Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki yasa hannu ya jawo hannun Giɗaɗo daya kifa kanshi jikin babanshi.
Cikin fillanci yace.
"Zo Giɗaɗo zomu tafi".
Da sauri ya miƙa hannunshi ya kama na Buba kana suka juya suka fita.

Appa kuwa kanshi ya kauda daga kallon wannan kekyawar halittar dake gabanshi a cikin ransa yace.
"Anya kuwa, wannan mutunce ba iskaba".
Inna kuwa gefe ta ɗan matsa cikin rawan murya na tsoro da hausar da sai ka dage zaka gane me take cewa tace.
"Ra ga Allah bewar Allah mutun ko al'jan?".
Ido suka tsurawa matar a zatonsu ko zata basu amsa.
Sai dai ganin yanayin da take cikine ya sasu cire tsammanin samun amsarta.

Domin gaba ɗaya jikinta karkarwa yakeyi, tamkar mazari.
Kana sai zufa dake tsastsafo mata tako wani hudan gashin jikinta,
ta rumtse idanunta da azaban ƙarfi, tasa haƙoranta ta datse lip ɗinta na ƙasa,
duk mace data taɓa haihuwa in ta ganta tasan naƙudace ke azazzabarta.

Tausayin ta ne ya cika zuƙa tansu baki ɗaya.

Arɗo Babayo ne yayi ɗan gyaran murya tare da kauda kanshi daga kallonta sabida kwarjininta yafi ƙarfin ƙwayar idanunsu cikin sanyi murya yace.
"Allahu wahidun ƙahhar, Mutunce ba al'jana bace, Allah shi ya barwa kansa sanin dalilin kasan ce warta a cikin tsuffofin tsuntsaye, amman kam tabbas al'amarine mai tarin girma da sarƙaƙiya, Tine taimaka mata, da zuciya ɗaya ina ji a jikina ba mai cutarwa bace. Kuma akwai tabbaci da kekyawan zaton musulmace".

Ido ta zubawa mijin nata da yake bata ƙarfin guiwa.
Appa ne ya kalleta tare da gyaɗa mata kai, alamun eh ta taimaketa,
Ita kuwa Parvina cikin tausayawa da zubda hawaye tace.
"Appa kalli hannunta ya kumbura gashi jikinta zafi Appa a taimaka mata".
Hannu ya miƙo ya kama Parvina cikin tausayawa yace.
"Zo nan Parvina za'a taimaka mata kinga bata da lfy tashi a jikinta,
kinga ki dena danne mata hannun da cikinta".
kai ta gyaɗa kana ta kalli matar cikin sanyi tace.
"Sannu!". Bata basu amsa bata kulasu bata kuma hafimtar komai daga garesu,
haka yasa su Arɗo Babayo juyawa suka fita, ita kuwa Inna matsowa gareta tayi cikin tarin ƙarfin guiwa irin na fulani. Fulaninma irinsu na daji ba irin wasunku na birniba.
cikin sanyi tace.
"Taso muje daga ciki".
ido ta zubawa Inna cikin yanayin wahalar da takeji,
hannu Inna tasa ta kamo hannunta mai lafiyar, ta miƙar da ita tsaye.
Allah da ikonshi, sai gata a tsaye cas.
Haka yasa Inna ta jata suka koma cikin gida, cikin ɗakinta ta kaita,
a bakin katifar da suka kwana ta ajiyeta,
da sauri ta koma woje wuta ta hura ta ɗaura ruwan zafi.

Kana ta dawo ciki.
Cikin mamaki take kallonta ganin taja ta jingina da jikin gini kana, ta rumtse idanunta ga hawaye nata kwaranya daga idanunta.
Gefenta ta zauna ta zuba mata ido.
Jin an zauna gefen tanne yasa ta buɗe kekyawan idanunta, cikin kula Inna tace.
"Sannu baiwar Allah, kamar naƙuda kikeji ko?".
Kai ta gyaɗa mata alamar eh naƙudar takeji,
murmushi inna tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah naji sanyi na ƙara gamsuwa ke mutunce, kuma kina gane me nake faɗa a yanzu, to amman kiyi magana mana".
Kanta ta jujjuya mata alamun.
"Bazan iyaba".
Jin muryarsu Arɗo Babayo ne yasa inna tayi maza ta fito,
Ganin Arɗo Babayo da Appa da kuma Malam Liman da sarkin bakansu wanda yake rugar makotansu ne yasata saurin fitowa tare da cewa.
"Sannun ku da zuwa Malam Liman, Baka barka da zuwa".
Taburma ta shimfaɗa musu, jin muryar Malam Liman ne na cewa.
"A a bar taburmarnan ina baƙuwar tamu?".
"Tana cikin ɗaki, da alamun tana fama da yanayin naƙuda ne".
Inna ta faɗa cikin alhini.

Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
"Ina son ganinta".
Arɗo Babayo ne yace.
"To bisimilla, shigo daga ciki".
Ɗakin suka nufa Inna na gaba Arɗo Babayo na biye da ita a baya, kana Appa da Malam Liman da Sarkin Baka suka rufa musu baya.

Suna shiga suka sameta zaune ta haɗe jikinta wuri ɗaya,
jin motsin shigowar mutanene yasa ta ɗago kanta,
da sauri ta kauda idanunta.
Shi kuwa SARKIN Bakan, kanshi ya rinƙa jinjina wa cikin al'hini yake cewa.
"Mutun ce ba al'janba, baiwar Allah an tozarta rayuwarki."
Sai kuma ya kalli Arɗo Babayo cikin sauri yace.
"Maza a bani madarar shanu mai ɗumi wanda aka tatsa yanzu".

To Arɗo Babayo yace tare da juyawa ya fita, a harabar gida yayi arba da Gainako da yake shigowa da kwaryar nono,
da sauri ya iso, kana yasa ƙaramar kwarya ya kamfati madarar shanun daketa tururi sannan ya juya ya koma cikin ɗakin.

Yana zuwa ya miƙawa sarkin Bakan,
yana amsar ƙoryar,
ya ajiyeta a gabanshi jakar fatar ruƙimi da yakesa magungunanshi a cikine ya sauƙe daga kafaɗarshi, kana a hankali ya fara harhaɗa magunguna a cikin madarar,
saida yasa komai sannan ya kalli Inna yace.
"A bani zuma da zam-zam".
Da sauri tace.
"To". Kana ta miƙo ta ɗauko mishi, koda ta kawo da sauri yasa zumar da zam-zam ɗin ya gaureyasu,'.
Kana ya bawa Malam Liman da Arɗo Babayo sukayi mata tofin ayatul shifa, a ciki, kana ya amshi kwaryar.
Inna ya miƙawa kwaryar yace.
"Gashi bata tasha".
Amsa tayi kana ta matso kusa da matar a hankali tasa mata bakin kwaryar a bakinta.
Tare da cewa. "Bismillah ki Sha".
A hankali ta buɗe bakinta, ta fara shan madarar shanun nan da magungunan, masu haɗe da zam-zam da zuma da kuma rahamar ayatul shifa.
Saida ta sha mai yawa sannan ta kauda kanta.

Ae fa a take saiga naƙuda ta tashi gadan-gadan. Ganin haka yasa su Arɗo kab suka fito woje ya rage daga ita sai Inna.

Ganin haka yasa Malam Liman tura Ori da yanzu ya shigo yaje ya kira matarsa ta taimakawa inna su amshi haihuwar.

Ba jimawa kuwa Iya laure tazo, kai tsaye cikin ɗakin ta wuce.

Cikin ikon Allah a take a sauƙaƙe Allah ya sauƙeta lfya, ta haifi yarta mace ƴar ƙanƙanuwa.

