Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 51*

*_Sorry for the late post nadanyi tafiya ne wallahi_*


Kuka tasa tana fadin haba Alhaji karkayi haka wallahi nayi nadama , kayi hakuri karka yanke hukunci cikin fushi .

Nan ta kallo Hajiya tace," Hajiya dan Allah kisa baki , Hajiya ko da farin ciki fal cikin ranta tace," yoo ke banda abinki kintaba gani anyi saki uku kuma andawo , ai kiyi Hakuri kawai kitafin, tunda ba kofar da zai dawo dake ,toh ko da kofar da zai mai dake ai bazan bari ba, kin manta cin mutuncin da kika mun .

Kuka Anti Hafsa ta kara fashewa dashi .

Alhaji muktar kuwa , yama kasa magana tsabar bacin rai da bakin cikin Hafsa.

Da sallama yaran suka shigo sun dawo daga makaranta .

Cikin rashin fahimta suke Kallan mutanen dake cikin falon, sukace mommy daddy lafiya ??.

Hajiya tayi saurin cewa , ina lafiya kunga kuje ku yi abun da ke gabanku.
Cikin matukar mamaki suka ce, toh wacece kee!!! .

Hajiya tace," Uwar ubanku , baku sanni ba koh ?? suka daga kai Alamar ehh , Hajiya tace," toh nice nan na tsuguna nahaifi ubanku .

Kallo Mahaifiyarsu sukayi ido jajawur , Kanta a kasa, sukace," mommy kikace mana maman daddy ta dade da rasuwa , yanzu kuma ita tace," itace maman daddy .

Sallati Hajiya tafarayi tana fadin, Hafsatu , ni kikayi ma fatan mutuwa Ehh lallai Hafsatu , muntari ,muntari kajita koh , lallai ma .

Kasa daga kai Anti Hafsa tayi balle har ta kallesu ta iya bada ansa.

Alhaji muktar ne ya kallosu yace," bata mutu ba , tanada rai mahaifiyarku ce ta rabani da ita , amma yanzu gata tadawo gareni .

Nan Alhjai muktar yadan basu kadan daga cikin zaman da yayi da Hajara mahaifiyar su Maimuna da kuma abubuwan da Hafsat ta aikata .

Kuka sossai yaran sukeyi , daga bisani sukayi shuru , cikin ransu suna jinjina irin rashin imani irin na mahaifiyarsu .

Cikin Fushi Alhaji Muktar ke fadin , kee!!.Hafsa , nabaki minti talatin maza maza ki barmun gida.

kuma ,yayana zasu zauna taredani , bazaki dauki ko daya ba , gudun karki koya musu mugun halinki na gado, zan nema musu uwa me mutunci, wacce zata basu kyakkyawar tarbiyya .

Hakuri tafara bashi tana kuka, amma ko kallanta baiyyi ba .

kallan Yaran Alhaji mukhtar yayi yace," kuyi Hakuri nasan Cewa ," zakuji ba dadi barin mahaifiyaku gidanan , amma bazan taba iya zama da mahaifiyar ku a gidanan ba , ta cutar dani , ta zalinceni , tasa na cutar da matata matar mutunci , tasa nayi nesa da mahaifiyata tsawan shekaru , tasa na wahalar da 'ya'yan cikina , taya kuma zan iya zama da mata irin wanan , tsawan shekaru , goma sha bakwai bana cikin haiyyacina, sai abun da mahaifiyarku tafada , duk abun data sani shi nakeyi mai kyau ko maras kyau, Sabida Haka , dole in rabu da ita .
Gaba dayansu kuka suke yi babu me ba ma wani hakuri.

Tashi Anti HAFSA tayi tashiga daki tadan hada kayanta , tafito , ta tafi.

Kuka sossai yaran sukeyi na tafiyar mahaifiyarsu , amma tabbas sun San cewa," mahaifiyarsu bata kyauta , bata cancanci duk wani na miji yaci gaba da zama da mace irin wanan ba .
Babu yanda suka iya haba suna gani ta tafi.

Da
A banagaren Sadik kuwa , bayan yafito daga gida ,gidan Hajiya ya nufa.

Bayan ya isa, ya tarar da Hajiya zaune tana lazumi .

Nan ya tsuguna dan gaisheta yace," Hajiya ina kwana .

batare da ta amsa gaisuwar shi ba tace," ka je ka koma ka kara gaida Rukaiyya??.

Sunkuyar dakai Sadik yayi yace," A,a gaskiya , cikin bacin rai Hajiya tace, " akan me ??.

Shuru Sadik yayi baice komai ba .
Cikin fushi Hajiya kefadin ," Sadik wai meyasa kake hakane??, miye damuwarka ?? ,wacce irin zuciya ce dakai haka , bakada hankali ne ?? Matar nan fa matar kace, kuma uwar 'ya'yanka , ko ba komai ai kaje kaduba lafiyarta, ko kana mantawa cewa kaine ummul aba isin kwanciyarta a asibitin ne?? , kasan Allah banasan naji ka ce komai , kana fita, yanzu kaje gida ka daukko matar ka , ka biyo tanan mutafi asibitin , banasan inji ka ce komai maza maza ina jiranka .

Sadik zaiyyi Magana , Hajiya ta daka mai tsawa tace," banasan inji komai maza maza ka tafi.

Dole Haka Sadik ya koma gida dan daukko Aisha .

Dawowarshi gida ya matukar ba Aisha mamaki , cikin rashin fahimta Aisha tace," lafiya kuwa,? naga kadawo gida a irin wanan yanayi??.

Murya a sanyaye Sadik yace", kishirya muje asibiti gun Rukaiyya .

Mamaki karara a fuskar Aisha tace," asibiti kuma da nii ??.
Yace ", Eh umarnin Hajiya ne , kishirya ina waje kisameni a moto , yana fadin Haka yafita .

Daki tashiga ta shirya daga bisani tafito suka tafi .

Gidan Hajiya ya koma , yayi mata horn , da Sauri Hajiya ta fito suka tafi .

Cikin ladabi da kunya Aisha ta gaishe da Hajiya tace," ina wuni ," cikin sakin fuska Hajiya tace," lafiya kalau Aishatu yakike ya gida ??.

Cikin kunya Aisha tace," uhm lafiya kalau Hajiya.

Hajiya tace," kiyi hakuri na tasoki batareda kin shirya ba koh?.

Aisha tace," laa Hajiya badamuwa wallahi ai a shiryema nake, dama kuma inaso inje .

Hajiya tace, " toh shikenan ,Allah shi Albarka , da murmishi Aisha ta amsa da Ameen .

Suka nufi Asibtin.


Anti Hafsa kuwa bayan fitanta Asibiti ta nufa , bayan ta je Abibtin Anti Sadiya kadai tasamu a asibitin.

Rukaiyya kuwa na kishin gide a kan gado , tayi matukar rama sossai , tana dan magana amma kasa kasa in ba ka kawo kunnanka ba ballai kaji ba , ta rame sossai kamar me shekara goma tana jinya , duk Wanda ya ganta yasan ce wa ta gala baita matuka, kamanin fuskarta duk sun canza .

Cikin matsananicin tashin Hankali , Anti Sadiya kefadin ,kee!! Hafsat lafiya naganki haka ??. Ko wanine ya rasu,.??

Kuka Anti Hafsa tasa tace," ba gara ma mutuwa ba Alhaji muktar yasakeni , kuma saki uku , tana fadin haka tafashe da matsanancin kuka .

Cikin rashin fahimta Anti Sadiya tace" yasakeki ?? .

Kada kai Anti Hafsa tayi tace," ehh .

Anti Sadiya kuwa cikin ranta farin ciki sossai tayi , tasan ko ba komai ita daya ce me aure cikinsu , a fili kuwa cewa tayi toh sai kiyi Hakuri , dama ai kinsan hakan zata faru , sai kidawo muci gaba da zama .

Mamaki sossai Anti Hafsa tayi da ganin ko inkula da Anti Sadiya tayi akan halin da ta tsinci kanta , Hawayen fuskarta ta share tace," Anti yanaga ko kinuna da muwa da hakan .

Wani kallo Anti Hafsat ta bita dashi tace," ha,a toh ya kikeso in miki ???, ko so kike in je in CE Alhaji muktar dole sai ya maidake dakinshi ?? ,
yazan miki bakiji na ce kizo muci gaba da zama a gida naba ?.

Anti Hafsa kuwa bata kara ce wa komai ba tayi , shuru , cikin sanyi murya tace," toh kiyi Hakuri ,dan tasan Anti Sadiya ba mutunci ne da itaba sai ta iya ce wa tafasa , baza ta zauna a Gidan ba .
shuru Anti Sadiya tayi batareda ta ce komai ba.

Da sallama su Hajiya suka shigo dakin .

Wani kallan rainin hankali , su Anti Sadiya suka bisu dashi .

Tashi Anti Sadiya tayi daga kan kujerar da take ta kallo Aisha tace," lafiya kika kara zuwa nan , wai ke meyasa bakida zuciya bakida hankali ne?? Ke wacce irin jaka kuma kidahumace , bamun fada miki cewa idan kika kara zuwa nan sai mum miki tsinanen duka ba .

Wani mari Anti Sadiya ta wanke Aisha dashi cikin zafin nama, Anti Hafsa ma ta kife Aisha da Mari, kuka Aisha tasa ta rike fuskarta .

Sadik da Hajiya ko mamaki ma abun yabasu.
Hajiya tace," Hafsa Sadiya me tayi muku haka zaku mareta ,?? Bayan duk cin mtuncin nan da zagin da kukayi mata be isaba sai kun hada da mari kuma?.

Sadik da rashin yayi matukar baci yace," Hajiya abun da nakesan fada miki kenan kika ki saurarata , jiya fa munzo , suka mata irin wanan cin mutuncin , yanzuma kinga sun maimaita , nan ya kallo su yace," Na rantse da Allah duk wacce ta kara yunkurin taba mun mata ,wallahi kun daki igiyar auran 'yar uwarku , kuma abun bazai tsaya a nan ba har sai na dauki kaukkwaran mataki akai tunda ku bakuda mutunci .

Cikin masifa Anti Hafsa ke fadin ka dade baka dauka ba oh kai har kanada bakin dazakayi magana , kamanta abun da kayi ma 'yar uwarmu, ance maka mudinma kyaleka mukayi , kajira warke warta kagani , kana wani ikirarin ce wa zaka saki Rukaiyya , to kasaketan mana seme?? Daman wallahi ko baka saketa ba zama da kai ya kare , babu kai babu ita tunda kai bakada mutunci , kai badan mutunci bane baka gaji arziki ba .

Hajiya kam kasa cewa komai tayi , kanta ya matukar daurewa , tace," Sadik kar inji kace komai mutafi , murabu dasu, Kallan Sadiya tayi tace," Sadiya nagode , har ki kalli tsabar idona ki farfadi magana San ranki , kin kyauta nagode .

Anti Sadiya ta galla harara tace," ba duk tarbiyar da kika bashi bace haka , da kin nutsu kin bashi tarbiya ai da ba haka ba , ke nifa bari kuji daga ke har dan naki wallahi na tsaneku , ni da kin isama da kinsa wanan dan naki yasaken mun 'yar uwa .

Kallan Sadik tayi tace," kai in ka haifu cikin wanan , tanuna Hajiyan Sadik da yatsa , tace," kasaki Rukaiyya .

A wanan karan ran Hajiya yayi mugun baci,
hakan yasata ta kalli Sadik tace," a wanan Karen bazan hanaka ba kadauki duk hukuncin dakaga yadace , tana fadin haka ta rike hanun Aisha da take gefe tana kuka, tace," mutafi , Aisha tabita suka fita.

Da karfi Anti Sadiya tace," Allah raka taki gona umma tagai da asha, dan naki yadauki matakin daya dace din in ya isa.

Ran Sadik yayi matukar baci, idanshi yayi jaa, dan kuwa bakaramin bata mishi rai kalaman Anti Sadiya yayi ba , cikin fushi yace," ni kuwa na haifu cikin uwata , sabida haka na saki matata Rukaiyya saki na har abada.

Yana fadin haka yafita a dakin .

Cikin ran Anti Sadiya farin ciki sossai kamar ta zuba ruwa a kasa tasha tsabar murna , dankuwa tayi haka ne daman da ganganka , dan so take dukkanin 'yan uwanta su fito gidan mazanjensu , itakuwa tanan a gidan mijinta sai abun da ta ce, dan haka dolema ta bazama gurin neman wani kasun gumin bokan da zai kara mata aiki .

Rukaiyya datake kwance takejin abun da suke fada, tayi wani razananan ihu jin ansaketa.......✍️✍️

*MUJE ZUWA MASU KARATU*

*IDAN NAGA COMMENTS KUJINI GOBE IDAN BAN GA COMMENTS BA WALLAHI SAI JIBI KO GATA KO BAYAN KWANA HUDU, IN YI BARCI NA IN HUTA , πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚*.


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING........✍️✍️✍️✍️✍*


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 52*

Ihun da Rukaiyya tasa sai da ya tsorata su Anti Sadiya .

Mikewa tayi ta zauna , tana hakki , hade da nishi sama _ sama, cikin muryarta wacce ba, a iya gane me take fada ,tanuna Anti Sadiya da yatsa tanafadin," kin cuceni , kin cuceni , cikin rashin fahimtar abun da Rukaiyya ke fadi , Anti Sadiya tace," Rukaiyya mene? Ki kwanta barin je in kira likita .

Ko karin tashi Rukaiyya tafara yunkurin yi , da sauri , Anti Hafsa ta riketa , Anti Sadiya kuma tayi saurin zuwa dan kiran likita .

Aman jini Rukaiyya tafarayi , tana wani irin nishi .

Da sauri likitan ya shigo dakin , ganin yanayin da Rukaiyya take yasa shi sauri kiran wasu daga cikin ma, aikatan .

Daukanta sukayi suka kaita dakin taimakwan gaggawa ( Emergency).

Hankalinsu Anti Sadiya yayi matukar tashi , ganin halin da 'yar uwarsu take ciki.

Anti Hafsa ce tace," Anti ai da ma bakiyi saurin ce wa," Sadik ya saketa ba , yanzu ga abun da ya janyo , na tabbata sakin da taji yayi mata ne , yasa hakan ta faru .

Harara Anti Sadiya ta galla ma Hafsa tace," ke baki da hankali ne , dama kina tunanin Rukaiyya zata koma gidan ne , ai gara ma da akayi komai ya kare.

Anti Hafsa bata ce komai ba , dan ta lura ,Anti Sadiya najin rashin mutunci yau dinan , ta tabbata matukar bata yi a hankali ba , zata iya cewa bazata zauna a gidanta ba , gara ma ta bita a hankali .


Bayan Hajiya sun fita , jiran Sadik sukayi a jikin mota, Cikin ran Hajiya kuwa tana mamakin rashin mutunci irin na 'yan uwan Rukaiyya .

Hakuri Hajiya tadinga ba Aisha ,tanafadin Aisha kiyi Hakuri , bansan haka abun zai kasance ba da wallahi bance Sadik ya daukoki muje ba , kuma baku gaya mun cewa sun taba miki abu maka mancin haka ba , kiyi hakuri .

Cikin ladabi , da sanyi muryar Aisha tace," la Hajiya ba komai wallahi komai ya wuce .

Sadik ne yakaraso gurin ranshi a bace yace," Hajiya kiyi hakuri da hukuncin da na yanke , amma nasaki Rukaiyya .

Da sauri Aisha tace," haba kai kuwa yaza ka yanke hukunci cikin Sauri haka , ai a wanan karan ba laifin Rukaiyya bane, bai kamata ka saketa ba a wanan hali da take ciki .

Wani murmishin da tafi kuka ciwo Sadik yayi yace," bazaki gane bane , ni nasan waye Rukaiyya , duk da cewa kema kin ga kadan daga cikin halinta , haka nayi fama da irin wanan hali nata na tsawan shekaru goma sha tara, sabida haka ,bazan iyaba ba , wanan hukuncin shine daidai .

Dan numfasawa Hajiya tayi tace," Allah yasa hakan shine mafi Alkairi ,Ameen sukace .

Bude motar Sadik yayi suka shiga , daga bisani suka tafi gida .


Gida Sadik ya kai Hajiya , bayan ya ajiyeta suma suka wuce gida , gaba dayansu jikin a sanyaye.

A bangaren Rukaiyya kuwa likitoci , ne akanta sossai suna iya bakin kokarin a kanta , dan duk Wanda yaga Rukaiyya tabbas zai iya cire rai da rayuwarta.

Likitocin sunyi nasarar daidai tuwar numfashinta , dan Amman jinin ma da takeyi ya tsaya , Allurai suka yi mata , Alluran da sai tayi kwana biyu zuwa uku batareda da ta farfado ba , bayan sun samata Ruwa .

Dakin Hutu suka kaita , da sauri su Anti Sadiya suka nufo kanta , dan ganin lafiyarta .

Nan likitoci suka shaida musu cewa kar suyi wani abun da zai kuma sata haka , in ba haka ba zata iya rasa rayuwarta , dan a halin yanzu zuciyarta ta kumbura sossai , kuma jininta ya mugun hawa .

Nan suka dan kara gwaja gwajansu , daga bisani suka fita a dakin .

A bangaren su Maimuma kuwa , yau kawai da barin Anti Hafsa gidan sunji kamar a Aljannah suke.

Bayan fitanta wanka sukayi suka ci abinci , dan rabansu da wanka kwana hudu kenan, abinci kuwa sai yaran sun kawo suke ci duk da cewa su suke dafawa .

wunin ranar hira suka dingayi da mahaifinsu da Hajiya , gwanin ban sha,awa.

Sadik kuwa bayan sun dawo gida , kwanciya yayi , yadinga tunani iri_ri .

Gunshi Aisha tazo , tadinga mishi kalaman kwantar da hankali , da lallashi dahaka har hankalinshi ya kwanta .


Wasa wasa yau Satin daya kenan Rukkiayya na kwance a Asibiti , ta farfado sai dai bata magana sossai , kullum sai hawayene ke fitowa a fuskarta , dan likita yayi mata kashedin ce wa matukar takara sa wata damuwa a ranta zai haifar mata da bugawan zuciya , kuma zata iya rasa rayuwarta, hakan yasa idan ta tuno cewa Sadik dinta ya saketa kuma yananan da matarshi , takejin kamar ta kurma ihu , tadingajin zuciyarta na wani irin tafasa , Shiyasa idan ta tuno take kokarin , kawar da tunanin gudun kar hakan yayi sanadiyyar salwantar rayuwarta .

A bangaren Sadik kuwa, kulawa sossai yake samu a gurin Aisha matuka, duk da cewa har yanzu bai Santa a matsayin mace ba , amma yana matukar samun kulawa .

Cikin Daren yau kuma yake sa ran angwancewa da amaryarshi Aisha , dankuwa yaga alamar tayi tsarki , hakan yasa yake matukar farin ciki a yau .

A bangaren Anti Sadiya kuwa , tafara ganin canji sossai gun Alhaji madu , dan duk abun da takeyi kallanta kawai yakeyi , dan shi kanshi a jikin shi yanajin wani irin yanayin da bai San ko na miye bane .

A satin kullum baya mantawa dayin wanka da Ruwan maganin da Aljana tabashi , Shiyasa yake matukar ganin canji , dan a halin yanzu , ko magana Anti Sadiya tayi mishi ba lallai ya aminta ba , dan ko zuwan Anti Hafsa gidan dakyar ya yarda ta zauna a gidan , dan cewa yayi ai bashi ne yasa taje ta kashe auranta ba , sai da Anti Sadiya tahada da lallami sossai kafin ya amince , dan kuwa Anti Sadiya tunda taga yafara miyar mata da martani kuma baya jin maganarta yasa tagane cewa yanzu kam ta san asirinta yafara karyewa , gudun itama kar yayi waje da ita yasa take lalabi shi kuma take shakkarshi .

Su maimuna kuwa kowa yagansu yasan sun samu canji matuka dan kuwa , har sun fara dawowa da kibarsu da dan kyansu, mahaifinsu yafara kokarin mai dasu makaranta , , amma yace matukar sun samu mazajan aure , toh aure zai musu, sun kuma yi na,am da zancan .

bakaramin kulawa suke samu ba , yanzu suna cikin farin ciki sossai , Hajiya Ramatu ma na jan su a jiki sossai sossai , kullum cikin nadama da danansanin abun da ta aikatama mahaifiyarsu takeyi .

Karfe tara na dare na hango Sadik sai rawar kai yakeyi , Aisha kuwa tunda ta fuskanci yau gogan nata a matse yake , gabanta yadinga faduwa , dan kuwa tasan yau ba bu fashi sai Sadik ya maida ta cikakkakiyar mace , hakan yasa jikinta yin sanyi .

Gashashiyar Kaza ya je yasiyo , bayan yadawo yasamu Aisha kwance tana kallo .

Batareda ya ce mata komai ba ya sunkume ya dauketa sai dakinshi .

Aisha mamaki tadingayi tanafadin ya sauketa amma ko kallanta baiyyyi ba balle ya bata ansa .

Ajiye ta yayi a kan katan gadanshi .

Rage kayan jikinshi ya shiga toilet danyin wanka .

Bayan yayi wanka , ya dauro Alwala .
Daure da towel ya fito a kugunshi .

Ganinshi haka yasa Aisha jin kunya , rufe fuskarta tayi , da sauri ,cikin muryar shagwaba tace," dan Allah kasa kaya, dariya yayi tace," A,a bazan sa ba , maza kema kitashi kije kiyi wanka ki dauro Alwala , in kuma ba haka ba in daukeki in miki da kaina , zaro ido Aisha tayi tace," kamun fa kace ?? dariya Sadik yayi yace," ko kina shakkar Hakanne in gwada ?? .

Da sauri Aisha ta mike , tashiga toilet dan yin wankan .

Bayan tayi wanka tayi Alwala , tafito , samunshi tayi har yasa farar jallabiyarshi , yana jiranta dan yin sallah , dakyar ta iya fitowa da daurin kirji a jikinta , ganinta a haka yasa Sadik yaji wani irin feeling ya bijiromishi , dakyar ya iya seta kanshi yace," saka kayanki muyi sallah .

Da mamaki Aisha tace ," sallah kuma ?.
Eh , Amsar da Sadik yabata kenan .
Batareda ta ce komai ba tasa doguwar rigarta da hijabi , ta shimfidamusu darduma .
Nan shima yatashi yajasu sukayi Sallah.

Bayan Sun idar , sun yi Addu,a nan yayi mata Addo,i da tambayoyi kamar yanda addini ya tanadar .

Bayan sun idar ya tashi ya daukko wanan kazar da yasiyo , ya fara bata , hade da abun sha.

Ci tafarayi amma gabanta na dukan uku _ uku , dan bakaramin fargaba takeyi ba .

Bayan sun gama nan suka shiga toilet dan yin brush , suna fitowa , Sadik ya canza kayanshi zuwa ,gajeran boxers da singlate.

Nan yafara kokarin cirema Aisha mata kayan, haka ya cire mata rigar da take jikinta , Aisha taso hanashi , amma yanayin yanda taganshi , yasa tayi shuru dan kuwa bakaramin kwarjini ya mata ba .

Pant da bra ne kadai sukayi saura a jikinta , kashe wutar dakin yayi , ya kwantar da ita a kan gado .

Nan yafara bata wani kyakkyawan romance , sossai yake sarrafata , dan kuwa jikin Sadik har rawa yake ganin irin surar jikin Aisha .

Ta ke ya rikice , Aisha kuwa tsorone fal cikin ranta , dan yanda taga Sadik tamkar mayun wacin zaki .

Tun Aisha najin dadin abun da Sadik yake mata , har tafara ganin ya wuce gona da iri , dan kuwa yarabata da duk wata suttura dake jikinta , shima kuma ya cire nashi .

Nan yafara kokarin Neman hanyar Shiga , wani ihu naji Aisha tasa ,
_nikaina sai da na tsorata da jin ihun da Aisha tayi_.
_Da haka na tattara inawa inawa nabaro dakin ,dan nasan su Sadik an Dade ba,a hadu ba , Aisha sai hakuri_.

Bayan komai ya kankama ,kuka sossai Aisha takeyi , dan kuwa bakaramin azaba tasha ba ta dirzu iya dirzuwa a gun Sadik sai da ta gwammace dama ba,a haifeta ba , magiya iya magiya tamishi , amma ina Sadik baya ma cikin hankalinsa balle ya ji me take fadi .

Sai da yayi sau uku , ganin halin da Aisha take

Please Login or Register in order to submit comment