Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara kawoshi".
Ummi ce ta kalleshi tare da cewa.
"Naga Shatu tafi sonshi ne yasa nace akawoshi".
Kai ya gyaɗa tare da cewa.
"To nima bari in taɓa shi".
Nan ya fita falon.

Su kuwa suka ƙarisa aikin.
Suna ƙoƙarin fitowa ne.
Jamil ya leƙo tare da cewa.
"To yau kuma meye za'ayi mana na sahur ne".
Jalal dake bayanshi ne yace.
"Yo azumi ɗaya ai ko tazarce zamuyi".
Hararan Jalal yayi tare da cewa.
"Hege daka ci kaji kayi tak ba, mutun kamar kura".
Murmushi Jalal yayi tare da cewa.
"Yes naci in kuma ƙara".
Hararanshi Jamil yayi tare da cewa.
"Mutun sai son nama kamar ba bafulatani ba sai kace babarbare".
Da sauri
Jalal yace.
"Yo dama aini Arbabarbare ne".
Dariya Ummi tayi,
Ita kuwa Shatu Jalal ta kalla tare da cewa.
"Me zan dafa mana to?".
Tsaki ya ɗan ja tare da cewa.
"Kiyi mana Coucous da miyar hanta kawai".
To tace kana ta juya ta fara aiyin.
Cikin sa'a ɗaya ta gama ta fito.

A falo ta samesu suna.
Waya da Sheykh yana ce musu kadafa suyi sakaci suyi sallan, dan babu lbrin ganin wata.

Hakan dai suka haƙura.
Bayan yaga waya da sune.
Umaymah ta shigo ta sameshi zaune yanacin inabi.
Gefenshi ta zauna da wata jakar.
Miƙa mishi tayi tare da cewa.
"Kace ranar salla da safe in an sauƙo idi dai zaku tafi ko?".
Kanshi ya gyaɗa tare da cewa.
"Haka dai Wannan tsohon Galadiman ya buwayeni da zancen komawar".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Abbanka ma yace min ranar sallan zaku tafi".
Kai ya gyaɗa.
Ita kuwa gyara zama tayi tare da cewa.
"Tsarabar me ka sayawa Shatu da ƴar ɗakinta Hibba".
Da sauri ya kalleta tare da cewa.
"Umaymah tsaraba kuma.
"Yo tsarabar me zanyi sai kace wani sabon zuwa, Ni ibada nazo yi ba tsaraba ba".
Jakar ta nuna mishi tare da cewa.
"To ni kam ga tsaraba ka kai musu, wannan na Shatune Hibba gobe zan dawo da nata.
Kai kuma in kaso ka koma hannu rabbana".
Kanshi ya sunkuyar kamar baijiba.
Sai kuma tace.
"Jazrah tace in gaidaka, wai tunda kazo bata ganka ba".
Cikin sanyi yace.
"Yoh dama ya zanyi in bari ta ganni yarinya sai kallon masifa".
Miƙewa Umaymah tayi ta fita.
Tana fita Haroon da Ya Hashim suka shigo. Nan suka ɗanyi hira kafin suka tashi suka tafi masallacin dan shabiyu ta kusa a fara tuhajjudin.

Nan suka tafi.
Washe gari aka tashi da azumi na talatin.
Allah cikin ikonshi aka kaishi lfy.
Watan Shawwal ya baiyana Ramadan ya tafi kuma sai mai nisan kwana.

Shatu kuwa a wunin ranar Yar aikin Aunty Juwairiyya Sato, ta zana mata jan lalle mai ɗan karen kyau.

Koda ta dawo kuma jarakuna madarar shanu data gayawa Gimbiya Aminatu tanaso
Aka kawo mata ta tafasashi kana tasashi a manyan kware da ƙananan kwore da kyawawan robobi tasa tsami kaɗan a ko wanne kwarya da roba.
Ta rufesh ta jerasu a Fridge a ƙalla sunfi kore goma madaidaitan ƙananan sun kai kore takwas sai robobin su kuma sun kai goma suma.

Bayan sallan magriba ansha ruwa anyi nak.
Hibba sai tsalle da farin ciki da kiraye-kirayen ƙawaye da yan uwa da abokai sai tsiya Jamil ke mata.

Bayan sun gama shirya komai na aikin da zasuyi gobene.
Suna zaune a falo Ummi ta kalli Jamil tare da cewa.
"Jamil wai sai yaushe zaka share Side ɗin Sheykh ne, munyi waya da Umaymah ɗazu tace min gobe fa zasu dawo.
Anayi sallan idi a can zasu taso".
Gyara zamanshi yayi tare da cewa.
"To naga mutun ga matarsa ace Ni in mishi shara".
Ko inda suke Shatu bata kalla ba.
Ummi kuwa jingina tayi da jikin kujera tace.
"Ai bazata san ƙaidar yadda yakeson a gyara mishi ɗakinshi ba.
Dole sai ka nuna mata."
Cikin gamsuwa da hakan yace.
"To ba matsala sai gobe da sasafe mu hau kan aikin abinda ɗakin ba wani ƙura da tarukucene da shiba".
Eh hakane Ummi tace tare da kallon Shatu tace.
"Gobe in Allah ya kaimu Shatu ku gyara mishi ɗakin nashi".
"To Allah ya kaimu. tace ba tare da ta kalli inda sukeba.

A can ƙasa mai tsarki kuwa.
Ana idar da sallan isha'i da yawa suka fara ɗawafi.
A cikinsu kuwa harda Sheykh Jabeer da mai sunanshi kana da Haroon
A nitse bisa tsari suke ɗawafin sunje ƙafa biyu ana uku sun isa dai-dai. Maƙama Ibrahim.
Sheykh Jabeer ya juyo kanshi ya kalli gefen damanshi da sauri cikin tarin mamaki al'ajabin Fuskar mutumin da ya ga ya wulgawa a idonshi...!




Littafin GARKUWA na kuɗine idan kina buƙatar saya ga number 09097853276 katin mtn na ɗari uku. Normal group in kuma special Group kikeso 1k zakiyi min TRANSFER ta ac ɗina 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa.

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*GARKUWA*
NA

*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🐄🕊️🌈🦚🐍🤴🏻💘

ASSALAMU ALAIKUM. MASOYA NA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA, WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA, INA MUKU FATA ALKYAIRI da fatan muna lfy, kana kuma ina mai bawa dubban mutanen da sukayi min mgn ta kafafan sadarwa kamarsu, WHATSAPP, FACEBOOK, INSTAGRAM, WATTPAD, BAKANƊAMIYA, WASUMA A TIKTOK daga jiya da yamma zuwa safiyar yau haƙurin rashin basu amsar tambaya ɗaya dai da aketa memeta min. GARKUWA WAI KIN SAIDAWA ƳAN HAUSA FILM LBRIN GARKUWA? WAI DA GASKENE BAZAKI ƘARASA MANA LITTAFINBA? TO DUK GA AMSARKU NAN. Alhamdulillah, ngd matuƙa da kulawarku. Kana ina mai baku tabbacin EHHH TABBAS NA SAIDA LITTAFIN GARKUWA GA ƳAN HAUSA FILM KAMAR DAI YADDA KUKAGA YAKETA YAWO, TABBAS NA SAIDASHI WA ƊAYA DAGA CIKIN MANYAN INDOSTIRI. DA IZININ UBANGIJI ZASU JUYASHI ZUWA FILM MAI ZAMAN KANSHI, IN LOKACIN YAYI KUMA ZAN SANAR MUKU. DA FARI NASO IN SIRRANTA ZANCEN NE, SABIDA SEDA MUSU DA NAYI BAWAI YANA NUFIN BAZAN ƘARASA LBRIN GARKUWA BANE, ZAN ƘARASA MUKUSHI HAR ƘARSHE DA IZININ UBANGIJI. TO SAI DAI NAYI MATUƘAR MAMAKIN YADDA AKAYI MGNAR TA FITO FILI TA BAIYANA HAR TA BAZU, domin naso barinta sirrin kai da kaina sabida gudun kada hankalin makaranta na ya tashi. To amman ba komi ku kwantar da hankalinku masoya na zan ƙarasa GARKUWA lfy lau. Kana suma ƴan film zasuyi abunsu lfy lau. Duk wacce ta/ya sayi littafin GARKUWA sun san uzurina da yasa kwana biyu bana Update, so ku kwantar da hankali ku, in sha Allah ni AYSHA ɗiyar ALIYU GARKUWA, Jikar Malam Muhammad Babayo mai Murare. Zan ƙarasa mukushi lafiya in Allah ya aramin rai da lfyar.
KUYI HAƘURI WAƊANDA SUKAYI MIN MGN TA PC BABU TABBACIN ZAN BIKU ƊAYA BAYAN ƊAYA IN BAKU AMSA.

FATAN AL'KHAIRI MASOYANA MAKARANTA LITTAFIN GARKUWA WAƊANDA SUKA BIYA DA WAƊANDA KE KARANTA NA SATA🤝🏻😘🥰😘🥰😘. Dan naga masu karanta na satan ƙarfin halinsu yawa gareshi, har ƴar guntuwar nasiha sukemin wai kada in zalinci mutane na fara musu ban ƙarasa ba🤣🤣😂. Ɗan Adam kayan Allah ana ɗauke damu muna ɗauke da halayenmu🤗🤗🤗🤗.Cikin sassarfa bisa tsarin addinin yaci gaba da ɗawafin.
Yana mai bin bayan tawagar mutanen da yaga fuskar wannan mutumin a cikinsu.
Idonshi yaketa karkasawa amman ina ya kasa sake ganinshi.
Zuciyarshi nike da mamaki.
Haka yaci gaba da ɗawafin.
Saida sukayi. Kana suka fito.
A hanyarsu ta komawa gidane ya haɗu dasu Jannart da Jazrah da Umaymah da Sitti da kuma Aunty Hafsat ƙanwar Umaymah dake ƙasar Masco.
nan Aunty Hafsat tayi ta sayan kayan tsaraba tana bawa Sheykh wai a kaiwa surkarta.
Dan dole ya amsa sai kuma Aunty Rahma ƴar autar Sitti itama a gaban Aunty Hafsat ta girma.
Kuma sa'ar Sheykh Jabeer ce shiyasa akwai yar tsama a tsakaninsu.
Cikin hausarsu data fara basu wuya tace.
"Ba dai kayi auren sirri ba, in sha Allah zanzo zamuzo auren Haroon zamuga amaryar, inga surkar tawa ya take"

Taɓe baki yayi tare da cewa.
"Ke tafi daga nan da Allah ki bar manya suyi mgna ba irinki ba".
Murmushi Umaymah da Aunty Hafsat sukayi dan sun san tsamarsu.
Kuma suna masifar shiri.
Ammi suke kiranta ita Aunty Rahman.

Jazrah kuwa hakanan take jin daɗi in ta ganshi.
Shiyasa taketa murmushi.
Haroon kuwa girarshi ya ɗagawa Jannart tare da cewa.
"Wai auren ya kusa ko?".
Cikin jin kunyar Umaymah tace.
"Ban saniba."
Haka dai sukaci gaba da tafiya.

Washe gari da safiya.
Duk kan al'amur musulmai na duniya suna farin ciki da ranar salla.
Manya da yara tsoffi maza da mata duk anata shirin zuwa idi. A dukkan ƙasashen duniya a ko wani saƙon da suke da musulmai.

Hakace ta kasance a ƙasashen Afrika ma.
Wanda ciki ƙasar Nigeria yake.
Tun daga idar da sallan asuba.
Saratu da Larai sukazo.
Nan suka samu Ummi da Shatu suna kitchen.
Its Ummi fura take kirɓawa mai ɗan karen laushi da ƙamshi yaji sugar.
Ita kuwa Shatu dakkeren Couscous tayi, dambu inji hausawa.
Bayan sun gamane suka killace shi gefe.

Kana ita Shatu. Ta haɗa kajin nan tayi Pepper Checken mai ɗan karen kyau yaji jajjagen taruhu da al'basa mai yawa ga kayan ɗan-ɗano dana ƙamshi sunji komai yayi maɗau.
Su Sara kuwa robobi ta miƙo musu, suka rinƙa mulmula gumbar nan manya manyan mulmulellen masu kyau sai sheƙi da ƙamshi gumbar keyi, dakkeren kuma a robobi Ummi ta rinƙa zubasu.
Hibba ce data shigo tare da kuloli a hannunta tace.
"Wow Aunty Shatu lallai yau masarautar Joɗa zata amsa sunanta masarautar Fulɓe zata kuma gane an auro mata cikekkiyar ba fulata, gsky tsarin yayi kyau".
Cikin jin daɗi Ummi tace.
"Gsky nima naji daɗin wannan abu.
Dama ace ko wanne yare ranar salla tayi abincin da yarenta keyi ta rabawa maƙota.
Hakan zaisa asan cimar juna, kuma yasa aci abincin salla da marmari, amman kayan haushi duk sai a tafi kan shinkafa taliya masa, da dai ire-iresu.
Su kuma akeci kullum".
Murmushi Shatu tayi tare da cewa.
"Ha Ummi ai yanzuma sai nayiwa su Jalal koda dafadukan taliyace, nasan zasuce wannan ai sai mu".
Da sauri Hibba tace.
"Tab wlh Aunty Shatu karkiyi komai, kinga yanzuma an kawo abincin gidan Barrister Kamal.
Ga kuma na gidan Aunty Juwairiyya.
Sannan kuma Gimbiya Aminatu ma zata aiko".
Cikin sauri tace.
"Allah ko Ummi mu huta kawai kenan?".
Da sauri tace sosaima.
Dan duk yawanci sai an kawo abinci nan wai tunda ke baƙuwace, wannan karamawar masarautar Joɗa akan bago.
Kuma koda kin dade ana aikawa juna abincin salla part 2 part".
Ajiyan zuciya ta sauƙe tare da cewa.
"Shike nan mu haɗa wannan a kai ko wanne sashin".
Ta ƙarishe mgnar tana rufe ƙatuwar Foodflaks ɗin da ta juye Pepper Checken ɗin.
Bayan ta ɗebawa sashin Ya Jafar da kuma Lamiɗo da Hajia Mama.

Ƙananan robobin da a ƙalla suma nonon dake cikinsu zai kai kwanon sha ɗaya da rabi ta fara firfitarwa.
Kana ta fito da madaidatan ƙoren da zasuci kwanon sha biyu da kaɗan sai manyan da sukaci kwanon sha uku da rabi-rabi.
A hankali ta jerasu kan table ɗin dake tsakiyar kitchen ɗin.
A hankali ta buɗe ƙwaryar forko dake gabanta.
Wani irin murmushi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah kunɗirmo ya konta yayi bacci yayi kyau".
Leƙowa Ummi tayi tare da buɗe na kusa da ita.
Nonon yana konce yayi lib ya daskare yayi fari ƙal-ƙal sai alamun maiƙon man nonon da yayi ɗan yellow-yellow kaɗan.
A hankali suka fara bubbuɗe fefeyayen tsakan zaren taburma da aka rufe ƙoren dashi.
Gaba ɗaya duk sun konta sunyi kyai
Yan madaidai robibin da akasa take ɗauka na fura ɗaya na dakkere ɗaya sai na sugar ɗaya kana da ludayin duma. Sai ta jerasu kan fefeyayen da robobin.
Ganin haka yasa Saratu da Laraima suka matso suna taya.
Har saida ta jerasu kab. Gwanin sha'awa.
Manyan ƙore biyu ta maida cikin Fridge.
Kana ta irga sauran tsakanin manya da ƙananan
Ƙoren da robobin su
Talatin da tara
Juyowa tayi ta kalli Ummi tare da cewa.
"To Ummi gashi mun gama ki gaya musu duk inda zasu kai.
Zasu isar ko".
Cikin jin daɗi Ummi tace sosaima kuwa harma da sashin bayi zai isa sabida part-part talatin garemu a cikin masarautar Joɗa.
Sai sashin bayi part takwas.
Cikin jin gamsuwa da tsarin Shatu tace.
"Yanzu a kai ƙore biyu sashin Lamiɗo kana duk manyan iyayen Sheykh akai musu kwarya ɗaɗɗaya, sai sashin Ya Jafar kinga manyan ƙoren sun ƙare sai abin na tsakiyan a kai sauran sashin ƴaƴansu robobin kuma akai sashin bayi".

Haka kuwa akayi su Sara suka fara rabawa.
Ita kuwa Ummi ita da kanta da Hibba suka kai na sashin Gimbiya Aminatu.
Kana suka dawo da kuloli har uku na abincin sallan da Gimbiya Aminatu ta basu.
Kana ɗaya daga cikin tace na Sheykh ne a ajiye mishi.
Koda suka dawo samu sukayi su Saratu sun gama rabawa kab.
Kamar yadda Ummi ta tsara.
Har sun tattare ko ina sun gyara sun share sun goge sun tafi.
Zuwa lokacin kuwa gaba ɗaya kan dinning table ɗinsu cike yake da Foodflaks iri da kala abinci kala-kala.
Wani irin kallo Shatu tayiwa kulolin kana tayi murmushin da ita kaɗai tasan ma'anarsa ta juya ta nufi tsakiyar falon.

A gaggauce sukayi wonka kowa yayi shirin idi.
Ƙarfe tara saura kwata duk suka fito falo.
Tuni lokacin kuma liman har ya fara huɗuba.
Su Jalal, Jamil Ya Jafar suna tsaye cikin shiga ta al'farma.
Karon forko dataga manyan kaya a jikin Jalal.
Sai kamanninshi da Hamma Jabeer ɗin nasu ya fito sak-sak kamar an tsaga kara hatta rashin yawan dariyarsu iri ɗaya ne.
Sai dai shi Sheykh ko yaushe zakaga lips ɗinshi na motsawa yana tasbihi saɓanin Jalal da zaka ganshi baki a tsuke.

Hibba ce ta fito cikin tarin farin ciki da son Jalal yayi murmushi tare da cewa.
"Masha Allah ya Jalal kayi kyau kafisu duka".
Ya Jafar dake karatu kamar ko yaushene ya kalli Shatu da Hibba da sukayi shigar atampa iri ɗaya da manyan hijabai har ƙasa ga sallaya da carbi a hannunsu sunyi matuƙar kyau, murmushi yayi musu kana ya juya yayi gaba.
Jamil ne yace.
"Aunty Shatu sai mun dawo, in munci abinci sai mu sharewa.
Oga, Dr, Garkuwa, Malam, akarmakallahu, Sheykh, mijin Sayyada, ɗin ɗakinshi".
Dariya sukayi dukansu yadda ya jero masa sunayen nashi.
Ummi dake cikin shiga ta al'farma ta miƙa tare da cewa mu tafi.

Suna fita suka rufe ƙofar.

Suka tafi masallacin. Masarautar Joɗa ɗan yin sallan idi.
Suna fita su mata sukayi gefen mata su kuwa maza sukayi gefen maza.

Bayan an idar da sallane kuma sai suka zagaya suka shigo ta asalin ƙofar sukayi yadda sunna ta koyar.

Suna dawowa kuwa a falo suka zube nan sukaci suka sha sukayi
haniƙan.


A dai-dai lokacin kuma su Sheykh dama sauran al'ummar Annabi duk an sauƙo sallan idi.
Suna ɗawafin ban kwana.
Sosai Sheykh ke baza ido ko zai sake ganin wancan mutumin amman ina hakan bai samuba.

Koda suka fito daga ɗawafin ban kwana.
Kai tsaye gidan Sheykh Abdulkareem suka wuce.
Nan yayi musu addu'o'in komawa lfy.
Kusan duk baƙin gidan a ranar suka bar gidan.
Da su Aunty Hafsat ma ranar suka juya Masco hakama Ibrahim.
Koda suka iso Airport kowa da inda ya nufa.
A nan Ibrahim ya ruggume Sheykh tare da ɗan dukan bayanshi yace.
"In Sha Allah Auren Haroon dani za'ayi".
Shima Sheykh ruggumeshi yayi gam-gam tare da cewa.
"Allah yasa, ina kewar rashinka a ƙasar mu".
Aunty Rahma ne tace.
"Kai jirgifa ba jiranku zaiba oga Sheykh".
Sakin juna sukayi kana kowa ya nufi inda jirgin ƙasarsa yake.

Bayan duk matafiya sun shiga, jirgin ƙasar Nigeria wanda zai sauƙa jihar Ɓadamaya.

A hankali ya zauna.
Ya Hashim na gefenshi.
Kasan cewar yana kusa da window ne, ya ɗan juya yana kallon mutanen daketa hada-hadar nufar inda jiragan ƙasar su jihohinsu suke.
Can cikin wasu ayarin mutane maza da mata ya hango wannan fuskar da ya gani.
Sun nufi can ciki suna tafiya yankin da jiragen ƙasar Cameroon suke.
Cikin tarin mamaki ya bishi da kallo tabbas badon jirginsu ya fara ƙugin tashiba da ya fita yaje ya tabbatar da fuskar dattijon da yake hangowa.

A haka dai suka ɓacewa ganinshi.
Kana jirginsu ya ɗaga zuwa ƙasarmu ta haihuwa.

Ana gida Nigeria kuwa cikin Jihar Ɓadamaya a Masarautar Joɗa.
Zaune suke a falon.
Shatu na waya da Junaidu nan yake ce mata,
Sun samu sauƙi dukansu.
Ance za'a sallamesu bayan salla.
Kuma harda ɗinkunan kayan salla akayi musu.

Bayan sun gama waya da shine ta kira Rafi'a.
Nan suka gaisa har ta bawa Ummi su gaisa.
Bayan ta bawa Ummi wayarne.
Jamil ya ɗan kalli agogon hannunshi a hankali ya miƙe tare da kallon Shatu yace.
"Muje mu gyara Side din boss kar ya dawo ya samu da datti".
Kai ta gyaɗa mishi kana ta amshi wayarta da Ummi ke miƙa mata.
tare da ce mata.
"Eh dan Allah Shatu tashi maza-maza kuje share wurin da kyau".
A hankali ta miƙe tare da cewa.
"To."
Hibba ce ta bisu a baya.
Jamil na gaba ita Shatu'n tana tsakiya.
Hibba na bayanta.
A haka suka shigo falon. Da komai na ciki yake fes-fes babu wani daddi ko ƙura ko hargitsewa, sabida an share falon safiyar yau, sai ƙamshi da sanyi ke tashi.

A hankali Jamil ya ɗan sa hannunshi tsakanin ziri-zirin igiyoyine masu sarkafe da jeren duwatsu masu sheƙin Daimond dake matsayin labulen Dinning area ɗin shi.
Ita dai Shatu ido ta zuba mushi,
ganin ya zaro key ɗin a cikinsu.
Ƙofar bedroom ɗin ya nufa tare da cewa.
"Muje."
To sukace kana suka biyo bayanshi.
Tana nazarin wurin da suke ajiye key ɗin.
Key ɗin ya saka cikin raminshi tare da murzawa.

Da sauri Shatu ta rumtse idanunta.
A hankali take jin zuciyarta na harbawa da sauri-sauri.
Shi kuwa Jamil tura ƙofar yayi bayan ya murɗa key ɗin ya buɗe.
Wani irin masifeffen harbawa da azaban ƙarfi zuciyar Shatu tayi.

Kutsa kai cikin Jamil yayi.
Tare dasa hannunshi jikin ginin a hankali ya kunna wutan ɗakin hasken ya gauraye ko ina,
jikin window ya wuce ya yaye labulen tare da buɗeglass ɗin.
Iskam cikin Garden ɗin dake bayan window wanda ɗawisu yake ciki.
Ya buso ɗakin.

Juyowa yayi ya kalli Shatu da ke tsaye bakin ƙofar.
"Ku shigo, in nuna miki yadda zakiyi mishi".
A hankali Hibba ta ratsa gefenta tare da cewa.
"Aunty Shatu mushiga".
Ido ta buɗe a hankali tare da bin bayan Hibba da kallo.
Kana ta ɗaga ƙafarta da kyar ta.
Taka cikin ɗakin, wani irin azabebben sarawa kanta yayi tamkar ana buga mata guduma a tsakiyar kan.
Cikin rawan ƙafa ta ɗaga ƙafafuwan ta,
Tayi taku huɗu zuwa biyar.
Ta kusa isa tsakiyar ɗakin.
Kenan.
Wani irin jujjuyawa taga kanta nayi.
Wasu irin ababe masu ban tsoro ta fara gani suna gilmawa cikin ƙwayar idanunta, shiyasa taketa jujjuya kanta.
Ta kalli gabas ta kalli yamma ta kalli kudu ta kalli arewa.
Hibba ce ta juyo tana kallonta jin Jamil nata mgna bata bashi amsaba.
Cikin sauri ta matso kusa da ita ganin yadda taketa jujjuya kai, ga idanunta da suka juye suka zama kamar harari garke, kana sai Rollin ball eyes ɗin ta take da sauri-sauri.
Cikin Mamaki Hibba tace.
"Aunty Shatu! Aunty Shatu!!".
Shiru ba amsa hakane yasa.
Jamil juyo kanshi ya kalli inda suke, da sauri ya juyo gaba ɗaya jikinshi ganin.
Wani irin karkarwa da jikin Shatu keyi.
Hibba kuwa da ƙarfi cikin tsoro tace.
"Aunty Shatu lfy kuwa?".
Ita kuwa Shatu, zuwa yanzu bata jinsu bata kuma fahimtar me suke faɗa hankalinta ya juye.

Cikin wani irin layi da rawan jiki tamkar mazari ta nufi tsakiyar ɗakin.

A nan ta tsaya gis gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi.
Cikin tsananin tsoro da firgita.
"Hibba ta juya a guje tana cewa.
"Wayyo Ummi! Ummi!! Ummi!!! Kizo zakiga yadda Aunty Shatu keyi."
Ummi dake falo ita da Aunty Juwairiyya,
Kamar daga sama suke jiyo muryar Hibba tana rabka musu kira cikin firgici da razani.
Haka yasa Ummi da Aunty Juwairiyya miƙewa da sauri suka nufi corridor'n da suke jiyo muryar Hibba na fitowa.
Kiciɓis sukayi a bakin ƙofar falon.
Cikin sauri Ummi ta ture Hibba ta wuce da gudu ta nufi cikin ɗakin.
Sabida jiyo muryar Jamil na cewa.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun hasbunallahuwani'imal wakil. Ummi! Ummi!! Kizoooo".
Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka shigo.
"Dai-dai lokacin kuma rawan da jikin Shatu keyi ya tsananta.
Wani irin kuka tasa tare da tafiya ƙasa luuu zata faɗi

Kusan a tare Ummi da Aunty Juwairiyya suka tarota.
Bisa jikin Ummi ta faɗi hakan yasa itama Ummi tayi ƙasa ta zauna.

Babu abinda suke maimaitawa sai innalillahi wa innailaihi rajiun.
A kiɗime cikin tsananin gigita Jamil yace.
"Subahanallahi Ummi ta sumafa".
Jiki na rawa Aunty Juwairiyya ta juya da gudu babban falon ta fito tare da ɗauko goran ruwan sanyi.
Kana ta juyo a da sassarfa ta nufi can.

Hibba kuwa a gigice take gayawa Jalal da Ya Jafar abinda ke faru.
Da sauri ya Jafar ya tashi ya nufi can.

Jalal kuwa ya zauna dan ya lura Hibba tayi masifar tsorita.

A ɗakin nashi kuwa,
Shiru ta lafe jikin Ummi kamar babu rai koda.
Ummi ta yayyafa mata ruwan sanyi a fuskarta, a banza saida ta kuma watsa mata a karo na uku ne.
Kafin taja wani dogon numfashi cikin sanyi da tsoro Ummi tace.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ta sunkuyo kanta tana ɗan kiranta.
"Shatu! Shatu!! Shatu!!!".
Ba amsawa kuma bata buɗe ido ba,

A hankali ya Jafar ya zauna gefensu, karatun da yakeyi yaci gaba dayi.

Cikin sanyi ta buɗe idanunta.

Sai kuma ta yunƙura a hankali ta tashi zaune.
Da sauri Ummi ta zaro ido ganin yadda idanunta suka juye a murɗe.

Ita kuwa Shatu miƙewa tsaye tayi, cikin rawan sanyi da karkarwa, ta fara zagaya ɗakin a hankali taje baki Bathroom nanma buɗe ƙofar tayi ta shiga.
Jim kaɗan ta fito.
Idanun suna yadda suke sai dai.
Yanzu hawayene keta shatata babu ƙaƙƙautawa.
A hankali tazo bakin gadon.
Sai kuma kawai sukaga ta faɗa kan gadon a sune!
Wannan shine tashin hankali da ba'a samishi rana.
Da gudu suka kumayi kanta, cikin firgici da tsananin tsoro Ummi ta ƙara yayyafa mata ruwan.
Amman shiru, haka suka tsaya cirko-cirko, shi kuwa Ya Jafar sai gashi yana karatu yana kuka kamar dai yadda yakeyi kafin a auro Shatu a masarautar Joɗa in Sheykh baya nan.

Gaba ɗaya sun birkice sunma rasa me zasuyi.

Aunty Juwairiyya kuwa itama kuka ta farayi.
Jiyo kukanta da na Ya Jafar ne yasa, su Jalal da Hibba shigowa.
Ganin tana can yashe kan gado a sumene yasa Hibba ma kuka.
Cikin ƙarfin hali Jamil yace.
"Aunty Juwairiyya Hibba kada kuyi kuka, kuja hankalin mutane nan.
Gashi yau salla ba mamaki akwai mutane a cikin Garden."
Cikin tashin hankali Ummi tace.
"Bari inje in sanarwa Gimbiya Aminatu abinda ke faruwa, ta sanarwa Lamiɗo, sai in biya in sanarwa Hajia Mama."
Da sauri Aunty Juwairiyya tace.
"Eh yafi kam".
Ta juya zata fita kenan sai sukaji tayi wani irin nakasheshen dogon numfashi mai sassanyan sauti.
Da sauri Ummi ta juyo ta dawo jikin sanyi tace.
"Shatu! Shatu!! Shatu!!!".
Shiru babu amsa sai binsu da ido tayi ɗaya bayan ɗaya.
Ganin hakane Jamil ya matso.
Tofi ya farayi mata.

Ummi kuwa ci gaba da kiran sunanta tayi.
Cikin tsoro Hibba tace.
"Ummi kinga idonta ya koma dai-dai."
A tare sukace Alhamdulillah.
Sai kuma Ummi ta kuma kiranta.
"Shatu!".
A hankali tace.
"Na'am Ummi".
Sai kuma ta kalli inda take, kana ta juya ta kallesu baki ɗayansu, cikin mutuwar jiki ta yunƙura ta tashi.
Murya a sanyaye tace.
"Jamil sharan kenan ka tsaya kanata kallona.
Gaya min ya za'ayi sharar".
Cikin sauƙe tagwayen numfarfashi suka kalli juna,
Cikin mamaki Jamil yace.
"No ki huta kawai my Aunty zan share".
Bata da ƙarfi a jikinta ko ta dage tace sai tayi sharar.
Bazata iyaba jikinta duk a mace.
Hakane yasa tace to.
Hannu ta miƙa Ummi tare da cewa.
"Ummi ɗan jamin hannuna mana".
To tace tare da kamo hannun.
Ta tsaida ita, cikin tafiyar sanɗa ta juya ta nufi hanyar fita.
Binta sukayi a baya gaba ɗayansu.

Jamil kuwa dube-dube yayi a cikin ɗakin kana.
Ya fara tattarewa da kimtsawa da sherawa, ya canza mishi beshit and blanket, da rigunan pillows.
Kana ya goge ko ina fes
Sannan ya shiga bathroom ya wonke ya goge mishi.


Su kuwa suna biye da ita har falonta.
Ganin ta wuce bedroom ɗinta ne yasa Hibba da Juwairiyya suka tsaya.

Ita kuma Ummi tabi bayanta.

Ganin tana shiga ta hau gado ta kwanta ne a take sai bacci yasa Ummi ta juyo ta fito.


Can babban falon suka koma suka zauna.
"Ikon Allah sai kallo wannan abu da ban tsoro da ban mamaki".

Ummi ta faɗa cikin al'hini.

Jiki a mace Aunty Juwairiyya tace.
"Sosai kam wannan al'amari ya firgitani".
Hibba dai sai zuru-zuru tayi da ido.

Nan sukayi ta mamakin wannan abin.

Jamil na fito shida Jalal suka tafi.

Shi kuwa Ya Jafar bayan matarsa yabi suka tafi.


Hibba kuwa da Ummi nan suka zauna.
Ummi ce ta kalli Hibba tare da cewa.
"Sai anjima zan kira Umaymah na sanar mata abinda ya faru".

Kai kawai Hibba ta kaɗan mata.

Ita kuwa Shatu baccin tayi mai nauyi sai kiran sallan azahar ne ya tasheta.

Su Sheykh Jabeer kuwa suna can sunata keta hazo.
Tafiya awa huɗu ne zai kawosu ƙasar mun.

A hankali ta buɗe idonta, miƙa tayi tare da yin salati.
Kana ta tashi zaune.
Bathroom ta shiga, wonka tayi da ruwan ɗumi.
Kana tayi al'wa tana fitowa.
Ta zura Hijabi tayi salla.
Bayan ta idarne, ta zauna gaban dreesing mirror.
Simple makeup tayiwa fuskarta.
Sannan ta sauya shiga, wani tattausan lace mai ɗan karen kyau da tsada tasaka duguwar rigace tayi cib-cib da jikinta. Kasan cewarta kalar pink guava da ɗigo-ɗigin mint green ne yasa tayi masifar dacewa da kalar jikinta.
Gyara gashin kanta tayi ta tubƙeshi tare da kitsen jelar.
Ta saketa bisa kafaɗunta.
Ɗaurin asseta tayi

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment