Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

irin harara Rukkaiyya tabi Sadik da shi tace " Bansani ba dalla mallam ka debi tsiyarka kafitamun a daki wallahi tunkafin ranka yabaci , ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya , Sadik yace " toh shikenan yi hakuri , amma zakiyi taro ne ??.

Rukkaiya da tagama kula tace "bur urban taro zanyi , ta kara fashewa da wani matsanancin kuka .

Abun yaso ba Sadik dariya yace" kiyi hakuri uwargida Allah baki hakuri natafi .

Kuka Rukkaiyya takara fashewa dashi me cin rai .


Yau takama Alhamis ,inda ake ta shirye shiryen Kamun bikin auren Sadik da Aisha .

Amarya na hango cikin wani rantstsan , lace dinkin Riga da siket sun matukar ansan jikinta sossai pink colour da blue , jikin lace din duk manya manya stones ne sai kyalli suke , kowa yazo yaga lace din sai ya tambayi Aisha Amarya a ina ta je ta siyo leshi me kyau haka , Aisha tace" wallahi Sadik ne yasiyo min a gurin mum irfaan , kunsan kayanta a kwai kayau .

Nan mutanen sukayita ce ma Aisha tabasu lambar wayar mum irfaan Dan wannan kayan yazama dole suma su mallakeshi , Aisha tace"la bani da number nta amma bari kira Sadik ya turomin sai in Baku koh .

Kiran layin Sadik Aisha tayi , da Sauri tace" ya turo mata numbrn mum irfaan , ba a dau wani lokaci ba Sadik ya turo ma da Aisha Numbern wayan mum irfaan 08130515037.

Bama mutanen gurin Number mum irfaan Aisha tayi , godiya suka dinga mata cikin farinciki .

Shaharariya mai make up dinanan ce wato *muzeee* tazo ta cancada ma Aisha kwalliya , wata powder nagani mai hawa Biyar ,a cikin kayan kwalliyar muzee mamaki abun yabani , nan na dauka na fara bude powder naga kalolin powder sun bambanta , kasa rufe bakina nayi saida na tambayi muzee me kwalliya nace" muzee yanaga powder haka kala daban daban ??

Nan muzee tace " humm toh ai powder ta farere daban ta bakake da sanan ta choclate colour daban , kowa akwai dai dai fuskarshi , mamaki sossai na dingayi , nace " kuma duk a container daya ?? Muzee tace" eh mana kuma wallahi kudi ne kalilan nasiyeta , Dan bana ma fada , duk amaryar da nayima kwallliya , sai aga tayi haske tayi kyau mutane suta mamakin Suna tambayata da wacce powder nake amfani da yakesa mutane suyi kyau basusan sirrin powder ce kawai ,kuma kin san ko kinsa ruwa a fuskarki powder nan ,nanan a fuskarki bata gogewa muzee tace hummm kardai in cika ki da surutu , kidaiyi ma zainab magana ga number zainab din 09066366347 itakuma zataimata magana sai a kawo miki ki gwada , dan har sari tana bayarwa , aiko godiya mum fu'ad, tadinga yi ma muzee sossai .

Duk Wanda ya kyalli Aisha to tabbas sai yaso yakara kalanta tsabar kyan da tayi da kuma haduwa , ga jikinta sai fitar da wani siritacen kamshi yake yi , duk Wanda yazo gun Aisha sai ya tambayeta dawani irin turare tayi amfani .

Dariya Aisha tayi tace" hummm , wallahi turaren da na siyo ne a gurin maman yahaya mai turaruka , ga turarukanta wallahi basu da tsada , ga kama jiki , Aisha Takara dacewa , nifa rum turaren da kukaga inasawa masu kamshi to wallahi a gurinta nake siya , ga tuarukanta masu kama kaya ko kin wanke kaya wallahi kamshin yananan a jikin kayan , akwai su iri iri sai Wanda mutum ya zaba .

Aisha Takara dacewa bari kuji wallahi akwai randa nasa wani turare da nasiya a gun maman yahya , sai da Sadik ya kusa haukacewa tsabar dadin turaren dayaji a jikina wai turaren yayi mishi dadi , kuyi ma maman fu,ad magana idan kunaso za a kawo muku kuma fa bashida wani tsada , nan suka dinga murna , sukace aikuwa zamu kirata wallahi .

Shiryawa sossai Aisha tayi ta daukko wani lafiyayyen takalmi da Sadik ya siyomata a gun mum irfaan blue da yar jaka itama blue , Tasha gwaggwaro , Duk wanda ya kalli Aisha sai ya matukar yabawa da kyan da tayi .

A bangaren Sadik ango kuwa , shima yasha kyau dan in ba kasani ba bazaka taba Kallan Sadik kace ya haifi 'ya budurwa ba kyau iya kyau Sadik yayi, wata rantsatsiyar shadda geznal tasha farin design yasa tanata sheki daukko hularshi fara da dan dugo dugon zanen blue a jiki ya murza ta zauna daram a kanshi , hununshi yasha dankarenren agogo fari da zobuna , takalminshi fari da dan bleu a jiki , sajanan nashi ya kwanta luf a fuskarshi ga hakorin makkan dake bakinshi sai yalli yakeyi , Idan yayi dariya sai kyanshi ya matukar kara baiyyana.

Tabarakallah masha Allah , abun da na iya furtawa kenan gani Sadik.

Fitowa yayi ya tarar da Rukkaiyya a falo tayi uban tagumi, Gyaran murya Sadik yayi yace" uhmmm Rukkaiyya ni zan tafi , nayi kyau kuwa?? .

Kallo ma Sadik bai ishi Rukkaiyya ba tace " bansani ba, tatashuu fuu ta bar falon , tashiga daki tafara kukan da ta saba .
zumudi, sossai ,Sadik yake kiranshi abokananshi suka farayi akan yafito su tafi shi kadai a ke jira to yace " ganinan .

Ganin su khairat yayi yace bazakuje bane??
Khairat tace " munaso muje amma mama bazata barmu ba ,Sadik yace " tashi ki debo kayanku ,muje in kaiku gidan Hajiya kutafi da salma , da Sauri khairat tace toh " amma mama ta yaiyyaga mana kayan sai dai in daukko mana wasu.

Sadik yace " ta yaga kuma , Khairat tace" ehhh Sadik yace shikenan , Ku yi sauri kusameni ina jiranku a mota , toh khairat tace.


Bari muyi Sauri mu tattare mutafi gurin kamun Sadik da Aisha.

*Muje zuwa*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING....* ✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGES 39*

Rantsatsan hall ne mai Kyan gaske , ya kawatu da abunwan ado sai kyalli da haske gun yake.

Shigowan Sadik da Aisha gurin yayi daidai da lokacin da DJ ya sake lafiyayen kida.

Bakin Sadik kasa rufuwa tsabar murna da farin ciki, shigowansu yasa muatanen cikin halla ihu nan ga guri ya gauraye da ihu da tafi.

Can na hango yan group din mahaukacin kishi da mum fu'ad fans group sunata tikar rawa , kamar ba gobe , suna ta murna suna taya Sadik murba bakinsu ya kasa rufuwa .


Rukkaiya nagani dasu Anti Sadiya sun doso hall din tsabar firgici sai da nayi kaman zan fadi , bangaje mutane sukadingayi , suka shiga cikin hall din , kan upstair din Rukkaiyya ta hau ta kwace , abun magana a gurin MC din tace" hummm sannunku tsinannu , duk Wanda ya hallarci wanan biki , inshallahu bazai gama da duniya lafiya ba , nan fa mutane kowa kallo ya koma gun Rukkaiyya .

Sadik na zaune shida amaryarshi, yana kallan Rukaiyya cikeda mamaki .

Rukkaiyya tace" hmmm nasan duk dangin amarya sun halarci gurinan koh , to bari kuji , wallahi tallahi kusani matukar a ka daura auranan , babu yarku babu zaman lafiya a gidanan , bakusan ko ni wacece bane , wallahi tun wuri gara ma kuce kun janye in kuwa ba haka ba , hmm ba yarku ba wallahi har Ku kunshiga uku .

Nan Rukkaiyya ta dinga zaginsu tas , tana ta masifa da tsantsar rashin mutunci .

Babu wanda ya kulata .

Gurin Aisha da Sadik Rukkaiya ta nufa Aisha kanta a sunkuye da alama kuka Aisha takeyi Rukkaiya , tace" hmm la anannu kawai ta dago fuskar Aisha tace" miye abun dadi a auran mjin wata , kuma mazinaci , in bandake sakaryace , dadin me zakiji a nan , ta nuna Sadik da dan yatsa .

Wata kanwar maman Aisha ce me suna Anti , Umaima , ta taso ta doso gun da Rukkaiya take , takifeta da wani gigitaccen mari , tace " eh lallai sai yau na tabbatar da abun da mutane suke fada akanki na cewa ke mahaukaciya ce , toh bari kiji , tun wuri ku wuce kufita da jakanin yan uwanki wa inda basu da hankali suke tayaki barni , inkisaba hauka da dabbanci toh nan , munsan me mukeyi mu ba mahaukat..... bata rufe baki ba Anti Sadiya ta wanka mata wani mari , kan kace me guri fa ya rikice da hayaniya .

Tashi Sadik yayi da sauri ya wanke Rukkaiya da mari , idanshi sun kada sunyi jajir , ran maza yabaci , yafara magana cikin kakkausar murya , yace Rukkaiya ki wuce ki fita kafin ,yanzu a fita dake a kaiki emergency .

kuka Rukkaiya tasa , tace" bazan fitaba din tsinanne kawai , dukkanta Sadik ya farayi ko ta ina.

Bashiri a rikice Rukkaiya tafita a hall din tana kuka , tana fadin , ohooo dai koma miye nadai watsa maka taro ehee , su Anti Hafsa suka biyota a baya bayan zagin da suka dungayi ma Sadik , Suna tsinemai kancewa akan me zai daki kanwarsu.

Mota suka shiga suka tafi , gidan Anti Sadiya suka nufa kai tsaye .

A waje kamu kuwa kowa ya watse sai mutane kadan sai amarya sai ango .

Kamo hanun su khairat salma tayi suka tafi gidan Hajiya , bayan kuka da yaran suka dingayi lokacin da ake fadan.


Kamo hannun Aisha Sadik yayi yace" muje in mai daki gida .

Kasa magana Aisha tayi , sai binshi datayi a baya .

Kafin Aisha ta isa gidan har yan tsaigumi sunkai gulma gidansu Aisha mamaki mahaifiyar Aisha tadinga yi tace" aikuwa wannan karan yazama dole mahaifinta yaji wanan batu .

Amma fa lallai nasan matukar mahaifinta yaji zancenan bafa lallai ne ya yarda da maganar auren , zai iya cewa a hakura dan kunsan ba mutum ne me san tashin hankali ba .

Anty umaimah ce tace" to ke Anti miye shawararki akan wanan batu ??.

Mahaifiyar Aisha tace" hummm ni kam wallahi Allah ya sani auren Aisha da Sadik yafara fitamun akai , dazata hakura da yafi , amma idan taga zata iya shikenan , zan bita da addu,a .

Anty umaima tace" haba Anti munji tsoro kenan , tamasamu galaba akanmu kenan wallahi bazaiyuyuba , ai ba tsoronta akeji ba .

Mahaifiyar Aisha tace " humm umaima nifa kinsan banasan tashin hankali , amma Allah zaba mafi Alkhairi, Anti umaima ta ansa da Ameen , amma shigan Aisha gidan Sadik babu fashi inshallahu.

A bangaren Sadik da Aisha kuwa , babu Wanda ya iya cewa komai , in banda kuka da Aisha takeyi .

Dan farka motar Sadik yayi a gefen titi , yace" haba Aisha dawanne zanji, da tashin hankalin da nake ciki ko akan kukan da kikeyi ?? .

Dan tsagaita kukan Aisha tayi tace" wallahi ba wai kukan abun da yafaru nake ba ina kukan shawara da mahaifina zai yanke ne akan maganar auranmu wallahi ta yuyu yace afasa auran , nikuma bansan halin da zan Shiga ba idan na rasaka wallahi , ta kara fashewa da kuka harda shesheka .

Gyara zama Sadik tayi yace" innalillahi wa inna illahiraju ,un , ni kaina Ina tunanin nan Aisha , bansan halin da zan shigaba idan narasaki ,
wallahi .

Amma ni zanje in ma baban magana ta fahimta har Allah yasa ya fahimceni kinji , sannan akan Rukkaiyya ni nasan matankin da zan dauka .

Aisha ta girgiza kai tace" hummm bakasan baban bane wallahi India akan wanan ne duk yanada zakayi dan ganin ka shawo kanshi ba fa lallai ya yarda ba .

Amma bari dai muje mugani muji abun da ya yanke.

Sadik yace" toh Allah sa muji Alkhairi , yafada murya a sanyaye .
Aisha tace" hummm Ameen.

Daga bisani yaja motarshi suka tafi.

Shigowar Aisha yayi daidai da dawowar mahaifinta , fitowa Sadik yayi a mota yadan duka ya gaishe da mahaifinta, mahaifinta ya ansa cikin sakin fuska ,yashiga gidan .

Cema Aisha Sadik yayi sai sunyi waya, yaja motarshi ,bai zarce ko inaba sai gidan Hajiya.

*To fa kudai biyonin danjin yanda zata kasance shin mahaifinta Aisha zai amince da auren ko yaya kudai biyoni a next page*

*Rashin comments me yawa shiyasa ban muku long page ba*

*MORE COMMENTS 😎😎😎😎*
*MORE TYPING ....*✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️ (MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 40*

A bangaren Rukkaiya kuwa , zama tayi a kujera tace hummm, Anti kiduba abun da Sadik yamun a gaban Jama,a ,tasa kuka.

Anti Hafsa tace hummm nikam ma narasa mezance barin tafi gida nabar yara , duk da wa incan yan iskan sunanan, in kunyi shawarar abun da ya kamata let me know , toh sukace ,Anti Hafsa ta tafi gida .

Anti Sadiya ce tace" toh ke yanzu miye Abun yi ?? Zaki komane ko yaya ???.

Rukkaiya tace" Anti bazan komaba wallahi kinji na rantse , har sai yazo yabani hakuri.

Anti Sadiya tace" toh aishi kenan Allah ya kyauta Allah sa yazo din, zaimazo abun da Rukkaiya ta fada kenan.

Alhaji madu ne ya shigo gidan , Rukkaiya tamishi wani kalllo, yace" Rukkaiya lafiya baki tafi gidan mijinki ba naganki a nan??
Wata harara Anti Sadiya tabanka Mishi tace" banasan munafurci akan ka take ?? Ya girgiza kai kamar wani munafuki yace A,aa ta daka mishi tsawa tace dallah wuce kabani guri .

Jikin Alhaji madu har rawa yake da sauri ya yabar gurin , tace " dawo , bashiri yadawo , tace" kaje ka samamin abun da zanci da sauri yace toh badamuwa , ya tafi jikinshi narawa.

Rukkaiya tace" waiyyo Anti inama ace ni nasamu wanan gatan dan Allah ki gani abun birgewa , amma ni wancan tsinanan Sadik din yaki juyuwa.

Anti Sadiya tace" ai ke kikaso hakan , da kin rabu dashi ki auri Wanda zaki juyashi sai yanda kikace .
Rukkaiya tace " hummm baridai mugani .


Gidan Hajiya kai tsaye Sadik ya wuce , nan ya samu Hajiya yace" Hajiya nifa wallahi nagaji da halin Rukkaiyya gara kawai in hakura da ita.

Hajiya tace" A,a baza ayi haka ba kayi hakuri , kaje ku yi magana ta fahimta , Murmishi Sadik yayi yace" Hajiya wallahi Rukkaiya bazata taba fahimtana ba , sau nawa nake magana kusan Abu baya canzawa, nayi fadan nayi masifar amma duk abanza ,bazafa ta canzu ba kawai nasan abun yi .

Hajiya tace " kaje nayi hakuri kabata dama kaje kuyi magana kaji , dakyar Hajiya ta rarrasheshi yaya yarda , akan zaije ya mata magana .

Yace"barinje ,.Hajiya tace"toh Allah ya maka Albarka Sadik ya amsa da Ameen ya fita


Gida ya shiga yaduba ko ina baiga Alamun kowa ba ,kiran Rukkaiya yafara yaji ba ansa , dudduba ko ina yafarayi bai ganta.

Hakan da yaji ya tabbatar mai da cewa batanan.

mamaki abun ya bashi yace"hummm lallai ma Rukkaiya tamun laifi takuma fita wai da suan yajii, hummm lallai kam ma .

Kiran Hajiya yayi ya shaida mata cewa Rukkaiya batanan , Mamaki sossai abun yaba Hajiya tace " hummm toh Kasan miye kayi hakuri kaje ka dawo da ita nasan yanzu tana gidan yayarta, kaje kazo min da ita yanzu.

Murmushi Sadik yayi yace" Hajiya wallahi tallahi idan naje gidan da Rukkaiya take dasunan tadawo gidana to wallahi naje a ajalina .

Cikin Bacin Rai Hajiya tace " Sadik kana hauka ne zakayi irin wannan furucin , Sadik yace " kiyi hakuri Hajiya, abun Rukkaiya yayi yawa ne , Hajiya tace " toh Allah ya kyauta , nan ta kashe wayar .

*KUYI HAKURI KWANA BIYU INADA MATSALAR CAJI NE WLHY SHIYASA BAKWA JINA , YANZUMA, WLHY NA DAI DANYI A DADDAFENE KAR KUJI SHURU*


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 41*

A bangaren mahaifin Aisha kuwa bayan yashiga ya ci abinci ya zauna .

Nan mahaifiyar Aisha takwashe ta fada mishi duk abun da yafaru mamaki sossai ya dingayi , yace" dama da irin matar nan Sadik yake zaune amma bai fada mun ba , wallahi da tun farko ban amince da auranan ba .

Katseshi mahaifiyar Aisha tayi da cewa " A,a gaskiya yafada Aisha halin matarshi yace mata tanada *MAHAUKACIN KISHI* duk Abun da Sadik yafadamata wallahi tafadamun , mundaiyi shuru ne mukace bari muga abun da Allah zaiyi .

Shuru mahaifin Aisha yayi yace " toh gaskiya amayar musu da duk abun da suka kawo na janye auran dan kinsan ni mutun ne da bayasan tashin hankali ko kadan.

Jeran kayan Aishan ma da ,akayi za,a je a debo , to ma wai ya ma akayi matar ta yarda har akayi jeran tunda kunce ga irin halinta batace komai ba ??

Numfasawa mahafiyar Aisha tayi tace," hummm dakyar ta yarda sai da aka kai ruwa rana dasu umaima kafin tayarda akayi jeran tadinga musu hauka tana bala,I dakyar suka samu akayi jera .

Nan mahaifin Aisha yace" toh kinji fa gaskiya auranan bazai yuyuba .


Aisha da take akwance a daki tana jin me suke fada ta fito da sauri jin mahaifinta ya ce anjanye auren tace" baba dan Allah kar kace haka ,baba kayi hakuri wallahi komai zaizo da sauki kumama Sadik din yace zai dauki mataki akai .

Mahaifin Aisha yace" ke shashace in banda abunki , yama za,ayi kiyi tunanin zan bari kije gidan mutunin da matarshi takeda *MAHAUKACIN KISHI* dalili amincewa ma danayi dan bansan haka abun yakeba , kuma kee" ya nuna mahaifiyar Aisha da yatsa yace " kece duk kika janyo indan da ace tun farko da matar tazo tanuna halinta toh da ba,aja lokaci ba an hakura da yanzu anmanta dakomai, amma kika boyemun abun mai muhinmanci haka .

Shiru mahafiyar Aisha tayi.
bayan yagamaa maganganunshi ta numfasa tace" wai dama hakan muke gudu kar kace afasa .

A hassale mahaifin Aisha yace," aikuwa gashi nace a fasa , auren gobe gobe a tattara komai nasu da suka kawo a mai damusu Allah ya yi ba matarshi ba ce dan dai yanzuma dare yayi ne da an mayar musu , kekuma yanuna Aisha yace" sai ki kirashi ki fada fada mishi hukuncin da na yanke .

Kuka Aisha tasa ta shige daki da gudu .

Tashi mahaifinta yayi ya fita.

Da sauri mahaifiyar Aisha tabi bayan 'yar tata.

Kwance take tayi ruf da ciki tanata faman kuka.

Dagota mahaifiyarta tayi tace" Aisha kiyi hakuri ,haka Allah ya kaddara cewa ke ba matar Sadik bace ki yi hakuri ki daina kuka .

Cikin muryar kuka Aisha tace" mama meyasa kika fada ma baba kinji ga abun da yafada , tamara fashewa dakuka me cin rai

Murmushi mahaifiyar Aisha tayi tace " humm lallai yaro yaro ne , in banda abunki Idan ban fada mai ba wani Abu yazo ya faru da wa zaiyyi kuka ??dani fa zaiyyi kika ,

Kinga dole nayi aikina a matsayina ta uwa inyi Abun da ya dace kiyi hakuri kita fadawa Allah shi zai yayemiki San Sadik tunda shi yasamiki , tana fadin haka ta fita a dakin .

Kuka sossai Aisha Takara fashewa da shi , ta lalubo wayarta tafara kokarin kiran Layin Sadik dan shaidamishi hukuncin mahaifinta .

Kiranshi ta farayi ringing daya yayi .

Saddik ya kashe sai ya kirata .

Da kuka ta fara mishi magana tace"shikenan matarka ta rabamu burinta ya cika , mahaifina yace " ya janye maganar aurena dakai , yace ma wai gobe za,a mayar maka da duk wani abun da ka kawo gidanmu .

Zufa Sadik ya farayi da Sauri yace" barinzo gidan barinzo gidan yafada cikin Sauri da inda_inda, ya kashe wayar .

Keyn motar shi ya dauka da Sauri yafita bayan yashiga mota sai gidansu Aisha .

Ikon Allah ne ma kawai ya kaishi dan cikin tashin hankali yake tukin a matukar dimauce yake .

Minti biyar ya kaishi gidansu Aisha .

Samun mahaifiinta yayi yana kofar gida yace" sannu baba " baba dan Allah karka yanke hukuncin rabani da Aisha wallahi ina matukar Santa , idan ban sameta ba bansan wani irin halin zan Shiga ba .

maganar matata kuma wallahi yanzu haka ma bata gidana .

Baba kadubi girman Allah kar ka rabani da Aisha .

Shikanshi mahaifin Aisha sai da yaji tausayin Sadik dankuwa bakaramin tausayi ya bashi ba ,amma kuma cikin ranshi yana jin cewa lafiyar 'yarshi da kwanciyar hankalinta yafi mishi komai .

Numfasawa yayi yace"Sadik ni bance ka kori matarka ba kawai dai gaskiya bazan iya barin rayuwar yarta tashiga cikin tashin hankali ba da rashin kwanciyar hankali ba

Tunda matarka ta iya aikata abun makamamancin wanan toh fa zata iya aikata komai akankan , sabida haka kayi hakuri dan Allah .

Durkusawa Sadik yayi a gaban mahaifin Aisha yace" baba wallahi tallahi matukar karabani da Aisha wallahi kamar karabani da rainane , zan tafi nagode sai anjima .

Mamaki sossai abun yaba mahaifin Aisha cikin ranshi yana fadin mutun babba kamar Sadik har ya dinga durkusawa akan mace eh lallai ya yarda so bala,i ne .



Please Login or Register in order to submit comment