Bayan sun yanke cibiya sun gyara,
komai na wurin.
Kana Inna ta taimaka mata tayi wonka,
ita kuwa iya laure wonka tayiwa jaririyar ta haɗeta cikin zanin Inna ta bawa Parvina daketa tsalle.

Koda suka fito daga wonka,
konciya tayi a kan katifar, kana iya laure ta kontar mata da ƴar a gabanta.

Ajiyan zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana a hankali ta lumshe idonta, tana son ta tuno wani abu na rayuwarta ta baya amman ina ta kasa tunowa,
Abu ɗaya takeji bata manceba sunan Allah wanda tunda ta dawo mutun taketa maimaita kiranshi a zuciyarta dan taji bakinta bazata iya magana ba, amman a ranta tanaji tana bitar karatun al'ƙur'ani mai girma da tarin addu'o'in kamar yadda takeyi tun tana a tsunstsuwar ma.


Ganin tayi shiru ne kamar maiyin bacci yasa inna da iya laure suka fito woje.
Sashin Arɗo Babayo suka nufa,
suna shiga sukayiwa juna barkar haihuwarta lfy.
Shiru sukayi baki ɗayansu bayan duk sun zauna kamar yadda Sarkin Baka ya umarcesu, gyaran murya yayi kana a hankali ya fara magana.
"To da forko dai sai dai muce. Alhamdulillah, mun godewa da yasa sanadinmu wata baiwar Allah zata samu waraka daga mugun cuta na magauta maƙiya azzalumai marasa tsoron Allah".
Kai suka jinjina alamun gamsuwa, shi kuwa tonkoshe ƙafa yayi kana yaci gaba da cewa.
"Kamar yadda kuka gani a yanzu mutunce bani adam ce ba tsunstsuwa bace kamar yadda kuka gani da zata a baya, aikin sihirine kawai ya maidata haka.
Amman Alhamdulillah tunda gashi yanzu Allah yayi ikonshi ya karya abun da akayi mata ya kuma sauketa lfy dama shi asiri tasirinshi kaɗanne ga wanda yayi imani da Allah kuma dole gsky zatayi halinta watan-watarana".
Arɗo Babayo ne yace.
"Allah mai iko, mutun a maidashi tsuntsuwar Boleru kai abinnan da al'ajabi".
Kai ya gyaɗa mishi tare da cewa.
"Ɗan Adam kenan mai wuyar gane hali babu mai sanin halin mutum sai Allah, domin shi ɗan adam dare".
Sai ya kuma kalli Inna tare da cewa.
"Yanzu tayi magana ne?".
Da sauri Inna tace.
"A a batayi mgna ba sai dai in anyi magana tanaji kuma tana ganewa".
Kai ya rausayar tare da cewa.
"Zatayi magana in sha Allah, yanzu aci gaba da kula da ita yadda ya dace zan bata magunguna kuma,
sannan kada kuji tsoronta ko kaɗan in sha Allah ba mai cutarwa bace".
Malam Liman ne ya gyara babbar rigarshi tare da cewa.
"To wannan baiwar Allah'n ko daga ina ta fito? Ko ta yaya zamu gano yan uwanta danginta ahlinta ko wani nata a duniya?".
Sarkin bakanne yayi ɗan gyaran murya kana yace.
"In sha Allah ita in ta dawo haiyacinta, zatayi mana bayanin komai zata faɗa mana sunanta sunan garinsu sunan iyayenta sunan mijinta da anguwarsu sai mu mikata garesu".
Appa ne ya ɗanyi ajiyan zuciya tare da cewa.
"Allah ya bata lfy ya kuma dawo da ita cikin haiyacinta, kuma in sha Allah duk wani abu daya kamata ayimata a duniya zan mata har sai munga ta samu' lafiya ta koma ga iyayenta".

Da haka sukayi ta tattauna duk abinda ya dace ayi mata.
Anan kuma sarkin baka yaje da kanshi ya ɗaure mata karayar hannunta yayinda Parvina kuwa ke like da ita...!

Haka Inna da iya laure sukayi ta kula da ita a cikin wannan satin sunan...!

************

...Bayan shekaru Goma sha biyu...

Cikin Ƙasar Kautal A Jihar Ɓadamaya state.

A wani yanki na Ɓadamaya state, cikin Shikan local Government area a wata rugar FULANI mai suna.
*RUGAR BANI*

Garin Shikan wani yankine daga yankunan Ɓadamaya yankine mai tarin ƙabilu ma banbanta addinai da al'adu wanda duk yankun Ɓadamaya shida Bimu sune sukafi tarin ƙabilun sai dai babbancin mafiya yawan kabilun Bimu musulmaine saɓanin mafiya yawan ƙabilun Shikan kafurine maƙiya Allah da Manzonsa.

Shikan shine sashin da yafi tara ƙabilu mafiya yawa, masu baƙaƙen zuciya ƙabulun da hasken addini bai cimmusuba.
Ƙabila mafi rinjaye a yankin Shikan itace ƙabilar ɓachama. Mafi akasari Ɓachamawa mutanene kafurai ne marasa ɗigon imani a zuƙatansu marasa son zaman lfya, mugunta da kisa shine abinda ke sasu farin ciki, abinda kawo ya sanine duk sanda akaji jihar Ɓadamaya cikin wani tashin hankali to daga ƙabilar ɓachama ne.

Duda yawan ƙabilu na garin Shikan hakan baisa fulani sun sakar musu garinba, domin tushen garin na fulanine, sabida kowa yasan makiyayi basa nesa da wurin damshi da ruwa, domin rayar da ababen kiwonsu.
Haka yasa akwai musulmai Hausawanmu da tarin yawa cikin garin Shikan, wanda duk rintsi da wahala sunƙi barin garin, koda yake hakan baya rasa nasaba da irin al'barkatu da ni'imomin da Allah yayiwa garin.

Daga gefen. Garin Shikan akwai babban kogin da yakeda ruwa biyu wanda ko wucewa zakayi ta kan babban gadan da titin da zai kaika cikin Ɓadamaya zaka hangi ruwane kala biyu a kogi ɗaya basu kuma taɓa haɗewa wuri ɗaya ba da izinin ubangiji.

Gefen kogin ta dama wata babbar *Rugar fulani mai suna Rugar Bani* ce mai tarin tarihi, rugace mai girma wacce Ubangiji ya ƙawatata da ababen buƙatar yau da kullum, wannan Ruga itace yanki mafi sanyi a yanki Ɓadamaya state rugace damu fulani muke ce musu *JOTTAN MA'EN* Bi ma'ana fuli mazauna wuri ɗaya, ba ire-iren fulani makiyaya masu tafiye-tafiye bin rugageba, fulanin Rugar Bani fulanine makiyaya masu tarin dabobi masu tarin yawa, Rugar Bani Rugace da aƙalla fulaninmu sunyi sama da shekaru dari da ashirin awannan Rugar, shiyasa harda gini zamani da kyawawan gidaje fulanin sukayi, yayinda kuma akwai bokkokinma a cikin Rugar tasu wanda kuma suka sayi filin da kuɗinsu zufansu a hannun sarkin Shikan na wancan zamanin ya sayar musu yankin wurin gaba ɗaya sun biya kuɗinsu ya kuma basu takardu su, suna zaune a nan suna noma suna kiwo.
Rugar Bani na zagaye da ƙauyukan ƙabilun Ɓachamawa da tarin yawa, wanda nan gefensu ƙauyen Bonon yake wanda nanne dodon tsafin ƙabilar ɓachamawan take wanda sunan dodon tsafin nasune suka sawa suna ƙauyen suna Bonon. Kauyen Bonon shine zuciya da karfin kafuran nan, sunyi imani dashi, fiye da zaton mai zato, koda laifi wani yayi bonon ake kaiwa ƙara kuma muddin bonon ya tsinewa mai laifinsun to zai lalace ya ɗai-ɗaice dashi da zuriyarsa baki ɗaya, da yake sunyi imani da hakan kuma yana faruwa suna gani shiyasa bonon yake tamkar zuƙatansu, kamar dai yadda in jikin ɗan adam idan zuciya ta ɓaci gagganji na ɓaci to haka bonon take a wurinsu... Wannan kenan

Rugar fulanin Bani yafi ko wani yanki na Ɓadamaya sanyi mai ɗan karen daɗi.
Koda yake hakan ya samune sanadin ƙawanya da wani babban dutse mai fesar da numfashin sanyi yayi musu, wanda ya kasance musu tamkar rufar garin.
Gefen hagun Rugar Bani kuwa wani babban fadama ne mai cike da lamɓu mai ɗauke da ababen more rayuwa wanda ya kasance mallakinmu Fulanin Rugar Bani, lambun yana da duk wasu kayan marmari kamarsu.
Lemu, mangoro, gwaiba, ayaba, dabino,kwakwa, kashu, kankana, abarba, da jefi-jefin tuppa da inabi.
Wanda wannan fili yake mallakin Fulanin Rugar Bini'nne, kana bayan filin kuma akwai wani rafin da ya kasance masarrafin noman shinkafawa ne wanda suke yinshi noman rani da damina, kuma shina mallakin Fulanin Rugar Bani ne, wanda komawa yasan iya filinshi,

Daga gaban Rugar Bani kuwa kogin Shikan ne malale a gabansu iya ganin mai hange da ido biyu gefen hagunsu kuwa nan garken shanunsu ke shimfiɗe bila adadin.

Rayuwar Fulanin wannan Rugar rayuwace mai cike da aminci da amana da hakuri da kauda kai duk da tarin zalunci da kafurai ƙabulun Ɓachamawa keyi musu.

"Kamar yadda duk kowa ya sani duk duniya anyi ittifaƙin ba fulatani ko ba fulatana basa neman tsokana ko tada husuma bare tada zaune tsaye. Akan cutar da bafulatani yayi kamar bai san an cutar dashi ba ko bai ganeba, wannan dalilin yasa duk ƙabilun ƙasar Afirka sukeyiwa ƙabilarmu kallon wawaye ne ko basu san abinda sukeyiba ko sokayene, masu ƙarancin wayewa Gidadawa.
Mu kuwa a namu sashin fulani mun kasance masu kauda ido kan cutarwar forko data biyu, sai dai a haƙiƙinin gsky bama lamunta ko jurar cutarwa ta uku! Domin rama cuta ga macuci ibadace. Kuma Ba'a sarar mumini a rami ɗaya sau uku".
Wannan shine jawabin da wani farin dottijon bafulatanin dake zaune tsakiyar al'ummar wannan rugar bayan sun dawo daga jana'izar mutun ɗaya da ƙabilun ɓachama suka kashe musu cikin sunkuru, a daren jiya wanda ya kasance ɗane ga Arɗon Yabani shugaban Rugar tasu kenan.
Hannu yasa ya share zafafan hawayenshi dake kwaranya daga ida nunshi cikin ɗaga sauti yaci gaba da cewa.
"Fulani basa ɗaukar mataki domin yaƙi ko zalumci sai dai dan kare kawunansu. Kuma kun sani duniya duk ta sani FULANI BA ƳAN TA'ADDA BANE! Ba ƴan bindiga daɗi bane, makiyayene masu ƙare rayuwarsu dan samawa mazauna cikin birane jin daɗin rayuwa, muyi kiwo mu kai musu suci naman susha madarar shanu kana muyi noma mu ciyar dasu.
Meyasa su mutanen birane basa ɗaukar matsalarmu tasu matsalar ana kashemu tamkar kiyashi kuma babu masu kulawa".
Tsagaitawa ya ɗanyi tare da shashsheƙa cikin bada umarni a matsayinsa na shugaban Rugar uban wanda aka kashe kuma yace.
"Na roƙeku da Allah kada wanda ya ɗauki makami domin ramuwa duk da munga yankan rago akayiwa Hashimu amman bamu san wayeba kuma bamu da hujja, dan haka kada wanda yace zai ɗauki makami.
Muyi rubutu mu aikawa maimartaba sarkin Ɓadamaya, domin Al'ƙalami yafi tokobi, mu kai kukanmu gareshi, tunda shi sarkin wannan yanki na Shikan mun kai mishi kukanmu a karo na barka tai bai kulaba, kuyi hakuri mu miƙa lamarinmu ga sarakuna mu, inada yaƙinin zasuyi mana adalci".
Shiru mutanen da aƙala sun kai ɗari da ashirin sukayi.
Yayinda kowa ya keta zubda hawaye.
Sai ɗaya daga cikine da ya kasance baƙin jakada Ɓachama ruwa biyu uwarshi ƙabilar ɓachama, wacce ubanshi bakura babarbaren borno wanda shike saida kanwa a rugartasu ya auro Uwar Ba'ana. yana naɗa komai a wayarshi,
domin miƙawa shugaban mayaƙan ƙabilar ɓachama, komai ya gani, domin shi ɗin ya kasance, makashinsu ne kuma taburmarsu ne, domin dama bahaushe yace sai da ɗan gari akanci gari da yaƙi!...


A cikin babban birnin Ɓadamaya kuwa. *Land of beauty* Garin Modibbo Joɗa,
Mai tutar fulɓe garinda duk arawacin ƙasar Kautal mune kaɗai muka rage da tutar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo.
Wanda ya dasashi ya kafashi da hannunshi masarautar fulbe mai ƙarfi Masarautar Joɗa...

Cikin birnin matsarautar Joɗa.

A cikin babban birnin Ɓadamaya.
Wasu irin tsala-tsalan motocine wanda a ƙalla sun kai Goma suke jere suna fitowa daga harabar shaharerriyar makarantar Jami'a ta dake cikin babban birnin Ɓadamaya wato J.U.B Joɗa University Ɓadamaya

Yayinda suke tafiya a jere a jere cikin tsananin gudu tamkar zasu tashi sama kana ga jiniya daya karaɗe illahirin sashin wurin wanda dole yaja hankali duk wanda ke wurin gudu sukeyi tamkar zasu tashi sama da titin.
Motoci huɗune a gaba, wanda suka kasance masu kyau.
Sai wata Rolls Royce, mai kuɗi kimanin naira million 4, 959,630. Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai sheƙi da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine ƙal sai glass ɗinta daya kasance tin tek mai duhu.
Wani kekyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine ƙal wanda da ka ganshi kasan tabbas bafulatani ne, kuma zaka gane ya haɗa jini da larabawa.
Wata iriyar shigace a jikinsa shiga mai ƙara daraja da kamala farin yadin Super Nour a jikinsa wanda a ƙalla zai kai tamanin ɗ kuɗinshi, ya ɗaura baƙar al'kebbarsa ta jinin larabawan saudia Al'kebbar baƙace mai faɗi, kana yasa farin hirami a kanshi da zagayen baƙin saman hiramin.
Fuskarshi nan ta fito ras sajenshi mai tsananin kyau yayi lib a fuskarshi sai sheƙi yakeyi, kana gashin girarsa ya komta lib a saman siraran idanunshi masu kyau da ɗaukar ido, wani irin tsabtaceccen gemune da bazai wuce kamu ɗaya ba ne yayi lib a haɓarsa.
Zaune yake cikin motar ya jingina bayanshi da sit ɗin, ya lumshe fararen idanunshi,
A hankali yake motsa tattausan jajayen laɓɓansa yana tasbihi.
"Subahanallahi wal'hamdulillah wa la'ilahaillah Allah Akbar, Astagafillaha wa'atubu ilaik".
Yanaji a jikinshi kudun da akeyi yayi yawa, to amman dolene ayi irin wannan gudun domin lokaci na gab da ƙurewa, dan sosai sallan jumma'ar ya gabato, yasan yanzu masallacin ya fara cika, wannan dalilin yasa bai hana drevernshi gudunba, kuma bai hana fadawanshi sakin jiniyarba, dan ta hanyar jiniyarce zaisa a basu hanya su samu su isa kan lokacin daya dace.
Bawai ya bari ayi jiniyar da gudun dan nuna isa da ɗagawa bane, sai dan son isa masallacin Masarautar Joɗa da yake limanci kuma yake gabatar da Hudubar jummar matuƙar yana ƙasar tiyatar da yayiwa watace ya sa lokaci yaso ƙure mishi.
Motoci, biyar kuma na bayanshi wanda uku daga ciki na ɗaliban J U B da ya fitone, wanda yana aiki cikin Hospital ɗin makarantar, bayan kuma asibitinshi da kuma Genaral Hospital Ɓadawaya da yake zuwa sau ɗaya cikin ko wanne sati.
motoci biyun bayanshin kuma, Jalal ne da abokanshi.
Shiyasa motocin suka taho a jere-a jere dan shi bai fiye yarda ya fita da mota sama da biyarba, suma ba kullum ba, wani lokacinma yakan fita shi ɗaya.

A haka dai har suka fara ratsowa cikin Ɓadamaya, a dai-dai mashigar laleko ne,
Cunkoson ababen hawan ya yawaita, yayinda suka danno kai wurin yasa da yawa suka fara komawa gefen titi suna kauce musu dan basu hanya dan jiniyar dake musu nunin akwai uzurin gaggawa ga kuma fadawa a motocin.

Wani mai keke Napep ne ya gangara gefen titi har kusa da wani mai saida su Oranges Banana da dai sauransu.
Dogon tsaki mai Napep ɗin yaja tare da cewa.
"Wannan ai mulkin mallaka ne da izza duk an tsaidamu sabida wani can zai wuce ai duk nan muma saurin mukeyi munada babban uzuri, saurin da duk mutanen wurin nan keyi duk an katse mana hamzarinmu na son isa masallaci kan lokaci muji huɗubar jumman wannan rana".
Mazan dake cike a bayan napep ɗin ne suka haɗa baki wurin cewa.
"Wallahi kuwa, gashi motocin nasu nada yawa.
zasu sa mu rasa jin hudubar wannan fasihin Malamin".
Wani mai motane dayake gefensu ya amshi zancen da cewa.
"Kuma gaba ɗaya mutanen nan wurin masalacin zasu tafi, sabida duk mai son jin huɗuba mai ratsa jiki da zuciya baya ƙaunar ko furuci ɗaya na wannan malamin ya wuce shi domin Allah ya rigada ya mishi baiwar lafazi mai shiga zuciya".

Wanda ke gefensu ne ya amshi zancen da cewa.
"Gaskiya ne wannan sabida shi Allah yayi mushi baiwar lafazi da iya tabsiri mai nusar da gafalelle".
Mai saida kayan yayan itatuwan dake gefen sunne yayi ɗan murmushi kana ya miƙawa ƴan matan daketa kallon motocin da ido, lemun da suka saya ya miƙa musu.
Kana ya kalli dan-dan zo matasa daketa wuce da kafa,
mutanen daketa maganar Malamin ya kalla tare da cewa.
"Eh kam gsky duk malaman ƙasar nan babu yashi a lafazi, cikin second ɗaya zai yi maka lafazin da zai gamsar da kai tsawon shekaru Talatin,
koda yake hakan baya rasa nasaba da tsatson mahaifiyarshi, da ta kasance balarabiya kuma alarabawanma a cikin ƙabilar da tafi dukkan ƙabilun duniya a baiwar lafazi da iya sarrafa harshe".
Cikin mamaki suka kalleshi,
Alhajin dake cikin zazzafar motar shin nanne yace.
"Haba sai haka mana ashe Balarabe ne wani yanki na tsatsonshi Allah yayi mishi rahamomi masu tarin yawa.
Gashi wannan zai hanamu muje muji Kuɗubar".
Murmushi mai Appul ɗin yayi tare da kallon gefen baya yadda ya hango dandazon motoci da keke Napep dama masu tafiya da sawu ma.
Wasu na meda motocinsu gefe sukayi suna fitowa da sallayoyinsu a hannu suna takowa da ƙafa,
kanshi ya ɗan rausayar ya kalli mutanen dake gaban nashi tare da cewa.
"Kasan su wayene a cikin motocin nan da kuketa zagin kuwa?".
Da sauri suka jujjuya kai tare da cewa.
"A a waye ne?".
Tsala-tsalan motocin ya zubawa idanu zazzafar farar mota kirar Rolls Royce ɗince ya zubawa ido a hankali ya maida kallonshi garesu tare da cewa.
"Shine Sheykh J....!



Uhummmm wasa farin girgi.



By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘

*GARKUWA*

PAGE 3

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

📝🍇🍇🍇🕊️🐄🌈🦚🐍🤴🏻💘


*FREE PAGE*



*LITTAFINA NA KUƊI NE. TURO 300 DOMIN samun damar KARANTASHI. Ko ki turo 1k domin shiga SP Group, inda zaku samu posting fiye da na 300. Ayyah Ƴan SPG bana son katin, turo dubu ɗayan ta asusuna na, 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo shaidar biyanki ta layina na 09097853276. Kuma masu 300 in dai kinada damar turawa ta ac tura,in kuma baki da dama to turo katin mtn na ɗari ukun ta layina na 09097853276, ba hoton katin zaki turoba, numbers ɗin zaki kofa ki turon*


```ALHAMDULILLAH MASU NEMAN TSOFFIN LITTATAFAINA, NA SAMESU GABA ƊAYA, SAI RIGAR KOWA NE BAN SAMUBA. IN KINASO KIZO DA KATIN MTN NA ƊARI UKU kacal IN BAKI DUK LITTAFIN ƊAYA DA KIKESO, A CINSU.ƳAR FULANI, MU'WASMITI, NAMIJI BAYA KAƊAN, A TAUSAYAWA JUNA, BANDIRAWO, RUBUTACCEN AL'AMARI, HUKUNCIN ALLAH, NAKASA BA KASAWA BACE, DA KUMA GARKUWA.```




"Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero Joɗa ne.
Doctor Jabeer Habibullah Nuruddeen Bubayero kenan. Ina nufin GARKUWAN FULANI".
Da mamaki a fuskokin su sukace.
"Astagafirullaha. Bawan Allah ashe sauri yake ya rigamu kada muje muyi ta jira".
Kai mutumin ya jinjina musu tare da nuna motoci biyu wanda Jalal da abokanshi ke ciki, wanda kiɗan dake tashi cikin motocin ya cika ko ina, a hankali yace.
"Wannan kuma Jalaluddin kenan ƙanin Sheykh Jabir Habibullah Nuruddeen Bubayero".
Dai-dai lokacin kuma motocin su Jalal keta gilmawa suna bin bayan nasu Sheykh da azaban gudu har kamar zasubi ta kan motocin gaban nasu, cikin mamaki mutanen sukace
"Ikon Allah to wannan saurin duka na menene? shi kuma".
Kai ya jinjina musu lokacin da yake rurrufe kayayyakin shi dan shima shirin tafiya masallacin yakeyi cikin yin ƙasa da murya yace.
"Kuyi a hankali kada ya jimu domin takadirinin yarone, saurin da yakeyi kuma, yasan muddin Sheykh bai gansu a masallaci ba ranshi zai ɓaci".
Cikin nisawa mai Napep ɗin yace.
"Kai masu saida kaya a titi iyayen gulma, dasa ido to kai ina kasan su haka?".
Da
Murmushi mai lemun ya ɗanyi tare da cewa.
"Wallahi sam ba gulma bace, akwai ƙaninshi Jamil abokin tagwaicin Jalal ɗin

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment