Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta zaba , amma niyyarshi sunan mahaifiyarshi yayai niyan sawa , Amma sabida baya San fitinan Rukkaiyya haka yasa sunan da take so

Babu irin danasani da Sadik baiyyiba na auran Rukkaiyya , yayi danasani matuka , dan kuwa Rukkaiyya bata ganinshi da mutunci kwata kwata , hakuri kawai yake da halinta , baitaba gangancin fadama Hajiya halin dayake ciki ba , dan kuwa yasan zata ce Allah shikara , duk da tsakanin daa' da mahaifi sai Allah .

Wani lokacin Sadik in yaje gidan Hajiya baya kaunar komawa gida, Sai yaci Abincinshi a gidan Hajiya kafin ya koma gida ,

Hajiya ta fuskanci Halin daya ke ciki ,amma ko kadan batai mishi magana ba , dan kuwa tayyi alkawarin Indai bashine ya fadamata ba bazata taba tambayar shi ba .

Kullum in yazo sai dai tace " kuna lafiya Sadik ya amsa da lafiya kalau .

Yau shekarar Rukkaiyya uku da aure amma sau hudu ta taba zuwa gidan Hajiya ,shima sai da kwakwaran dalili , kuma ko taje ma , shafshaf , take Barin gidan kamar Ana koranta , Hajiya kuwa hakan bai taba damun taba , dan tasan wannan ba Wani Abu bane indai akan irin halin su Hajiya Amina ne wannan ba komai bane , a irin halayensu , shiyasa Hajiya koh a jikinta , itadai kullum , Addu arta Allah ya daura dannta Akansu , ya kareshi da duk wani mugun nufinsu akanshi .

A 'yan shekarunan , duk Inda Hajiya Amina taji cewa Akwai shahararren boka toh sai taje dan ganinta samu biyan bukata , amma ko taje duk amsa daya suke bata na cewa baza su iyaba , A haka har tagaji da nema , tacigaba da kitsa ma Rukkaiyya , akan ko ba boka ba mallam , tayi kokarin ganin ta maidashi mijin Hajiya , kar ta taba bari yaji cewa tana tsoronshi , tayi kokari yayi abun da sai dinga shakkarta ,cikeda gamsuwa Rukkaiyya tabi kan turban mahaifiyarta .

Sadik yayi kokarin ganin ya kai zuciyarshi nesa akan abun da Rukkaiyya takemai , har ya kai ya kawo in tana mishi yana mayarwa itama tana mayarwa .

In kuwa suna shiri suna zama dadi soyaiyya suke yi San ransu , su faran tama juna raii , amma in kuwa yan bala ,in suka motsa haka suke kwasan yan kallo , dan kuwa a cikin layin babu Wanda baisan halin da suke cikiba ,

Babban abun da yake damun Sadik bakomai bane illa *MAHAUKACIN KISHIN* da Rukkaiyya take a kanshi , duk wata mace da ta rabeshi sai tayi mata rashin mutunci ,ga bala ,in zargi , ba dama yayi waya tata zarginshi kenan , in sunyi fada tana zage zage tana kiranshi mazinaci , cewa take " in ba zina yakeyi ba tasanshi da tsinanniyar sha,awa kamar me ,in sunyi fada ina yake zuwa , tunda wani lokacin ba ya taba kulata sai ta sakko dan kanta , ko yana jin sha,awa baya taba zuwa ya nemata , haka yake daurewa yasha tea yasa lemun tsami a ciki har sha,awar ta lafa mai .

Dangi kuwa ta daina kula rabi a cikin su , hatta danginta bata kaunar ganin wata ta rabi Sadik ko suna hira , yanzu zata ci mutincin mutum ba Abu ne me wahala a gunta ba , ga tsinannen yawo karya Rukkaiyya ta wuni chur a cikin gidan mijinta ba tareda ta fita ba ,

ko waya Sadik yakeyi sai ta tuhumeshi dawa yake waya,

*A gurguje*

A irin wannan Rayuwar wasa wasa yau har , Sadik da Rukkaiyya sun shekara goma da aure ,
Babu Wanda bai san halin da suke ciki ba , layi da dangi kowa tasan halin da Sadik yake ciki na rashin dacan mata da yayi , ita koRukkaiyya ko a jikinta , duk Wanda ya nunata ,zagewa take taci uban mutum San ranta , har gida take shiga ta ci ma mutum mutunci ba abun da ya dameta .

Kwanaki har yansanda ta debowa makwafciyarta akan wai Sadik ya bats ajiyan wasu files din shi , haka ta dinga zagin ta tana ihu wai kwartuwar Sadik ce ,ta tarama ta jama,a ta haka dakyar aka shawo kan Rukkaiyya ta hakura (settling) abun .

Cikin haka Rukkaiyya ta kara haifan 'ya mace mai suna saudat , inda Sadik yayi ma mahaifiyarshi takwara , ansha fama kafin Rukkaiyya ta yarda Sadik yasa sunan mahaifiyarshi , A cewarta sai dai yasa sunan mahaifiyarta ,

Sadik kuwa murdewa yayi yace bata isaba kuma wannan , haka dai ta dinga zage zage , ba yanda ta iya, kuma tadinga rantsuwa cewa baxata kara haihuwa da Sadik ba , Sadik ko ,ko kulata baiyyiba , sai dai yayi dariya kawai dan ko tun cikin khairat Rukkaiyya take cewa bazata kara haihuwa da sadik ba.
_Niko nace mata da miji sai Allah_

saudat Nada shekara biyu ta kara samun wani cikin duk lokacin dasukayi fada da Sadik sai Rukkaiyya tayita burga tace sai ta zubar da cikin ,bazata kara haihuwa ba da mazinaci,Sadik ko sai yace" tazubar din , haka zataita kunkuni

Rana tsaka Rukkaiyya tagane tana daukeda ciki ,

Bashiri ta tafi Asibit ta zubar , bayan Sadik yadawo gida ne , ya tambayeta ina taje ? Ba boye boye tace" cikin da kamun naje na zubar , ai nace bazan kara haihuwa da mazinaci , mayaudari munafiki ,

Sadik da abun ya daure mai kai yace " Rukkaiyya me nayi kike mun irin wannan zagin cin mutunci, Rukkaiyya har kije ki zubarmun da ciki , Rukkaiyya ko cikin shegene bai kamata ki zubar ba balle cikin sunnah,

Rukkaiyya tayi budi baki tace " toh in ba iskanci kake ba miye hadin ka da zainab da take yawan zuwa gunka ?
Sadik ya girgiza kai yace , Eh lallai sai yanzu na gane Ashe mahaukaciya na auro , Rukkaiyya tace kaje ga mahaukaciya can a gida ehee dan ni ba mahaukaciya bace .

Sadik ya kalleta da rinannun idanshi dasukayi jaa yace" me kike nufi ? Waye mahaukaciyar ? Hajiyata, Rukkaiyya tace " ohh.....bata gama rufe baki ba ya zafga mata wani rikitaccen mari yakara zafga mata wani ,
Rukkaiyya tace " kan ubancan ka mareni ? yace an Mara kuma " kije na sakeki , kuma kar ki yarda in je in dawo in sameki a gida na , wallahi idan nasameki sai na miki dukan mutuwa tunda baki da mutunci .
Bai jira jin me zatace ba ya Debi 'ya'yanshi yasa a mota suka bar gidan yabarta dafe da kuncinta ,
Bayan sun fita Rukkaiyya ta fara hada kayanta ko a jikinta , tama fijin haushin Marin akan sakin dan tasan dole zai nemeta.

Haka ta tattara da tafi gidansu , tana zuwa ta tarar da mahaifiyarta zaune , Hajiya Amina na ganinta hankalinta yatashi tace " ai nasan za a rina , yaji kikayi ko ko sakinki yayi? Rukkaiyya tace sakina yayi ,amma kar ki daga hankalinki nasan dole sai ya nemeni , Hajiya Amina tace Allah sa Rukkaiyya tace " zai ma zo,Hajiya Amina tace humm shikenan .

Sadik ko bayan ya fita bai zarce ko inaba sai gida Hajiya , tace lafiya na ganka da yara ,haka ? danko ba kawo su akeba , sai dai ran wunin sallah Sadik zai dibosu , suzo , A hakanma sai taita nasifa ,tace yaranta bazasuje a koya musu munafurci ba a cewarta haka zaiyyi banza da ita yashirya yaran yakaisu ,suyita murna,dan ko har ba sa San dawowa gidan .


Sadik ne yace " Hajiya nasakii Rukkaiyya, Hajiya nagaji bazan kara iya jure cinmutunci da takemun ,ba Hajiya cin mutuncin yayi yawa nayanke shawara kawai aure zankara ,zan nemi yar mutunci wacce zata dinga ganina da mutunci ba mace irin Rukkaiyya ba , Hajiya tayi shuru ,tace" toh Kai ya zaka Yanke hukunci cikin fushi haka karda saki , bazan hanaka aureba ,danko na Riga na fuskanci duk halin da kake ciki Sadik , Maganabe kawai banma ba amma nasan halin da kakeci dan Nasan mata da miji sai Allah ,Amma dan Allah...Sadik yayi saurin katseta yace " Hajiya dan Allah bana so kice komai, Kozan dawo da ita bayanzu ba sai nayi aure ,


*muje zuwa*๐Ÿ˜Ž

*MORE COMMENTS*๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž
*MORE TYPING*โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*STORY AND WRITTEN BY โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ(MUM FU 'AD*)

*PLS SHARE*๐Ÿ‘๐Ÿ‘


๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

*MALLAKIN* ๐Ÿ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 27*

*Gaskiya ina jin dadi matuka da addu, ar da kukemun nagode Allah saka da alkhairi masu bina ta pc da masuyi ta group nagode Allah barmu tare Allah bar kauna*
*Ina matukar bukatar addu,ar Ku yan uwa kudinga sani a addu a Allah daurani akan makiya na , dan Allah na gode, luv u all my fan*

Hajiya tace" Sadik bazan hanaka aureba , amma inaso kasan cewa" kun haihu tare , in kaga aure yarabu to Sai dole , Dan Allah Sadik kayi hakuri kadawo da matarka ,badan halinta ba Sai dan'ya'yanka ,ba dadi a raba yara da mahaifiyarsu , Sadik yayi shuru yace" Hajiya kinsan me Rukkaiyya tamun kuwa?? Hajiya tayi saurin cewa ni banaso inji kawai nace kayi hakuri ,

Sadik yace" aa Hajiya gara dai in fada miki, Hajiya Rukkaiyya ciki taje ta zubar ,sannan taci mun mutunci , bayan haka tayi kokarin zaginki , yakara dacewa " Hajiya wallahi tunda nayi aure nake fuskantar matsala a gidana Hajiya tun washe garin da aka kai Rukkaiyya gidana a matsayin matata , tun lokacin nafara fuskantara mastsala Hajiya , wallahi tun randa aka kai Rukkaiyya gidana nafara ganin tashin hankali , gashi narasa me yarinyarnan khairat tamata in har mukayi fada to fa akan ta take hucewa , ta tsaneta , kwata kwata shekara yarinyarnan nan fa tara ne , amma duk yarinya kullum cikin damuwa take ,

Jiya ina zaune tazo tanata kuka wai a school ana cemata mamanta na fada da mijinta, haka zataita kuka abin tausayi , Hajiya kawai yaranan su zauna a gurinki yana magana kamar me shirin yin kuka.

Hajiya tayi shuru tace " gaskiya kama Rukkaiyya bata kyauta ba gaskiya amma kayi hakuri zan yi mata magana, sannan inaso kadawo da ita kafin tagama iddah, ni zan zaunar da ita zamuyi magana da ita ta fahimta inshallahu .

Sadik kam humm kawai yace , yace" Hajiya amma kibari Sai nanda sati biyu Sai in dawo da ita , a wannan karan Hajiya bata jaa ba tace " Allah ya kaimu, Sadik ya amsa da Ameen .

Ya tashi ya koma gida Dan debo ma yaranshi kaya, yanashiga yatarar da Karamar takarda a kan dressing mirro din dakin , har yawuce ya dawo dan ganin abun da me ciki , Dan ko yasan Rukkaiyya ce kadai zata iya rubuta sako a takardan ,ko da yaduna yafara karantawa kamar haka ... _*matsiyaci ,mazinaci munafiki wawa jahili Sai me dan kasakeni, kadubeni ina da kudi inada ilimi inada kyau har ka isa ka wulakantani , toh barikaji in ka haifi cikin uwarka da ubanka ka aiko min da takardata ka karasa saki biyu , kaga in ba auro cikin sauri ba , sannan kuma ka kawo mun 'ya'yana ,kar ka yarda ka kaimu yara wannan gidan tsiyar gaiyyar munafukai ,in kaji haushi ka sakeni in ka kai namiji namiji mai zuciya*_ .

Sadik ko ajiye takardar yayi dan kuwa Abun ba karamin mamaki yabashi ba wai kamarshi mace tamishi irin cin mutuncinan,gaskiya dole ya nunamata shi dan halak ne.

Da sauri sauri ya Debi kayan yaran yasa a moto ya ja motar da mugun gudu yabar layin zuciyarshi na mishi wani irin zafi tana tafasa idan yakada yayi jajir kamar wuta _*ran maza yabaci*_ .
Yana Shiga yace Hajiya barinje gidansu Rukkaiyya , ga kayan su yafada yana huci .

Hajiya tace" lafiya naganka haka nadai San ba haka ka fita a gidanan ba kafadamun meke faruwa , Sadik yace " Hajiya kiyi hakuri idan nadawo zan miki bayani .

Hajiya tayi saurin cewa " wallahi tallahi in ka fita kaje gidansu Rukkaiyya batare da kafadamun abun da ke faruwa ba wallahi tallahi kaji na rantse ban yafeba , Sadik da ranshi yagama baci yace " Hajiya kinsan me tamun kuwa Hajiya ni Rukkaiyya zata cima mutunci ,Sadik yakwashe komai yafadama mahaifiyarshi .

Hajiya tayi shuru tace" Sadik abun da nagudamaka tun farko kenan yanzu wa gari ya waya ,Sadik tundakaga nadage akan maganar auranka da yarinyarnan nace baza ayi ba amma kakiyarda yanzu wa gari yawaya , daga karshe har karata kayi agun mahaifinka Akan Sai na bari kayi auran, amma kuma duk sona duk kina tunda Allah ya kaddara ba makawa sai hakan ta faru , tunda gashi harda rabo, rabon ma kuma na ' ya'ya mata toh abun da Allah ya shirya ba makawa Sai hakan tafaru, Sabida haka kayi hakuri kakai zuciyarka nesa kar kabi ta rudin zuciyarka , a bakacin kaje ka kaiwq mataraka takarda kaje da niyyan ka mai da ita .

Sadik ya kallo Hajiya yace" Hajiya kinsan me like fada kuwa ,Hajiya ta kada kai tace kwarai kuwa ,kuma nayi imani da Allah kana dan Rukkaiyya Sabida haka kadawo da ita .

Sadik yace " Hajiya bantaba sabama umarnin ki ba Hajiya amma kiyi hakuri wannan karan bazan iya zuwa in mai da Rukkaiyya ba gaskiya amma nayi miki alkawari idan nayi aure zan je in dawo da ita,
Dan ni a halin yanzuma nasami matar da nakeso in aura , Hajiya tace " toh hakan ma yayi Allah tabbatar da Alkhairi, Sadik ya amsa da Ameen!

Hajiya tace" Amma yar gidan waye ? Sadik yace" Hajiya Nafisa zan komawa kawai nasan zata amince , Hajiya tace " toh shikenan yarinyar ai yar mutunci ce iyayenta ma haka sabida haka nagoyi baya Allah hakan yazama Alkhairi , Sadik yace " Ameen Ameen.

Sadik na fita a gidan Hajiya bai zarce ko inaba Sai gidansu Nafisa , Nafisa tayi mamakin ganin Sadik dan kuwa bata taba tunanin ganishi ba tayi tunanin sun rabu kenan har abada .

Nafisa taohuwar budurwar Sadik ce kafin yasama Rukkaiyya amma ba wata soyaiyya sukayi ba dan ko Nafisa ce takesanshi ba shike Santa ba .
Nafisa yayi saurin cewa" lafiya kuwa ? Sadik yayi murmishi yace lafiya kalau wallahi Sai alkhairi .

Nafisa tace " toh inaji Nan Sadik ya Sanar mata da kudirinshi akan ta,sannan ya shaidamata inta yarda zai turo Nan da sati daya a gama magana , Da farko Nafisa taki amincewa daga bata bayan Sadik yayi katabkalamai maau raysa zuciya taji ta yarda da kudirinshi sannan ta Amince da auran shi.
Sadik yayi Murna ba laifi ,suka dan taba hira daga bisani sukayi sallama .

Kusan yau sati biyu kenan da Rabuwar Sadik da Rukkaiyya , duk a tunanin Rukkaiyya Sadik dole zai zo bikon ta ya maidata dakinta amma da mamaki taji shuru gashi wasa wasa har yau sati biyu kenan da rabuwarsu ga kewar yaranta da ta mijin nata na damunta , dan bata jin dadin zaman gidan kwatakwata kullum Sai sunyi fada da Hajiyanta tadinga mata gori tace " wai tayi sake har tabari miji ya korota , wai taji kunya ga yan uwanta can Sai abun da sukace a gidan mazajansu ,itako Sai aukin haihuwa ba abun arziki , ta ce " Sadik zaizo amma shuru kakeji.

haka Rukkaiyya wataran ta zauna taita kuka taji cewa da ma bata aikata abun da yasa Sadik ya saketa ,ba dan tayi danasani gashi har yau mahaifiyarta nayi mata gori.

Rukkaiyya ce zaune a falon mahaifiyarta abun duniya duk ya isheta tanata tunani iri iri tayi shuru tana tunani yanzu haka Sadik na can yanata kallon yanmata suna wasa suna dariya .
Tamike a zabure tace " kaiii..

*Muje zuwa*

*KUYI MANAGE DA WANNAN WALLAHI HANNUNA NA YANKE SORRY*

*MORE COMMENTS*๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž
*MORE TYPING.....*โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ

*STORY AND WRITTEN BY โœ๏ธโœ๏ธ(MUM FU 'AD*)

*PLS SHARE*๐Ÿ‘๐Ÿ‘


๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

*MALLAKIN* ๐Ÿ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 28*
Rukkaiyya ta mike tace kaiii ,gaskiya dole in koma gidan Sadik , tayi saurin fara kiran layin Sadik amma bai dauka ba , Hanklinta yatashi sossai , dan kanta ta hakura tadaina kiranshi .

Sadik ne ya fito daga wanka, yana fitowa ya duba wayarshi dan yaji ringing tun a yana bayan gida , yana dubawa ya tarar da kiran Rukkaiyya har 15 missed call, dubawa yayi yaja uban tsaki yace ko ubanme zatamun ohoo, inaga dai takira takara mun cinmutuncin da tasaba ne , haka ya ajiye wayar yashirya ya fita yanufi . gidansu Nafisa ,

Wasa wasa yau sati hudu kenan , inda Sadik yana kokarin kai Sadikin Nafisa , dan kuwa yana matukar bukatar kasancewa da mace, amma bayanda zaiyyi , shiyasa ya yanke shawarar kai kudin auren Nafisa ayi auran cikin gaggawa.

Da safe Rukkaiyya ce tafito harabar gidan , tana zaune tanata tunani iri iri.

Sallamar da ta jiyone ya fargar da ita daga dogon tunanin da takeyi .
Kawarta ce Habiba tazo , Rukkaiyya tace "A habiba kece , habiba tayi saurin karasowa tace " hummm nice ,Rukkaiyya tace toh shine da sassafe Allah sa lafiya , Habiba tace " tab wallahi ba lafiya ba tun jiya naso inzo ,amma ban samu dama ba dan kuwa shiyasa nace barin zo da sassafe dan ba, a bori da sanyin jiki.

Rukkaiyya tace " toh mushiga muyi magana ,Habiba tace " dayafi kam .

Suna shiga suka zauna Rukkaiyya tace "_ina jinki Habiba , Habiba da gulma take cinta , cikeda zumudi tace" uhmm Rukkaiyya kunnenki nawa? Rukkaiyya tace " kunnena biyu , Habiba tace " toh maza ki kara biyu kisha labari dan bama daya ba , Rukkaiyya tace " ke na kara ,ni kiyikiyi kiban labarin dan Allah sai wani Jamun rai kike ki fada mana,

Habiba tace hummn Sadik dai aure zaiyyi ,kuma wallahi nanda sati daya zai kai Sadaki , Rukkaiyya data ji maganar kamar a mafarki tace " Habiba banasan wasa kinsa wasa irin wannan zai sa zuciyata ta buga.

Habiba tayi saurin cewa wallahi bawasa nake miki ba kuma ni kinsan bana fadan Abu sai na tabbatar .

Rukkaiyya ta mike tsaye tace " sa ihu tace " kaiiiiii wallahi karyane ni zaima kishiya to wallahi tallahi Sadik nawane ni kadai har Abada,

Habiba tace " toh ke dama in banda abinki yaza ,ayi mutum yasami miji kamar Sadik kuma yayi wasa da damarshi irin haka ai kema da gangan kiki bari kika rasa Sadik yanzu gashi wa gari ya waye ,

Rukkaiyya da zufa tagama rufeta tace " uhmm Habiba bani wayarki , Habiba tace " toh me zakiyi ??
Rukkaiyya tace" kedai bani kawai, Habiba ta miko mata wayan.

Rukkaiyya ta Karba tafara kokarin kiran layin Sadik.

Bugu biyu Sadik yadaga yace "Assalamu Alaikum waye ?yafada da muryarshi me dadin sauraro, Rukkaiyya da magana ma takasayi tace uhmm nice fah !! Sadik yace ke wa? .

Rukkaiyya tace " haba mijina ya kake magana kamar bakasan da wa kake magana ba , nice fa matarka uwar ' ya'yanka , dan Allah kayi hakuri ka mai da ni dakina nayi maka Alkawari wallahi bazan kara bata maka ba , dan Allah .

Sadik yayi shuru yace ina jinki , kiyi ki gama magana ni zanje gun Amaryata tana jirana , Rukkaiyya jin yace Amaryarshi taji wani kololon bakin ciki ya turniketa , dakyar ta iya danne bakin cikin da takeji tace " toh shikenan zankiraka anjima ,Amma dan Allah waye Amaryar taka?sannan aure zakayi ne ?

Sadik yasa dariya yace " sossaima kuwa nanda wata daya inshallahu, zan auro diyar mutunci wacce tasan mutunci ba irinki ba , Rukkaiyya tasa kuka ta kashe murya , sanin cewa in takashe muryanan yana matukar tafiya da tunanin Sadik , yanzu zai fara jin matsanancin sha,awa , Rukkaiyya tafara magana cikin salo da iya kirssa hade makirci ,tace" haba my soul mate dan Allah kayi hakuri kadawo dani dakina wallahi nayi danasani bazan karaba ,kasan ka sabarmin da daddadar soyaiyyarka, kasani inasanka , bazan taba iya rayuwa da wani da na namiji in ba kai ba , sharrin shaiddane dan Allah kayi hakuri kaji mijina, tana magana tadan nishi duk dan ta tayar mishi da hankali .

Sadik yayi saurin cewa "uhmm kinga kikashe zankiraki anjima , Rukkaiyya tace" toh mijina , ina jira ,Sadik yace ok.

Bayan ya kashe wayar ne yaji wani irin sha ,awa na bijiro mishi , haka yayi maza ya tafi gida , yana Shiga yayi saurin hada Lipton da lemon tsami yasha , yanasha yadan kwanta yafara tunani iri iri , yana tunanin tunda Rukkaiyya tacanza mai zai hana ya dawo da ita gidanshi , sai kuma wani sashi na zuciyarshi ta tuno da irin wulakancin da ta mai , kawai sai yaji bazai ma dawo da ita ba ,

Rukkaiyya ko bayan sun gama murna tayi, tace " ma Habiba ke inaga fa zai amince Habiba tace toh Allah yasa dai ya yardan , Rukkaiyya tace" inshallahu ma zai yarda ,

Washe gari Rukkaiyya taji shuru Sadik bai kirata ba

*KUYI MANAGE DA WANNAN DA BABU GARA BADADI*

*STORY AND WRITTEN BY โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ(MUM FU 'AD*)

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

*MALLAKIN* ๐Ÿ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 29*
Taji shuru bai kirata , daukko waya tayi tafara kokarin kiranshi , tayi ringing amma shuru bai dauka ba , a na biyun ne Sadik ya dauka , yana kwance a daki yace " wai ke lafiya kuwa Dan Allah kar kidameni , mu hakura da juna Allah baki wanda ya fini , nima Allah bani wacce ta fiki .

Rukkaiyya tasa kukan kirsa da makirci tace " waiyyo dan Allah mijina kayi hakuri badan ni ba , karka manta ka sabarmin da soyaiyyarka da kulawaarka nasan cewa bankyauta ba amma nayi danasani inshallahu bazan sake ba, da haka Rukkaiyya tadinga tsara Sadik iya tsaruwa , tadinga mishi kalamai masu dadi da kwantar

Please Login or Register in order to submit comment