Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana ihu , sai da yaga ta lillisu ya barta , ya ajiye mata hamsin ya fita .

Yana fita ta kara fashewa da kuka.

Bayan wani lokaci wani ma yafito dan Neman auran Rukaiyya , cikin farin ciki Rukaiyya ta amince .

Dan kuwa ba karamin San mutumin take ba , ita kanta tana mamakin irin San da take mishi , dan kuwa San da take mishi ko Sadik iya kaci kenan , ta mutun mishi a so , shiyasa takeji ko a wani irin hali zata iya auranshi .

Jin Rukaiyya zatayi aure yasa Anti umma nema duk inda mijjn yake dan tafada mishi halin Rukkaiyyan .

Bayan ta sameshi tafadai, take ya gwaleta yace," shi yaji a haka yake Santa .

Cikin rashin samun nasara Anti umma tadawo rai a bace .

Cikin watanni biyu akayi auran yarage sauran Anti HAFSA kawai itama kuma tana addu,ar Allah ya fito mata da ko dan giya ne ta aura .


Bayan bikin Rukaiyya da kwana biyu , mijinta ya shigo rungume da wasu mata a jikinshi sanye suke da matsatsun kaya Riga da wando , sin sha karin gashi da Alama ma karuwai ne .

A firgice Rukaiyya ta tashi tace" lafiya Wa inan fa .??
Kallan yan matan yayi ya manna musu kiss a fuskar yace, " wai kunji tana tambayarku suwaye Ku.

Ganin yayi ma 'yan Mayan kiss yasa Rukaiyya jin wani Abu ya tokare mata kirji .

Cikin takun kasaita dayar ta kalli Rukaiyya ta karemata kallo saf , sama da kasa tace," hummm karuwanshi ne mu.

Baki San mu mukasa ya auroki ba ??, sabida muna bukatar yar aiki .

Cikin matukar mamaki, da daure kai Rukaiyya tace," bangane ba .
muryarta na rawa tace," dama kai menemin mata ne ???, shine ka auro ni , har kasa karuwarka take ikirarin ita tasa ka auro ni ?.

Wata shu,umar dariya yayi yace," eh kwarai kuwa , toh ke dama an Fada miki sanki nake ??.
Dama bebs dina ne sukace yakamata in nemo musu wacce zata dinga musu aiki, da girki , shiyasa kawai danaga kina gararamba a titi nace barin kwasheki kawai .

Wani kuka Rukaiyya tasa me tsuma zuciya , tace," wallahi baka isaba, ni zaka ci amana , tun wuri su fita kafin in musu lahali .

Wani mari ya kifeta dashi yace," wazaki ma lahani , baki da hankali ko ??, to barikiji in kinsaba ma tsohon mijinki ni ba ki isa kimun ba .

Hawaye ne kawai ke fita a fuskar Rukaiyya tama kasayin kukan , sai hawaye dake fita a idanta .

Nan ya kallo 'yan matan yace mushiga koh ??.
Binshi sukayi a baya suna kada mazaunai suna hararar ta .

Har zai shiga daki yace," yauwa kafin mu fito ki tabbata kingama mana abinci ki hada mana Ruwan wanka .

Kasa cewa komai tayi , sai binsu da kallo kawai da takeyi .

Nan suka shiga dakin.

Wani kukan kura Rukaiyya tasa ta dire a gabansu , cikin kuka take fadin,' wallahi Baku isa ba Baku isa kuzo har gidana kuyi iskanci ba , sai dai Ku fita kunemi wani gidan amma ba nan ba .

Da gudu ta karasa ta haye gadan tana huci tace," zanga ta inda zakuyi iskancinku a nan .

Wata shu, umar dariya yasa tace," Au haukan da kika saba yima mijinki shi zaki mun , toh bari kigani .

Wata 'yar dariya yayi yace," ni fa abun kunya fa gaba nabashi ba baya ba , bari kigani .

Kokarin cire kayan jikinshi yafarayi , yayi ma 'yan matan nuni da suma su cire nasu .

Nan suka fara kokarin cirewa .

Mutuwar tsaye Rukaiyya takusanyi, tana San ganin ikon Allah.

Gadan gaba dayansu suka hau , suka fara yin abun sa zasuyi .

Rukaiyya kuwa runtse ido tayi , dan baza ta iya ganin badakalar da suke aikatawa ba .

Ganin halin da suke cike yasa Rukaiyya bazata iya jurar gani ko jin gurnani da nishinsu ba yasa tafita a dakin da gudu tana kuka .


Falo tadawo tadinga kuka , sai da tayi me isarta , ganin kukan da takeyi zaiyi mata lahani yasa ta hakura dan kanta tayi shiru .

Cikin ranta tana tuna Sadik dinta , tana Tina lokacin da take kiranshi da mazinaci , gashi yau an wayi gari mijinta na aikata zinar a gabanta , lallai Allah ba ,azzalumin sarki bane, tunawa da tayi da hakan yasa ta fashe da kuka tace," dole taje tanemi ya yafiyar Sadik .

Da wanan tunanin ta tashi dan ta yi abun da ya umarceta gudun bacin ranshi .

Bayan sun fito bata iya bari sun had a ido ba .

Cikin tsawa yace " kinyi abun da nasaki ,??.
Muryarta na rawa tace," eh eh nayi .

Batareda ya kalleta ba, ya wuce hanyar toilet suma suka bishi a baya .

Muryarta a sanyaye tace,' wankan ma tare zaku shiga ??.

Dawowa yayi ya wanka mata wani wawan mari , cikin zafin rai yace," idan kika kara mun katsalandan a zance wallahi sai na miki dan banzan duka, yana fadin haka ya rike ma 'yanmtanshi kugu suka wuce bayan gida .

Kuka me cin rai tasa , jin zuciyarta nayimata zafi yasata ta dan tsagaita kukan , ta tashi ta je dan gyara dakin.



Bayan wasu 'yan watanni Anti Hafsa ma tasami miji, inda yayi mata karyar kudi har ta amince da aureshi.

Tun randa ta tare a gidan taga yara sama da ishirin da biyar a dakinta ,.

A tunaninta yaran makwafta ne , ganin yanda suke walwala a gidan yasata tunanin ko yayan gidanane , cikin ranta tace," kai babu yanda za ayi hakan ta kasance .

Bayan ango ya shigo nan yake sanar mata cewa yanada yara talatin maza da mata yara da manya ,ya Aurota ne dan ta kula da yaranshi badan komai ba , kuma shi baya San haihuwa , nan yadinga fadamata dokoki da tsare tsaren gidan.

Kasa magana Anti HAFSA tayi tace," wai wai kana nufin ni zan kula da yara talatin ???.

Wallahi bazaiyiyu ba ni nasaka aure aure har ka haifi yara talatin kuma kace ni zan kula maka da su , wallahi bazai yuyu ba, dama badan Allah ka auro ni ba ???.

Wani tsawa yadaka mata yace," wallahi tallahi sai kinyi dolenki , ance miki dan Allah na auroki ,me kulamin dasu Allah yayi mata rasuwa shiyasa na auroki ganin kina gararamba , banasan yawan magana fatan kinji abun da nafadamiki, yana fadin haka ya fita .

Kuka tasa me cin rai tana tunanin yanda zata fara tunkarara kulawa da yara talatin , da tunanin barci me nauyi yayi awun gaba da ita .

Washe gari da Asuba Anti Hafsa taji hayaniyar yara duk ya tasheta , toshe kunne tayi dan kuwa ba karamin damunta hayaniyar yayi ba .

Fitowa tayi taga yara rututu .

Nan duk suka nufo gunta suna fadin, " Anti kingama mana abinci ne kuma baki samana ruwan wanka ba zamu tafi makaranta , baban mu yace," ke zaki dinga mana koh ??.

Kasa magana Anti HAFSA tayi sai hawaye dake fita a idanta , tana tunanin yanda take azabatar dasu maimuna , yau gashi zata dauki ragamar kulawa da yara talatin , lallai dole tanemi yafiyarsu

Da wanan tunanin tafara kokarin yin aiyyukan tanayi yaran suna fadamata yanda abuwan suke da tsarin gidan,.

Tanayi tana kuka dan kuwa ba karamin jinjiki take ba , yara gomasha bakwai tama wanka , sha uku kuma sun iya da Kansu .

Nan ta hadamusu abun karyawa , suka tafi makarnata .

Ta gyara gidan da kunan dakauke kwana .
tun Asuba take aiki bata gama ba har lokacin daura abincin ranansu yayi ga na dare ,kuma .

Haka tadingayi kamar zata karye tsabar wahala .

Da suka dawo haka kowa ya wancakalar da kayanshi , Gidan ya kara baci ya hargitse .

Kuka ta fashe dashi me cin rai cikin fada tace," haba haba ya kukeso inyii in gyara wanna kubata in gyra kubata , wallahi bari ubanku yadawo ni kam sai ya sakeni , ni bada haifanku ba ni da wahala ,bazan iya ba kuka take sossai harda majina .


A gurguje

Haka rayuwa ta kasance ma su Anti Sadiya dukkansu haka suke fama da mazajansu .

Ba karamin wahala suke sha ba , sumyi baki sun lalace, sunyi muni .

Rukaiyya dole ta hakura da *MAHAUKACIN KISHINTA* tazubama sarautar Allah ido , dan a gabanta mijin zai kawo mata suyi abun da suka ga dama.

Anti Sadiya ma kullum cikin wahala , abu Kadan tayi mijin zai mata dukkan tsiya , har sai jikinta ya fashe ga shaye _ shaye da mijinta yakeyi , wataran haka zayi ,amai ta wanke , kuma ya jibgeta .

Anti HAFSA kuwa itama taji jiki , kullum sai tayi kuka , tsabar azaba , tayi wanan tayi wanan, gashi in tayi mistake daya tashiga uku agun mijin .

Haka duk rayuwar ke tafiya musu, dadi ba dadi .

Hakan yasa gaba daya suka yanke shawarar zuwa nema gafara gurin mazajansu , da 'ya'yansu , ko zasu samu sauki .

Bayan sunje , duk sun tarar da tsofaffin mazajan nasu da matansu cikin farin ciki.

Haka suka nemi gafararsu kuma suka yafemusu .

Duk da hakan basu sami wani canji ba kullum cikin nadama da danasani suke , irin mugun halin da suka aikata da rashin bin umarnin mazajansu da sukayi .


Haka rayuwa tayita tafiyar musu , suna masu nadama ........

Khairat da Hashim ma sunyi aure, suna zaune cikin farin ciki, sai da goranta mata akan halin mahaifiyarta da wasu a cikin dangin Hashim din da sukeyi ,,amma bai dameta ba dan tasan mahaifiyarta ta aikata hakan ne dole a fada...

Sadik kuwa kullum cikin jin dadi da farin ciki yake , dan kuwa yanzu yasan yayi aure , dan kulawa sossai Aisha take ba shi da yaranshi ...............

*TAMMAT BI HAMDULLAH*


*_ALHAMDULILLAH_*
*_ALHAMDULILLAH_*
*_ALHAMDULILLAH_*


_*ALLAH NAGODEMAKA DAKA BANI DAMAR KAMMALA LITTAFINA MAI SUNA MAHAUKACIN KISHI, FATAN ABUN DA NA FADA DAI DAI ALLAH YA BAMU LADAN SHI AKASIN HAKA KUMA ALLAH KA YAFE MANA , ALLAH YASA MU AMFANA DA ABUN DAKE CIKI, ALLAH YASA YAZAMA IZINA GA MATA MASU IRIN HALAYEN*_.


_*ALLAH YA JIKANMU YA JIKAN IYAYENMU , YASA MIYI KYAKKYAWAN KARSHE ,AMEEN*_


_*IUNA MIKA GODIYATA GA DUK WANDA YAKARANTA WANAN LITTAFIN NAGODE NAGODE ALLAH SAKA DA ALKHAIRI ALLAH BAR KAUNA*_.

_*SAI KU TARA DANI A WANI SABAN LITTAFINA MAI SUNA HATSABIBIYAR MACE INDA ZAIZO MUKU RANAR 12 MARCH INSHALLAHU , KUMA INASO IN GAMA DA WURI , BANASO YADAUKI LOKACI MAI TSAWO , ZANYI KOKARIN POSTING DA WURI INSHALLAHU , FATAN ZAKU BANI HADIN KAI WAJAN SUBURBUDO COMMENTS DA SHARING , NAGODE*_


*_SANNAN INA KARA SANAR DA KU CEWA ZAKU IYA SAURARAN AUDIO LITTAFIN MAHAUKACIN KISHI AGIDAN RADIO NA NAGARTA_*


*_SUBHANAKALLAHIMA WABI HAMDIK NASHAHADU AN LA,ILA HA ILLA ,ANTA NASTAGFIRUKA WANA TUBI ALAIKI , WA AKIRI DA,AWANA ANAN HAMDULILLSHIRABBIL ALAMIN_*


_*DAGA TAKU HAR KULLUM ZAYNERB MUHAMMAD KABEER MUM FU'AD*_.


_*MA,ASSALAM*_.👋👋👋👋👋👋👋

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment