Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏNAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾



*1-5*

Bismillahir Rahmanir Rahim
Alhamdulilah Allah kulli Halim.

Da sunan Allah mai rahama da jin kai duk kan yabo ya tabbata ga Allah da kuma annabin sa Muhammad (SAW).

Ina godiya da Allah da ya baninikon kammala *MIJIN UMMUNAH* Ya bani damar fara wani sabon littafi *NAJWAH*

To Alhamdulillah ina godiya ga rabbil samati wal ardi. Kuma ina rokan Allah ya bani ikon farawa lafiya tare da kammalawa lafiya
*Ameen*

Ya Allah ka jagorance ni wajen mika sakon da nake son mikawa. Allah ka shigen gaba.

Allah ka sa mu gama lafiya.
*Ameen!*

Yau gani na shigo da wani sabon littafi me suna *Najwa*

*ASMA'U HUSNAH* nayi niyar farawa to Allah yayi *Najwa* ne zai fara zuwa ina fatan zaku biyo ni cikin dan jin me ya kunsa

*Najwa* labari ne wanda na kirkire shi bakoyi rayuwar kowa ba.

Ni na zauna na tsara ban juua labarin wani ko wata ba. Hasali.ma sai zama da nayi na tsara.

In wani yaga nayi irin rayuwar sa to banyi dan shiba.

Ni na kageshi kuma ina fatan ya fadakar sannan ya nishadantar.
Allah yasa Ameen.

*Nagode*



.

Dedicated to u Sis *Rashida A Kardam.*
*Aunty Rash*

Allah ya daukakai ya sa kifi haka yasa ki gama da duniya lafiya. *Aunty Rash!*

Allah bar mu tare ya kara mana dankon soyayya da zumunci Sis *Rash*





Addu'ar ta gareki baza ta taba karewa ba. *Mahaifiya ta abar alfahari na a ko ina*

Allah sanyaya miki zuciyar ki yasa miki farin ciki ya saki a gidan aljanna.
*Mommy nah.*

Ur love make me feel like crazy.
So much love u dear tah.

Tnx for all ur supporting *Mamah!*

Kanwqta bazan manta dake ba. Kina sona kina taimakona. Kina ddamin gwarin gwiwa Nagode sosai.

*---*--*--*--*--*--*
Babban falo ne wanda ya hadu iya haduwa, Manyan kujeru ne a dakin bakake da ruwan zaiba.

Haka nan komai na adon dakin ruwan zaiba akai masa ado dashi.

Zaune take akan kujera, sai danta dake Kwance akan cinyar ta sai shaggwaba yake zuba mata.

Baki ne amman bakin nasa me mkyau ne, wanda ya dace da tsarin halitar sa ta ba fulatani.

Dogo ne sannan yana da faffadan kirji, Yana da manya idanu da dogon hanci bakin sa karami dashi, sai girar sa dake cike kansa ma gashi ne kwance irin na yan indian.

"Mami ni dai gaskiya muje kano wannan satin kinsan fa muna da bikin abokina."

Ya fada cikin shagwaba. Mami ta ce,
"Naki, bazani ba ince wancan satin ki kayi muje."

"Kiyi hakuri. Dan Allah!"
Najib ya fada yana daga kan kafar ta,

Mami ta ce,
"Aah in Dadyn ka ya yadda."

"Nasan zai yadda ma tinda sauran sati biyu ya dawo."

"Kai ni na fasa ma."
Mami ta faa tana kallon fuskar sa.
Fuska ya bata.

Ya ce,
"Mami na please kinji,"

Murmushi Mami tayi, ta ce,
"To shikenan zan fadawa Dadyn naka sai yadda mukayi."

Dariya yayi dan yasan Ddy ma kamar ya bari ne.
"Zan ma same shi tukunna."

Murmushi tayi Kawai.
"Wai kai sai yaushe zaka fito da matar auren taka."

Murmushi Najib yayi, ya ce,
"Mami ai kema kin sani. Addu'ar ki nake jira Allah ya bani irin wacce nake so."

Itama Mami murmushi tayi, ta ce,
" *Najib* kenan! Addu'a kullum munayin ta sai dai lokaci da muke jira."

Dariya Naijb yayi, ya ce
"Yauwah Mami na. Mami ina da son samun mace ta gari wacce zata kula da tarbiyar yara na."

"Allah baka *Najib* "
"Ameen!"

"Son kayi hankali da har kake hangen yarinya me tarbiya dan samun tarbiyyar yaran ka."

"Wallahi Mami, kyau bai dibata nidai nasamu yarinyar yar mutunci me hankali da nutsuwa, mai ilimi kuma me amfani da shi"

"Masha Allah! Nima zan samu zuri'a ta gari kenan. Allah ya baka mace ta gari."

Juyar da kansa yayi, yana kallon ta, sannan ya ce,
"Ameen! Mami nah. Bari naje nayi wanka zan fita."

"To *Najib* "

Fita yayi ya nufi bangaren sa. Waje ne guda wanda yake kamar gida. Daki ne guda daya na bacci sai falo da ban daki a falo da cikin daki.

Dakin a gyare yake sai kamshi dake tashi. Komai na dakin fari ne tas dashi. Kamar a lokacin aka zuba su.

Ban dakin sa ya shiga yayo wanka ya dauro alwala.

Yana fitowa ya goge jikin sa ya zauna ya shafe jikin sa da mai me kamshi ya feshe jikin sa da turaruka.

Farin jeans ya dauko da farar T-shirt sai takalmi boot da ya saka shima fari. Glass ya dauko, fari tas dashi ya saka.

Turare ya kara fesawa sannan ya fito falo. Gefen Mamin sa ya zauna.

Mami ta kalle shi, sannan ta ce,
"Masha Allah gaskiya yaron ya hadu, kyaun sa ya kara bayyana.

Murmushi yayi, yace,
"Mami nayi kyau kenan."
"Masha Allah! Kayi kyau yaro na."

"Nagode bari naje."

"Ince gun suruka ta zakaje,"
Mami ta tambaya da tsokana.

Murmushi yayi, ya ce,
"Mami ban da ita ai. da nayi Budurwa ke zan fara fadawa"

"Allah ya sa."
"Insha Allahi!"

Ya fada yana mikewa. Kumatun sa ya mika mata.

Sumbatar sa tayi. Murmushi yayi.
"Nagode Mami na sai na dawo.

Harabar gidan ya nufa, katon waje ne wanda zaici akalla motoci guda goma.

Wajen wata mota ya nufa, baka wulik da ita, sai sheki take yi.

Drivern gidan ne, ya nufoshi da sauri
"Barka da zuwa Alhaji. Dan Alhaji."

Murmushi yayi, ya ce,
"Ya akayi dan juma."

"Ranka ya dade ina zuwa kuma."
"Gari zan dan zaga."

"Nazo na kai Kane."
"A'ah aboki na. Nagode sai na dawo."

"Toh dan gidan Alhaji. Allah kiyaye hanya Allah ya dawo dakai lafiya."
"Ameen! Ga wannan."

Ya zaro kudi a aljihu ya mika masa.
"Nagode Alhaji nah."

"Ba komai."
Ya bude masa kofa, ya shige.

Baba me gadi na hango sai ya bude masa gate
"Sannun ka dan Alhaji. Allah kiyaye hanya."

"Ameen Baba ya aikin."
"Lafiya Alhamdulillah."

"Kai ma ga wannan kaci goro."
"Nagode Alhaji Allah kara budi da daukaka."

"Ameen!"
Ya fice.





*INDABAWA*

ο»Ώο»Ώ*NAJWA*



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*





🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


PAGE *11-15*






DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

SO MUCH LOVE U









"Honey!"
Dady ya fada daga dayan bangaren.

Ido Najib ya zaro ya sheke da dariya.

Hararar sa Mami tayi. Ta amsa da
"Na'am sweety nah'

Ido ya kara warewa yana dannen baki dan kar dariyar sa ta fito.

Kai Mami ta dauke. Ta maida hankalin ta kan wayar.
"Baby na kina lafiya ya gidan wallahi sai kewar ki nake."

Wani murmushi ta saki me kayatar wa.Β  Ta ce,
"Nima haka ya aikin?"

"Aiki Alhamdulilah! amman ba kamar yadda zaiyi sauki ba in kina gefe na."

Mami ta rausayar da kai. ta ce,
"Ayyah kayi hakuri ai yanzu ma kana dauka ina gefen naka."

"Zan na gwadawa."
ya fada daga dayan bangaren.

Sannan ya ce,
"Me kike yi yanzu."

Mami cikin sanyin murya, ta ce,
"Bacci zan kwanta."

Murmushi yayi me sauti sannan, ya ce,
"Kin min kwalliyar da kika saba min."

Ido Najib ya kara ware wa ya mike zai fice. Janyo shi tayi.

Sannan ta ce,
"Wallahi ba inda zaka, sai da nace a'ah ba kaki."

Dady ya ce,
"Ke da waye ne?"

"Kai ma ka sani ai."
Dady yayi dariya dan yadan Najib da tsokana.

"Me yayi miki."
Ya tambaya daga dayan bangaren.

"Ka kira ya nace sai nasa a speaker. Shine yake ta wani ware min ido da yin dariya yanzu kuma ya mike zai fice."

Dady ya kira shi.
"Son!"

Najib ya sunkutar da kai, ya amsa da,
"Na'am Dady!"

"To ai sai ka zauna ka koyi soyayya tinda abinda kake son gani kenan."

Najib ya rufe fuska da hannun sa, ya ce,
"Nifa Dady ba haka nake nufi ba. Kawai hira nake son muyi gaba dayan mu."

"Kai ka sani dai. Ka bari in kayi budurwa da kai na zan na koya maka yadda zaka sace zuciyar ta. Kamar yadda na dauke ta Mamin ka."

Dariya sukayi gaba daya daga nan kuma yake tambayar sa ya aiki.
sai hira ta barke kamar duk suna tare.

Sun jima suna hira sannan sukai sallama. Alwala Mami ta mike tayi ta canza kaya ta kwanta.

Najib ne ya gyara mata rufa sannan. Ya duka gefen ta. Ya ce,
"Mami sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Ta sumbace sa a kumatu.

Ya mike ya kashe mata kwai sannan ya fita.

Dakin sa ya nufa yayi wanka yayi alwala sannan ya haye gadon sa.

Addu'ar bacci yayi ya tofe jikin sa sannan ya lumshe idanun sa.

Karfe biyar nayi ya mike. Bandaki ya shiga ya watsa ruwa sannan ya dauro alwala.

Karatun kur'ani yayi na minti ashirin sannan ya wuce massalaci. Raka'atanil fijir yayi sannan suka tada sallah asuba.

Sai karfe shida ya fito daga masallaci sannan yayo gida.

Yana dawo wa dakin Mami ya shiga. Tana zaune akan sallaya tana jan carbi.

Durkuswa yayi. Ya ce,
"Mami ina kwana."

Mami ta kalle shi cikin kulawa ta amsa,
"Lafiya lou Najib. Ka dawo!"

"Eh Mami."
Ya fada yana shirin Zama.

Kallon sa Mami tayi,
"To tashi kaje ka shirya, kar ka makara bari na shiga kitchen nima."
Ta fada tana Mikewa.

Shima mikewa Yayi, ya ce,
"muje tare."

"Kar ka makara fa."
"Bazan makaraba."

Kitchen suka shiga. Dankalin da ta bayar aka feraye mata shi ta wanke ta bade shi da gishiri ta fara soyawa.

Ruwan tea ya daura wanda ya zuba masa kayan kamshi.

Sai kwai da ya dauko ya fasa. Mami kuma ta miko masa albasar da ta yanka.

Magi ya zuba akai ya soya musu. Tean da ya dafa ya juye afulas. Wani ya dauko ya dibi nashi.

Lokacin Mami ta gama suyar dankali. A fulas ya zuba mata sannan ya juye sauran a wani fulas ya dauko basket ya zuba a ciki.

Tare suka wanke kayan da suka gama amfani dasu. Sannan suka fita dakin Mami yayi wanka ya fito ya shafa mai ya bude doruwar ya dauko wata suit ash colour yasaka ta.

Kansa ya taje, ya shafa masa mai sai kyalli take. Sai bakin takalmi da yasaka.

Mami na zaune tana kallon sa. Sai da ya gama sannan ta dauko turaren ta fesa masa. Sanna ta gyara masa kwalar rigar sa.

Murmushi ya sakar mata. Ya duka ta sumbaci goshin sa.

Sannan ya ce,
"Mami na tafi "

Mami ta ce,
"Muje na rakaka."

Suka fice a daining ya dauki basket din sa da briefcase din sa ya fita.

Yana Fita dan juma ya mike. Yana washe baki.
"Barka da fitowa dan Alhaji."

"Yauwah!"
Ya mika masa hannu sukai musabaha.

Durkusawa yayi yana gaishe da Mami.

Ta amsa masa cikin sakin fuska. Mukullin motar ya amsa, ya tafi ya bude masa.

A sit din gaba ya zuwa abubuwan hannun Sa sannan ya juyo.

Najib ya dubi Mami, ya ce,
"Mami na, sai na dawo."

"Allah kiyaye hanya. Allah bada sa'a!"
"Ameen! Mami nah"

Ya shige motar.

Sai da ta daina hango sa sannan tayi wani part dake gefen can.

Tana shiga wata dattijuwa ta karaso wajen ta.

Murmushi ta sakar mata.







*INDABAWA*

*TNX U ALL*

NAJWA*



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾




PAGE *16-20*



DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

GODIYA MAI TARIN YAWA GARE KI. ALLAH YASA KI GAMA LAFIYA AMEEN.



MASOYA NAGA SAKON KU NAGODE ALLAH BAR KAUNA DA ZUMUNCI.

*AMEEN*







Tana shiga. Wata dattijuwa tayo gun ta.

Murmushi ta sakar mata. "Barka da fito wa Hajiya."
matar ta fada.

Murmushi MamiΒ  tayi, ta durkusa tana gaishe ta.
"Baba ina kwana."

Tsohuwar matar ta ce,
"Lafiya lou. Dafatan kun tashi lafiya. Ya najibullahi."

"Ai daga rakiya nake. Ya dan makara shi yasa be shigo ba."
"Allah sarki bawan Allah kenan. Allah bada sa'a toh!"

"Ameen Baba. Me kuka yi na karyawa ne."
"Kunu da kosai."

"Baba ke dai bakya gajiya da kunu nan."
"Yo ai dashi muka saba Ki bazan tacin wannan dankalin ba. Ya sani basir. Su dai in suna so suna yi."

Mami tayi murmushi ta ce,
"To shikenan. Ina talle da Bara'atu."

"Suna can wai indimo zasu dafa."
"Baba kenan ke bakya ci."

"Ina ni ina abincin yara."
"To bari na shiga daga ciki. Daman gobe zamu tafi kano nida Najib. Shine nace bari na fada miki."

"To Allah ya kaimu goben."
"Ameen. sai anjima."

"To sai anjima."
Mami ta mike tayi ciki.

Wanka tayi sannan ta gyare gidan ta zauna cin abinci.

Karfe sha biyu nayi, sai ga kiran Dady nan. Sun jima suna hira sannan sukai sallama.

Kiran Najib ne ya kara shigowa.

"Son Ya akayi ne?"
"Na kira naji lafiyar ki."

"ina lafiya. Shine kabar aiki ka kira ni ko."
"A'ah Mami na gama aiki sai karfe biyu zamu shiga aiki kuma."

"Ok Allah bada nasara."
"Ameen""

"Kaci abinci dai ko?"
"Yanzu zan ci."

Mami ta bata fuska ta ce,
"Yanzu Son!"

Najib ya marairace. Kamar tana ganin sa. ya ce,
"Eh! Aiki ne ya hanani ci."

Mami ta dan saki fuskar ta, ta ce,
"Oh toh maza kaci kaji."
"To mami sai na dawo."

"A dawo lafiya!"
ta kashe wayar.

Kafin dai ya dawo sai da ya kira Mami sau uku. Bai shigo gida ba sai bayan sallah isha'i.

Dakin Mami ya shige da sallama. Amsa masa tayi tana daga kan sallaya.

Fuskar sa a shagwabe, ya c,
"Mami nagaji."

Harara sa tayi.

Murmushi yayi. ya ce,
"Mami sannu ya gida?"

"Lafiya! Ya aikin?"

Najib ya marairai ce fuska. ya ce,
"Aiki da wahala kiga fa Mami wai sai yanzu na shigo gida yau mutum uku mukayi wa aiki wallahi."

Murmushi Mami tayi, dan tana son yaron ta yana kwazo ba lalaci ba. Duk da tasan beda lalaci.

Tasan ya aikatu amman tana nuna masa kamar ve ba dan kar ya sangar ce da rashin son aikin.

"To Sannu kaji. Allah sa anyi a sa'a. Tashi ga ruwan zafi can, kaje ka gasa jikin ka."
"Toh!"

Ya fada yan cire kayan sa.

Bandakin ya shiga ya gasa jikin sa sannan ya fito. Mami bata dakin.

Mai ya sha a jikin sa ya saka kayan bacci riga da wando.

Kan gadon ta ya hau ya kwana. Bude dakin tayi ta shigo da katon faranti a hannu.

Mikewa yayi da sauri ya karbo mata. Ya ce,
"Sannu Mami. Yau ke kadai kikai girki."

"Yauwah. kuma kaga abincin ka nayi maka ba."

Ido ya bude, yana murmushi, "Wayoo dan Allah fa. Wanne daga ciki."

"Wanda kafi so."
"Wow Mami Allah saka miki da gidan aljanna."

Ya fada yana bude fulas din gaban sa.

Waina shinkafa masa ita ta bayyana. Murmushi yayi. Ya sumbaci mamin sa a kumatu.

Miyar ya bude, wani.kamshi ya daki hancin sa. Ido ya lumshe yana hadiyar yawo.

Miyar agushi tayi wacce ta zuba mata naman kasuwa sai kamshi ke tashi tayi kyau da ita.

Sai lemon karas da tayi wanda ta saka tufa da lemon tsami da madara ya dau sanyi.

Zuba musu yayi suka fara ci. Sai santi yake mata. Har Mami ta koshi shikuwa zurawa yake.

Ragowar ya saka a firij yace da safe zai ci. Mami sai dariya take masa.

"Son Allah ya baka wacce ta iya girki dai dan bakin nan naka ko!"
"Ameen! Mami na."

Dady ne ya kira. Kallon sa Mami tayi, ta ce,
"Nasa a speaker."

Najib ya bude ido, ya girgiza kai ya ce,
"A'ah ku gama gaisawar ku tukkuna."

Dariya tayi ta dauki wayar.

Sai da sukayi kus kus din su sannan ta bude a speaker suka fara hira gaba daya.

Sai da suka gama sannan sukayi sallama. brush Mami tayo ta canja kaya ta kwanta.

Sallama Najib yayi mata. Sannan ya tafi dakin sa.

Yana zuwa ragowar abubuwan da yake bukata ya diba ya hade su gaba daya.



Kamar ko yaushe biyar saura ya tashi yayi wanka ya zauna karatu sannan ya shiga dakin Mami ya ganta zaune akan sallaya tana ta zikiri.




*INDABAWA*

NAJWA*



BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*


🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾


PAGE *21-25*




DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTU RASH*

ALLAH YASA KI GAMA DA IYAYEN KI LAFIYA.
ALLAH KAWO MIJI NA GARI. MUSHA BIKI.
*AMEEN*




Masallaci ya tafi inda bai dawo ba sai karfe shida. Yana dawowa ya wuce kitchen.

Bread ya hada dasu kifin kwankwani da tumatur albasa da kwai yai beakingΒ  nashi sannan ya daura musu tea.

Ya gyara kitchen din ya dauki kayan yayi Dakin Mami dasu.

Fitowar ta a wanka kenan.
Kallon sa ta tsaya yi.

Durkusawa yayi yana gaishe ta. Amsawa tayi cikin kulawa.

"Me kayi ne?"
"Abin kari."

Ido Mami ta bude, ta ce,
"Oh sai kace mace!"

"Ai gara na iya dan ina taya matata."
"Ni kake gayawa haka "

Baki ya danne da hannun sa. Alamar be san ya fada ba. Ya ce,
"Oh ashe ba Dady bane!"

"Oh in Dadyn ne shi baka jin kunyar sa ko?"
"Shi da zai koyan soyayya ma."

"Kaga shige kaje kayi wanka."

Dariya yayi ya shige ban daki kafin ya fito har ta shirya cikin wata super holland din ta ruwan ganye da adon ja da yellow.

Firij ta bude ta dauki masar sa ta nufi kitcehn komai a gyare ta same shi kamar ba ayi amfani da kitchen din ba.

Turara masa tayi sanna. Ta dumama miya.

Yana fitowa ya shirya cikin Jar riga da farin wando, ya bade jikin sa da turaruka sai tashin kamshi yake.

A dai dai lokaci Mami ta shigo rike da masar sa.

Najib ya kalle ta, ya ce,
"Mami me kika dafa mana."
"Masar ka."

"Wow kinsan kuwa na manta."

Ya sauko ya hada mata tea ya tura mata hadin bread din da yayi.

Mikewa yayi ya shafe jikin sa da me, sannan ya saka gaajeren wando da singlet din sa.

Kusa da mami ya koma ya zauna.

Dauka tayi, ta ci. Kallon sa ta tsaya yi. Ta ce,
"Son kai kayi."

Murmushi Yayi,
"Eh! Man ci kiji."

Gustura tayi, ta lumshe ido. Ta ce,
"Uhmm gaskiya yayi dadi."

Murmushi yayi ya hada tea sannan ya janyo masar sa ya fara ci.

"Son ci kaji yadda abin nan yayi dadi."
"Ci ki koshi tukkuna."

Suna gamawa ya tattare kayan da suka ci yayi bangaren masu aiki dashi.

Baba ya gani a tsakar gida gaban ta kofi da faranti.

Karasawa yayi yana. Murmushi.Β 
"Baba ina kwana?"

"lafiya lou Najibullah!"
"An tashi lafiya?"

"Lafiya."
Najib ya leka kwanin gaban ta ya ce,

"Me ake ci ne?"
"Koko da kosai ne."

"Sannu da kokari ga abincin da nayi na kawo miki."
"Kai rabu dani da gamje gamjen nan naku."

"Wallahi kici wannan da dadi."
Ya mika mata.
Karba tayi ta gutsura. Ta ci.

"Uhm uhm wannan abu da dadi yake. Meya sunan sa."
"Bread ne akayi masa hadi ya kika ji dadin sa."

"Ba'a bawa yaro me qiwa."
"To gashi nan dai. Duka naki ne."

"To madallah nagode."
"Kai Baba mene abin godiya anan."

"Ai dole nayi."
"Shikenan bari na shiga ciki yanzu zamu tafi ma."

"To sai kun fito."

Ya mike ya fito da kayan su yasa a boot. Dakin sa ya rufo ya nufi dakin Mami.

Tana tsaye tana yafa mayafin ta. Jakar ta ta dauka, ya amsa.

"Muje ko?"

Murmushi tayi, suka fita. Part din ya kulle ya riko makullin.

Ban garen su Baba suka yi.

"A'ah har kun fito."
Cewar Baba tana mikewa zaune

"Wallahi Baba!"
Mami ta fada tana durkusa. ta ce,

"Ina kwana?"
"Lafiya lou kun tashi lafiya."

"Lafiya lou. Yasu Bara'atu da talle."
"Suna lafiya suna ciki."

Baba ta kwadawa su Talle kira
"Talle, Bara'atu!"

Da sauri suka amsa suna fitowa. Suna ganin su Mami suka zube suna gaishe ta. Sanna suka gaida Najib.

"Baba ai kin fada musu ko?"
"Na fada musu."

"Masha Allah. To zamu tafi sati biyu zamuyi sai mun dawo."

Suka hade baki suka ce,
"Allah kiyaye hanya."

Mami ta Amsa, da,
"Ameen!"

"Baba ga mukullin can bangaren."
Najib ya mika mata makullin.

Karba tayi, ta ce,
"To Allah tsare."

Mami da Najib suka hade baki, suka ce,
"Ameen!"

"Ga wanan."
Mami Ta fada tana mika musu kudi.

"Kayya Hajiya. Ki bar kudin nan. Dan nasan ba abinda zamu nema mu rasa."

"A'ah Baba ki amsa baki sani ba dai."
"A'ah fa!"

Mami ta dan bata fuska ta ce,
"Baba dan Allah ki karba."

"To shikenan nagode Allah kara budi ya kai ku ya dawo daku lafiya"
"Ameen ya Allah!"

Ta fada tana mikewa. Bayan su suka biyo, har wajen mota.


Najib ne ya bude mata mazaunin gaba ya rufe ya koma mazaunin driver

Sai addu'a suke musu ta zuwa da dawo wa lafiya.

Driver sune ya karaso, ya ce,
"Hajiya tafiyar ce!'

"Eh wallahi. Ga wannan kaima."
Karba yayi, ya na mata addu'a"

"Nagode Allah saka da alheri Allah tsare."
"Ameen! Wannan ka bawa yaron can me shara."

Ta kuma mika masa wasi kudin.
"To Allah kiyaye hanya."


*INDABAWA*

NAJWA*


BY *MARYAM S INDABAWA*
*MANS*



🌐HAJOWπŸ“πŸŒ

πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§πŸ‘©β€πŸ‘§β€πŸ‘§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏾✍🏾✍🏾





Page *26-30*



DEDICATED TO *RASHIDA A KARDAM*
*AUNTY RASH*

LOVE U








Najib ne ya bude mata mazaunin gaba ya rufe ya koma mazaunin driver

Sai addu'a suke musu ta zuwa da dawo wa lafiya.

Driver sune ya karaso, ya ce,
"Hajiya tafiyar ce!'

"Eh wallahi. Ga wannan kaima."

Karba yayi, yana mata addu'a,
"Nagode Allah saka da alheri Allah tsare."

"Ameen! Wannan
Mami ta ce ka bawa yaron can me shara."

Ta bashi wasi kufin.
"To Allah kiyaye hanya."

"Ameen""
Najib yaja motar suna dago musu hannu.

Wajen me gadi suka nufa. Shima kudi ta bashi ya dinga musu godiya da addu'ar zuwa da dawo wa lafiya.

Sannan suka dau hanya. Suna tafe suna hira abin su.

A kaduna suka yada zango gidan wata kawar Mami. Anan suka ci abinci sukai sallah sanna suka dau hanya.

Bayan la'asar suka isa saboda ba gudu yake ba gashi sun tsaya a kaduna.

Nasarawa GRA Suka tafi can gidan su. Yana yin horn me gadi ya bude.

yana ta fara'a dan yasan yau akwai gara da zasu kai gida.

Gida ne kato dan ko harabar gidan zaici motoci shida, Sai katon mension sai wani bangaren me kyau daga gefe.

Shi ya fito ya budewa Mami kofa, ma'aikatan gidan ne suka nufo su kowa da fara'a akan fuskar sa.

Suka hau yi musu
"Barkan ku da zuwa."

Su Mami na amsawa, da
"Yauwah!"

Nan suka fara gaishe gaishe. Sai da kyar Mami ta samu tayi cikin gida.

Katon Falo ne, sai matatakalar bene. falon an cika shi da kujeru. Daga gefe wani daki ne da kitchen.

Sama kuma dakunan bacci ne guda uku. Gidan tsab dashi dan duk da basa nan akwai masu kula da gidan.

Sama suka haye kowa ya shige dakin sa.

Wanka suka shige kowa ya gasa jikinsa. Sannan sukayo alwala sukai sallah.

Dakin Mami ya isa. Ya ce,
"Mami sannu ya gajiya."

"Gakiya akwai ta."

Fuska ya dan bata, na rashin jin dadi. Ya ce,
"Ayya sannu bari na kawo miki magani."

Fita yayi daga dakin. Bai jima ba ya dawo ya kawo mata maganin.

Karba tayi ta sha ta kwanta. Kasa ya sauka. Ya dan zaga gidan.

Ana yin magariba ya tafi massalaci bai dawo ba sai isha'i da leda a hannu ya shigo.

Dakin Mami ya shige,
"Son ka dawo."

Najib cikin fara'a da kulawa, ya ce,
"Eh ya jikin?"

"Gajiya ta tafi."
"Masha Allah sannu."

Ya mike ya fita. Kitchen yaje ya dauko, plate da kofuna da kemo.

Dakin ya dawo ya bude ledar da ya shigo da ita.

Gasasun nama kaza ne, sai hadin dankali a gefe juye musu yayi ya zuba musu lemo.

Suka fara ci. Karfe goma Mami ta canja kaya ta kwanta.

Kafar ta ya dan matsa mata sanna yai mata sai da safe.

Dakin sa yaje yai wanka yayo ya kwanta.

Karfe biyar ya mike, wanka yayo sannan ya fito.

Dakin Mami ya wuce! Ya same ta akan sallaya tana lazimi. Juyawa yayi ya wuce massalaci acan yai karatun sa.

Bai dawo ba sai karfe shida.

Yana dawowa dakin Mami ya shige, tana zaune akan sallaya ya same ta.

"Barka da safiya Mami da fatan kin tashi lafiya."

"Lafiya ka tashi lafiya? "
"Lafiya Alahamdulilah "

Ya mike ya hau kan gadon ta ya kwanta.

Bacci ne ya dauke shi bai

Please Login or Register in order to submit comment