Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amma alamar girma sun baiyyana sossai a cikinshi kasancewar ya gada ne a gun mahaifinshi , mahaifine agun mahaifiyar Aisha , suna zuwa Aisha tamai bayani akan yayi mata istihara akan sadik , ai kuwa ya alhaji baba yaje yayi alwala sannan ya zo ya hau kan darduma ya feshe jikinshi da turare sannan ya daukko wani carbi yana ja , ya na karanta wasu a addu oi , bayan ya idar da addu oin ne ya kalli Aisha yace , tabbas sadik na sanki son na gaskiya da hakika , sadai matar shi kam , alhaji baba yadanyi shuru sannan yacigaba da cewa gaskiya matar shi makirace hatsabibiya zata iya kashe mutum har lahira akan mijinta sabida *MAHAUAKCIN KISHIN* da take mai ,amma gaskiya game da auranku za a sha fama amma tabbas akwai aure tsakaninku amma.. sai dai alhaji baba yayi shuru don yakarayin istikahara akai , yakarayin shuru sannan a yace akwai alkhairi sossai gameda auran , amma sai mun Dage sossai da addu a , dan gaskiya matar shi ba azaune take ba ba imani a ranta , sabida haka sai mun tashi tsaye wajan yin addu a , mahaifiyar Aisha ce tace , toh alhaji baba mungode Allah kara girma alhaji baba ameen, yakara da cewar , kar Ku karaya , sabida 'yar wannan matsalar inshallahu zamuyi maganini komai ,tunda munriga munce Allah , sabida haka tun daga yanzu zanfara ba aishatu maganin tsari da kaikaiyi koma kan mashekiya , kafin ma ace ta shiga gidan , dan gaskiya akwai mugun nufi gameda matar , sai dai aishatu zanfadamiki abu daya karkitaba karaya akan lamarinan kisani babu wanda ya isa ya ma mutum wani abu in ba da yardar Allah ba , mubaiga muce Allah shi zai wuce mana gaba , sannan karkiyarda ko da kinshiga gidan kisa ka tsoro aranki yawan tsoro na tasiri sossai akan mutum ba , sannan tun yanzu kidinga karanta , WAMAKARUN MAKRUN WALLAHU KAIRUL MAKIRIN , toh in Allah ya yarda duk wani makircinta zai karye, inshallahu zandinga aikomiki da aduo i sannan in dinga baki rubutu kinasha , kema kuma sai ki dage da addu a , jiki a sanyaye Aisha tace inshallahu alhaji baba nagode ,Allah saka da alkhairi , yace toh kutashi kutafi , suka karamai godiya suka fito suka nufi gida
Bayan sun isa gidane se kara tattaunawa akan lamarin, mahaifiyar Aisha ce tace nifa wlhy Aisha duk na ji wani iri akan wannan lamarin , Allah yasani aure tsakaninki da sadik harga Allah ya fita a raina , ke kinsani ke kadai na mallaka a duniya , karwata tazo tayi sanadin salwantar da rayiwarki , ni kam Aisha harga Allah dazakirabbu da sadik gaskiya da nayi farin ciki , dan wlhy duk na karaya da lamarin nan gaskiya , Aisha tace haba mamana kinmanta da abun da alhaji baba yafada dan Allah karki karaya mama in kika karaya nima kinga banda kwarin gwiwa , amma Indai kikace in rabu da shi zan rabu dashi din , mahaifiyar Aisha tace gaskiya naga alama kinasan sadik kam , amma ni bazan iya cewa komai ba sai dai kawai Allah ya zaba abun da yafi alkhairi , in sadik mijinki ne duk runtsi duk wuya sai kin aureshi , abun da zamuyi kawai sai dai muce Allah zaba abun da yafi alkhairi , Aisha ta amsa da ameen
A bangaren hashim kuwa bayan ya dawo gidane yake sanar ma da mahaifiyar shi a yanayin da yaga rukkaiyya , mahaifiyar hashim tace , kai hashimu ni kam anya bazaka rabu da yarinyar nan ba , nifa gaskiya ban aminta da mahaufiyarta ba , gaskiya da alama dai bamasu mutunci bane gaskiya , hashim yace toh mama ai ba laifin khairat , ita kanta khairat din in ka kalleta zaga fuskanci akwai Damuwa cikin ranta , amma dai zan cigaba da sa ido nagane , mahaifiyar hashim tace toh Allah ya kyauta ,
