Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta koma gidan bansani ba ??

Anti Sadiya tace " wallahi Hafsa bansani ba , da alama dai a daren nan taje gidan .

Dan yana kirani naduba dakin ta wallahi banganta ba , hakan ya tabbatar mun cewa ta je gidan kenan , batareda Sanina ba takara da cewa barin yi Sauri , sai inzo mutafi , idan munje maji komai ,

Toh Anti Hafsa ta ce .

Cikin tashin hankali Anty Hafsa ta tashi mijinta tace"Sadik ya kashe Rukaiyya ,Anti sadiya zata zo yanzu mutafi .

Kisa kuma ??? Abun da Alhaji muktar yafada kenan cikin muryar jin barci , eh Anti Hafsa tace " idan nadawo zakaji komai , ni yanzu Anti Sadiya zata zo ta daukeni motafi .

Kiran Anti Sadiya ne yashigo wayarta tace" ki fito gamu a kofar gida .

Da sauri tasa hijab ta Fita.
Tashiga mortar suka nufi gidan Sadik , Dan ganin halin da 'yar uwarsu take ciki .............


*TOFA MASU KARATU KUBIYONI MUJE ZUWA*😎😎😎

*AMMA FA SAI NAGA RUWAN COMMENTS TUKUNNA ZAN CIGABA*

*IN BANGA COMMENTS BA WALLAHI TALLAHI BAZAN CIGABA BA*

*MORE COMMENTS 😎😎😎*
*MORE TYPING.....*✍️✍️✍️

*STORY AN WRITTEN BY✍️✍️✍️ (MUM FU'AD*)

*PLSS SHARE*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 44*

*Kuyi hakuri da rashin update kwana biyu, wallahi na danyi busy ne*

*I NEED YOUR PRAYERS PLSS*

*INA BUKATAR ADDU,ARKU MASOYA*

Bayan ya kira Anti Sadiya a waya ,

Daukan Rukaiyya yayi , da take a sume , ya kaita can part dinta ya direta a dakinta .

Duk yanda Aisha tayi kokari dan ganin ta shawo kanshi dan sukaita asibiti .

Amma fur Sadik yaki yarda, kuka sossai Aisha takeyi tana mishi magiya akan sukaita asibiti , daga, karshema ,rantsewa Sadik yayi yace", bazai je ba , kuma in takara magana ranta zai baci, babu yanda Aisha ta iya haka tayi shuru dan kanta .

Bayan yadawo daga dakin Rukkaiyya, kokarin gyara da dakinsu suka farayi.


A ban bangaren su Anti Sadiya kuwa "

Cikin tsananin hankali Anti Sadiya da Anti Hafsa suka shiga gidan , duba dakunan suka farayi .

Shiga dakinta sukayi suka tarar da ita cikin jini da alama ma bata numfashi

Hankali a tashe suka fara tattabata , ko zata tashi ,amma ina babu alamar numfashi tattare da ita .

Tashi Anti Sadiya tayi a zuciye ,ta nufi bangaren Aisha cikin sauri.

Wani daki tagani , hakan ya tabbatar mata da cewa" toh tabbas shine dakin Amaryar kuma Sadik na ciki .

Bubbuga kofar tafarayi kamar zata ballata , Sadik da Aisha suna ta kokari gyara dakinsu .

Jin irin bugun da akeyi
ne yasa Sadik zuwa bude kofar cikin fada yanafadin," wai waye ne??., yakesan balamun kofar daki .

Cikin tsananin masifa , da daga murya Anti Sadiya take fadin, lallai Sadik , wato , har dadin aure yasa kamanta abun da kayima 'yar uwarmun koh?? , kabude kofarnan.

Bude kofar Sadik yayi yana budewa yaji saukar mari a kuncinshi , a zafafe Anti Sadiya tace," wallahi Sadik kayi karya, munfi karfin a wulakanta zuri,ar mu, me tayi maka kayi mata irin wanan dukan rashin imanin ?, kodan ka na tunanin kayi aure?.

Mamaki sossai Marin da Anti Sadiya tayi mishi yabashi yace," ba laifinki bane , laifi nane , da nahada zuri,a da irinku , kamarni zaki daga hannu ki Mara ,??

A zafafe tace,"eh na mareka , Ai wallahi baka ga komai ba, kuma Kasan Allah duk abun da yasami kanwata wallahi tallahi bazamu yarda ba .

Gurin Aisha Anti Sadiya ta nufo ,ta daga hannu tana kokarin dauketa da mari , caraf Sadik ya rike hannunta , yace", gaskiya duk abun da zamuyi yatsaya a kaina , bazaiyuyu ina ji ina gani a ci mutuncin matar da take farantamun ba , me matata tayi miki ??

Cikin matukar mamaki Anti Sadiya ta girgiza kai , tana fadin eh lallai , Sadik.
Wato har auren wanan 'yar matsiyatar yasa kamanta da cewa ni yar matarkace kake fadamun irin wanan maganar, koh.

Toh bari kaji in ka haifi cikin uwarka ka sakan mun Rukaiyya yanzu yanzunan .

Cikin jin zafin , maganar da Anti Sadiya tafada ,Sadik , yace," Anti Sadiya dan Allah kifita karkisa yanzu rai na yabaci , kar yazamana kina fada ina fada .

Da gudu Anti Hafsa ta shigo dakin tace," Anti kizo fa mu kaita asibiti , kar Rukaiyya ta mutu .

Wani harara Anti Sadiya ta galla musu tace," bari muje mudawo , wallahi tallahi in wani Abu yasami kanwata narantse da Allah kajira sammaci daga kotu , tanafadin hakan ta fita a dakin , rai a bace .

Kuka sossai Aisha takeyi , tanafadin , wannan wani irin bala,i wanan ? An batamun rana mai muhimmaci a rayuwata , amma nasan haka Allah ya kaddara .

Jawota jikinshi Sadik yayi, yana rarrashinta , yana fadin ," kiyi hakuri my love , inshallahu , komai zai tafi daidai kinji , ?? Shuru tayi tana shashekar kuka , tana ajiyar zuciya .

Wani barci me nauyi ne ya dauketa , jikinshi.

Jin kukanta ya tsagaita yasa yadan dagota a hankali , yaga har tayi barci , dan matsar da ita yayi a jikinshi , ya kwantar da ita a kan gado , ya gyramata kwanciya.

Dan mika tayi cikin magagin barci , tadan botsaro boobs dinta , nan lafiyaiyyayun bobs dinta suka baiyyaiyana cikin hadaddiyar rigar barcinta .
Ido Sadik ya zura musu , yana me sha,awar tabasu amma yana tunani gudun kar ya tasheta a barci, take wani irin feeling ya bijiro mishi , ba ya da ya iya haka ya kurama boobs din nata ido , yana hadiyar yawu.

Bayanda ya iya haka ya kwanta dan yin barci , amma tunani halin da matarshi Rukaiyya take ciki da matsananciyar sha,awar da yakeji ya hanashi yin barcin , kurama surar jikinta ido yayi ,yana me kwadayin kasancewa tareda ita , bai ankaraba sai da yaji ana kokarin kiran Assalatu , mamaki sossai abun yabashi , da saurin da lokacin yayi .

Tashi yayi ya shiga toilet ya dauro Alwala ya shinfida darduma ya hau ,yayi sallar raka,a tainun fijir raka,a biyu , bayan ya iddar yafara Addu,o,i.

Sai da yaji an shiga Salla ya tashi Aisha a barci , saida yatabbatar tashiga ta dauro Alwala kafin yafita masallaci dan yin sallah.


A bangaren Rukaiyya kuwa bayan su Anti Sadiya sun kaita asibiti a cikin daren likitoci sukayi caa a kan Rukaiyya , basu karbeta ba sai da Anti Hafsa ta kira wani dan sanda ( police ) yazo yasa hannun kafin su karbi Rukaiyya.

Emergency suka shiga da ita nan suka fara bata taimakon gaggawa , sunkai kusan awa daya akanta , sai da suka tabbatar da numfashinta yafara fita, sanan suka kaita dakin hutu sukasa mata oxygen.

Kiran su Anti Sadiya doctor yayi , yace", su biyoshi office .

Suna shiga doctor yace,," su samu guri su zauna , zama sukayi , akan kujeran .
Cire gilashin fuskarshi doctor yayi yadan numfasa yace," ya kuke a gurin , mara lafiyar ,?? da Sauri suka hada baki sukace yayun tane mu .

Kallo su yayi yace," toh gaskiya i,am very sorry to say , yar uwarku takamu da high blood pressure , kuma takamu da heart attack , har zuciyarta tadan fara kumbura , da alama tanasa danuwa a ranta da tashin hankali da rashin nutsuwa , duk shine ya haifar mata da wanan damuwa

Kara nunfasawa yayi ya kara dacewa ", bayan kuma dukan da tasha , ya haifar mata da matsanancin ciwo a kai , sabida haka zuwa gobe zamu dauki hoton kan mugani ko yasami damuwa ko bai samu ba , yanzu haka mun mata allurar barci sai zuwa gobe zata farka .

Cikin tashin hankali Anti Hafsa tasa kuka tace," Sadik ka cucemu , ma haddasa ma yar uwarmu ciwo zuciya , ka cutar da mu , bazamu taba yafe maka ba , kuma wallahi sai mun dauki fansa .

Kasa magana Anti Sadiya tayi tace," tadan mumfasa tace", hummm doctor for how long Rukaiyya take daukeda ciwon nan ,???.

Mai da hankalin shi doctor yayi akanta yace," eh toh yakai wasu yan shekaru a jikinta yana cinta , amma bai yi yawa ba sai tsakankanin , watanni biyar , shine abun yayi yawa, amma idan muka daurata a kam magunguna, komai zaiyyi daidai inshallahu , sanan akwai allurai da za mu dinga yi mata .

Tashi sukayi suka ma doctorn godiya suka Fita a office din .

*MUJE ZUWA*

*KUYI MANAGE DA WANAN PLSS*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING....*✍️✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY (MUM FU'AD*)✍️✍️✍️✍️


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 45*

Bayan Sadik ya dawo daga Masallaci , samun Aisha yayi har tayi barci , dan yasan dole tarama barcin jiya, ga gajiyar biki gata bala ,in Rukkaiyya.

Shima kwanciya yayi ta gefenta yaja musu bargo sukayi barci,bayan ya kashe wayarshi gudun kar a dameshi , dan yanasan yadan samu barci .


Su Anti Sadiya fitowa sukayi rai a bace , Anti Sadiya ta daukko wayarta tafara kokarin kiran layin Sadik amma wayan a kashe , kwafa Anti Sadiya tayi rai a matukar bace tace," hummmm lallai ma kingani kashe wayar shima yayi .

Anti Hafsa tace," toh Ai shikenan , bari Rukkaiyya ta farfado sai muji abun da zatace , sai mu dauki duk matakin da zamu dauka koh,?.

Anti Sadiya tayi murmishi tace," har sai munjira Rukkaiyya ta tashi mu bazamu iya daukan matakin da yadace ba,"?.

Hummm Anti hafsa tace" ta kalli Anti Sadiya tace," karmiyi saurin zartar da hukunci , kinsan fa mata da miji sai Allah , sabida haka mujira farfadowarta tukunna .

Toh shikenan , Allah tashi kafa dunta , Anti Sadiya takara dacewa," ni wallahi Hafsa Rukkaiyya bataji ne , ance tayi hakuri , bokanan yace ," komai zai tafi daidai , amma taki yarda, kuma kinsan Allah yau dinan dama nake cewa ,zan biya gidanki , muje gun bokanan .

Da Sauri Anti Hafsa tace," wallahi Anti Sadiya ni kaina ina san inje yakaramun aiki , dan nadan fara ganin canji agun Alhaji mukumma tunda yanzu har abinci yake ba su maimuna , idan namishi magana nace karya yarda yabasu , sai yace," wai Ai ba kyau barin mutum da yunwa, indan kuma na matsa sai yaki basu a gabana , sai yabasu a bayan ido na , kijifa , sabanin da,a da ko kallansu ma bayayi .

Numfashi Anti Sadiya taja tace," nikaina nadan fara ganin wasu' yan canji tattare da Alhaji madu, amma kinsa miye anjima mutafi gun bokanan mu mishi bayani kawai , inyaso sai mukira umma (cousin dinsu )tazauna da Rukkaiyyan , eh hakan yayi ,Anti Sadiya tace, " yanzu ni barinje in yi wanka , idan nadawo sai kema kije kiyi wankan , toh Anti Hafsa tace," ta ciro wayarta tace," barin kira su Maimuna su dafa abincin sukawo asibitin koh , Anti Sadiya tace," eh toh shikenan , ni barinje sai na dawo .


Bayan Anti Sadiya ta dawo ,kara gwada numbern Sadik sukayi , wanan karan wayar shi a kunne take sai dai baya daukan wayar , mamaki sossai Anti Sadiya tayi , kallo Anti Hafsa tayi tace," kinga tsinanne yaki ya daga mun waya koh ,Anti Hafsa tace," kinsan me ?? Mu kira uwarshi , mu fada mata karya da Gaskiya , aikuwa hakan zamuyi Anti Sadiya tafada .

A bangaren Sadik kuwa sun tashi a barci kenan , bayan Hajiya ta aiko Salma break fast , ta kaimusu ta tafi , yanayin da salma ta samesu bata ji dadi ba, dan dukkaninsu babu walwala tartare dasu.

Da haka taimusu sallama ta koma gida ranta ba dadi, tana tunani Abun da ya hanasu walwala , a Daren su na farko .


ko bayan ta koma bata fada ma hajiyansu komai ba tadai ce suna lafiya .


Sadik Na kallan wayanshi , lokacin da Anti Sadiya take kiranshi a waya, amma yaki dagawa , Aisha tayi tayi yadauka , amma fur yaki yadaga wayar .

kokarin daukan wayar Aisha tayi , amma ya hanata, haka wayar tagama ringing amma bai dauka ba .

Shiryawa yayi yafita yanufi gidan Hajiya .

Bayan su Anti Sadiya sunkira Hajiya a waya ," daukan wayar Hajiya tayi tace," Rukkaiyya kina lafiya,? , dan da wayar Rukkaiyya Anti Sadiya takirata ,

Cikeda rashin mutinci tace," ba lafiya ba , sanan ba Rukaiyya ba ce , Sadiya ce ," Hajiya tace," toh Sadiya lafiya ,?? .

Anti Sadiya tace," Kinsan da cewa," danki yayi ma Rukaiyya daukan mutuwa ,? Yanzu haka tana kwance a gadon asibiti , rai a hannun Allah , kuma mum kira Sadik yace" wai ai ba zaizo ba , wai yama fii San ta mutu ya huta .

cikina tsananin tashin hankali , Hajiya tace," innalillahi wa inna illaihir raju,un duka!!! kuma Sadiya,??.

Anti Sadiya tace," kwarai kuwa , Hajiya tadan numfasa tace," me taimishi yamata haka,?

Anti Sadiya ta banka harara tamkar Hajiya na ganinta tace," banda lokacin miki bayani , idan danki yazo ki tambayeshi, Hajiya tace," toh yanzu a wane asibiti kuke ," fadamata sunan asibitin tayi , tana fada ta kashe wayarta .

Cikin tsananin jimami , Hajiya take fadama salma , duk sun matukar jimanta .

Salma tace," wallahi Hajiya Shiyasa danaje kai musu abinci naga dukkansu basa walwala , Ashe ga dalili nan .

Su Khairat da suke zaune sunajin Abun da su Hajiya suke fadi , basuce komai ba sai ta gumi da sukayi .

Suna tsaka da tattauna wa Sadik ya shigo dakin, kallon mamaki Hajiya tabishi dashi , bata ce mai komai ba .

Neman gurin zama yayi , Hajiya tayi saurin cewa," karka yarda ka zauna , kawuce yanzu yanzu ka kaini a asibiti gun Rukaiyya , kuma banaso inji kace komai .

Dan dole babu yanda ,Sadik ya iya haka ya tashi ya fita, Hajiya ta daukko lullubinta tasaka suka tafi.......

*muje zuwa*

*kuyi manage da wanan sai gobe ko anjima , inshallahu , yanayin comments dinku dai*


*MORE COMMENTS😎😎😎*
*MORE TYPING....*✍️✍✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU"AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 46*

Bayan Sadik da Hajiya sunfita , mota suka Shiga , Sadik ya jasu suka tafi .

Tambayar Hajiya Asibitin Sadik yayi yace," Uhmm Hajiya wani asibiti ne,??

Hajiya takalleshi tace," eh lallai ya tabbata , bakaje dinba ba .

Sadik baka da hankali ne me ke damunka da zakayi ma matarka kuma uwar'yan'yanka irin wanan duka,?? ko me taiyi maka ai bata cancanci duka ba .

Jiki a sanyaye Sadik yace," Hajiya wallahi Rukaiyya ta kureni ne , Hajiya karfe shadaya fa tazo gidan fa ta tayar mana da hankali .

Nan Sadik ya kwashe komai yafadawa Hajiya , yakara da cewa,"ni bansan abun zai yi haka na kasa danne zuciya na a lokacin .

Shuru Hajiya tayi tadan numfasa tace," toh meyasa da suka kira ka bakaje ba , kuma har kana ikirarin wai gara ta mutu kahuta , hakan dakayi ka kyauta kenan ,??.

Kallon mamaki Sadik yabi Hajiya dashi yace," Hajiya wayace miki nafadi hakan,? .

Hajiya tace," Sadiya mana ba ta kirani ba , a waya , ai ita take shaidamun cewa , kadeki Rukaiyya.

Mamaki sossai Sadik yayi yace," Hajiya wallahi ban fadi haka ba ,na dai San takirani naki dagawa , amma ni bance haka ba .

Hajiya tace, " Hummm Allah ya kyauta , amma karka kuskura ka karayin irin wanan gangancin , kuma da zaran ta warke , zata koma gidanka kaji na gaya maka .

Bude baki Sadik yayi zaiyyi magana , Hajiya tayi saurin katseshi da cewa ," banasan kace Komai matukar akan maganar dawowar matarka gidankane .

shuru Sadik yayi yacigaba da tuki , zuciyarshi ba dadi , da haka har suka isa asibitin .


A bangaren Hajiya Ramatu kuwa mahaifiyar Alhaji muktar , anata kokarin magani , sossai , inda me maganin ya umarci , Hajiya da ta koma gurin danta , dan ganin yanayin da zai karbeta , ta hakane zasu gane ko aikinsu yana tafiya yadda ake so, ko kuwa .

Hajiya tashirya cewa jibi zata tafi , gun dan nata.


Alhaji Madu ne ke tafiya a Mota hankali kwance , Hango wata 'yar dattijuwa yayi a gefen titi ,zata tsallaka titi akalla zatayi shekara tamanin.

Dan Alamar tsufa ya matukar ya baiyyana sossai tattare da ita .

Dan Parking yayi a gefen titin ya fito dan tsallakar da ita titin .

Cikin girmamawa yace," baba ina wuni , ko in tsallakar dake ne , shuru tayi bata komai ba, sai gyada masa kai da tayi.

kama hannunta yayi ya tsallakar da ita titi, yana kallanta .

Curo kudi yayi dubu Biyar ya mika mata , yace," baba ni zan tafi ga wannan , hannun tasa takarba tace," nagode da muryarta da ba,a gane me take fadi sossai dan numfasawa yayi yace," to sai anjima, ko kina da bukatar wani abu ne , ko kuma kifadamun ina ne gidanki sai in kaiki ??.

Dan murmishi dattijuwar Nan tayi tace," Yaro banda gida , amma karka damu da rashin gidan danace maka bani da shi , nasan kana cikin Matsala , kuma akwai a sihiri a jikinka , sannan matarka tana juya Kane dan tariga ta malleka , sanan tabbas zaka haihu , amma bada matarka ba da wata matar daban zaka haihu, yanda ka taima kamun Nima yanzu zan taimakeka , k'asa ta debo a 'kasa ta damka mishi a hannunshi tace", Kasan me zakyi da wanan ??.

Yace,"A,a amma kuma naga Ai kamar k'asa ne koh ? .

Murmusawa tayi tace," kajikata a babban abu, kadinga diban Kadan kadan kanasha a ruwan shanka, kadinga kuma zubawa kadan a ruwan wankanka , batareda matarka ta sani ba , amma na sati biyu kawai zakayi hakan , idan kayi zaka gane abun da nake nufi , ni zantafi sai anjima .

Mamaki sossai Alhaji madu yakeyi .

Yace," amma dan Allah baba a ina kike ??

Dan murmishi tayi da yabiyyana , wawulan hakwaranta tace," ni ba bila dama bace , ni ba mutum ba ce," ni Aljana ce , nakasance ina fitowa irin haka , toh duk Wanda ya taimakeni , Nima sai in taimakamishi , sabida haka ni natafi , batajira cewarshi ba tabace bat a gun.

Tsoro da firgici sun matukar baiyyana a gun Alhaji madu , jikin na rawa ya Shiga motar ya nufi gidan .

A hanya yana tunanin kamar yazubar da kasan , yana cewa , yanlma za,ayi ace k'asa ce zatayi magani, yana kokarin zubarwa yaji ance , idan ka zubar kama kanka , baisan daga Inda muryar ta fado ba , hakan yasa ,yaji matukar tsoro yakara damke kasar a hannunshi yace," kai ina bazan zubarba .

Gida yashiga yazauna yane me tunanin matar .

Tashi yayi ya daukki abu yazuba kasar a ciki ya sa ruwa , sanan yakai dakinshi ya boye , a karkashin gado , bawan da yaganshi dake shi Kadai ne a gidan , samun kamshi yayi da tunani iri _ iri na maganar da wanan Aljanar tayi mish .


A bangaren Hashim da khairat soyaiyya me karfi ta Shiga tsakaninsu .

Tunda Hashim yaji labarin Khairat ta koma gidan kakarasu yayi murna da hakan.

Haka yasa yake zuwa gidan Hajiya hira , dan su Hajiya ma duk sun sanshi .


Bayan Hajiya sun shiga asibitin basu samu su Anti Sadiya ba sai Anti umma Kawai da suka samu ,.

Ganin jikin Rukaiyya ya matukar tsorata Hajiya , juyawa tayi ta kalli Sadik ta zuba mishi mari a fuska .

Mamaki sossai Sadik yayi yace," Hajiya !!! Me nayi miki haka kika mareni , ko da baki mareni ba sai da na fara manyanta Hajiya kumama marin nasan sai dalilin Rukaiyya !!.

Yimun shuruu Hajiya tafada zafafe ....

*MUJE ZUWA*

*KUYI MANAGE DA WANAN DAN ALLAH DANMA DAI KAR IN BARKU HAKA NE BA UPDATE NAMUKU WANAN*

*MORE COMMENTS 😎😎😎*
*MORE TYPING.....*✍️✍️✍️✍️✍️


*STORY A D WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 47*

Cikin bacin rai Hajiya ke fadin , Sadik irin cin mutuncin dakayi ma matarnan kenan , da girmanka , da tunaninka , karufe ido kiyi ma matarka dukkan fitar haiyyaci , toh wallahi duk abun da yasameta , to kasani tabbas dakai zanyi kuka .

Anti umma dake hakimce tana danne danne waya bata ko kallesu ba balle sa ran zata gaishesu .

Cikin girmamawa Sadik yace," Hajiya kiyi hakuri inshallahu bazan kara ba .

Cikin bacin rai Hajiya ta hararreshi .

Juyawa tayi taga Anti umma na danna waya tana taunar cingum .

Hajiya tace," uhmmm Umma nace su Sadiyan basanan ne ,??.

Batareda umma ta kalleta ba tace," uhmm basanan , tafada ba yabo ba fallasa .

Cikin sanyi muryar Hajiya tace," yaushe zasu dawo ,?? Ko kunyi nisa ne dan Allah .

Cikin muryar tsawa umma tace," kai dan Allah karki dameni nadai ce miki basanan , kinsan da cewa kinaso ki gansu

Please Login or Register in order to submit comment