Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shashanci kirasa Wanda zai kara zuwa gurinki sai me rober rober amma kinyi asara ,ni wlhy sanda nake kamarki saurayi had keyn mota yabani ubanku ma Allah ne yayi zan aureshi dan wlhy nafi karfinshi , amma ke ko kayan kwalliya ba asami me baki ba ,tirr da wannan bakinjini irin naki da kika gada . ,jiki a sanyaye khairat ta tashi ta nufi daki bata ce komai ba rukaiya kuwa bakin cikin ubane yasa ta huce akan 'yartata tanufi daki ta kwanta
Kairat da ta tafi daki cikn xuciyarta ta cewatayi , da Allah saisa dagaske zai aureta da yafi mata , babu ruwanta da kudin shi , mutane uku sunafasawa amma wannan yazo mamanta na kokarin kusheshi , cikin ranta tace, lallai mahaifiyarta na bata mamaki , to so take tayi iskanci Kennan ko me. Tunda tanasa mata kwadayin abin hannun na miji amma Allah ya tsareta. Ta kwanta ranta bai mata dadiba ko kadan
Alhaji madu nagani adurkushe yanata uban bawa anty sadiya hakuri , amma ita tana kwance ko ajikinta tayi saurin cewa kaga mallam dan Allah karka dameni kataffi yawuce kawai , cikin murna alhaji madu yace nagode sossai hajiya allah saka da alkhairi ,
Da safe rukkaiya na tashi ta kira anti hafsa cikin sauri tace anti hafsa na Shiga uku aikina ya karya wlhy na manta boka hantaru yace kar inmish maganar auren amma na mishi , cikin bacin rai anti hafsa race ke wacce iri wawiyace ,anfadamiki karkiyi magana amma kinki ai ga abin da kika ja nan kinga kin hutu, kishirya gobe zamu koma gun shi mumishi bayani, rukaiyya cikin zumudi tace, anti ko dai in zo mutafi yanxu , anti hafsa tace ke wlhy kin fiye zumudi uban waye yasa ki ki bata aikin ai sai kibari goben, dan anty sadiya ma tamun waya tace yakamata a kara wani sabon aiki sabida. Alhaji madu yafara maganar aihuwa , tace toh shikenan Allah ya kaimu goben

*WAIYYOO MY BATTERY IS LOW* *DAN GIRMAN* *ALLAH KUMUN AFWA* *WLHYBANDA* *CHARGE* *KUYI MANAGE DA WANNAN*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️

*STORY*AND*WRITTEN BY*✍️✍️✍️✍️✍️✍️
*(MUM FU, AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE08*

Sadik kuwa bayan ya bar gida yanufi gurin aiki yana tashi a aiki bai zarce ko inaba sai gidan masoyiyarahi Aisha , yana isa gidan yakirata a waya yace gashi ya karaso jikinta ba rawa ta shirya , tadanyi dan light make up tafiti sanye da doguwar riga ta rolling gelen akanta tayi kyau gwanin ban sha awa , tana karasowa ta Shiga mortar kasancewa a moto suke tadi , tanashiga tagaisheshi ya amsa da murmushi dauke a fuskarshi tace wai dan Allah meyasa kace ka janye auren , lokaci daya kuma kace zamuyi auren , cikin Murya kasakasa sadik yace wlhy tallahi Aisha bansani ba maganar gaskiya dai lokaci daya naji bana sanki sannan ajiya da da daddare naji kuma sanki ya karu a zuciyata , cikeda mamaki Aisha tace toh ikon Allah amma gaskiya abun da mamaki , Allah dai ya tabbatar mana abun da yafi zama alkhairi, sadik ya amsa da ameen ,Aisha tajuyo takalleshi tace dan Allah sadik barin tambayeka dan Allah matarka na son aurena dakai kuwa , sannan tataba nunamaka kin amincewa dani a matsayin abokiyar zamanta , Aisha tafada ta kakkafeshi da ido tana jiran amsar da zai bata
Sadik yayi dariyar da yafi kuka ciwo yace hmmm ,Aisha tace na am kalleni , takalleshi , sannan yace , kinsan tsakanina dake babu yaudara babu munafurci babu cin amana ko takalleshi tace eh , yakaracewa bai kamata in boyemiki komai nawaba ko tace eh sannan yace ,sabida munasa ran rayuwa da junanan mu zama na har abada koh ,Aisha tace inshallahu , sannan yace wlhy tallahi Aisha tunda nayi aure tun lokacin danatare amatsayi ango , tun bayan lokacin wlhy Aisha narasa farin ciki har izuwa yanxu danake magana , shekara ta goma sha Tara da aure Aisha amma bansan miye dadin aureba , Aisha narasa farin ciki ,kinsan Allah duk Wanda a rayuwa akace baiyi sa ar mata ba toh wlhy yana cikin wahala , Aisha Allah ya sani ina cikin wani hali , sannan maganar aurena kuma babu zagin da bansha ba , babu irin cin mutuncin da bangani ba sannan bata tsaya aiya kaina ba saida ta karemiki zagi , wlhy Aisha narasa yanda zanyi , duk cikin zuri armu wlhy zan iya cemiki nikadaine banyi sa ar mataba , Aisha dan Allah kimun alkawari indai munyi aure ki tausayamun karkijuyamin baya Aisha , dan Allah wlhy ina ciki. Damuwa yakarasa maganar idonshi yayi ja kamar Wanda ke shirin yin kuka , Aisha kuwa tunda sadik yafara maganar hawaye ne kawai suke fita a idonta ,tace cikin muryar kuka , tace haba wlhy no nasan baka cikin kwanciyar hankali daga ganinka , ni nasan akwai abun dake damunka kaboyemun , amma in Allah ya yarda zan zamemaka farin ciki inshallahu , zan samamaka farin ciki na har abada indai ina raye ka kwantar da hankalinka mijina in Allah yayarda saikayi alfahari dani , karkadamu , cike da farin ciki sadik yace Allah da gaske matata , hawaye nabin fuskarta ,tayi murmushi tace inshallahu , sadik yayi murmushi yace , nagode sossai matata , amma dan Allah ya isa wannan hawayen naki banason gani plss Aisha tayi murmishi tace na daina tasa hanni ta share hawayen fuskarta. Daga bisani sadik yace yakamata ki shiga gida ,dare yayi ki kwanta ki huta , tace toh mijina har ka gaji dani , yace shhiiii game da san yatsanshi akan lebenshi yace shuru ta ina kika taba gani miji ya gaji da matarshi , tace uhmmm toh shikennan barin shiga saida safe my deee,yace OK byee my soulmate cike da farin ciki tasa dariya ta suka a motar ta nufi gida , sadik kuma ya tada motarshi yabar Layin , ,
Aisha kuwa bayan tashiga gidane ta zauna tana tunanin magangannun sadik cikin zuciyarta tace kai anya wannan matar haka tabar bawan Allah nana kuwa gaskiya akwai wani abu, amma ace duk irin cin mutuncin nan da matarnan take mishi ace yakasa sakinta toh gaskiya akwai wani abun in Allah yayarda da safe zanyi ma mama bayani. Asamu alhaji baba afadamai yayi mana istihara ,akai da tunani iri iri aranta ta kwanta barci
Sadik kuwa yana Shiva gida yanufi daki , yatarar duk iyalan nashi suna kallo , suka mai sannu da zuwa ,sannan yashiga daki rukaiyya tabishi a baya tana mai sannu dazuwa , tace ya kadade Baka dawo ba yau , yace eh nabi wani gurina ne, tace ina kaje ,cikin fada sadik yace dan Allah karkidameni , ni yaro karamine da sai kin tambayeni inda naje , sadik yaja tsaki, cikeda haushi rukaiiya tafita , cikin ranta kuwa cewa take gobe zanyi maganinka dani kake zancen ,takwanta cike da zumudin gobe tayi su tafi gurin boka hantaru

A bangaren hashim kuwa yana ta tunani iri iri a ranshi zuciyarshi na rabuwa maiboyi yaje gun kairat ne ko ya rabu da ita , daga bisani zuciyarshi ta raya mai gara kawai yacigaba da zuwa ya kara kula da yanayin iyayen nata dakuma tarbiyarta ,
Anty hafsat ce ta shigo dakin su maimuna ta dakamusu tsawa tace dan ubanku Baku da hankalin da zakutashi kuyi aikin gida cikin tsoro da fargici maimuna da rahama sukatashi cikin tsoro suke maganar da inda inda sukace , anti..dan ..allah kiyi..hakuri ,mungajine wlhy , cikin bala i tace lallaima yaranan wiyanku yayi kwari , dan kunga babarku kuncigaba da zama a gidansn shine harkuke da bakin magana , toh wlhy in kuka sa wasa duk sai kunbar gidanan , kuka suka fashe dashi sukace anti dan girman Allah kiyi hakuri wlhy zamuyi duk abun da kikace kar kikoremu a gidanan dan Allah , anti hafsa race dallah munafukai kutadhi kubani guru
Anti sadiya ce takira anty hafsa ta shaida mata anjima su hadu a gidanta ita da rukaiyya zasuje gun boka hantaru
Rukaiyya kuwa dama Allah Allah take gari ya waye kodan ta tafi gun boka hantaru yayimata aiki , takira anti hafsat tace a ina zasu hadu tace su hadu a gidan anty sadiya ,rukkaiya ko bi takan yaran batayi ba khairat ce ta hadamusu breakfast daga bisani suka taxi school , rukkaiya ko sadik na fita gun aiki ta sa kafa tafita
Aisha ce zaune kusa da mahaifiyarta race mama dams inado muyi wata magana da Kene akan sadik naso jiya da dadare muyi bayan nada wo na samu kinyi barci , Aisha takwashe duk abun da sadik yafadamata Aisha tafadawa mamanta , ta daura da cewa mama shine nakeso muje dan Allah kima alhaji baba magana yayi mana ko istiharane akan maganar aurenmu.
Cikeda jimantawa maman Aisha tace tab Aisha wlhy in har na karaya da maganar auranki duk Nashiga ga rudani , Aisha tace haba mama keda naketunanin zaki karfafamun gwaiwa dan Allah kidaina sa wannan tunanin a ranki babu abun da ta is a tayi inshallahu ai mun Riga munce Allah , kikwantar da hankalinki , mahaifiyar Aisha tace ,toh Allah ya wuce mana gaba ,gobe in Allah yakaimu saimuje mu sami alhaji baban ko,
Cikin Farin ciki Aisha ta amsa toh mama Allah ya kaimu
Rukaiiya da anty sadiya da anty hafsa be suka nufi gidan kasungumin boka hantaru, kamar yanda suka saba suka nufi cikin da jin suka kusa wani karamin kogo sai ga kasugumin bokanan ya baiyyana , cikin muryarshi mara dadin sauraro yake magana bakinshi na fitar da wani irin wari , yace ke , yanuna hafsat da hannu yace dole sai kin kara zage dantse domin mahaifiyar nijinki tasa anata addu ar juyo da hankalin mijinki , cikeda tashi hankali hafsat tace boka nashiga uku yanzu miye abun yi , boka ya ce abunyi kawai anan shine dole sai ankara sabon aiki ,aikin da za ayi kuwa shine ,ko takalmi sai kin bashi izinin sawa kafin yasa cikeda farin ciki hafsat tace ran boka ya dade, ina godiya , boka hantaru yace amma akwai sharadi , cikin sauri hafsat tace totoh menene sharadin boka boka yace , karki yarda ki bari yayi ido biyu da mahaifiyarshi indai suka hadu to karfin aikin Zai ragu ,sannan na biyu kidinga hanashi ibada tanan ne zamu samu aikin yata fi daidai ba tangarda , sai kuma na uku shima karki bari yadinga yawan hada ido da 'ya'yanshi , cikin farin ciki hafsat tace toh angana boka , boka yace yanzu sai kibiya mu ladan aiki ko cikin , jikinta na rawa tace angama , boka yanuna mata wani daki ta shiga shima ya shiga, hafsat ta tube aihuwar uwarta ,bayan boka ya kalleta tsaf yace maida kayanki , hmta mayar ta fito ,

*MUJEZUWA*

*MORE COMMENTS*😎😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY*✍️✍️✍️✍️

*(MUM FU AD*)


*PLSS* *SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*PAGE 9*

Boka hantaru ma yafito , ya kalli rukaiyya yace , kekuma bakyaji aljanu since sukusa sudaina miki aiki surutun ki yana yawa , bakya bin dokoki da ka idojin aikin mu sabida haka wannan shine karo na karshe da zamu miki ai ki karya ,inkika kara toh bazamu karamiki aiki ba , cikin sauri rukaiyya tace ran boka yadade ayi hakuri ammun afwa bazan karaba ,cikin boka yafada cikin muryarshi ma dadin saurara yace, ke aikin ki yafi na kowa wahala ,sabida mijinki mutumne mai yawan addu a da ibada , shiyasa aiki akanshi yakada matukar wuya , amma zamusan abunyi , cikin farin ciki rukkaiyya tace eh eh boka ayi duk abun da ya dace , boka hantaru ya bushe da wata mahaukaciyar dariya , ga bakinshi na fitar da wani irin doyi yace nasha fada miki matukar kinaso aikin ki yayi yanda kikeso sai kin barshi yayi aure wanan *MAHAUKACIN KISHIN* da kike mishi dole ki rage yayi aure in kuma ba haka ba aikinki bazai tafi yanda kikeso ba
Rukkaiyya da duk zufa ce take karyomata , cikin inda inda tace, toh..to.. boka ba..bu wa..ta hanyar, cikin tsawa boka hantaru yace keeee bakiji abun da muka fadamiki bane , kitashi ki bani guri in baki shiryaba , cikin tsoro da figici rukkaiyya tace ran boka shidade ayi hakuri, anti hafsat da anti sadiya suka tayata ba boka hantaru hakuri , yace dole in kinaso dole kibari yayi aure, cikin matsanancin damuwa rukkaiyya tace toh shikennan ranka shi dade
Sannan boka hantaru yace , karki kuskura kikaramishi maganar auren sannan duk abun da zaiyyi karki ce zaki daga muryarki , kibishi a hankali ta haka ne kadai zamu samu biyan bukata , ba shiba ma har matar da zai aura sai yanda kikayi da ita, cikin rukkaiyya tayi farin ciki wani gefe na zuciyarta na bakin ciki ,hakadai tace toh shikenan boka godia nake, haka itama tatashi tamike ta shiga cikin wani daki ta cire kayan jikinta bayan boka hantaru ya gama kalleta yace ta maida kayanta, haka tamayar tafito a dakin , shima boka hantaru ya biyo bayanta , yace ma anti sadiya saura ke, mijinki na matukar san haihuwa ,amma aikin da mukayi akai shiya sa yake tsoron miki magana , dankuwa a ranshi yana ji aure zaiyyi said dai kuma , bazai taba iya tunkararki da maganar ba sabida haka , me kikeso ayi mishi , da sauri anty sadiya tace boka kawai asa yamanta da maganar haihuwa gaba daya, boka hantaru yace angama , haka ta tashi ta nufi dakin itama tayi kamar yanda sauran sukayi , tafito , suka bashi kudi me yawa sannan sukabar dajin, a hanya ne suke hira rukkaiyya tace kai anti hafsa nifa gaskiya zancanza gurin bokanan nikam bazan iya bari said sadik yayi aureba zansamu in mallakeshi yanda nakeso , kunsan inasan shi wllhy ina tsananin kishin mijina bazan iya bari yakaro aure ba , yakawo wata cikin gidan ama tsayin matarshi har su kusanci junansu wlhy bazan iyaba ,zuciyata bugawa zatayi ,, cikin bacin rai anti hafsa tace ke kikasani ,inkiyarda ruwanki in baki yarda ba sai ki je can kinemo Wanda zai miki aikin ke kikasani , anty sadiya kuwa dan haushi ma ko magana bata mata ba , tayi kwafa tace ,uhmm hafsa kinsan ni nakusa sauka , in kungama , da wananan shashashar mayi magana , rukkaiyya dai tayi shuru bata ce komai ba , haka suka fito a motar rukkiyya akafara saukewa sai aka sauke anti sadiya sai ita anty hafsan ta wuce gida ,
Hashim ne tsaye a cikin machine dinshi yazo gun khairat, khairat tafito fuskarta dauke da murmushi tace ina wuni cikin sakin fuska Hashim ya amsa da lafiya kalau gimbiyata , khairat ta sa dariya tace uhmm , sai ga rukkaiyya ta nufo gida rai abace , tsabar bacin ran da take ciki ma ko kallon Inda suke batayi ba ,hashim ya kalli khairat yace , ina mamace , khairat cikin jin kunya da takaici ,tace eh itace ,cikin sauri hashim ya je gabanta ya durkusa yace ina wuni mama , rukkaiyya ta tabe baki tace lfy, bata ko kara kallanshi ba ta wuce gida cikin gida , jiki a sanyaye hashim ya nufo gun khairat ,yace da alama dai ambata mata rai a daga inda take ne , cikin murya me sanyi khairat tace eh ba bamamaki, barin shiga gidan , hashim ya ce toh gashi , ya miko mata sabuwar waya a leda , tace me wannan hashim yace wayace , akwai sim card da memory card a ciki tace toh nagode Allah yasaka da alkhairi , yace haba miye na godiya kin karfin haka a gurina , khairat tace nagode barin shiga gida , yace toh a gaida maman tace toh.
Ta shiga gida , hashim kuma yaja machine dinshi ya tafi, cikin ranshi yana ta sakesake anya wannan matar Nada mutunci kuwa , gaskiya wanna bata dace , ace itace mahaifiyar khairat ba , amma dama haka allah yake ikonshi yakan fidda macace cikin rayaiyye , yakan fidda rayaiyye cikin matacce , amma gaskiya khairat batayi sa ar uwa ba , cikeda da tausayin khairat din ya nufi gida .
Itako khairat bayan tashiga gida ,ta tarar da mamantata tana ta kuka, kannanta duk sun sa uwar a gaba sunyi jugumjugum sunyi shuru sunyi tagumi , gaban khairat ne yayi mugun faduwa tace mama lafiya
Rukkaiyya tace munafuka ko na fada miki kinda a sara ne , kinje kin kwaso ma matun wani dan matsiyata , shegiya me bakin jini wlhy akanki zan huce , haka ta rufe khairat da duka, _ni kuwa nace anya rukakkaya kankidaya kuwa ko duk_ *MAHAUKACIN KISHIN* ne ,bayan tagama dukan kahairat ta kalli sauran yaran tace da ubanku kutashi kubani guri , haka suka tashi jiki a sanyaye suka bar gurin khairat kuwa tana kuka ta tashi ta bar gurin ta nufi dakinsu , haka wayar da hashim yabata tana manta inda ta jefata , cikin sauri ta dauko hijab dinta ta fita ta bar gidan , tana fita ta nufi gidan makwaftansu , ta shiga dakin kawarta , kawartata na kwance tace khairat lafiya badai wani ne yarasu ba , cikin kuja khairat tace gaba jamila nagaji wlhy dan Allah kibani kudin mota , in kinadashi wlhy guduwa zanyi in barmata gidan , in banana ta huta , cikin rashin fahimta jamila tace ke banganeba kimun maganar da zan fahimta bakida hankaline da zakice zakibar gida , jamila tayi sauri ta ta nufi daki mahaifiyarta tace mama ga khairat can taxi tana wasu irin maganaganu marasa kan gado wai gida zata bari in bata kudin moto , da sauri ma mahaifiyar jamila ta zo dakin , tace ke khairat bakida hankaline da zakice zaki bar gida , tukunna ma wai me ya faru , ne cikin kuka da shashekar kuka tace ,wlhy mama nagaji ,kullum cin mutuncin yau da ban na gobe da ban , in dai sukayi fada da babanmu wlhy akaina ta ke huce wa ,khairat ta kwashe komai tafada ma maman jamila , mahaifiyar jamila tace tashi mu je gidan naku , jiki a sanyaye khairat ta tashi ta tabi maihaifiyar jamila a baya , mahaifiyar jamila ce tayi sallama tashiga cikin gidan tace maman khairat kina ina , cikin izza da gadara rukkaiyya tafito a daki ta tabe baki tace ya akayi lafiya , mahaifiyar jamila tace , haba rukkaiyya wai miye damuwarki yakamata kisan me kikeyi ya zaki dinga dukan yarinya budurwa kamar wanan , ki dan kinga ita me bayyaiya ce , wlhy gun wuri kisani Allah zai tambayeka , miye amfanin wannan , kuma yarinyar nana ba wani laifi tayi ba , cikin rashi mutunci rukkaiyya ta budi baki tace , ehh ai ba uban wani ne ya Haifa mun 'yar ba kekuma dan ubanki , har kika iya fita kika bar gidanna. Ko wlhy tallahi yau sai na jimiki ciwo a gidannan ,mahaifiyar jamila kuwa tace lallai rukkaiyya nagode tabbas bada ubana aka haifi 'yarki ba, amma kisani in nakara shiga lamarin gidanki duk abun da kika ga dama kimin , rukkaiyya tace toh dama in banda munafurci ina ruwanki , ranar ma ina kallo kina ma mijina magana toh wlhy kika kara mai magana sai na miki rashin mutunci , aikin banza , mahaifiyar jamila tace nagode rukkaiyya ba laifinki bane , haka tafito jiki a sanyaye ta nufi gida , jamila na ganin mamanta ta shigo ta ce , mama yanaga yanayinki ya canza ko ta miki wani rashin mutuncin ne dannasan zata aikata , mahaifiyar jamila takwashe komai tafadawa 'yartata tace daga yau sai yau na rabaki da khairat bake ba ita , jamila tace mama ai ko baki fadaba mama bazan kara kulata ba tunda har mahaifiyar ta ta ci miki mutunci
Khairat kuwa bayan mahaifiyar jamila ta fita kuka tadingayi , ai kuwa rukkiyya ta kamota tafara duka kamar Allah ya ya aikomata , sai da tama khairat duka sannan ta ce kuma yau wlhy bazaki ci abincin gidannan ba sannan tace in kika sake kika fadawa ubanki wlhy sai na ci ubanki , haka khairat ta tashi ta shiga daki ta
dinga kika harda ajiyar zuciya , duk Wanda yaga khairat sai ya tausayamata
Anty hafsat kuwa bayan ta koma gida maimuna da rahama ta kira tace ,kuna ina da sauri suka zo suka durkusa , sukace sannu anty gamu ,ko kallon kirki basu isheta balle su samu damar da zata amsa musu , tace daga yau kar in kuma ganinku a Fallon nan , in har ba ni na nemi kuzo ba kunci ko jikinsu na rawa suka ce toh , tayi saurin cewa kutashi kutafi , suka bar Fallon suka shiga dakinsu
Alhaji mukhtar ne yadawo gidan , da Sauri anti hafsa ta tatareshi tayi saurin cewa , kadawo yace eh ranki ya dade, tace toh kasan me nakeso dakai , daga yau karka kara zuwa gun mahaifiyarka matukar baka sanar dani ba , da sauri yace ai ranki yadade rabon da inje ai na manta ma bazan ma je ba , tace yauwa ,
Anti sadiya kuwa bayan tadawo gidane ta tarar da mijin nata a daki ya zaune yayi uban tagumi da alama tunani yakeyi , cikin sauri ya kalleta ya ce sannu da dawowa ,rai a hade tace, me kakeyi naganka duk wani iri tunannin me kakeyi , cikin fara a yace haba ranki ya dade tunanin mai zanyi ina tare dake ba tunanin da nake anty sadiya tace aihoo , akwai abinci a gidan ,da sauri yace aa amma kifada mai zan je in dafa miki , cikin isgikanci tace ko indomie ne kadafa mun,da kwai kuma kartayi ruwa jikinshi na rawa yace toh angama , haka ya nufi kitchen yafara aikin dafa mata kamar wani dan aiki, abun tausayi.

*MUJE ZUWA*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️✍️( MUM FU,AD*)

*PLS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE10*
Da safe Aisha suka nufa gidan Mahaifinnata , suna isa aka shaidamusu yana dakinshi , suna shiga ya ce su shiga cikin dakin da yake istihara
Aisha ce zaune kusa da alhaji baba ,da mahiafiyarta , shahararan mallamin addini ne yana istihara sossai ,tsoho ne ba wani tsoho canacan ba

Please Login or Register in order to submit comment