Sadik kuwa bayan ta tashi a gun aiki bai zarce ko ina ba sai gidansu Aisha , ta na fitowa kana ganinta kasan akwai 'yar matsala tareda da ita , tanshiga moton suka gaisa ya kalleta yace ya dai Aisha akwai wani matsalane ta ce aa babu kawai ya ce OK naga ba haka kika saba fitowa ba, tace aa bakomai fa kawai dai kainane yakedan ciwo ,da sauri sadik yace subhanallah , sannu Allah baki lafiya , tace ameen ta kalleshi tace sadik , yace na am , yazakayi idan akace yau mun rabu ma ana bama tare? Sadik cikin wani irin yanayi yace haba Aisha wacca iri. Maganace wannan dan Allah in ma wasa like kidaina banaso , Aisha tayi murmushi tace aa wlhy ba wasa nake maka ba , kawai dai mudinga addu ar zabin alkhairi , sadik cikin tashin hankali yace , toh wai ma Aisha me nene ya faru da har kike ikirarin rabuwa dani? Aisha tace bakomai kawai nafada ne , kasan ba lallai in zama matarka , sabida kana naka ne Allah na nashi , tace ni barin shiga gida , idonta fam da hawaye ta buds motar ta fita
Sadik shima yafita da sauri yace Aisha tsayamana ya zaki tafi bamu gama magana ba , Aisha kam ko juyowa batakarayi ba , ta shiga gida da sauri ,tana kuka,
Hankalin sadik ba karamin tashi yayi ba ,zufa ce take karyomai ko ta inaa duk ya bi ya rikice , a take yafara kiran number Aishan Amma taki dauka haka ya Shiga motarshi yaja ya tafi,
Aisha kuwa tana shiga gida ta shige dakin mamanta tace mama dan girman Allah karkice in rabu da sadik wlhy mama inasanshi, shima yanasona, kar halaiyyar matarshi yasa ki ji tsoro , dan Allah mama kiyi hakuri , mahaifiyar Aisha tace toh shikenan Aisha Allah ya wuce mana gaba dama ai ni bance dole sai kin rabu da shi ba kawai dai na tsorata da halin matarshi ne ,sabida haka Allah ya zaba abun da yafi alkhairi, cikin farin ciki Aisha ta amsa da ameen mamana na gode , Aisha ta tafi dakinta tafara kokarin kiran nubern sadik din , ta kira sai ya rejecting kiran , yakirata , tace fatan dai mijina baishiga damuwa ba , cikeda mamaki sadik yace wai dan Allah miye haka ne zakisa zuciyata ta buga ne , karki karamin irin wanan , Aisha tace , wlhy ba wasa nake maka ba ansamu 'yar Matsalane shiyasa ,amma yanzu kamanta kawai komai yayi daidai.
Cikin farin ciki sadik yace alhamdulilah , bai nemi tafada mai wani irin damuwa bane , hakan yasa yayi shuru tunda tariga tace yawuce , sabida haka watarana zata fadamai ,
Haka sukayi salama cikeda farin ciki sadik Yakoma gida , bayan yadawo yashiga gidan , yasamu duk suna falo amma banda khairat , yakalli kausar yace ,ke ina khairat take , kausar duk ya kamata tace tana daki , yace ita meyasa bata fito ba ,kausar tayi shuru, sanin halin mahaifiyar tasu indai tafada toh tabbas ta shiga uku yau, sadik ya daka mata tsawa yace badake bake maganaba , aikuwa kaninsu yayi saurin cewa , mama ta mata duka tana daki , kuma tace karta yarda ta fito , sadik ya kalli rukkaiyya yana mata kallan tuhuma yace , metayi kika dake ta , rukkaiyya ta cuno baki tace ai bai zama lallai kasani ba , ai ni mahaifiyar ta ce , ko ban isa in mata hukunci ba tafada tana harare harare da murguda baki , yace eh wani irin laifi tayi, dan nasan matukar kina jin haushi to akanta kike hucewa, me ta miki , rukkaiyya ta tabe baki tace ohoo, to ina ruwanka , har zaiyyi magana , kawai yakada kai ya shiga cikin, dan shi bayaso yadinga biye ma rukkaiyya suna tashin hankali , dakin khairat ya Shiga, yaganta a kwance tana kuka , yadagota ya kalleta yace me kikamata ta miki irin dukannan, shuru tayi tafashe kuka mai cin rai ,sadik yace ba kuka nece kimin ba kifadamun me kika mata ta miki irin wannan duka , khairat tandan tsagaita kuka , ta fadamai duk abun da yafaru sadik yayi shuru yace , kiyi hakuri watarana sai labari , yace yanzu kinci abinci khairat ta kada kai tace aa, yace OK barin kawo miki , tace toh , haka sadik ya shiga kitchen ya dauuko abinci da kanshi ya ba khairat , yace taci , shima yaje ya daukko nashi yafara ci dan yasan rukkaiyya bazata taba kawomai abinci ba ,ita ko rukkaiyya ko a jikinta ta tattarasu ta watsar daga sadik har khairat din ,

TUNA BAYA WACECE RUKKAIYYA ??
WAYE SADIK ??

*MUJE ZUWA*😎

*KUYI MANAGE DA WANANA PLSS*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️
*STORYAND WRITTEN BY✍️✍️✍️✍️( MUM FU,AD*)

*PLS SHARE*πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 11*

wacece rukkaiyya?
Rukkaiyya Muhammad mai dala, shine cikakken sunanta ita dai yar asalin garin bauchi ce , mahaifinta yayi suna sossai a garin kasancewar me kudi ne na gaske , alhaji muhammadu mai dala kenan , yana da mata uku da yara , goma , mahaifiyar su rukkaiyya itace ta farko wato hajiya amina , hajiya amina bata da mutunci , duk ta bi bokaye ta mallake alhaji muhammadu , alhaji muhammadu baiyajin maganar kowa sai tata , baiyya taba shiga sauran dakunan matanshi in ba rabo me karfi ya ratsa ba , wato rabon 'ya'ya kenan, kwata kwata ta asirceki ,shiyasa duk abun da rukkaiyya da 'yan uwanta sukeyi kamar sun shashine a nono , dan duk rashin mutuncin su ko kwatan mahaifiyar su basu kai ba , alhaji muhammadu mutum ne mai mutuncin da sannin ya kamata sannan yasan darajar dan adam , ga kyauta ga fara a ga karamci , babu Wanda baya yabon shi , Sai dai kash tunda ya auri hajiya amina duk ta mallake komai , ta hanshi yima kowa alkhairi , haka yanaji yana gani zai hakura.
bakamar mamatarshi da sauran 'ya'yanshi ba ,hajiya amina itace me yara biyar namiji ne farko , me suna kamal , Sai tabiyu anti sadiya , sai ta ukun anti hafsat Sai ta hudu rukkaiyya ,Sai na miji auta a dakinsu me suna Ibrahim , duk cikin yaran babu wanda ya daukko hali na gari , dan duka yaran dakin hajiya amina basu ki ace babansu baya doron kasa ba ko dan suci dukiya , domin babban dan har kudi ya bayar a kashe babansu , Amma allah bai nufa ba,
Watarana yayi tafiya cikin dare aka farmusu Sai ga 'yansada sunzo gurin bayan an kamasune ,suke cewa kamal ne yace akashe alhaji muhammadu,
Alhaji muhammadu yayi kuka kamar ranshi zai fita, yana kuka yana cewa allah mai na maka zaka jarabceni da irin wannan yaro allah kadubi halayena allah ka tausayamun , wai ace yaron da nahaifa da shi zai aika akasheni , alhaji muhammadu ya dade yana tunanin da mamakin abun , amma hakan baisa ya fadawa kowa maganar ba , hatta dan nashi bai bari ya gane cewa yasan shi ya aiko a kasheshi ba ,hakan yasa yabar abinshi shi Kadai a cikinshi
tunda alhaji muhammadu ya gane cewan hajiya amina da 'ya'yanta naso ya mutu hakan yasa yake matukar tsoron cin abincin gidan , dan ya gwammace ya ci abinci a waje,
Ko ya dawo gida in hajiya amina ta kawo mai abinci Sai ya ce yakoshi , hak zataiyita masifarta ta gaji ,duk da cewa yana matukar tsoron masifar ta in ta na mishi ruwan masifa amma bazai taba cin abincin ba , duk Wanda yaga alhaji muhammadu mai dala saiya tausayamishi. Sabida kwata kwata ba ya samun nutsuwa a tare dashi , balle kwanciyar hankali ,
Haka rayuwa ta kasance mishi , ba dadi, Dan duk abun da hajiya amina tace shi yakeyi.
Sai ta biyun hajiya zainab , hajiya zainab yaranta uku nafarko na miji mai suna auwal ,sai tabiyu macece me suna , sa adatu , sai ta uku me suna farhana .
Sai hajiya khadija , itama yara uku ne da ita ta farko , hauwa ,sai ta biyun balkisu sai ta ukun safiyya wato autan alhaji muhammadu mai dala kenan ,
Duk yaran alhaji me dala na sauran dakunan , matukar Suna bukatar wani Abu dole said sunbi ta hannun hajiya amina kafun ayi musu , da haka har suka saba , sauran matan su biyun basa taba daga ma Kansu hankali addu a kawai suka sa a gaba ,na Allah ya waiwayo da hankalin mijinsu garesu .
Basu ko damu da rashin zuwa dakin su da bayayi ba kullum cikin addu a suke .
A kullum hajiya amina hudubar da take ma 'yayanta shine su kasance , masu muliki a gidajansu , ita kanta ma Dan Allah ya nufa ne da kuma rabo shiyasa , akayi mata kishiyoyi har biyu, amma su kar su sake su zauna ayi musu kishiya , dan a danginta bame zama da kishiya ,Dan sunfi karfin ayi masu kishiya , daga kanta akafara kuma da ga kanta angama , kullum cikin hudubar Nan take musu shiyasayaranta suka tashi a Mara sa mutunci , Dan sunsha shi ne a nono ,

*PLSS* *KUYI MANAGAGE DA WANNA WALLAHI DAKYAR NA IYA TYPING KAINA CIWO YAKEMUN DAN ALLAH KUYI MANAGE KUYI HAKURI*πŸ‘πŸ‘πŸ‘

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU AD*)



*PLSS SHARE*πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 12*
Cikin hakane duk suka aurar da 'yayansu dadi ba dadi dai .
Kwata kwata 'yan ubansu basa taba shiga sabgarsu, ko kadan duk wani Sha ani da zasuyi basa taba zuwa ,sabida ko sunje kallan wulakanci ake musu , kamar ba ubansu daya ba , mutane har mamakin rashi jituwa irin nasu suke, kowa baya shiga Harkan kowa, amma 'yan dakin hajiya zainab da hajiya khadija suna zumunci sossai , sabani 'yan dakin hajiya amina, sabida su sunajin kansu,shiyasa ko takansu basayi sunagani sunfi karfinsu , haka rayuwa takasance musu ,har sukayi aure inda kowa take zaune a dakinta , har Allah ya karbi ran alhaji muhamamdu mai dala ,
Kafin alhaji Muhammadu yarasu , sai da hankalinshi ya dawo jikinshi , yana kwance A gadon asibiti yana rashin lafiyarshi ta ajali , ,
kasancewar yana dauke da ciwon zuciya.
Yana kwance ne yake bada wasiyar cewa " ,bazantaba yafe ma hajiya amina ba kuma inshllahu bazata ga gawata ba hajiya amina ta cutar dani ta rabani da 'ya'yana hajiya amina Allah ya isa banya fe miki ba , nabarta da allah , alhaji muhammadu ya kalli autarshi yace , safiyya ta , je ki kiramin liman , liman abokinshine
Tayi sauri takirashi ,bayan limam yazo ne alhaji Muhammad yace
Kowa ya fita suna so suyi maganar sirri da limam , bayan kowa ya fitane alhaji Muhammad yake cema limam ,limam kasan kasan matata hajiya amina da 'ya'yanta wlhy basu ki ace na mutu ba , ba sa kaunata sunfi son abun duniyan da na tara a kaina
Alhaji Muhammad da kuka yazubuce mai ya ce ma limama kaduba ka gani tun da na kwanta jinya ta sa kafar ta bar gidan bansan ma Inda taje ba , duk cikin yaranta babu Wanda yazo dubani kamar ba nine ubansu ba wlhy abun na damuna. gashi ina ji a jikina kamar yau zan bar duniyar ,yana maganar muryarshi kasa kasa , bata fita sossai
Limam ne yace haba alhaji ai cuta ba mutuwa bace , kayi hakuri watarana sai labari

Alhaji Muhammad yayi murmushin da yafi kuka ciwo yace , hummm limam Kennan , barin fada maka babban dalilin dayasa nakiraka
alhaji Muhammad ne yayi gyaran murya shine yake shaidamishi cewan akwai kudadinshi masu yawa a kasar waje to yanaso ko ya mutu kar a karbo da sunan a raba gado ya gwammace , abarshi a can kawai dan tabbasa yasan in aka karbo toh In Allah yayarda sai sunyi rigima akai shiyasa yace abarshi a can .
Alhaji Muhammad yayi gyaran murya yace , limam , abun da nakeso dai kai ko bayan raina banyarda a CE za a karbo ba , sauran Kudaden da suke nan , sai su karata dashi , su dinma wlhy da ina da lafiya gara ma in konasu kowa ma ya huta , ko kuma duk in kyautar , tunda duk akansu akesan ganin bayana , alhaji Muhammad ya fashe da kuka mai cin rai ,
Daga haka yace akiramishi sauran yaran ya karamusu nasihamai ratsa jiki , yakara da cewar suji tsoron Allah su so junanasu , kar abun duniya ya rudesu ,
Duk yaran suna sa kuka , daganan rai yai halinsa ,
Duk wannan abun da ake babu yaran dakin hajiya amina ko daya kenan balle kuma , ita kanta hajiya amina , dan ko sa sukaji babansu bai da lafiya basu ko zoba , sukace amai, Sannu , Allah ya bashi lafiya , basuje sun gaisheshi ba

Bayan yarasu ne hajiya amina ya dawo daga gantalinta , hajiya zainaba ce ta tareta da cewa ,wlhy hajiya amina kinji kunya , daman alhaji yace in Allah ya yarda baza ki ga gawarshi ba kuma yace , bai yafemiki ba duniya da lahira ,sannan yace kin cutar dashi kuma kin cutar damu , kin nisa tashi da 'ya'yanshi gashi yanzu ya barmiki duniyar ,sai Ku xauna kuci dukiya keda 'ya'yanki .
Aikuwa hajiya amina tasa shewa tace ke kikasani kanki akeji , kuma ki ka kra gangancin fadamun magana wlhy sai na miki tsinannan duka , hajiya ,zainab bata kara cewa komai ba , ta wuce ta tafi dakinta
Hajiya amina ma wucewa tayi ta tafi

Hajiya amina bata ko nutsu tama alhaji Muhammad takaba mai kyau ba yawanta kullum take tafiya , tagirma bata san ta girma ba, sauran matan kuwa sun nutsu sumishi takaba Mai kyau .
Bayan rasuwar alhaji Muhammad mai dala
da kwana hamsin aka raba gado kowa akabashi kasanshi ,

haka matan suka ci gaba dazama a gidan , kullum cikin fada domin hajiya zainab da hajiya khadija kowa gashin kanshi yakeji , basa yarda da mulikin mallakar da hajiya amina ta kemusu

Hajiya amina bata da wani buri da yawuce ganin 'ya'yanta cikin daula , hakan yasa take ma 'ya'yanta hudubar tsiya .

Shiyasa duk 'ya'yanta mata su ukun , bata bari su auri talaka ba ,duk masu kudi suke aura , dan tayi fariyar nan , yaranta sunfi karfi su auri talaka , kuma ko da sun auri me kudin ma baza su zauna da kushiya ba
Kullum cikin musu hudubar nan take , wannan *MAUKACIN KISHIN* da Duke da shi da bakin hali da rashin mutunci , a nono suka sha , dan kakarsu ma ba bayaba .
'Yarta ta farko anty sadiya , ta auri alhaji ahmadu ( shine ake kiranshi da alhaji madu ) shahararen mai kudi , ba laifi yana da kudi sossai , babban mutum ne meji da kanshi , yana kasuwanci sossai
Yana fita kasa shan waje saro kaya , iri iri
Yana shaguna masu yawa a cikin garin bauchi ,harda sauran garuruwa ma , me kudi ne sossai
Tun kafin anty sadiya ta aureshi mahaifiyarsu ta kai sunanshi gun malamai , dan a mallakeshi , shiyasa yake matukar musu Barin naira , duk wani abun da tace sai yayi mata shi , har sukayi aure , bayan sunyi aure ne , shurushuru babu alamar ciki bare haihuwa.
Alhaji madu mudu mutum me me matikar San haihuwa , kullum cikin addubar samun 'ya'ya yake , hakan yasa yake tunanin Karin aure .

Tunda anty sadiya ta fuskanci haka batayi kasa a gwaiwa ba takai sunanshi gun malamai, akan a rufe mishi Baki akan maganar haihuwa ,sannan , ayi mata aikin da sai abun da tace , hakan kuwa akayi , alhaji madu baya jin maganar kowa sai tata yan uwanshi ma baya zuwa gurinsu , itama bata zuwa , mahaifiyarshi da mahaifinshi sun dade da rasuwa ,

A haka a haka , anty sadiya taita ta tatsarshi san ranta , har takai tattalin arzikinshi ya karye,
Dan a halin yanzu ta fishi kudi nesa ba kusa ba , dan ta fara business sossai , matukar kaga yanda anty sadiya takema alhaji madu sai kadauka danta ne , dan duk abun da tasashi sai yayi mata shi
A haka rayuwar gidan anty sadiya da alhaji madu take tafiya har iyanxu , da suka kai shekara ashirin da aure babu d'aaa balle jika ,
Rashin haihuwan ita kanta anty sadiya yana damunta amma bata taba nuna ma alhaji madu hakan ba .
Dan shi a halin yanzu ma ya daina maganar kwata kwata yazubama sarautar Allah ido
Haka rayuwar gidan alhaji madu da anty sadiya ta ke tafiya

Sai anty hafsa ta biyu.
Kubiyoni dan jin ya rayuwar gidan anty hafsa take !!!!!!!

*MUJE ZUWA*😎

*GASKIYA IN BANA GANIN RUWAN* *COMMENTS ZAN DAINA POSTING AKAIAKAIBA , *COMMENTS DINKU SHI ZAI* *KARAMUN KWARIN GWAIWAR YIN TYPING*
*AMMA IN BAKWA COMMMENTS ZAKUSA IN KARAYA*

*PLSS I NEEDS YOUR COMMENTS*πŸ‘πŸ‘

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️ (MUM FU AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 13*
Bayan anty sadiya sai anti hafsa , 'ya tabiyu a gidan alhaji Muhammad mai dala ,
Anty hafsa ta auri alhaji muktar tafida , shahararen mai kudi ba laifi , yana aiki a wani babban comapany a garin bauchi
Yanada mata daya mai suna hajiya hajara da yara biyu maimun da rahama ,

Please Login or Register in order to submit comment