Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi ɗaya ba cikin jam'iba, gashi su Jalal ma yau duk basa nan ɗin.

A nitse ya juyo.
Falon Aysha ya nufa.
Shiru ba kowa sai TV'n da suka bari a kunne.

Kanshi ya ɗan juya ya kalli ƙofar ɗakinta,
TV'n ya kashe sannan ya nufi ɗakin.

Da sallama a bakinshi ya shiga,
tsayuwa yayi a tsakiyar ɗakin, ganin ba kowa.
juyowa ya ɗan yi kana, ya fito falon,
ƙofar ɗakin Ummi ya nufa,
a bakin ƙofar ya ɗan tsaya tare da cewa.
"Assalamu alaikum".
Da sauri Ummi tace.
"Wa laikassalam, Sheykh ka shigo".
Kanshi ya ɗan shafa tare da yin jim kaɗan kana yace.
"Umm Aish tana nanne?".
Da sauri Ummi tace.
"Eh gata nan muna tare".
Ta ƙare mgnar tana nunawa Aysha hanyar fita alamun taje.
Shi kuwa Sheykh ɗan juyawa yayi tare da cewa.
"Ummi magriba ta kusafa".
Miƙewa Ummi tayi tare da cewa.
"To Sheykh".

"Aish". Ya kira sunan a mutunce.
A hankali tace.
"Na'am".
"Kizo".
Yace yana mai juyawa.
Miƙewa tayi ta fito.
Da ɗan sanɗa ta isa gefenshi tare da cewa.
"Gani".
Juyowa yayi ya ɗan kalleta sama da ƙasa kana yace.
"Je kiyi al'wala kizo ɗakina muyi salla, bazan samu zuwa Masallaci ba".
Cike da gamsuwa da mgnar sa ta ɗan karya wuya tare da cewa.
"To amman zanyi wonka kafin nan".
Kanshi ya gyaɗa mata tare da cewa.
"To Kiyi sauri kada lokacin yayi baki fitoba".
To tace kana ta nufi ɗaukinta.

Shima ya wuce ya nufi Side ɗinsa.
Kai tsaye bedroom ya wuce.
Babban sallayarshi ya shimfiɗa musu a tsakiyar ɗakin kana ya zauna a wurin, tare da lumshe idonsa ya fara bita.


Ita kuwa Aysha Kai tsaye bathroom ta wuce.
Ruwa mai ɗan zafi sosai ta haɗa, bayan tayi Brosh wonka ta farayi mai rai da lfy.
Sosai ta cuccuɗa jikinta lungu da saƙo kamar ko wani lokaci tana gama wonkan tayi al'wala kana ta fito.

Tana fitowa ta wuce gaban dreesing mirror, gashin kanta ta taje ta gyarashi ta tubkeshi a ƙeyanta sabida saurin da takeyi bata tsaya kitse jelarba.
body lotion mai ɗan karen ƙamshi ta shafa a jikinta, kana ta shafa humranta mai sassanyan ƙamshi.
Kasan cewar yanayin Weather'n garin ya sauya ko ina yayi sanyi iska mai sanyi nata busawa tana kaɗawa da sassayan ruwane yasa.
Ta saka dogon wondon blue jeans sai kuma tasa wani Baby top fari wanda ya lafe a jikinta yayi mata cib-cib kana ta ɗaura wani pink jacket wuyanshi da tattausan suma fari, sai dai jacket ɗin ba irin ƙattin nan bane ƴar cafalce dai-dai da jikinta kuma ya tare mata sanyin.

Gaban dreesing mirror ta koma wasu turaruka masu ƙamshi guda biyu ta fesa.
Kana ta zato wani ƙaton hijabinta Black blue mai ɗan karen kyau da sheƙi, ta zurashi har ƙasa ko idon sawunta bazaka iya ganiba.

Sallayarta ta ɗauka kana ta fito da ɗan sauri ta nufi Side ɗinsa.

Ganin baya falone yasa ta wuce bedroom da sallama a bakinta.
"Wa laikissalam".
Ya amsa mata lokacin da ta turo ƙofar ta shigo.
A gogon hannunshi ya kalla tare da cewa.
"Iso muyi lokacin na tafiya."

To tace tare da ƙarasowa tsakiyar ɗakin.
Sallayan dake hannunta ya kalla tare da taɓe fuska kana yace.
"Duk sallayan dake ɗakin nan bazasu isheki bane sai kinzo da naki?".
Girgiza kai tayi alamun a a.
Hannunshi yasa ya amshi sallayar, kana ya juya ya fuskanci gabas.
Ita kuma ta ɗan matso gefenshi ta tsaya daga bayanshi kaɗan. Ganin ta kimtsa ta nitsu yasashi tada kabbara.

Masarautar Joɗa kuwa, an dai kira salla amman ba'a samu mutane da yawa ba sabida laruran ruwan sama.

Bayan sun idar da sallan ne, sukayi addu'o'in kana sukayi nafila raka'a biyu, sannan suka zauna.
Tasbihi ya ɗanyi kana ya gyara zamansa da kyau, Al'ƙur'ani dake kan durowar dake gaban wurin da yake sallan ya dauko,
juyowa yayi ya fuskanceta kana ya miƙa mata.
Kallonshi tayi tare da amsar ƙura'an ɗin.
"Ki karanta inji yadda kira'arki take".
Ya faɗa idonshi na kanta.

Shiru ta ɗanyi tare da kauda idonta daga kan nashi.
Cikin sanyi ta miƙo mishi ƙura'an ɗin".
Ba tare da ya amsaba yace.
"Bazakiyi ba, inji ki samu lada ba?".
Kai ta jujjuya kana a hankali tace.
"Zanyi".
Cikin kauda kanshi daga kanta yace.
"To bismillah".
Miƙo mishi ƙura'an ɗin ta kumayi tare da cewa.
"Ka riƙe min sai inyi kana duba min haddana yayi ko da gyara".
Wani irin sassanyan numfashin da bai shiryawa bane ya subce mishi.
Cikin nitsuwa yace.
"Ba sai na duba mikiba, kada ki damu kiyi inaji in kin ɓata zan gane ba sai ina duba surar ba".
Cikin sanyi ta ɗan ɗago idanunta ta kalleshi kana ta ruggume ƙura'an ɗin a ƙirjinta.
Lumshe idonta tayi tare da cewa.
"Wacce sura zan karanta?".
Kanshi ya jingina da jikin gado kana ya zubawa fuskarta dake zagaye da hijabin ido a hankali yace.
"Surar da kikafi jin daɗin haddarsa".
Cikin nitsuwa tace.
"Suratul Noor".
Kanshi ya jinjina mata tare da cewa.
"Bismillah".
Kai ta rausayar ba tare da ta buɗe idonta ba, ta gyara zamanta kana a hankali tayi gyaran murya tare da cewa.
"Aaoozubillahi minashaiɗani rajen.
Mismillahi rahmaniraheem.
(Suratu anzalnaha wa farad'nahah wa'anzalnaaa fihahhhhhhhhhhh Aayati baiyinati la'allakum tazakarun."
Ida nunshi ya lumshe a hankali tare da sauƙe numfashi jin yadda ta bada taƙib a wurin fihahhhhhh, kana ta rufe ƙarshen ayar da bawa Wawun iya damarsa.
A hankali ya buɗe idanunshi ya zubawa lips ɗinta su, sabida jin taci gaba da aya ta biyu.

Karatun takeyi cikin sanin ƙaidarsa da bawa ko wanne harafi haƙƙinsa tsakanin ɗauri da wasalin sama dana ƙasa da kuma wurin ja mai shida da huɗu da uku.

Sosai yake jin sautin zazzaƙar muryarta na ratsa mishi kunnuwa har zuwa ƙahon zuciyarshi.

Kanshi ya jingina da gado yana jin yadda take fitar da Tajwid da kyau da fidda Qalqala, iglab, idgham, ikhfa'a Ghunna.

A hankali ya ɗan ɗago kanshi lokacin da ta iso aya ta 31 gyaran murya ya ɗan yi,
wanda yasa ta buɗe lumsassun idanunta da sauri.
Kallon alamun tambaya ta mishi.
Kanshi ya jujjuya tare da mata alamun taci gaba.

Nannauyan numfashi ta sauƙe tare daci gaba.

Kai ya sake ɗagowa lokacin da tazo aya ta 61 still yayi gyaran murya.
Ci gaba tayi da karatun dan ta fahimci alama yake mata.
Kasan cewar suratul Noor ayoyi 64 gareta.
Aya uku ta kara kan na 61 da ya mata gyaran murya tazo ƙarshen ayar.
Da sauri ta buɗe idonta jin yace.
"Sadakallahul azeem".
Kanshi ya jinjina tare dayin murmushi.
Ita kuwa cikin sanyi tace.
"Ɓata nawa nayi?, Yah Sheykh a gyara min?".
Murmushi yayi tare da cewa.
"Baki ɓataba kinyi ƙoƙari sosai".
Cikin sauri tace.
"To kuma naji kayi gyaran murya".
Gyara zamanshi yayi ya fuskanceta da kyau kana yace.
"A aya ta nawa da ta nawa nayi gyaran murya?".
Hannunta tasa ta tallaɓe fuskarta tare da cewa.
"Aya ta 31 da 61".
Hannunsa yasa ya ɗan shafa gemunsa kana yace.
"Ayoyin sun kasance ɗaya daga cikin dogin ayoyin da aka ƙiyasta tsawonsu dake cikin al'ƙur'ani mai girma".
Kai ta jinjina alamun gamsuwa kana tace.
"Ayyah, wato shiyasa lokacin da nake haddarsa aya ta 31 saida na kusan sati a kanta, bappa yayi ta faɗa wai nasa wasa a gaba".
Kanshi ya jinjina kana yace.
"Sosai ma kam gskyar Bappa kinyi wasa".
Cikin sanyi tace.
"Kai a kwana nawa ka haddaceshi?."
Murmushi yayi tare da cewa.
"A kwana bakwai sati ɗaya na haddace suratul Noor".
Cikin ware ido tace.
"Kai ai ƙwaƙwalwarka ta musamman ce Yah Sheykh."
Miƙe tsaye yayi yana cewa.
"Ko?".
Eh tace tana kallon dunduniyar ƙafarshi.
Wayarshi ya ɗauka, ɗan daddan nawa yayi kana ya kara a kunne jim kaɗan ya fara mgna.
"Ayyah Ummi zanci gashinki".
Murmushi Ummi dake zaune bisa sallaya tayi tare da cewa.
"Kaza ko zabuwa?".
Juyowa yayi ya ɗan kalli Aysha kana yace.
"Zabuwa, Ummi ta gasu da kyau".
Cikin sakin fuska tace.
"To Sheykh bari inyi sallan isha'i".
To yace kana ya katse kiran.
Ya dawo ya zauna.

Ummi kuwa
har ta zauna sai kuma ta tashi.
Ta nufi kitchen a cewarta kafin tayi sallan zabuwar ta sulala.

A gudanta haka ta wonketa fese.
Kana tasa a tukunta, sannan tasa al'basa, kanamfari citta tafarnuwa kaɗan sai kurry, sannan tasa Maggi da gishiri kaɗan, sannan ta ɗaura a wuta kana ta wonke hannunta ta koma ɗakinta.

Ruwa kuwa har yanzu tsugashi akeyi kamar ba gobe.

Tana gab da shiga falon ne ta jiyo muryar Jalal.
"Ummi".
Da sauri ta juyo tare da cewa.
"Yauwa Jalal ɗaukar muku abinci tun ɗazu ku nake tunawa".
Kanshi ya sunkuyar yana kallon yadda yake ɗigan ruwa.
Dinning table suka nufa.
Foodflaks ɗin ya ɗauka tare da plate kana ya juya ya fita da sassarfa.
Yana fita Ummi ta meda ƙofar ta rufe kana ta koma ɗakinta.


A can ɗakin Sheykh kuwa.
Kallonta yayi tare da cewa.
"Bappa ya baki tabsir a kan surar ne?".
Da sauri tace a a.
A gogon hannunshi ya kalla kana yace.
"Kina son ki san abinda Allah madaukakin sarki yake cewa a Suratul Noor ɗin?".
Da sauri tace.
"Eh sosai ma."
"To tashi muyi sallan isha'i sai in fassara miki ita ko a taƙaice".
To tace kana ta miƙe.

Bayan sun idar da sallan isha'i sukayi addu'o'in kana ta miƙe tayi shafa'i da wutri".
Sannan ta zauna tana tasbihi.
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana ya meda kai yaci gaba da Addu'o'in.

Ummi kuwa tuni ta fita tazo kitchen.
Gashin tukunya mai masifar daɗi da ƙamshi tayiwa zabuwar.
Bayan ta kwashe robon, ta sake sata ta hasata da kyau.
Gaba ɗaya gidan ya cika da ƙamshi mai tada yunwa.
A wani kekyawan Foodflaks tasa dangwaleliyar zabuwar kana tasa, romon mai cike da ɗan-ɗano da kayan ƙamshi a ƙaramar kula.
Sassayan madarar shanu, ta haɗa da zuma ta gaureya kana tasa a flaks ɗin riƙe sanyi. Kamar yadda tasa yana son zabuwa da madara da zumar.
Plate, cup, spoon, fork, knife, ta jera bisa plate ɗin kana ta kife ɗaya a kai.
Sannan ta jerasu a tray.
Sannan ta fito tazo ta ajiyesu kan dinning table, ita kuma ta ɗebi tuwo da miyar kasenta taci tayi haniƙan kana ta koma cikin ɗakinta ta ɗauki wayarta, ta kirashi ta shaida mishi ta gama yana kan dinning table.
"Sannu Ummi ngd matuƙa Ubangiji ya biyaki da mafi kyawun sakamako".
Yace cikin girmamata.
Amin Amin tace kana ta katse kiran.


Ita kuwa Aysha zaman jiran ya ida addu'o'in sa ne ya fassara mata surar take jira.
Kallonta ya ɗanyi, kana yace.
"Tashi muyi nafila".
A hankali tace.
"Nayi ai".
Gyara tsayuwarsa yayi ba tare da ya kalleta ba yace.
"Na sani ai ƙarawa zamuyi ko bakya son ƙarin lada".
Kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ina so mana".
"To taso muyi ba yawa raka'a biyu ne".
Yace yana kallonta.
To tace kana ta miƙa tsaye.

Nafilan sukayi raka'a biyu kamar yadda yace ɗin kana sukayi zaman tahiya.
Bayan sun sallame ne, duk suka gyara zamansu.
Tasbihi ya ɗanyi kana a hankali yace.
"Zo nan".
Ya faɗi yana nuna mata gabanshi.
A hankali ta ɗan musukata sai dai bata iso inda ya nuna matan ba.
Kanshi ya kauda kana ya juyo ya fuskanceta da kyau.
da sauri ta ɗan sunkuyar da kanta.
ƙara matsota yayi har guiwowinshi na gogan nata.
Da sauri yasa hannunsa ya riƙe nata ganin ta yunƙura zata ɗanyi baya.
Cikin juya fuska ba wasa kuma ba tsanani yace.
"Tsaya mana".
Ido kawai ta zuba mishi.
Shi kuwa a hankali ya ware tafin hannunsa na dama ya buɗa yatsunshi kana ya kife tafin hannun kan goshinta.
"Uhhhmmm". Haka ta fidda wani ɗan sauti na tsoron jin yadda tafin hannunshi ya sauƙa a goshinta.
Sama kaɗan yayi da hannun ya zama rabi na kanta rabi na kan goshinta.
Babbar yatsarshi na kan babbar jijiyar kanta na gefen dama.
Doguwar yatsarsa ta tsakiya tana kan jijiyar kanta na gefen hagu.
Cikin ɗan ɗaga sauti kaɗan ya fara karanto addu'ar marabtar amarya ga ango.
Addu'ar Neman Zaman lfy ce.
*"Allahumma inni As'aluka min khairi ha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa a uuzu bika min sharri ha wa sharra ma jabaltaha alaihi".*
Ma'ana
"Ya Allah ina roƙon ka Al'khairin ta, da Al'khairin da ka Halicce ta akan shi.
Kuma ina neman tsarin ka daga Sharrin ta, da kuma sharrin da ka Halicce ta da shi ko akan shi.
Amfanin Addu'ar
Idan ka yi ta.
Allah zai cike Soyayyar da ke tsakanin ku 100%. Zai tsare Shaiɗanu da Miyagu daga cutar da zaman Auren ka da ita da sauran su...

Wani irin nauyinshi mai yawa ta rufeta.
Shi kuwa a hankali ya janye tafin hannunsa daga kanta, kana a hankali yaja ba ya koma mazauninsa.
Jingina kansa yayi da jikin gado kana murya can ƙasa yace.
"Ɗauko min abinci a can falo Ummi ta ajiyeshi bisa Dinning table ki kawo min shi nan ɗinan!".
Da sauri ta miƙe kamar dama umarnisa take jira.

Ƙofar fita ta nufa. A hankali ya bita da idanu har ta ɓacewa ganinsa.

Meda idon yayi ya lumshesu.
Yana mai jin zuciyarsa na bugawa.
"Meyasa lokaci ɗaya rana ɗaya, zuciyashi da jikisa suka amince da ta zamo sutura a gareshi, shima ya zama sutura a gareta kamar yadda Allah maɗaukakin sarki yace.
Ya akayi yakejin yau zai iya haɗa shimfiɗa da ita, meyasa ya yanke wannan hukuncin na tabbatar da ita matsayin matarshi ta sunna suturarsa?".
Wani dogon numfashi mai sanyi yaja ya fesar, yana mai jin yadda iska mai sanyi ke ratsa fatarshi.

Ita kuwa Aysha a tray'n ta ɗauka ta nufi falonshi da nufin tana ajiye mishi zata juyo.

Tana shiga ta sameshi yadda barshi haka ta sameshi.
Zaune,
ta jiye tray'n a hankali, shi kuwa tuni ya miƙe tsaye.
bakin ƙofar ya nufa, tsayawa tayi ta jira ya fita kafin ta fita.

Can babban falon ya nufa, tana biye dashi a baya.
Ƙofar falon ya rufe, tare da addu'a kamar kullum.
Ya juyo kenan sai ya ganta tana ƙoƙarin shiga falonta,
Yafitota yayi da hannunsa tare da cewa.
"Zo". Yayi mgnar a hankali.
juyowa tayi ta nufi inda yake a zatonta ko wani abun zai sa tayi mishi.
Tana isa wurin yasa hannunsa a hankali ya kamo nata.
Kana ya juya ya nufi Side ɗinsa bayan ya kashe wutan ko ina.
Ita dai tana biye dashi kamar raƙumi da akala sai tsoronshi dake ƙara tsananta a zuciyarta.

Suna shiga falonshi ma ya meda ƙofar ya rufe, nanne ta kalleshi a hankali tace.
"Zanje in kwanta ne bacci nakeji".
Kanshi ya gyaɗa mata alamar to.
Wutan ya kashe da komi na wuta kana ya nufi bedroom ɗinsa da ita.
suna shiga ya meda ƙofar ya rufe da key a hankali tace.
"Zan tafi ɗakina".
jawo hannunta yayi suka iso gaban tray'n kana a ya zaunar da ita shima ya zauna suka sa tray'n a tsakiya cikin hikima da ɗan sakin fuska yace.
"Nawa kika sayi ɗakin ya zama naki?".
Cikin kwaɓe fuska tace.
"Ban saya ba".
Kanshi ya ɗan sunkuyar kana yace.
"Shine kuma kike cewa ɗakinki.
Rau-rau tayi da ida nunta. Tuni sun ciko da ruwa.
Ganin haka ne yasashi ɗan matsowa ta inda take kana a hankali yasa hannunshin ya jaw...!







Littafin GARKUWA na kuɗine Special Group 1k Normal group 300 babbancinsu a yawan posting ne. In special Group kikeso kiyi min TRANSFER ɗin 1k ɗin a asusuna na Jaiz bank 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, in kin tura sai kiyi screenshort na shaidar biyanki ki turo min ta whatsapp 09097853276. Kuma yan 300 ta nan accutan ɗin zaku turo, ku turo shaidar biyanku ta whatsapp. In baki da halin turawa ta Account ki sayi katin Mtn na ɗari uku ki copy numbers ɗin ki turo min ta whatsApp 09097853276 bana son VTU ko transfer'n kati, in kinyi ba ruwana.
Yan special Group Please bandaku a kati mtn ɗin ma. Ku ku bada a POS a tura.




By
*GARKUWAR FULANI*
[3/17, 9:03 PM] +234 806 559 0880: Ya jawo hannunta na hagu ya haɗe da nashi hannun.
Kana a hankali yace.
"Kici abinci sai muje in rakaki, tunda bakya tsoron kwana ke ɗaya ko?".
Da sauri tace.
"Eh bana tsoro".
Foodflaks ɗin ya buɗe tare da cewa.
"To kici abinci tukun, ba kyau kwanci da yunwa".
A hankali tace.
"Na ƙoshi ɗazu da muka gama girki naci abinci".
Plate ya ɗauka.
Kana ya buɗe kular,
yasa Fork ya soko zabuwar ya ɗaura kan plate ɗin kana yace.
"Me kuka dafa?".

"Tuwo ne". Ta bashi amsa a gajarce da kuma yanayin tsoronshi.

"Miyar me". Yace mata yana mai kallon ƙwayar idanunta.

"Miyar kase ne".
Kanshi ya ɗan juyo ya kalleta kana yace.
"Uhumm shine ko ki kawo min".
Shiru tayi, shi kuwa ƙaramar kular ya buɗe.
romon ya ɗan sa a gefen plate ɗin.
Kana yace.
"Uhumm duk wanda yaci shi ɗaya shi ɗaya zai mutu ai".
Ya ƙare mgnar yana murmushin gefen baki".
Still shiru tayi.
shi kuwa, cikin son sama mata nitsuwa dan ya lura ta firgita da shi.
A nitse yace.
"Rowa ba kyau".
Cikin sanyi tace.
"Ai nasa maka, yanzuma na sameshi a can, in kawo maka in kana so?".
Kanshi ya jujjuya kana yace.
"A a, saida na roƙa meyasa tun ɗazu baki kawo min ba".
Ɗan kallonshi tayi a fakaice kana tace.
"To ai naji kace Ummi ta gasama zabuwa".
Kai ya jinjina alamun gamsuwa kana yaci gaba dasa Fork yana saɓule kasusuwan zabuwar yana turesu gefe sai tururi da ƙamshi naman yakeyi.
Ruwa kuma har yanzu tsugashi akeyi.
Saida ya gama saɓule sokokin ya zare ƙasusuwan ya medasu gefe, kana ya tura mata plate ɗin gabanta, sannan yace.
"To muci, sai ki tafi tunda bakya tsoron Jahan yazo ya sameki a ɗakinki ke ɗaya."
Cikin sanyi tace na ƙoshi".
Kanshi ya ɗan kauda kana, ya fara cin naman da sauri-sauri kuma yana taunan da ɗan ƙarfi kamar dai yadda ko yaushe inda fushi a zuciyarsa haka yake komai.
Ta fuskar ibadace kawai fushinsa baya tasiri bare ya sashi yin abu da gaggawa ko da karfi.
Duk fushin da yake ciki, in dai ya fuskanci abu na ibada ne to a take nitsuwarsa ke dawowa.

Kaɗan yaci kana ya tsiyayi sassanyan madara da zumar nan, cikin kofi, ya kafa kai bai ajiye ba saida ya shanye.
Kana ya sake tura mata plate ɗin gabanta, sannan ya cika mata kofin da madarar zuma, kana ya miƙe tsaye tare da cewa.
"Zan shiga wonka in kin cinye kafin in fito to na miki al'ƙawarin zan buɗe miki ƙofar ki koma ɗakin naki, in kuma kinƙi cinyewa to dole a nan zaki kwana".
Yana faɗin haka ya shiga bathroom.


Shiru tayi tana nazartan kalamansa, da kuma abubuwan da suka wakana.
Wannan nafila raka'a biyu da addu'arga da yayi ya ɗura mata ruwa a cikinta, ya kuma kaɗa mata hanjin cikinta tsoronshi ya rufeta.

Ta lura gaba ɗaya ya sauya komanshi na yau wani sabon al'amari ne.
Jawo plate ɗin tayi sabida tasan ya fita sanin girman al'ƙawari da mahimmanci cikashi.

Fork ɗin tasa tana sokan naman tana sawa a baki tana tauna tana haɗiyewa, sabida ɗanɗanonsa yayi mata daɗi.

Ci takeyi tana kallon ƙofar Bathroom ɗin.

A hankali ta ajiye fork ɗin kana tasa hannunta ta ɗauku cup ɗin madarar, tasa a baki.
Ido ta lumshe sabida wannan shine haɗin da tafi so.
Sabida dashi Ummey ta raineta.
Zuƙeshi tayi har kusan rabi.
Kana ta janyeshi daga bakinta, tare da buɗe idonta data lumshe cikin sanyi tayi wata gyatsa mai tabbatar da ƙoshi.

Dai-dai lokacin kuma ya fito daga bathroom,
daga ƙafarshi ta fara kallo har zuwa sama.
wasu tattausan riga da wondo masu masifar kyau Sky blue ne mai ɗigo-ɗigon fari.
Wondon dogone har ƙasa rigar kuma irin mai hular manne ya kwantar da hulan a bayanshi bisa kafaɗunsa.

Hannun rigar yan dadai.

Wani irin ƙamshi yakeyi mai masifar daɗin shaƙa.
Sejenshi yayi lib sai sheƙi yakeyi.

Kanshi ya ɗan jujjuya kana yace.
"Kada ma kiyi ta turawa a dole, barshi kawai kin faɗi sharaɗin.
Janye plate ɗin yayi kana ya juye naman cikin kular.
Cikata mata cup ɗin yayi da madarar zuman kana ya ture tray'n can gefe, sannan yace.
"Shanye madarar kizo ki hau gado ki kwanta".

Tura baki tayi alamun zatayi mgna, sai kuma tayi shiru ganin ya shimfiɗa sallayarsa can gefe, ya kuma ɗauki al'ƙur'ani,
alamun karatu zaiyi.

Hakane yasa tayi shirun.
Shi kuwa karatu ya fara kamar yadda ta zata.

A hankali tasa kofin a baki taci gaba da shan madarar, tanayi tana lumshe idonta, sabida haɗin yayi iri ɗaya sam dana Ummeynta kamar itace ma ta haɗashi.

A hankali ta shanyeshi tas, kana ta ajiye cup ɗin kan stoll dake gaban gadon.

Zama tayi tana jin ƙira'arsa mai daɗin sauraro.
Ƴar ƙaramar wayarshi dake gefenta ta kalla, ƙarfe goma harda rabi.
Zuwa yanzu kuma ruwan saman ya tsaya cak sai walƙiya da rugugin da akeyi tako ina wanda haka ke nunin da hadarin bai gama hucewa na zubda ruwanba, ko ma wani hadarin ne ke tasowa daga ƙasa.

Wani sassanyan hamma tayi mai cike da bacci.
Inda yake ta kalla, sam hankalinsa baya kanta.

Hakane yasa ta miƙe a hankali, sabida hankalinta ya ɗan kwanta dashi ganin bai kulata ba.

A hankali ta zagaya can gefe, ta zauna bakin gadon.
Tana mai lullumshe idanunta.
Minti talatin tsakani ta ɗan gyara zamanta ta mirgina ta kwanta, kana ta bashi baya.
sannan ta gyara ƙaton hijabinta ta duƙunƙune a ciki.

A hankali take jiyo muryarsa yana karatun.
Shi kuwa Sheykh duk abinda takeyi yana sane bai kulata bane, dan yana son ta nitsu.

Sha biyu dai-dai agogon wayarsa ya nuna masa.
A hankali yayi addu'an samun zuriya ta gari da Addu'o'in kariya da kuma cikar burinshi ya shafa sannan ya miƙe ya ninke sallayar,
ya ajiye al'ƙur'ani.
Kana ya tako ya iso jikin gini, gudun A/C ya dai-dai-ta kana ya kashe wutan ɗakin.

Sannan ya kunna hasken wayarsa ya nufo kan gadon.
A hankali ya zauna a bakin gadon bakinsa ɗauke da tasbihai.

A hankali ya ɗaga hannunshi ya haɗesu kana ya buɗe tafin hannunshi yayi addu'o'in bacci ya tofa, ya shafawa jikinsa.
Kana ya hawo saman gadon da kyau.
Cikin sanyi da nitsuwa ya isa inda take.
A hankali yasa hannunshin ya fara jan ƙaton hijabin dake jikinta.

Da sauri tasa hannun ta ta kamo nashi,
sabida dama baccin nata ba wani nauyi yayiba.
Jin yadda ta riƙe hannunshi ne yasa ya sunkuyo ya kawo bakinshi kusa da kunneta kana yace.
"Addu'a zan shafa miki, kuma bazan shafawa hijabiba".
Cikin muryar bacci tace.
"Sanyi nakeji ai".
Ci gaba da janye hibajin yayi tare da cewa.
"In na shafa miki sai ki meda".
Sake mishi hannun tayi kana, tayi shiru tana jinsa yana karanto addu'o'in yana tofawa a tafin hannunsa.
Saida ya gama kana ya sunkuyo ya kife tafin hannunshi kan fuskarta. Ya fara shafawa daga saman kanta har zuwa ƙasa kana har bayanta.

A hankali tace.
"To bani hijabin".
Konciya yayi tare da cewa.
"Yayi nisa".
Shiru tayi tana jin wani irin fitinenne ƙamshin jikinsa da sanyin ɗakin suna ratsata.

A hankali ta fara fidda numfashi.
walƙiya kuma in ya haska har cikin ɗaki.
Har yana ɗauke ido.

Hannunsa yasa ya kamo hannunta na dama ya joyota rigingine.
Ɗan sunkuyowa kanta yayi.
Hakan yasa suka ɗan fidda numfashi a tare,
Cikin nitsuwa taji ya manna mata kiss a goshinta,
tare dasa tafin hannunsa bisa nata tafin hannun.
Cikin wani irin sassanyan numfashi ya cusa kanshi tsakankanin wuyanta da kafaɗarta hancinshi ya manna kan fatar wuyanta, idonshi ya lumshi tare da ƙara shaƙan ƙamshin jikinta.
Iya kuwa Aysha wani irin harbawa zuciyarta ya fara can ƙasa yake.
Dib-dib-dib.
Shi kuwa Sheykh a hankali ya dawo da kanshi kan fuskarta.
ƙasa yayi da bakinshi.
Harshensa ya ɗan zaro ya manna da tattausan lips ɗinta,
lasarsu yayi tare da fidda wani matacce sauti.
"Hiehhhhhhh".
shiru tayi kamar mai bacci,
sai kuma taji ya zira mata harshensa cikin bakinta,
A hankali ya lalimo tong ɗin ta wanda haka yasa jikinta ya fara tsuma rumtse idanunta tayi da ƙarfi jin ya,
naɗe tong ɗinta cikin nasa, tare da fara tsotssarshi tamkar ya samu tom-tom mai yaji.
Ƙasa yayi da hannunsa cikin wuyan rigarta yasa yatsunshi yana neman inda zip ɗin.
gaban rigar tata yake.
meda hannunshi yayi ya tallabeta da kyau.
Kana yasa yatsunshi biyu kan zib ɗin gaban jacket ɗin.
hannunshi yasa cikin gashin dake wuyan jacket ɗin.
Zib ɗin ya kamo kana yaja yayi ƙasa dashi, yayinda kuma tong ɗinsa na kanainaye da nata.
da sauri ta riƙe hannunsa tare da alamun kada ya cire mata shi.
Bai kulata ba kuma bai sake zib ɗin ba.
a hankali ta kuma riƙe hannunsa tare da fara jujjuya kanta.

Wani kiss ya ƙarayi mata mai cike da sabgogi masu birkitarwa.
A hankali ya ture hannunta kana ya zuge zip ɗin da ƙarfi yayi ƙasa dashi.
kana ya buɗa rigar tare da wareta.
shiru tayi tana jinsa sabida karkarwan da jikinta keyi ya fara yawa. hannunta ya zare cikin hannun rigar, ya zare shi kana ya jefar dashi gefe.

Ya rage daga ita sai Baby top da jeans ɗin jikinta.
zare bakinshi yayi daga nata.
Haka yasa ta juya da sauri ta bashi baya tare da haɗe hannunta a ƙirjinta ta ƙanƙame kanta gam tana jin yadda zuciyarta ke buga lugude.
shi kuwa matsowa ya kumayi a hankali ya manna ƙirjinsa da bayanta,
Ɗan ronƙofowa yayi kanta ya cusa fuskarshi tsakanin wuyanta da kafaɗunta.
yana shaƙan ƙamshin turaren dake jikinta hannunshi ɗaya kuma bisa cikinta ya ɗaurashi a hankali murya can ƙasa yace.
"Aish!". Shiru tayi ba amsa mishiba, sai wani tsuma da jikinta keyu.
"Aich". Ya kuma kiranta a hankali cikin kunnenta.
Murya can ƙasa tace.
"Na'am".
Kanshi ya ɗan manna da fuskarta kana a hankali yace.
"Bana son wanna shigar a irin ya wannan lokacin".
Kawai ta tsinci bakinta da cewa.
"Kayi haƙuri".
Kafaɗarshi ya maƙe tare da cewa.
"A a bazanyi haƙuri ba."
A hankali murya na rawa tsoro da sanyi tace.
"To Yah Sheykh ya zanyi".
Ƙara manneta da jikinsa yayi tare da cewa.
"Cireshi zanyi".
Da sauri tace.
"Yah Sheykh".
Bai

2 Comments On GARKUWA
avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

avatar
nafisa-9-6

1 year ago

Reply

Masha Allah

Please Login or Register in order to submit comment