Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

can ƙasa yace.
"Ya Jafar! Yana buƙatar kulawata, baya son nayi nesa dashi, Umaymah Jalal da Jamil basu da hankali yaran basu da nitsuwa Umaymah basu san ciwon kansuba Affan kuma baya nan".
A hankali wacce ya kira da Umaymah ta gyara zama cikin tarin kula da bege da tausayi da ƙaunar Jazlaan ɗin nata cikin tausasan laffazi tace.
"Daɗewa zakuyi ne Jazlaan?".
Hannunshin yasa yana ɗan shafa sumar kanshi cikin rumtse ido murya can ƙasa yace.
"Sitti tace zamu daɗe a can, kuma Maimartaba ta gayawa kai tsaye, shi kuma ya faɗawa Abba kai tsaye umarni suka bani".
Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
"Ba komai Jazlaan in sha Allah babu abinda zai samu Jafar, in kaje kayi ta mishi addu'o'in kamar yadda ka saba, in sha Allah yana cikin kulawa da kariyar Allah".
Kanshi ya ɗan gyaɗa mata,
Domin bai fiye yawan maganaba in ba amɓaton Allah ba, dan ma ta kasance cikin mutun biyar ns duniya da yake iya yin doguwar magana dasu, musamman Maimartaba da mafi akasari faɗa ke haɗasu, sai ita sai kuma Umminshi Jakadiyarsu kenan wacce tun yana jariri itace uwar rainonshi sai Sitti da Jadda".
shiru ta ɗanyi tana kallon yadda ya lumshe ido tamkar bazaiyi magana ba,
bata dai katse kiranba har tsawon 3 minutes kafin ya ɗan motsa laɓɓansa ba tare daya buɗe kwayar kekyawan idanunshi yace.
"Umaymahhhh".
yadda ya kira sunanra ya tabbatar mata halin da zuciyarshi ke ciki, tafi kowa na duniya sanin matsalarki Sheykh Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero.
Cikin kulawa tace.
"Na'am Jazlaan".
tashi yayi zaune a hankali ya fuskanci wayar tasa da kyau, hannunshi ya haɗe wuri ɗaya tare da cewa.
"Umaymahhhh Jalal".
Cikin kulawar da ƙanwar uwa shaƙiƙiya kan iya bawa ƴaƴan ƴar uwarta, da tarin son da takeyiwa ƴaƴan ƴar uwarta Tata, musamman shi Sheykh, a hankali tace.
"Me Jalal yayi".
Kanshi ya ɗan ranƙofar tare da cewa.
"Umaymahhhh Jalal bayaji, ya fiye gagara, da son jawowa Ahlinmu abin faɗa.
Ɗazuma kwalaɓen giya fa ya shigo dasu cikin masarautar da ta kasance tsarkakkeya.
Ga Jamil kuma babu nitsuwa tattaredashi, duk inda yaga mace, jikinshi na rawa yakebi ya zama kamar ɗan akuya, Umaymah in nayi nisa da gida, zasuyi abinda zai sasu a matsalar rayuwa".
Wani dogon ajiyan zuciya Umaymah ta sauƙe a hankali tace.
"Kada ka damu, in sha Allah babu abinda zasuyi da izinin Ubangiji rayuwarsu bazata lalaceba kodan addu'o'in da kakeyi musu, da irin tarbiyar da kake basu".
Kanshi ya gyaɗa tare da taune lips ɗinshi na ƙasa yayinda lokacin ɗaya kwayar idanunshi sukayi wani irin kala su ba jaba sunba fariba.
Cikin rauni miskilar muryarshi yace.
"Na sanifa Umaymah babu abinda sukeyi, nasan Jalal ba mashayin giya bane baya shan komai, amman ya rigada duniya tanayi mishi kallon mashayi, tantiri kana taƙadirin yaro.
Haka nan nasan Jamil ma ba mazinaci bane Umaymah amman a idanun mutanen duniya shi tamkar ɗan akuya suke ganinshi,
Kamar yadda Ya Jafar yake ba majanuni bane amman mutanen duniya kallon majanun suke mishi".
Kanshi ya sunkuyar cikin sakekkiyar murya yace.
"Duk an liƙa musu munanan tabo, a cikin rayuwarsu, Umaymah, ni ma ɗin bazan tsiraba tabbas nasan nima akwai wani tabon da ake kallona dashi, nasan nima bazan tsiraba".
Da sauri Umaymah ta sunkuyar da kanta ƙasa wasu zafafan hawaye masu azabar zafi da ƙuna a zuciya suka fara kwaranyowa a idanunta, wani zazzafan shessheƙan kuka ya kwabce mata.
Jin shessheƙan kukan natane yasa Sheykh Jabeer ya ɗan ɗago kanshi cikin jarumta da ƙarfin hali yayi wani murmushi mai ciwo a rai.
A hankali yace.
"Kuka kuma Umaymah, inada yaƙinin ƙarfin zuciyarkine da yasani sanar dake matsalar ƴaƴan ƴar uwarki, tunda ita bazata iya yin komai a kaiba".
Cikin shessheƙan kukan tace.
"Ba komai Jazlaan in sha Allah babu komai face al'khairi a cikin rayuwarku, insha Allah babu wani tabon da mutane ke ganinka dashi.
Yanzu yaushe zaka wuce Leddi julɓe?".
Cikin miskilar murya mafi karamci yace.
"Yau da dare zan wuce, gobe da asuba zamu wuce Saudiyya Sittin ta matsa tana so taje taga ahlinta".
Kai ta ɗan gyaɗa kana tace.
"Ibrahim ma yace ya kusa dawowa".
Kanshi ya ɗan rausayar kana yace.
"Eh munyi mgna dashi ɗazu".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalli sauran woyoyinsh dake bisa Stull ɗin dake gefenshi,
Kiran shugan ɗaliban J.S.U Ɓadamaya ne ke shiga,
bai kula kiranba yaci gaba da magana da Umaymahnshi, har saida yaga ta samu nitsuwa kafin ya barta.

Tashi yayi a hankali yake taku cikin kamala da nitsuwa irinta manyan limamai a hankali yake manna farar tattausar fatar ƙafarshi da in ya taka sai kaga kamar jini zai tsallo.
Yana shiga cikin ɗakin nashi, al'kyabbarsa ya cire tare da buɗe wani sashi na durowarsa ya sanƙala a masanƙalinta.
Da tattausan farar jallabiyar dake ƙasanta ya shiga bedroom da ita,
Wannan lokacin wonkansa ne, babu abin da zai katse mishi uzurin domin ya kasance mutun mai mutunta lokacin rayuwarsa ko wani lokacin da abinda yakeyi.

Wonka yayi cikin tamfatsen bathroom ɗin nashi.
Yana fitowa, ya wuce gaban dreesing mirror, kimtsawa yayi a gaggauce dan lokacin tafiya aikinshi ya karato.

Koda ya gama kimtsawa cikin wasu tattausan manyan kaya riga da wondone da kuma babbar gariyarsa, kayan sun kasance farare ƙal-ƙal ne, sai zazzafan aikin kufta da akayi mishi mai blue color, kana sai hular zanna bukar daya murza bisa kanshi da yake wadace da tattausan suma baƙiƙƙirin mai sulɓi da sheƙi,
hular itama farace sai ratsin blue, hakama takalman sawunshi da suka kasance irin na sarakuna ne,
Agogon Daimond dake hannunshi shima yanada yanayin ɗigon blue mai garai-garai,
Sai kuma ya sunkuyo ya ɗauƙi biyu daga cikin woyoyinshi yasasu a al'jihun babbar rigar tasa,
jakar system ɗinshi ya ɗauka da hannunsa na dama, kana hannunshi na hagu kuma sajenshi yake shafawa a hankali har zuwa kan madai-madaicin tsabtaceccen gemunshi mai ɗan karen kyau da burgewa.

A haka ya fito daga cikin ɗakin nashi.
Yana fitowa cikin tamfatsen falon nashi da ya kasance yanada iyaka da bayi da hadimai duk iya karsu can bakin ƙofar babban falo bai yarda da wai bayi su shigo suyi mishi hidima har cikiba,
Jamil shike kula da tsabtan sashin sirrin ɗan uwan nashi.
Ido ya lumshe jin wani irin sassanyan ƙwamshi da sanyi mai ratsa zuciya daya ziyarci jiki da zuciyarshi.

A hankali yake taku, har zuwa dinnin area, a hankali ya ɗan juyo, jin an jamishi kujerar.
Jamil kenan.
Zama yayi bisa kujerar, kana, ya miƙawa Jamil jakar system ɗin nashi.
Amsa yayi ya rataya a kafaɗarshi,
sannan ya matso gab kusa da ɗan uwan nashi,
baƙin Tea ya haɗa mishi da zuma sai bredy wanda shima da zuma a jikinshi ,
wanda yasan iya abinda zai ci ya sha kenan duk da tarin. Abinci da hadiman Aunty Juwairiyya, suke kawowa dominshi ga kuma na Hadiman Hajia Mama, wanda duk Umminshi Jakadiyace ke kawosu, domin ita tana shiga har cikin falonshi ɗakin konciyarshi ne dai bata shiga, amman falo ukun nan duk tana shigarsu da kitchin da sauran ɗakunan sashin.
Suna zama babu jimawa, wayar Jamil ta fara tsuwa, da sauri ya ɗauka tare da karawa a kunne,
sai kuma yayi zuru-zuru da idanu ganin yadda Hammanshi ya tsareshi da fitinannun idanunshi masu sa hanjin cikinsu kaɗawa, cikin yin ƙasa da murya yace.
"My love Sheykh yana kusa".
Ya ƙarishe mgnar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Sheykh kauda idonshi yayi yaci gaba da zuƙan tea ɗin a hankali a hankali.
Shi kuwa Jamil cin abinci yai haninƙan kana.
Shi kuwa Sheykh ido kawai yake zubawa ƙanin nashi bai tashiba har saida yaga ɗan uwan nashi ya gama cin abincin.

Sannan suka jero suka fito falo,
A can bakin ƙofar shigowa babban falon suka samu sarkin ƙofa da kuma hadimai na jere a wurin suna hangosu duk suka rusuna har ƙasa har suna haɗa baki wurin cewa.
"Takawarka lfy ɗan Babban Yaya jikan mai martaba sarkin Nuruddeen jika ga mai Alfarma Sarkin Musulmai Jalaluddin.
Malam ɗan Malam Habibullah jinin Limamen Saudia malamai magada annabawa, jika ga ƙabilar da tafi ko wacce ƙabilar duniya d...".
Hannun shi biyu ya ɗaga musu alamar amsawa gaisuwar da sukayi mishi, da kuma dakatar dasu da kirarin da sukeyin.
Kana yaci gaba da taku Jamil na biye dashi a baya, Sarkin ƙofane yayi saurin rusunawa tare da cewa.
"Hajia Mama ta turo jakadiya a sanar maka cewa tana buƙatar ganinka".
Kanshi ya gyaɗa kana yaci gaba da tafiya,

Gefen dama ya nufa, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali hadiman dake tsaron wannan ƙofar suka fara rusunawa tare da bashi hanya da gaidashi.

Tafe suke har cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi.

Wasu ƴan yarane guda biyu duka mata,
Suna ganinsu suka ruga a guje jikin Sheykh Jabeer suka faɗa tare da cewa.
"Sabahul khair Uncle MJ".
Sunkuyowa yayi ya ɗan shafa kansu tare da cewa.
"Sabahul noor ya Habittey".
murmushi sukayi kana suka sakeshi suka isa gaban Jamil sunkuyowa yayi ya ɗauki ƙaramar bayan sun gaidashi ne babbar ta juya da gudu tana cewa.
"Ummi ga Uncle MJ".
tsayawa tayi tare da kamo hannun wata kekyawar mace matashiya yar duma-duma, tayi shiga irin ta larabawa, kamo hanunta tayi suka fito falon.

Murmushi ta ɗanyi tare da cewa.
"Barka da safiya GARKUWAN FULANI, GARKUWAN ahlin Sitti".
Fuska ya ɗan sake still bawai yayi murmushi bane, a hankali yace.
"Barka da safiya".

"Barka dai Sheykh Dr Garkuwa".

Babbar rigarshi ya ɗan gyara tare da cewa.
"Ya jikin Ya Jafar?".
Kai ta ɗan ranƙwafar tare da yin rau-rau da idanunta murya na rawa tace.
"Jiya kwana yayi baiyi bacciba, Sheykh, hankalina yana tashi, sabida duk randa baiyi bacciba, to kwana yake karatu yanayi yana kuka, kukan da yakeyi ɗin ne yake sashi zazzaɓi da ciwon kai, gashi ba cikin zuciyarsa yake karatunba ya wuni karatu a baiyane ya kwana karatu a baiyane babu bacci".
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da nufar kofar wani ɗaki.
Jamil da Juwairiyya na biye dashi a baya.

Suna shiga cikin ɗakin, da sauri Sheykh ya karisa gaban wani kekyawan mutun fari ƙal mai tarin tsabta wanda yake tsananin kama da Jamil duk da duk suna kama da juna amman Jalaluddin yafi kama da Jabeer, Jamil kuma yafi kama da Jafar.
Zaune yake bisa sallaya, ya jingina kanshi da jikin gado, karatun al'ƙur'ani yakeyi cikin nitsuwa da da cikar tajwid, babu ɓata ko na ɗigo, yana karatun ne hawaye na kwaranya daga kwayar idanunshi,
A hankali Sheykh Jabir yasa Hannu ya kamo hannun ɗan uwan nashi,
A hankali Ya Jafar ya buɗe idanunshi ganin mutumin da shi kaɗai ke sashi yin abu yayi ko ya hanashi ya hanune ya sashi gyara zama still yana karatu.
A tausashe Sheykh Jabir ya ɗan ranƙwafar da kanshi cikin salon tausayawa da muryar larabawa yace.
"Sadakallahul Azeeeeeem".
Jin hakane yasa wannan bawan Allah'n ya ɗago tafin hannunshi addu'o'in ya, fara karantawa kusan tsawon 3 minute sannan suka shafa a tare,
Cikin wani zafi da ƙuna Sheykh Jabeer ya taune lips ɗin shi na ƙasa hannunshin yasa ya kamo na Ya Jafar ɗin,
ba musu ya miƙar dashi,
kan gadonshi ya zaunar dashi,
A hankali ya juyo ya kalli Juwairiyya cikin sanyi yace.
"Yaci abinci kuwa?".
A hankali tace,
"Tunda asuba daya dawo masallaci na bashi yaci abinci, kuma yanzuma na bashi ya ɗan ci".
Kanshi ya rausayar kana yace.
"Maganin shi fa kin bashi".
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Eh na bashi maganin yasha".
Jin hakane yasa Sheykh ya kamo hannun kekyawan Yayan nashi ya kontar dashi bisa gadon blanket yaja ya rufe mishi rabin jikinshi a hankali yace.
"Ya Jafar kayi bacci, kaji jikinka zafi".
Shiru bai kulashiba sai dai, ya lumshe idonshi.

A hankali ya juyo ya kalli Matar ɗan uwan nashi kuma ƴar kawunsu yayan Mamansu yace.
"Juwairiyya Nagode".
Hawayen dake zubo mata ta sharce tare da kamo yaranta ta ruggumesu,
Jamil kuwa tuni yaketa zubda hawaye.
Cikin rawan murya Juwairiyya tace.
"Sheykh ka dena gode min nimafa Ya Jafar ɗan uwanane kuma mijinane, uban ƴaƴana, to in ban kula dashiba da waye zan kula a duniya?."
Kanshi ya kauda kana ya juya ya nufi hanyar fita a ranshi yanajin ko sai yaushe manyan burukan rayuwar da fatanshi da addu'o'in shi zasu ƙarɓu yana ganin daraja da girman Juwairiyya domin tayi musu tsantsar halacci ta zauna da ɗan uwanshi a matsayin majanuni, a haka suke tafiya yana zancen zuciya.
Jamil na biye dashi a baya.

A haka suka fito, suna tafe hadimansu na biye dasu a baya.
A hankali ya ɗan juyo ya kalli Jamil da yasan yanada rauni dan Jamil yanada tausayin ɗan uwanshi duk da yanada shekiyanci amman yanada rauni a kansu abu kaɗan ke sashi kuka,
Sashin dake tsakanin sashin su Jamil dana Ya Jafar suka wuce wanda nanne sashin Sheykh, sashin su Jamil ɗin suka shiga.
Kai tsaye suka wuce har cikin bedroom.
Tsaye suka sameshi yana taje suman kanshi mai yawa ga wondo iya ƙugu duk rabin boxes ɗinshi a woje ga wondon da rabin jiki duk woje waishi kirezi ko? da alamun fita zaiyi.
"Meya hanaka zuwa masallacin jumma'a da wuri jiya?
Waɗannan kolaben barasar na waye ne?".
Sheykh ne ya jero mishi tambaya biyu a lokaci guda,
A hankali Jalal ya juyo cikin shakku da shayi da kwarjin Hamma nasu ke sasu ji yace.
"Mamace ta aikeni, jiya shiyasa na dawo a ƙurerren lokaci.
Kolaben barasar kuma nasu Ashid ne, na kwace ne lokacin da suka saya, dan karsu sha".
Kanshi ya gyaɗa dan ya gamsu ya kuma yarda dan yasan duk rintsi ƙanennshi basa mishi ƙarya.
Cikin faɗa yace.
"Ka kula da salla, ka tsaida ita kan lokacinta, kasan irin abokan da zakayi yawo dasu, ka tabbatar kaikeyi nasara akan juya halaiyarsu daga mummuna i zuwa kekkyawa. Shiyasa ban hanaka mu'amala da suba, domin manzon Allah yace.
"Mutun ɗaya ya shiryu ta dalilinka, tarin ladan yafi a baka tarin jajayen raƙumi.
Kada ka bari suyi nasarar juya rayuwarka daga kekkyawan i zuwa mummunan.

Kanshi ya gyaɗa cikin ladabi yace.
"In sha Allah".
Daga nan suka juya baki ɗayansu,
Kai tsaye sashin Hajia Mama suka wuce.
Inda hadimanta sukayi musu iso,
Har cikin bedroom ɗinta suka shiga,
A bakin gado suka sameta, zaune, yayinda baiyawarta Mansura keyi mata tausa.
Murmushi tayi tare da kallonsu yadda suke a jere, koda maƙiyinsu ne sai sun burgeshi sun bashi sha'awa yayi fatan inama da ƴaƴansa ne.
Kan dantsatsetsen shimfiɗar kilisa mai kyau da zanen tsuntsuwar ɗawisu, suka zauna,
Cikin kula tace.
"GARKUWAN FULANI, Jamil, Jalal, Allah yayi muku al'barka".
Amin Amin, Sheykh da Jamil suka amsa,
Jalal kuwa shiru yayi,
Ita kuwa Hajia Mama murmushi tayi tare da cewa.
"Babanmu mai Al'farma Sarkin Musulmai Jalaluddin meya farune naga fuskarka a haɗe?".
Kanshi ya girgiza alamar.
"Babu".
Shi kuwa Sheykh ido kawai ya zuba kan wayarshi,
Jamil ne ya ɗan gyara zama, tare da cewa.
"Mama Abba fa".
Kai ta ɗan jinjina tare da cewa.
"Abinda yasani nemanku kenan, Abbanku ya tafi Abuja jiya da dare, yanzu kuma Gimbiya Samira zatabi bayanshi".
Shiru Sheykh yayi a ranshi yake jinjina al'amarin mahaifinsu.
Babusu a cikin dukkan sabgogin rayuwarsa komai nashi saidai suji a bakin Hajia Mama ko kuma a jaridu ko gidajen Radio ceɗi meɗinshi da amaryarshi Gimbiya Samira ƴar sarkin Nokan ce ita kuwa mijinta shine rayuwarta babu ruwanta da sabgar kowa.
Sam Abba bai shaƙu dasuba da wuya ka ganshi zaune dasu yana hira dasu kamar uba da ƴaƴan shi.
Saɓanin Maimartaba ko meye zaiyi Sheykh zai sani shine mutumin da yake shawara dashi akan duk abinda ya shafi addini.
Kanshi ya ɗan kauda tare da cewa.
"Allah ya dawo dashi lfy".
Amin Amin sukace baki ɗayansu,
Cikin kula yace.
"Hajia Mama Affan fa sai yaushe zai dawo?."

"Next month?". Ta bashi amsa a gajarce.

A gogon hannunshi ya ɗan kalla kana a hankali ya miƙe tare da cewa.
"Zan wuce Hospital shugaban ɗaliban makarantar ya kirani cewa sunada mara lafiyar da take buƙatar kulawar gaggawa".

Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
"A dawo lfy".
Amin Amin sukace kana suka fita suka tafi.

Daga nan kai tsaye FADA suka nufa.
Inda sarkin fada yayi musu iso zuwa ga Maimartaba kakansu.

Suna shiga suka samu fada na cike da dattawa karsu Waziri, Matawalle, Galadima, Wambai, Ɗan isa, ɗanm' buram, sairkin Dogarai sarkin Gida, da kuma Duba gari, kana, sai kuma hadiman dake tsaye bayan sarki sunayi mishi fifitar sarauta da maficin fiffigen Ɗawisu.

Farin dattijo bafulatani, mai cikar haiba.
Yana cikin manyan kaya na sarakai, wanda al'kyabbarsa kaɗai ta kai kuɗin mallakar wani gidan,
A gabanshi suka zauna gaba ɗayansu uku,
A hankali Sheykh yasa tafin hannunshi kan rumfar sawun kakan nashi da suke kan wani tim-tim mai girma da masifar taushi.
taɓa sawun kakan nashi yayi tare da cewa.
"Barka da hantsi Maimartaba, ya sawun naka?".
Duk maganar nan da yayita a hankali yake yinta ko Jamil da Jalal dake gefenshi basujiba.
Shi kuwa Maimartaba hannunshi ya ɗaura kan tsakiyar kan Sheykh wanda tun kafin ya zauna ya tura hulanshi ya koma baya, dafa tsakiyar kanshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah".
Sai kuma ya kalli Jamil da Jalal da suke gaidashi,
dan su sai yanzu suka haɗu dashi tunda gari ya waye,
Tsaɓanin Sheykh da kullum tare suke dawowa masallaci sallan asuba daga nan kuma ɗakin hutunshi suke shiga kakarsu mace ta kawo musu abin taɓawa.

Bayan sun gaggaisa ne da mutanen fada, suka fita suka tafi.

Sashin kakarsu Gimbiya Aminatu suka nufa.
Basu da hijabi da sashin kakar tasu shiyasa kai tsaye suka shiga a falo, suka sameta,
Da alamun yanzu ta fitito Dan ga al'kyebba a jikinta ga kuma hadimanta a zagaye da ita.

Cikin tarin so da ƙaunar Jazlaan ɗin nata take kallon su,
Murmushi tayi tare da cewa.
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi, kai dai kaji abinda malam zaice kada kace zaka binciki aikin malam".

Shiru Jamil da Jalal sukayi, shi kuwa Sheykh ido ya zuba mata.
Ita kuwa rausayar da kai tayi tare da cewa.
"Eh mana kaji abin da malam yace kada ka duba aikinshi, dazu na gama jin wani wa'azin ka da kayi kan falala da ni'imomin dake cikin aure, kana bayani duk maluntar mutun darajarsa bata cikaba in bashi da aure.
Sai najima wa'azin kamar da kanka kakeyi.
Meyasa ne Jabeer kayi niyar yin aure mana ka cikata nasabarka da kamalarka da martaba da darajar ka data masarautar Joɗa".
Jalal ne ya miƙe tare da cewa.
"Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya ni na tafi dan inada aikin yi".
Haratanshi tayi tare da cewa.
"Tafi daga nan mai ƙugu kamar buzuzu hegiyar masifa".
Hararanta yayi kana ya juya ya fita.
Ita kuwa Gimbiya Aminatu.
Jamil ta kalla wanda shima ya miƙe yabi bayan Jalal.

Shi kuwa Sheykh numfashin ya fesar tare da cewa.
"Maganinki ya kare koda saura?."
Da sauri tace.
"Yauwa magani ya ƙare a kawo min wani".
To yace kana ya mike ya fita.

Daga bakin harabar sashin kakar tasu,
Fadawanshi ke biye dashi a baya har parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau.
Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi.

Da sauri Ado drevernshi ya buɗe mushi ƙofar wata mota mai ɗan karen kyau wacce bada ita ya fita jiyaba, dan ita sai ranakun jumma'a-jumma'a yake hawanta,
wannan ta yau mai kalar ruwan tokace sai sheƙi takeyi,
yana shiga sauran fadawanshi suka yi yunƙurin shiga motocin dake jere a wurin a gefen wurin wanda dasu akeyi mishi rakiya.

Da sauri ya ɗaga musu hannu, cikin in in narsa da in yana saurin mgna yake fitowa yace.
"Kkku ba bari ba'a bukatar rakiya".
Da sauri suka ɗan rusuna tare da haɗa baki wurin cewa.
"Aje lafiya a dawo lfy Allah ya kiyaye gabanka da bayanka Sheykh".
Amin Amin yace a taƙaice kana ya shiga motar, sarkin ƙofa ya rufe mishi marfin sannan Ado yaja suka tafi.

Suna fita kai tsaye Babbar jami'ar dake cikin babban birnin Ɓadamaya suka nufa.


A can cikin makarantar kuwa,
Kasan cewar duk ɗaliban jami'ar sun san babban Doctor zai shigo yasa gaba ɗaya harabar asibitin dake cikin jama'ar cika da taron tsala-tsalan ƴan mata ƴaƴan manya, duk mai matsalar lfy tana fatan ya dubata sabida ƙwarewarsa.

A hankali wasu ƴan mata biyu suke taku a farfajiyar shiga asibitin, bisa alamu duka ɗayar bata da lfy dan ɗayar na rike da hannunta, kuma a hankali suke tafiya.

Cikin tausayawa ɗayar ta kalli wacce ta riƙewa hannun a hankali tace.
"Garkuwa ki daure kiyi sauri mu isa, wallahi zamu samu layi da yawa, kuma wannan Sheykh ɗin kasaitarsa nada tarin yawa, yanada doka da ƙa'idoji da tsari, yanada tsauri kan tsare kima da darajar addininshi, daga shigar jikinki in kinyi kuskure kaɗan na shigar kima wallahi bazai dubaki ba.
Shiyasa ahlul kitabi dake cikin makarantar nan suke masifar shakkarsa,
kinga gashi azahar ta kusa, kuma wallahi ko sarkin garin nanne yazo ya dubashi in dai lokacin salla yayi to tashi zaiyi ya fita ya barshi, gashi shiru-shiru da ido yake hukunta mutun".

A hankali wacce aka kira da GARKUWA tasa hannu ta gyara niƙab ɗin dake fuskantar, wacce ta dace da wata kekyawar arabian gawn dake jikinta
wanda dama shigartace haka kullum sabida gudun kada wani ya ganta ya tsaida ita dan tasan duk namiji daya nuna yana sonta har lahira ake kasheshi wanda kuma duk Rugarsu akeda yaƙinin Ba'ana ne dan mutunne mai masifar baƙin kishi, yasha sanar mata a kanta zai kashe kowa ba damuwarsa bane da fari duk wanda ya nuna yana sonta da bulalin shaɗi yake korarshi, to yanzu duk wanda yace yana sonta sai dai a wayi gari ya rasu.
Cikin sanyin muryar dake nuna azabar da takeji, murya na rawa tace.
"Rafi'a, bazan iyaba marata ciwo kamar zata ɓalle, ki sakeni kije ki amsar mana foldana kafin in ƙaraso".
Jin haka yasa Rafi'a cewa.
"Zaki iya tahowa ke ɗaya?".
Kanta ta gyaɗa mata a hankali.
Hakan yasa cikin sanyi ta saketa kana ta wuce cikin Hospital ɗin da sauri.

Dai-dai lokacin kuma motar Dr Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero ta kutso kanta cikin farfajiyar.
Bayan Ado ya dai-dai ta parking ne a cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Jabeer a samanta.
Ado ne ya fito da sauri ya buɗewa, Sheykh marfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito.
Cikin nitsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin.
Kasan cewar ta gabas ya fito Aysha kuwa ta yamma ta fito sai ya zama suna fuskantar juna.
Yayinda sai sun haɗu wuri ɗaya zasuyi kwana sun fuskanci kudu inda nanne mashigar cikin asibitin.

A hankali suke takowa suna fuskantar juna.
Sosai ya zuba mata ido sabida ya lura gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi alamun tsananin ciwo takeji gashi a hankali take taku.
Ita kuwa Aysha, tafiya takeyi da kyer sabida azaban ciwo da mararta keyi.
Kanta a sunkuye take tafiya, hakan yasa bata san da mutunba a gabanta.

Da sauri Sheykh ya tsaya sabida wani irin bugawa da ƙirjinsa ya fara. Ganin ta tunkaroshi gadan-gadan, kuma daga yanayin tafiyarta tamkar zata faɗi ƙasa.
Ganin tayi wani irin sunkuyawa tasa hannunta duka biyu ta damƙe mararta da takeji tamkar caccakarsa akeyi da allura.

Gefe ya ɗan tsaya yana kallon ikon Allah, ita kuwa GARKUWA rumtse idanunta tayi da karfi, wata fitinenniyar zuface ke tsastsafowa tako ina,
a hankali ta fara buɗe idanunta jin kartan da mararta keyi ɗin yana ɗan lafawa,
a hankali ta zubawa kyawawan sawunshi idanu, cikin sauri ta ɗago kanta, ganinta tsaye gab kusa da namijin da bata saniba ne yasata ja da baya da sauri tare da miƙe tsawonta cikin firgici murya na ɗan rawa tace.
"I'm very sorry".
Bai kulata ba, sai kauda kanshi da yayi gefe.
Ita kuwa Garkuwa cikin sanyi tace.
"Dan Allah kayi haƙuri".
Kai ya ɗan gyaɗa mata alamar Uhumm.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
"Uhumm kaima Doctor Sheykh ɗin kazo ganin ne?".
Da mamaki ya ɗan kalleta da gefen idonshi, sai kuma ya ɗan juyo kanshi kaɗan jin muryarta a sanyaye taci gaba da cewa.
"Muyi sauri mu shiga ance yanada shegiyar ƙasaita da isa, wai ko sarkine yake dubawa in dai lokacin salla yayi tashi yakeyi ya fita".
Cikin tarin mmki ya ɗan waro kyawan idanunshi tare da cewa.
"Umh".
Ita kuwa Garkuwa, hannu tasa ta matse mararta tare da cewa.
"Muyi sauri mu shiga, kaga kuwa kayi sa'a kayi shigar mutunci dan ance shi baya son ganin musulmi da lalatacciyar shiga, ancema in mace tayi shigar banza baya dubata, kaji shishshigin mutunfa ko meye ruwansa da rayuwar wasu ai kowa yayi mai kyau dan kansa ko?".
Rolling Ball eyes nashi yayi tare da gyaɗa mata kanshi.
Kana ya tsuke fuska yaci gaba da tafiya.
Ita kuwa Garkuwa cikin yin ƙasa da murya tace.
"Uhum shidama akace shine shugaban tuzuran ƙasar nan, yana zaune baiyi aureba, ai zama ba aurema ba kyau tunda dai yanada damar yi ko?".
Ɗan tsagaita takunshi yayi tare da cewa.
"Hummh".
A hankali ta bishi a baya cikin yanayin muryar mara lfy tace.
"Dan Allah ka tsaya in rigaka shiga kar yace sai ya dubaka kafin ya dubani".
Dai-dai lokacin kuma suka kutsa kansu cikin asibitin.
Da sauri Garkuwa ta zazzaro idanunta baki ɗaya, tare da dafe ƙirjinta ganin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa.
"Barka da hantsi Sheykh".
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, har ya shiga cikin wani ɗan corridor ya shiga wanda zai sadashi da tamfatsetsen Office dinshi ba tare daya ratsa ta cikin Reception ɗin su ba.

Ita kuwa Garkuwa gaba

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment