Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Dasuri sukace" menene hanyar boka ?
Boka yace ""aiki bazai yuyuba har sai ta aureshi mugani , ko zamu iya !!
Sannan mufada mata duk abun da ya kamata tayi da ka idojinmu , in anyi auran
Hajiya Amina tace " toh badamuwa, zamusa auran nan kusa , boka yace dayafi dan kuwa in ba auran shi tayi ba aiki ba zaiyuyuba ,
Hajiya tace"" toh boka zamu iya tafiya ? Yace eh kutashi kuje ,

Suka tashi sumisumi da jin haushin rashin samun nasara da basuyi ba akan Sadik .

Da haka suka koma gida sunata kulle kullen yanda zasu bullowa Al amarin , Hajiya Amina ce ke fadama Rukkaiya tadinga mishi dabara ta na nunar mishi anfani suyi aure da wuri , Rukkaiyya ta amsa da toh ! Ai hakan zanyi zan ta Jan ra ayinshi da muyi aure cikin gaggawa,

Hajiya Amina tace ai kuwa dayafi , dan ba a bori da sanyin jiki .

Soyaiyya mai karfi tashi ga tsakani Rukkaiya da Sadik , dan har takai Rukkaiyya har gida take biyo Sadik , Har daki , suna hira ,

Wsa wasa, har shaidan yaso yayi tasiri akansu , dan tun Sadik na kokarin ganin ya saita kanshi amma inaa , saidan yayi nasarar hura mishi wutar sha ,war Rukkaiya , Domin kuwa duk Inda mace da na miji suka kebe to fa na ukun su shaidanne ,

Duk da cewar bai Santa a matsayin mace ba , sai dai sunfarantama , junansu ta hanyar wasa , tsakan.

*MUJE ZUWA*😎

*Jan hankalina gareku masu karantun littafin MAHAUKACIN KISHI* *kuyi kokari gani gun gina so a kan turbar da ta dace kar shaidan yayi nasarar dasa ma zuciyoyinku sh ,awar junanku kafin aure ,domin Kuwa bayan aure ana samun matsala ,babba ,yana haifar da zargi da rashin yarda , dan Allah mu kiyaye*

*BANGA COMMENTS SOSSAI AB SABIDA HAKA BAZANYI TYPING DA YAWA BA ,*

*SANNAN BAZAN KARA POSTONG A GROUP DIN DA NAGA BA SA COMMENTS BA DAN KUWA BANGA AMFANIN TUROWA BA TUNDA BAKWA COMMENTS*

*MORE COMMETS*😎😎😎
*MORE TYPING*.....✍️✍️✍️

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺
πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabir
*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 24*

Cikin haka suke gudanar da rayuwarsu , har takai takawo ,Watarana ita tazo wataran shi yaje gidansu in har zatazo to sai ta dafa mishi abinci lafiyaiyye , suna ci suna hira .

Hajiya ce ta lura da yawan zuwan da. Rukkiyya take, hakan yayi matukar bata mata ,yayi fada sossai, tanafadin ya za a ace macece zata dinga zuwa gun namji hira gaskiya ita bata ji da din hakan , ba dan kuwa ta yanke shawarar fadawa sadik cewa dole ya fada mata ta daina zuwa dankuwa hakan zubar da mutuncine , duk da cewa ko da tazo ma bata zuwa gaida Hajiya sai jifa jifa, tunda Hajiya tags Haka tagane cewa ,tabbasa Sadik zai sha fama da Rukkaiyya , Dan kuwa ,taga duk take taketa tajebta , Amma tana fatan ,kar hasashenta yazama gaskiya .

Hajiya ce keta fama yima Sadik fada kancewa ya bar mace ta shigo har dakinshi , tana faman fada tace karta kuskura takara , in kuwa Takara zuwa Ransu zai matukar ba daga ita had Shidin

Jiki A sanyaye Sadik ya ce inshallahu zanmata magan , Hajiya tace " da yafi kam ,

Tunda lokacin ko Rukkaiya tace zata zo sai Sadik yayi kokarin hanata , sai yace" basai tazo ba shi zaizo, haka kuwa yake kullum A hanyar zuwa gidansu Rukkaiya yake .

Kwana A tashi ba wuya A gurin Allah , Sadik ya tura magabatanshi , Anyi magana , A Inda biki yarage saura wata daya yanzu , murna gurin su ba , a magana dankuwa , Sun zaku Suyi aure kamar su hadiye junansu suke ji.

Sadik ne zaune Gun Abokinshi Hamza, Hamza yayi gyran murya yace , uhmm Sadik wai da gaske bikinka saura wata daya , cikin zumudi yace Eh ,Hamza yace" amma , Sadik Nafisa ta ban tausayi naji Ance tana ta kuka dataji anca bikinka ya kusa , Sadik yace hummm daman ai ni bance ina Santa ba kawai dai ita ce taketa wahalar da zuciyarta , Hamza yace" Sadik Amma kasan cewa yarinyace ,Mai hankali ga nutsuwa kowa yana shaidar hankali irin nata, kuma ni wallahi nafi maka sha,awar aurenta , akan Rukkaiyya
Sadik yayi Dariyar keta yace ,Eh lallai sai yau nasan kai dan Adwar Rukkaiyya ne ,toh wallahi ni bazan taba san Nafisa ba kaji na Rantse , Allah ya kiyaye , Rukkaiyya tafi Nafisa komai da komai , Hamza yayi saurin katse shi yace"" hali fa!! Sadik yace eh harda halin , Hamza yace " toh shikenan Allah sa hakan shiyafi Alkhairi dasauri sauri Sadik yace Ai shine ma Alkhairin , Hamza yasa dariya , yace Allah sa! Sadik ya kuma cewa Ameen!!!


*A gurguje*
A yaune dubbanin ,jama a suka shaida daurin auren , Alhaji Sadik
Sule mai turare tareda Amaryarsa, Rukkaiyya Muhammad , Mai dala , Akan sadaki Naira dubu , Dari da hamsin.

Anci, Ansha Ayi bidiri iya bidira ,Sadik ya narka kudi kamar ,hauka A bikin,dan kuwa duk Abun da Rukkaiyya tace tanaso Toh , Sai yabata domin kuwa bakaramin So yakema , Rukkaiyya ba , dinner Reception, da sauran kanan bidi,a, duk anyi ,Amarya Tasha kyau ba laifi .

Inda Ranar lahadi aka kai Amarya gidan , bayan Abokaina sun Rako Ango kowa da kowa ya watse, Akabar daga Amarya sai Angonta,
Sadik ne yashigo daukeda murmishi A fuskarshi , Yamatso kusa da Amaryarshi , yace" ina godiya da Allah subhanahu wata,ala daya A zaurtani, dake A matsayin mata , wallahi yau na tsinci kaina cikin farin cikin da bantaba , Shiga irinshi ba .
Cikeda murmishi , Rukkaiyya ta kalloshi tace" hummm Nima haka ina matukar farin ciki yau dinan ,Sadik yace" yanzu mutashi muyi Alwala muyi sallah koh ? Rukkaiyya ta yunkura ,ta tashi ,sukayi sallah Raka ,a biyu ,bayan sun idar yadafa ,kanta yayi Mata Addu,oi
daga bisani ,yayi mata ,tambayoyin da Addinin musulunci yatanada ,Ango yayi ma Amaryarsa ,

Bayan sun idar ,suka canza kayansu sukasa kayan barci,
Daga bisani Sadik ya dauko kaza ,da Abinsha ya bata taci ,shima yaci.

Bayan sun gama ne suka fara kokarin kwanciya, suka nufi gado suka kwanta cikeda farin ciki .

_Nikam na tattara inawa inawa na bar dakin , Sadik da Rukkaiyya Asuba tagari_.

Washe gari da safe Hajiya Amina tanufi Hanyar zuwa gun boka dan shaidamai , Anyi Aure, sai aiki , _
_Niko nace anyi uwar banza_, _Allah karabamu da San_ _duniya_

Tana isa tayi mishi bayani ,
Bayan boka yayi duba dubansa ne , ya tabbatar ma da Hajiya cewa ,sadik ba zai juyu ta sauki ba ,domin kuwa bakaramin Addu ,a mahaifinshi ya kafesu da shi ba , sai dai zaiyyi kokarin gwadawa , ko za a dace!
Dasauri Hajiya Amina tace boka A taimaka Ayi Aikinan , tunda kace sai Anyi Auren yanzu Anyi Auren fah,
Boka ya kara duba dubenshi ,yace " toh kije bayan wata daya kidawo muga , Hajiya Amina da rana yayi matukar baci ,tace" Amma boka Har wata daya?
Boka ya dakamata tsawa yace , keeee!!!!!! Kar kiyi jayaiyya damu
,ba yau mukasaba yimiki aiki ba , muntaba cewa kije kidawo ?, toh wanan Aikin ba karamin wahala bane dashi sabida haka , nace kije ki dawo , in kuma ba haka ba toh Kar ki kara dawowa.

Sauran mutane da nakemusu Aiki Ai suna jin dadin Aikin, had sauran yarannaki ,
amma kuma yanzu kinaso kiyi jayaiyya dani .

Cikin tsoro da nadama Hajiya Amina tace" Allah huce Zuciyar Boka tuba nake zandawo bayan wata dayan Cikin bacin rai boka yace " tashi kitafi ,
dasauri Hajiya Aimna ,ta tashi ta bargun bokan ,

A bangaren Sadik Da Rukkaiyya kuwa, bayan sun tashi , Salma takawo musu break fast , din da Hajiya ta aiko musu dashi , salma bats safe ba ta tafi gida ,
Bayan sun gama break fast ne Rukkaiyya tafara magana , tace"kasan me ?? Sadik ya Amsa daukeda fara,a , A fuskarshi , yace Aa sai kinfada , tace " Nifa Macece mai zafin kishii , ina fatan bakada Ra ayin zama damata sama da daya koh?? yayi shuru Takara dacewa
Dan zuciyata , zata iya bugawa , Dan kuwa bazan taba iya jurar wata ta mallakeka A matsayin miji ba tayi shuru tana kallanshi ,dankuwa zuciyata zata iya bugawa , Dan wallahi tallahi natsani kishiya ,

Cikeda mamaki , Sadik ke kallon Rukkaiyya , yace " toh Rukina ,me yakawo wannan magana ? Rukkaiyya tace " Kawai kaban amsa na ,

Sadik ne yace ,gaskiya ni mutum ne me ra ayin zama da mace sama da daya , Rukkaiyya ta mike ta zabura tace" kan uba

*TOH FAH MAFARIN RIGIMA DA RASHIN ZAMAN LAFIYA ,A GIDAN SADIK*

*muje zuwa*

*in banga comments ba wallahi sai nadau lokaci banyi update ba*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.....*✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️ (MUM FU ,AD*)

*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

_______________________
*PAGE 25*
Rukkaiyya tafara magana tana daga murya tace " kan uba , wlhy Sadik karka fara wannan gangancin na cewa zakamun kishiya, ni kadaice mallakin ks bazan taba yarda ka kawo wata A matasayin kishiyata ba.

Sadik da ya gama suman tsaye , yakejin maganar kamar a mafarki , yace " hummm Haba my Ruki Akan wannan maganar kike ta wani daga murya , Dan Allah kiyi hakuri Abar maganar , yaushe mukayi auran da har kike irin wannan maganar , ko zanyi aure ai bayanzub.

Rukkaiyya tace" ta ina za a bar magana ,bayan baka ce ka janye maganar ba, ooo kana nufin zama kamin kishiyar kenan koh??

Sadik yayi murmishi yace , hmmm Rukkaiyya kinada hankali kuwa?? Miye abun daga hankali a Anan , gaskiya yakamata ki nutsu , ki daina wannan fadace fadacen kina daga mun murya , nifa mijinki ne , in maganar Aurene in har Allah ya kaddara , mun Auren mace fiyeda daya toh kinsan ba makawa sai nayi ,
Amma yanzu bazan iya miki Alkawarin cewa bazan iya Rayuwa dake ke daya ba , sabida bansan Abun da Allah ya shiryamun ba, gara kisani yakara da cewa ", Sannan bazan miki Alkawarin haka ba , na cewa dake kadai zan rayu , Sadik yafada fusace ya tashi ya fita , a gidan.

Wayar Rukkaiyya ce tayi kara , tana dubawa taga mahaifiyarta ce, tayi maza ta dauka , tafara magana tace" yauwa mama dama ko baki kiraba inada , niyyar kiranki ,Hajiya Amina tace " lafiya daiko , Rukkaiyya tace" wlhy mama Sadik ne kiga
dan na tambayeshi , Nace karyamun kishiya shine yafara wasu irin maganganu , Cikin tuhuma Rukkaiyya tace"
wai ma ,mama kinje gurin bokan kuwa?? Rukkaiyya tafa.

Hajiya Amina tace" hummm ai managar da nakiraki muyi kenan , Akwai matsala fah , wannan mijin naki , sai munsha fama A kanshi, Hajiya Amina takwashe duk yanda sukayi da boka ta fada ma Rukkaiyya, takata da cewa , Amma yace zai San Abun yi , Rukkaiyya tayi shuru tace toh shikenan ,mama sai Anjima , Rukkaiyya takashe wayar.

Tana kashe wa tafara kokarin kiran layin Sadik , Takirashi tace" kai daga magana sai ka fita, Sadik yace" toh ai kece kika bata mun rai , Amma yannzu zan dawo komai ya wuce , Rukkiayya ta tabe baki tace " sai ka shigo , Sadik yace " shikenan, Sadik mutunne mai saukin kai , yarinya karama ma zata iya juyashi gaskiya .

Haka Rayuwa ta kasancer kullum Da Dadi ba dadi haka , suke gudanar da Rayuwarsu da Sadik , dankuwa Rukkaiyya batada hakuri ko kadan ga tsiwa da rashin kunya , ko kadan bata ragama Sadik matukar yayi mata ba daidaiba , Dan wani lokacinma , shine yake sakkowa ya rabuda ita taita famanyi yin banbaminta ,dan abun kadan zata fara masifa , bata da hakuri ko kadan ,
Sadik ko Nada hakuri sossai ba komai ne yake bata mai Rai ba dankuwa in watarann Rukkiayya na hararraminta, dariya kawai yake sawa yabar gidan , ko yace " kiyi hakuri , duk da kuwa wani sashi na zuciyarshi baya mishi dadi ko kadan , Amma haka yake dannewa ya hakura .

Rukkaiyya kuwa datagane Sadik na da matukar sha,awa , shiyasa in sunyi fada take horashi tanan ,
Dan wataran in yana bukatarta taita mita tana fadin shi yafiye takura ,

Haka wataran in sunyi fada zai saukko Dan kanshi yanemeta , ita ko taita shan kanshi tana ji dakai , har saiyya samu ta biya mishi bukatarshi, ta lallami.

Wasawasa yau har sun yi wata daya ,
Hajiya Amina ko damadai jira take yau su kai wata daya ta koma gidan boka , Dan kuwa har kirga kwanaki take , Dan ta je taji ya ake ciki gun boka ,
Da sassafe Rukkaiyya ta kirata tace mama yau fa wata daya kenan da maganar zuwa gun bokan nan Dan naga da Alama in ba fara juya mutumin nan nayi ba Abun bazai tafi yanda mukeso ba
Hajiya Amina tayi murmishi tace " Rukkaiyya kenan, ai ni nafiki zumudi inje gun bokanan,Dan kuwa yanxu haka ma nashirya zan tafi, kenan,cikin jin dadi Rukkaiyya tace yauwa mamana shiyasa nake sanki ,Fatan samun Nasara , Hajiya Amina ta amsa da Ameen!!!

Hajiya Amina ce zaune gun boka , bayan boka yayi 'yan bigebigenshi ne , ya kallo Hajiya Amina yace" , Tab nifa wanna mutumin bazan iya dashi ba , Dan yanzu haka bakiga Aikin da mahaifinshi yake A kanshi ba bakaramin Addu,oi ya kafe yaranshi dashi ba , yakara da cewa ""
babban Malami irin wannan jaa dashi ba karamin wahala bane , sabida haka ki tashi ki tafi kawai bazan iya ba , babu Aikin da yataba bani wahala kamar wannan sabida haka kije kawai ,

Cikin tashin tashin hankali Hajiya Amina ta zaro ido tace " boka dagaske ,
boka ya daka mata tsawa yace " kitashi kitafi nace bazan iya Wannan Aikin ba na ce miki , kuma kije duk wani gun boka ki ji ko zai iya , zai ce miki bazai iyaba duk aikin da ya gagareni toh faa bakaramin aiki bane sabida haka kitafi , in naga da hanyar da za ayi ayi aikin zan kiraki .

Da sauri Hajiya Amina ta tashi tabar gurin , zuciyarta kamar ta fashe dan bakin ciki,
Tana komawa gida ta sanar ma da Rukkaiyya da 'yan uwanta halin da ake ciki , takara da cewa" "tunda boka yace bazai iya ba , ai sai kiyi da kanki , Rukkaiyya tace" dakaina kuma mama!! , ta ya zan iya yin Aikin da kaina , ? Hajiya Amina tace " ta hanyar daga mishi hankali ,da Nuna jarumta , sanna kar ki taba daukan rainin hankalinshi , tunyanzu kifara muna mai kinda *MAHAUKACIN KISHI*, ki nuna mishi a tsaye kike, zaki iya aikata komai a kan kishi ,

Rukkaiya ta dau hudubar da mahaifiyarta tayi mata , cikeda gamsuwa,


Abun da masu karatu Baku sani ba tunda Sadik ya auri Rukkaiyya ,Alhaji sule bai zauna haka ba dankuwa ba karamin aiki yake akai ba , ya tsaya tsayin daka ganin ya tsirar da Sadik daga sharrinsu ,
Dankuwa tunda Sadik yazomai da maganar Auren, yayi istihara akai , yagano cewa Hajiya Amina ba a zaune takeba , shiyasa yayi iya kokarinshi ganin ya toshe duk wani hanyar da zasubi ganin sun mallake mai d'aa
Ko da za ayi Auren ya zuba musu ido ne kawai Dan kuwa yasan waye Hajiya Amina, bayaso yajaa da ikon ubangiji , shiyasa bai jaa , A maganar Auren ba .

Duk sanda Sadik yazo wani lokaci sai Alhaji Sule yabashi Ruwan Rubutu da kuma tsari , Sadik bai taba tambayarshi dalili ba , dankuwa yana yawan bashi tun suna yara , shiyasa ko Alhaji Sule ya bashi maganin tsari bai cika tambaya Akan na miye bane , shidai kam shaa kawai yake.

Sadik din ma ba bayaba wajan Rike Addu, a Sabida turban da iyayenshi suka daurasu akai kenan , mutum ne me ruko da Addu ,a da Addini ba laifi .
Shiyasa boka duk inda zaibi ganin yayi Aiki Akan Sadik abun yaki, Dan bakaramin Addu,a Alhaji sule keyi ba .

Tunda Rukkaiyya ta yi auri Sadik kusan wata Bihar kenan , bata tako ko kofar gidan Hajiya ba , Dan ko A waya bata kokarin kiranta ,
Hajiya kuwa Abun bai dameta ba danko tasan dole haka zata faru ,shiyasa ta tattarata ta watsar.

Bayan wasu ' yan wattanni Rukkaiyya tasamu ciki , murna A gun Sadik ba a magana , cikeda kulawa Rukkaiya da Sadik suke Rainan cikin , har Allah yasa ya girma , Har ta haifi ' yarta mai suna Fatima , amma suna yimata lakabi da khairat,

Ko da ta haihu mutanen layin basu ko jemata barka ba Dan kuwa , basa kulata bare kuma su kula mijinta ,
Dan kuwa tun watarana da tana Amarya ta fara fita ,Sadik zai kaita gidan rasuwa , kasancewar Anyima ,Sadik rasuwa zai kaita tayi gaisuwa .

,Sadik ne yake jiranta A moto , saiga wata matar layin zata wuce har zata wuce ta dawo ganin Sadik yasa tace " bari taimasa gaisuwar mutuwa tana zuwa tayi mishi gaisuwar mutuwa , saiga Rukkaiyya tafito tana fitowa kuwa , ta kutuntuma uban Ashar , tafara zagin matar tana fadin"kee uban me kika tsaya kike ma mijina??

Martar tace," laa Rukaiyya ,wallahi gaisuwar rasuwa namai , kinga ai ba dadi ana tare kanwar mahaifiyarshi ta rasu banyi mai gaisuwa ba koh ?
Aikuwa Rukkaiyya tafara zage zage tana daga murya tana fadin " , toh Dan ubanki daga yau ko kallon mijina karki yarda ki karayi uban meyasa ni bazakizo kinmun gaisuwar ba inyaso sai na fadamishi , Amma in banda munafurrci Ina ruwanki da mijina, toh wallahi daga yau bake ba mijina

kee, bakeba ko yan uwanshi ma baso nake suna kula min mijinaba balle kuma yan anguwa .

Kafin kace me layi an cika fam ana kallo Rukkiayya nata zage zage tana daga murya , Sadik kuwa , yama rasa bakin magana dankuwa , kanshi yagama daurewa yayi shuru yana kallanta , Dan kuwa yama rasa ta Inda zai fara magana
Sadik ne yayi jarumta yadaka ma Rukkaiyya tsawa yace " ke Bako da hankaline ,ki rufemana Baki kafin ranki ya baci .

Rukkaiyya ta fara magani cikin tsiwa tace " bazanyi shurun ba eheee, narantse da Allah banzayi shuru ba ,sai na gama maganata ,

matar kuwa ,kasa magana tayi , banda kuka ba abun da taketi ,tafara maganana , cikin muryar ,kuka tace" kin manta ni fa matar aurece ,me zanyi da mijin ki inada nawa mijin ,daga yi mishi gaisuwar ,rasuwa toh kiyi hakuri in Allah yayarda bazan kara kula mijinki ba tasa kuka tabar gurin ,

Yan layi kuwa tunda suka ga haka suka sha jinin jikinsu , dankuwa ba Wanda take Shiga harkar Rukkaiyya balle kuma mjinta , tunda hakan ta faru ,

*MUJE ZUWA😎*

*MORE COMMENTS* 😎😎
*MORE TYPING*....✍️✍️✍️

*IDAN NAGA RUWAN COMMENTS IN MUKU POSTING ANJIMA IN BANAGANIBA , SAI GOBE KO JIBI*

*STORY ABN WRITTEN BY✍️✍️ ,(MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 26*
Tunda Sadik yaga hakan ya gane cewa lallai sai yau ya tabbatar da abun da Hajiya take nufi.
Yayi saurin daka mata tsawa yace " ke bakida hankaline , wai meke damun ki ne, wani irin *MAHAUKACIN KISHI* Ne dakee , kin haukace ne wai.

Rukkaiyya cikeda masifa tace " eh na haukace in dai a kanka ne ,dan ina *KISHIN* akanka , shine zaka ce na haukace , toh a haukac din ehee.

Sadik ko da ranshi
yagama baci, yace " shikenan sai kiyi duk abun da zakiyi ki karata , yanzu gidan mutuwa, zamuje in kingadama kinutsu in bakiga damaba kar ki nutsu kekika sani, Rukkaiyya taja uban tsaki jikake msstttt, Sadik ko girgiza kai yayi .

Suna shiga gidan rasuwan mutane na taima Sadik magana yana gaisuwa , Rukkaiyya ko hada rai tayi kamar ta fashe , dan yanda mata suke ma Sadik magana jitake kamar ta danna musu Ashar , takeji , dakyar ta iya yi ma mutane gaisuwar , rasuwar , tana gamawa ko ta kara gaba abunta .

Kiran Sadik tayi akan su tafi , gida tunda sunyi gaisuwa,Cikeda mamaki Sadik yace " ke kanwar mahaifiyata ta rasu kice in zo mutafi , ni zan zauna a gun zama makoki ne , Rukkaiyya taki yarda fafur sai dai sutafi , Sadik ko kinyarda yayi yace " bazai yuyuba, Rukkaiyya kamar tayi kuka tace" in har kayi ma wata dariya ko kukayi hira Allah ya isa ban yafemaka ba .

Sadik kam ma dariya abun yaso ya bashi, yayi saurin cewa toh shikenan bazan yi ba .

Rukkaiyya ta wuce ta tafi kamar me shirin yun kuka

Tundaga lokacin ko Abun yafaru ko me yafaru a gidan Rukkaiyya ba Wanda yake zuwa, dangi ma sai dai kawai aje dan Allah da kuma dalilin sadik, dan kuwa kowa na gudun rashin mutunci irin nata.


Bayan shekaru uku ,Rukkaiyya ta kara haifan " ya mace me suna Hafsat suna yi mata lakabi da khairat ,

Rukkaiyya ta daga hankalinta , akan dole sai dai Sadik yasa Sunan Anti Hafsan ta , dole haka Sadik yasa sunan da Rukkaiyya

Please Login or Register in order to submit comment