Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

an cika anyi maƙil.
Sallama na tsaye can bakin ƙofar shigowa.
Dogari kuma suna tsaye gefen hagu da daman Lamiɗo.
Suna rike da mafici sunayi mushi fifita, ɗanzagi kuma yana gefe,
Kana wasu fadawan duk suna gefen.
Gyaran murya Lamiɗo yayi tare da gyara zaman shi cikin shugarsa ta sarakuna masu al'farma, a hankali yace.
"To da farko dai fatan duk kowa na lfy".
Da sauri Ɗanzagi yace.
"Sarki ya gaisu yana yi muku fatan alkhaiy".
Sai ya kuma juyo ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Godiya suke."
Kanshi ya ɗan jingina da tattausar kujerarsa da masu son gadonta sunfi a ƙirga, cikin ƙasaita yace.
"Kamar dai yadda muka tattauna, kwanakin baya akan sarkin Garin Shikan,
to yanzu zan zantar da hukunci.
Sarkin aike na bada umarni kaje garin Shikan ka karɓo min sandar sarautar Shikan ka kawo min shi, yau ɗin nan.
Kaje da jagorancin Galadima, da Matawalle da Makawa, sai sarkin yaƙi".
Da sauri duk suka runsunar da kayu kansu tare da cewa.
"An gama".
Nan take kuwa suka miƙa suka tafi.

A cikin gida kuwa. Tunda asuba da Jabeer da tawagar ahlinshin suka dawo masallaci.
Kai tsaye ɗakin Umaymah ya nufa, suna biye dashi a baya.
Bisa sallaya suka sameta riƙe da al'ƙurani mai girma tana karatu cikin tsananin nitsuwa.

Ganin hakane duk suka fito falo.
Nan Aunty Juwairiyya taja Ummi suka tafi side ɗin ta da Hibba da ƴar aikinta suka shiga kitchen.

Jalal kuwa shine yaje wurin Ya Jafar, don bashi mgni kamar yadda Jabeer ya umarceshi.

Jamil kuwa waya yakeyi da sabuwar budurwarsa da ya samu.
Wacce yake masifar sonta,
Ko yaushe suna liƙe da juna a waya.

Haroon kuwa a falon Jabeer ya zauna yana kallon lbrin CNN.

Shi kuwa Sheykh Jabeer.
A hankali ya wuce ta gaban Haroon.

Gefen gabas ya fuskanta, inda labulaye sukayiwa wurin ƙawanya.
A hankali yasa hannunshin ya yaye labulen.
Wani ƙofa ya buɗe a .
Sai ga wani ɗan siririn corridor.
Shiga yayi, kana ya saki ƙofar ta koma ta mannu da ƙofar sai dai bata rufuba.

A hankali yake taku cikin nitsuwa,
Lips ɗin shi na ɗan motsawa alamun tasbihi yakeyi.
Tafiya mai ɗan tsawo yayi sai gashi ya kuma riski wata ƙofar.
Hannunshi yasa ya murɗa key ɗin ya buɗe, ƙofar.
Sai ga kuma wata ƙofa irin ta ƙarafuna kana dai iya hango woje.
Buɗe wannan ƙofarma yayi.
A hankali ya kutsa kai.

Wani irin sassanyan ajiyan zuciya mai tsawo yaja ya sauƙe a hankali.
Idonshi ya lumshe sabida wani irin sanyi mai masifar daɗi daya ratsa mishi jiki da zuciya.

Wani irin ɗan madaidaicin Garden Park ne mai masifar kyau.da sanyi da tsaruwa.

Daga nan bakin ƙofar daya fito ɗin.
Tayis ne fari tas a malale iya ganinka, sai gefen damanshi da bishiyoyin ayaba masu masifar duhu da sanyi dake jere reras.
Gefen hagunshi kuma bishiyoyi mangoro ne irin yan duƙus-duƙus ɗin nan ke jere,
Reras.
A hankali yake taku yana tafe yana tasbihi.
Yana jin kukan tsuntsaye mai daɗin ji yana ratsashi.

Tafiya kaɗan yayi sai gashi ya baiyana a wani irin wurin mai masifar kyau.
Wasu yan zagayen gini dakalin bulok bibbiyu akayi a ƙalla sunfi hamsin.
A ciki ko wanne zagayen akwai bishiyar dabino. Na gabanta inabi na gaban inabi tuppa, kana sai Yazawa, sai kuma na tsada, daga tsada sai na kanya, sai goruba da na giginya.
Cikin ko wanne zageyen kuma ƙasanshi koriyar ciyawa ce mai sanyi.

Can tsakiyar filin kuma wata iriyar ƙoramace mai masifar sanyi,
Ruwanshi na kwance fari ƙal-ƙal bakin wurin kuma jeren bishiyoyi goibane wanda sukayiwa kwaramar inuwa.

Gaban ƙoramar kuma wasu irin kujerun silver ne masu masifar kyau da sansi a jere a ƙalla sun kai goma zuwa ashirin.

Can gefenshi kaɗan kuma wani shingene aka zagaye da waya.
Shuke-shuken gargajiya akeyi a wurin.

Nan kusa da ƙoramar kuma shingen farar waya akayi a cikin ta wanda akayi ƴan ɗakuna-ɗakuna a cikin.

Tsuntsaye ne a ciki iya ganinka ko wanne da muhalli shin.

Kama daga Tattabaru farare ƙal-ƙal.
Sai kuma tsuntsu carki jajaye masu kyan launi ga kuma kanari da suke blue.

Sai kuma zabbi da suke yawo a ƙasa tako ina.
Can bakin ruwan kuma agwagin ruwa ne sunfi ɗari ƙwa-ƙwa.

Sai kuma zabbin daji.
dangin tsuntsaye dai babu irin wanda babu.

Ido ya zubawa tsuntsaye tamkar mai son yin magana dasu.


A hankali ya sunkuyar da kanshi jin tattausan gashin Ɗawisun Masarautar Joɗa da ya kai shekaru masu tarin yawa.
A hankali ya rusuna tare dasa tafin hannunshi ya shafa dai-dai ƙunɗun Ɗawisun inda wurin yake mai kalar blue mai kyau sabida Sheykh blue ne kalar da yafi so.
A hankali ta fara taku, ta juya mishi baya kana ta ɗaga bindinta sama samɓal har yana iya taɓo geminshi.
Wani irin takun ƙasaita tayi kana ta buɗa fikafikinta ta bazasu, ta fara tafiya a hankali.
Wannan itace suntsuwar da muddin mutun ba jinin Masarautar Joɗa bace, in ka shigo mata gaba gaɗi ba tare da an gabatar mata kai ba, zatayi ta yagune mutun tana caccakarshi.
Amman muddin dai kai jinin Masarautar Joɗa ne, kana shiga zata zo gabanka.
Tayi maka hakan.

Sai dai kuma bayan yin hakan in mutun nada wata zazzafar nasaba a masarautar misali shine sarki maici to in tayi wannan baza fikafikinta takanyi ta zagaya sarki sau bakwai kafin ta tsaya a gabanshi sai sarkin ya umarceta data tafi kafin zata tafi.

To babban abinda ya ƙara jazawa Jabeer matsala a rayuwarsa shine,
Duk sanda yazo gaban tsuntsuwar Ɗawisun nan sai tayi mishi wannan abin da zagaya sau bakwai abinda a tarihin masarautar sarki kawai yakeyiwa abin.

Matsalar abin a gaban Barrister Kamal da kuma Baba Bashiru da Abba sai Lamiɗo ne ta fara yimishi wannan abun.
Tofa ta bakin Baba Basiru ne mgnar ta zaga kunnen mazauna masarautar Joɗa.

Babban tashin hankalin masu son gadar wannan kujerar, shine yadda side ɗin Jabeer ke kusanci da Garden ɗin da take ciki.
Tashin hankalinsu ya ƙara tsananta ne tun randa Suka ga Lamiɗo yasa an buɗawa Jabeer hanyar shiga wurin ta cikin falonshi ba sai ya zagaya yabi hanyar da kowa ke bi ba,
Ya zama shida Lamiɗo sune masu hanya kowa daga falonshi zai shiga wurin.

A hankali Jabeer yayi murmushi tare da kallon yadda tsuntsuwar ta gama zagayashi kana tazo ta tsaya gabanshi tare da baza fikafikinta.
Cikin harcen Larabci yace mata.
"Fatana dai ba bauta min kikeyi ba! Domin babu wani abin bautawa da gsky sai Allah, wanda shine ya halicce ni ya halicceki.
Ni kuma ba kowa bane face halittarsa, sai dai na kasance cikin halittarsa mai girma da karrama fiye da komai, dan shi da kanshi yace.
Walaƙad karramna bani Adam."
Wani irin juya kai tsuntsuwar tayi kana ta meda fiffigefa ta rufe, kafin ta juya ta nufi wani kekyawan wurin da aka ware mata, inda take tare da yayanta da mijinta.

Juyawa yayi can gefe ya hango wasu yan kyawawan tsuntsaye farare
A bakin ruwan.

Ga tattabarun sun zagaye wurin da sauran tsuntsayen.

A hankali ya zauna a wata kujera mai kamar gado.
Kishinƙiɗa yayi kana ya lumshe idonshi yana maijin yadda sassanyan iskar wurin ke ratsashi.
Karatun al'ƙur'ani ya fara cikin sassanyan murya mai daɗin sauraro.


Umaymah kuwa tunda ta fito, sai ta nufi sashin Hajia Mama, hira sukayi sosai cikin shaƙuwa irin ta yan uwa.

Suna zaune a nan Abba ya shigo.
Tana ganinshi tai murmushi,
shima murmushin yayi tare da cewa.
"Maman yara".
Cikin sakin fuska tace.
"Na'am Yaya".
Murmushi mai cike da zafi da ƙuna wanda ya baiyana har kan fuskarshi yayi kana ya zauna gefenta.
Gaisawa sukayi cikin danne ababen dake cin ransu.
Hajia Mama kuwa, tuni sai hawaye take zubdawa.
A hankali Umaymah ta miƙa mata handkin dake hannunta alamun ta share hawayenta.

Bayan ta share hawayenta ne,
Abba ya miƙa tare da cewa.
"Kin gaisa da Mom Imran kuwa? Da Salma".
Fuska a ɗan haɗe tace.
"A a".
Miƙewa yayi tare da cewa.
"To muje ku gaisa."

Binshi tayi a baya suka nufi inda yace ɗin.

A falo suka samu Mom Imaran tana ganin.
Sun shigo tare da Hajia Mama tayi wani irin haɗe fuska, cikin nuna ko in kula tacewa Umaymah.
"Yaushe kikazo?".
A daƙile tace.
"Jiya".
Kanta ta ɗan kauda tare da cewa.
"Ya hanya".
Alhamdulillah tace a taƙaice.
Cikin kufula Hajia Mama tace.
"Mu tafi".
Miƙewa Umaymah tayi kana Abba ma ya miƙa sashin Amaryarshi Salma ya nufa da ita.

Suna shiga tana jin muryarshi ta fito, da sauri ta nufe shi da nufin zata ruggumeshi da sauri yace.
"Ga Umaymah tazo".
A take taja birki ta tsaya cikin gyatsine tace.
"Ya kike kinzo lfy, ki gaida mutan gida".
Cikin wani irin kallo Umaymah tace.
"Uhummmm kema ki gaida mutan gidanku".
Tana faɗin haka ta juya ta tafi abinta.

Hajia Mama na biye da ita.
Ita kuwa Salma tana ganin fitansu ta ruggume mijinta.

Koda suka koma Side ɗin Hajia Mama bata daɗe a nanba ta nufi sashin Gimbiya Aminatu.

To bata fito nan ɗinba sai shabiyu saura.
Koda ta dawo Haroon da Jakadiyarsu da Aunty Juwairiyya kawai ta samu a falon.
Sai kuma Jalal da Hibba da suke dinning area suna zaune bisa kujerun Dinning table ɗin.
Sun sa plet a tsakiyarsu da kofunan tea a hannunsu, alamun sai yanzu sukeyin breakfast.

Cikin kula Aunty Juwairiyya tacewa Ƙanwar mahaifinta ɗin.
"Umaymah muje kuci abinci rana tayi fa".
Murmushi tayi tare da son danne ɓacin ranta tace.
"Alhamdulillah Juwairiyya Ni kuma da nakeda Hajia Mama ga Gimbiya Aminatu, ai naci nayi nak."
Cikin sauri Jakadiyarsu ta e.
"Ga kuma Matar Barrister Kamal ma ta aiko miki abin kari.
Gimbiya Saudatu ma ta aiko miki".
Murmushi tayi tare da cewa.
"A ajiye minshi sai anjima, kinga Juwairiyya kada ki shiga kitchen yau kizo mu wuni hira abinmu, abinci tako ina zaizo".
Cikin sanyi Juwairiyya tace.
"Uhummm Umaymah ke har zaki iya cin abinci waɗanan mutane ai Gimbiya Saudatu ba abin wuya bane tasa mana guba muci duk mu mutu.
Sai dai muci na gidan Barrister".
Kai Jakadiyarsu ta jinjina alamun eh.

Cikin ɗan ɗaga murya Umaymah tace.
"Haroon!."
Da sauri ya amsa tare da tahowa inda take.
Gefenta ya zauna tare da cewa.
"Umaymah gani".
Ba tare da ta kalleshiba tace.
"Ina Jazlaan?".
Ajiyan zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Y shiga Garden".
Kai ta ɗan jinjina mishi tare da zubawa Jalal ido.
Ita Hibba sai murmushi takeyi shi kuma fuskarshi kamar boss.

A hankali ta miƙa ta nufi falon Jabeer ɗin.

Da sauri ta kalli Haroon tare da cewa.
"Ina zakaje".
Baki ya ɗan tura tare da cewa.
"Umaymah inda zakije mana".
Cikin tsokana tace
"Sirri zanyi da ɗan".
Tana faɗin haka ta juya ta nufi can. Shima Haroon yana biye da ita a baya.

A hankali take taku har ta isa inda yake.
Gefenshi ta zauna tare da zuba mishi ido.
Cikin kula tace.
"Jazlaan".
Cikim nitsuwa ya buɗe idonshi tare da kallon inda tarin tsuntsayen nan suke,
Lokaci ɗaya idanunshi suka kaɗa sukayi jazir.
lips ɗinshi ya fara motsawa da nufin yin mgna amman ya gagara,
sai wani irin kuka mai ƙarfi da yake son ƙawance mishi daga can ƙasan zuciyarsa.
Hakan yasa lips ɗinshi karkarwa tamkar mai jin sanyi.
Umaymah kuwa. Tuni hawaye sun wonke mata fuskarta tana mai kallon tsuntsayen.

Ganin Haroon yasa tayi mishi alamun ya kawo mata ruwa.
Ba musu ya juya ba tare da yayi mgn ba jim kaɗan ya dawo da goran ruwa da glass cup. Ruwan ya tsiyaya a kofin ya miƙa Umaymah.
Cikin sanyin murya tace.
"Ga ruwan sanyi kasha, nasan zakaji sanyin ƙunan da kakeji a ranka".
Ta ƙare shi mgnar tana miƙa mishi cup ɗin.
Amsa yayi yayinda gaba ɗaya jikinshi karkarwa yakeyi alamun tsananin tarin baƙin ciki duniya.

Da kyar ya iya shan rabin kofin.
Nan ta gyara zamanta tare da kamo hannunshi ta fara tausar zuciyarshi kan abinda tasan shine babban matsalarshi.

A garin Bani kuwa zuwa yanzu hankali ƙabilar ɓachama yayi matsifar tashi, tsoro mai tsanani ya rufesu.
Tsoron da yasa da yawansu suka rinƙa guduwa suna koma cikin babban birnin Ɓadamaya,
Wasu kuma su tafi wasu jihohin.
Sabida sun gama tsinkewa da goron gaiyata da fulani keta raɓawa babu dare babu rana birni da ƙauye duk inda suka san fulani na nan sai da suka aika musu goro
Wannan ne yasa mafiya yawan kafuran aran na kare.

Inda hakan ya fusata Habban Ɓacama.
Har ta kaishi ga cewa, duk ba ɓacamen da yasan tsoron fulanine ya sashi guduwa to kada ya kuskura ya sake dawo mishi garinshi garin Shikan.
To wannan abun shiyasa wasu suka fasa guduwa, wasu da basuyi nisaba suka dawo.

To kuma kwatsam sai gashi yau an aiko an karɓin sandar sarautar Shikan dake hannunshi
Wannan abun yasa da yawa mutanen cikin Shikan Maza da mata hausa fulani da Ɓacamawa da sauran ƙabilu suka kuma rinƙa fecewa sabida, suna ganin yanzu dai shi kanshi Sarki Shikan bashi da madafa bashi da ƙarfi tunda an karɓe sandar sarautar shi.

To hakane yasa, ya rinka bin ƙauyuka Especially mutanen Bonon da kewaye ya rinƙa zugasu da ingiza su cewa, nanfa garinsu ne ya zasuyi su gudu kan Fulani.
Kuma ma suda sukeda dodon tsafinsu Bonon ai shi kadai ya ishi fulanin.
Da haka yasa duk ƙabilun Ɓacamawa na ƙauyukan basu guduba.
Sunata shirin faɗa yayinda cikin garin Shikan kuma yayi shal ko ina shiru babu mutane.


Cikin garin Bani kuwa, iya tsoronsu da suka gani a cikin kafuran ya sasu jin daɗi tunda gashi har suna guduwa subar garin da suke musu gadara da gori a kanshi da cika bakin sai sun kori Fulani a garuruwansu.
To tabbas sunada nasara akan fansar da zasu ɗauka, zasu ramane dan nemawa kansu enci.
Sun san iya sau ɗaya in sun nunawa arnatakun nan zasu iya gwabzawa dasu zasu barsu su sarara.

Haka yasa suke jin ƙarfin guiwar yin abun.

Ba'ana kuwa yanata ƙara shirya kanshi, sabida ramuwar gasar da za'ayi.

Ya Salmanu kuwa yanzu ya fara jajir cewa, yana fakewa da jarumtar Jabeer yana gasawa Ba'ana maganganu.

Sosai ya ƙara shigewa Shatu a mako ɗayan nan.
Kuma tana jin daɗin hakan.
Ta sake sosai.
Zuwa yanzu kuma jikin Ummey yayi sauƙi garawau sai dai har yau bata taɓa yin mgna ba ta zama tamkar kurma.

Da dare bayan sallan isha'i,
tana zsune ita da ya Salmanu suna hira cikin nitsuwa tace.
"Ya Salmanu gobene zamuje asibiti mu dubo su Junaidu da sauran marasa lfy dake cikin Genaral Hospital Ɓadawaya, dan naji ƙishin-kishin ɗin wai har yanzu babu likitan daya dubasu."
Cikin gamsuwa da hakan yace.
"Eh hakan yana da kyau, kuje in sha Allah muma jibi asabar zamuyi gamgami muje, danma goben jumma'a ne da munje tare".
Sai kuma ya ɗan kalleta tare da cewa.
"Da yaushe zakuje?".
Cikin sanyi tace.
"Da safe zamuje, in anyi sallan azahar zan dawo, amman Rafi'a zata wuce makaranta".
yace.
"To ke sai yaushe zaki koma?".
"Sai Ummey ta ɗan ƙara samun sauƙi. Ni da na so mu kaita asibiti kan batun rashin mgnar tata.
Gyara zaman shi yayi tare da cewa.
"Wannan ba matsala bace, wlh firgici da tsoro ne yasata hakan".
Haka dai sukaci gaba da hirarsu.

Washe gari ranar jumma'a, misalin karfe sha biyu dai-dai suka fito zasu tafi asibitin.

A bakin lambun garinsu sukayi kiciɓis da Ba'ana nan ya tsaidata dole suka zauna.


A can cikin masarautar Joɗa kuwa,
Lamiɗo, Galadima, Sarkin Shaɗi, da Jabeer ne tafe a hankali suka shiga cikin Garden ɗin nan.
Ta gefen Lamiɗo, suna shiga suka nufi inda katon curin dake wurin shekara da shekaru.
Shi dai Jabeer binsu yakeyi baiyi magana ba,
Koda suka isa wurin zama sukayi dabas a ƙasa.
Dole shima ya zauna, cikin sanyi Lamiɗo yace.
"Assalamu alaikum Jaimi".
Da mamaki Jabeer ya kalleshi,
Hiraminshi ya gyara tare da cewa.
"To yau kuma".
Da sauri Galadima yasa hannunshi ya rufe mishi bakinshi.
Hannunshi yasa ya janye hannun Galadima tare da cewa.
"Yo ai ba sai ka rufe min bakiba, in kace nayi shiruma zanyi, sai dai ina naga abin saɓon Allah ko tsireni za'ayi sai na faɗa".
Dafe kai Galadima yayi tare da tsuke fuskarsa.
Ganin haka ya taɓe baki tare da ɗaga kafaɗunshi ya ɗan buɗasu alamar, ban damuba.

Sarkin Shaɗi kuwa bai kallesu bama.

Wani irin zabura Jabeer yayi cikin tsananin firgici da kaɗuwa lokacin da yaga wani irin h ....!






By
*GARKUWAR FULANI*Ganin wani irin hayaƙi fari tas yana fitowa, tako wacce ƙofa na jikin curin.
Da sauri Galadima yasa hannunshi ya kamo hannun Jabeer yaja da ƙarfi.
Alamun ya nitsu ya zauna, cikin mamaki ya zubawa tarin hayaƙin dake bulbulowa daga ƙofofin ramin shirgegen curin.
Su kuwa ga ɗayansu hankali konce suke zaune.
Ido ya zuba musu tare da cewa.
"Me hakan?".
Da sauri Lamiɗo ya girgiza mishi kai hakanne ya sashi jan gajeren tsaki tare da cewa.
"Nifa ba son wannan soki burusun naku da surkunlenku nakeyi ba. Me gamina da ku da tsare-tsaren naku. Fisabilillahi me wannan?".
Cikin faɗa Lamiɗo ya sa hannu zai bugi bakinshi da sauri ya kauce.
Cikin hatsala Lamiɗo yace.
"Wannan bakin naka da baya mutuwa, komai sai kayi inkarin a kai tabbas sai na kashe bakin nan".
Wani kallo yayi mishi tare da cewa.
"Uhumm ai babu mai kashe bakin Muhammad Jabeer sai Allah".
Ganin zaija suma suyi surutune ya sasu kauda idonsu kanshi.

Bayan kusan mitinu goma, sai ga hayaƙin nan ya bar fitowa,
Sai wani irin huci.
Da sauri Jabeer yace.
"Nifa zan tafi, inma kun mance in tuna muku yau jumma'a ace, inada abinda yafi wannan abun naku mahimmanci a rayuwata ta duniya da ƙiyama, yanzu gashi har kusan sha biyu."
Murmushi sukayi baki ɗayansu ba tare da sunce mishi komaiba.
Sabida dama sun san za'ayi haka kam.
Sabida kowa ya sani shi Jabeer yana barranta da duk irin waɗannan ababen gado na sarauta shiyasa sarautar kanta shi bata ɗaɗashi da ƙasa ba.

Da sauri ya buɗe siraran idanunshi da kyau.
Sabida ganin wani irin ƙaton maciji ya sako kanshi cikin babban ramin da yafi girma.

Da sauri yace.
"Innalillahi wa innailaihi rajiun!."
Sai kuma ya zubawa maciyar nan idanu.
Tana fitowa cikin ramin ta, zuɗuɗuɗuɗuɗu. Haka yake zaro jikinshi.
Haƙiƙa dole duk wanda bai taɓa ganin macijinba bai kuma san da zamanshi ba, dole ya razana.
Dan ma shi zuciyarshi na cike da tsoron Allah so irin wadannan ababen ba kasafai suke firgitashiba.
tashinsa fahimtar ko wani ɗan abin sihirin za'ayi mishi ne.
Wani dagon numfashi yaja mai ƙarfi ya sauƙe ganin. Yadda macijiyarna taketa keta fitowa taƙi ƙarewa.
Su dai su Lamiɗo shiru sukayi a zaune.
Saida ta gama fitowane, ya rage iya bindinta sai gashi ta fito bindinta na kananmaɗe da wasu irin kitsastsun bulalin da ka gansu kasan tsoffine.
A hankali ya turo bindinshi gaban Lamiɗo,
Ya ajiyesu, sai kuma ya sumkuyo da kanshi ya zaro harshensa ya rinƙa lasar bulalin nan saida suka fito ras kamar an wonkesu.
Kana ta juya ta nufi cikin curin zuɗuɗuɗuɗuɗu ta koma,
Kamar forko sai ga hayaƙin.

Wani nannauyan numfashi Jabeer ya sauƙe tare da cewa.
"Uhum inda ranka kasha kallo. Oh ni Muhammad Jabeer an ɗauramin jakar tsaba za'a jazamin kaji su bini su tsastsageni.
Du wai wadannan abubuwan na menene wai dan Allah".
Ya ƙarishe mgnar yana kallonsu baki ɗayansu,
fuskarshi cike da alamun fargaban gudun saɓawa ubamgijinshi.

Su kuwa saida hayaƙin ya gama ɓacewa baki ɗaya sannan Lamiɗo ya fara miƙewa kana suma duk suka miƙa.
Sarkin Shaɗi ruggume da bulalin.


Juyawa sukayi zasu nufi hanyar da zata ɓullo ta falon Lamiɗo,
da sauri ya ɗan motsosu tare da cewa.
"Dan Allah shi wannan abun me amfanin zamanshi a nan? Wurinda Kum san duk baƙin da suke zuwa tako wani sashi na duniya ganin abin tarihin masarautar Joɗa muna kawosu nan.
Yanzu in wata ran yunwa ta koroshi ya fito ya cutar da mutane fa me zakuce?".
Cikin ƙosawa da mgnar Galadima ya gyara riƙon da yayiwa sandarsa cikin sanyi yace.
"Bata tare da yunwa, macijiyar da duk wata sai an ajiye mata motar ƙwai a cikashi da kiret-kiret na ƙwai shine abincinsa".
Da sauri Galadima ya nufi hanyar fita.
Lamiɗo kuwa tuni sun tafi.


Ganin sun tafi sun barshi a nan a tsayene. Yasashi sauƙe numfashin tare da juyawa ya nufi, ƙofar da zata sadashi da falonshi.

A hankali yake taku, cikin kasala da mutuwar jiki, da mgnar zuci.
"Wai ya zanyine? Wanna wacce irinyar masifeffiyar rayuwace? Yaushe zamu samu Allah ya gama tsarkake mana wannan masarautar Joɗa ya rabata da wadannan tsarabe-tsaraben gargaji.
Wannan wacce iriyar fitinace?".
Dogon numfashi yaja lokacin da ya shigo falonshi,
babu kowa, can babban falo ma babu kowa bisa dukkan alamu duk sunje shirin sallan jumma'a ne.

A hankali ya kutsa kai cikin bedroom ɗin shi.
Kai tsaye bathroom ya wuce.
Jallabiyar jikinshi da hirami da vest ɗin ya cire,
Cillasu yayi cikin injin wonki.
A hankali yake taku kanshi a sunkuye dagashi sai boxes Sky blue.
A hankali ya shiga cikin wurin wonkan.
Kamar yadda ya saba haka yayi wonkan jumma'a anshi.

Bayan ya fitone ya nufi drower'n glass ɗin dake cikin bathroom ɗin.
Wani tattausan Baby towel ya ɗauka bisa saman kafaɗunshi ya ɗauri ya fara gogewa, yana tsane ruwan jikinshi.
Kana a hankali ya ɗauki wanni babban towel ɗin ya ɗaura daga saman ƙirjinshi.
Wanda ya sauƙo har guiwa shi, a hankali yasa hannun ta ciki ya fara murza boxes ɗin yayi ƙasa, dashi yana zuwa sharabanshi ya riƙe shi ya zare ƙafa ɗaya, kana ya zare ɗayar ma.
Lallaɓeshi yayi ya matse kana ya shanyashi kan ƙarfin silver da yake na shanya.
Farar jallabiya ya zura a jikinshi, kana ya kwance towel ɗin. Dashi ya goge suman kanshi.

Cikin hamzari ya fito bedroom,
Kai tsaye gaban dreesing mirror ya nufa, mai ya shafa a dukkan sashin jikinshi. Kana ya taje tattausan suman kanshi tare da shafa mishi manshi, wani Duaol jannah mai masifar daɗi ya shafawa jikinsa, kana ya ɗauki wani ƙaramin kum ya tace tattausan sajenshi ya kontar dashi lib-lib hakama gemunshi.

Saida ya gama komai na gaban Mirror kana ya nufi babban drower'nshi da sauri-sauri yakeyin komai.
Wani tattausan jallabiya mai masifar kyau da taushi fari ƙal ya zaro.
Kana ya ɗan yi sama da kanshi ya kalli cikin tsep ɗin ƙarshe na drower'n inda al'kyabbanshi suke jere a kimtse tamkar shagon saidasu.
Hannu yasa ya zaro wata sabuwa dal tana cikin ledanta tana haɗe da hiramin ta da komai.
Rufe wannan wurin yayi kana, ya buɗe wani sashin inda ƙananan kayan shi ke jere, boxes and singlet ya zaro farara ƙal suma sabbi ne.
Da sauri ya rufe drower'n kana yazo ya ajiyesu bakin gadonshi.
Ba tare da ya cire jallabiyar jikinshi ba, ya saka boxes ɗinshi saida ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi da kyau ya kimtsa komai nashi yadda zaiji daɗi tafiya, kana ya zare jallabiyar ya ajiyeta bakin gadon
Singlet ɗin ya yasa, sannan ya ɗauki farar tattausar jallabiya mai dogon hannun ya saka, jallabiyar daya cire ya ɗauka ya gaban ƙaton drower'n nashi ya nufa, wani side ɗin ya buɗe nan ya saƙalata.
Kana ya dawo bakin gadon.
Ledan al'kyabbar ya farka da ƙarfi da kuma sauri sabida ganin tuni ƙarfe ɗaya da rabi tayi, yasan yanzu masallacin ya cika maƙil da mutane.
Ɗan gajeren tsaki yaja, tare da ci gaba da warware al'kyabbar.
Yana gamawa ya zurata a jikinshi, al'kyabbar baƙace, sai gefen bakinta da akayiwa kolliya da wani zare mai masifar kyau Golding color irin mai sheƙi da ɗaukar ido, hakama, kan kafaɗunsa har zuwa hannunta anja zirin irin wannan kolliyar.
da sauri ya dai-dai-ta zamanta a jikinshi, kana
Ya juya ya nufi, gaban dreesing mirror da hiraminshi a hannunshi,
Yana isa ya ajiye baƙin abin, kana ya ware farin hiramin shima da kolliyar Golding color a jikinshi, ya ninkeshi kamar yadda muke ninke dankwali, bayan ya gama ne.
Ya ɗaurashi a kanshi ya dai-dai-ta zamanshi kana, ya ɗauki baƙin abin wanda shima an zagayeshi da Golding color ya sakashi a akanshi, ya fito ras tamkar a Saudia.
Allah ya sani yana masifar son wannan shigar da jin daɗinta a jikinshi babu takura babu matsi gashi ka suturtu da kyau mayu masu kallon tsiya irinsu Jazrahda Batool duk basa iya ganin komai a jikinshi ba.

Da sauri ya nufi wurin aje takalma shi wanda yake na glass ne marfin ya buɗe kana, ya ɗauki wasu takalma irin nasu na sarauta Golding color ne kuma half cover ne, zura jajayen sawunshi yayi a ciki, kana ya koma gaban mirror, wani kolba turaren OudKareem mai masifar ƙamshi mai sanyi, ya fesa a duk sashin jikinsa.
Kana yasa hannunshi ya ɗauki carbinshi. Farin galashi ɗan siriri ya manna a idonshi.
Kana ya juyo da sauri zai fita, sai kuma ya tsaya cike da mamakin ganin. Haroon tsaye ya zuba mishi ido.
Ya buɗi baki zaiyi faɗa sai kuma yayi shiru jin Haroon na cewa.
"Kada kace zakayi faɗa Lamiɗo ne yace inzo in kiraka, lokaci na tafiya fa."
Bai kulashi ba kawai yayi gaba, da sauri Haroon ya bishi tare da cewa.
"Wannan baza ƙamshi haka sai kace wurin amarya zakaje, gsky kayi kyau sosai masha Allah".
Bai kula Haroon ba sabida addu'o'in da yakeyi.
Amman duk da haka saida ya bawa Haroon amsa a zuciyarshi, yake cewa.
"Akwai wani wuri da yafi cancanta da ɗan adam yayi shiga ta tsabta da kyan shiga da ƙamshi sama da masallacin ne? Innal masajida lillafa, duk duniya da babu wurin da Allah ya keɓanta yace dakinshine sai masallatai. Nan zamu gana dashi. Domin idan mu bama ganinshi ai shi yana ganin mu".
Murmushi Haroon yayi, dan Jabeer bai san mgnar da yakeyi a zuci ta fito filiba.

A haka dai suka shiga Masallaci.

Dole yau a gaggauce yayi Kudbar jumma'a dududu 15 minutes yayi yana kudbar kan halaccin mace

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment