Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da hankali , hade da magiya da nuna tsatsar danasani , har sai da Sadik yaji yafara gamsuwa da maganganunta ,amma wani sashi na zuciyarshi na tunani mishi halayen Rukkaiyya nadaa , Sadik yayi shuru yana sauraranta tanata maganganuta , yace "kingama tayi saurin cewa ehh yaushe zakazo ayi magana toh in dawo .

Sadik yace " zanzo ni zan kwanta , kinsan yau week end , I need some rest please banaso ki dameni sai anjima , Sadik ya kashe wayarsa .

Bayan ya kashe Rukkaiyya tayi shuru kamar me nazarin wani Abu , daga bisani tace " yauwwa .

Tayi maza ta Shiga daki tafara kokarin canja kaya , tasa wando jeans da riga top pink , colour ta zauna ta rangada kwalliya , ta feshe jikinta da daddaden turare , tayi saurin ta dauki handa bag dinta , tasa wani shegen takalmi hill , ta daukko wani katon bakin glass ta saka , daga bisani ta daukko Affter dress ta daura akai , tanada veil din akanta ba laifi tayi kyau ,taje gaban madubi ( mirror )ta karema kanta kallo , tace " hummm yau Sadik duk taurin kanka ka ganni A haka sai ka zauce , da sauri tafita , tatarar da mahaifiyarta a falo, Hajiya Amina tace " kekuma inazakije naganki haka , Rukkaiyya tace " uhmm mama idan nadawo zanmiki bayanni, Hajiya Amina cikeda rashin kulawa tace sai kin dawo .

Da sauri tafita tabar gidan tayi saurin taran Abun hawa, sai da ta dan biya Saloon ta wanke kai sannan ta nufi gidan Sadik .

Bayan ta isa ba kunya ba tsoron Allah Rukkaiyya ta Shiga cikin gidan Sadik kowa na kallanta mutane suna ta mamakin , cewa tazo kuma bai mai da ita ba , ana jimama rashin hankali irin na Rukkaiyya , ko dayake *MAHUKACIN KISHIN* da take ne yasa idanta rufewa ba Abun da yadameta.

Kwankwasa kofar tafara ( knocking) gidan tafara yi Sadik yana kwance yaji kamar ana knocking , yayi saurin zuwa yabude , yanabudewa Rukkaiyya tayi saurin Shiga cikin gidan , da mamaki Sadik ke kallantace , shima binta yayi ya koma cikin gidan yace " ke lafiyan ki kuwa me ya kawoki gidana ?

Da mamaki Rukkaiyya take kallon gidan ko ina tsaf fiyeda take gidan tace " uhm Mijina waye tmyake gyara maka gidanan ne naganshi tsaf , nayi zatan indan nadawo sai nasha aiki Ashe ka gama komai , Sadik yayi murmishi yace" toh wai ke dama kina tunani rayuwata bazata tafi dai dai bane idan babuke , toh barkiji ,ni nama fi samun kwanciyar hankali fiyeda idan kina gidan .

Rukkaiyya tayi gyran murya tace" uhmm kaga nifa ba wannan ya kawoni ba kawai Dama so nake mushiga ciki zamuyi magana, Sadik yace A,a gaskiya bazan taba bari kishiga mun daki ba wai kinma manta ba aure tsakanin mu ne

Yace kinga ni nama manta inaso kizo ki kwashe kayanki kaf , dan anan nakeso in sa Amaryata .

Rukkaiyya jitayi kamar zuciyarta zata fashe tsabar tsananin kishin da tak Wai har ita Sadik zai kalla yace zai sa amaryarshi a dakinta , maganar da yacigaba da yine yasata saurin dagowa ta kalleshi yace ni na ma rasa me kike jira da bazakizo ki kwashe kayanki ba .

Rukkaiyya tasa kuka kirsa tace " haba Sadik me yayi zafi haka da har ka kemun irin wanan Abun gaskiya Abun da kakemun bana jin dadin , tana magana tana wani irin kashe murya ,tun anan tafara tafiya da tunanin Sadik , takara da cewar dan Allah mushiga ciki muyi magana, Sadik yace " toh mushiga amma karki Dade, dan banaso mudauki lokaci me tsawo .

Rukkaiyya da wata 'yar kwallar muna furci ta zubo mata tace " eh nayarda.

Suna Shiga Rukkaiyya tafara kokarin cire After dress din da tasa , tayi wata irin mika tace " wash wallahi na gaji ,tafara kokarin yaye veil din dake nade akanta .
Sadik yace " ke miye haka ko kin manta ba aure tsakaninmu ne kike kokarin cire tufafinki, Rukkaiyya tawani botsaro kirji ta matso kusa da Sadik tace" wallahi mijina nagaji da rashinka kusa dani kayi hakuri ka mai dani dakina , kafin ma nagama iddah wallahi nayi nadamar Abun da nayi , har yanzu nakasa sabawa da rashinka kusadani kayi hakuri dan Allah , yanda take maganar cikin kirsa aa shagawaba da kisisina da kuma salon yaudara .

Sadik ko duk yagama fita haiyyacinshi , yama rasa magana ba bu Abun dayake bakuta kamar kasan cewa da matarshi Rukkaiyya , dan ko ta zo ta tayarmishi da matsananciyar sha,awar da ta dade tana damunshi , kwata kwata ya kasa controlling kanshi , dakyar ya iya tattaro nusuwarshi yace" Rukkaiyya kije gidan zanzo in sameki , A satinan zaki dawo kinji .

Rukkaiyya ko da farin ciki yagama rufeta tayi saurin rugumar Sadik , dagangan tayi hakan, kafin kace me Sadik yakara fita , haiyyacinshi har yafara kokarin biyemata dan kwata kwata baya cikin haiyyacinshi ,saurin matsar da Rukkaiyya yayi yace "ki bari Rukkaiyya kar kisa muyi Abun da ba shine ba , kinga yanzu ba aure tsakanin mu .

Rukkaiyya tace" toh shikenan mijina natafi sai anjima , tafara kokarin maida After dress dinta , ta fita ta tafi cikeda farin ciki fam ranta,

Tana zuwa gida da far in ciki tashiga gidan ta Tarar da mahaifiyarta a falo ,da sauri ta karasa tace " hummm mama a satinan dai zankoma gidan Sadik ,

Hajiya Amina cikeda murna tace toh Allah yasa hakan , ni kuwa zan tafi can mai duguri ni da Sadiya da Hafsat dan yakamata suma akara musu aiki mai kyau

Dazu mukayi waya da Hajiya sailuba ta ce" wai akwai wani shahararren boka a can ya iya aiki iya aiki , idan Allah yasa kika koma sai muje a yi mana aikin saura kuma in kin koma ki kara wasa da damarki ki bari ya sakeki batareda kin yagi rabonki ba ,

Rukkaiyya tayi saurin cewa " haba mama hauka nakeyi kinsan irin wahalar da nasha kafin ya Amince ai bazan kara sakaci ba ,Hajiya Amina tace ai dayafi kam ,

Sadik ko bayan Rukkaiyya ta tafi kasa sukuni yayi burinshi bai wuce yajishi tareda mace ba , dan her ga Allah bakaramin sha, awa Rukkaiyya ta tayar mishi ba, dakyar ya je kitchen yanemi lemon tsamin da Lipton yasha dakyar ya dan samun relief .

Washe gari da safe, kiran Rukkaiyya yashigo wayar Sadik, dauka yayi, bayan sun gaisa yace " kinsan jiya kinbarnida kewa kuwa , dakyar nasamu nutsuwa bayan tafiyarki , Rukkaiyya tasa dariya tace " toh yanzu ya make ciki , ni kaina ina mutakar bukatarka mijina Sadik yace hummm ai baki fini ba , zanje in fada ma Hajiya yanda ake ciki zakijini , Rukkaiyya tace " toh Allah sa muji Alkhairi , Sadik yace" inshallahu zakiji Alkhairi , Nan Rukkaiyya takara tsarashi sossai , tadinga mai lallashi hade ba da hakuri da Nuna danasani akan bazata karaba aikata maka mancin Abun da ta aikata ba a baya har sai da Sadik yagamsu sossai yakuma mata Albishir cewa nanda kwana biyu tafara hada kayanta zai mai data dakinta farin ciki agun Rukkaiyya ba a magana , daga bisani sukayi sallama

Shiryawa yayi yatafi gidan Hajiya , kafin ya wuce aiki yana zuwa ya yake sanarwa da Hajiya cewa" yanaso ya dawo da Rukkaiyya . _*to fah masu karatu wa ance matada miji... ......*_

*MUJE ZUWA*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️ (MUM FU 'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 30*

*MATUKAR KUNASO IN CIGABA DA TYPING AKAI AKAI SANNAN INDINGA YAWAN READMORE TOH KUDINGA KOKARIN COMMENTS NAFI BUKATAR DOGON SHARHI BANSAN ACE TNX KO EMOJI SIGN KO KUMA STICKER BANA BAUKATAR WANNAN NAFI BUKATAR DOGON SHARHI PLSS HAKAN SHI ZAI KARAMIN KWARIN GWAIWA*

Hajiya ko murmishi kawai tayi irin nasu na manya tace toh Sadik ai bazan hanaka dawo da matarka ba , hasalima ni nafiso ta dawo din ko Dan ta zauna akan 'ya'yanta, Allah sa hakan shiyafi Alkhairi , dama hakane idan zama bai kareba dole sai ankoma .


Fatan kunyi magana tw fahimta , dashardin kar hakan Takara faruwa koh ??
Sadik yace eh munyi hajiya tace " bazata karaba .

Hajiya tace " Toh Allah yasa , kaima kuma sai kaji tsoron Allah kayi kokarin kyautata zamantakewarka da ita, ka kiyaye duk Abun da zai batamata ,

Hajiya tayi mishi nasiha me ratsa jiki .

Toh ya maganar auren naka fah ?? Sadik yada sosa keya yace , uhmm Hajiya inaga ko in dan dakata da maganar auren tunda naga ai mun sulhunta da matata koh .

Hajiya tace ," toh ni dai bazan cemaka dole sai ka Kara aureba , sanan bazan cemaka bazakayi aure ba , Allah yasa yanda tace zata gyra halinta hakanne dagasken ta gyara , amma a shawarce yin auren zai fiye maka Dan kuwa in dai ba kara auren kayi ba toh fa ba lallai Rukkaiyya ta gyaruba amma ina maka fatan dacewa , Allah sa hakan shiyafi zama Alkhairi, sannan zan shaidawa mahaifinka halin da ake ciki indan yadawo

Sadik yace " toh amma Hajiya Ina kina ganin aurena da Nafisa shine dai dai toh kawai zan hakura da dawo da Rukkaiiyya sai in auri Nafisa .

Ganin tsantar san da Sadik yakema Rukkaiyya Hajiya ta hango a fuskar dan nata yasata saurin cewa , A,a ni bance kar ka dawo da matarka ba , Kaje Allah sa hakan shiyafi Alkhairi .


cikin ranta kuwa tana aiyyana , wani irin abu Rukkaiyya tama Sadik haka da cikin kankanin lokaci tasa yamanta da duk cinmutuncin da tamishi , tayi imani badai asiri suka ma Sadik ba dankuwa tasan cewan asiri bazai taba cin zuri ar mallam babba ba wato kakansu Sadik ,

Amma zuciyarta ta rayamata cewa , kirsa fa da kisisina da makirci yafi boka yafi mallam , toh tabbas da wa inan abubuwan Rukkaiyya tayi nasarar samun zuciyar danta, amma zataita addu,a Allah karya Duk wani mugun nufinsu, Sadik ne yadawo da ita daga tunanin da take yace "

Uhmm Hajiya barinje in sanarma da Nafisa ko , Hajiya tayi murmishi tace" humm yanzu baza kaji kunyar tunkarar Yarinyarnan da wannan magana ba , kuma ta ina ma zaka fara mata bayani , sannan dawani ido zaka kalleta kafadamata ,baka gani zatace ka yaudareta , Sadik yace " A,a Hajiya nasan yanda zanyi in fadamata zanmata bayani yanda zata fahimta , Hajiya ta yi murnushi tace " hummm Sadik duk wani bayani da zakamata bazai taba gamsar da itaba , sannan karkamanta , karwani matsala ta biyo baya kazo kana danasani , sanan kar ka maida babban mutum kamar mahaifinka , karamun mutum , karkazo daga baya kace suje sukara nema maka auren Nafisa , wallahi tallahi Sadik baka isa kazo kace zaka komama Nafisa ba Idan hrr takuta hadaku da matarka ,kayarda ka amince ,????

Sadik yayi shuru yana tuna kalaman Rukkaiyya A lokacin da take mishi magiya da tsantsar danasani baiyyane a fuskarta .

Yace Hajiya inshallahu ma naga tayi nadama sossai Hajiya tace toh shikennan Allah yayi jagora,Sadik ya ansa da Ameen!!!.

Gidansu Nafisa Sadik ya nufa , yanazuwa Nafisa tafito daukeda murmishiba fuskarta ,bayan sun gaisa tace " lafiya naga jiya bakazo ba , Sadik yayi murmushi yace" lafiya kalau dama akwai wata 'yar magana da zamuyi ne dake, Nafisa ta tattaro dukkanin hankalinta tace " inajii

Sadik yace"Nafisa kinsan dlk abun da Allah yashirya babu makawa saiya faru ko idan har Allah yakaddara ni mijinkine babu makawa sai na aureki , in ko Allah bai kaddaraba toh fa babu yanda muka iya duk kuwa sandamukewa junananmu , Yakara dacewa" bawani bata lokaci Nafisa barin fadamiki kai tsaye kawai Nafisa na hakura da aurenki .

Wani irin faduwar gaba Nafisa tayi da taji maganar Sadik , sai kuma tayi murmishin da yafi kuka ciwo tace " hummm nasan hakan zata faru , nagode da batamun lokaci da kayi ,Sadik inshallahu tunda *Annabi Muhammad S A W* yabar duniya Sadik nabarka har abada, karkamanta sanka duk shi yajamun idan da ace nabi ta zabin iyayena tayuyu ma yanzu haka inada yara uku ko ko hudu amma natsaya na ce sai kai amma badamuwa Allah sa hakan shi yafi Alkhairi , garama da Allah yasa baka kawo sadakina ba Dan dayanzu abun zai fi min ciwo nagode .

Sadik yace" wallahi Nafisa ni kaina ba a San raina na aikata hakan ba , amma in hakan yabata miki kiyi hakuri zan aureki,amma ina tsoron kuyi kishi tareda matata , in kinga hakan yamiki shikenan zan aiko da sadakin ,

Nafisa tayi murmishi tace , hummm Sadik tundaganan nariga nagane cewa baka fi karfin gidanka ba hakan yasa nagane cewa kai ba tsayaiyye bane a gidanka , idan da a tsaye kake toh tabbas da bazakadinga shakku ko kuma jin wani tsoro Dan zaka kara aureba, wannan alamace ta kana tsoron matarka , takara dacewa" ni zan tafi Allah bamu Alkhairi , wata 'yar kwalla ta zubumata ,tayi saurin sharewa ,ta shiga gida a guje, Sadik nata kiranta amma ko waigowama batayi ba ta shige gida .

Sadik ko motarshi yaja ya tafi duk da cewa Sam baiji dadin abun da yafaru ba cikin ranshi , amma haka Allah yakaddara , tabbas yasan bai kyautama Nafisa ba amma yazaiyyi

Wani sashi na zuciyarshi ya tuno mai da Rukkaiyyanshi , yanda suka kasance jiya ,take murmishi ya baiyyana a fuskarshi yaji wani irin felling na bijiro masa , yaji anya ma zai iya bari har gobe kuwa kafin Rukkaiyya tadawo gaskiya a matse yake yana matukar bukatarta , dahaka ya yanke shawarar zuwa dakanshi ya daukkota a daren yau .

Gidan Hajiya yakoma yashaidamata ya je yafadama Nafisa komai , yakuma cemata yau da daddare zai je daukko Rukkaiyya ,Hajiya bata ce komai tace" Allah ya kaimu.

Fita Sadik yayi ya kira Rukkaiyya a waya yace , tayi sauri tashirya anjima da daddare zai zo ya dauketa , murna a gun Rukkaiyya ba a magana , tace " ai ni na ma dauka sai gobe in dawo Sadik yace kai bazan iya hakuri har gobe ba gaskiya kawai dai zanzo anjima , Rukkaiyya tace" toh shikenan badamuwa, sai kazo din ,Sadik yace" OK fatan dai kinmun tanadi na musamman ko my Ruki Rukkaiyya tace" hummm sossaima kuwa , Sadik yace toh tanadin me kikamun fadamun inji , Rukkaiyya tasa dariya tace hummm kai dai sai dai anjiman , Sukasa dariya baki dayansu , daga bisani sukayi sallama.

A bangaren Nafisa kuwa tana zuwa tasanarwa da iyayenta abun da Sadik yace ,basu ko damu ba sukace " Allah sa hakan shine yafi Alkhairi ,

Nafisa tace " mama Dan Allah kuzabamun duk Wanda kukaga yadace yazama miji gareni , Mahaifiyar Nafisa tace" toh badamuwa Allah miki Albarka , ta ansa da Ameen

Karfe Tara 9:00 na dare

Rukkaiya na hango cikin wani irin shiga Wanda duk na miji lafiya indai yaganta kwadaitu da ita, rigace halfvest tasa iyakacinta Kasan nononta , tasha adon stones sai kyalli suke, dawani Dan iskan boonshort, iyakarshi bai ma kai gwaiwartaba , tasha kyau ba laifi , da Sauri Sauri take shiri , gudun kar Sadik yazo yaga bata gama ba ,

Hajiya Amina da taketa kallon Rukkaiyya tace " hummm saura ki kara wani shirmen kisa ya sakeki , jibi zamu shirya mutafi Maiduguri da sassafe,

Rukkaiyya tace " ni na isa Hajiya tab ai zan kiyaye , Allah dai yasa mudace da bokanan , Hajiya Amina tace " ke wanan hatsabibine inaji a jikina za a dace , Rukkaiyya tace " toh Allah yasa .

Kara kinsatsawa Rukkaiyya tayi tsaf.


Tasha wanan ta ci wannan , ta bunka wannan ta matse wananan ,dahaka har tagama shirinta tsaf , tayi kyau ba laifi , Sadik kadai tazauna zaman jira .

Horn taji a kofar gidansu Alamar Sadik yazo da hanzari ta dauki abun da zata dauka, tasa Abaya tafita , tayima Hajiyanta sallama, tafita.

*MUJE ZUWA*


*MORE COMMENTS*😎😎😎

*MORE TYPING......*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️ (MUM FU'AD*)

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 31*
Mota tashiga daukeda murmishi a fuskarta ,

Sadik ya karema matar tashi kallo yace " kinyi kyau sossai Rukkaiyya tayi murmishi tace " hummm ai duk kyauna ban fika ba , gaba dayansu sukasa dariya .

Rukkaiyya tace ' toh yanzu zamu biya mu daukko yara kenan??

Sadik yace' A'a bayau ba yau ai nidake amarya da Ango ne , yau Amarci zamuyita cii ,
Rukkaiyya tasa dariya tace " toh shikenan ,

Sadik Jan motarshi yayi suka tafi.

A hanya ya siyamusu kaji ,bai siya abun shaba kasancewar akwai shi a gida .

Suna isa suka fito suka shiga gida hannunsu sakalle da na juna , daki suka shiga ,Rukkaiyya tafara kokarin cire Abayan jikinta , nanfa Sadik yakara rudewa ganin kayan dake jikin Rukkaiyya , gunta ya nufo ya kura mata ido , take ya janyota yafara bata wani hot romance .

Take yafita haiyyacinshi , dankuwa bakaramin sha,awa yakeji ba gameda matar ta shi

Rukkaiyya kuwa magana tayi tace" kai dear kadai bari muci abinci koh ?

Sadik dayake magana a wahale dan tsananin bukata yace " kai bazan iyaba ,kinsan yanda na missing dinki kuwa , wallahi ina matukar San kasancewa dake kitaimaka mun my Ruki ,

Rukkaiyya tace" nifa bacewanayi zan hanaka kaina ba , kawai dai nace yakamata muci abincine kafin mukwanta koh .

Dakyar Sadik ya iya tattaro natsuwarshi ,yace toh shikenan kiyi sauri dan Allah.


Kitchen Rukkaiyya ta shiga tadan dafamusu Indomie suka danci , da kazan suka kora da abunsha , daga bisani sukayi brush , suka nufi daki .

Jawo Rukkaiyya Sadik yayi yacigaba da bata hot romance take hankalinshi yafita a jikinshi , nanfa Rukkaiyya ta fara mayarmishi da martani take yakara rikicewa , babu abun dayake bukata kamar yajishi tareda ita _*nidai mum fu'ad na tattara inawa inawa nabar Sadik da Rukkaiyya dankuwa andade ba a hadu ba dan nasan kam yau Rukkaiyya zata gurzu a hannun maza ,asuba tagari Ruki and Sadik*_

Da Asuba Suka tashi sukayi wanka,bayan sunyi wanka sunyi sallah suka kara komawa barci , cikeda annashuwa dankuwa ba karamin dadin Sadik yaji ba.

Da safe bayan Rukkaiyya ta hada musu break fast, sun karya, sunata hira , daga bisani Sadik yace" bari yaje gidan Hajiya ya daukko yara


Rukkaiyya tace "toh sai kundawo ,

Gidan Hajiya Sadik ya nufa , duk Wanda ya kalli Sadik yasan cewa yana cikin farin ciki .

Dankuwa Hajiya ma kanta saida ta lura da cewa yana farin ciki , ta raya a ranta cewa Allah yasa a dore ,

Fadawa Hajiya yayi cewa yazo daukar su Khairat ne ,
Hajiya tace " toh badamuwa , nan aka shiryamusu kayan su , suka tafi.

Yaran basuso komawa gidan mahaifiyartasu ba dankuwa sunfisan zaman gidan Hajiya akan gidan mahaifinsu , Dan khairat har kuka tadingayi akan ita bazata koma gidan ba dakyar suka rarrasheta ta tafi .

Bayan sun isa gidane yaran suka shiga gida Koda yaran suka ga mahaifiyarsu basuwani yi murnan ganinta ba ,

Rukkaiyya tace" Ku Dan ubanku baku ganni bane ?
Sukace munganki , inawani , Rukkaiyya tace" ina wunin ubanku ,

Take ran Sadik ya baci, yace " haba Rukkaiyya yaza kidinga zagin yaranan a gaba na haka me suka miki ne wai haka??
Rukkaiyya tace " eh lallai bangane me suka min ba baka ganin abun da sukamun ne , yara sai kace banice na haifesu ba kaikuma sai ka dinga dauremusu gindi gaskiya ni banasan haka .

Sadik yace " toh ai kece yaranan bakya jansu a jiki ba dole sudinga baya baya dake ba ,
Rukkaiyya tace oooo kai kuma gaba gaba suke da kai ko , ka daure musu gindi sidinga mun rashin kunya , ai da kai sukema bazakayi magana ba.

Sadik yace " wacce irin magana kike haka ne Rukkaiyya??
Rukkaiyya tace" ohoo abun da kunnenka ya jiye ma ka , da haka suka fara cece kuce tana fada yana fada , dan kanshi yayi shuru ya kyaleta tana tayi .

_toh fa masu karatu Allah yakawomu tun ba a je ko inaba_

Bayan yadawo gida da daddare ne yasamesu suna kallo yace" Rukkaiyya ina abincina , Rukkaiyya takalleshi tace" yananan ke khairat tashi ki daukko mishi abincinshi a kitchen , tacigaba da kallanta .

Sadik yace " uhm Rukkaiyya kenakeso ki kawomin, kizo kisameni a dakina , ya wuce batareda yaji amsar da zata bashi ba .

Tashi Rukkaiyya tayi tana kunkuni ta daukko abincin , ta nufi dakin Sadik dashi.

Shiga tayi kai tsaye ko sallama babu tafara magana tace" ni gaskiya banajin dadin abun da kakemun yazakadinga kaskantar dani a gaban yara sai kace wata baiwarka , Kaduba Inda kawani mun magana sai kace 'yarka gaskiya ni nagaji wallahi .

Sadik yasa murmishi yace" oohhh lallai ma Rukkaiyya ni ne nake kaskantar dake , wai ke meyasa kikeso mudinga yawan sa insa dake agaban yaranmu ne , kece a kasa na dole ke zakiyi biyaiyya a gareni Rukkaiyya ,

sannan banaso kina daga murya akan abun da bai taka kara ya karyaba inaso mudinga fuskantan juna in wani a cikinmu yayi badaidaiba muyi kokarin fadamasa bawai mudinga sa insa ba kiduba kiga duk layinanan waye akejin Kansu in ba muba , babu wanda baya fada da matarshi , kuma su shirya , waye yake jinsu amma sai mu gaskiya yakamata kigyara .

Aiko Rukkaiyya ta mike tace " eh lallai ma , kanaso kace nice ma mara gaskiya kenan koh ? Ai barikaji indai har zakamun Abun danace da abun da nakeso toh zaka samu kwanciyar hankali , amma fa in bahaka ba toh fa munyita tashin hankali kenan .

Sadik yace "eh lallai ma ni kikeso in zama matar ke kizama mijin kenan koh ?? Toh wallahi karyane badai a gidanaba , dan sauran yan uwanki suna juya mazajansu toh ni ba haka nakeba na fadamiki ,tun wuri ki gyara , ko dan kinga ina biye miki toh barikiji , kar ki bari ki

Please Login or Register in order to submit comment