Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace baku da tunanin da zaku tambayeni abun da za Ku dafamun in ciko , suka ce kiyi hakuri me zamu dafa miki , tace inaso kumin farfesun kifi , sai ku mun yam balls , ku hada da spring rolls , da kuma potatoe sandwich, aikuwa zuka zaro ido suka ce anty duk mu kadai , wlhy bazamu iyaba ,sai dai 'yan aiki suyi , wannan dinma da kika ga munyi mommah muce tasamu ,mu miki , amma wlhy bama girki , kuma yau munada lecture karfe tara,

Aikuwa Alhaji mukhtar ne yadaka musu wata irin tsawa yace baku da hankaline tace kumata abu kuce bazakuyi ba , common kuje ku girkamata abun da ta lissafo.
Hajiya hajara ce tace kunga rahama maimuna kutafi daki ina zuwa zanzu in sameku , suka ce toh suka nufi daki , bayan sun shiga dakine ,
Hajiya hajara tace gaskiya Alhaji ni fa banga laifin yaranan ba suna da lecture a makaranta ta yaya zasu iya wa innan uban girki , sai dai masu aiki suyi mata , amma gaskiya bazasu iya ba
Hajiya hajara takara dacewar , gaskiya antyn su rahama banji dadin maganarki ba ko kadan , yaza a yi kice ban basu tarbiya ba, kuma naga kina kiransu sukazo , ba wai sunki gaisheki bane , sannan gaskiya wannan hukunci da kika dauka na marinsu da kikayi banji dadi ba gaskiya , sannan bawai ina miki magana ne a matsayina na mahaifiyarsu ba as ina yi ne a matsayina ta wacce in kikayi ba daidai ba zanfadamiki ,
Amma in nabata miki rai a maganar da nayi kiyi hakuri, barinje ni in daura miki abun da zan iya tunda naga bakyaso yan aiki su girka miki , amma gaskiya, yara makaranta zasuje zasu iya makara

Da haka hajiya hajara ta bar gurin ta nufi dakin yaran tace , kuyi hakuri , watarana sai labari , ni barinje in dauramata abun da zan iya ,

Maimuna tasa kuka tace , mommah mun shiga uku , karo na farko da baba ya taba zagin mu a rayuwa, dalilin amaryarsa , rahama ma tace , mommah inaga gabagaba , wataran koranmu ma zata sa baba yayi a gidan , dan tun ba a je ko inaba , kiduba kiga laifi ba laifi ba munsha mari akai ,
Hajiya hajara ta ce kar in karaji kun fadi irin wannan maganar , kuyi hakuri da sanin Allah , duk abun da tazo mana dashi Allah ya fita ,

Hajiya hajara ta ce kuyi kuyi ku fara kokarin tafiya makaranta , dan karku makara ,ni zanje kitchen in fara dauramata abun da zan iya , suka tab mommah me zaki daura mata abincin , ? Wlhy gaskiya bazakiyi ba akanme ai ke ba baiwar ta bace ,
Mommah tace ba ruwanki , miye a ciki ai da ba yan aiki , baku , da dole ni ce zandafa mata , ai hakkinane a matsayinta na amaryata ,
Maimuna tace , toh amma fa mommah , mundafamata ,kina gani tace bazataci ba mommah tace kunga ya isa haka dan Allah , kubar maganar ,
suka ce toh , amma mommah ai da sauran lokaci , muje mutayaki kafin lokaci yayi , tace toh muje ,
Suna kitchen ne rahma tace , tab mommah rabonki da shigowa kitchen har na manta , amma dalilin anti yau gashi kece a kitchen , mommah tace humm toh ya za ayi haka Allah ya kaddara , wataran sai labari ,suka cigaba da aikinsu .

Alhaji mukhtar ne yayi musu sallama ya nufi office dinshi ,
Hafsat ce ta shigo kitchen , cikin isa da rashin mutunci tace , ammm hajara , kinga in kingama mun abincin ki zo ki fadamun dan barci zanyi , kafin kigama , hajiya hajara ta ce toh badamuwa , hafsa ta juya ta nufi dakinta ,
Maimuna ce tace kai mommah gaskiya rain in hankalinan yafara yawa tsabar raini kece na zaki je ki kirata ,
Mommah tace ba ruwanku , maza kubar nun aikin zan karasa kuje kushirya lokaci yakusa , suka ce toh suka nufi dakinsu dan shiryawa.

Hajiya hajara tana kitchen tana ta kokarin girki ta daura wanna ta sauke ta daura wannan , tayi matukar gajjiya, hakan ne ma yasa takasa yinmata potatoes sandwich dab gaskiya in ta takurama kanta ,at a sha wahala ,
Cikin ranta take cewa , badan bata son fitina da, da tashin hankaline ba , da gaskiya baza iya girkegirkennan ba, zadai tayi dan Allah da kuma far in cikin mijinta .

Bayan tagama abun da za ta iya ta nufi dakin hafsa , kafin taahiga sai da ta karanta , *lahaula wala kuwa ta illabillah*
_masu karantu duk wani abun da yaahige muku duhu kudinga karanta ta domin tanada zafi_, _matukar mutum na karantata , toh makiyanka , sai sun ganka sun barka , sannan matukar mutum na karantama makiya shi ,to in makiyinka ya ganka , sai gabanshi yafadi domin tanada zafi sossai_ ,

*MUJE ZUWA*

*TAKU KAR KULLUM* *(MUM FU,AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 18*

*gaskiya wlhy in har banga kuma comment ba wlhy zandaina posting, zandinga posting a group din danake samun comments sossai wlhy , banason sticker ko kuma sign of emoji , dogon sharhi nakeso in ba haka ba wlhy tallahi zan daina posting , amma mutum zai dinga westing time yana typing amma kalilan ne zasu yi comments , gaskiya ku gyara , kudinga bani kwarin gwaiwa dan Allah , nagode*


Hajiya hajara nashiga dakin , tasamun hafsat na kwance tana latsalatsan waya , tace antynsu rahama gashi na gama abincin,
Dan Allah antynsu rahama , kiyi hakuri kidaina saurin fushi da harzuka , wlhy ni banasan tashin hankali ko kadan , inaso naga mun hada kanmu kodan kwanciyar hankalin mijinmu , matukar muna tashin hankali , mijinmu bazai taba arziki ba kuma bazai samu kwanciyar hankaliba , dan Allah in namiki badaidaiba ki fadumun, na miki alkawari zangyara , kema inaso ki fadamun matukar na miki ba daidai ba , wlhy hakan zai fi mana kwanciyar hankali ,
Aiko hafsat tayi mata wani kallo , tace ni kinga ba wannan na tambayeki ba kinga mun abun da nace, hajiya hajara tayi murmishi tace , eh nagana, amma kiyi hakuri dan Allah banyi potatoes sandwich ba , nagaji wlhy,
Hafsat tace dan wulakanci, da kinsan bazakiyi ba ai da kinfadamun kinga nasa mijinki ya girkamun , aikin banza , ta tashi fuuuuu ta nufi hanyar dinnig,
Tana zuwa ta bude taga abubuwan da hajiya hajara ta dafa, ai kuwa haka tafara ci, bayan ta gama cine tace, tab gaskiya ki je makarantar koyan girki , dan da alama da sauranki ,
Hajiya hajara tace aa bana bukatar zuwa makarantar koyon girki , dan kuwa ba girkin nake ba , hafsat tace uhmmm kanki akeji , ta tashi tabar gun, hajiya hajara tayi murmushi kawai, ta kira musu aikin gidan su kwashe kayan,
Itako hafsa daki ta nufa, ta kira mahaifiyarta, mahaifiyarta ta kara kitsa mata makirce makirce , iriri , akan karta yarda ta ragawa , hajiya hajara, dan itama bata ragama sauran kishiyoyinta ba, har sai ta tabbatar da bata cikin gidan , ta kara dacewar , zata koma gun boka domin ya kara aiki mai zafi , aikin da ko takalmi, sai tabashi i zinin sawa , hafsa, tayi farincikin hakan tace , mamana ina alfahari dake, hajiya amina tace, haba hafsa ai dukanku , sai na tabbatar da cewa , ko ji dadi sossai a gidan mazajanku , kun malleki dukiya mai yawa, hafsat tace , hakane mamana ,
Daga bisani sukayi sallama , hafsat ta kashe , wayar takwanta , tana sakesaken yanda zata gasama hajiya hajara da yayanta , aya a hannunsu ,

Washe gari hajiya amina da kanta ta nufi gurin boka domin yayi akai mai kyau akan Alhaji mukhtar , boka ya tabbatar na da hajiya amina cewa , zai mata aikin da sai ta dawo tamishi godiya amma da sharadin cewa hafsat zata bar salla na sati daya, sannan bazatayi wankan janaba ba , in tayi jini, ko kuma tayi taraiyya da mijinta hajiya amina tace badamuwa , ai in da sabo ta saba domin kuwa , itama haka take matukar boka zai mata aiki toh sai ta aikata hakan , shiyasa ma koda boka yafada bata damuba ,
hajiya amina tayi farin ciki da hakan , daga bisani ta zuba mai kudi masu yawan gaske ta nufi gida , takira hafsa ta shaidamata abun da boka yace , hafsat tayi na am da zancan , tace zatayi koma miye matukar zata samu biyan bukata ,

*MUJE ZUWA*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️* *(MUM FU,AD*)

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 19*

A gugrguje ,
Abubuwa da dama sunfaru ciki kuwa , harda sauyawar halin allhaji mukhtar , domin yanzu kwakwata ya canzamusu, baya kulasu ko kadan , baya jin maganar kowa sai ta hafsat , dan ko gidan mahaifiyarshi rabon da yaje har ya manta ,

Hajiya Hajara da yayanta kullum cikin kuka da rokon Allah suke, akan hankalin mijinta ya dawo garesu , don a halin yanzu banda tsangwama da tsana ba abun dake shiga tsakanin Alhaji mukhtar dasu, dan ko dakin hajiya hajara baya zuwa , yaran ma kwata kwata yadaina biya musu kudin makaranta, da bukatun rayuwa,
Hajiya Hajara ce me kokari da fafutikar biyan kudin makarantar yaran nata, iya gwargwado , dan a halin yanzu itama dan abun da ta tara yafara karewa domin kuwa yau da gobe ta wuce wasa , ko abincin ci ma sai hafsa ta ga dama take samusu , ko sukoshi ko karsu koshi duk daya, dan Alhaji mukhtar yace kar su kara shiga kitchen bada izinin hafsa ba ,
Hafsa kuwa tace kar suyarda su shiga kitche n indai ba da izininta ba ,
Girkinma Rahama da maimuna ne suke amma sai sun ga dama take basu suci ,
Haka watarana zasu yi sauri in sungama , su kulla a leda in sun shiga daki suci , kamar almajirai ,

Hajiya Rahamatu kuwa, mahaifiyar, Alhaji mukhtar , kullum cikin tunanin dan nata take akan tashin zuwanshi , tana mamakin sauyawan da yayi a kwanakinan ,tunda yayi aure raban da yazo har ta manta , gashi tana bukatar abubuwa , a halin yanzu abubuwan ta na bukata sun fara karewa kamar su abinci, dadai abubuwan bukata,hakan yasa ta yanke hukuncin zuwa gidan ta sameshi dan ta ciccimai mai mutunci, da jin dalilin rashin zuwa dubata da bayayi .
Da sassafe hajiya ta nufi gidan dan nata Dan k o karyawa batayi ba taje da niyyar ta karya a can .

Hajiya na shiga gidan ta ji kida na tashi a falon , tana shiga ta tarar da hafsa taci Riga da wando tana ta tikar rawa,kamar tsohuwar karuwa , hajiya tace ke hafsatu lafiya kuwa ,ko kinfara hauka ne,
Hafsat ta kashe kidan , ta nufi inda hajiya take , tace aa hajiya kece !! Sannu da zuwa ya hanya ?? Hajiya ta galla mata wata harara , tace too kyace ya hanya mana , tunda mukhtari ya aure ki kikarabani dashi rabon da yaxo har na manta , hafsat tace , toh shi muktar din yarone dazan rikeshi ince kar ya fita , hajiya tace a lallai ma nikike fadawa wannan magana , toh ina mukhtar din yake, hafsat tace oho kije kiduba mana,
hajiya tace tab a lallai nayarda da abun da mutane suke fada duk Wanda ya hada zuri a da danginkubya hada zuri a da bala,i sai yanzu na tabbatar da hakan, tsabar baki da mutunci kidubi tsabar idona kice zakimun rashin kunya ,
Hafsat na karkada jiki ta taunar cingum , tace kinga hajiya dan allah karkizo gidan mijina kice zaki dagamun hankali , ko kifadamun bakar magana wlhy ba mutunci bane dani sai yanzu narufe ido in miki tashin mutunci eheee , tafada tana karkada jiki
Hajiya rahamatu da mamaki yagama kamata tace, ehh banyi mamaki ba dan ance ubanki ma bai wanye lafiya da uwarki ba sabida haka ,in kikayi abun da yafi haka ma ba mamaki , billahillaxi la ila ha illahuwa sai kin bar gidanna wlhy tallahi yau yau dinan ,sai ki kina gaban uwarki hajiya amina da bata baki tarbiya ba , hafsat tace toh bismillah ki shiga ki kira dan naki in kin is a dashi kice yasakeni din, tsohuwar banza, anfadamiki in kina Hajara yana kyaleki ni zan barkine wlhy tallahi bazan barkiba , ai naji labarin irin wulakancin da kike mata to barikiji ni ba hajara bace ni hafsa ce ehee,

Hajiya rahmatu tadaga murya tace , kee hajara kina ina Ashe dama haka kike, zauna da wanna dangin tsiyar a gidan nan , kina ina ne !!
Hajiya Hajara da yayanta suka fito , badan sinyi niyyar fitowa ba , domin kuwa duk abun da yake faruwa suna ji , hajiya hajara tace suyi shuru du zauna ba ruwansu ,
Hajiya Hajara tace" hajiya lafiya kuwa", hajiya tace hajiya uhmmm ina ko lafiya hajara ,ashe haka kuke fama da dangi n tsiyar nan a gidanan ,
Hajiya takarema hajara kallo , itada yaran tace yanaga duk kun rame ciwo kukayi ne haka ?
Hajiya Hajara tace , aa wlhy hajiya ba ciwo mukayi ba lafiya kalau , hajiya tace kai bayardaba hajara , anya wannan matsiyaciyar matar bata muzgunamuku kuwa ,tanuna hafsa da yatsa , dataketa faman harare harare, hajiya hajara tace uhmmm hajiya ni barin shiga ciki in kin tafi sai anjima ,ta juya zata tafi , yaran ma suka marama ta baya ,
Hajiya tace ke hajara zo shiga ciki ki kiramun muntari , hajiya hajara tace wlhy hajiya bansan ko yanan ba dan wlhy rabon da in ganshi yafi wata , tun randa ya debo kayan hafsa yace in wanke ban karasa sashi a idona ba,
Hajiya tace tabb ai kina nufin harku da kuke gida daya baya zuwa gunku ,?
Hajiya hajara tayi murmishin da yafi kuka ciwo tace ehh ,
Aikuwa hajiya fuuuuuu ya kutsa kai zata shiga daki , da sauri hafsa ta shagabanta , tace ke wacce irin sirikace, baki da kunya ne da zaki shiga dakin sirikarki , kinga ina ce kira miki shi zanyi kisa ya sakeni toh jirani , barin kirashi dan allah in kin isa kar in kara ko awa daya a gidanan,
Hajiya tace ai ko na isa dan ubanki har nayi yawa , in haifi daa da cikina kidinga nuna iko , a lallai , nayarda , sai yanzu na gane dalilin dayasa 'yar albarka hajara tace ma muntari yayi bincike sossai kafin ya auroki , nida shi mukayi kunan uwar shegu da zancan , ashe ita tasan abun da ta hango , hajiya tafashe da kuka

Hafsa ta kutuntumo uban ashar tace lallai ma hajara , wato dan munafurci , shine harda wani cewa ayi bincike akaina , tsabar ke munafuka ce , a lallai ma , toh wlhy sai na gasa miki aya a hannu , duk abubuwan nan da nake muku bakiga komai ba wlhy , Rahama ce tace , dan allah anty in kin tashi kar kibarmu da rai , ke wacce irin matace wacce bata da imani ne !!Me muna miki , aikuwa ji kake tassssss hajiya hajara ta wanke rahama da mari ta na magana cikin bacin rai tace baki da hankaline , wayasa bakinki ban fada miki kar ki kyskura inji bakinku ba ,
Hajiya tace kar ki kara dukan ta Hajara , ke bakiji rashin kunyar da takemun bane , kar ki kuma dukanta aiini Rahmatun tamun daidai ,

Hajiya Hajara tace kiyi hakuri hajiya bai kamata ace tayi magana irin wannan ba tunda ko ba komai a matsayin uwa take a gurinsu , hajiya tace nikuma a matsayin me nake a gurinta? fadamun , tunda ita bata dubeni a matsayin sirikarta ba balle kuma tadubi tsufa na , tadinga fadamun magana san rants ,
Ta kalli hafsa da takau da kai gefe , tace ki kiramun muntarin ko ,
Hafsat tace toh barin kira miki in kin isa kisa ya sakeni , hajiya cikeda isa da gadaara tace zako kiga aiki da cikawa , tunda ba gidan ubanki bane ,

Hafsa na shiga daki ta tarar da Alhaji muktar nata sharar barci dan da alama bai San ma me akeba , kasancewar yau weekend ne ba aiki ,
Tana shiga dakin tatsaya kikam akanshi , tafara kiran sunanshi , tace kai mukhtari, dallah tashi ka fitar da wannan tsohuwar kafn raina yabaci ,Alhaji muktar da yake magana cikin murya irin ta masu barci yace , hafsa na lfy kuwa wacce tsohuwa ,
Hafsat tace Ohoo kafito ka ganta mana , har ma ta budi baki tace wai sai tasa kasakeni , to kasakenin ,
Aiko Alhaji mukatar yayi wani irin zabura , ya mike daga kan gadon yace, bangane tace in sakeki ba , in sakeki kuma toh ma wai waye , toh akanme ma , muje muje in ganta ,

Aikuwa ya na fita ya yaga hajiyanshi ce , yace aa hajiya kece , ya kalli hafsat yace dama hajiya kike magana ita ce tace in sakeki , hafsat ta galla wata harara tace katam bayeta mana
Aa hajiya dama kece kike so in saki hafsa??

Hajiya tace ,yauwa kafito , tunkafin inyi fadi abun da ke tafe dani ,in ni na haifeka , matukar kanason farin cikina toh kayi maza kasake wanan 'yar dangin tsiyar.

*toh kubiyoni dan jin yadda zata kasance ,shin Alhaji muktar zai bi umarnin mahaifiyarshi ya saki hafsat ko kuwa??*

*idan naga comments sossai anjima ma zaku jini amma in banga ruwan comments ba sai gobe in allah yakaimu gaskiya*

*MUJE ZUWA*

*MORE COMMNETS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY*✍️✍️ *(MUM FU,AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 20*

Alhaji mukhtar in banda zufa ba abun da yake fitar wa , yayi saurin cewa kai hajiya in saki hafsa fa kikace?? ,
Hajiya tace eh kasaketa, in har ba ka saketa ba wallahi sai na matukar bata maka raii.

Hajiya Hajara kuwa dataga abun bana karebane tace uhmmm hajiya ni zan shiga ciki sai anjima , ta tasa kan yaranta a gaba suka tafi ,

Alhaji muktar yace ,gaskiya hajiya kiyi hakuri wlhy tallahi bazan iya sakin hafsa ba , dan in rasa hafsa wlhy gara na gwammace na rasa raina, hajiya farin cikina ce fah , hajiya dan allah kar ki kara maimata maganar nan ,da bata da dadin jii ,
Hajiya tafashe da kuka tace lallai muntari ,yau kanunamin ni ba komai bace , kuma ban isa da kai ba muntari har ni insaka abu kaki ai katawa , toh wlhy ko kasaketa ,ko in tsinemaka ,kuma kabiyani nono da kasha ,
Hafsa da take a hakimce a kujera tana kallansu kamar me kallan TV tace uhmmm kaga!!, alhaji muktar ya juyo ya kalleta yace ranki yadade , hafsat tace in kun gama dramar kazo ciki ka sameni , ina daki ina jiranka.
Hajiya tace dan ubanki dawo kar ki yarda ki shiga cikin dakinan ki fito ki tafi gidan ubanki,
Hafsat ta kalleta ,taja uban tsaki jikake mssssssttttttt , ta galla mata harara ta shiga daki tana tafiya cikeda da kasaita ,

Hajiya tasa uban salati tace laa ila haillallah muhammadu rasulillah sallallahu alaihi wasalam,nashiga uku ni ramatu yanzu muntari kana ganin abun da tamun amma bakace komai ba , lallai muntari nagode ,hajiya tafashe da kuka me cin rai ,harda sharce majina

Alhaji Muktar yace hajiya kinga kije gida zanzo na sameki, yanzu ga wannan , Alhaji muktar ya Ciro dubu da daya daga aljihunshi yace gawannan kiyi kudin moto gobe zanzo,
Hajiya Rahmatu tace ah lallai muntari wlhy ba haka a kabarka ba , rabon da ka bani dubu daya har na manta ,tun kafin kayi arziki mai yawa, baka taba dauko naira dubu daya kabani ba , amma yau ka mikomin dubu daya , me dubu daya zata mun muntari , duk kayan abincina sunkare , komai nawa yakare, in banda allah yasa makota na taimakamin , da bansan yanda zanyi ba , muntari nasan baka taba yi mun hakaba, amma zanje gida zanjira har lokacin da allah zaisa ka farga ka gane , inshallahu muntari bazan kara zuwa gidanka ba nagode.

Alhaji muktar yace kiyi hakuri hajiya ki karbi wannan, kije zanzo gobe , hajiya tace allah kawoka , tafada a takaice, ta karbi dubu dayan ta nufi hanyar fita shikuma, ya juya ya nufi daki.
Hajiya Hajara ce tayi saurin fitowa daga dakinta , ta nufi gun hajiya ,tace hajiya mushiga ciki muyi magana , akan wannan matsalar, hajiya tace , hajara wacce magana zamuyi ,ai ni naga komai hajara , ni dai kawai zan zubama sarautar allah ido , hajara tace eh hajiya duk da haka ,yanada kyau muyi magana, hajiya tace to shikenan, bayan sun shiga cikin dakin , hajiya hajara tace , gaskiya hajiya wlhy tallahi nayi imani ba haka hafsat tabar abbansu Rahma ba hajiya ,hajara takwashe komai tafadawa hajiya duk abun da yake faruwa a gidan , har hanasu abincin da hafsa take , da nuna rashin kulawar , da alhaji muktar yake a kansu , takara da cewar , nayi mamakin yanda abun bai tsaya akan mu , amma ace harke !! Gaskiya hajiya yakamata mu nemi mafita muta fadawa Allah munasawa ana taimaka mana da addu a dan gaskiya abun yayi yawa ,hajiya hajara ta kara da cewa ,wlhy hajiya a halin da ake ciki yanzu idan

Please Login or Register in order to submit comment