Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki yasa ya kyaleta yabarta haka , badan yaso ba .

Tashi yayi yafara kokarin daukanta dan kaita bayan gida , nan ya hada mata Ruwan wanka, ya gasa mata kasanta , kuka sossai Aisha takeyi , dan kuwa bakaramin azaba taji ba , shikanshi Sadik din sai da ya tausayamata , Aisha kuwa wani haushinshi takeji , cikin ranta tana aiyyana cewa kamar bashida imani _nikuwa nace ba laifinshi bane andadde ba,a hadu ba_.

Dakyar Aisha ta iya yin wankan ta fito a bayan gidan , ta dauro Alwala tayi Sallah .

Shima cire bedsheet din yayi dan kuwa duk ya baci, bayan ya cire, yashiga toilet yayi wanka yayi Sallah ya nufi masallaci .

Bayan Aisha ta idar barcin wahala ne yayi awun gaba da ita.

Shima bayan yadawo ya kwanta rugume da ita, yaso yadan kara , amma tausayinta yasashi ya hakura , ba dan yaso ba .


Karfe tara sadik ya farka , da kanshi yaje ya hadamusu break fast yazo ya shirya musu , yakarayin wanka yana jiran Aisha ta tashi .

Karfe shadaya Aisha ta farka , dakyar ta iya tashi , dan kara tasa jin zafin dayake kasanta .

Da sauri Sadik ya Shiga dakin jin ihunta , dan riketa yayi ya taima kamata ta fito a dakin .

Sannu yafarayi mata hade da sa mata Albarka dan kuwa bakaramin dadi Aisha tajiyar dashi a Daren jiya ba .

Ita kuwa haushin shi takeji .

Taimaka mata yayi tashiga toilet tayi brush tafito ,ta karayin wanka.

Fitowa tayi ranta a bace , cikin muryar shagwaba r
Tace," kafita zansa kaya .

Yanayin yanda tayi yaso bashi dariya , yace," ko in tayaki sawa ne ?, cikin shagwaba Aisha tasan cuno karamin bakinta talangwabar Sakai tace ,"banaso .

Dariya sossai Abun yaba Sadik , batareda yace komai ba yafita a dakin .

Shiryawa tayi , dan powder ta shafa a fuskar sai tasa kwalli , tadan sa janbaki , tadaukko Atamfarta mai kyau tasa, ta murza daurin ture kaga tsiya , tayi kyau sossai , duk da cewa batayi wani heavy make up ba , amma hakan bai hana kyanta fitowa ba .

Fitowa tayi ta nufi falan dakyar take iya daga kafarta ,
Rai a bace ta nemi guru ta zauna .

Kallanta Sadik yayi yace," wai fushi gimbiyar take dani??.

Batareda ta kalleshi ba ta dan daga kafa dakyar taje gurin dinning dan yin break fast .
Shikenan tunda bazaki kulani ba , Sadik yafada cikin sigar tsokana .

Zuwa yayi ya taimaka mata sukayi a break fast a tare.

Bayan sun gama ya kwashe kayan ya kai kitchen ita kuwa tadan kwanta a kan kujera .

Wunin ranar kulawa da riritawa Aisha ke samun sossai a gun Sadik .

Dakyar ya iya shawo kanta , ta saukko daga Fushin da takeyi dashi .

Kusan kullum Sai Sadik ya lallaba Aisha ya biya bukatshi , duk da cewa har yanzu Aisha na jin zafi , amma bata iya hanashi idan yazo mata da bukatarshi, dan tasan a gurinta ne kadai zai samu , Shiyasa bata hanashi .

Sadik har wani dan kyau yakara , yayi Kyan angwanci , dan kuwa abun da yakeso yasamu , Shiyasa yake jin shi sakat babu abun dake damunshi , dan wani lokacin har mantawa da Rukaiyya yake .


Yau satin Rukaiyya biyu a Asibiti , ba laifi tadan samu sauki , dan kuwa ana saran sallamarta a cikin satin , tayi rama sossai .

Hajiya ce tace su khairat suje su gaisheta , kausar kuwa kinzuwa tayi , dakyar Hajiya tamata magana taje gaisheta.

Ko da suka je Asibtin basu wani dade ba suna zuwa suna gaisheta suka fito suka tafi .

Sadik ya kara Zuwa gaisheta sau daya yana zuwa batareda ya Dade ba ya tafi.

Ganin irin Kyan da yayi na amarci yasa Rukaiyya taji kamar ta kurma ihu , dankuwa yanzu tasan cewa yasan Aisha a matsayin mace , kuka tadingayi sossai , tana tuna yanda Sadik zai kasance da Aisha ........✍️
*MUJE ZUWA*


*ABUN DA YASA NAKE DAN LATE UPDATE NAFISO INDINGA MUKU LONG PAGES SABIDA MUSAMU MIYI MUGAMA LITTAFIN , DAN WALLAHI ALLAH ALLAH NAKE IN GAMA*


*IDAN NAGA CIMMENTS IN KARA MUKU LONG PAGE GOBE , IN BABU , SAI RANDA ALLAH YAYIπŸ™„πŸ™„πŸ™„πŸ’β€β™€οΈπŸ’β€β™€οΈπŸ’β€β™€οΈπŸ’β€β™€οΈ, YADANGANTA*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.......*✍️✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 53*

*_WALLAHI INASAMUN KARANCIN COMMENTS , KO KUNSAN COMMENTS DINKU SHIKE KARAMUN KWARIN GWAIWAR YIN TYPING , TOH MEYASA BAKWAYI ???, WALLAHI JIKINA NA MUTUWA RASHIN SAMUN COMMENTS MAI YAWA . LABARIN NAN NADA TSAWO ,AMMA RASHIN COMMENTS SHI ZAISA IN GAJARTA LABARIN , DAN GASKIYA ALLAH ALLAH NAKE IN GAMA , DA INA SAMUN COMMENTS DA MUN CIGABA DAN LABARIN NADA TSAWO AMMA BAKWA COMMENTS , DA KUMA NADINGA POSTING AKAI AKAI , AMMA RASHIN COMMENTS DA DOGON SHARHI WALLAHI SHIYAKE HANANI MUKU UPDATE KULLUM, NAGODE_*


Anti Sadiya Rukaiyya ta kalla , cikin muryarta me sanyi tace," Anti ni gaskiya kin cuceni , wallahi baki kyautamun ba , yazaki ce Sadik yasakeni , tana fada ta fashe da kuka .

Wata Uwar harara Anti Sadiya ta gallamata tace" dake baki da hankali , ke in akace ki koma gidan komawa zakiyi kenan?? , har kina wani ikirarin na cuce ki , Rukaiyya ni na cuceki , ? Duk gatan da na nuna miki , miye a ciki basai kije ki auri Wanda zaki juyashi ba hankali kwance .

Kunkuni Rukaiyya tadinga , amma cikin ranta tasha Alwashin sai Aisha ta bar gidan Sadik kota halin yaya, dan Sadik nata ne itakadai har Abada .

Bayan kwana biyu aka sallemusu , gidan Anti sadiya dukkansu suka nufa .

Samun Alhaji madu sukayi akan kujera yana kallo .

Ganin su yasa yatashi yace," ina zakuje ba na kiraki a waya kince an sallameta ba , to ta tafi gidan mijinta mana .

Cikin kasa da murya Anti Sadiya tace," kayi hakuri , zata zauna anan wanan tsinannen mijin yasaketa, tsabar mugu ne shi , bai duba halin da take cikiba ya saketa .

Alhaji madu yace," toh me tayi mishi haka ,kuma kince Hafsa ma auranta ya mutu koh ??

Cikin ladabi Anti Sadiya tace," iyi ai kabar tsinannu dabasu san mutuncin aure ba .

Alhaji madu kuwa cikin ranshi yake fadin, humm Sadiya da kinsan me nake shirin miki da kin hada da kin tsinewa , amma zan zuba miki ido daga ke har kanan naki.

A fili kuwa cewa yayi toh shikenan Allah ya kyauta , murna sossai Anti Sadiya tayi tace ," humm Ameen fa Alhaji na .

Cikin daki zuka shiga suka zauna ,ran Anti Hafsa ya matukar baci, cikin ranta take fadin cewa, wato Anti Sadiya duk ta janyo auransu ya mutu amma ita ji yanda takeyima mijinta ladabi , eh lallai ma , nan tafara kullakullan irin makircin da zata shiryamata har Sai ta bar gidan ita kuma Alhaji madu ya aureta .

Rukaiyya kuwa shuru tayi dan ita tasan abun Dake damunta , duk minti daya Sai tayi tunanin Sadik ,tana raya cewa yanzu haka yana tareda matarshi , in ta tuno, takejin wani irin bakin ciki ya tunkareta , wani Abu ya tokare mata kirji , Sai kuka ya kubce mata .

Sanin dalilin kukan da Rukaiyya take Shiyasa ma ba bu Wanda ya tambayeta balle subata hakuri , suka zuba mata ido.


Duk Wanda ya kalli Sadik tabbas yasan cewa yana cikin farin ciki , sabanin shekarun baya , kulawa sossai Aisha take bashi tamkar Yaro karami .

Kullum san Aisha kara karuwa yake a zuciyar Sadik , dan kuwa Aisha bata taba daga ma Sadik murya balle yana fada tana fada, indai yace Abu hakane toh hakane bata taba musu ko jayaiyya da shi .

Shikanshi yasan yanzu Allah ya dubeshi ya mallaka mishi matar Albarka ,Shiyasa kullum cikin godema Allah yake.

Kullum Aisha cikin Nacin cewa a dawo mata da su khairat take amma fur Sadik yaki amincewa , haka hartayi nacin tagaji .

A bangaren KHAIRAT da Hashim kuwa , Hashim na kokarin turo magabatanshi dan asamu ayi maganar Aure, kuma Sadik yayi na,am da hakan , Shiyasa khairat take cikin farin ciki .


A gidan Anti Sadiya Kullum cikin fada suke dan Abu kadan su Hafsa sukayi Sai tafara musu masifa tanafadin su sun dameta Gaskiya tafara gajiya dasu taita bala,i , haka watarana zasu ta kuka Hafasa da Rukaiyya.

Kullum cikin neman gidan bokaye suke, duk kudinsu na gado sun karar da su gun bokaye .

Rukkkaiyya da Anti Hafsa duk sun siyar da kayan dakinsu , duk gurin bokan da suka je Sai dai ya ci kudinsu , amma babu biyan bukata .

Duk wani kadara sun siyar gurin bokaye amma babu biyan bukata , amma Rukaiyya tasha alwashin ko zatayi yawo tsirara Sai ta tabbatar ta koma gidan Sadik , kullum cikin tunanin yanda zata bullowa Al amarin take .

Alhaji madu kuwa akwai shirin dayake na musamman , Sai ya gama ne zai yanke hukuncin da ya dace akan Sadiya , Shiyasa duk abun da Anti Sadiya atake da 'yan wanta zuba musu ido kawai yake.


Watarana Anti Sadiya da Rukaiyya sun tafi neman bokaye , yarage Anti Hafsa ce kawai a gidan .

Kasan cewar weekend ne Alhaji madu na kwance a kan kujera , Anti Hafsa ce tafito sanye da wando da riga sun matseta kwar,kwasa take tayi tana taku , daidai , zama tayi kusa da Alhaji madu tana kashe ido hade da taunar cingum .

Mamaki Alhaji madu keyi yace lafiya ?? miye haka ?.

Cikin kasa da murya hade da kashe muryar , Anti Hafsa ke fadin , nazo tayaka hira ne .

Cikin fushi Alhaji madu yace bana bukata ,dan Allah kitashi ki bani guri.

Kashe murya Anti Hafsa tayi tace," toh dama inaso muyi magana ne , cikin bacin rai Alhaji madu yace" inajinki .

Dan gyara zama Anti Hafsa tayi tace," Kasan nagama idda ta , shine nakeso kamun wani taimako daya .

Cikin mai da hankali ,hade da mamaki Alhaji madu yace," ina jinki , Anti Hafsa tace," yauwa dan Allah so nake ka aureni.

Alhaji madu yace," Aure !!!!??.
Batareda wata fargaba ba Anti Hafsa tace ehh aure.

Cikin mamaki Alhaji madu yace," taya kike tunanin zan aureki Bayan ina auran yayarki ??. Kin taba gani Anyi haka ??, ko bakida hankali ne ??.

Batareda wata fargaba ba Anti Hafsa tace kasaketa dan Allah Sai ka aureni , wallahi ina matukar sanka kuma nayi maka Alkawari zaka sameni me biyaiyya ,kuma za ka samu haihuwa taredani , Kasan Anti Sadiya na da matsala a mahaifa ba zata taba haihuwa ba , nikuma Kasan ina haihuwa kasaketa kawai ka aureni .

A zafafe Alhaji madu ya mike , Wani wawan mari ya saukewa Anti Hafsa a fuskarta yace," ina neman tsari dakara hada zuri,a da irinku , wallahi ko a kafa a ka daura mun aure daga cikin danginku banaso , kuma yanzunma ki tsaya kikaga matakin da zan dauka akan yayarki , tanafadin haka ya ficewarsa .

Cikin takaici da rashin samun nasara Anti Hafsa ta tafi da gudu , amma tunawa da tayi cewa Alhaji madu ya ce zai dauki mataki taji sanyi a ranta , tana Addu,ar Allah yasa yasaketa su zama daya .


Yau takama juma,a Alhaji madu Sai shirye shirye yake.

Dama tun Rukaiyya na Asibiti yasa aka gyara wani part dake Bayan gidanshi batareda sanin Anti Sadiya ba .

Yau sai shirye _shirye yake, karfe goma da Rabi yayi wanka yafita , yasaka rantsatsiyar shaddarshi geznal ,yasha babbar Riga .

Anti Sadiya kam mamaki tadinga yi ganin irin zumudin da Alhaji madu yake, yasa tasa kasa boye maganarta tace," wai yau ina zakaje ne naga sai zumudi kakeyi , kuma naga har saban dinki kasa .??

Batareda da ya kalli in take ba yace," daurin aure zanje , yafada a takice .

Dan murmishi Anti Sadiya tace," daurin auran wa kuma ???.

Cikin tsawa Alhaji madu yace," bansani ba , yazaki dinga mun tambayar titsiye , ni danki ne ??.

Shuru ,Anti Sadiya tayi cikin sanyin murya tace," Allah baka hakuri , tana fadin haka tafita , shima yakarasa shirinshi yafita.

Tunda Alhaji madu yafita bai dawo gidan ba .

Da yamma karfe biyar da rabi, motaci suka faka a kofar gidan Alhaji madu , da guda suka shigo gidan , Amarya ce fuskarta lullube da mayafi , anata rangada gud'a , jin gud'a yasa su Anti Sadiya fita da gudu dan ganin a ina ake gud'a .

Da sauri suka fito , mamaki sossai sukadingayi ganin mutane a cikin gidan .

Da sauri Anti Sadiya takarasa gurinsu tace," bayin Allah lafiya ??, gun wa kukazo ,??.
Nagama kamar Amarya kuka kawo koh ?? ina tunani ba gidanan, bane kunyi batan hanya , banan bane .

Wata 'yar dattijuwa ce tace," yarinya banan ba gidan Alhaji Ahmadu bane ??.

Wani yawu Anti Sadiya ta hadiye tace," eehh ehh nan ne , dattijuwar tace," toh ai Amaryarshi muka kawo mishi .

Batareda taji abun da Anti Sadiya zata ce ba ta wuce suka nufi bangarem Amaryar suka bude suka shiga........✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*_HUMMMM MUJE ZUWA_*

*_TABB KAKAKARA KAKA, ALHAJI MADU YAYI AMARYA , KENAN ????KU DAI KUBIYONI ,DAN JIN YANDA ZATA KAYA , NIDAI COMMENTS NAKE BUKATA, NIKUMA ZANTA SUBURBUDO MUKU RUBUTU ,INSHALLAHU , IDAN NAGA COMMENTS KUJINI ANJIMA_*


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.......*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU"AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 54*

Anti Sadiya kam tsayawa tayi kamar mutun mutumi , tana mamakin Abun da tsohuwar tafada.

Su Anti Hafsa ne suka riketa suka tafi daki .

Ko da suka je dakin Anti Sadiya kasa cewa," komai tayi ta zama kamar mutun mutumi .

Anti Hafsa ce tayi karfin halin cewa," nifa ban yarda ma da abun da wanan tsohuwar ta fada ba , taya za,ayi tace ,Alhaji madu ya yi aure , nifa abun ya dauremun kai .

Anti Sadiya ce tadan numfasa tace," wallahi da gaske ne , dan yau naga sai rawar kai yakeyi , kuma yasa saban dinki , dana tambayeshi yace , daurin aure zaije , dana matsa yafasamun daurin auran was zaije sai yaki Ashe daurin Auranshi za,a..... Kuka ne ya kufce mata sossai ,hakuri 'yan uwan suka shiga bata, amma cikin ransu farin cikine fal cikin ransu .

Kuka Sossai Anti Sadiya takeyi kamar wacce aka aikomawa da mutuwa .

Tana jin yan uwan Amaryar suka tafito suna guda .

Da Sallama'yan uwan Amaryar suka shigo.

Zama sukayi suka ce ," sannuku , toh gadai Amana mun kawo miki dan Allah kirike mana Fareeda Amana dan Allah kinga kece babba.

Kutumar bura,uban babba ce, Anti Sadiya ta fada a zafafe , cikin tsiwa tace," tsabar rashin mutunci Ku sa 'yarku ta aure mun miji kuma bada Sanina ba , har kuzo kuna cewa in riketa Amana , tun wuri kufitarmun a gida kafin ranku yabaci.
Mikewa Anti Hafsa da Rukaiyya sukayi , suka fara masifa , suna kutumtuma ashar kamar jikokin maguzawa .

Cikin isa Anti Sadiya tace," bakuna murna kunkawo 'yarku ba toh bari kuji ", Ku ma tsaya kutafi da ita dan wallahi yau babu makawa sai ' yarku ta bar gidanan sai nasa Madu yasaketa , in kuwa bai saketa ba said ta gwammaci zaman makabarta akan zaman gidana ,ina shawartarku kudauki 'yarku kutafi da ita kafin takardar saki ta biyo baya.

Cikin mamaki sukace," toh anya kinada hankali kuwa ?? ,saki fa mukaji kina kira .

Cikin masifa Anti Sadiya ta tashi tace,"zaku fita ko sai Na Nina muku in din mahaukaciya ce tuburan .

Tashi sukayi suka ce," toh fa !! Mun barki lafiya sai da safe Allah ya hada kanku , suna fadin haka suka fita ,suka tafi.

Ko bayan 'yan uwan Fareeda Amarya sun fita, maganganun Anti Sadiya bai ko damesu ba dan kuwa Alhaji madu yayi musu bayanin komai , kuma yafadamusu matakin da zai dauka Shiyasa ,shirmenta da hararaminta bai daga musu hankali , suka tafi gida abunsu .

Bayan sun fita bakin cikine yakara turniketa .

Kuka take sossai tana sambatu , tana fadin Alhaji madu menayi maka tsinanne , wallahi bari kadawo narantse da Allah sai Kasan kaci Amanata , tsinanne matsiyaci .

Kuka sossai takeyi , kusan karfe tara taji horn dinshi .

Cikin sauri tace ma su Rukkaiya Ku shirya gashinan zuwa , in yashigo kutayani ,mishi masifa da ruwan hauka , yau zan nuna mishi *MAHAUKACIN KISHI* na zai san cewa zuri,ar mu ba,a musu kishiya ,kishiyar ma ta munafurci bada Sanina ba , wallahi sai ya saki matar da ya auro a daren yau , zugata suka dingayi suka ce toh .

Da Sallama ya shiga cikin falan , tashi sukayi a zafafe Anti Sadiya ta nufi gunshi tace, matsiyaci aure kayi Ashe ???.

Batareda da tsoro ko fargaba ba Alhaji madu yace," Eh Aure nayi , menene ??.

Cikin masifa Anti Sadiya tace," Ehh lallai, wato har ka kalli ,ido kace mun kayi aure ko madu?

Yaushe kafara neman Aure bansani ba ??.
Kuma har yaushe akayi gyaran part dincan bansani ba , kuma had akayi jere bansani ba ??.


Wani Shu, umin
murmishi yayi yace," cikin wata daya akayi komai a ka gama .

Dariya yasa yace bari kuma kiji Karin bayani , lokacin da bakyanan kina jelan zuwa Asibitin gun 'yar uwarki , nayi gyara nasa ma Amaryata komai na bukata a daki,na kuma rufe dakin baterada saninki ba .

Kuma cikin kankanin lokaci muka fahimce juna da yarinyar , bayan naje na samu iyayenta nafadamusu damuwata suka tausayamun matukar suka yarda suka amince suka ban 'yarsu cikin gaggawa , dan jin halin da nake ciki , Sadiya bazan boye miki ba nasan duk wani makirci da bin bokayen da kike, bi , bayan nasan cewa bakya haihu 'yar uwarki Hafsa, jin Alhaji madu ya Ambaci Hafsa sai da gabanta Anti Hafsa ya mugun faduwa ,Alhaji madu yace," takara fadamun cewa bazaki haihuba kinsamu matsala a mahaifarki , kuma ta bijiromin da bukatar aure cewa in sakeki in aureta .

Kan uba Abun da Anti Sadiya tafadi kenan , tace," kafin ince komai inaso maza maza kasaki tsinanniyar matar da ka auro , kafin in dawo kan ki Hafsa , ta nuna Anti Hafsa da yatsa , kuma maganar cewa bana haihuwa eh naji bana haihuwa kuma ina bin bokayen saime, tafada hade da cuno baki.
mamaki sossai Alhaji madu yake da jin kalaman Anti Sadiya _humm nikuwa nace Anti Sadiya karfin hali_.

Cikin masifa tace," ko kasaki Amaryarka a cikin darenan ko kaga tashin hankalin dabaka taba tunani ba .

Wani murmishi Alhaji madu yayi yace," toh shikenan yanzu kuwa , cikin samun nasara Anti Sadiya tayi murna cikin ranta .

Alhaji madu ne yace," toh anan zanyi sakin ko a gabanta ??.

Cikin isa da gadara Anti Sadiya tace," muje gabanta taji dakyau cewa kasaketa ,toh yace,.

Ta sa keyarshi Anti Sadiya tayi tace," muje ,nan su Antk Hafsa da Rukaiyya suka bisu .

Suna shiga suka tarar da Amarya da kawayenta suna ta hira,jin shigowarsu yasa da sauri Amaryar ta rufe fuska .

Cikin tsiwa Anti Sadiya tace," dan ubanki bude fuskar yanzu zaki tafi gidan ubanki .

Kallan kawayen tayi tace," bakune 'yan rakiyar Amaryaba kuma yanzu zaku tashi kusan Inda dare ya muku munafukai .

Cikin isa da gadara tace", maza ka aiwatar da umarnina .

Nan Alhaji madu yayi gyaran murya yace," ni Alhaji madu nasaki matata Sadiya saki daya biyu uku , saki na har Abada .

A kidime Anti Sadiya tace," kai Kasan wa kasaka kuwa ??.

Alhaji madu yace," eh matata Sadiya mana Uwar gidana .............✍️✍️✍️


*WALLAHI DARIYA TASA NAKASA CIGABA DA PAGE DINAN , DAN YABAN DARIYA🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣🀣*


*KUYI COMMENTS MUJE ZUWA*🀣🀣


*MORE COMMENTS*😎😎😎

*MORE TYPING........*✍️✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 55*

Wata zufa ce tafara karyoma Anti Sadiya , a rikice tace," lallai Alhaji to ni me na mamaka ko baka cikin haiyyacinka ne?? daga cewa kasaki Amaryarka sai ka sakeni , kuma in ma zaka sakeni ai ba a gaban tsinanniyar nan da kawayenta ba .

Cikin bacin rai Alhaji madu yace" idan kika kara cewa matata tsinanniya narantse da Allah zan miki abun da baki taba tunani ba , kuma sanan da kike cewa bana cikin haiyyacina ai kece bakya cikin haiyyacinki , ke in banda mahaukaciya ce ke baki duba irin rashin mutuncin da kikamun ba, naje na auro 'yar mutunci har kina ikirarin in saketa , tsabar ke bakida hankali , kinyi karatu amma bai tsinana miki komai ba , an ce miki yanzu d'a ne da sihirinki yake yawo a jikina , toh tun wuri ki farga ,kisan Alhaji madu ba na d'a da kika sani bane , sabida haka yanzu yanzu ba sai gobe ba ki tattara ki barmun gidana tunkafin a fita dake a sume, tareda wa inan marasa tarbiyar yan uwanki.

Anti Sadiya tsayawa tayi kamar mutun mutumi , tama rasa abun fada , tsugunnawa tayi a kasa ta kamo babbar rigar Alhaji madu , tayi kasa da murya hawaye ba fita a idanta tace," dan Allah kayi hakuri , munji zamu bar maka gidanka , amma kayi hakuri zuwa gobe .

Cikin zafin rai Alhaji madu yace,' wallahi tallahi ko minti talatin banaso ki karayi a gidana , maza maza Ku fita kafin in muku rashin mutunci , duk kayan da kikasan mallakinki kine ki kwashe su a yau , in ba hakaba zan kona, sanan ko allura ne matukar ni na siyeshi ki barmin kayana

Please Login or Register in order to submit comment