Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma bakizo da wuri ba , sun fita inzaki jira kijira in bazaki jiraba kitafi.

Shuru Hajiya tadan numfasa tace," toh shikenan nagode .

Kallanta Sadik yayi yace," umma baki gane Hajiyata bane kike mata irin wanan magana ??.

Umma na cin Cingum tana kas kas tace," ehh Na ganeta mana , ya kakeso in mata magana , tana magana hade da galla harara .

Bude baki Sadik yayi zaiyyi magana Hajiya takalleshi tayi mishi nuni da ido akan yayi shuru .

Bayanda Sadik ya iya haka yayi shuru, badan yaso ba Sai Sai bin umarnin Hajiya , yana me jin zafin abun .


Anti Sadiya da Anti Hafsa ne zaune gurin kasungumin bokansu, suka fada mishi bukatunsu , nan yayi 'yan duba dubanshi da muryarshi mara dadin ji , yana magana bakin shi na tashin doyi yace", kucewa 'yar uwarku matukar tanasan mallakar mijinta , toh fa sai ta rage duk wani kishin da takeyi , sanan kuma matukar bata bari Sadik ya kusanci matar da ya auro ba toh babu yanda za,ayi aikinmu ya tafi daidai , dole sai Tayi Hakuri .

Cikin tsawa yakara da cewa ," kuma wanan shine karo na karshe da zamuyi mata aiki , in takara lalata aikin toh bazan kara mata aiki ba ,sabida haka tun wuri Ku fada mata.

Cikin ladabi Anti Sadiya tace," ranka yadade ai hakan ma bazaiyiyuba , bazata kara saba umarnin ka ba ayi hakuri .

Ba tare da yabata ansa ba yace," kekuma , daf aikin ki yake da rushewa , dan kuwa ba da dadewa ba sihirin da mukayi mishi zai karya , kuma ni naduba banga hanyar da zan bi in kara wani aikin akanshi ba , dan naga taurarinshi lullube yake cikin duhu , bana ganin komai , da alama ya hadu da wata Aljanar da ta bashi makari , Wanda bansan wani iri bane," Shiyasa suka boye mun komai gameda shi.

Zufa ce ke karyoma Anti Sadiya ta ko ina, cikin tsananin tashin hankali tace," ran boka yadade kataimaka ka kara bin cikawa , kataimakeni tana magana kamar me shirin yin kuka.

Cikin matukar tsawa boka yace," da akwai wata hanya ai da na fada miki, banasan ana jayaiyya ko gardama dani , wanan shine magana , babu wata hanya kuma .

Cikin ran Anti Hafsa farin ciki tayi da hakan tana murnan cewa ,duk cikinsu ita kadai ce zata dinga juya mijinta , zataji dadi da hakan .

Shuru Anti Sadiya tayi hankalinta a matukar tashe , cikin ranta tana aiyya , Allah yasa itama Hafsa nata aikin yabaci tunda nata ya lalace , tunda nata yabaci na uban kowa ma ya baci .

Da sauri tace,"uhmmmm toh boka na 'yar uwata fa ,??.

Nan yadan kara duba dubanshi yadago yace," kaii!!! Ya kallo Anti Hafsa yace ," matukar kikabari mijinki yayi ido biyu da mahaifiyarshi , to fa kisani daga ranar aikinki ya karye kuma kema basan yanda zanyi in gyara ba .

Murna Anti Sadiya tayi cikin ranta tayi matukar farin ciki da hakan .

Wani yawun azaba ne yadirarma Anti Hafsa makoshinta , ta hadiye tace," boka mamartashi zatazo ne?? .

Boka yace," nankusa ma kuwa ,
Cikin tashin hankali Anti Hafsa tace," nima babu hanyar da za,abi dan taimakamum ??.

A takaice boka yace," babu, kutashi kushiga in sallameku kutafi inada masu zuwa .

Anti Hafsa tace," uhmm boka bukatar mu bata biya ba yau ma kuma sai munshiga ??.

Wata razananniyar tsawa boka yadaka mata yace," Ai tunda kuka tako kukazo ko da bukatarku bata biya ba ni sai kun biya mum tawa bukatar .
Basu kara Cewa komai ba .

Tashi sukayi suka Shiga cikin karamin bukkar suka tube ya kallesu tsaf kamar yanda suka saba .

Bayan ya kallesu , yace," su sa kayansu , su tafi .

Haka suka sa kayansu suka fiti jiki a matukar sanyaye.

Mota suka shiga suka nufi asibiti ransa Sam ba dadi .



A bangaren Hajiya Rahmatu kuwa , shiryawa takeyi dan tafiya gida , gurin mallamin taje dan bata wasu magun guna, wani , rubutu ya daukko ya bata yace," tasan yanda zatayi tabashi yasha , Batareda matarshi tagani ba , ya kuma daukko wani turare yace," shima ta shafa a jiki kafin tashiga gidan , sanan yakara da cewa bayan hankalinshi ya fara dawowa jikinshi tayi kokari wajan fada mishi ya rike addu,a magunguna sossai ya bata da hayaki , godiya ta dinga mishi daga bisani ta wuce ta tafi tana farin ciki da hakan .


Su Anti Sadiya na shiga suka tarar dasu Hajiya da Sadik zaune .

Bayabo ba fallasa sukace," ina wuni , murmishi dauke a fuskar Hajiya tace," lafiya kalau ya me jikin , da sauki suka ce, a takaice .

Cikin sanyi murya Hajiya tace," akwai abun da kuke bukata ne ?? gashi sai kumishi magana .

Harara Anti Sadiya tabanka , tace ," bama bukatar komai , illa ya fara shirye shiryen kiran sammaci da ga koto dan wallahi bazamu yafe ba , jira Muke Rukaiyya ta farfado Mu maka ka a kotu , da na kiraka ai kin zuwa kayi sai yanzu zakawani zoo , toh Allah dai yasa Mu ba matsiyata ba ne , kuma babu abun da muke bukata daga gareshi .

Mamaki sossai Hajiya tayi da jin kalaman Sadiya , tace," Haba Sadiya kiyi hakuri zan dauki matakin daya dace, namiki Alkawari , Sadik bazai sake makamancin haka ba , inaso ma tana jin sauki takoma dakinta ,.

Tab Anti Sadiya tace," cikin fushi tace," kinsan abun da danki ya haddasa mata kuwa ,?? Ya je ya samata ciwon zuciya , dalilinshi takuma da hawan jini da ciwon zuciya , ga dukan da tasha a gurinshi sabida haka wallahi bazamu yarda ba ehee ,ai ki ma daina maganar komawa gidan Sadik ya ma rubuta mata takardarta kawai .

Tunda ake magana Sadik bai ce komai ba, duk da cewa ranshi ya mutakar baci.

A fusace ya tashi zai fita a dakin .

Da Sauri Hajiya tace," dawo , badan ranshi yaso ba ya dawo , Hajiya ta kalleshi tace," basu hakuri .


Yaso yayi jayaiyya akan hakan , amma gani fuskar Hajiya babu Alamar wasa , zai zallar bacin rai yace," kuyi hakuri .

Harara suka bishi dashi batareda since komai.

Shima ba tare da yaji amsar da zasu bashi ba yafita rai a bace , yanufi moto ya shiga , ya zauna yana jiran fitowar Hajiya ya kaita gida , dan yasan ba dadewa zatayi ba .

Kallansu Hajiya tayi tace," dan Allah kuyi hakuri irin haka bazai sake faruwa ba inshallahu nayi muku Alkawari .

Hajiya na fadin haka tace" ni zantafi sai anjima, mujima dayawa , amsar da suka bata kenan.

Fitowa tayi ranta Sam ba dadi , mota tashiga , batareda tace ma Sadik komai ba .

Shurun da Hajiya tayi ne ya tabbatar ma da Sadik ranta yabaci .

Cikin sanyi murya Sadik yace," Hajiya kiyi hakuri , nasan duk abun da suka miki baki ji dadi ba , kuma nasan duk nine sila , inshallahu nayi alkawarin duk abun da Rukaiyya zatamun zan jutlre bazan kara kallantaba , ballantana kuma in biye mata har insa hannu a jikinta ,

Duk da cewa ba,asan raina zandawo da Rukaiyya gidana ba sai dai dan in cika umarnin ki , Allah sa hakan shiyafi zama Alkhairi .

Numfasawa Hajiya tayi tace", Ai duk abun da kamun Kaine sila kai ka daki 'yar uwarsu , dole su gayamun magana , amma yawuce Allah ya kyauta , Ameen Sadik yace.

Sadik yace Maganar su tacewa wai za a je kotu aje din , Hajiya tace," toh bari muga abun da Allah zaiyyi .


Bayan fitar Hajiya, Anti Anti Hafsa tace, uhmm nikam Barin je gida dan wallahi hankali na a tashe yake kar wanan Muna fuskar tsohuwar tazo , bananan su hadu inshiga uku.

Anti Sadiya tace," toh yanzu me zakiyi ,?? Anti Hafsa tace," uhmmm zanje in ma me gadi magana akan karya kuskura yabarta tashigo gidan batareda izinina ba.

Anti Sadiya tace, " toh ai sai ki hanzarta nima yanzu zantafi gidan muga abun da zai faru .

Tashi Anti Hafsa tayi ta tafi gida .


Tana isa gida bata tsaya ko ina ba sai gurin me gadin gidan .

Kwalamishi kira tayi , da Sauri yafito yace," ranki ya dade gani, yafada cikin risinawa .

Anti Hafsa tace," kasan Uwar megidanan ,?? Megadi tace," kwarai kuwa , amma raban da inganta har na manta , Anti Sadiya tace," bawanan na tambayeka ba , abun da nakeso shine daga yau karka kuskura kabarta tashigo gidanan , batareda izinina na ba ko tazo kace bayanan yayi tafiya , kasan Allah idan kabarta tashigo wallahi tallahi a bakin aikinka , Kasan zan iya koh ??, cikin girmamawa yace," inshallahu bazan barta ba.

Anti Hafsa ta galla harara tace," zabi yarage naka , tana fadin haka ta yi tafiyar ta .

Kwalama su maimuna kira tafarayi , jin kiran da takemusu sai da gabansu ya dadi .

Da Sauri suka fito , cikin girmamawa da risinawa sukace gamu .

Harara ta galla musu tace," ina yarana , Rahma tace," suna dakinmu .

Ashar Anti Hafsa ta kutuntumo tace," dakinku??? Shine zasuka shiga wannan kazamin dakin dalllah kiramunsu .

Kiransu maimuna tayi tace," Anti tadawo kuje tana kiranku , badan ransu yaso ba suka tashi suka fita.

Bayan Sadik ya ajiye Hajiya a gida , direct gidanshi ya nufa ......✍️


*MUJE ZUWA*


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.....*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 48*

Gida ya nufa cikin bacin rai .

Aisha datake kwance akan kujera tayi saurin tashi ganin yanayi da yake ciki tace," lafiya naganka haka ,?? .

Cikin sanyi jiki yace," wallahi nayi danasanin hada zuri,a da su Rukkaiyya .

Da sauri Aisha ta katseshi da cewa , bai kamata kadinga fadin haka akan Uwar 'ya'yanka ba , komai yayi farko akwai karshe , tadan numfasa tace," bana bukakar kafadamin abun dayafaru , ina me baka hakuri akan koma menene , sanan dan Allah ina neman Alfarma a gurinka .

Sadik yace," ina jinki mene ne Alfarmar matukar batafi karfi na ba inshallahu zan miki.

Cikin matukar girmama mawa, tace," dan Allah inaso kabarni Inje asibiti in duba jikinta ,dan Allah ??.

Kije fa ki duba jikin Rukaiyya kikace ??

Aisha tace ", ehh dan Allah

Sadik yace," gaskiya banyarda ba , yan uwan Rukaiyya , zasu miki cin mutuncin da bakya tunani , ko Hajiya ta basu kyale ba balle kuma kee , sabida haka ban yarda ba , bazan iya jurar cinmutuncin da zasu miki da ga garesu ba .

Cikin sanyin murya Aisha tace,"dan Allah kayi hakuri kabarni in je duk abun da sukamin naji badamuwa , amma nidai ina rokonka kayi hakuri kabarni in je.

Magiya sossai Aisha tadinga yima Sadik har sai da tasa ya amince ya barta , yace," amma shi zai kaita dakanshi zai jirata har ta fito sai su dawo tare .

Tashi tayi da sauri dan shiryawa .


Karfe shida na yamma Hajiya rahmatu ta iso garin Bauchi bata zarce ko inaba sai gidan tillon danta.

Kwankasa gate din tafarayi bayan ta yi duk abun da mai maganin ya umarceta tayi .

Da Sauri me gadi yatashi dan zuwa ya bude kofar gate din .

Gabanshi ne yafadi ganin Hajiya Rahmatu a tsaye a bakin kofar .

Tsaye yayi yana kallanta , yana tunanin barinta shiga cikin gidan .

Mamaki sossai Hajiya tayi , da yanayin kallan da mai gadi ke mata , cikin mamaki tace," kai bala , baka ganeni bane ???.

Cikin girmamawa bala yace," naga neki Hajiya , wallahi Hajiyar cikin gidan ce tace,' idan nasake na bude miki kofa batareda izininta ba to a bakin aikina , nikuma ina tsoro in rasa aikina .


Mamaki sossai Hajiya tayi , cikin ranta tana aiyyana cewa wato har bokanta ya shaida Mata zuwanta koh , eh lallai .

Cikin sakin fuska tace," toh Yaro ko zakaje kafada mata kace nazo.

Yace," eh barinje.

Ya juya zai tafi tayi saurin dakatar dashi tace", uhmm muntarin na cikine ???.

Cikin girmamawa yace," eh bai dade da shigowa ba gaskiya .

Hajiya tace," toh kaje kace mishi yazo yayi baki .

Bala me gadi yace," toh toh shikenan barinje .

Dakin yashiga yayi sallama .

Hakimce Anti Hafsa take a kujera , ganin me gadin yasa gabanta ya mugun fadi , tace," kai lafiya kuwa .??

Cikin girmamawa da rawar baki yace," daa..ma.. Hajiyan tazo ne tana kofar gida .

Cikin tsananin yashin hankali Anti HAFSA tace," tashigo ne?? , cikin girmamawa yace,"A,a na hanata shigowa amma wai ta ce in kira mata Alhaji .

Da Sauri Anti Hafsa tayi kasa kasa da muryar tace", kayi Sauri Kaje kace mata bayanan .

Zaro ido bala me gadi yayi yace," toh ai na Riga nace yana ciki .

Tsawa Anti HAFSA ta Daka ma bala me gadi.


Sai da tsawar yasa Alhaji muktar fitowa a daki . tace," kai wani irin Mara hankali ne , me nafada maka ,??.

Cikin rashin fahimta Alhaji muktar yace", wai lafiya kuwa naji hayaniya .

Da Sauri Anti HAFSA tace", koma cikin , tafada rai a hade lafiya kalau , katafi tunda ban kiraka ba , yana magana tamkar tana magana da danta .

Kallan mamaki ya bita dashi baice komai ba yashige daki .

Da sauri Anti Hafsa tace," kai fita fita kace bayanan .

Da Sauri yace toh toh shikenan .
Komawa yayi yace" Hajiya Ashe bayanan .
Mamaki sossai Hajiya tayi tace", amma kai kace mun yananan koh ??.

Cikin Inda inda yace", eh yanzu naje naduba ashe wai bayanan .

Batareda ta gamsu ba ta juya zata tafi.

Rahama na kallan duk abun da sukeyi, ganin Hajiya zata tafi yasa tayi sauri , ta nufi bakin gate din .

Bayan ta tabbatar bala mai gadi yashiga dakinshi .

Da sauri tayi kasa da muryar tace ," Hajiya , juyowa Hajiya tayi tace," Allahu Akabar Rahamatu kece kika dawo haka ?? duk kin lalace Ina Maimunatu ??? , kuka Rahma tasa tace" tana cikin gidan .

Da sauri tace," Hajiya wallahi babbanmu na cikin karya ne da yace miki wai bayanan , yana nan , amma ki dawo gobe ni nasan yanda zanyi ki ganshi , kinga gobe lahadi babu Inda yake fita , ni nasan yanda zakiyi ki ganshi


Albarka Hajiya tadinga Samata ,har sai da tayi wata 'yar kwalla tace," kiyi hakuri kinji komai yakusa zuwa karshe inshallau kinji , sossai Rahama tayi farin cikin da hakan.

Daga bisani sukayi sallama .......✍️


*MUJE ZUWA*

*KUYI MANAGE DA WANAN DABABU GARA BA DADI*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.......*✍️✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 49*

_*DAN ALLAH DAN ANNABI , I,AM VERY SORRY FOR THE LATE POST , WALLAHI , BA,ASAN RAINA BANE , KARKUCE JAN RAI NE PLSS*_


Aisha da Sadik ne ke hanyar su ta tafiya Asibiti .

Suna dan taba hirarsu ta masoya a hanya .
Bayan sun isa asibitin parking yayi , yace," tashiga zai jirata a cikin mota .

Aisha tayi tayi Sadik yashiga dakin amma fur yaki , kwatanta mata dakin da take yayi ,tatafi .

Shiga dakin tayi da sallama dauke a bakinta , wani kallo Anti Sadiya tabita dashi .

Cikin masifa Anti Sadiya ke fadin kee !! Uban me ya kawoki nan ?? Munafurci ko me ?? duk munafurcin da kikayi a gidan bai isheki ba sai da kikazo har nan koh??.

Murya a Sanaye Aisha tace," kiyi hakuri dan Allah , wallahi ni ba nufi na ba kenan , nadai zo duba jikinta , ne .

Da sauri Anti Sadiya tace," munafurcin banza , kice dai kinzo gani ko takusa mutuwa dai .

Anti umma da take sauraransu tace," Sadiya , badai wanan ce amaryar da Sadik yayi ba ,?? Ta nuna Aisha da yatsa .

Anti Sadiya tace," wallahi ita ce tsinanniya ba .
Ashar Anti umma ta kutuntumo tace," Eh lallai zaki ci bura ubanki , tsabar rashin mutunci , Ku hadu da mijinki kumata duka , kuma tsabar makirci ki wani taho, da sunan dubata , ko kitashi kifita , ko yanzu in miki dukkan da yafi Wanda kukayi ma Rukkaiyya.

Cikin rawar murya Aisha tace," dan Allah kuyi hakuri wallahi ba abun da kuke tunani bane ,wallahi basa hanuna a cikin dukkan da Sadik yamata , nima fa mace ce taya zan bada goyon baya ci mutuncin 'yaruwata mace ina kallo kuyi....... bata karasa magana ba taji saukar kyawawan muruka a kuncin ta , a gigice Aisha tace," menayi miki haka ,??.

Cikin balbalin masifa Anti umma ta ce," ko kifita ko kuma wallahi in kara miki abun da yafi haka , kifita!!! nace" tafada da kakkausar murya .

Wani kuka Aisha tasa tafita a dakin asibitin da mugun gudu .

Bata tsaya ko inaba sai cikin motar Sadik , tun fitowar Aisha daga dakin Sadik ya hangota da gudu tana kuka .

Tambayarta yafarayi yana cewa lafiya me yafaru me suka miki???.

Shuru Aisha tayi batace komai ba banda shashekar kuka da takeyi.

Ran Sadik yayi mugun baci , ko ba,a fada ba yasan su Anti Sadiya sun mata wani Abu ne .

A zuciye Sadik zaifita a motar , da sauri Aisha ta ruko rigarshi tace," dan Allah mijina kayi Hakuri dan Allah mutafi gida kawai .

Cikin zafin rai Sadik yace," yazakice mutafi bayan baki fadamun abun da suka miki ba , kuma kice kar inje inji .

Gogge hawayenta tayi , tadanyi murmishi tace," kayi hakuri , idan mukaje gida zan maka bayani kaji mijina.

Zama yayi ya tada motar suka tafi gida , badan yaso hakan ba.

Anti Sadiya ce tace," wallahi Anti umma kin mum daidai da kika tsinke tsinanniyar nan da Mari , kiji tsabar munafurci tawani tattaro shirmen kafarta tazo wai wani taro dubiya .

Anti umma tace," shegiya ba manta da ita kawai .

Uhmmmm Anti Sadiya tace," ta mike tace," barin zo in tafi gida , tunda ke zaki kwana a nan koh ??.

Anti ummah tace," iyi toh yazanyi tunda takama , amma kunsan da inada aure bazan kwana ba wallahi .
Anti Sadiya tace," toh nidai barin tafi , sai Nazo gobe da safe .

Allah yakaimu Anti ummah tace.

Bayan Aisha da Sadik sun koma gida , Sadik bai ma bari Aisha tazauna ba yace," toh munzo gidan fadamin abun da suka miki .

Murmishi Aisha tayi tace," kai mijna baka mantuwa ne ?.

Sadik yace", yaza ayi na manta naga amaryata a cikin wani irin yanayi.

Zama Aisha tayi a kujera tacire gylen jikinta , tace," amma kafin in fada maka inaso kamun alkawari bazakace komai ba game da hakan , idan nafadama anan zaka barshi .

Sadik yace," ya zakice haka , gaskiya bazan iyaba idan kuma maganar mai muhinmmancin da yakamata a ce dole sai an dau mataki fah .

Aisha tadan numfasa tace," toh bakayi Alkawarin ba kenan ?? .
Sadik yace," gaskiya banyi ba .
Aisha tace", toh shikenan nikuma bazan fada ba gaskiya , da sauri Sadik yace," kifada nayarda , anan zamuyi kuma anan zamu barta .

Nan Aisha tafada mishi duk abun da su Anti sadiya da Anti umma suka mata .

Ran Sadik yayi matukar baci dajin abun da Aisha tafada mai , cikin Bacin rai yace," amma baki kyauta mum ba da kikace wai kar in ce komai akan wanan muhimmin abu , yaza,ayi tadau hannu ta mareki akan me?? .

Dan kasa da murya Aisha tayi tace," dan Allah komai ya wuce , nida akama na hakura , kaima kuma inaso dan Allah ya wuce a gurin ka , badan Sadik yaso ba yace," shikenan , amma wallahi wanan zai zama na karshe bazan Kara yarda irin haka ta faru baa, bazama yakara faruwa ba inshallahu , shine abun da Aisha tafada.

Kiran Sallar magriba aka farayi .

Tashi Sadik yayi yashiga toilet dan dauro alwalaya .

Bayan yafito nan yake cewa Aisha itama ta tashi taje tayi Alwala tayi sallah.

Cikin jin kunya tace," uhmm banayi ,gaban Sadik ne yafadi yace," kina nufin kina period ?? cikin jin kunya Aisha tace", uhm dazu nima naga yazo mun .

Jikin Sadik a Sanaye yace," amma banji dadi ba , nagama tunanin yau dinnan daddare sai na miyar dake cikkakkiyar mace, amma wanan abun yabatamun komai , yafada yana dariya , kamota " yayi yace,ke banma yarda ba sai na duba.

Da gudu Aisha tabar gurin tana dariya , kiranta yafara amma tanaji taki zuwa .

Masalaci Sadik din yafita ya tafi .

Koda Anti Sadiya tada wo gida samun Alhaji madu tayi akan darduma yana addu,a .
Ko kallanshi batayi ba tawuce daki .

Bayan ya idar daki ya biyota yace," Sadiya ya me jikin ?? .
Batarreda takalleshi ba tace," da sauki , yace," Allah kara sauki , batareda da ta am saba yafita a dakin ya nufi massallaci .

Tunani maganar da boka yayi Anti Sadiya tafara , take ta mike tashiga dakinshi tafara bincike ko zata ga wani Abu , amma inaa tagama bincikenta tsaf bataga komai ba , haka tafito a dakin cikin matukar jin haushi .


A bangaren Hajiya Ramatu kuwa , tsohon gidanta ta tafi.

Samunshi tayi duk yayi kura yayi datti , dan goggewa wa tayi ta dan gyara Inda zata kwanta , bayan tasiya abinci a waje taci.

Bayan Sadik yadawo saga sallah bai shigo gida ba sai da yaje restaurant yasiyo musu abinciin da

Please Login or Register in order to submit comment