Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

, yana fadin haka ya fita rai bace .

Amarya fadeela kuwa kalansu kawai takeyi ,da kawayenta.

Jiki a sanyaye Anti Sadiya dasu Anti Hafsa suka fita .

Da gudu Anti Sadiya ta shiga daki tafara hada kayanta , nan ta kalli su Rukaiyya da rinannun idanuwanta da suka ci kuka cikin fada tace," kun wani tsaya toh sai kuje Ku tattara naku kayan musan inda dare yamanata ,kundai ji ya ce, mu barmishi gida .

Wata harara Anti Sadiya ta galla ma Anti Hafsa tace," Hafsa kin dauka mantaa abun da kika mun ne? Toh ban mantaa ba wallahi sai na ci ubanki , ina ni zaki ciwa amana , wallahi sai nayi maganiniki .

Harara Anti Hafsa ta galla tace," ha,a kema ba ke kika cuci Rukaiyya ba kika kashe mata Aure, toh ni kuma miye dan nace mijinki yasakeki ya aureni , caraf Rukaiyya tace", ai wallahi Gaskiya ne , Anti Sadiya ke kika kashemun aure dayanzu inan a Gidan mijina , ni wallahi kin cuceni , wani mari Anti Sadiya ta zabgawa Anti Hafsa da Rukaiyya tana huci tana fadin, " dan ubanku duk gatan da na muku Baku gani ba , da auranku ya mutu ba a gidana kuka sauna ba shine kuke ikirarin na cuceku .

Cikin bacin rai Anti Hafsa ta yunkuro zata rama , ta kifeta Anti Sadiya da mari tace," ance miki zan yarda ki mareni ne in barki , karya nayi baki cuce ta bane , ai nasan da gangan kika ce Sadik ya saki Rukaiyya, kuma ya saketa , kema gashi an sakeki , nan fa fada ya kaure tsakaninsu harda dambe .

Jin hayaniya yasa da sauri Alhaji madu fitowa a daki , ganinsu suna dambe yasashi da sauri ya rabasu

Cikin bacin rai yace," Ku barmin gidana kuje waje kuyi dambe in kunga dama Ku kashe kanku , nabaku minti biyar Ku barmin gidana.

Kasa da murya Anti Sadiya tace," zamu tafi amma kayi hakuri in debi kayana , sauran kayan kayi hakuri gobe zan zo in iba, kasan yanzu dare ne , dan Allah.

Cikin bacin rai Alhaji madu yace," OK naji kutafi amma ki tabbata gobe gobe kizo ki Debi kayanki , toh tace, "


Dukkaninsu suna huci , suka shiga kowa yafara tattara kayanshi , suka fita .

Cikin tsananin tashin hankali Rukaiyya tace," toh wai ma yanzu ina muka nufa ???.

Anti Hafsa ce tace," ai kawai tunda hakane , muje gidanmu da mukasa haya mudaga musu hankali sai sun fita a daren sun bamu Gidan mu.

Cikin gamsuwa da maganar su Anti Sadiya tace," eh hakan yayi mutafi .

Tafiya suka farayi suna ta Neman abun hawa basu samu ba , kasancewar shadaya saura'yan mintuna ne , haka suka dinga tafiya suna fada suna cacar baki , kowa nacewa kowacce ta cucesu , da haka har suka iso wani karamin gida..

Knocking suka farayi kamar zasu balla kofar , wani dan dattijo ne yafito da baigaza shekaru sittin a duniya ba.

Mamaki ne karara ya baiyyana a fuskarshi , tsugunnawa yayi cikin girmamawa yace," su hajjaju kune tafe Allah dai yasa lafiya ,??.

Cikin tsiwa Anti Sadiya tace," lafiya kalau tashi zakuyi Ku bar mana gidanmu zamu dawo ciki da zama ،yau yau kuma yanzu.

Cikin matukar mamaki mutumin yace," toh toh Hajiya ai baku bamu notice ba, kuma in munfita muje ina?? .

Nan Anti Hafsa tace," MU da gidanmu har sai mun baku notice , naga ba hidan ubanka bane , tafada hade da zunguremishi kai, kuma da Kake cewa ina zakuje to mu ina ruwanmu .

Ganin Abun da suka mishi ya matukar bata mishi rai ,yasa yace," to Ku jirani ina zuwa .

Anti Sadiya da Rukaiyya ne suka hada baki sukace," kaje kadawo muna jiranka .

Da Sauri yashiga cikin Gidan .

Jim kadan sai ga mutumin ya fito da wani matashin Yaro , hannunshi daukeda wata katuwar Adda .

Cikin firgici suka kalleshi sukace," kai lafiya miye haka ,??.

Mutumin ne ya kalli matashin saurayin yace," kai mamuda kamun maganin wa Inan marasa tarbiyar .
Aikuwa da Sauri ya nufo Kansu zai kai Sara .
Kwasa sujayi da gudu cikin matukar tashin hankali .

Gudu suka dingayi, ganin dare yayi sossai motoci kalilan ne suke wucewa yasa suka dan tsagita gudun, sun rasa inda zasu nufa , dan kuwa duk 'yanwansu sun musu rashin mutunci a lokacin da suke da kudi suna ji da Kansu , Shiyasa a cikin 'yan uwan babu Wanda suke kulawa In ba halinsu yazo daya ba , yan ubansu ma ba kulasu suke ba .

Zama sukayi gefen wata bishiya , suna hutawa , cikin tsoro da firgici .

Wani irin kuka suka jiyo tagurin da suke , take tsoro ya darsu cikin zuciyoyinsu,

Batareda kowa yacema dan uwanshi komai ba suka kwasa da gudu , ga uban kaya a hannunsu.

Bayan sunyi nesa da gurin , Anti Sadiya tace" muje gidan Anti umma kawai .
Da sauri Anti HAFSA tace," a wanan Daren?? Kinsan fa da sauran tafiya kafin aje , gashi kuma dare yayi .

Cikin masifa Anti Sadiya tace," to in bamuje ba a gidan uban wa zamu kwana , Rukaiyya da duk ta galabaita tace," ni wallahi nima nagoyi bayan muje , in ba muje ba toh ina zamu kwana .

Tafiya suka dingayi suna hakki , ga dare ga uban kaya a hannunsu , ga yunwa ga kishin ruwa.

Tafiya suka dingayi a lokacin har kusan karfe uku , kafin su isa gidan Anti umma.

Bubbuga kofar gidan suka farayi ,amma babu Wanda ya fito .

Ciro waya Anti Sadiya tayi tafara kokarin kiran number, Anti umma , amma sai dai a kashe , bubbugawa suka dingayi kamar zasu balla kofar amma babu Wanda ya fito .

Zuwa lokacin sin matukar galabaita , kuka Rukaiyya tasa tace,," ni wallahi Anti Sadiya kin cuceni , wai ni uban wa ma yasa kice ya sakenine , ai ni yadaka Ina ruwanki da zaki ce yasakeni , wallahi Allah ya isa , ni da yanzu ina gidana cikin kwanciyar hankali , yanzu ga Sadik can shida matarshi, kuka me karfi ne ya kubcemata ...........✍️✍️✍️

*MUJE ZUWA*


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.........✍️✍️✍️*


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️ (MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*👏👏👏

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

💔💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 56*

*_DAN ALLAH 'YAN UWA KUSA MAHAIFIYATA A ADDU,A DA BAKUNAN MASU ALBARKA, ALLAH YA YAYEMATA CIWON DAKE DAMUNTA , AMEEN , NAGODE_*

Nan Anti Sadiya ta kalleta tace , dalla matsamun , ni auran ne dani yanzu , ai in hakane ma mahaifiyarmu zaki zaga ,kima Allah ya isa ,domin kuwa ita ta daura mu a turba irin wannan , kuma tsabar baki da mutunci akan mijinki kike mun Allah ya isa ko Rukkaiyya??.

Cikin rashin kunya Rukaiyya tace," toh ba dole in miki ba , nagadai ga Anti Hafsa cewa kawai tayi zata auri mijinki kika dinga fada kina zaginta , to miye dan na miki Allah ya isa akan mijina , kuma wallahi duk Inda naje ke ko tambayata akayi me ya kashemun aure wallahi ke zance , tunda ke kikasa mijina yasakeni , muguwa .

Cikin mamaki Anti Sadiya tace," Rukkaiyya ni kike fadawa haka ,nice muguwa ??.

murguda baki Rukkaiyya tayi ta juya kai gefe tana kunkuni.

Nan suka dinga musu hade da caccar baki, kafin su ankara sukaji anfara kiran sallar farko.

Mamaki sossai sukayi , zama sukayi a gefe suna me jimantawa ,barci ne yafara debansu.


An Fara kiran sallah , mijin Anti umma yafito , tsoro ne da firgici ya kamashi ganin mutane a kofar gidan , haska fitilan dake hannushi yayi , mamaki sossai yayi ganinsu Rukaiyya a kofar gidan .

Magana yafara , yana fadin Sadiya!! Rukaiyya!! Hafsa, !! A firgice suka tashi , tashi tsaye sukayi sukace ina wuni .

Cikin mamaki ya amsa yace," amma me kukeyi anan.?
Cikin matukar gala baita suka ce," yanzu dai bari mushiga ciki mungaji , ga yunwa , idan kadawo za mu maka bayani , toh yace , ya nufi masallaci .

Shiga gidan sukayi a matukar galabai ce .

Da sallama suka shigo gidan , ganinsu yasa Anti umma tayi matukar tsorata, da mamaki dan tabe baki tayi tace," lafiyanku kuwa ? Naganku kamar 'yan gudun hijira??.

Guri suka samu suka zauna , Anti Sadiya ce tayi karfin halin cewa," Anti umma dan Allah yanzu dai kibamu abinci muci sai mu miki Karin bayani , dan wallahi yau a titi muka kwana, ga gajiya ga yunwa ga kishiruwa .

Cikin matukar mamaki , Anti umma tace," toh , nan takira yaranta suka hadamusu musu break fast .

Bayan sun gama su Anti Sadiya suka fara cin abinci hannu baka hannu kwarya kamar tsofaffin mayu .

Ganin sun dan fara dowowa haiyyacinsu , Anti umma tace," tunda Allah yasa kun fara dawowa haiyyacinku sai kufadamun Abun dake faruwa , dan ni namatsu in ji abun dake faruwa .

Nan Anti Sadiya tafara bata labarin cin mutuncin da Alhaji madu Yayi mata dakuma sakin dayamata da wahalar da sukasha da kwana a waje ,da kiran da sukayi mata wayanta akashe .

Tausaya musu Anti umma tayi tafara zaga_zage tana masifa ,tanata tsinema mazajan, tanafadin Alhaji madu yaci ma Anti Sadiya mutunci .

Bayan ta tsagaita masifar , Rukkaiyya tadanyi kasa da murya tace," Anti Umma dan Allah ko zaki taimakemu mu dawo nan dazama, kafin muga abun da Allah zaiyyi ??.

Tabbb!!! A ina din ??, Anti umma tafada da Sauri , Anti Hafsa ce tace anan mana Anti , kinsan fa duk mun rabu da 'yan uwanmu , ke kadai ce muke sa ran zaki yarda muzauna a gidanki , kuma munsan zaki amince da hakan .

Juya kai gefe tayi cikin fada tace ni wallahi banmuku alkawrin kuzauna a gidanan ba , nima din ina fama da kaina wallahi bazan iyaba , kuma ma ko tunkarar mijina da maganar nan bazanyi ba dan nasan bazaiyyarda ba , zan dai muku alfarma kuma in Baku shawara .

Jiiki a sanyaye Anti Sadiya tace, eh munaji .

Gyara zama Anti umma tayi tace ," kunsan me zaifaru yau zan dai muku alfarma Ku kwana , amma sai kuje Ku bama 'yan hayan gidanku notice domin kuwa ni bazan iya cigar da kartai ba , ke kuma Sadiya kije ki kwaso kayan dakinki kisiyar , Ku kara bazama gun boka ko Allah sai sa a dace , ko Baku koma gidan mazajenku ba kusamu Wa, inda zasu dinga kashe muku kudi , kuna juyasu
kamar tsoffafin mazanjanku nad'a, in kun dauki shawarata Toh in Baku dauka ba toh , dan kuwa ni kaina kusan ba a zaune nake ba , kulllun yawan Neman bokaye nake , dan kuwa so nake in juyashi nima San raina , dan mazan yanzu sai an asircesu zakaga daidai , gashi naji yana maganar Karin aure, so nake in bi duk yanda zanyi dan ganin anfasa auran , dan nayi alkawarin bai isa ya kara aure ba muddin ina da numfashi .
maganar da Anti umma take tun data fara maganar mijinta na tsaye a bakin kofar yana ji , har ta gama , mamaki sossai ya dingayi, amma tawani fanin baya mamaki dan kuwa yasan zuri,ar su Hajiya Amina .

Shiga yayi rai a bace , da murmishi Anti umma ta tarbeshi, ta rikice tana dan Sosa kai alamar rashin gaskiya , cikin Inda_ Inda tace," sannu da zuwa , wanin kallo yayi mata yace," umma kin ban mamaki da girmanki da shekarunki , tsabar baki da girma har ki iyazuwa guriin bokaye dan a mallekeni , kuma ki sa afasa aurena koh ?.toh duk abun da kika fada ina jinki sarai , tob bari kiji , yanzu ki tattara kayanki na sakeki saki biyu , dama kawai hakuri nake da halinki , in ban mata ba har mari na kin tabayi , nayi hakuri na sauna dake, amma hakan bai miki ba har sai kinje gun boka dan ki mallakeni koh? sabida haka ki tashi ki fitan muna gida , yafada cikin tsawa .

Suman tsaye Anti Umma takusan yi , tashin hankalin da take ciki bazai misultu ba ,dan kuwa bakaramin tsorata da tashin hankali tayi ba , kuka ne ya kubce mata tace," haba baban ramlat me nayi maka haka zaka Yanke mun hukunci cikin Sauri da fushi .

Da Sauri ta kalli gurin da su Rukaiyya suke tace," yan bura uba tsinannu , matsiyata kutashi Ku barmin gidan kun cuceni , bani baku , dama uwarku ce 'yar uwata ni babu abun da muka hada da Ku sabida haka yanzu kutashi kubarmin gida munafukai , kun je kun kashe auranku nima kun kashemun nawa , mugaye kawai azzalumai .

Nan tafara fatattarkarsu , tana koransu , haka suka debo kayansu suka fito a gidan .......✍️

*MUJE ZUWA*


*KUYI MANAGE DA WANAN PLS , ABUBUWA SUNYI YAWA NE WALLAHI , I AM VERY SORRY FOR THE LATE UPDATE*

*AND PLSS KARKU MANTA KUSA MAMANA A ADDU,A DA BAKUNANKU MASU ALBARKA*👏👏


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING....*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*👏👏👏

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

💔💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 57*

*_Ina godiya Sossai da adduo,in Ku ga mahaifiyata, wa inda sukasamu dama dama wa Inda basu samu ba Allah ya saka da Alkhairi , nagode nagode sossai Allah saka da Alkhairi , Amen !!!_*

_*sanan ina mika sakon ta,aziyata ga maman Yusuf me kayan mata , Allah ya jikansu Allah musu rahma Allah sa mutuwa hutuce a garesu da mu baki daya , Allah kuma yabaki hakurin rashinsu ,muma in tamu tazo Allah sa mu cika da kyau da imani Ameen Ameen!!!!*_

Bayan sun fita, Anti Umma ta tsuguna a kasa tana fadin ," wallahi Abban ramlat ni ban taba zuwa gurin boka ba , nidai na fadamusu ne kawai dan su barmun gidana , tsinannu matsiyata , da mamaki Abban ramlat yace," wai ba 'ya'yan yarki bane kike musu irin wanan zagin .?


Da sauri tace," ni ba bu abun da ya hadani da su, uwarsu ce yar uwata , amma ni ba abun da yahadani da matsiyatanan , ni dai dan Allah kayi hakuri kamaidani , sun kashe nasu auran sun zo zun kashemun nawa shekara da shekaru muna tare munfara mun tara yara , sai yanzu lokaci daya kace ka sakeni , dan Allah kayi hakuri.

Wani kallan rainin wayo ya bita dashi yace," wallahi tallahi sai kin barmun gidana , bayan nayi aure in Allah yasa kinada Raban dawowa sai kidawo , gara run wuri kitafi kafin kije ki shiga bokaye kisa auran bai yuyuba , kuma inshallahu aurena babu fashi .
Yana fadin haka ya fita a dakin .

Kuka Anti umma Takara fashewa dashi me tsuma zuciya tana kara jin tsanarsu Anti Sadiya a ranta , Wanda ta kudiri Aniyar sai ta dauki fansa tunda sune silar mutuwar auranta .

Bayan su Anti Sadiya sun fita , dabarar zuwa gidan hayansu ce tafado musu .
Nan suka nufi gidan.

Da sallama suka shiga cikin gidan , samun masu gidan sukayi suna aiki , mutumin da yafito jiya yana zaune akan taburma da matarshi , cikin girmamawa sukace in kwanan ku.

Da mamaki mutumin ya amsa yace ," lafiya yanzuma kunzo Ku ce in fitanmuku a gidane da sassafenan ??.

Jiki a sanyaye Anti Sadiya tayi kasa da murya tace," A,a dama Alfarma mukazo nema a gurinku , wallahi babu inda zamuje ne shine mukeso kudan bamu daki daya muzauna a ciki in yaso sai kudinga biyan kudin hayan sauran dakuna, dan Allah kar ka ce A,a dan Allah.

Cikin ransu sun matukar tausayamusu , cikeda gamsuwa mutumin yace," toh shikenan tunda yanzu kun saduda na amince sai Ku zauna a can dakin yanuna wani dan karamin daki da yatsa, yace," toh dakin yarana samari ne sai Ku zauna anan koh ??.

Amma Ku tafi gidan ubanku mana , waye baisan ubanku attajiri bane , meyasa kuma kuke San zama a nan ??.


Cikin gamsuwa sukace toh mungode, Anti Sadiya tace," ai amma bamu da gado a gidan , tafada a takaice , zamu iya shiga mu ajiye kayan mu ??.

Matar gidan ce tace," eh kafin kushiga sai kun ajiye kayanku kun gyara dakin .

Anti Hafsat ce tace," gyran daki kuma? yanzu dakinma sai mun gyara duk da cewa gidanmu ne ko kunmanta ne ??.

Mutumin ne yace," oh zaku kara nuna mana isa da ikone ? toh wallahi kukasa wasa sai in fasa baku dakin , dan kuwa yanzu ne lokacin da zamu rama cin mutuncin da kukayi mana babu irin torzarci da wulakancin da bakwa mana akan gidanku , sabida haka ku kiyaye in ba hakaba ba kudin hayan ma sai muki biya in kuma sa yara su fatattakeku .

Da Sauri Rukkaiyya tace," A,a baba dan Allah kayi hakuri baza,ayi haka ba zamu gyara bamu tsintsiya sai mu share mugyara .

Nan matar ta nuna musu wata tsintsiya .

Dauka Rukkaiyya tayi tashiga dakin tafara kokarin gyarawa , suma suka bita a baya , sun matukar tsorata ganin dakin

Anti Hafsa ce tace," tab yanzu anan zamu zauna ? ni wallahi bazan iya zama ba .

Durkusawa tayi tace," Anti Sadiya dan Allah dan Annabi kiyi hakuri ki siyar da kayan dakin ki mu samu haya mu tashi ni wallahi bazan iya rayuwa a gidanan ba .

Wata Uwar harara Anti Sadiya ta galla mata cikin bacin rai tace," sabida da kudin ubanki aka siya ai dole Kice haka , wallahi ko na siyar bawata shegiya a cikinku da zan bawa kudina , dan yanzu kowa yayi ta kanshi , nikam duk inda shahararren boka yake sai na neno dan in koma gidan mijina , ko in samu wanda zan aura in dinga juyashi yana kashemun kudi , sabida haka kowa yayi ta kanshi kuma kuje kunemo kudi eheee dan bada kudi na ba .

Cikin matukar mamaki da kalaman da Anti Sadiya tafada Rukaiya tace," humm lallai ma kuwa , shikenan tunda hakane kowa ya iya Allanshi ya wanke , kowa tashi ta fisheshi .

Anti Hafsa ce tace, " toh sai me kar Allah yasa ki taimakemu , amma ai mu da muka siyar da kayan dakin mu dake aka dinga fafutukar zuwa gurin bokaye har kudin yakare , kuma har dake za,ayi ma aikin amma yanzu abun da zaki mana kenan koh??toh shikenan.

Daukan tsintsiya sukayi suka fara kokarin gyran dakin .

Bayan suna gama Anti Sadiya tace," ni zanje in nemi motar fa zata kwashemun kayana , dan ba lallai in zo dassu nan ba ,zan wuce in da za,a siya in siyar , dan ko na kawo nan babu Inda zan ajiye su gara kawai in wuce dasu, daganan kuma zan bazama gurin neman bokaye , ko zakuzo mutafi ?? .

Da sauri suka ce eh hakan ma yayi zamu biki din .

Anti Hafsa ce tace," amma dai bazaki siyar da katifanki ba ??, kinga wanan duk ta mutu , kidan barmana mudinga kwana , dan tabe baki tayi tace," uhmm toh shikenan .

Tashi sukayi suka fita , bayan sun nemo motar kwashe kaya suka nufi gidan.

Knocking din gate din suka farayi , da Sauri me gadin ya bude musu yace lafiya ??.

Harara Anti Sadiya ta gallamishi tace,"ni Kake cema lafiya ??, ko ka manta matsayina a gidanan ne ,??, dallah bani guri mu wuce.

Shiga ciki tayi, ganin motar Alhaji madu a harabar gida ya tabbatar mata cewa yana ciki.

kai tsaye dakinta ta suka nufa , kiran masu kwashe kayan sukayi suka shigo , nan suka kwashe kayan tas.

Anti Sadiya ta jira dan ganin Alhaji madu yafito amma ina bai Masan da zuwanta ba yana can gurin amaryarshi .

Bakin cikin da take ciki bazai misultu ba ji take kamar ta hadiyi zuciya ta mutu , dan kuwa ba mamaki ya ma manta da ita , wata 'yar kwalla ce ta fito a cikin idanta , hannu tasa ta goge , cikin ranta ko ta kudiri aniyar indai akwai bokaye aduniya sai ta tabbatar ta koma gidan mijin ta ko ta halin yaya ko ta hanyar auran kisan wuta ne .


Bayanda ta iya haka tagaji da jira daga bisani suka tafi gurin siyar da kaya .

Nan aka siya aka bata kudin suka bazama Neman bokaye.............✍️

*MUJE ZUWA*😎

*KUYI MANAGE DA WANAN PLSS, KUNSAN IN ASKI YAZO GABAN GOSHI YAFI ZAFI, TYPING DIN WAHALA YAKEMUN YASIN🙄🙄*😅😂😉😉


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING......*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*👏👏👏

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

💔💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 58*

Kai tsaye garin mai duguri suka nufa, gidan kawar mahaifiyarsu Hajiya sailuba .

Da mamaki Hajiya sailuba ta tarbesu , tace, " kwana biyu, ko a waya ba kwa kiran mutane ,tunda mahaifiyarku ta rasu , yanzu ma nasan akwai abun da ke tafe daku Shiyasa kukazo .

Da sauri Anti Sadiya tace," hummm wallahi kuwa , kinganmu mu ukunan wallahi duk auran mu ya mutu , yanzu shine mukazo ki hadamu da wani shahararren bokan da zai mana aiki , me kyau .

Cikin mamaki Hajiya sailuba tace," kuna nufin dukkan baku da aure??

Anti Sadiya tace," eh wallahi , dukkanmu , bamu da aure , duk tsinannun mazan nanan sun sakemu ,shiyasa muka zo gurinki munsan zaki taima kamana .

Sa sauri Hajiya sailuba tace," humm inshallahu, fatan dai akwai kudi tattare daku??.

Cikin dimuwa da sauri Anti Sadiya tace,"

Please Login or Register in order to submit comment