Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai a matso mata da wuƙa, in kuwa mutum ne to, tabbas zai sha azaba mai raraɗi.
In jifa ne ma sukayi ma basa saɓawa saiti sai sun samu abin harinsu, in kuma tsuntsune ko ƙananan halittu tofa in suka harba sai lahira."
Sai kuma ya ɗan tsaya ya kallesu cikin dakiya yace.
"Munada buƙatar sabon shiri, akanshi, zamuyi mgnin bakinshin nan da baya mutuwa".
Cikin takaici Gimbiya Saudatu tace.
"A duk cikin ababen da ake dangantawa dasu babu, abinda yafi cimin rai kamar meda, zoo ɗin masarautar sade ɗin Jabeer.
Wlh duk sanda najiyo kukan Ɗawisun Masarautar da sauran tsuntsaye nakiji kamar in je in samisu shinkafar tsuntsaye suci su mace kab ɗinsu kowa ma ya huta."
Barrister Kamal dne dake,
Jinsu ta window ɗin falon.
Ya jinjina kai tare da jan hannun Sulaiman suka tafi yana mai cewa.
"Uhum naku burin dai baza taɓa cikaba in sha Allah".
Su kuwa nan sukaci gaba da tattaunawa yadda shirunsu a kanshi zai kaya.

Jakadiyarsu kuwa saida taga fitansu ta sauƙe ajiyan zuciya.
Jafar kuwa saida yaga Barrister Kamal ya fita kafin jikinsa ya dena rawa da karkarwa.

Shi kuwa Haroon da sauri yabi bayan Jabeer cikin sauƙe nannauyan numfashi yace.
"Wato kai bakinka bazai mutu bako."
Cikin kufula ya juyo ya kalli Haroon jin ya yace mishi irin
Abinda kullum Abba yake cemishi.
A hatsale yace.
"Eh bakina bazai mutuba ba kuma zan bar ko wanne taƙadirinba, duk wanda yace dani tak zai samu amsa dai-dai da zancensa.
Wannan zarerriyar matarfa ta kiyayeni, kadafa ta fusatani, tam!".
Ya ƙarishe mgnar da taune lips ɗinshi.
Cikin sanyi Haroon yace.
"Nifa tsorona ɗaya Jabeer kada su cutar da kai, so dan Allah duk abinda zasuyi maka kosu Jalal da ya Jafar kada ka tanka musu.
Yanzu wannan sharrin ya zamuyi dashi?".
Wani irin kallo yayiwa Haroon cikin sauƙe numfashin yace.
"Tuni na magance ta, na saye jaridun, tun kafin a fiddasu, shima dan ya ɗauka ne tun kafin inji inje wurin.
Kuma gashi shima a hannun yanzu sai dai su nemo wani sharrin. Kuma batun basu amsa, da sun gane sun dena sako Mahaifiyata a duk abinda zasuyi min da Ni dai ko kallo basu isheni ba."
Cikin sauƙe numfashin Haroon yace.
"To Alhamdulillah Allah ya kare gaba".
Amin yace tare da zama bisa kujerarshi ta musamman wacce take kyautace ga Sheikh Abdulkarim. Tab ɗin shi ya ɗauka ya fara wasu yan dube-duben.

Anan falonshi suka zauna, shida Haroon.
Jin muryar Gimbiya Aminatu na ratso falon ne yasa Haroon yin murmushi cikin sabo da tsohuwar yace.
"Yauwa Gimbiyar Lamiɗo kizo kiyiwa wannan jikan naki faɗa".
Murmushi tayi mai ƙayatarwa,
a hankali ta ƙara so cikin falon ita ɗaya hadimanta suka tsaya a can babban falo da abincin data kawo mishi.
A hankali tayi taku zuwa gabanshi gefenshi ta zauna,
cikin sanyi ya kalleta.
Ita kuwa cikin kulawa tace.
"Jabeer, ya jikin naka".
Cikin harshen fillanci yace.
"Da sauƙi".
Yadda ya bata amsa a taƙaicene yasa ta kalli Haroon tace.
"Yaci wani abu kuwa?".
Da sauri yace mata ehh.
Cikin kula tace.
"Me yaci!?."
Murmushi yayi cikin tsokana yace.
"To da sanyin safiyar nan dai an sanshi magantuwa".
Dariya ta ɗan yi tare da cewa.
"Taso kuzo kaci abinci".
Kanshi ya girgiza mata tare da cewa.
"Bana buƙatar komai, kawai ki gayawa wannan dottijon mijin naki da sufanshi baya gaya mishi dai-dai ya gargaɗi Gimbiya Saudatu ta dena zuwa min side ɗina.
In kuwa taƙi wata ran zan bar Jalal yayi mata ɗan karen duka".
Murmushi tayi tare da cewa
"To naji taso muje kaci wani abun".
Dai-dai lokacin Lamiɗo da Galadima suka shigo.
Ɗanzagi da dogari kuma suka tsaya a can bakin ƙofar shigowa falon.

Bayan sun zauna ne Lamiɗo yace.
"Ya ƙarfin jikin?".
Rai a ɓace yace.
"Ai baka da case da raina da lfyata, ko in samu sauƙi ko kada in samu ba matsalarka bace, tun da gani kake iyayena sun haifa maka nine dan ka bawa wasu ƙattin daji su dakani".
Murmushi Lamiɗo yayi cikin tsokana yace.
"To wai in ban basu kaiba wa kake son in basu?".
A hatsale yace.
"Ka basu kanka mana, me zai hana kai ka tuɓe gwanjinka a zaneka, dan masifar rainin wayo sai ka nunani, duk da tarin jikokinka da suke wurin."
Murmushi Galadima yayi tare da cewa.
"Yanzu dai jikin da sauƙi gashi, har zanar ta maidaka mataɗaci, ka fara shiri nan bada dadewa ba za mu koma ka rama".
Da sauri ya ɗago kanshi daga kallon Tab ɗinshi ya zuba musu tare da nuna kanshi.
Ido suka zuba mishi. Shi kuwa cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi ruwan jini yace.
"Ni! Ni!! Ni!!! Muhammad Jabeer Kuma a wancan garin, me zanje inyi a can, wannan garin ko a mafarki bana fatan Allah ya gwada minshi, dan Wallahi Allah kenan duk duniya babu garin da na tsana sama da wannan garin.
Na tsani garin bana ko son jin makamacin sunan garin. Da garin da mutanen garin gaba ɗaya basa cikin jadawalin jerin mutanen da zuciyata zata sosu har gaban abadan me na samu a wannan garin banda tozarci da ɓaƙar azaba."
Murmushi Lamido yayi kana cikin son jikan nashi ya dafa kafaɗarshi tare da cewa.
"A makon-nan ma kuwa zaka koma wannan garin da izinin Allah".
Mgnar Lamiɗo ta ƙarshe da yace da izinin Allah ne yasashi yin shiru.
Haka suka ƙaraci mgnarsu bai kuma ɗago kanshi ya kallesu bama bare ya kulasu.

Bayan sun tafine.
Ummi da Gimbiya Aminatu suka samu suka sashi ya ɗanci abinci.

Zuwa azahar kuwa sai ga Sarkin Musulmi Jalaluddin da Sitti.

A sashin Gimbiya Aminatu Sitti ta sauƙa shi kuwa Jalaluddin a sashin amininshi Lamiɗo ya sauƙa.
Saida akayi sallan la'asar kafin suka isa sashin, Jabeer.
Sosai suka nuna mishi kulawa da gata,
Inda yaketa son huce haushin da yakeji a kansu tunda sune dai suka sashi yin wannan abun a bisa dole.
Hajia Mama kuwa daɗi kamar ta goya Sittin dan kulawa da so.

Sai washe gari. Suka koma Laddi julɓe sunan jihar da nanne asalin tushen masarautar sarkin Musulmai yake.

Mama kam hankalinta ya konta ganin jikin Jabeer yayi sauƙin sosai.

Batul kuwa babu nacin da batayiba ta samu ta ganshi ido da ido abin yaci tura.

A haka kwanaki sukayi ta tafiya, ana bawa Jabeer kula tamusamman.

Yayinda Sarkin Shaɗi kuwa yake ta tsuma bilalin Shaɗin masarautar Joɗa wanda a ƙalla tsawon kusan shekaru ɗari biyu da wani abu. Suna binne cikin ramin tsuminsu
Wanda da dafin macijin gadin masarautar ake tsumashi.

Umaymah kuwa tana shirin zuwa duba jikin ɗan ƴar uwar tata ɗa mafi soyuwa a gareta sama da ƴaƴan data haifa a cikinta ma.

Yau kwana biyar da faruwan abun.
Sosai jikinshi yayi ras.

Yaune kuma Umaymah ke tahowa jirgin yamma zata biyo.

Shi kuwa Jabeer zuwa yanzu ko mgnar kowarshi wannan garin ba'ayi sabida irin ɓacin rai da yake baiyana a fuskar shi, in an mishi mgnar zuwa garin.

Allah ya sani yana jin ya tsani wannan gari tsana mai tsanani.
Yana masifar jin kunyar komawa na wannan garin da a tsakiyarshi akashi cire suturarshi ya zauna dagashi sai boxes.

Yakanji kamar ya faɗi ya mutu in ya tuna garin.

Ƙarfe biyar dai-dai motocin da suka ɗauko Umaymah suka iso cikin harabar masarautar.

Dai-dai lokacin kuma Hajia Mama da Batul suna gab da shiga sashin Jabeer,
A tsakiyar falon sukayi kiciɓis dashi. Yana sanye cikin tufafin da sune suturarshi, al'kyabbar ruwan madarace, sai kayan dake cikin al'kyabbar su kuwa ruwan bonbitane, yayi wani irin masifar kyau, sai ƙamshi yake bazawa tako ina.
Fuskarshi ta fito ras cikin hiraminshi ruwan madara,
Wani irin ƙyalli da sheƙin kyau yakeyi.
Duk da ba murmushi a kan fuskarsa amman ana iya gano tsantsar farin cikin da yake ciki.
A hankali yake taku, Ya Jafar na biye dashi a baya,
Cikin tarin kula da nuna soyayyarsa Hajia Mama tace.
"Masha Allah, Ɗan Umaymah yayi kyau, ga farin ciki ya wadaci kekyawan fuskarnan taka".
Kanshi ya ɗan kauda ya kalli Ya Jafar daketa jan hannunshi su fita, cikin nitsuwa yace.
"Sun isoma".
Cikin jin daɗi tace.
"Eh haka dai Jamil ya gaya min".
Ta ƙarishe mgnar tana juya baya tare da Batul da cikin sanyi tace.
"Ya Jabeer ya jikin?".
Cikin jan gajeren tsaki yace.
"Lfyata lau".
Murmushi tayi sabida jin zazzaƙar muryar shi.

A tare suka fito su Mama na gaba shida Jafar suna baya.

Suna fitowa harabar Side ɗin shi.
Motarshi da Sheykh Abdulkareem yasa aka taho mishi da ita wacce bai taɓa hawantaba, asalima gani yake tamkar almozzaranci ne,
sai yau ya bawa Haroon key ɗin ta yace a ɗauko mishi Umaymahnshi, shi bazai je ɗaukotaba sabida.
Lamiɗo yace bazai fitaba.
A hankali ya tsaya ganin hancin motarshi ƙirar Mercendes benz maybach Exelero wacce ta kai kimanin $8 million dollars.

Da sauri ya ƙarasa jikin motor. Hajia Mama na biye dashi.
Yana isa inda suke yasa tattausan hannunshi ya buɗe marfin motar.
Karo na forko da naga murmushi a fuskarshi, cikin tarin shaƙuwa da kulawa yace.
"Marhababuki ya Umaymah, ta faddal".
Wani irin murmushi Umaymah tayi cikin tsantsar so tasa hannu ta kamo hannunshi daya nuna mata alamun ta fito.
Wani irin yalwataccen murmushi mai nuna tsantsar jin daɗi ya kumayi lokacin da yaji tasa hannunta tsakiyar kanshi.
Da sauri ya rusuna a bakin motar cikin sanyi ya manna kanshi da guiwowinta dake zuro woje,
kanshi ta shafa tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka ya kare mana kai da kariyarsa mai tarin yawa ya iya maka abinda idonka baya gani".
Amin Amin, su Haroon da Jalal, Jamil, Hibba, ƙanwar Haroon, da kuma Imran, Sulaiman, Aunty Juwairiyya dake kusa da Umaymah.
suka amsa tare da murmushi a fuskokinsu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer a hankali ya tashi kana ya buta hanya ta fito.
Tana fitowa Hajia Mama ta ƙara so gareta cikin tarin baiyana jin daɗi ta ruggume Umaymah tare da cewa.
"Ta ɗanki kawai kikeyi, mu har mun kusa mu bushe a tsaye".
Murmushi Umaymah tayi tare da cewa.
"Afwan ya Aunty kin san in Jabeer na yana wuri bana ji da ganin kowa sai shi".
Haroon ne ya taɓe baki tare da cewa.
"Uhumm ai mun saba ganin wariyar launin fata".
Hannunta tasa ta ɗan zunguri Haroon tare da cewa.
"Kishi".
Jamil ne ya ɗan kallesu lokacin da suka ɗunguma suka nufi Sade ɗin Jabeer cikin tura baki yace.
"Allah ko Mama kada ki bari Umaymah ta sauƙa a sade ɗin Hamma in dai ba sade ɗinmu zata sauƙaba Muda muke ƙanana sai ta sharemu saishi.
Tunda hakane ta sauƙa side ɗinkin".
Cikin dariya Umaymah ta juyo da sauri ta kalleshi tare da cewa.
"To Jamil harda kai, wato kaima ɗan team ɗin Haroon ne ko?
To sha kuriminka Aunty bazata shiga tsakanin uwa da ɗaba, ko Hajia Mama?".
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Hajia Mama daketa murmushi cikin jin daɗin tace.
"Haka kuma ɗa bazai shiga tsakanin ya da ƙanwaba,
Gaba ɗaya Jabeer ya kwace mana ke".
Murmushi mai kama da dariya sukayi gaba ɗayansu lokacin da suka shiga cikin falon.

Shi dai Jabeer sai murmushi yakeyi.
Ya Jafar kuwa in yaga Jabeer na murmushi sai shima ya ɗanyi murmushi.
Aunty Juwairiyya ce ta ɗan kalli Batul dake gaida Umaymah sakin fuska tace.
"Matar ƙani yau tun safe ban jikiba".
Wani irin murmushin jin daɗi tayi Allah yasani in Aunty Juwairiyya tace mata matar ƙani tana jin daɗi.
Cikin happy tace.
"Yau a kitchen na wuni inayiwa Umaymah girkinsu na larabawa".
Murmushi Juwairiyya tayi tare da cewa.
"Yo ai na rigaki, dama girkin bare bari kikayi mata".
Kanta ta ɗan juya takalli Sheykh Jabeer dake zaune kusa da Umaymah, in zaiyi mata mgna sai ya juya harce zuwa larabci.
A ranta take addu'o'in Allah ya nuna mata ranar da zata zauna kusa dashi haka a matsayin abar sonshi.
Tattausan Lips ɗin shi masu kama da kunnen fure ta kalla.
sunan jazir sai sheƙi sukeyi a cikin tattausan sajenshi da gemun tamkar an shafa musu mai.
Allah ya sani randa ta samu lips ɗin nan a matsayin mallakinta, tabbas sai ta kusan haɗiyesu.

Hajia Mama da kanta da ita da Aunty Juwairiyya ne suka rinƙa kawowa Umaymah abubuwan motsa baki yaran yar uwarta na zagaye da ita, Hibba ce yar autarta ta ƴar kimanin shekaru 16 kalli Jabeer cikin cikin sanyi tace.
"Hamma Jabeer Aunty Jazrah tace in gausheka, wai yaushe zamuje".
Kanshi ya juyo ya ɗan kalli Hibba cikin son yarinyar yace.
"Hibba auta yaushe kikeso muje".
Da sauri tace, sai na tambayi Aunty Jazrah".
Murmushi yayi kana ya kalli Aunty Juwairiyya yace.
"A shigar mata da kayanta, a ƙara gyara mata masauƙinta, yafi fadar Jalaluddin kyau".
Dariya sukayi baki ɗayansu.
Shi kuwa Sheykh Jabeer kamar ba shi yayi mgmar ba.
Ita kuwa Umaymah da Hajia Mama hararanshi suka ɗanyi tare da cewa.
"Ai babu fadar da zatafi fadar shi kam, shinefa gatanka".
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"A a kam Allah ne gatana, shi kuma da yake son ayi ta ɗimata".
Juwairiyya kanta tayi mamakin sakewar Jabeer sosai
Duk wanda ya ganshi zaiga tarin farin ciki tare dashi.

Nan dai suka zauna akayi ta hira.

Saida aka kira magriba ne, duk suka miƙe sukaje sukayi al'wala.


Batul kuwa tafi kowa farin cikin, zuwan Umaymah ko ba komai ta samu ganin Jabeer yadda take so.


Bayan an idar da sallan isha'i ne suka dawo masalacin.
A nan bisa dinnin area. Suka zauna nan sukaci abinci.

Koda suka gama ne, sunata hira a falon harda Jakadiyarsu.
Jabeer ne da yanzu ya fito falonshi cikin nitsuwa yace.
"Kai dan Allah ku barta ta huta mana".
Sai ya kuma ɗan kalli Umaymah tare da cewa.
"Umaymah muje ki gaisa da Lamiɗo, ya kirani yanzu yanata min ihu a kunne wai yaji kin iso tunda yamma kuma ban kai mishi keba".
Da sauri ta miƙe tare da cewa.
"To muje".
Hibba ce ta tashi da nufin binsu sai kuma ta zauna, jin Jabeer nace mata.
"Zauna Hibba saida safe kuje da Jalal."
Sai ya kuma kalli Jakadiyarsu cikin taushin murya yace.
"Ummi muje".
Itama da sauri ta miƙa.

A tare suka fito yana gaba Umaymah na binshi,
Jakadiyarsu na bayansu.
Suna tafe cikin jin daɗi ko ina yayi lib sai sanyin korayen ciyawi da furannin da dogayen bishiyoyin gwanda da ayaba da sukayiwa ko ina ƙawanya.

Suna isa ƙofar Gimbiya Aminatu da sauri.
Sallama ya basu hanya, wanda a ƙa'ida sai ya shiga ya nemawa mutun izinin shiga kafin ka shigo.
So amman Jabeer baida hijabi da sashin kakanin nashi,
shiyasa kai tsaye suka wuce.
Shiru babban falon babu kowa.
Haka yasa suka wuce sashin Lamiɗo, a hankali yayi sallama,
Cikin murmushin Lamiɗo ya amsa sallamar tare da cewa.
"Bismillah, ku shigo".
Kusan a tare suka kutsa kai cikin tamfatsen falon nashi.

Wani irin kallo sukayiwa juna,
Ganin...!






By
*GARKUWAR FULANI**MEVYASA? ME YAYI ZAFI SHI BA WUTABA? ME RIBARKU A CIKIN FIDDA LITTAFINA WOJE KU WATSASHI WA DUBBAN MUTANE? ME FA'IDAR HAKAN? NIYARKU KO TUNANIN KI, KADA WASU SUZO SU SAYA NE? A ZATONKI DANKU DAN KU ƁATA MIN RAINE? KO KUNA ZATON ZAKU HANANI SAMUN BINDA ALLAH YA RIGADA YA ƘADDARA YA RUBUTA RABO NANE? Nayi matuƙar mamakin al'ummar Annabi, Ni a zatona a iya hasashena, idan mace dan Allah da Manzonsa da darajar iyayen na kai ƙololuwar makurar roƙonda duk musulmi zai yi min al'farmar abinda na roƙa! Sai dai abin tsoro ashe abin ba haka bane, to wannan abun shine kadai ya bani tsoro, lallai kam tabbas muna akiruzzaman. Ai na sani kuma kuma mutanen kirki waɗanda kuka sai littafina da zuciya ɗaya kun sani dole za'a fitar da littafi. Sabida ba kaina farauba kuma ba kaina ƙarauba. Sabida haka kuyi haƙuri, dan Allah kuyi haƙuri, kuyi haƙuri da abinda wasu daga cikinku keyi. Alhamdulillah tunda na'annabi basa ƙare wa, tunda har gobe saya akeyi, wasu suna ganin gana satan a gabansu, amman sai su kauda ido suzo gareni su biya kuɗinsu a sasu a group ina godiya gareku*

Bayan Allah da Manzonsa da darajar iyayen dana haɗa mutane dasu bani da wani tsumi ko dabarar tsira daga sharrin masu zuciyar da basu san girman Allah da Manzonsa da darajar iyayensu ba. Domin duniya gaba ɗaya tana fama da gubar irin waɗannan. Iya tsaro dai kamar na bankuna, to amman me ana samun masuyin kutse a ciki har suyi sata. Manyan kampanunnuka na duniya ma suna fuskantar ɓarayj yan kutse, hakama ƴan Film suke fama da wannan matsalar, to mu ma rubuta suwaye mu da zamu tsira dasu, Roƙona anan dan Allah da Manzonsa abar maimaita mgnar a cikin groups ɗin GARKUWA. Su masu fitarwa dai na fita haƙƙinsu tunda inai musu posting sau biyu a rana kamar yadda na faɗa, su sukaji suka gani suka fitar, to wannan can musu. Ina da mutanen da nake matuƙar ganin kimarsu da darajar su a SPG shiyasa, bazan tanka musuba.


*Fatan al'khairi VIP groups ƴan dari uku ina al'fahari daku, kun bawa maras ɗa kunya, shiyasa tun forko nace Ni kune VIP na, duk da nasan kuma ɗin a cikinku tabbas akwai masu fiddawar, to amman dai naku baya zama illa kamar na SPG. Ina yinku ɗari bisa ɗari.*

Wlh rubutu yafi sauƙi akan mu'amalat da wasu taƙadiran da yake jarabtan marubuta da mgna dasu, ya ilahi ya mujibadda'awati, kai ina jinjina muku marubuta fama da wasu mutanen, wato da a haɗaka mgn da wasu gwara kawai a baka renon shanu garke guda na wuni ɗaya, domin shi dabba yasan abinda ake kira da makiyayinsa, amman wasu mutanen basu san darajar Allah da Manzonsa ba bare iyayensu. Allah ya kyau. Allah ka haɗamu da mutanen kirki.


*Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan layin 09097853276, ko ki turo dubu ɗaya ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai 09097853276.*

*Zan ƙara roƙo ba domin irinku kangararruba a a sai dan masoyan Allah da Manzonsa, dan Allah kada ku fitarmin da littafina. In kin san kin sayane dan ki fitar min da littafina to dan Allah da Manzonsa kizo kimin mgn ta pc kice kawai GARKUWA bani kuɗina bazan iya saya ban fitarba, wlh Salim alim zan meda miki kuɗinki in biki da godiya, in kuma baki sayaba zaki saya dan ki fiddane dan Allah kada ki saya. Dan Allah in kin rigada kin saya kuma Please turo ac no ɗinki kawai kadama kiyi mgnar kamai a take zan meda miki kuɗinki in cireki in miki godiya🙏🏻*



Lamiɗo da Galadima da Sarkin Shaɗi. Bisa alamu wata mgna mai mahimmanci suke tattaunawa.
Murmushi Lamiɗo yayi tare da kallon Umaymah cikin kulawa yace.
"Khadijah lale da zuwa Masarautar Joɗa."
Da sauri Umaymah ta ƙarasa gabansu, cikin ladab ta zauna gabanshi tare da duƙar da kai tace.
"Allah rene Barka da dare".
Kanshi ya jinjina irin na sarakuna kana yace.
"Barka dai Khadijah kinzo lfy, ya Sarki Aliyu?".
kakan Haroon kenan wanda ya haifi baban shi.
Cikin girmamawa tace. "Yana lfy yace yana gaidaka".
Kanshi ya jinjina, kana ya ɗan kalli Jabeer dake danne-danne a wayarshi.
Ya hakimce ya ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
Jakadiyarsu kuwa tayi shiru a gefe kusa dashi.
Galadima da Sarkin Shaɗi kuwa, murmushi sukeyi suna kallon Jabeer.

Gyaran murya Lamiɗo yayi kana cikin dattaku yaci gaba da cewa.
"Ina amsawa, ya kika samu jikin ɗan naki?".
Cikin murmushi ta juyo ta kalli Jabeer kai ta rusunar ganin samfa hankalinshi baya kansu cikin yin ƙasa da murya tace.
"Alhamdulillah na samu jiki ya worke!".
Galadima ne wanda yake ƙanine ga baban Lamiɗo ya amshi zan da cewa.
"To sai ki sanar mishi batun komawa Rugar Bani, dan ramuwa bisa cika ƙaidar..".
Shiru yayi bai ƙarisaba jin muryar Jabeer yana cewa.
"Ƙa'idar Allah da Manzonsa ne da zai zama dole sai an cika, ba ƙa'idar wani zalumci da tozarcinba".
Kanshi ya ɗan tanƙwara a wuyanshi.
Kana ya zamo kaɗan ya zauna gaban Umaymah cikin nuna rauninshi yace.
"Ayyah Umaymah kada kice min inje, Please Umaymah ki fahimci wannan abunfa al'adace ba addini ba, kuma abune da kai tsaye zamu iya ce mishi makaruhi in ma bamu haramtashi ba, ya za'ayi inje in sake tuɓe kayan jikina a gaban duniya wai dan in daki wani. Ni bana so.
Ba dai sune suka kainiba, suka kuma ce a dakeni, to dan me zasu buwayeni da sai munje na rama".
Haɗe fuska Umaymah tayi cikin kafeshi da ido tace.
"Ni bana iya yiwa iyayena musu. Jabeer tabbas na sani al'adace ba addiniba, amman ka sani duk wani abun da zakaga ya faru a duniya to akwai dalilin faruwarshi, kada kace zaka tsananta bincike tabbas lokacin zai baiya mana dalilin.
Bana son gardama kawai kaje Dan ALLAH".
Hannunshi yasa ya dafe kanshi,
kana yayi shiru Umaymah ta gama dashi da tace dan Allah, ya sani tabbas da a madadinsa Ayyah ɗin da yace forkon mgnar da ya mata da ya rigata cewa Dan Allah da shike nan yasan zatayi shiru.
Shi kuwa Lamiɗo murmushi yayi tare da kallon Umaymah cikin jin daɗi yace.
"Allah ya miki al'barka".
Da sauri tace.
"Amin ya Allah".
Galadima kuwa, murmushi yayi tare da jinjina kai.
Jakadiyarsu ma cikin jin daɗin tasirin mgnar Umaymah akan Jabeer take murmushi sabida ta sani.
Shi mutunne mai kaifi ɗaya, in yace eh tofa eh ɗince inko yace a a to a'ance.
Especially baya son duk wani abu da zaici karo da addininshi.
Kanshi ya jinjina Umaymah alamar shikenan idonshi yayi jazir alamun dole akasashi yin abinda baya so.
Kana ya kalli kakarsa dake murmushi tsuke fuskarsa yayi tare da cewa.
"Gimbiya Aminatu muje ki bani gashin da kikayiwa Lamiɗo".
Cikin dariya Gimbiya Aminatu tace.
"Iye gashinsama zan baka?".
Da ƙarfi yace.
"Eh shi zaki bani, ai in dukane kam ya iya zille kanshi ya turani.
Shine dan gashinsa zakice iye".
Murmushi tayi tare da bin bayanshi,
ganin Lamiɗo na mata alamun taje ta bashin.

Nan sukaci gaba da hira, suna tattauna wasu mahimman al'amuran da sirrine garesu iya su biyar.
Wato Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, Umaymah, Jakadiyarsu.
Bayan su babu wanda suke yarda da sanin sirrin Jabeer.
A hakanma kuma a suɗinma akwai wani sirrin da babu wanda ya sanshi sai Lamiɗo da Umaymah.


Suna zuwa har falonta suka wuce.
Wani kekyawan akoshi mai masifar kyau ta ɗauko mishi.
Ta ajiye a gabanshi.
Inda yake zaune a ƙasa bisa carpet ya naɗe sawunshi.
fork ɗin dake saman fefeyin ya ɗauka.
Daddageggen gaseshen jan namane wanda yaji wuta ya gasu gashin tukunyar ƙasa yayi tiɓis.
Sai wani irin ƙamshi na musamman yakeyi,

A hankali yake sa Fork ɗin yana yagan tattausan tsokokin yana sawa a baki.
Ita kuma tana zaune gefenshi.
Tafashesshen madaran shanu mai ɗan ɗumi ta miƙa mishi a wata ƴar ƙwarya mai kyau.
Taune naman yayi tare da haɗiyewa kana cikin zuba mata ido yace.
"Dole sai na karɓa da hannun nane? Ki ajiye mana.
Da wanne hannun zan amsa tunda inacin abinci dana daman".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Dole sai ka amsa, bazan baka shi a ƙasa".
Kanshi ya ɗan rausayar tare da cewa.
"Allah ya nuna min ranar da za'a bar.
Wannan tsare-tsaren shamfi na masarautar Joɗa. Komai da ƙaida da yadda ake yinshi".
Ita dai miƙa mishi ƙwaryar takeyi dole ya ajiye spoon ɗin yasa hannunshi ya amsa.

Nan suma sukaci gaba da hira.
Sai kusan sha ɗaya Umaymah da Jakadiyarsu suna fito.
A nan Gimbiya Aminatu ta ajiyesu suma saida sukaci gashin nata kafin suka tafi.

Kafin su isa Side ɗinsa dai sha biyun dare tayi.

Haka yasa suna isa suka samu ba kowa a falon.

Sai Haroon da suke jiyo muryar sa, a falon Jabeer.

Cikin nitsuwa ya matso kusa da Umaymah a hankali yace.
"Sai da safe Umaymah kiyi bacci ki huta."
To tace har ta juya zata tafi sukaji Muryar Haroon yana cewa.
"Abba yazo wurinki zaku gaisa bai samekiba, nace mishi kun tafi wurin Lamiɗo yace, to saida safe ya gaidaki da hanya Hajia Mama ma yanzu ta fita, tace Lamiɗo ya riƙe mata ƙanwa".
Murmushi tayi tare da cewa.
"To Allah ya bamu al'khairi saida safen".
Amin Amin suka ce.
Kana shida Haroon suka wuce Side ɗinsa.

It's kuma Umaymah da Jakadiyarsu suka wuce.
Side ɗin da kullum in dai Umaymah tazo nan take sauƙa.

Suna shiga suka samu, tuni Hibba tayi bacci, wannane ya basu damar tattauna wasu mahimman sirrukansu.

Nisawa Umaymah tayi bayan ta saurari jawaban Jakadiyarsu Jabeer cikin tsantsar tafasar zuciya da tarin baƙin ciki tace.
"Uhummm suyi dai Ni nan ina dai-dai- da ƙugun ko wanne shege da shegiya,
In sha Allahu zasusha mamaki.
Zasuga yadda Ubangiji ke ikonsa, ban cire raina ƴar uwarta zata sake rayuwar enci da salama, da izinin Ubangiji zataga sakayar waɗanda suka cutar da ita da yaranta a gaban idonta.

Cikin zubda hawaye Jakidaya tace.
"In sha Allah, sai farin ciki ya dawo, a sashinta, inata addu'a a kullum a cikin dukkan sallolina, Allah ya kare ahlinta, ya kuma baiya gsky tayi halinta kowa ya gani".

Amin Amin Umaymah tace tare da share hawayenta.

Washe gari ranar Alhamis. Ta kama yau kwana shida da faruwar gasar Shaɗi, kana gobene za'a koma dan ramuwa,
A goben kuma zai cika kwana goma da kisan gilla da kafurai ƙabulun Ɓachama sukawa Fulanin Rugar Bani.

Misalin ƙarfe sha biyu na safe.
Fadar Sarkin Nuruddeen Bubayero Joɗa, cike take maƙil da tawagarsa kama daga.
Galadima, Waziri, Wambai, Dan buram, Dan iya, Ɗan isa, Ɗan Kade, Sarkin fada, Sarkin yaƙi, Sarkin Dowaki, Sarkin Gabas, Sarkin Kudu, magayaƙi, Jarma uban doma, Makawa Ɗurɓi, Turaki, Da dai sauran members ɗin masarautar baki ɗayansu,

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment