Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kauda Shirka da waɗannan mushirkan a wannan yankin."
Ido ta rumtse wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mata.
Cikin muryar dake nuna ƙunar ranta tace.
"Ya Salmanu wane mataki ake ɗauka kan neman su ya Giɗi kuma?".
Kanshi ya jinjina tare da cewa.
"Yana cikin matakin shiga cikin ƙabilar mu yaƙesu, mu kuma bincika ko sun ɓoye su Giɗi a cikin garin nasu".
Ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Allah ya taimaka".
Amin Amin.
Murmushi yayi kana yace.
"Kinji batun gasar da akayi ko da nasarar dake tinkarar rayuwarki ko?".
Cikin sanyi tace.
"Kaiya ya Salmanu ina kake da tabbacin nasara mutumin da bamu san irin fansar da zai ɗaukaba, naso ace kaine kai wannan nasarar da nafi kowa farin ciki".
Murmushi mai ciwo yayi a ranshi kana yace.
"Nan ɗin ma muna zaton farin ciki, duk da akwai tarin ƙalubale, mu dai in mun samu wani ya ci Ba'ana a gasar Shaɗi kin san yayi al'washin zai bar ƙasar nan gaba ɗaya ko?".
Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Uhum in bai sauya salon ba dai".
Cikin jin daɗi yace.
"Ba zai sauya saloba, dole zai bar ƙasar sai dai shiri zaije ya ƙara, kafin ya dawo kuma, an aura min ke, shi kuma jikan sarki.
Muyi musu mubaya'a, mun yarda su masarauta Joɗo fulani ne".
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Allah ya tabbatar da haka ya Salmanu yasa kuma a samo su Ya Gaini cikin Bonon don Ni dai nafi zaton can suka kaisu.
In anyi gasar an cishi, ya bar kasar, a ɗaura aurenmu a ranar".
Da sauri tasa tafin hannunta ta rufe idanunta alamun jin kunya,
Shi kuwa Salmanu murmushi yayi tare da cewa.
"Iye yan Matana an girma, me ma za'ayi mana?".
Cikin kunya tace.
"Ban saniba".
Murmushi yayi kana yace.
"Ni ai bazan manceba tunda yanzu burin mu na kusa da cika, ayi mana aure, nima haka ne tsarina ana watsewa gasar suna tafiya, za'a ɗaura mana aure.
Kinga gashi dama na samu aiki a babban birninmu.
Sai mu tafi can abinmu ko Wannan mugun saurayin naki ya dawo bazai samemu ba".
Murmushi tayi shi kuwa ido ya zuba mata yana jin tarin farin ciki.

*DAN ALLAH DA MANZONSA DA DARAJAR IYAYENKI DA SUKA HAIFEKI SUKA BAKI TARBIYYA, KADA KI FITARMIN DA LITTAFINA DAN AL'FARMA ANNABI DA AL'ƘUR'ANI, KU DENA FITAR MIN DA LITTAFI DAN ALLAH🙏🏻😭😭😭 Especially ku ƴan SPG na roƙeku da Allah🙏🏻😭😭

Da sauri ta gimtse dariyarta, cikin sanyi da tsoro ganinshi tamkar gilmawar walƙiya sai gashi a gabansu.
Wani irin azabebben tsorone ya rufe Salmanu amman sai ya dake, cikin ƙarfin hali da kalato jarumta ya kame jikinshi dake rawa.
Cikin ɗan rawan murya yace.
"Me haka, zuwa babu sallama?".
Wani mugun kallo ya watsa mishi tare da cewa.
"Kiyaye bakinka idan maza suna wuri."
Cikin dakiya Salmanu yace.
"Ina mazan!? Ai ni banga wani na miji a nanba sai mata maza. Ai namiji shi zai iya sa namiji ɗan uwanshi zubda hawaye ko tsuma da faɗuwa, a dai yanzu ai babu wani namiji a Rugar Bani da kewaye sama da Jarumin da bulalar SHAƊI bata sashi zubda hawaye ba Sheykh nake nufi".
Wani irin zabura Ba'ana yayi ya nufi kansa alamun zai shaƙeshi.
Da sauri ya tsaya jin Shatu ta saki ihu tare da cewa.
"Bana so ya Ba'ana in dai kana son farin ciki na, to kada ka dakeshi ko ka cutar dashi da komai".
Wani irin kallo ya mata mai cike da tuhuma da razana da kuma karaya,
Ita kuwa Shatu cikin rawan murya tace.
"Ya Salmanu ka tafi, bana so kaje ka bar koya min komai".
Cikin sauƙe ajiyan zuciya na tsoro.
Salmanu ya juya ya tafi.

Shi kuwa Ba'ana, zama yayi inda Salmanu ya tashi, cikin taraddadin ko dai Shatu bata sonshi ne, ya nuna mata gefenshi.

A hankali ta zauna, shiru tayi tana sauƙe shessheƙan kuka.
Cikin ƙuna da baƙin cikin rashin sa wancan ɗan birni mai fata kamar ta jariri kukanne ya sakar mishi fargaba,
cikin sanyi yace.
"Mata!".
Bata kalleshi ba kuma bata dena shessheƙan ba.
Kiranta ya kuma yi a karo na uku.
"Mata!".
Cikin disashewar muryar tace.
"Na'am".
Juyowa yayi ya fuskanceta da kyau a hankali yace.
"Mata bakya so nane!?".
A bazata tambayarshi tazo mata,
ta ina kuma ta yaya zatace mishi bata sonshi, bayan tasan abin da yayi mata shekarun baya, dama fansar shi ta soshine kuma ta aureshi, da wanne bakin zatace mishi bata sonshi.
wasu zafafan hawaye masu ɗumi ta zubda.
Haƙiƙa ya Ba'ana mugune amman a iya saninta a kanta ya zama mugun, tunda sai wanda ya nuna baya sonta dashine yakewa mugunta,
Babbar matsalarshi mushirkine kuma baya salla.
Cikin rawan murya da kuka tace.
"A a Ya Ba'ana Ni bance bana sonka ba".
Da sauri yace.
"Uhhmmm to meyasa bakya ganin laifin Salmanu akan duk abinda yake min, ko dai shi kikeso ne Mata!?".
Da sauri ta jujjuya mishi kai sabida sanin ko jinkirin bashi amsa tayi zai iya yiwa Salmanu illa.
Cikin rawan murya tace.
"Bana son ka cutar da shine sabida, shi ya janye batun soyayyarsa gareni. Ka kuma sani karatu yake koya min amatsayinshi na wanda ya samu karantarwa a wata jami'a,
Yana sona da al'khairi kai kuma kana ƙinshi, ko dai ka manta ka ce min zaka so duk wanda yake sona da al'khairi yake kuma taimaka min".
Jiki a mace ya gyaɗa mata kai,
sai kuma ya rumtse idanunshi da yakejin suna cikowa da hawaye yace.
"Lokuta da dama sai inga kamar bakya farin cikin ganina, a madadin farin ciki sai inga tsorona cikin ƙwayar idonki."
Juyowa tayi gareshi da kyau cikin kuka tace.
"Ba kai ke bani tsoroba, abinda kakeyi ne yake sani tsoronka, ya Ba'ana ka bar wannan asirce-asircen babu kyau shirka ne, wanda yake ɗaya daga cikin manyan zunuban da Ubangiji ya haramtawa mumini yin tsafi haramun ne".
Kanshi ya jingina da jikin gini yana kallonta tamkar yau ya fara ganinta,
A hankali ya fara mgna cikin muryar da bata taɓa jin rauninta a muryarsa ba yace.
"Mata ina sonki, wallahi Allah kenan rantsuwar musulmai, ina sonki, son da ni kaina bansan adadinshi ba,
Duk abinda nakeyi a kanki nefa, Shatu ki min uzuri, na roƙeki kiyi min ɗa'ar riƙe tukuicin abinda nai miki a baya,
Ki soni koda rabin yadda nake sonki ne.
Kiji tausayina Shatu ina jin tsoron kada ƙaddara ta rabamu,".
Kekkyawar fuskarshi ta zubawa ido, tana gani. Irin kyan da Allah yayi mishi sai dai sam babu kyan hali ya zama kyan ɗan maciji.
Cikin sanyi tace.
"Ya Ba'ana tsoro kuma?".
Kai ya gyaɗa mata cikin sanyi yace.
"Eh sabida muddin aka rabamu, zan zamewa fulani babban ƙalubale a rayuwarsa, kuma duk wanda yayi sanadin rabuwata da ke, wallahi zaiga toskun rayuwar duniya, zaiyi dana sani, zan zama mugun zahiri. Na san ke Kum bakya son hakan.
Yau kuma fargaba na, yafi na baya yawaita da wannan jikan sarki ya iya daurewa azabar bulalina baiyi ƙollaba."
Wani irin ajiyan zuciya taja tare da cewa.
"Babu komai ya Ba'ana Ni dai ina tayi mana addu'an ALLAH yayi mana zaɓi mafi al'khairi a rayuwata, ya kuma shige min gaba a dukkan motsina".
Ido ya zuba mata babu ko ƙebtawa, cikin sanyi yace.
"Nine mafa al'khairinki Mata".
Da sauri tace.
"Baka saniba".
A zafafe yace.
"Na sani mana".
Cikin tsoro tace.
"Kai masanin gaibu ne kenan?".
Miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Ehh kusan haka tunda nayi duba a kanki".
A hankali tace.
"Wa'iyazubillah. Duba ba gsky bane, zai iya maka ƙarya".
Hannu ya ɗaga mata da sauri kana ya nuna mata hanyar shiga gida.
A hankali ta tashi tsaye cikin sanyi tace.
"Allah ya baka haƙuri ya shiryeka".
Ta ƙarishe mgnar tana ƙoƙarin yin kuka.
Da sauri ya juyo cikin sanyi yace.
"Kada kiyi kukan mata, nayi haƙuri.
yanzu na fasa jiran Sai kin gama karatu ayi mana aure.
Duk randa wancan malamin ya dawo ya rama gasar Shaɗinsa. Za'a ɗaura auren mu a ranar, domin
Koda duk bulalin duniyar nan zai zabgeni dasu wlh bazaici nasara a kainaba domin idona ba idon da zai zubda hawaye a kanki bane bilali ɗaya nake tsoro kuma babu wanda yasan inda suke.
In kuwa aka samu wani akasin dama bazai samuba, to zan bar ƙasar nan zan koma ƙasar Cameroon can babban birnin Yahunde, inbi cikin Rugar wasu fulanin.
Sai dai ko bana nan duk wanda ya aureki ya auri ajalinsa."
Bata iya tanka mishiba, a haka ya juya ya tafi.

Kana ita kuma ta koma cikin gida.


A cikin masarautar Joɗa kuwa.

Sai da akayi sallan isha kafin.
Su Haroon suka dawo gida.
Suna tafe,
Abba da Lamiɗo da Galadima, da Dr Aliyu da kuma Sarkin Shaɗi.
Suna biye dasu a baya.

Kai tsaye wucewa sukayi har bedroom ɗin Jabeer har yanzu bacci yakeyi.
Sai dai tunda lokacin salla yayi yaketa jin baccin ba daɗi sai dai kuma Allah bai bashi ikon farkawa ba.
Dubashi sukayi tare da ƙara shafa mishi wasu magunguna kana suka fita suka tafi.

Hakama Gimbiya Aminatu tazo itama har ɗaki sai dai samunshi yana bacci yasa ta tafi.

Bayan fitanta ba daɗe Barrister Kamal da ɗan sa Sulaiman sukazo.
Suma har ciki suka shiga suka dubashi.
Kana suka tafi.


A ranan a daren gaba ɗaya mutanen masarautar kowa yaji lbrin abinda ya faru.

A falon su Jafar duk sukaci abinci.
Ganin dare ya tsalane yasa Juwairiyya jan hannun Jafar suka tafi.
Jalal, Jamil, Ya Hashim kuma sukayi musu saida safe kowa ya tafi side ɗin shi.

Jakadiyarsu kuwa itama ta nufi sashinta,
Ya zama dagashi sai Haroon.

Sha biyu da rabi dai-dai na dare.
Haroon zaune kan wata doguwar kujera irin ta sarakuna dake cikin ɗakin.
Waya yakeyi da Jannart,
yana konce ne dagashi sai boxes.
Waya sukeyi irin ta mosoyan da shaƙuwarsu tayi yawa,
Wani irin miƙa yayi wanda gaba ɗaya gabban jikinshi suka amsa.
Cikin tarin kasala da masifeffen shauƙi yace.
"Wash Allah na".
Cikin kashe murya da ta ingizo Bukatarsa tace.
"Ohhh sorry Ya Haroon meya faru gaya min me yasameka".
Cikin sakaliyar murya yace.
"Haroon yunwa yakeji".
Sam bata fahimci inda batunshi ya dosaba haka yasa cikin haɗa fuska tace,
"Ya Haroon ka dawo gida, shi Hamma Jabeer ba matace dashi ba, bare ya kula da cikinku, na kuma san in kuna Side ɗinsa ba wani zuwa wurin Aunty Juwairiyya zakuyiba, kuma itama fama takeyi da mijinta.
Ni gsky ka dawo Tsinako nasan Umaymah zata kular min da kai da kyau, ko kuma kazo Masarautarmu Leddi julɓe, nida Sitti mu kula da kai".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Masarauta Joɗo fa masarautace mai daraja, da karrama baƙo baki san asalin tarihin inda masarautar tasamu suna Joɗa bako.
Baby kada ki damu kular da muke samu ko sarki mai mata huɗu da kwarkawara biyar baya samu.
Tako wani sashi na gidan abinci hadimai ke kawowa Side ɗin Sheykh a ƙalla wani lokacin kusan abinci kala goma muke riska, kinsan fulani ba marowata bane.
Kawai matsalar wannan yunwar rashinki ne, a kusa yasa nake jina ina tashi sama kamar doki".
Cikin kunya da kauda zancen tace.
"Ya jikin Hamma Jabeer shugaban tuzuran ƙasar mu?".
A hankali ya juyo kanshi ya kalli bisa makeken gadon da Jabeer ke kai.
Da sauri ya katse kiran bayan yace mata.
"Ina zuwa".
Kan gadon ya nufa, jabeer ɗin yana ƙoƙarin tashi zaune.
Hannunshi daya miƙa zai taimaka mishi, ya buge cikin haɗe fuska yace.
"Yanzu ƙarfe nawa?".
Wayarshi dake hannunshi ya duba cikin zuba mishi ido yace.
"Ƙarfe ɗaya dai-dai".
Cikin tsuke fuskarsa tamkar zaiyi kuka yace.
"Shine ka barni ina bacci kamar kafurin da bashi da addini.
Anyi sallan bamgrib baka tasheniba, anyi Isha'i baka tasheniba, daga wannan masifeffen bacci mara daɗi mai cike da mafarkai marasa daɗin da nasan rashin yin salla a lokacin sane ya jazamin su.
Iya wunin yau duk so kuke kuyi min asarar lokuta masu muhimmanci da daraja, kun sani na makara la'asar da magriba hakama isha."
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye,
Tare daci gaba da cewa.
"Da fari ansa ni na tsaya gaban jama'a da baiyana surata,
Aka ɗora min da duka kana, akasa na makara sallan la'asar,
Yanzu kuma mangriba da isha'inma kun barni ina baccin asara na makara, sabida baka san darajar yin salla a cikin jam'i da kuma yin ta cikin lokacin ta ba ko?".
Cikin taɓe baki Haroon yace.
"Kasan ai ni ba musulmi bane, ban san komaiba".
Harara ya dannawa Haroon tare da cewa.
"Kai ka gayawa kanka, Ni bana kafurta mutum, abinda na sani dai kai tsarin yahudu da nasarane,
To bari kaji, Ni bani da laifin komai sabida bacci nakeyi, mai bacci kuma al'ƙalami ya sauƙa kansa har sai ya farka.
Kai dake ganina ina bacci lokacin salla yayi idonka biyu baka tasheniba haƙƙin a kanka ya rataya."
Ya ƙarishe mgnar yana shiga bathroom tare da cewa.
"Ka cire idonka a kaina banza mai kallo kamar mayun wancan garin mugayen".
Murmushi Haroon yayi tare da komawa ya zauna bisa kujerar.

Shi kuwa Sheykh Jabeer wonka ya kumayi da ruwan ɗumi,
kana ya kimtsa cikin irin suturun da yake ta'ammali dasu, in yana gida.
kana ya ɗaura wata farar jallabiya kai.
Sannan ya fito bayan ya shafa mai ya fesa turare.

Yana fita ya fara ramuwar sallan daya wuceshi yana bacci.

Haroon kuwa falo ya fita abincin da yasan zai iya ci ya kawo mishin

A ƙalla awa ɗaya yayi kafin ya tashi kan sallayan
Gaban gadonshin ya dawo ya zauna bisa tattausan carpet ɗin da ke shimfiɗe a wurin mai kalar Sky blue and white.
Sosai yaji daɗin jikinshi, sai dai har yanzu yana jin raɗaɗin bulalin.
Tea kawai ya iya sha.
Kana a hankali yace wa Haroon.
"Canza min beshit ɗin nan da blanket ɗin."
Hararanshi Haroon yayi tare da cewa.
"Zan koma, yaseen na gaji da mulkinka da sarautar da kake ji dashi. Ji yadda ka medani tamkar wani bawanka ko hadimin gidanku, kuma duk abinda zanyi maka sai ka cini gyara, mutum ba'a iya mishi sai masifa kake min kamar dai nine nace a zaneka".
Ya ƙarishe mgnar yana miƙewa tsaye tare da gimtse dariyarshi, sabida ganin kallon da Jabeer ke mishi.
A haka dai ya sauya komai na gadon kafin suka, hau suka konta.
Tsaki Jabeer yaja tare da cewa.
"Ni dama ka tafi wancan ɗakin sabida zancen gsky kasan ni bana son takura.
Sabida zaka hanani sakewa yadda nakeso".
Cikin gajiya Haroon yace.
"Allah babu inda zan fita inje".
Da haka dai Haroon yayi bacci.
Shi kuwa Sheykh Jabeer karatu yayi tayi har biyu da rabi tayi kana, ya buɗe tafin hannunshi yayi addu'o'in bacci.
Falaƙi 3 Nasi 3 ƙulhuwa 3 Ayatulkursi'u 1 kana amarrasulu 1 tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikinshi.
Kana ya kuma yi. Haka ya tofa a tafin hannunshi ya shafa a jikin Haroon Wanda tuni ya ɓingire,
Shi kuwa Jabeer wannan al'adar rayuwarsa ce daya saba, kan Jalal da Jamil sabida suma haka suke bingirewa, shikeyi tofi ya shafa musu.

Washe gari Lamiɗo baiyi zaton Jabeer zai samu fitowa masallaci ba,
Shiyasa limamin dake jansu salla in baya nan ya fito ya jasu salla,
yayinda Jabeer ke cikin sahun forko.

Wannan yasa mutane sukayi zaton ciwon ne yayi tsamari bai samu ya fitoba.
Ana idar da salla kuma ya fito yayi cikin gida sabida.
Fushi yakeyi da wannan tsohon ya sani in ya tsaya kuma zai dameshi da wata falsafarshi da zaici karo da addini.


Ƙarfe takwas dai-dai. Barrister Kamal da Ya Jafar, da kuma Baba Basiru ne zaune dashi a falon shi.

Suna zaune anan Jalal ya shigo cikin yanayin damuwa yace.
"Hamma Jabeer, Umma na falo tazo dubaka da jiki."
Cikin yamutsa fuska yace.
"Wacece hakan?".
Cikin fusata Baba Basiru yace.
"Ashe uwarka ma bazaka santa ba, ina dai baka san wacece Umma ba".
Wani irin kallon ido cikin ido Sheykh yayiwa Baba Basiru,
sai kuma ya ɗora ƙafarshi ɗaya kan ɗaya, cikin ƙasaita ya kalli Jalal tare da cewa.
"Mene Umman!?". Ya sani sarari Gimbiya Saudatu ake cewa Ummu .
Gyara tsayuwa Jalal yayi tare da gyara zaman belt ɗin ƙugunshi yace.
"Matar tsohon Galadima marigayi, Baba Muhammad ce Ummar Gimbiya Saudatu."
Da sauri Baba Basiru yayiwa Jalal daƙuwa tare da cewa.
"Kan uwarka hegen yaro ɗan shila".
Shi kuwa Jabeer ƙafarshi ya fara kaɗawa.
Barrister Kamal kuwa ido ya zubawa Fuskarta Jabeer da Jalal. Cikin sanyi da tausasan laffuza yace.
"Jabeer tashi muje ka gaisa da ita tunda ta taso tazo har nan dubaka da jiki".
Kanshi ya gyaɗawa Barrister Kamal ɗin wanda suke cewa Baba Kamal wanda yake mahaifin Sulaiman, sa'an Jabeer.
Da hannu yayiwa Jalal alamun yaje yace, yana zuwa.
Shi kam Baba Basiru bayan Jalal yabi.
A babban falon suka zauna shida Gimbiya Saudatu da Laminu da kuma Baba Nasiru.

Jalal, Jamil, Haroon, Jafar, kuwa duk suna can Dinning area kan dinning table sunayin breakfast.

A jere suka fito falon shida Barrister Kamal.

Suna isowa tsakiyar falon.
Cikin wani irin taku mai cike da ƙasaita da rashin tsoro.
Ya kalli Gimbiya Saudatu dake zaune bisa kujerar zamanshi.
Yatsunshi biyu ya haɗa ya kaɗa mata tare da mata alamun tashi min kan kujera.
Cikin wani irin kallo mai nuna tsantsar fushi da tsana da zazzafan ƙiyayya ta fara mgna cikin ɗaga sauti tace.
"Hegen yaro mai idanun mujiya, Ni kakeyiwa wannan iskancin dan kan uwar..!".
Kasa ƙarisa zagin da tayi nufin yi tayi jin yana cewa.
"Kan uwarki ko? Ki ƙara sa mana kikaga ikon wanda ya hana mata gemu ya baiwa maza!
Maza tashi min kan kujerar zama tunda ba wancan jiɓeɓɓen tsohon akun bane seyota".

Wani irin zabura Baba Nasiru yayi tare da ɗaga hannu zai kifeshi da mari, kamar a mafarki yaji an riƙe mishi hannunshi da sauri ya juyo.
Ido ya zaro cike da mamakin ganin wanda ya riƙe mishi hannunshi cikin tafasar zuciya da ƙuna yace.
"J....."






By
*GARKUWAR FULANI*
Cikin wani zare ido na masifa yace.
"Jalal ni ka riƙe wa hannu".
Shima idon ya zare tare da cewa.
"Ba iya rikeshi kaɗai zanyi ba, in dai zai taɓa lfyar ɗan uwana a gaban idona, datseshi zanyi gaba ɗaya in wurgar". Ya ƙarishe mgnar da ƙarfi tare da yarfa hannunshi.
Wani irin asirtaccen murmushi Barrister Kamal, yayi tare da kallon ɗan shi Sulaiman hannunshi ya dunƙule ya jinjina wa Sulaiman ɗin.
Kana suka koma suka zauna bisa kujera.
Shi kuwa Jabeer hannun ya nunawa Gimbiya Saudatu alamun ta tashi.
Mirtsitsi tayi tare da gyara zamanta.
Wani irin firgitacen tsawan da Jalal ya danna matane yasa, ta miƙe tsaye ba tare datasan ta miƙa ɗin ba.

Cikin ƙasaita Jabeer ya baza tattausar al'kyabbar jikinshi,
Kana ya matso ya zauna bisa kujerar ƙafarshi ɗaya ya ɗora bisa ɗaya.
Gyara hiramin kanshi yayi tare dayin gyaran murya kana ya kalli ƙannen mahaifin nashi kauda kanshi yayi ganin yadda suke wani irin cika da batse sun cika sunyi tamtsan da fushi.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu zama tayi a kujerar dake kallon tashi
kujerar.
Itama ɗaura ƙafa ɗaya tayi kan ɗaya.
Cikin iya tijara ta watso sabbin jaridu gabanshi.
Jaridar bankaɗa da kuma kamfanin jaridar hantsi wato leƙa gidan kuwa.
Murmushin muguntan tayi tare da cewa.
"Ga sakamakon sa insa da kayi dani jiya, na yau kuma shima yana nan tafe.
Nayi maka murna darajar labarin ya kai matsayin da shine a shafin forko na jaridun".
Da sauri Jalal ya sunkuyo yasa hannunshi ya ɗauki jaridar banƙaɗa.
Jiki na tsuma ya ɗago ya kalli Gimbiya Saudatu cikin tashin hankali yace.
"Wannan ƙarya ne, da babu jahilin da zai yarda dashi, wlh bazaku taɓa cin nasara ba."
Hankali a tashe ya miƙawa Haroon jaridar tare da cewa.
"Ya Haroon gani zancen banzan da aka rubuta kan hotunan Hamma."
Da sauri Haroon dake sauƙowa kan stpes ɗin sauƙowa falon daga dinning area,
ya ƙaraso. Hannuyasa ya amshi jaridar.
Wani irin azabebben zufane ya fara keto mishin ganin abinda aka rubuta a jikin jaridar.

Jin jikinshi na rawane ya sashi zama kusa da Sulaiman.

Ummi kuwa dake tsaye a dinning area tana haɗawa.
Jafar abin da zaici, gaba ɗaya ido ta zubo musu cikin taraddadin me aka rubuta.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wata iriyar shaƙiyiyar dariya tayi tare da cewa.
"Ya haka dai ƴan kanzagi, ku bawa shi uban gidan naku, jaridar yage me aka rubuta, daga nan sai inga bakinshi da baya mutuwa da bada amsa ko zai iya cewa wani abu."
Baba Nasiru da Baba Basiru, ma fuska cike da farin ciki suka zauna.
Laminu kuwa miƙewa tsaye yayi tsakiyar faffaɗan falon cikin ɗaga sauti yace.
"To tunda bazaka iya bashi ba, bani ni in karanta mishi."
Yana ƙarishe mgnar yasa hannunshi ya amshi jaridar.
Cikin ɗaga sauti ya fara karanta rubutun dake rubuce a ƙasan hoton da gefe da gefenshi.

"Abun kunya, ya baiyana jikan sarki Nuruddeen Bubayero ɗaga Habibullah,
Yayiwa ɗiyar Fulani fyaɗen da yasa.
Hanun Sarki Lamiɗo ya kama hannun Sheykh Jabeer Habeebullah Nuruddeen Bubayero wanda yake limamin masalacin ƙofar sarki ya miƙa shi ga hukumar addini musulunci.
Gashi anayi mishi bulalin haddi kamar dai yadda Musulunci ya wajabta.

Wani irin murmushi Jabeer yayi, hannunshi yasa ya shafa tattausan gemunshi.
Cikin rashin karaya ya kalli Haroon cikin nitsuwa yace.
"Ɗan wannan abun ne kuke zaton zai kashe wannan bakin nawa da yake rayuwa da ambaton Allah!?
Shin ko kun mance tsawon shekaru da dama ana fataucin rufe bakin Ya Jafar, shima har yau baku samu nasarar hanashi ambaton Allah ba,
Duk sharrinku ya zame mushi al'khairi, tunda baya wani motsi ba tare daya kira sunan Allah ba, ikirarin ku na ya zauce, ya tabbata kune zautattun".
Sai kuma ya ɗan kalli Gimbiya Saudatu, murmusawa yayi tare da cewa.
"Baki nafa bazai mutuba sai in nufashina ya bar jikina, batun shiga ɗakin sirri kuma, nifa wannan abin da kuketa haƙilo a kai ba wani baƙon abun bane a wurina.
sarauta a cikin jin jikina yake."
Sai ya kuma juyo ya kalli Haroon da jikinsa yayi la'asar da lamarin su, miƙewa tsaye yayi tare da cewa.
"Haroon wai ɗan wannan makircin nasune ya kashema jiki.
To kontar da hankalinka. Ni nan Muhammad Jabeer ƙi gudune sa gudu.
Tun kan suyi tunanin yin abu a kaina na nazarci abun."
Juyowa yayi ya kalli Baba Nasiru cikin tsareshi da ido yace.
"Kaje duk inda ake saida jarudu ka bada farashin one million akan ko wanne jarida kaga in za'a fito maka da wannan jaridar, in bada wannan ƙwaya ɗayar kaga dai itama kuma gata a gabana."
Cikin tarin mamaki suka zuba mishi ido.
Shi kuwa gaban Laminu ya isa cikin isa ya miƙa mishi hannunshi tare da cewa.
"Bani shi nan".
Cikin tsananin tsoro da firgici ƙarara. Jiki na rawa Laminu ya miƙa mishi. Sabida kwarjin Jabeer ya mishi nauyi a idonshi ya kuma san artabu dashi ba daɗi.

Ita kuwa Gimbiya Saudatu wani murmushi tayi mai cike da taraddadi da al'hini da nazarin yadda zataga bayan wannan yaron mai bakin tsiya.
Jaridar gabanta ta miƙa mishi.
Kanshi ya girgiza tare da kaɗa mata yatsarshi manuniya cikin rashin tsoro da ƙasaita yace.
"Ba kifa kai matsayin da zaki nuna min wani abin da idanuna basu rigaya sun ganiba ko basu san dashiba domin ke a makance kike rayuwarki, Ni kuwa nan da kike gani idona buɗe suke ras.
Ita wannan itace tayi bayanin abinda ya faru na gsky a Rugar itace tai bayanin cewa bulalin shaɗi akayi min bana Haddiba to sai me kuma!?".
Shiru sukayi gaba ɗayansu.
Kowa da abinda yake nazarta a ranshi sai bugawar da zuciyoyinsu keyi.
Buɗa al'kyabbar jikinshi yayi tare da kuma haɗe ta cikin fillanci yace.
"In kun gama ihun ku ficemin daga Side ɗina Dan ba haɗamu akayi ba. Kuma ku sani (MOH ALLAH WUJI FURƊATA)."
Yana faɗin haka ya juya ya nufi falonshi.

Ita kam Gimbiya Saudatu ta cika tayi maƙil.
Baba Nasiru da Baba Basiru kuwa,
A kufule suma suka fita.
Haroon kuwa ido ya zuba musu.
Barrister Kamal kuwa murmushi yayi mai tarin ma'anoni kana shima ya fita Sulaiman na biye dashi.

A hanyarsu ta komawa side ɗinsu ne, Gimbiya Saudatu ta kalli Laminu cikin takaici tace
"Banza kawai me tsoron zuci me dan ya matso kusa dakaii ka wani firgita ka razana har ɓari jikinka keyi ka miƙa mishi jaridar, da zamu iya kaita a tallata".
Wani irin wawan ajiyan zuciya Laminu yayi tare da cewa.
"Uhummmm Umma kenan wato, fa duk wannan kumfar bakin da kikeyi abinda yasa kike yinta da jin daɗin yinta, dan wancan Jabeer ɗin bai taɓa kifa miki bari bane shiyasa.
Wallahi Allah da ya taɓa marinki da waɗannan hannayenshi da kike ganin taushinsu kamar na jarirai shakka babu, wlh suma zakiyi sai an yayyafa miki ruwa".
Cikin kufula Baba Basiru yace.
"Kai tafi daga nan banza mai zuciyar mata, ji abinda kake cewa kan mari ɗaya tak daya taɓa yi maka".
Wani irin kallo Laminu yayi musu kab lokacin da suka shiga falon Gimbiya Saudatu.
Cikin rumtse idonshi sabida tuno marin da Jabeer ya kifa mishi randa yayi gangancin zai zageshi.
Da sauri ya buɗe idanunshi cikin kara yace.
"Yesss sabida baku ya shararawa mari ɗayanba shiyasa.
Kuna sanefa mari ɗayan da yayi min. A take kunnena ya rinƙa zubda jinin da Ni dai har yau bansan ta inda ya ɓulɓuloba, wlh Allah lokacin daya mareni kusan suma nayi, har yau in na tuno marin sai inji kunnena yayi gummmmm".
Cikin zafi Gimbiya Saudatu ta yunƙuro zata surfawa ɗan nata masifa, sai ta kuma komawa ta zauna jin Baba Nasiru na cewa.
"Uhummm Dafa gskyar Laminu, in dai Jabeer ya ɗauki hannun mahaifinshi to tabbas, suna da zafin hannu mai ban tsoro,
In dai ya gado hannun Ya Habibullah to fa duk abinda suka mara wlh in dai dabbace sai

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment