Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaisa ne take ce mishi sun isa lfy.

A hankali ita kuma Aysha ta turo ƙafar bedroom ɗin ta shigo.

Ido ta zuba mishi sama da ƙasa a karo na forko kenan da ta ganshi babu riga a jikinsa.
Damatsan hannunshi ta zubawa ido zuwa kan ƙirjinshi da tattausan gargasa tsilli-tsilli ya mishi ƙawanya a farar fatarshi.

Shi kuwa ido ya zuba mata dan rabonta da shigowa ɗakinshi yafi kwana goma.

Umaymah kuwa cikin murmushi mai sauti tace.
"Ina ɗiyata, tanata kuka ko?".

A hankali yace.
"Gata".
Wani irin farin cikine ya rufe zuciyar Umaymah tasan burinsu bazai tabbataba muddin babu shaƙuwa da kusanci tsakanin Sheykh da matarsa.

Cikin jin daɗi tace.
"Bata wayar".

Uhum yace kana ya miƙo mata wayar.
A hankali ta iso gabanshi kusa dashi gab-gab ta tsaya.
wayar ya miƙa mata yana kallon yadda take matsoshi.
Amsar wayar tayi ta kara a kunne tare da yin sallama.
Kana idonta kuma yana kan zanen macijiyar dake konce har kan cikinsa zuwa saman haƙar-ƙarinshi.

Da Ido yabi wurin da take kallon.
Fuskarshi ya haɗe tare da ɗaga ƙafarshi zai ja da baya.

Sai kuma ya tsaya cike da mamaki ya kalli hannunta da tasaka ta kamo bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Hannunshi yasa ya bugi hannunta,
Amman sai ta ƙara matsoshi.
Cikin sanyi ta....!




Littafin GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta number nan da nake whatsapp da ita, 09097853276 ba hoton katin zaki turoba, ba kuma TRANSFER ɗin katin zakiyi minba, ba kuma BTU ba, numbers ɗin katin zaki rubuto ki turomin. In kuwa special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank. 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai ki turo min screenshort na shaidar biyanki ta wannan number tawa ta whatsapp 09097853276.
Kada kiyi min TRANSFER ko BTU na kati wlh in kinyi ba ruwana.


By
*GARKUWAR FULANI*
Ta ƙara matsowa gabanshi.
A hankali tasa ƴar yatsarta ma nuniya dai-dai inda taga kan macijin.
Wurinda shi kuma yake masifar yimishi ƙaiƙayi.

Hannunta ɗayan kuma ta maidashi ta riƙe bakin robar gajeren wondon dake ƙugunshi.

Ido ya zuba mata, cike da mamaki da kaɗuwa, da al'ajabi to me hakan me zatayi.

A hankali ta fara bin zanen kan macijiyar tana danna yatsarta, tanayi ƙasa da yatsar.
Wani irin yam-yam haka tsikar jikinshi ke tashi tana zubawa wani irin abu yakeji yana zir-zir-zirrrrr cikin jikinshi gaba ɗaya, abune da bai taɓa jin makamancinsa ba a rayuwarsa.

Cikin wani irin masifeffen da kasala daya diro mishi ya buɗi bakinshi a hankali yace.
"M.. me h hakan.".

Manna kanta tayi da ƙirjinshi ta kife kunnenta dai-dai kan ƙahon zuciyarshi dake harbawa da sauri-sauri dib-dib dib-dib.

Cikin wata muryar data ganar dashi,
ba ita bace, bata haiyacinta mutanenta ne a kusa tace.
"Kayi shiru da Allah".

Kanshi ya sunkuyar a hankali.
Idonta a lumshe hawaye na zuba.
Cikin raunin muryar tace.
"Wurin yanayi maka ƙaiƙayi wasu lokutan ne?".

"Uhummmmmm". shine abinda kawai ya iya furtawa.

Ita kuwa ƙara shigewa jikinshi tayi.
tare da cewa.
"To kayi wa kanka jinyar wurin mana.
wannan zanen yana daga kan babbar yatsarka har zuwa nan.
Yana bin jikinka, kayi ma kanka aikin irin wanda kayi wa Aysha a ciwon hannunta.
Kana sha kana shafawa a wurin.
Zai bar jikinka zai ɓace duka.
Yanzu dai baya ci gaba da tafiya,
tunda Aysha ta tone aikin".
A hankali yace.
"Yau kuma zuwa kika sakeyi kenan? Bazaki bar jikinta ba kenan kike nufi? Sai ki biyota har ɗakina dan baki da tsoron Allah".
A hankali tace.
"Inada tsoron Allah wlh nima musulmace Kamarku.
Kafurun iska ko mugu bazai taɓa iya ratso cikin sashin kaba.
Sabida ka wadata wurin da ambaton Allah.
Ko yaushe madadin kallace- kallacen tv na banza da wofi karatun al'ƙur'ani kake sawa.

Duk sashin gidanka majigine na ƙura'an.
Ni ba muguwar iska bace.
Bana sata faɗuwa, ko kuka bare ihu.
Bana samata koda ciwon kai.
Ina kuma kareta ne ga wasu ababen cutarwa
wasu lokutan idonta kan iya ganin abinda ba kowa ke ganiba. Wanda wannan baiwar tace tun tana ƴar ƙaramarta"

Cikin dakekkiyar murya yace.
"Ki bar jikinta bana so.
Kina sata yin abinda in tana haiyacinta ba yinshi zatayi ba."

Kai ta gyaɗa tare da cewa.
"Shike nan na tafi, amman in buƙatar zuwana yayi zaka gane nazo.
abinda ma babu wanda ya taɓa gane ina jikinta sai kai daga nayi mgn sai ka gane.
Zan tafi, amman tanada buƙatar daya kawota wurinka.
Zata roƙekasa yayunta a addu'o'in kane.
sabida sun ɓata tsawon lokaci har yau babu lbrinsu."
Cikin haɗe fuskarshi yace.
"Na sani ai, ba sai kin gaya minba, Ni nan nasan komai a kan matata, nasan abinda ya faru da yayunta jeki kawai".

Atishawa tayi a hankali.
Sai gashi ta narke a jikinshi tayi lib ido a lumshe alamun tayi bacci.

A hankali ya gyara tsayuwarshi.
Tallabeta yayi da kyau.
Hannunshi yasa ya cire hijabin jikinta.

A ranshi yake mgna.
"Na fahimta kenan iyayenta ma, basuma san tanada wata iska a jikinta ba.
Shiyasa basu sanarba kafin a ɗaura auren".
Ido ya lumshe yana goge wannan ayar tambayar da ya bugawa Bappa cikin ƙoƙolwarshi na ya aurar da yarshi ba tare daya sanar musu tanada al'matsutsaiba kamar yadda shariya tace.

A hankali ya zauna bakin gadon da ita.

Yana nazartan abubuwa da dama.

Ya fara fahimtar wasu ababen a kanta musamman da yake Junaidu ya labarta mishi komai abinda ya sani a kan Shatu da Ba'ana lokacin da suke asibitinshi Valli.
konciya yayi a gefen daya kwantar da ita.

Kana yasa hannunshi ya kashe wutan ɗakin.

Ido ya lumshe ba tare da yayi baccinba.

Ita kuwa Aysha a hankali ta farka daga baccin, ido ta ɗan buɗe.
tabbas kam tasan tazo ɗakin shi kuma tasan ta ganshi babu riga daga nan kuma bata kuma sanin meke wakana ba.
cikin sanyi take juya kwayar idonta.
A hankali ta kalleshi yana konce yayi rigingine, cikin sanyin murya alamun baccin tace.
"Yah Sheykh! Yah Sheykh!".
A hankali ya ɗan juya kwayar idonshi ya kalleta.
cikin sanyi yasa hannunshi ya jawota jikinshi.
Kan ƙirjinshi ya kwantar da ita.
Yana mai jin wani irin baƙon yanayi yana game dukkanin sasan jikinsa gaba ɗaya.

Shiru tayi jikinta na wani irin sassanyan tsuma can ciki-ciki.

Cikin sanyi tace.
"Zan kwanta".

Cikin sanyi murya can ƙasa yace.
"Yanzu a tsaye kike ai".

Ya bata amsa a daƙile, shirun ta kumayi.
Shi kuwa gyara kwanciyar tasu yayi.
Tare da jawo blanket ya rufesu.
kana ya fara Addu'o'in yanayi yana tofawa a tafin hannunshi yana shafawa a fuskarta da sassan jikinta.
Idanunta ta lumshe yanaji sanyin tattausar fatar hannunshi.
A haka sukayi bacci, ɗaki ɗaya gado ɗaya borgo ɗaya pillow ɗaya a liƙe a jikin juna.
Karo na forko kenan da wannan kusancin ya samu tsakaninsu.

Washe gari kuwa.
Lamiɗo ya ƙara neman Sheykh akan batun tafiyar da dole zaiyita.
Shi kam yace zai tura wasu.
Dan yana son zuwa aikin haji,
Amman fir tsohon nan yaƙi.
Ya haɗashi da Abbanshi dole ya haƙura.


Washe gari da safe.
Mami matar Affan tazo, ita da Zahra'n Hamma Yusuf.
Bayan sun gaisane tace.
"Ga ƙanwata Zahra matar Yusuf".
Murmushi Aysha tayi tare da cewa.
"Ayyah ai kuna kama fa".
Da sauri Mami tace.
"A a na fita kyau duk gidanmu itace mummunar mu fa".

Dariya Zahra tayi tare da cewa.
"A daba".

Nan Aunty Juwairiyya ta shigo sukaci gaba da hira,
Ummi da Saratu suna kitchen.

To haka dai mafi akasarin lokuta Mami kanzo susha hira.

Tofa nan kewar ke ɗan raguwar mata, wani lokacin kuma ta kira Bappa susha hira ko ta kira Rafi'a ko Junaidu taji lbrin Rugar Bani.

Yau sallan layya saura sati biyu.
Kuma gobene Sheykh zai fita.
dole kuma tafiyar da motace bazai yiwu ta jirgiba.
Tunda rugogin manyan Arɗaɓe zai ziyarta wanda cikin dazuka suke.

Yana zaune a falon Lamiɗo shida Abbanshi da Galadima.
"Ka gama shiryawa ko Muhammad?".
Abba ya tambayeshi cikin kula.
Kanshi ya ɗan gyaɗa tare da cewa.
"Eh".
Lamiɗo ne ya ɗan shafi kan shi tare da cewa.
"Itama iyalin taka ta gama kimtsawa ko?".
Da sauri ya kalli Lamiɗo tare da cewa.
"Ta kimtsa taje ina ɗin?".
Abba ne ya bashi amsa cikin bada umarni yace.
"Ta kimtsa ku tafi tare, dole tare zakuje".
A hankali yayi ƙasa da kanshi tare da cewa.
"Dan Allah Abba tafiyar da nima ba sonta nakeyi ba, a kuma sake haɗani da wani jidalin".
Fuska a haɗe Abba yace.
"A bayanka akace ka goyeta ku tafi ne?".
A hankali ya jujjuya kai.
Cikin yanke hukunci yace.
"To ku tafi tare Muhammad bana son musu a kan yarinyar nan duk abinda akace kayi dan Allah kayi tunda ba wanda ya saɓawa shariyar musulunci za'ace kayi ba.
Baka san abinda muke zaton samu ta sanadinta ba.
Muna ganin nasarori kan matsalarmu. Kaje da matarka kaji ko Muhammad na".
A hankali yace.
"To Abba ba komai in dai zakayi farin cikin hakan zanje da itan".

Kanshi ya shafa tare da cewa.
"Allah yayi maka al'barka".
Amin Amin yace cikin jin daɗi.

Kana ya sallamesu ya fita.
A falo ya samu Ummi ita ɗaya tana kallon wata tashar da aka saka wa'azin shi.
Cikin sanyi yace.
"Ummi gani gaki sai kin kalleni a tv".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Ina ƙaruwa ne ai".
Kanshi ya jinjina tare da ɗan kallon gefe da gefe kana yace.
"Ummi ina take?".

Juyowa tayi ta kalleshi tare da cewa.
"Tana ɗakinta".
Kanshi ya gyaɗa kana yace.
"To Ummi Lamiɗo yace wai dole da ita zamuyi tafiyar zaga rugar Arɗabe.
A gaya mata ta shirya gobe sammako zamuyi inga ko zamu gama cikin kwana huɗun".
Cikin murmushin Ummi tace.
"To bari in gaya mata".

To yace shi ya nufi sashinsa.
Ita kuma ta nufi ɗakinta.

A gaban mirror ta sameta tanayiwa kanta kitson kalba manya-manya.
"Kitso kikeyi ne?".

Juyowa tayi tare da cewa.
"Har na gama ma!".

"Kuma yayi kyau sosai fa".
Dariya tayi tare da cewa.
"Allah ko Ummi".
Kai ta gyaɗa alamun eh.
Kana tace.
"Sheykh yace in gaya miki ki shirya gobe zaku tafi tare yawon ziyartan Arɗaɓen inda dama na gaya miki zaiyi tafi, duk an turawa Arɗaɓen saƙon zuwanshi ma".
Cikin jin daɗi tace.
"Kai naji daɗi na, zan fita in zagaya inga makiyayan in huta da zaman wuri ɗaya".
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Wato zakije kiga fulani yan uwanki ko".

"Sosai ma kuwa Ummi yanzu tayani shiryawa".
Ta faɗa tana buɗe drower'n.

Nan kuwa Ummi ta tayata ta kimtsa ababen buƙatar ta.

Sannan suka fito falon inda suka samu Jamil ya dawo aiki Jalal kuma dama yana sashin Hajia Mama ne.
Sai yanzu ya dawo nan ɗin nan suka zauna sukaci gaba da hira.

Washe gari da safe suka fito cikin shirin tafiyar.

Motoci guda bakwai ne uku a gaban ta Sheykh uku a bayan tashi.

Biyu na gaba fadawa sai ta ukun Jalal ne da wasu mutane su biyu.

Sai motar Sheykh shida Aysha suna baya Ado na jan motar.

Sai wacce take binsu Affan ne da Ya Hashim sai Sulaiman kana Laminu ɗan jaridar, da zai ɗauki komai.
Sai biyu kuma na baya kuma Galadima ne.
Sai fadawa da godarai sai hadimai mata biyu da zasuyiwa Aysha hidima.

Tafiya mai ɗan nisa sukayi.
Kana suka ratsa wata babbar hanyar birji, suka fara tafiya suna kutsawa cikin daji.

A ƙalla awa ɗaya suna tafiya.
Sunata wuce ƙananan rugagen Fulani makiyaya, da dabbobinsu.

Kasan cewar manyan motocine masu inganci yasa.
Basu jin wannan gargada ta buwayesu.

Jalal da abokanshi sunata hira, sosai Jamil yayi mamakin sakin fuskar Jalal cikin abokanshi.
Sannan sukanyi mgna da wani salo na musamman.

Shi kuwa Jamil waya yakeyi da Khairat sabuwar budurwarshi.

A can baya kuwa Affan ne liƙe da waya a kunne yana mgna da Yusuf.

A motar Sheykh kuwa, shiru kakeji kowa da sabgar da yakeyi.
Shi zaune yake da kyau ya buɗe system ɗinshi yana wani aiki a ciki.

Hankalinshi duk yana kanta.
Ita kuwa Aysha wani irin farin ciki mai zaman kashi takeyi.
Shiyasa hankalinta kab yana kan rugagen Fulani da suke wucewa.
Murmushi mai baiyana shauƙinta da begen irin wuraren takeyi, yana tuno mata Rugar Bani, da sauran inda suka zauna.

Kana tana farin cikin bin wannan tafiyar ne ko zataga wani abin da ya shafi su Ya Gaini.

Ɗan juya kwayar idonshi yayi ya kalli inda take.
Hankalinta duk yana kan window.
Taɓe baki yayi kana ya maida idonshi kan fuskar na'urar tashi.

Wani babban rugar Jafun suka fara isa.

Rugar a cike take maƙil da maza da mata matasa da sofaffi

Bisa alumun sun san da wannan ziyar shiyasa basu fita kiwo ba.
Bayan sunyi parking ne.
Fadawan suka fara fitowa.
Sukazo sukayi buɗe wa sauran motocinsu.
Galadima ne ya fara fita kana gaba ɗaya su Jamil Jalal dasu Affan suka fito.

Ita kuwa Aysha da sauri ta yunƙura zata fita kasan cewar ta gefen da take aka buɗe.
Hannunshi yasa ya riƙo nata.
Da sauri ta juyo ta kalleshi cikin sanyi tace.
"Ba fita zamuyi ba?".
Ido ya zubawa fuskarta yana kallon yadda take mgn da alamun tsiwa da tura baki.
Uhum wato yanzu ta worke tsiwar zata dawo.
Ya raya a ransa,
a zahiri kuma kai ya jujjuya mata, tare da ronƙofowa, kan cinyoyinta.
Hannunshi ya miƙa ya jawo marfin ya rufe.

Su Galadima kuwa kan zuwa sukayi suka zagaye motar tashi, suna jiran fitowarshi.

A hankali ya buɗe marfin dake kusa dashi.
Kana yasa ƙafarshi ta dama, ya fita.
Meda ƙofar yayi ya rufe ganin tana shirin fitowa.

Buɗe al'kyabbar jikinshi yayi kana ya gyara zamanta.
Bayanshi Galadima ya koma.
Sannan Jalal da abokanshi suka koma gefe-gefenshi.
Sauran ayari kuma suka rufa mishi baya.

Su kuwa can cikin taron fulanin da sauri Arɗo Maru ya miƙe da sauran ƙananan Arɗo na gefenshi,
kasan cewar shine Arɗon araɗabe na yankin gaba ɗaya.
Da sauri suka nufosu cikin mutumtaka da fara'a suka iso.
Hannu ya bawa Sheykh tare da nuna mishi hanyar shiga inda sukayi musu shimfiɗa can cikin manyan rufuna.
"Bismillah GARKUWAn mu, gatanmu a idon gwamnatin jiha data ƙasa, bismillah gacan wurin zama".
Kanshi ya jinjina kana yabi bayanshi sauransu suka biyo bayanshi.

Bayan suna zauna ne, duk Arɗo's ɗin suka zagayeshi ta gaba su Galadima da sauran tawagar kuma suna baya.
Kana dogorai kuma na tsaye.
Arɗon araɗabe kuwa, yana gabanshi.

Gyara zamanshi yayi ya fuskanci Arɗon araɗabe cikin tattausan lafazi yayi ɗan murmushi tare da cewa.
"Kuna lfy ko? ba wata matsalar ko?".
Murmushi Arɗon araɗabe yayi tare da cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah".
Kanshi ya ɗan ɗago ya kallesu baki ɗayansu kana yace.
"Masha Allah. To Allah ya taimaka".

Amin Amin sukace cike da jin daɗi, shi kuwa fuskantarsu yayi dukansu tare da cewa.
"Na kawo wannan ziyarar ne dan samar da Kekkyawar alaƙa da kauda fitina tsakanin makiyaya da manoma da sauran al',lummar gari.
Ina al'fahari da dukanku biyu uku makiyaya manoma jama'ar gari.
Bana son wani sashin ya cutar da wani sashin.
Ina neman al'farma daku zauna lfy da manoma banda yi musu ɓarna akan haƙinsu.
su wahala su noma kusa dabobbin ku suci su taka kunsa ya tabbata baku da gskya duniya zata ɗaukemu masu tada zaune tsaye.
Amman ina kuka bari manoma suka tattara kayan amfaninsu sai ku nemi izinisu ku shiga kuyi kiwo a gona kinsu".

Cikin gamsuwa da bayaninshi suka haɗa baki wurin cewa.
"In Sha Allahu zamu kiyaye,
bazaka samemu a layin masu tsokana ba mu nan Jafuna".
Kanshi ya gyaɗa cikin gamsuwa kana yace.
"Muddin manomi ya neme ku da fitina ko wasu sauran gama gari kada ku tanka musu.
Ga number wayata zan baku koda yaushe kuka kira zata shiga.
Zan sanar da ƙungiyar *MI YETTI ALLAH* itace ƙungiyar dake kula da matsalolin makiyaya da manoma.
Sannan duk inda kuke akwai mambobinmu a garuruwan dake kusa daku zasu shiga lamarin.
Duk wanda aka samu da rashin gsky zai fuskaci Hukunci.
Kana Ƙungiyar *TABITAL POOLAKU* tana tare daku a cikin dukkan al'amuran ku.
Kiyaye shigar banza kamar dai yadda na ganku yanzu cikin manyan suturu shine abinda yafi dacewa damu a matsayinmu na musulmai".

Cikin murmushin Arɗon araɗabe yace.
"Zamu kiyaye, kuma dama mu Jafunawa bamu ɗaya daga cikin ƙabilun dake yawo a daji da kiwo masu yaɗa barna.
Mu Jafunawa ko suturarmu ta banbanta data sauran makiyaya".

Hannu ya bashi bayan ya basu number miƙewa sukayi tare.
Da musu godiya
Kana suka rakasu har wurin motocinsu, nan Galadima ya miƙa musu kyautan kuɗin taimakon da Sheykh ya ware musu.
Nan suka shiga suka tafi a jere kamar dai yadda sukazo.

Tafiya mai ɗan nisa sukayi kana suka dawo kan hanya.

Jihar Jigawa suka nufa,

Dan yana so a ƙalla dai a yau ya zauna da Arɗaɓen jihohi uku

Kamar yadda ya tattauna da Rugar forko hakama ta biyu.
Sun amshesu a mutunce.
Daga nan suka nufi jihar (Tsinako) Katsina.

Daji suka nausa karfe biyar dai-dai suka isa Rugar da Arɗon araɗabe nasu yake.

Dai-dai lokacin kuma gaba ɗaya makiyayan sunata dawowa kiwo.
Bayan sun fitone, suka nufi inda suke.

Cike da mamaki Sheykh da tawagarsa duk ke kallon mutanen wannan Rugar.
Gaba ɗayansu maza garin kitsone a kawunansu reras har kafaɗunsu.
Ga wasu irin guntayen wondunan yadin atampa na mata,
kana rigunan tashi kabi shanu a jikinsu.
Kowa ka gani da sanda a wuyanshi.

Ba yabo ba Fallasa suka marab cesu.
Bayan sun gaisa ne yayi musu jawabin abinda ya kawosu.
Ɗaya daga cikin Arɗo's ɗin ne yace.
"To wannan shiga dai itace muka samu wurin iyaye da kakanni babu kuma abinda take mana mu ba a takure mikeba kamar yadda kace.
Sannan batun manoma kuma infa suka tsokanemu mu bazamu jira wata hukumar.
MI YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU ba.
Zamu rama".
Murmushi Jalal yayi tare da cewa.
"In kunfi ƙarfin kungiyar ku ta mi YETTI ALLAH da TABITAL POOLAKU.
Tabbas bazakufi ƙarfi mu mu rundunar tawagar sojojin ƙasar ba.
Ku iye harshenku tabbatar da zaman lfy ne ya kawomu nan ba musuba kuma umarnine."
Cike da mamaki Ya Hashim da Laminu da Sulaiman harma da Jamil suka zubawa Jalal ido.
Mgnarshi ta nuna cewa, shi sojane mai ƙarfin iko kenan.
Rigar dake jikinshi ta sama ya cire.
Sai ga rigar sojojin ƙasar Nigeria ta baiyana a jikinshi a saman kafaɗunshi.
Taurari biyu da kuma alamar Shaho colonel ne kenan.

Suma sauran abokanshi biyu rigunansu na sama suka cire.
Ganin hakane yasa waɗannan makiyayan sukayi ƙasa da kawunansu.

Shi kuwa Sheykh.
Gyara zamanshi tare da cewa.
"Zama lfy yafi zama ɗan sarki, inji bahaushe to, tabbas mu zauna lfy shine ci gabanmu."
Sai kuma ya kalli Galadima dake gefenshi yace.
"Waɗannan mutanen a dasawa Rugarsu ayar tambaya.
Ku tashi mu tafi, in naji wani kuskure ko tsokana daga gareku tabbas zaku fuskanci fushin ƙungiyar mu, zamu kuma miƙaku hannun hukumar ƙasa.
In kuwa wasune suka tsokaneku ga number ta ku gaya min haƙiƙa zamubi kadunku bazan lamunci a cutar daku ba."

Da sauri Arɗon Arɗaɓen ya biyo bayansu da sauran wasu dattawansu.
Haƙuri suka bashi tare da al'warin zaman lfy.
Kana bazasu bari ayi husumaba.

Da haka dai sukayi sallama suka tafi.
Madadin su kwana cikin jihar Tsinako indama sukeda cikekken ikon a masarautarsu Haroon ga uwa mai daraja Umaymah sai suka wuce jihar Noka bayan sunyi sallan mangriba da isha'i.

Suka ɗau Hanya.
Gajiya iya gajiya sunyishi.
Gaba ɗaya kowa jikinsa yayi nuƙui sabida ba ƙaramar tafiya sukayi ba.
Wuni a zaune tun karfe bakwai na safe har yanzu takwas na dare kan tafiya suke kuma babu alamun sun kusa jihar Nokan.

A cikin motarsu Jalal da abokanshi sunata hirarsu.

Laminu kuwa tuni ya sanarwa Gimbiya Saudatu ashe Jalal sojane.

Ta girgiza da jin lbrin sosai.

A motarsu Galadima kuwa shiru duk sukayi dan gajiya ga jikin tsufa.

Ita kuwa Aysha dama tunda aka hanata fita, ta kumbura ta cika tayi tib bata sake kulashiba, shima ko inda take bai kuma kallonba.

Bare yanzu aikin tura rahoton tsarin Rugar da suka fito yake turawa Haroon.
Ta E-mail address ɗin shi sabida shi baya whatsapp.
Bayani yake mishi ya isar da saƙon ga masarautarsu dan a sawa mutanen wannan yankin ido sosai, ya lura basu da nitsuwa.


Haroon kuwa Umaymah ya kalla cike da mamaki yace.
"Kinaji Umaymah Sheykh fa yau jihar nan ya wuni.
Wai yanzu madadin ya kwana a nan shine ya wuce Nokan a daren nan".
Murmushi tayi tare da cewa.
"Na sani ai munyi mgna da Aysha.
Tare da ita suke shiyasa bazai iso nanba".
Murmushi Haroon yayi kana sukaci gaba da hirarsu.

Sai ƙarfe Goma da rabi suka isa Nokan state.

Wani tamfatsetsen hotel mai zaman kanshi suka nufa.
A cikin motar ya rufeta.

Kana ya fita.
Su Jamil duk na biye dasu a baya.

Ɗakuna ya kama musu gaba ɗayansu sannan ya juyo ya dawo shi ɗaya.

Motar yazo ya buɗe tare da cewa.
"Bismillah".
Tura baki tayi tare da cewa.
"A barni zan kwana cikin motar".
Kanshi ya sunkuyar tare da kaurara muryarshi yace.
"Ki fito".
A hankali ta zuro ƙafafuwan ta woje,
sun ɗan kumbura alamun dadewa a zaune.

Sabida ko abinci saya sukeyi a cikin mota sukeci.

Sai dai shi wunin duka dabino yakeci.

Miƙewa tayi ta fito.
Hannunshi yasa ya ɗauki jakar kayanshi.

A hankali yayi gaba tana biye dashi a baya.

Hotel ɗin babbane mai matuƙar kyau.

Wani Side shi wai VIP can suka nufa.

Suna shiga cikin falon, ta zauna bisa kujera.

Shi kuwa ajiye jakar yayi kana, ya miƙe tsaye,
Jikin ƙofar ɗakin ya koma ya rufe kana ya zubawa ƙofor ido.
Tsawon mituna biyar, kana ya dawo wurin abun kunna fankan
daga nan kuma ya dawo tsakiyar falon saman jikin fanka ya tsurawa ido.
Ita kuma tana binshi da ido, ne ganin kamar wani abu yake nema.

Bedroom ya wuce.
Ya fara bincikar ɗakin.
A jikin masaƙalin Rimot ɗin AC yaga wani ɗan ƙaramin abu.
Hannunshi yasa ya cire abun.
Kana ya fito jakar ya ɗauka tare da cewa.
"Mu tafi".
Cikin gajiya da wani irin nannauyan masifeffen baccin daya cika mata ido ya kashe mata jiki da gajiya tace.
"Ina kuma zamu je? ni bacci nakeji! Ni na gaji".
Hannunshi yasa ya kamo nata hannun.
Wani ɗakin suka kuma komawa aka basu key tare da bashi haƙurin da ita dai bata san kanme suketa bashi haƙurinba sunata rantsawar basu sani bane.
Ma'aikatan hotel ɗin da kansune suka bi bincika ɗakin kana suka fita,
suna cewa.
"In sha Allah zamu kula zamu kuma kiyaye gaba".

Rufe ƙofar yayi kana ya wuce bedroom.
Ita kuwa bisa kujerar ta kwanta tana sauƙe numfashin gajiya da bacci a take bacci ya saceta.
Shi kuwa Sheykh wonka yayi kana ya fito yayi shirin baccinsa.
Leƙowa falon yayi.

Tuni tayi bacci bisa kujera sai numfashin gajiya take sauƙewa a hankali baccin kuma mai nauyi takeyi.
A hankali ya iso inda take,
"Ke Tashi kije kiyi wonka".
Yace yana kallonta.
Shiru kamar bata da rai ko motsi batayi ba.
Karo na uku ya kuma cewa.
"Ke tashi kije kiyi wonka ki kwanta".
Still ko mitsin batayi ba.
A hankali ya ɗan sunkuyo kanta.
Hannunshi yasa ya ɗan kamo hannun ta tare da cewa.
"Tashi kije kiyi wonka zakiji sauƙin gajiyar".
Cikin bacci tace.
"Uhum-Uhum.
Ni na gaji ka barni bazanyi wonka bacci zanyi".
Kanshi ya juya tare da cewa.
"Uhummm yanzuma tsami kikeyi, Ni in bakiyi wonkaba bazan kwana dake ɗaki ɗaya ba".
Cikin baccin ta ɗan kalleshi tare da lumshe ido tace.
"Ni Ko sati nayi banyi wonkaba bana tsami, kuma ni zan kwana a nan kaje can ɗakin".
Da sauri yace.
"Rufe baki yarinya ko yaushe bakinki baya shiru.
Muje kiyi wonka".
Komawa tayi ta konta, tare da lumshe idanunta, da suke cike da bacci mai nauyi da gajiya tuni ta meda baccinta".
Juyawa yayi ya koma Bathroom ruwan ɗumi mai ɗan zafi sosai ya cika baf ɗin kana, ya fito.

Gefenta ya zauna.
A hankali yasa hannunshin ya fara zuge zip ɗin rigarta,
shiru tayi tana baccinta.
Ƙarasa zuge zip ɗin rigar yayi tare da cewa.
"Tashi! Tashi!! Zan tuɓeki fa".
Shiru kakeji kamar bata da rai".
Kanshi ya jingina da kujerar.
Kana ya fara yin ƙasa dashi tare da ɗan ɗagota ya jinginata da jikinshi.

Still tana baccinta.
Ƙasa yayi da rigar ya cire mata hannayen ya rage bra ne a ƙirjinta, ɗan jawota yayi ya kifeta kan cinyarshi ya ɓalle masaƙalin yayi kana ya ɗan ɗagota ya cireshi a hankali.
Yana cewa.
"Tashi to! Tashi kinji!".
Shiru abinta, ɗan gajeren tsaki yayi tare da.
Manna bayanta da ƙirjinshi.

Shiru yayi tare da zuro kanshi tsakanin wuyanta da kafaɗanta,
Caɓɓullenta da suke tamfatse a cike tab a ƙirjinta ya ɗan kalla.
Da sauri ya rumtse idanunshi,
tare da ƙara mannata a ƙirjinshi.
Hannunshi yasa a hankali ya fara murza rigar yanayin ƙasa da ita,
shiru yayi jin ta ɗan riƙe hannunshi.
Sai kuma ya sauƙe ajiyan zuciya cin ta sake hannunshi ta koma tayi lib alamun ta koma nannauyan baccin gajiyar data kwasa ɗin.

Ƙafarshi yasa tsakanin cinyoyinta tura rigar yayi ƙasa gaba ɗaya.

A hankali yaji idonshi na mishi rawa,
buɗesu yayi ya zubasu kan surar jikinta.

Wani irin harbawa da azaban ƙarfi yaji Sheykh ɗin shi tayi.

A hankali yasa hannunshin kan santala-santalan cinyoyinta, yana kallon yadda gajeren wodon dake iya guiwarta yayi lib a jikinta.
a hankali ya sonkuyo sosai ya kai bakinshi saitin kunnenta cikin wata iriyar raunatacciysr murya mai cike da gajiya, Feeling, da sanyi yace.
"Aish! Aish!! Tashi muje kiyi wonka".
Ɗan buɗe idonta tayi jin ɗumin numfashinsa a kunnenta da ɗan sautin mgn da taji can cikin baccinta.

Mirginawa tayi a jikinshi da kyau, sabida, wani irin masifeffen sanyin ac da taji yana ratsa ta sabida cire kayan jikinta da yayi.

A hankali tasa hannunta ta kamo hannayenshi duka biyu ta mannasu kan ƙirjinta.
Tare da duƙun-ƙunewa a jikinshi.
Wani irin tsalle yayi lokacin da yaji ta manna tafin hannunshi kan C...!




Littafina GARKUWA na kuɗine turo katin mtn na ɗari uku kacal ta wannan number 09097853276 numbers ɗin jikin katin zaki rubuto ki turo min ba hoton katinba. Bana son VTU bana son transfer. In Kuma special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ta asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa. Sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo shaidar ta number ta da nake whatsapp dashi 09097853276. Banda VTN banda transfern kati.





2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment