Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

akwai kudi mudai burinmu bukatarmu ta biya .

Cikin ran Hajiya sailuba bakaramin dadi taji ba , tabbas tasamu dami a kala , dama tana matukar bukatar kudi gashi Allah ya kawo mata tsuntsu daga sama gashashe .


Cikin farin ciki tace," toh toh Baku da damuwa yanzu kuje Ku yi wanka kuci abinci , Ku huta, gobe sai mutafi gurin Wanda zai muku aiki .

Sunyi matukar farin cikin jindadin tarbar da Hajiya sailuba tamusu suka tashi suka nufi daki ...

Suna shiga Hajiya sailuba ta shiga dakinta tafara waya.......



washe gari da safe suka shirya suka nufi gurin boka .

Cikin farin ciki suka tafi , bayan sun isa Hajiya sailuba tace," Ku jira in shiga in fada mishi kunzo , koh .

Cikeda gamsuwa sukace," toh badamuwa .

Shiga cikin yar karamar bukkar Hajjiya sailuba tayi .

Cikin farin ciki Hajiya sailuba tace,"hummm kasan nayi maka bayanin komai a waya koh ??, sabida haka , kudin da suka bayar zamu raba kashi uku , zaka dauki kashi daya kabani kashi biyu , nasan cewa," aikinka bayayi yanzu , Sai dai kaci kudin mutane , sabida haka ka San karyar da zaka sharara musu ka karbi kudin kaji koh .??

Cikin farin ciki boka yace," toh toh badamuwa ,ai hakan ma yayi , kina gani kamar nawa zan karba ??

Hajiya sailuba tace," ko dubu dari da Hamsin ka karba , toh yace," .


Nan ta fita ta sanar dasu cewa yace su shigo .

Shiga sukayi , nan suka shaidama boka bukatarsu nacewa suna so duk yanda za,ayi sukoma gidan mazajansu , in kuma hakan bai yuyuba , yayi abun da zasu samu maza masu kudi fiyeda Nad'a, wa inda zasu dinga kashe musu kudi , sannan kuma tsofaffin mazajansu su kori duk matan da suka aura .

Nan boka ya tabbatar musu da cewa za,ayi aiki yanda yakamata , amma Sai sun ajiye kudi, naira dubu dari da Hamsin .

Jiki a sanyaye Anti Sadiya tace," boka dama duka duka kudin hannuna na dubu dari biyu ne , ina laifin in baka dubu dari, kaga sai in ajiye dubu dari a gurina da zan dinga juyawa kuma in rike kaina da 'yan uwana das, yanzu ba kudi a hanuna wanan ma kayan dakina na siyar wallahi .

Cikin tsawa boka yace," kinga in ba kyasan aikinan ki tashi ki fita, keda za,ayi miki aikin dasai kun sha hara a duniya amma kina wata magana,ki tashi ki fita in bakyaso .

Da sauri Hajiya sailuba tace," A,a baza,ayi haka ba ke Sadiya ki bashi abun da ya bukata .

Jiki na rawa Anti Sadiya tace," kayi Hakuri gashi gashi nan ta ajiye mishi kudin .

Nan boka ya tabbatar musu cewa zasu ga aiki , cikin farin ciki suka bar guri.

Washe gari da safe suka shirya suka bar garin maiduguri .

Gidan hayansu suka nufa , cikin farin cikin samun nasara..


Wasa wasa yau kimanin wata uku da kwanaki kenan , dukkansu sun gama idda sun jira sun jira amma babu wani labari kullum cikin jiran tsammani suke, koda yaushe Sai sun kira Hajiya sailuba , amma bata daukan wayan , basu da kudin motan zuwa da tabbas Sai sun tafi garin mai duguri....

Babu wani daya taba fitowa dasunan yana san auresu ,sai dai kowa yazo da iskanci, gashi zaman Gidan ya damesu ,a takure suke , a cikin gidan ,masu hayan ma sun daina biyansu kudin, kullum cikin gorantamusu suke, da habaice habaice .

Duk sunyi baki sun lalace , abinci ma wani lokaci gagaransu yake yi , kullum cikin fada da junansu suke.....


A bangaren Sadik kuwa farin cikin daya ke ciki baya misultuwa , dan kuwa yama manta dawata Rukaiyya indai ba yakalli'ya'yanta ba , kulawa sossai yake samu a gun Aisha , inda Yanzu Aisha ke dauke da cikin wata bakwai ,su khairat ma sun dawo gidan, sabida matsawa da Aisha tayi , har Sadik ya dawo dasu.

Iya kulawa suna samu a gurin Aisha tamkar ita ta haifesu , dan kuwa suma basu damu da rashin mahaifiyarsu a gidan ba .

Sadik kullum cikin godema Allah yake na musayamai Aisha da yayi , Arzikinshi kuwa yaci uban nada ,tsabar kwanciyar hankali .

kullum kara dawowa Yaro yake , duk da kuwa yanzu yanada shekaru hamsin a duniya amma kai kace dan shekeru tallatin da biyar ne, kullum cikin godema Allah yake .

Inda yanzu bikin khairat da Hashim yarage saura watanni biyu .....


A bangaren Alhaji madu kuwa , shima yana cikin farin ciki matuka , dan kuwa yanzu Amaryarshi na daukeda dakaramin cikin wattani uku , murna gurin Alhaji madu ba,a magana , kullum cikin sama Amaryarshi Albarka yake , kullum cikin mika ma Allah godiyarshi yake akan kyautar da yamai

Wataran har kuka yake yana fadin ,," Ashe zan ga gudan jinjina a duniya , a tunanishi ya cire rai da samun haihuwa sai gashi cikin kankanin lokaci Allah ya ansa Addu,arshi .

kullum cikin godiya da Allah yake , kulawa sossai yake bama amaryarshi , dan kuwa San duniya ya daura akan cikin , kuma suna zaune cikin so da kaunar juna .....


A bangaren Alhaji muktar kuwa , Hajiya nata kokarin ganin ya kara aure, amma shi Sam yaki , a cewarshi yana tsoron aure gudun kar halin da yashiga a baya ya kara Shiga , amma kasancewar Hajiyanshi ta takura mishi yasa dakyar ya amince zai kara aure , in yasamu 'yar gidan mutunci , Hajiya Rahmatu tayi farin ciki da hakan .

Su maimuna da Rahma ma duk sun samu tsayaiyyun samari , inda ake kokarin saka ranar auransu a lokaci daya .....


Su Anti Sadiiya ne zaune duk abun duniya ya ishesu , hakan yasa Rukaiyya ta fake da cewa ," zata je gidan Sadik dan ganin 'ya 'yanta , dan tun bayan rabuwarsu bata sa su a idanta ba .

Anti Hafsa ma da hakan ta fake , itama a cewarta zataje ganin 'ya 'yanta .

Shuru Anti Sadiya tayi tace," humm masu 'ya'ya nikuma fa wa zan je ganin??.

Ohooo !!Amsar da Anti Hafsa tabata kenan .

Tashi sukayi suka fita kowa ta nufi gidan tsohon mijinta ta............

*Hummmmm muje zuwa*


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.....* ✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 59*

*_NA MANTA BAN SANAR MUKU BA, GA WA INDA SUKE BUKATAR JIN VOICE DIN LITTAFIN NAN NA MAHAUKACIN KISHI ZAKU IYA KUNNE RADIO DINKU A KAN GIDAN RADI,O NAGARTA RADIO MURYAR HADIN KAN JAMA,A DOMIN SAURARAN LITTAFIN MAHAUKACIN KISHI , NAGODE_*

_*GA WA INDA BASA IYA JURAR KARANTASHI KO JIN RADI,O ZAKU IYA TUN TUBATA DAN TURO MUKU DA AUDIO DINSHI DAN KU SAURARA , NAGODE*_


Knocking din gate din gidan Sadik Rukkaiyya ta fara , bugu take sossai amma ba,azo an bude ba , kasancewar gaba daya Suna kitchen ,suna taya Aisha Aiki , sai mazan suna bayan gidan suna ball, Sadik kuma yafita yadawo ne kasancewar bai je gurin Aiki ba .

Bugu take kamar zata balla gate din .

Jin bugu da karfi yasa Aisha ta kallesu tace" uhm ni kam , kamar gate ake knockings koh ?.

suka ce eh muma munji , da sauri Kausar ta je dan bude gate din .

Wani kallon mamaki Kausar ta bita dashi tace," mama kece,??.

Cikin masifa Rukaiyya tace," eh ko in koma ne bakya san ganina , dan ubanku Ku na bar gidan ma ko a jikinku , jibi har wata kiba kikayi koh ??.

Turo baki Kausar tayi tace"toh toh ni ya kikeso muyi , da kin zauna lafiya da babanmu ai da yanzu kina zaune a gidanan, gashi yanzu muna zaune da Antimun lafiya kalau tana sanmu tana bamu kulawa , Wanda ke baki bamu ba a baya.

Bude baki Rukaiyya tayi ciki mamaki tace," eh lallai Kausar ni kike fadama haka??, abun da matar ubanki ta kitsa muku kenan ??, bani guri in je in ci ubanta , in ji dalilin ta na koyamuku wanan banzar magana , tsabar munafurci zata batamun yara , bani guri.

Cikinin zafin nama ta wuce cikin gidan tana huci .

Cikin tsantsar rashin mutunci, ta shiga rike kugunta, hade da takun kasaita tafara fadin , ina kike munafuka fito fito yau sai kin bar gidan nan , tsinanniya , kin cuceni kin shiga bokaye kin rabani da mijina .

Masifa takeyi kamar tsohuwar mahaukaciya ,har muryarta na dashewa , tanayi yawun Masifa na fita a bakinta, hade da kwalla, .

Da sallama Sadik ya shigo Fallon , mamakin ganin Rukaiyya yake yace," ke lafiya ko kin hauka ce ne??.

Cikin masifa tace," wallahi niko zan tabbatar maka da hauka matukar baka saki tsinanniyar nan ba .

Tsabar tsanin mamakin haukar da Rukaiyya take yasa Sadik kasa cewa komai , saima dariya da yayi yama me mamakin hauka da dabbanci da jahilci irin na Rukaiyya.

Cikin masifa tace ," dariya kakemun kamai dani ma mahaukaciya koh .

Da sauri Sadik yace A,a toh ai kinfi kama da mahaukaciyar dan kuwa mai hankali wallahi baza tayi haka ba.

Jin hayanniya a falo yasa Aisha da su khairat fitowa da gudu ..

Cikin tsananin mamaki Aisha take kallan Rukaiyya tace, " sannu da zuwa ashe kece??.

Gani Aisha daukeda da ciki yasa Rukaiyya tasa ihu tana fadin innalillahi wa inna illaihir raju'un, nashiga uku na lalace , ni Rukaiyya kuka take tana fadin ," Sadik!! Sadik!! Ciiki kamata , Sadik Ashe zaka iya taraiyya da wata mace bayanni Sadik , kacika munafuki kaci mazinaci tsinanne wato har ciki kamata , Sadik yaushe kukayi auran , har ka kunsa mata ciki , wallahi duk yanda akayi wanan cikin badan halak bane wayasan ko tun a wajen ma akayi cikin.

kuka take sossai tana magana , inda har muryar ta bata iya fitowa tsabar kuka da takeyi hade da ruwan bala,i.

Wani wawan Mari Sadik ya dauketa dashi rai a bace yanafadin ," ke wacce irin annoba ce na rabu dake amma ban huta ba anya ke mutun ce kuwa Rukaiyya ???.
Karki kuskura ki kara shegan tamun ciki , wai ke miye damuwarki ne??.

Da kuka khairat tanufi gun maman tasu tana fadin ,"mama wai meyasa hakane??? Meyasa meyasa bazaki shiryu ki gyara halinki ba , muna zaune zaman jin dadi zakizo ki tar watsamana jin dadi , kuka sossai take .

Nan ta tsaigaita kukan da takeyi tace,' mama kinsan miye ??, wallahi tallahi nayi danasanin kasancewar ki mahaifiyata baki can cancanci a kiraki uw.....bata karasa maganar ba Aisha tayi saurin rufe mata baki tace," ke baki da hankaline kike irin wanan furuci, ba furuci mai kyau bane , kar ki kara kinji ko.

Hummm Sadik yace ," kinji ko kinji koh Rukaiyya kinji abun da 'yar cikinki take fada akanki koh , wallahi kinyi a Sara .

Hannu Rukaiyya tasa ta wanke Aisha da mari tana huce tace," munafuka Algunguma ba duk ke kika kitsa ma yaranan munafurcin nan ba ba ke kika kitsa musu sudinga mun haka ba , kuma wallahi yau duk sai na kwashe yarana sun bar gidan nan kafin ki koya musu bakin hali irin naki .

Cikin kuka Aisha tace," dan girman Allah kar ki dauki yaranan, wallahi munsaba kuma mun shaku dasu..

Cikin bacin rai Sadik yace," in ke baki da hankali ke shasha sha ce ki tabamun yara kigani , kina maganar tarbiyyar yaranka , ke ishashiyar tarbiyar kike dashi da zakice za,a bata tarbiyar yara, toh bari kiji ," wallahi tun muna shiri da juna maza maza kificemun a gidana kafin ranki ya baci.

Cikin balbalin bala,I da masifa Rukaiyya tace," in ka fasa, kuma ni wallahi babu inda zanje sai da 'ya'yana tunda ba uban wani bane ya haifamunsu .

Kallan yaran tayi tazare idanta tace," Ku kira sauran kananku Ku debo kayanku mutafi .

Kunkuni yaran suka fara , walida da Kausar sukace," mu wallahi bazan biki ba tab .

khairat ma cewa tayi ni ma mama kiyi Hakuri ,amma bazan biki ba zan zauna a gidan mahaifina .

Cikin mamaki Rukaiyya tace," lallai baza Ku bini ba,??.

Gyada kai sukayi Alamar Eh .

Da gudu sauran kanansu maza suka shigo , suka nufi gun Aisha , karamin yace," Anti kinganshi zai dakeni koh ??.

Da sauri Rukaiyya ta fincikoshi tace," kai zo nan ita ba Antinku bace kaji ??.

Da gudu ya koma gun Aisha yace Anti nace ai.

Ganin Haukan Rukaiyya ba mai karewa bane, yasa Sadik ya kalli yaran yace," Ku shiga daki .

Toh sukace suka nufi dakin.

Masifa Rukaiyya tafara yi tanafadin wallahi kabani 'ya'yana ba zan bar gidan nan ba sai kabani yarana .

Sadik bai tankamata ba illa rugume matar shi da yayi a jikinshi yadan manna mata kiss a kumatu ,nan ya kalli Rukaiyya yace," in kingama haukan ki tafi sai Anjima , ya kalli Aisha yace," mushiga ko my love ,yana fadin haka ya tafi .....

Ihu Rukaiyya tasa tana kuka ta inda take shiga batanan take fita ba , masifa take kamar zararriya.

Ji takeyi kamar zuciyarta zata buga ganin mijinta rugume da wata har yana mata kiss , kuma tasan dagangan yayi hakan dan taji haushi .

Masifa take sossai da ta gaji dan kanta ta fita a gidan ganin babu Wanda ya kara fitowa balle ya kulata .

Tafiya take tana magana ita kadai hade kuka tanafadin ," ohhh yau wai yarana duk sun gujeni , wai har in ce suzo suki , ga Sadik har yayi ma matarshi ciki , da alama ma ko a jikinshi kasancewa bana gidan , har wani kyau yayi , ga yara na nace su biyoni sunki ,duk da cewa ita ma dai tadai fadane amma tasan bata da inda zata sasu balle abincin da zasuci , itama ita kadai ya takare .

Haka ta dinga sambatu tana tafiya kamar zarariya , hakan yasa mutane suka fara kallanta , tamkar mahaukaciya , ga yunwa dake damunta hakan yasata kara tunzura .


Da kuka tashiga gidan tashiga dakinsu .

zaune tasamu Anti Sadiya nashan garin kwaki .

Cikeda mamaki Anti Sadiya tace," ke lafiya??? daga zuwa ganin 'ya'ya sai dawowa da kuka .

Nan Rukaiyya ta tafada mata duk yanda sukayi, cikin kuka Takara da cewa ," ni wallahi Allah ya isa banyafe ba , ni da yanzu ina gidan mijina cikin koshin lafiya , tsabar mugunta kika kashemun Aure...

Lallai Rukaiyya yaushe zaki daina mun Allah ya isa ne ni ba yarki bace dan ubanki , Anti Sadiya tafada rai a bace .

Cikin rashin kunya Rukaiyya tace," eh an fada din karya nayi .

Cikin Bacin rai Anti Sadiya ta kife Rukaiyya da mari .
A zafafe Rukaiyya ta rama .
Take suka fara dambe suna kokuwa .......


A bangaren Anti Hafsa kuwa ko da taje gidan knocking tafarayi , da sauri me gadi yazo budewa yanafadin waye??.

Murya a sanyaye tace nice , bude gate din me gadin yayi yanafadin ," Hajiya Ashe kece??, barka da zuwa .
Batareda da ta bashi ansa ba tace ," uhmm Alhaji muktar nanan ??.

Gyada kai bala me gadi yayi yace ,"eh yanan .

Fitowar Alhaji muktar daga daki yayi daidai da shigowar Anti Hafsa harabar gidan .

Cikeda mamaki Alhaji muktar yace," ke wai lafiya ???, me ya kawoki gidana, me kikazoyi bayan kinsan babu igiyar aurena akanki, kuma babu wata alaka dake tsakanina dake ??.

Kasa da murya Anti Hafsa tayi tace،" haba Alhaji yazakace babu Alaka dake tsakaninmu kamanta mun haihu tare , kuma ai ni ba gurinka nazo ba gurin 'ya'yana nazo.

Wani kallan rainin hankali yabita dashi yace, " hummm 'ya'ya ai 'ya'ya inshallahu cikin watanan zan sama musu uwar da ta dace dasu bawai irinki maras tarbiya ba , ai ke baki cancanci a kiraki da uwa ba , sabida haka banaso ki batamun lokaci , ki maza kifita kibarmun gidana kafin ranki yabaci na fada miki.

Cikin kuka Anti Hafsa tace dan Allah.....bai bari takarasa ba yace, " wallahi kar ki bari in kirga uku baki fita ba in ba haka ba wallahi sai na miki abun da baza ki taba mantawa ba .

Da sauri tace," toh shikenan zan fita .

Wata razananniyar tsawa yadaka mata yace," *Out!!!!!*, bashiri ta fara kokarin fita .

Tsawar da su maimuna da sauran yaran da Hajiya sukaji Alhaji muktar yayi ne yasa su sauri suka fito .

Cikin rashin fahimta Hajiya tace lafiya muntari ???.

Cikin bacin rai Alhaji muktar ya nuna Hafsa da yatsa yace," ga wacca tazo nan tana Neman bata mun rai .

Nan Hajiya ta kalli Anti Hafsa dake kokarin fita , tace," yoh ke me yakawoki nan , maza maza kifita.

Kuka yaran suka farayi ganin inda mahaifiyarsu takoma kamar ba itaba .

Su maimuna kuwa sun ma rasa kukan me sukeyi na dadi ko na tausayinta , ko na jin dadin sakaiyyar da Allah yayi musu , sudai kuka kawai suke.

Da gudu yaran suka shiga ciki suna me tsanar halin mahaifiyarsu , da,ace ta gyara halinta, tanada kyakyawan hali dayanzu Suna zaune da ita cikin farin ciki .

Itama Anti Hafsa ganin yaran nata sun shiga ciki da gudu yasa kuka ya kubce mata , da gudu ta fita a harabar gidan .


Jiki a sanyaye ta dawo gida.

Samun su Rukaiyya da Anti Sadiya tayi sunsha dambe duk sun jima junansu ciwo sunata huci, hade da haki .

A rude tace ," kukuma lafiya ??.

Babu Wanda ya kulata a cikinsu , itama ta tattarasu ta watsar .....

Bayan yaran Anti Hafsa sun shiga kuka suka dingayi , Hajiya dasu maimuna suna ta basu hakuri .......


Bayan 'yan watanni Abubuwa da dama sun faru , ciki kuwa har da auran su maimuna da Rahma da akayi , inda dukkansu aka kaisu garin kano .

Mazajansu balaifi sunada kudi sossai kuma mutanene masu mutunci , sun rikesu maimuna Amana.

A kullum in su maimuna suka zauna suna tuna rayuwarsu na baya da sauyin da Allah yayi musu sukan gode Allah suna fadin no condition is permanent...., babu abun da idan yayi farko bazai wuce ba sai ikon Allah ..

bayan bikinsu ne Alhaji muktar yasamu bazawara ya aura, wacce mijinta ya rasu tanada kirki sossai , kuma suna zaune cikin jin dadi dazaman lafiya , kuma ba laifi tana kula da sauran yaran da Hajiya Rahma .


A bangaren Alhaji madu kuwa shima Amaryarshi farida ta haifi 'yan biyu mace da na miji gwanin ban sha,awa murna gun Alhaji madu ba,a magana , kullum sai yayi kuka yana mai mika godiyarshi ga Allah akan sauyin dayiyimishi .


A bangaren su Anti Sadiya kuwa ........✍️

*Hummm muje zuwa*


*MORE COMMENTS 😎😎😎*
*MORE TYPING.......*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU,AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘



🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 60*

*The last Page*

πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š.


A bangaren su Anti Sadiya kuwa .
Bala,I iya bala,i sun shiga , duk sun fita haiyyacinsu ,sunyi baki sun lalace , in ka gansu sai ka rantse basu bane , .
Wani lokacin ma sai su kwana uku basu ci abinci ba, sai watarana ne idan mutan gidan sun tausaya musu Sudan basu abincin .

Duk sun siyar da duk wani abun da suka mallaka , har katifar dake dakinsu sin siyar , kayan jikinsu ma duk sun siyar , kaya kala bibbiyune yarage musu .

Duk wani abun kyale kyalensu sun siyar dan su samu abun da zasu dinga ci .

Ba karamin wahala suke sha ba , hakan yasa duka dinga bi gidan ',yan uwa ko Allah zai sa wani ya taimakesu , amma duk Wanda suka je sai dai su musu Koran wulakanci .

Tabbas zuwa yanzu sun fara saduda da danasani .

'Yan uwansu da suke Lagos suna fama da cutar kanjamau , duk sin lalace , hakan yasa suka yanke shawarar zama a can batareda sun dawo ba , dan sun zama wani iri , sun lalace , kullum cikin danasani suke da zagin mahaifiyarsu suke akan rashin tarbiyar da bata basu ba ..

Su Anti Sadiya babu wani mutumin kirki da ya fito nemansu , duk sai na banza , in ko na kirkin ya fito , sai Anti umma tayi kutunkutun ta je ta fadawa mutumin karya da gaskiya akansu , dan kuwa Anti Umma na bibiye dasu, kuma tasha alwashin hanasu aure tunda suka kashe mata nata,sai dai kawai suga mutum yadaina zuwa ..

Cikin hakane wani ya fito dan Neman Auran Anti Sadiya , murna a gun Anto sadiya ba,a magana .

Duk da cewa Anti umma taje tasamu mutumin ta fada mishi karya da Gaskiya hakan baisa ya fasaba , yace," eh shi zai aureta a hakan .

Batareda bin cikeba Anti Sadiya tace ayi auran haka dan koma yaya ne gara tayi auran .

Cikin wata daya akayi auran ta tare a daki daya .

Bayan Sati Daya da auransu , Anti Sadiya batada walwala , kullum cikin tashin hankali take , dukan safe daban na rana daban , abinci ma basamu kullum take ba.

Zaune take tayi uban tagumi , mijn nata ya fito da katuwar bulala yafara zuga mata , ihu take sossai .

Cikin kuka take fadin wai me na maka ne kake azabtar dani haka ???.

Wata shu,umar dariya yayi yace," hhhhhhhhh ke dama an ce niki na aureki tsakani da Allah , bayan duk nasan wacece ke, ni dinan da kika ganni na auri mata sama da ashirin , kuma bantaba haihuwa ba sabida bana haihuwa, yanzu kowa ya gano ni duk wacce naje gunta sai tace batasona bana haihuwa , kece kadai nayi sa,a kika amincemun cikin sauki, ni da kika gani, ni mugune , bani da imani ,yanadaga cikin abun da yasa mata basa zama dani danni ni mugune .

Wata dariya ya kara yi yadinga laftarta

Please Login or Register in order to submit comment