Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda su kullum dama suna zuwa.

Wani irin hadarine mai ƙarfi ya taso daga ƙasa, ganin hakane yasa, Gaini kwallawa Shatu kira wacce take can cikin ƴan uwanta mata makiyaya, jin shiru bata amsa bane ya nufi wurin da suke zaune,
Cikin kula yace.
"Aysha tashi keda Hinde dasu Mero duk ku tafi gida, kunga hadarine mai ƙarfi ke tasowa daga ƙasa da alamun za'ayi ruwa mai ƙarfi".
Cikin ƙarfin hali da son wasa cikin ruwan da taketa hari murya a sanyaye tace.
"Ba komai ya Gaini zamu jiraku ai lokacin tashi kuma ya kusa ko?".
Su Giɗi dasu Aro da sauran makiyayan ne sukace.
"Ya Gaini barsu mana ba kiwo zasuyi ba ai makiyayin shanu da tumaki baya gudun ruwa duk yawa shi".
Cikin jin daɗi sukace, eh mana,
Shi kuwa Ya Gaini murmushi kawai yayi tare da cewa.
"Shike nan yau zakusha dukan ruwa".
Murmushi sukayi sukace "Babu matsala". daga nan mazan duk suka koma wurin kula da dabobbin nasu da suka duƙufa cin koren ciyawa.

Su kuwa Shatu da Hinde a hankali sukaci gaba da tafiya, sosai tsarin wurin da yanayin shigar suturar dake jikinta yayi tsananin dacewa da ita.
Doguwar rigace irin tamu ta fulani, yadin farine, sai daga samanshi akayi mishi kolliya da zaron huɗu, mai color red white, blue, yellow, and green, wanda aka ƙawata saman rigar da kolliyar zanen ɗawisu, inda daga kafaɗunta har zuwa saman ƙirjinta, duk an shimfiɗa zaren, bisa wuyan rigar mai V.
sai kuma hannun rigar shima duk an zagayeshi da kolliyar,
Kana sai tsakiyar rigar dai-dai kan ƙugunta shima an ƙawatashi da wannan kolliyar ulu irin namu na fulanin daji,
Kana sai ƙasar rigar can itama an ƙawata da wannan zaren.

Sai dogon gashin kanta da yake zube a kafaɗunta, yayinda daga saman goshinta kuma tasa, bandana amman irin namu na fulani mai kalolin ƴaƴan tsakiya, ta zagaye kanta dashi, sai kolliyar da tayi a fuskarta irin ta asalin fulani, a goshinta zanen kan shanu tayi, shaidar cikekkiyar bafulatanace, sai kuma ƙasan lip ɗinta na ƙasa zuwa kan ɗan gemunta shi kuma taja zane da kuma yin ɗigo-ɗigo a gefenshi.
Sai wata kekkewar jakar sakan ulun mai kalolin kolliyar jikin rigarta data rataya a hannun damanta, wanda cikin jakar kuma ruwan shantane a ciki sai sassanyan kinɗirmo da goran zuma, sai ɗan sandar mu ta gado, takalman sawunta irin sau cikin nanne daku mutanen cikin birane kuke masa laƙabi da tashi kabi shanu.
Tayi masifar kyau a cikin wannan shigar tamu ta gado, kyau iya kyau farar fatarta ta baiyana tamkar balarabiya gashin girarta ya konta lib lib.

A hankali suke ɗan tattaki a cikin dogayen saunukan, da koriyar ciyawa da tayiwa ƙasanshi ƙawanya. suna ɗan tafe
Suna ɗan tsinkar ya'yan kanya da gwandar daji da suke cike da wurin Chaɓɓulle wato tsada.

Hadari kuwa sai gamgami yakeyi gabas da yamma kudu da arewa, ko ina yayi dib babu motsin komai sai nasu dana dabobbin su,
Iska ta tsaya cak koda ganye ɗaya baya kaɗawa duhu ya kareɗe illahirin yankin.

A hankali Hinde ta kalli sararin samaniya cikin tsoron ganin gaba ɗaya duniyar tayi baƙiƙƙirin ko ina yayi dib, hakanne yasata ɗan zaro ido tare da cewa.
"Kai Shatu, kalli sama, fa hadarin nan yayi duhu da yawa gsky mu tafi gida".
Da sauri ta ɗago kanta kana tasa hannunta na hagu ta ɗan kare saman goshinta kaɗan, ware idanunta tayi ta kalli sararin samaniya, wani irin azabebben firgita da tsorone ya rufeta wanda yasa ta juya da azaban ƙarfi ta ruggume Hinde dai-dai lokacin, sukaga wani irin tartsatsin azabebben igiyar...!






Dan Allah da Manzonsa in dai kin san zaki sayi littafinane ɗan ki fiddashi na roƙeki da Allah da Manzonsa da darajar su. Kada ki saya bana so, ki riƙe kudinki.




By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 9

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘


*FREE PAGE*

*TURO KATIN MTN NA ƊARI UKU KACAL ta wannan number 09097853276 DOMIN SAMUN DAMAR KARANTA littafin GARKUWA, ba tare da haƙƙin kowa a kankiba. Akwai Special Group shi kuma na 1k rak, ki turoshi ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo shaidar biyanki ta wannan number dai ta WhatsApp 09097853276*


~Ga masu buƙatar kayan gyara na amare, akwai set-set masu kyau, a ƙananan robobi masu sauƙin kuɗi, akwai kuma na manyan robobi masu zafi, akwiasu dai-dai da tsarin al'jihun mai ƙarfi da mai rauni, ina araha ina hana bashi. Koda kuɗinka saida rabonka, kayan Kamfani daban dana shago.~

*Al'ummar Hausawa mazauna Saudiya wannan shafin nakune kyauta gareku, domin jiya da yau saida mai zaton babu wasu masu karanta littafi sama daku. Nasha mamaki da sanyin safiya naita cin karo da numbers ɗin ƙasa mai tsarki suna ta antayo min manyan kuɗi na ƙasa mai tsarki tun ina ƙidaya numbers ɗin +966 har dai abun yaci tura sabida yawansu, ashe daga zauren Umar Maisanyi sukayi ta antayowa gareni. Godiya mai tarin Yawa Umar maisanyi mai Tsakar gida You tube limamin tsakar gida*



Walƙiya mai tsananin haske da tartsatsi wanda saida ya haska gaba ɗaya, dajin ya zamana, har kana iya ganin inuwar dogayen bishiyoyin wurin da sukayi musu ƙawanys.
Wani irin tsoro da firgici da karkarwan ne ya bijirowa Aysha.
Cikin dauriya da sabo da ganin ire-iren irin waɗannan ababen a wurin kiwo, Hinde ta kamo hannun Shatu tare da cewa.
"Kai Aysha babu komai fa walƙiyace kawai fa kai".
Sai kuma tayi dariya tare da cewa,
"Uhum a hakan kike tunanin jurar taraddadin da muke gani cikin tsaunuka in muna kiwo".
Janye jikinta tayi daga jikin Hinde, hannun tasa ta tattare gashin kanta dake baje a kafaɗunta, tubkeshi tayi cikin, fidda numafashin tsoro take karisa addu'o'in datake tayi a bakinta, a hankali taja da baya ta jingina da jikin ƙatuwar bishiyar Gamji dake gefensu, jingina kanta tayi jikin bishiyar gamjin tana jin yadda zuciyarta ke harbawa, pat-pat da azaban ƙarfi domin tasan Hinde bata san me idonta ke shirin hango mataba,
ita kuwa Hinde, a gabanta take tsaye ya zamana sun fuskantar juna.
Su Ya Gaini kuwa sun duƙufa kiwonsu kamar dai yadda suka saba, ruwa ko iska ko zafin rana da ƙishi baya kora makiyaye daga kiwo a daji ya dawo gida.
So duk kowa yana yankin da yake bawa dabobbin tsaro, sam basuma hango su Aysha sosai.

Ita kuwa Shatu idonta dake lumshe ta fara ƙoƙarin buɗewa sabida wani irin tashi da taji tsikar jikinta nayi.
Hinde kuwa ido ta zuba mata tana ganin yadda ƙirjinta yake sama da ƙasa alamun tsananin firgita.
A hankali ta ware manyan kyawawan idanunta.
Wani ƙaton curi, dake can bayan Hinde ta zubawa ido sabida wani abu da take gani kamar hayaƙi yana fitowa ta ƙananan ƙofofin curin. Ita kuwa Hinde bata san meke wakana ba sabida, ita baya ta bawa curin, asalima yanzu kanta ta ɗaga sama tana shan ruwan dake cikin goranta.

Ita kuwa Shatu so take ta janye idanunta daga kan wannan CURIN amman sai taji ta kasa, bugun da zuciyarta keyine ya tsananta, lokaci ɗaya jikinta ya fara tsuma da karkarwa zufa mai azabar zafi ta fara tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta.
Yayin da zuciyarta. Ke harba jini one litter. A Cikin ko wanne one second. Bakinta ta buɗe da nufun furta addu'o'in dake jere a zuciyarta amman sai taji ta kasa, zuru-zuru tayi da idanunta lokacin da taga wani dogon abu yana fitowa daga cikin babban ramin dake tsakiyar CURIN nan, a hankali ta ɗaga kwayar idanunta sama tana bin abin da kallo, wani irin dogon numfashi taja, ganin abun nan yana miƙewa yana yin sama, abun dogo kamar igiya sai dai kuma yanada zane kala-kala red, yellow, green, blue.
Kuma abun biyune ɗaya a sama ɗaya a ƙasa, cikin ranta take iya ammabaton sunan Allah ganin zahiri fitowar bakan Gizo daga cikin curi Allah ya nuna mata, ras zanen bakan Gizon nan yayi kama da kalolin kolliyar jikin rigarta,
Kanta ta ɗaga sama, tana bin Bakan Gizon da kwayar idanunta, tana gani har ya haura sama can ya konta a gicciye gabas da yamma kudu da arewa, kana kuma mai hasken ras yana sama mai ɗan dishi-dishin yana ƙasa. Wanda a falsafar al'ummar Duniya ake cewa suma mata da mijine, muddin kaga mai hasken in ka zuba ido zakaga mai dishi-dishin wanda akecewa, mijin shine dishi-dishin kuma shike goyo matarsa shiyasa sai ake ganin mai hasken shine a sama.

Wasu irin numfarfashi take ja da azaban ƙarfi da razana, kar-kar haka jikinta ke rawa.
Cikin tsoron halin da take ciki Hinde ta wurgar da goran dake hannunta, tare da cewa.
"Hande en boni, yau munga ta kanmu Shatu me haka meya sameki?". Ina babu mgna sai zamewa da ta farayi tanayin ƙasa alamun zata faɗi, ganin hakane yasa, Hinde juyowa da ƙarfi ta fara rabƙawa su Ya Gaini kira.
"Ya Gaini! Ya Seyo! Ya Lado, Wayyo Ya Giɗi kuzo kuga abinda Shatu keyi".
Maganarta ta karshece ta sasu, tasowa a guje gaba ɗayansu suka nufosu da gudu,
kafin su isoma Aysha ta faɗi ƙasa zaune, sai karkarwa da rawan sanyi takeyi.
Suna isa Ya Gaini yasa hannu ya tallabota ganin yadda taketa karkarwa, idanunta na rufewa,
Seyo ne ya kalli Hinde cikin kiɗima yace.
"Subahanallahi Hinde me ya sameta?".
Cikin kuka Hinde tace.
"Ban saniba wallahi haka kawai naga tana karkarwa".
Giɗi ne ya zauna kusa da yayan nashi kanshi ya sunkuyo kanta yana kiran sunanta a jere a jere.
"Aysha! Shatu. Ayshatu tashi buɗe idonki ki gaya min meya sameki meke miki ciwo".
Ina babu magana saima kara rumtse idanunta da tayi tare ƙara ƙaƙƙame jikin Ya Gainin nata.
Ya Lado ne da Seyo suka sunkuyo kanta addu'o'in suka rinka tofa mata, duk addu'ar da tazo bakinsu tofa mata sukeyi, Giɗi kuwa ruwa yasa a tafin hannunshi yana shafa mata a fuskarta.

Cikin al'hini sauran makiyayan duk suka iso kansu, ganin yadda suke birkice ne ɗaya daga cikin ƴaƴan Alhaji Haro da kuma Alhaji Umaru sukace.
"Gaini mu tafi gida da ita, tunda dama lokacin tashinmu yayi, an kusa fara tafiya masallacin juma'a."
Cikin damuwa Giɗi yace,
"To ai bazata iya tafiya ba".
Seyo ne ya miƙe cikin sauri yace.
"Bari inje in kawo doki sai mu ɗaurata a kai".
Da sauri Manu ɗan Alhaji Haro yace.
"Yauwa yi maza, kunga ku kuma Gidi kuje duk ku haɗo mana kan dabbobi ku fuskantar dasu hanyan gida".
Ai kuwa haka akayi sauran yaran duk suka kaɗa shanun.
Koda Seyo ya kawo dokin, shida kanshi ya hau baya sannan aka ɗaura mishi ita a gabanshi, a haka suka nufi gida.


Koda suka isa gida, da kanta ta taka har zuwa cikin gida, suna biye da ita a baya.
Kai tsaye ɗakin Ummey ta shige, bisa gado ta konta ta duƙunƙune tana rawan sanyi.
Da sauri Ummey da Inna da Junainah suka biyota a baya.
Cikin tsoro Inna tace.
"Subahanallahi Shatu meya faru".
Ummey kuwa gefenta ta zauna, tare da jawo borgo tana rufe mata jikinta.
Giɗi ne da yanzu ya shigo, shine ya basu lbrin iya abinda suka sani.
Seyo kuma cewa yayi a mata hayaƙi.
Haka kuwa akayi sukayi mata hayaƙin kana Ya Gaini ya zauna yayi mata rubutu nanma aka wonke aka bata.

Jin jikinta yayi zafi jau ne, alamun zazzaɓi ne ya rufeta yasa, Ya Lado yaje ya ɗauko mata mgnin a ɗakin Bappa, nan Ummey ta bata tasha, a take bacci ya ɗauketa.

Ummey kuwa da Inna woje suka fito sunata dariya dan su a zatonsu ko gajiyane yasata hakan tunda ita dai bata saba zuwa kiwoba tunda tanada yayu maza da yawa.

Koda akayi sallam Juma'a aka idar, su Bappa da yaranshi kab basu dawoba saida akayi sallan la'asar kafin suka dawo gida.


Ummey kuwa da Inna aikin abincin dare sukeyi wanda girkin ranar jumma'a na dabanne, zabbi biyar suke yankawa kullum jumma'a wata rana kuma tattabaru wani lokacin kuma jan nama Bappa ke saya to yauma hakanne.

Inna ce zaune tanayi musu wonke-wonke yayinda Junainah kuwa keyin shara, dama wonke-wonke aikintane to duk randa takeji tsiya sai tayi ta ƙorafi, shiyasa yau tana farawa Inna ta fara aikin.
Ummey kuwa tana cikin kitchin ɗinsu, wanda dama da Shatu lfyarta lau muddin tana gida ita keyi musu, girki domin Ummey ta horeta da iya girke-girken na ban mamaki.

A hankali Shatu ta bude idanunta daga baccin da takeyi,
Cin karfin jikinta ya ɗan dawo, a hankali ta tashi zaune, da sauri ta fito woje, sabida ganin ita ɗaya ne a ɗakin.

Da sauri ta fito, Inna ce ta ganta cikin kula tace.
"Shatu kin taso?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh.
Cikin kula tace.
"To ya jikin naki?".
A hankali tace.
"Da sauƙi, Inna zanyi wonka".
Mikewa tayi dan dama ta gama wonke-wonken. Botiki ta ɗauka kitchin ta shiga, ruwan zafi ta ɗebo nan take cewa Ummey.
"Shatu ta farka".
Murmushi Ummey tai tare da cewa.
"Na jita ai wai zatayi wonka, ke kuma harda biye mata kamar ta shekara ba lfy, Shatu ba dai rakiba".
Dariya suka ɗanyi, ita kuwa a tsakiya gidan ta zauna kan dakalin da ke gindin bishiyar ceɗiya dake wurin.

Bayan inna ta kai mata ruwan ne ta kalli Junainah cikin sanyi tace "Junnu zoki rakani inyi wonka Mana."
Ido Inna ta zaro tare da cewa.
"Hahhh Shatu yau kuma ta rakaki wonkafa kikace".
Kanta ta gyaɗa cikin raunin fuska tace.
"Eh Inna tsoro nakeji shiyasa".
Ummey dake kitchin ne ta fito rike da aikoshn data zuba zabbin data soya a ciki, tace.
"Shatu ki rage tsorofa".
Kai ta gyaɗa kana taja hannun Junainah tare da ɗaukan kondon kayan wonkanta,
A bakin ƙofar mashiga bayan gidan tace.
"Yauwa Ƙanwaliya jirani a nan".
To Junainah tace,
haka ta tsaya tana jiranta,
Ita kuwa wonkanta tayi, a nitse kana, tana fitowa.
Tayi al'wala, ɗakin Ummey ta shiga, sallan azahar da la'asar ɗin tayi, sannan ta zira wata tattausar doguwar riga.


Turare ta ɗan fesa kana, ta fito,
Gefen katangar kitchin ɗinsu ta samu Ummey tana haɗa wuta a murhun dake wurin.

Inna kuwa zaune take a gefe, da turmi a gabanta, kana tana jajjaga tattasai da tumatur da kuma tarugu da al'basa.

Taburman data fito dashine ta shimfiɗa gefensu.
Inna ce ta kalli Junainah da itama yanzu ta fito wonka tace.
"Yauwa Junainah zoki kawowa Addanki abinci."
To tace kana tazo ta shiga ɗakin Inna.
Ta fito da tire a hannunta da wasu ƴan kananun robobi guda huɗu a kai masu marfi, sai kuma kula a tsakiyarsu.
A gaban Shatu ta ajiye kular.

Kana ta wuce ta nufi ɗakin Ummey.
Ita kuwa Aysha kular ta buɗe, dambun zogalenen a cikin wanda yaji, ganyen zogalen da kuma al'basa, sai tururi yakeyi.
Ƙananan robobin kuwa, ɗaya dakekken yajin ƙaragone wanda yaji magi da borkino da kuma tafarnuwa.
Kana ɗaya robar kuma, soyayyan man shanune a ciki.
Ɗaya kuma yankekken al'basane da kuma tumatur, sai dafeffe kwai duk a yayyanka,
Kana ɗayan kuma dambun namane mai laushi, a ciki,
ɗan karamin aikoshin dake gaban Ummey taja, ta zuba dambun, kana ta zuba sauran kayan hadin.
A hankali ta fara ci.
Junainah da ta fito yanzune ta kalla tare da cewa.
"Junainah bani ruwa".
To tace kana ta juya ta nufi gindin randunarsu inda suke jere a ƙalla sun kai shida ko dan ba manya bane dukansu na taɓone masu ɗan karen sanyi, ga kuma inuwar bishiyoyin ayaba da sukayiwa randunar ƙawanya,
Shiyasa ko yaushe ruwan zakajishi kamar na firiji,
A kofin silver ta ɗebo mata kana tazo ta zauna gefenta, sunaci a tare.

Ummey kuwa tukunyar ƙasa ta ɗaura a wuta tare da tsulala man shanu, a ciki.
Kayan miyan da inna ta kirɓa ta amsa ta zuba a cikin manda yayi zafin ta fara soya miyar, zabbin da zatayi musu.
Kana ɗaya murhun kuma ruwan tuwo ta aza a tukunyan ƙarfe.
Inna kuwa data gama kirɓa kayan miyar, shinkafar tuwon ta ɗebo tazo tana wonkewa.

Suna cikin haka su Bappa da yayunta maza suka dawo.
Nan suka shimfiɗa katuwar taburma a tsakar gidan.
kana Giɗi ya ajiyewa inna ledodin tsarabar jumma'a da Bappa kanyi duk ranar sati.
Tirirruka Ummey ta miko mata ta baza, juye kayayyakin a cikin.
Reke,Lemu, kwakwa, da Giginya, da kuma dafaffiyar gyaɗa, da ƙosai mai zafi da biredi da soyayyen doya da fulawa mai jawa.
kayan cimarmu kenan fulani

Zubawa maza nasu akayi, aka basu a tsakiyarsu suka ajiye sunaci da mahaifin nasu.
Shatu kuwa da Junainah aka basu nasu. Ummi da Inna kuwa sun ajiye nasu dan aiki sukeyi.
Ya Gaini ne ya ɗan danki ƙosai da bredy yasa a bakinshi,
tauwana yayi kana idanunshi na kan Aysha saida ya haɗiye kana yace.
"Shatu, ya jikin naki?".
Murmushi ta ɗanyi sai kuma ta ɗan harari Junainah dake cewa.
"Uhum ta worke ai dama kawai hegen tsorone da raki".
Dariya sukayi baki ɗayansu. Seyo ne wanda yakeda tarin jinƙai da nitsuwa,
ya ɗan afa geɗan daya ɓare a bakinshi tare da cewa.
"To Amman Shatu meya samekine lokaci ɗaya kika firgita?".
Giɗi ne da shi kuma doya yakeci yace.
"Kamar mai cutar al'janufa ta zama".
Bappa ne ya ɗan kalleta cikin kulawa yace.
"Shatu meya sameki ne?".
Murmushi ta ɗanyi tare da kallon Ummey dake cewa.
"Uhum tsorone da gajiya fa".
Kai ta jujjuya a hankali tace.
"Allah ko Ummey ba tsoro bane".
Sai ta kuma meda hankalinta kan Bappa cikin sanyinta tace.
"Bappa naga abinda ya firgitanine.
Shin Bappa dama bakan Gizon cikin curi yake fitowa ne?."
Cikin mamaki suka zuba mata ido baki ɗayansu.
Bappa ne da kanshi yace.
"Ban fahimceki ba Shatu".
Bredy dake gefenta ta gutsura kana ta dandola da zuman data sa Junainah ta kawo musu, a baki ta ɗansa ta tauna kana a nitse ta basu labarin abinda ta gani da kuma yadda taji, ta ƙara da cewa.
"Bappa dama bakan Gizo a curi suke fitowa ne?".
Cikin mamaki da al'hini yace.
"Allahu al'alamu. Sai dai koma menene, lallai tabbas akwai abinda ke tunkarar rayuwarmu, fatana mu dage da addu'a koma menene Allah ya kawo mana shi kan al'khairi ya kuma sauƙaƙa manashi, zan kuma bincika in sha Allah.
Sannan kada ku gayawa kowa mgnar nan".
Ya karishe mgnar da kallon Junainah.
Wannan labari ya sasu cikin dogon nazari. haka dai sukaci gaba hira kamar yadda suka saba.

A can cikin yola kuwa, yau tunda Ya Jafar yaje sallan juma'a ya dawo baiga Ƙaninshi Sheykh ba, gaba ɗaya ya tashi hankalin ƙanenneshi da iyayenshi.
Domin kama hannun Jalal yayi yana kuka, yana jan Jalal zuwa sashin Sheykh koda suka shiga, Jamil kuwa sashin mahaifinsu ya nufa. Ba tare da ya saurari
Hadiman ba ya wuce.
A babban falon ya samu , Abba
Haurawa sama yayi yana shiga kuwa ya sameshi a falo shida jarabebboyar amaryar tasa cingom dinshi.
Sai dai tana konce bisa kujera,
Shi kuma yana zaune bisa sallayane ya fuskanci al'ƙibla, da ƙur'ani a gabanshi yana karatu cikin suratul Khafi.
cikin rauni Jamil ya ƙaraso gabansa.
Bai kulashiba har saida ya kai ƙarshen surar kana ya shafa addu'a.
Cikin haɗe fuska da alamun faɗa yace.
"Jamil lfy kuwa mehakan?".
ido na zubda hawaye yace.
"Abba Ya Jafa".
Rai a hade yace.
"To me zan mishi?".
Cikin zubda hawaye yace.
"Abba tunda aka dawo aka sauƙo sallan jumma'a fa yaketa kuka yana bin Jalal yana kuka alamun a kaishi wurin Hamma Jabeer, yau ko abinci baiciba, Aunty Juwairiyya ma sai kuka takeyi hakama su, Jiddah."
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"To ni zaka gayawa? Kaje ka gayawa Mamanku mana".
Wasu sabbin hawayene suka zubowa Jamil a hankali ya juya ya fita".

A can sashin Sheykh ya samesu, Juwairiyya da Jalal ɗin da Affan sun tasashi a gaba, Affan yanata kuma, shi kuwa Jalal sai tattaune laɓɓansa yakeyi, da sauri Jamil ya iso cikin sanyi yace.
"Affan je ka gayawa Mama".
Da sauri Affan ya juya har zai fita kuma ya dawo jin Juwairiyya na cewa.
"No Affan kada kaje, ka gaya mata, nasan yanzu tana bacci ne".
Shi kuwa Ya Jafar sai ya shiga ɗakin nan ya fito ya shiga wancan ya fito yana kuka kuma.

Shigowar Abbane ya sasu su Jalal duka fita.

A hankali Abba ya kamo hannunshi suma suka fito, da mamaki a fuskar Jamil ya bisu da ido.

Shi kuwa Abba yana riƙe da hannun babban ɗan nashi suka wuce har makoncinsa,
Gefen gado ya kontar da dashi, kana a hankali yake shafa kanshi cikin taushi da tausayawa yace.
"Jafar kayi haƙuri kayi baccinka kabar kuka, Sheykh yana lfy lau, ya tafi ƙasar Saudia ne shida kakarku Sitti."
Shiru yayi yana kallon mahaifin nashi.
Shi kuwa Abba, kanshi yake shafawa yana kontar mishi hankali a take yayi baccinsa.


Bayan sallan ishane Jamil yaje wurin Kakansun ya sanar mishi halin da ake ciki ya ƙafarsa cewa.
"Allah rene, magar gsky kace Hamma Jabeer ya dawo, sabida abin ya Jafar yana tsananta in bayanan".
Murmushi kakan nasu yayi tare da cewa.
"Uhum ai Allah ya sauƙaƙa abinda zai taso Sheykh ya dawo ba tare da an gama dai-dai-ta abinda ya kaishi ba Dole shi wannan mai saɓulellen mondon Jalaluddin shi zai dena yawon iskanci ya zauna ya kula dashi tunda yafi kallonshi a madadin Sheykh".
Cikin takaici Jamil yace.
"To ni zan kai Ya Jafar saudia wurin Sheykh ɗin suci gaba da zama a can in sun so, tunda dai kun san Sheykh shine GARKUWAnmu".
Cikin kontar da murya kakan nashi ya ɗan tausasashi kana yace in yaje ya turo mishi Jalal.



A can Saudia kuma, sosai aketa shirya yadda ɗaurin Auren Sheykh da Jazrah zai kasance, duk da basu sanar mishiba, sabida kashedin da Sarki Jalaluddin da Nuruddeen sukayi musu dan ko yaushe in dai ana shirya batun aurenshi muddin yaji sai yaƙi fir yayi ta kaucewa dole a ƙarshe aure ya fasu, to wannan abunne yasa ba'a sanar mishiba.
Sai dai yasan batun zuwan da Jazrah take sashinsu wai nune da ita suke zaɓa mishi in tayi mishi.
To shi kuwa bayan gaisuwa ko sannu bai taɓa haɗasu da itaba.

Haroon kuwa da Jannart sunata shirye-shiryen dawowa gida Nigeria.


A garin Bani kuwa,

Yau tun bayan sallan isha'i yaro ya shigo yace, Ya Salmanu yana sallama da Aysha,
haka kuwa ta fita taje,
Suka zauna a dakalin ƙofar gidan nasu suna hango yadda,
Yara keta wasa a dandali domin ranar jumma'a tafi ko wacce rana a garesu wurin shanawa.

Ya Gaini ne ya fito riƙe da hannun Junainah, a bakin ƙofar suka wuce Su Shatu
Bayan sun gaisane ya wuce riƙe da hannun ƙanwar tasa,
Murmushi Salmanu yayi tare da cewa.
"Shatu, inaga dai aurenmu dana babban yaya rana ɗaya za'ayi shi".
Murmushi itama tayi, tare da cewa.
"Tab shifa har an kai kayan aure".
Ido ya ɗan lumshe tare da cewa.
"To ai in kin bani dama nima gobe-goben nan sai a kawo kayan aurenmu ko?".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta, alamun jin kunya.

Su Ya Gaini kuwa kai tsaye ƙofar gidan Ahaji Haro sukaje,
A bakin ƙofar suka tsaya, sunkuyowa ya ɗanyi a hankali yace.
"Yauwa ƙanwaliya maza shiga cikin gidan kicewa Addanki Bintu tazo".
Cikin happy tace. To kana ta shiga cikin gidan da sallama.

Kamar yadda gidansu yake hakama gidan Ahaji Haro duk suna zaune a tsakiyar gida da yaranshi da matanshi sunata hira, bayan ta gaidasune taje gefen Binto cikin raɗa ta gaya mata saƙon ƴaƴansu.

Wani ɗan kekyawan matashi ɗan kimanin shekaru sha takwas mai sunan Junaidu ne ya kalli Junainah cikin tsananin so da ƙaunar yarinyar yayi murmushi tare da taɓa mamanshi cikin raɗa yace.
"Inno ga surkarki in Allah ya yarda".
dariya suka ɗan yi dan kowa yasan Junaidu yasan son da yakewa Junainah tun tana ƙaramar ta.

Ita kuwa Junainah hannun Binto ta riƙo suka fito tare,
Junaidu na biye dasu a baya,
Koda suka fita, Gaini ne ya kalle Junaidu tare da cewa.
"Yauwa Junaidu raka min Junainah gida ko".
To yace kana yabi bayanta suna tafe suna hira, sunzo dai-dai ƙofar gidansu Ahaji Umaru ne suka samu Ya Seyo da Hinde suna hirarsu.

Koda suka wuce, murmushi Junaidu yayi tare da cewa.
"Junainah sai yaushe zan fara zuwa muma muyi hira ne?".
Cikin yin ƙasa da murya tace.
"Sai na ƙara girma kafin nan Addana tayi aure".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ko dai bakya so nane".
Da sauri cikin yarinta tace.
"A a ina sonka mana".
Dariyar jin daɗi sukayi baki ɗayansu, sun zo kusa da ƙofar gidansu.
Ya Ba'ana ne sukayi kiciɓis dashi, murmushi yayi tare da cewa.
"Yauwa Ƙanwaliya kuzo mu shiga in baki aike ki kaiwa Shatu".
To sukace kana sukabi bayanshi, a tsakar gida suka samu, Iya Bultu majaifiyar Ya Ba'ana kena ƙatuwar mace

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment