Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nace miki ina jin dadin gidan nan nayi karya , tabbas da akwai Inda zanje da na tafi nabar gidan nan ,dan wlhy ba kin cikinsu yakusa ya kasheni, allah yasani , ina zama ne kawai dan yarana ina tunanin randa kasa zata rufe ,ido ne , bansan wani irin halin yarannan zasu shiga ba, gasu 'ya'ya mata, da rai ma kiga irin rayuwar kaskancin da sikeyi a gidan, kamar ba gidan ubansu ba, inagakuma in bana raye,

Hajiya tayi shuru , tace tabbas sai yanzu nake da nasanin Duk abubuwan da na aikata miki, hajara kiyi hakuri , nayi kuskure babba da har nabari yar gidan hajiya amina tashigo zuri ar mu , nasan cewa basu da mutunci, kiyaiyyar da nake miki yasa nakasa , ganin illar auranta , amma ba abun da yafi karfin allah kiyi hakuri dan allah .
Hajiya Hajara tace haba ba komai hajiya ai yawuce yanzu kawai muyi kokarin ganin mu fuskanci abun da yake gabanmu .
Hajiya tace toh in Allah yayarda , hajaratu bakuda dan abinci ne a gidan wlhy yunwa nakeji dan ko karyawa ban yi ba , hajiya hajara tayi murmishi tace hummm hajiya kennan , wlhy tallahi muma yau ba abun da mukaci dan me gida ta hanamu shiga kitchen , dan yau ma tace kar ma su rahma su girkamata , ita zata girka , dama inaso in tayi barci ne mudan shiga musama ma cikin mu abun da zamuci.
Hajiya tace Tabb , a lallai wanna abu akwai daure kai , barin tafi gida , Hajiya Hajara tace toh ki gaida gida sai anjima .

Hafsa kuwa bayan tashiga dakine , ta kira mahaifiyarta tafada ma komai , duk abun da yafaru , mahaifiyarta ta kara zugata, akan tashiga ba da mulki san ranta a gidan dan itama haka tayi , hafsat taji dadin hakan daga bisani sukayi sallama ,

alhaji muktar ne ya shigo dakin , yasamu hafsat hakimce a kan kujera, ya durkusa kasa kamar mai neman gafara, yace dan allah hafas kiyi hakuri akan abun da hajiya tayi miki gaskiya banji dadi ba kiyi hakuri tun wuri zan ma tufkar hanci inshallahu
Hafsat da take ta karkakafa kafa tasa faya akan daya tace ba waninan munfuki , bansan munafurici , ai ina ji kana ce mata zakaje gobe to wlhy in kaje , kasan da cewa zama na dakai yakare a gidanan ,ehee, alhaji muktar yace haba hafsat me yayi zafi haka har kie ikirarin rabuwa , wlhy na miki alkaqari bazan je hafsat tace , yauwa sai kuma munafukar matarka , wlhy in baka day mataki a kanta ba no zan dauka a kan ka , alhaji muktar yake kiyi hakuri, zan dauka , amma ki fadumun abun da taiyi miki in yaso sai in mata kashedi akai , hafsa tace ooo lallai sai ma na fada , kai nifa bari kaji nama fara hajiya da zama da suba gidanan nikawaai kasaketa kowa ya huta, Alhaji muktar yacevamma hafsa in nacsaketa , bata da INDA zataje kinsan marainiyace , kiyi hakuri dan Allah mucigaba da zama da itako dan 'ya'yanta , inyaso sai kimusu duk hukuncin da kikagadama akansu ,hafsatvta be baki race shikenan ,

A bangaren hajiya rahmatu kuwa tanata zuba ido amma inaa har yanzu alhaji muktar bai zoba , ki takirashi awaya baya dagawa ,dan hafsat tamai gargadi India yakara daukan wayar hajiya toh lallai itada shi ne , hakan yasa hajiya ta daina kiranshi , dan kuwa tayi alkawarin ko yunwa ,zata kasheta bazata kara nemanshi , zata manta cewa tanada daa a duniya, ta sallama ma hafsat shi har zuwa lokacin da allah zaisa alkadarin su ya karye , zata cigaba da zubama sarautar allah ido .

Hajiya Hajarace kwance a daki ba lafiya , duk Wanda ya kalleta , sai ya tausayamata , domin kuwa tana cikin mawuya cin hali .
Bakomai ne yasata cikin wannan halin ba illa bakin cikin hafsa da alhaji muktar , dan tun a baya hajiya hajara na daukeda hawan jini da ciwon zuciya , shiyasa take kiyayema duk wani abu da zai bata mata rai , amma hakan bai yuyuba .

tana kwance yaran na ta faman kuka , maimuna tayi saurin cewa ,Rahma kiyi sauri ki kira baba kinga jikinta bai tabayin zafi irin na yau ba kije ki kirashi ki rokeshi , yazo , Rahma tayi murmishi da yafi kuka ciwo tace anti maimuna kinsan ,bazai zo ba ,yau tsawan wata daya kenan baba bai tabs takowa ya kalli inda mommah take ba , balle har yabada kudin da zamu kaita asibiti ,

Kafin kace me hajiya hajara tafara amman jini, dan bakaramin jin jiki take ba , ba abincin kirki babu magani , dole ta gala baita.
Da gudu Rahma ta nufi dakin hafsa , kasancewar da safe ne alhaji muktar bai tafi aiki ba ,

Ta shiga tasamu yana yi ma hafsa tausa , dan a halin da ake ciki hafsat na dauke da cikin wata biyar , shiyasa alhaji muktar ya dauki san duniya ya dauramata baya ganin kowa sai ita , dan a halin yanzu hajiya amina taje gun boka tasa anyi mishi aikin da mahaifiyarshi ma ya manta da ita , yaranshi da matarshi ma haka , sai dai in sun hadu ya kallesu , kamar bai taba ganinin su ba .

Rahama na shigowa yayi saurin cewa ke miye haka kika shigo ba sallama , hafsat tace dan ubanki bakida hankaline ?? fita a dakin nan ,

Rahma ta durkusa kamar me neman gafara ta fara kuka , tace anti dan girman allah kidubi girman allah ki taimakemu kusa baki baba yaa kai mommah mu asibiti ,narantse da allah aman jini takeyi , jikinta bai taba tsananta kamar yau ba , ta na kuka sossai muryarta dakyar take fita tsabar kuka da dashewa da muryartata tayi .


*waiyyo masu karatu bazan iya cigaba da typing ba sabida kuka da ya kubucemin, dan inada saurin kuka sossai kuyi hakuri da wannan sai kuma gobe inshallahu*


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️✍️(MUM FU ,AD*)

*PLSS SHARE*

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

💔💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* 👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 21*

Hafsat tace dalla matsa kibarmun muna fukar magiyar da kike mun , munafuka kinmanata ranar fa cemun kikayi idan naga dama kar in barku da rai , ko kinmanta??
Rahama da hawaye ya gama wanke mata fuska hade da majina tace ,
Anti shikenan kar kisa ya taimakamun , cikine a jikinki bakida masaniyat cewa zaki haihu lfy ko bazaki haihu ba sannan, in kin haihun zaki kasance a raye ko kuwa , amma kisani in har, kikabari mahaifiyarmu ta mutu baki ne me yafiyarta ba to tabbas sai allah ya hukuntaki abisa cutar da matar da bataiyi miki komai ba , wlhy anti kiji tsoron Allah kisani zaki mutu , zaki tarar da ubangiji ,kinsan cewa , duk abun da ka aikata mai kyau da Mara kyau mala iku na rubuta ma , kaset video ne , bakya tunanin in kinmutu mai zakije kice wa alla... bata rife baki ba taji saukar kyakyawan mari a fuskarta jikake tassss .
Hafsat tace dan ubanki har kinyi girman dazaki dinga fadamun magana , har kinsami fuskar mun magana dan ubanki .

Alhaji muktar daya ke kallon duk abun da yake faruwa bai ce komai ba yataso yace kee Rahama fita a dakinan , hafsat tace oo iya abun da zakace mata kennan , kanaji tana farfadamun magana san ranta , alhaji muktar yace zakifita ko sai na ci ubanki yanzunanna , dasauri Rahama ta tashi tafita tana kuka tanufi dakinsu , tanashiga ta tarar da maimuna nata faman kuka , hajiya hajara na kwance tana kallansu dauke da murmushi a fuskarta , tadan daga hannuta dkyar tace , zz..ooo Rahma, tafada da muryarta da bata fita , tace, kiyi hakuri nasan da kikaje , wulakanci tamki ko , Rahama ta fashe da kuka tace , mommah kiyi hakuri barin fita ko aran kudi nayi dan mu kaiki a sibiti , hajiya hajara tayi saurin riko hannunta tace barshi kawai 'yata , hakan kamar tonan asiri ne, in Allah yayi zan tashi zan tashi , haka in Allah bainufa zan tashi ba bazan tashi ba , dakyar take iya magana da muryarta ma bata fita , takara da cewa kije dai ki sanar da hajiya halin da nake ciki , duk da nasan itama takanta take, Rahama tace toh shikenan , da sauri ta tafita .

Tana isa gidan ta ga hajiya Rahmatu ta rafka uban ta gumi sai gamma takeyi , da sauri Rahama ta karasa gurinta tace hajiya lafiya kuwa , hajiya tasa kuka tace wlhy Ramatu rabona da abinci tun jiya, makota da suke bani ma sun gaji , nikam na yanke shawarar kauye kawai zan koma , Rahma tace eh ki koma gaskiya zaifi , nima nazo fada miki ne mommah mu batada lafiya , daxu aman jini ma tagama yi , naje gun baba amma matarshi ta hana shi ya bamu mudi mukaita a sibiti ,dan allah hajiya kizo muje kimai magana ko allah zai sa ya bamu kudin wlhy hajiya mommah mu na jin jiki.
Hajiya tace hummm Rahmatu da alama kin manta abun da yafaru a baya , kiduba cin mutuncin da matar muktar ta mun amms bai iyacewa komai , nikam na salllama , zanta zubawa sarautar allah ido , in kuma rai yayi halinshi shikenan, amma kuyita tofa mata addu, a ki tashi kitafi gida yamma tafarayi , Rahma tace toh hajiya sai anjima.

Rahma na na shiga gida ta tarar da jikin maman ya kara tashi , jikinta yayi zafi sossai kamar wuta , tana wani irin jijjiga , a lokacin har an kira sallar la magriba, alhaji muktar ne yafito zai nufi masallaci , maimuna najin motsinshi tayi saurin fitowa ta durkusa tace , baba dan girman Allah kataimaka kabamu kudi musiyo magani , wlhy jikinta ya tsananta , alhaji yace ke karki dameni dan Allah , hungo , yaci dari biyu ya mikata mata , da sauri ta karfa , tafita da sauri ta siyo paracetamol , tadanyi ma Mao pharmacy din bayanin halin da mahiafiyarsu take ciki ,

Mai pharmacy din yace kukuma kukabarta a irin halin da take ciki , wai tsaya ma ke ba 'yar gidan Alhaji muktar Tafida bace tace eh nice ,tafada a takaice yace"" toh shine bazaku kaita asibiti ba mahaifinku baisan bata da lafiya bane ??
Tace uhmm kaga ba lokacin yi sauri kawai kabani abin da yasamu sauri nake , yace okk tov shikenan , da haka ya harhada mata magani , sannan yace sai taxi abinci kafin tasha, maimuna tayi shuru cikin ranta , tana tuna rabon da suci abinci mai kyau kwan uku kenana sai dai sudansha Lipton ,
Tayi saurin cewa mai pharmacy uhmm toh kaga karage magungunan , kabani na dari inaso inyi afani da darin, yace kai aa baza ayi haka ki karba duka , ga Dari , yamika mata Dari ta Karna tana godiya ,ta tafi da sauri.
Mai pharmacy din ne ya ce Kai anya lafiya kuwa , ace mutum kamar alhaji muktar amma yarshi tazo siyan magani , na dari biyu da alama ma abinci zata siyo da darin , kai allah sarki , amma gaskiya akwai lauje cikin nadi,

Maimuna kuwa gurin wani me soya da kwai ta tsaya da yake dan gaba da layin sunkadan ta siya ta naira Dari , mai doyanne ne yace , kai ina ke 'yar alhaji muktar ce , maimuna tace eh menene , ya aahhh ba komai kawai dan naga kamar ki kizo siyan doya a nan kuma ta dari, tace ehh sha awarcin doyan siye kawai nake , mai doya yace yauwa ko danaji amma ace Kamar ki ki siya doyan dari, maimuna tace kaga nagode sai anjima.

Maimuna ta nufi gida , tana shiga tayi sauri ta daga mahaifiyar tasu tace sanna mommah tashi kici , Rahma tace a ina kika samu kudi , maimuna ta fada mata komai , tanata kokarin bawa mahaifiyar tasu abincin amma bata iya ci ,
Wani irin tari hajiya hajara tafara dauke da jini , tanasan yin magana amma takasa, dakyar suka dagata suna kuka , suna fadin munshiga uku mommah dan allah kar ki tafi ki barmu a wannan gidan , dakyar hajiya hajara tace , Rahama "" maimuna""inaso ku saurareni dakyau kujini , duk in da kuke kuji tsoron Allah kusani duk abun da kukayi zaku girbi abu da kuka shuka , kusan da cewa ku 'ya'ya matane kuma gidan wani zakuje , ku kiyaye mutincin ku , kar san abun duniya yasa kuyi kokarin zubar da mutuncin ku , hajiya hajara na magana dakyar hade da tari , takara da cewa , karkuyarda halin da kuka tsinci kanku a gidanan yasa kuje ku lalata rayuwarku , ku kiyaye duk wani abu na saban allah , dan allah yarana nasan irin tarbiyyar da na baku , karkuyi abun da zai bata wa antinku rai , duk wani halin da kuka tsinci kanku watarana sai labari , kusani Baxa ku taba dawwama a haka, ba, kucigaba da yimata ladabi da biyaiyya kamar yanda kuke mata , kar karkufasa , nayi imani cewa ba haka hafsa tabar maihaifinku ba, dan nasan kunsan san da alhaji yake mana, duk abu da yake aikatawa ba a haiyyacinshi yake ba sanna kuma, kudai kucigaba da addu a kina tashi sallah in Allah ya yarda komai zai wuce , wani irin tari hajiya hajara tafara tana fadin ku kiramun mahaifinku muyi bankwana dan nasan bazan tashi ba , Maimuna da Rahama da kuka yagama wanke musu fuska hade da majina , suka tashi dukkansu da gudu , suka nufi dakin hafsa , da sauri suka ce babba dan allah kazo mommahn mu nakira kazo kaga halin da take ciki, tace kazo ku gana dan allah , suka rike hannunshi , yayi saurin janyewa yace baku da hankaline dallah ku sakeni ,
Hafsat ce tace uhmmm jeka ko ba komai tamaka kallan karshe , alhaji muktar yace toh muje,

Suna shiga suka tarar tanata amma jini tafado akan gado , da sauri yaran suka nufi gunta suka riketa , Rahma tace , babba kaga halin da take ciki, dukda Alhaji muktar baya haiyyacinshi sai da yaji tausayin matar tashi , ya karasa gurin , ya kalleta yace sannu ko , hajiya hajara datakw kwance a hanun Rahama, tace allah ya karya duk wani abun da akayi maka, in Allah yasa hankalinka yadaqo jikinka ga amanar yarana , tana magana hade da tari , dan dakyar take magana muryarta bata fita , tace ni zan ban muku duniyar ,

Hafsat ita ma ta shigo dakin dan ganin halin da hajiya hajara tame ciki murna suk ta kamata , ganin halin da take ciki, dan tasan cewa wanna dole ne ma tamutu. _niukuwa nace ai ran ba a hannunku yake ba_

Hajiya hajara takallo hajira tace , ni zan barmiki duniyar , kuma kiji tsoron allah , da haka wani irin tari ya kubcemata , kamar kirjinta zai fito , tafar sallati dakyar muryarta bata fita , take taja wani dogon numfashi , idonta yakoma kallan sama , kanta yayi gefe ,
Innalillahi wa inna illaihir ra ju un allah yakarbi ran hajiya hajara, abun da alhaji muktar ya furta kenana , da sauri Rahama da maimuma suka kalloshi suka ce ta mutuu!!!!! ya kada musu kai alamar ehh, wani irin ihu sukasa , sukafadi kasa a sume ,
Hafsat kuwa daki tashiga da sauri tafara kiraye kirayen waya , yana sanar da 'mutane allah yayi ma hajiya hajara rasuwa ,cikin ranta kuwa murna take da hakan, dan zata kara cin karanta ba babbaka, dan kuwa ,har ya hango yanda zata bautar da yaranan ,

Alhaji muktar e ya kira limam da sauran ja ama , akayi mata sallah aka kaita gidanata na gaskiya , _*UBANGIJI ALLAH SA MUYI KYAKKYAWAN MARSHE*_ lokacin har su Rahama sun farfado , sai hawaye kawai suke fitarwaa dan kukan ma sun kasayin shi , duk me imaani in har yaga su maimuna toh saiyya tausaya musu sun fita haiyyacinsu ,sun rame kamar basuba , kowa yazo sai ya bamu hakuri akan su dau dangana,

Bayan anyi bakwai ne yan uwan Hajiya hajara da suke kauye suka bukaci da alhaji muktar ya basu yaran su tafidasu amma fafur hafsat ta hana shi , tace wai miye amfaninta daba zata rikesu , amma cikin ranta ba dan allah zata rikesu, zata rukesune dan ta gana musu azaba san rantaa .

yaran basu zama a gun hafsat ba hakan yasa suka amince da basason yin jayaiyya da su akan hakan ,amma cikin ransu suna tuna halin daza su shiga a gidan a gun hafsat dansun san tabbas kashinsu yabushe.
Haka yan uwan hajiya hajara suka hakura , basu wani damu dan ya hanasu yaran ba dan dama sun san hakan ba mai yuyuwa bane , sundai yine dan kara , amma su Kansu in suka tafi dasu hidima zata musu yawa , gashi hidimar 'ya'yamata bata karewa , tunda ubansu nafa hali , shikenan, dahaka suka koma abinsu , amma tabbas daga yanayin hafsa sunga take taken rashin mutunci , a dan zaman bakwai dinan da sukayi , amma sinyi alkawarin zuwa dubasu akai akai dan ganin irin rayuwar da su ke a gidan.

Bayan 'yan wattanni ne in kaga su maimuna sai karantase ba su bane duk sunfita haiyyacinsu kamar ba suba , dan ko makaranta sun daina zuwa , in ka gansu sai karantse da allah 'yan aikin gidan ne , dan hafsat ta kori duk yan aikin gidan ,su maimuna ne suke komai , har gyra flowers komai su sukeyi ,
Bata barin su fita balle su sami Samarin da zasu auresu ,

'Yan uwan hajiya hajara sunyi sunyi alhaji muktar yabasu su hajara amma hafsat ta hana shi ya basu , sam yaki yarda ,
Suna yawan zuwa akan yayi hakuri ya basu amma yaki yarda , dan har kaahedi hafsat tamusu akan kar su kara zuwa mata gida.

Ta gargadi me gadi akan kar yakara barinsu su shigo gidan in ko yabarsu a bakin aikinshi ,
Shiyasa tunda suka zo sau daya me gadi ya hanasu basu kar zuwa ba, suna ta adduar allah juyo da hankalinshi ya gane gaskiya dan sun san ba banza ba , aka barshi ba .

Hajiya Rahamatu kuwa ta dau dangana , wataran haka zata ci kukanta koshi tana matukar danasanin auren da alhaji muktar yayi , dan a halin yanzu alhaji muktar kwata kwata baya zuwa gunta , watarana haka zata kwan da yunwa, abinci in tasamu taci in bata samu ba ta hakura , in yan uwanta suka zo sukan dan kawo mata dan abinci da dan kudi , dan bakowa yasan halin da take ciki ba , dan tayi alkawarin bazata fadawa kowa halin da take ciki ba , dan nasan ba yin kanshi bane , zataiyita fadawa Allah .

zuwa yanzu , hafsat ta haihu ta haifi danta na miji me suna faruq murna gun alhaji muktar ba a magan ya daura san duniya akan faruk , dan ya shagwaba yaran sossai sossai , ya sangartashi , yanada shekara biyu , hafsat takuma haifan mace , mai suna nusaiba , yanzu nusaiba Nada shekara ,uku duniya , faruk kuma Nada shekara biyar.
Gaba daya yaran suna San sun maimuna dansu sanba da su dan komai su suke musu shirin school makaranta komai su suke musu , hakan yasa suka shaku sossai , amma hafsat bata san hakan kullum tana nuna ma yaran hanya dan abun raina su maimuna , amma yaran basa yi , dan susan cewa basa musu mugunta , duk da cewar suna ganinsu kamar yan aikin gidane , dan basu san cewa yayinsu bane, dan hafsat nunar musu take cewa su maimuna yan aiki ne.

Wanna kennan rayuwar da take faruwa kennan a cikin gidan anti hafsat mata a gidan alhaji muktar tafida.

Kubiyoni a next page dan jin gundarin labarin rukkaiyya da sadik , ma farin soyyaiyarsu harzuwa aure !!!

*MUJE ZUWA*

*ina alfahari daku mu fans ina godiya da dukkanin addu oin ku gareni*

*bazakujini gobe ba gaskiya zai jibi ko gata in Allah ya kaimu , sabida inada dan uzur PLSS ,*

*Luv u all my fans*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY*✍️✍️✍️ *(MUM FU A,D*)

*PLSS SHARE*👏👏

🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLLAHIR
RAHMANIR RAHIM

💔💔💔💔💔💔

*MAHAUKACIN KISHI*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*👉zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabir
Facebook zaynerb Muhammad kabeer
Email address zainab m kabeer,s @gmail.com..
*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7




*PAGE 22*



*wanene sadik*
Abubakar Sadik sulaima shine cikakken sunanshi , haifaffen garin bauchi ne,
Mahaifinshi alhaji sule mai turare, babban mutum ne a garin , kasancewarshi babban mallami , mai fada ajii kuma dan siyasa , sannan me tarin dukiya , Abaya yayi sana ar siyar da turaruka shiyasa , ake mishi lakabi da mai turare,

Alhaji sule mai turare yana da mata biyu , hajiya saude da hajiya asma ,u
Hajiya saude itace farko, mahaifiyarsu sadik , tanada yara biyu , sadik shine na farko sai kanwarshi budurwa , wato salma , sadik allah ya fara bata , kasancewar ta dade bata haihuba daga baya sai ta kara haifan salma tundaganan haihuwarta ta tsaya .

hajiya asma ,u itace ta biyu tanada yara biyar mata uku maza biyu , Inda matan kowacce na gidan aurenta.

Sadik yaro me matashi me ji da kanshi , kyau kaurjin ba a magana , uwa uba iya daukan wanka da iya sanya turare , sadik irin black beauty dinan ne , in har yafito , yana takun kasaita kamar bazai taka kasa ba.
Sadik na aiki ne a wani banki na NDIC ,
Shiyasa 'yan mata suke rubibi a kanshi , kowacce mace na burin mallakarshi a matsayin mij.
Sun hadu ne da rukkaiyya a layi , kasancewar gida jan iyayensu basu da nisa tsakani.
Rukkaiyya farace doguwa, ba laifi tana kyau iya gwargawado , tunda sadik ya ganta yaji yana matukar san ya mallaketa a matsayin mata , koda yaje ya tunkareta da bukatarshi,

Please Login or Register in order to submit comment