.

Hibba ce ta janye mata hankali da cewa.
"Aunty Shatu kin gaji kam. muje ki huta, gashi azahar ta kusa ma."
Ɗan guntun murmushi tayi tare da cewa.
"Uhum".
Umaymah ce ta miƙe ita da Ummi kana sukace.
Taso mu tafi, yanzu Hibba zata cikaki dan zance."
Cikin murmushi Aunty Juwairiyya tace.
"Ayyah Umaymah ku bar mana ita mana".
Ummi ce tace.
"Lokacin sallafa ya ƙara to".
"Hakane kam". Juwairiyya tace tare da ɗaukar Foodflaks dake kan dinning table, tabi bayansu tana cewa.
"Hibba ɗauko sauran!".
To tace kana ta suggumi sauran tabi bayansu.

Nan suka bar Jabeer da Ya Jafar ɗin.

A babban falon suka zauna.
Aunty Juwairiyya da Hibba suka ajiye Foodflaks ɗin bisa Dinning table,
kana suka dawo tsakiyar falon.
Umaymah ce ta miƙe tare da kallon Shatu, tace.
"Taso mushiga ciki, kiga tsarin wurin naku".
Miƙewa tayi cikin alamun gajiya, domin zagaye masarautar Joɗa babban aikine mai zaman kanshi. Donma su sun saba, ita kuma bafulatanar dajine tafiya baya bamu tsoro.
Bayan Umaymah tabi, ta gefen Dinning area ta ɗan ratsa da ita,
Suka shiga cikin kitchen, juyowa tayi ta kallesu Ita da Hibba,
"Nan shine babban kitchen ɗin ki, dake babban falonki.
Shine wanda in kinada aiki mai yawa, kamar na salla ko azumi, ko zakiyi ki aikawa surakanki.
Hadimai zasu iya shigowa su tayaki."
cikin fahimta tace.
"Toh". Hibba ce ta ɗan ƙara so shigowa ciki tare da cewa.
"Kai wanga kitchen badai girmaba, gashi komai a tsare gonin kyau. Kalarsa green and white komai na ciki gwanin kyau".
Murmushi suka ɗan yi kana, Umaymah ta juya dasu.
Daga nan cikin kitchen ɗin ta gefen dama akwai wata ƙofar da sai ka hau stpes huɗu.
A gefen ƙofarne wani datsetstsen Fridge mai girma yake kwance.
Haurawa sukayi kana Umaymah ta tura ƙofar ta shiga.
Store ne mai zaman kanshi.
akwai komai na buƙatar rayuwa, sai dai ba mai yawa bane.
Shatu ta ɗan kalla tare da cewa.
"Ga kuma store ɗinki. Nan za'a ke aje miki duk wani abun buƙata".
Kai ta gyaɗa, kana suka fito.
Wata ƙofar daketa hannun hagu ta nuna mata suna buɗe wa suka fito.
Sai gasu bisa wata baranɗa mai girma, kana can ƙasan barandar fulawine da kuma pompona ke jere iya ganinka,
Daga sama kuma igiyoyin shanya ne da a ƙalla sun kai huɗu.
sai saman barandar kuwa, injin wanki ne.
Nan dai ta nuna mata komai na wurin kana suka dawo cikin gida.

Suna shigowa falo. Sheykh na shigowa.
A nitse yake taku, kanshi na sunkuye yana kallon wayarshi da yake lallatsawa.
Umaymah ce ta ɗan bi bayanshi tare da cewa.
"Zo nan Shatu".
Cikin zuba bayansu ido. Ta ɗan gyaɗa kai, tare da taka sawunta a hankali tabisu.
Hibba kuwa gefen Aunty Juwairiyya ta zauna.
Shi kuwa yana shiga falon nashi, ya juyo ya ɗan kalli Umaymah cikin kwaɓe fuska yace.
"Umaymah, Dan Allah ni bana son ana shigomin da wasu ababen cikin Side na, bare rayuwata, me wancan abun da kika kira zaizo yi anan?".
Ido ta kafeshi dasu hakane, yasa yayi ƙasa da kanshi.
tare da shigewa bedroom yana cewa.
"Dan Allah iya kar abun can falo".
Ƙeyanshi Umaymah ta zubawa ido.
"Wato ma wai wancan abun, lallai ma Jazlaan".
Juyawa tayi ta ɗan leƙo a corridor ta hangota, murmushi tayi tare da cewa.
"Taho mana".
Kai ta kuma gyaɗawa tare da ƙara saurinta tafiyarta a hankali.

Suna shiga falon, tayi wani irin ɓoyeyyen ajiyan zuciya mai sanyi,
sabida wani irin masifeffen sanyi mai gauraye da ƙamshi mai ɗan karen daɗi da taji ya bugu jiki da zuciyarta.
lumshe idonta tayi, kana ta buɗe su a hankali jin Umaymah na ce mata.
"Nan falonshi ne, namusamman ba kowa ke shigo mishi wurin kai tsaye ba.
dan ko Juwairiyya bata shigo mishi nan, kana akwai ƙannenshi ƴan uba maza da kuma Jalal basa shigo mishi nan.
Jamil kan shiga in baya nan in zai dawo shikeyi mishi shara da gyaran wurin.
Jalal kuwa yakan iya shekara ƙafarshi bata tako nanba.
Sai kuma Ya Jafar ɗin sa, shi kam bashi da hijabi da Side ɗin Jabeer, yakan shiga har cikin Bedroom nashi wani zubin har bathroom.
Sai kuma Haroon da Ibrahim su dama, dan su yasa aka gina sama wai masauƙinsu in sunxo.
To ammanfa in sunzo a ɗakinshi suke ko motsi zasuyi tare zasuyishi.

Sai kuma yayan Hibba, Hibbab shi na hannun damanshi ne.

Dan haka daga yanzu in dai yayi tafiya kece, zakiyi aikin da Jamil keyi".
A hankali tace "to".
Haura step ɗin Dinning area ɗin shi dake falon wanda akayiwa ƙawanya da wani irin labule mai masifar kyau.
Labulen ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu kama dana Daimond. wasu farare wasu Sky blue wasu Royal blue. suna da wani irin haske mai wal-wal. Cikinsa kuma.
Wani badaidaicin Dinning table ne mai kujeru shida nan uku nanma uku sai wani fridge ma daidaici. Gefensa show glass ne mai kyau wanda yake ɗauke da cups and plates and spoons and forks Mug. Da dai sauran ƙananan abeben buƙata.
sai woshing hand Baby, dake liƙe a can gefe.

sosai tsaruwan wurin yayi kyau, komai Sky blue and white. Abun sai ya zama kamar a duniyar taurarin yake yadda walwalin ke haska ko ina.
Falon kuma yanada ɗan karen duhu, domin saida Umaymah ta kunna musu wuta.

Bedroom nashi ta nuna mata da yatsa.
"Ga makwancinsa, sai kuma wancan ɗakin shi ba mai kwana a cikin ɗakine na musamman babu mai shiga ciki sai shi ni Lamiɗo Galadima, domin ɗakin aikinshi ne".
Ita dai da to take bin Umaymah, sabida sanyin falon yana gab da sata kuka.
Allah ya sani bata son sanyi ko kaɗan. Ta kuma lura su kuma mayun sanyi ne.

Falon suka fito. Nan dai suka samu su Hibba nata hira da Ummi.
Side ɗin ta suka nufa.
Cikin kula tace.
"Ga Side ɗinki ga falonki ga kitchen ɗinki."
Ta ƙarishe mgnar suna shiga kitchen ɗin. A hankali take kallon komai na Kitchen ɗin kalarsa Pink and white. Sosai tsarin wurin yayi kyau.
daga nan Dinning area Suka shiga ta nuna mata kana suka fito falon.
Suka shiga bedroom ɗinta komai ya tsaru.
Kuma komai sabone fil gwanin burgewa.
juyawa Umaymah tayi tare da cewa.
"Wancan ɗakin kuma masauƙi nane in nazo."
Cikin ɗan murmushi tace.
"Ayyah". Ƙofar Bathroom Umaymah ta nuna mata tare da cewa.
"Azahar tayi shiga kiyi al'wala kiyi salla sai kizo muyi Lunch".
to tace kana Umaymah ta juya ta fita.


Shi kuwa Sheykh Jabeer, yana shiga ya maida ƙofar Bedroom ɗin ya rufe shiyasa Umaymah bata gwada shiga da itaba.

Shi kuwa bathroom ya wuce wonka da al'wala yayi, ya sauya kaya. Kana ya fito cikin shigarsa ta musamman ya nufi. Masallaci.


Koda sukayi salla suka fito.
Falon ganin bata fito bane yasa, Umaymah cewa Hibba.
"Jeki kiramin ɗiyata". Da sauri Hibba ta juya ta nufi ɗakinta.
Kwance ta sameta bisa sallayar da tayi salla, ta kife kanta cikin hijabin jikin nata,
bisa dukkan alamu kuka takeyi.
jin shigowar Hibba ne yasa tayi saurin share hawayenta,
tare da juyowa,
cikin mamaki Hibba ta zuba mata ido.
A hankali tace.
"Aunty Shatu meya sameki kike kuka".
Murmushin ƙarfin hali ta ƙaƙalo tare da cewa.
"Kuka kuma Hibba".
Cikin sauri tace.
"Eh mana gashi idonki yayi ja".
Miƙewa zaune tayi da kyau cikin sanyi tace.
"No bacci na fara, shiyasa kikaga hakan".
Kai Hibba ta gyaɗa kana tace.
"To taso mu tafi falo Umaymah tace kizo muyi Lunch".
Hannu tasa ta ɗan shafa cikinta tare da cewa.
"Kamar na ƙoshi fa".
Murmushi Hibba tayi tare da cewa.
"Tab ai Wlh taso kawai mu tafi, dan Umsymah bazata barki bakici abinci ba".
To tace kana ta miƙe ta ninke sallayan. Sabida gajiya ne da bege da kewar yan uwanta ne ya sata kuka da kuma jin yunwar ta mutu a cikinta.

Suna fitowa su Umaymah duk suka miƙa, Dinning area suka nufa.

Bayan duk sun zaunane, Ummi, ta miƙe da nufin saka musu abincin.
Da sauri Aunty Juwairiyya ta miƙe tare da cewa.
"A a Ummi ki huta bari in saka mana".
Foodflaks ɗin dake kusa da ita ta ture tare da jawo wanda suka shigo dasu.
Ummi ce ta ɗan kalleta tare da cewa.
"Ya kika ture wancan?".
Baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
"Uhummm wai fa Gimbiya Saudatu ce, ta turowa amarya abinci dan salon munafurci".
Wani irin kallon ƙasa-ƙasa Shatu tayi mata tare da zuwa abincin data buɗe ido, cikin mgnar zuciya take cewa.
"Uhumm wai zata cewa wata muna fuka, muguwa Itan ko meye sunanta!?".
Sai kuma ta kalli Umaymah jin tana cewa Juwairiyya.
"Ni zubo min na gidan Hajia Mama naga tuƙeƙƙen tuwone da biyar zogale".
To Aunty Juwairiyya tace kana ta zuba mata.
da sauri Shatu ta ɗan kalli Umaymah lokacin da aka saka mata mal-malan tuwon farar ɗanyar shinkafa,
tare da miyar a side sup.

Sai kuma ta juyo ta kalli Hibba da Ummi da tuni sun ja plate ɗin da Aunty Juwairiyya ta saka musu. Couscous and vegetables sup, mai ɗan karen kyau da ƙamshi.

Da sauri ta jujjuya kanta lokacin da Aunty Juwairiyya ta turo mata na plate ɗin gabanta, cikin sanyi tace.
"La da baki saminba". Da mamaki Umaymah tace.
"Sabida me?". Sunkuyar da kanta tayi tana tunanin.
suma ta yaya zata hanasu cin abincin. jin Ummi ta kuma mata tambayar da Umaymah tayi matane yasa ta ɗan kallesu.
Ta buɗe baki zatayi mgnar kenan.
Sheykh ya shigo da sallama, a bakisa.
kusan a tare, suka amsa masa.
A fakaice ya ɗan kalli Aunty Juwairiyya kana yace.
"Kije ki bawa Ya Jafar mgninshi".
To tace tare da miƙewa da sauri ta fita.
Ita kuwa Shatu, wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauƙe.
Kana tasa hannunta ta ture plate ɗin gaban Umaymah tare da jawo na gaban Ummi da Hibba,
Ido suka zuba mata cike da mamaki.
Ita kuwa cikin sanyi ta kallesu tare da cewa.
"Dan Allah kada kuci wannan abincin.
Kuci wancan ne".
Jabeer dake ƙoƙarin shigewa falonshi ne, a ranshi yace.
"Uhumm lallai kam wannan abun wato itace ma zata zaɓa musu abinda zasuci".

Hibba kuwa da sauri tace.
"Aunty Shatu abincin gidan Gimbiya Saudatu fa kike cewa muci."
Ganin kallon mamaki da tuhuma da Umaymah da Ummi keyi matane yasata yin ƙasa da kanta cikin jin tausayinsu a ranta tace.
"To in bazaku cishiba, Umaymah bari ni in shiga kitchen nida Hibba yanzu zan girka muku duk abinda kukeso".
Ko inda suke Sheykh Jabeer da yanzu ya fito zai wuce baiba, yacewa Umaymah.
"Zan fita".
Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya, ya bada Sa'a".
Amin Amin yace, hakama Ummi tai mishi addu'a.

Ita kuwa Shatu kanta na sunkuye,
Umaymah ce ta ɗan kalleta cikin nazartan yanayin ta, da yin tunani hakafa ɗazuma taƙi shan madarar Barka da shigowa masarautar Joɗa da Hajia Mama ta bata,
ta kuma amshi tuppar da Gimbiya Saudatu ta bata,
yanzu kuma tace kada suci abinci Juwairiyya.
Wannan abun shi yafi komai tsayawa Umaymah a rai.
Yaya daga shigowarta zata kasabto wasu hasashen a ƙwaƙwalensu.

Kai ta jinjina tare da cewa.
"Hibba sa mana abincin Gimbiya Saudatu, muci".
Jin hajane yasa Shatu jawo Foodflaks ɗin ta fara saka musu.
Ita kuwa Hibba ta kwashe plate ɗin da Juwairiyya tasa musu

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment