Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

.

Aisha tayi murmishi tace " hummm Indan takamarki bokayi toh ni nariga nace Allah kije iyi duk abun da zakiyi jaka .

Aisha na fadin haka takamo hannun mahaifiyarta ,suka Shiga daki tace" in kun gama dabbanci Sai anjima kekuma ta nuna Rukkaiyya da yatsa tace " duk da bansanki ba haukarki yasa nagane cewa kece kishiyata sabida haka in kin koma gida kice ina gaishe da maji dadina wato mijinki , kice his wife to be inshallahu kuma mutu karaba , tanafadin haka tashiga daki taturo kofa jikkake bum.

Rukkaiyya tsabar bakin cikin kalaman Aisha saida wata yar kwalla ta zubo Mata, zuciyarta nayi mata wani irin zafi da kuna, Anti Sadiya ce tayi karfin halin cewa " toh ai sai
mutafi koh .

Jiki a sanyaye suka fito suka Shiga mota suka nufi gida .

Suna cikin tafiya a moto Anti Hafsa ce tace " nifa inada shawara idan kinga daman dauka , Rukkaiyya tace" Anti Hafsa wani shawarane??, Anti Hafsa tace" me zai hana kjiyarda Sadik din yayi auran kinga idan yayi auran mukaje bokanan yayi mana aiki akai kinga ta hakane zaki samu damarda zaki rama abun da tsinanniyar yarinyar nan tayi mana , kijuyasu kamar waina daga karshe kisa Sadik ya saketa Bayan kingama gana mataa azaba , kamar yanda nakema Maimuna da Rahma , ki maida ita tamkar baiwa kikuma dinga Sa Sadik yana ma ta rashin mutunci har tagaji dan kanta tanemi saki da kanta .

Anti Sadiya tace " aikuwa wannan shawarar taki tayi Hafsa kekuma in kinga dama ki dauka .

Rukkaiyya tayi shuru kamar me nazarin wani abun tace" toh yanzu fa sai Sadik ya San wata mace Bayan ni ko ?? Kuma sai ya sadu ita ,waiyyo Allah wallahi Anti bazan iyaba bazan iya ganin Sadik shi da wata mace ba a daki daya balle kuma har wani Abu yashiga tsakaninsu wallahi na gwammace in yake gaban nashi kowama yarasa , Anti Sadiya ranta ya matukar baci tace , wallahi tallahi kinsan Allah daga yanzu na cire hannuna a maganarki in banda shashanci ana ne ma miki mafita kina kawo wata magana daban , to daaa idan anyi auran kallanta kawai zaiyi .

Rukkaiyya tace" toh ai kallanma banaso yayi, Anti Hafsa datake driving tace" Anti Sadiya kinsan miye ? Murabu da ita taje tayi duk abun da taga yafi mata , tunda haka ta zaba , tunda mu mun Gina kanmu ina ruwanmu , idan akayi auran ba nadan lokaci kadan bane , sai ki sa ya saketa , kinga muncuceta kenan ma mun maida ita karamar bazawara , amma in baki yarda ba kije kiyi duk abun da kikaga ya fi miki , nan sukayimata tatas , suka dinga yi mata fada , bacin rai sossai suka nuna mata , nan Rukkaiyya tace" toh na amince kuyi hakuri , Sukace toh daaa karma ki amince din .

Da haka suka sauketa a gida , Anti Hafsa ma ta sauke Anti Sadiya , daganan itama ta wuce gida.


Anti Hafsa na shiga ta kwadama Maimuna da Rahama kira tace" kai ku
na inaa , da Sauri suka karaso sukazo tace " me kuka dafa ?? Maimuna tace" uhmm Anti ,ai bakice mudafa komai ba , kuma kin hanamu Shiga kitchen Indai ba ke kika ce ba shiyasa tunda kikafita babu abun da muka dafa gudun kar ranki yabaci , amma yanzu ki fada sai muje mudafa yanzunan, saukar mari maimuna taji a kuncinta , A hasale Anti Hafsa take fadin , dan ubanku shine kuka barmin 'ya'ya da yunwa kuma kuka barni da yunwa , in banda mugunta aikunsan zandawo gidan ba sai Ku dafamun Abun danafiso ba , sukace eh da farhan da fariha sunci buscuit da bobo sun yi barci tace" toh iya wanan ne zai ishesu , dalla Ku wuce kuje Ku nema mun abun da zanci .

Basukara cewa komai ba da guru suka Shiga kitchen suka fara kokarin girkamata abincin .

Bayan sun gana suka dawo kan dining , Anti Hafsa tace kunsa next week , nusaiba da faruk zasu zo hutu sabida haka ko gyara musu dakunansu sossai , sa nan Ku tanadi abincin da zakuyi musu , cikin girmamawa sukace toh , tayi musu wani kallan banza tace " sai kutashi kubani guri , da Sauri suka tashi kamar zasu fadi kasa , dan tsabar yunwa data gala baitatar dasu , Anti Hafsa ta fuskanci hakan amma mugunta ya hanata ta basu abincin , tashi tayi ta tafi daki ta kwanta tayi barcinta .

Jin ba motsi a falo ya tabbatar ma da Maimuna da Rahma cewa bakowa a falo, da Sauri suka fito kamar marasa gaskiya suka nufi kitchen suka debo sauran abincin suka Shiga dakinsu sukafara ci.

Allah ya taimakesu har suka gama bata tashi ba , sukayi Sauri sukayi wanke wanke suka gyara gurin .


A bangaren Hajiya Rahmatu kuwa Mahaifiyar Alhaji muktar kauyensu ta tafi dan Neman maganin dazai karya asirin da Hafsa tayi a kan danta.

Ba laifi ana mata kokari sossai dan ganin ankarya sihirin dake jikin Alhaji muktar.



*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING.....*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️ (MUM FU'AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 37*

A bangaren Rukkaiyya kuwa bayan tadawo gida ,kaitsaye daki ta wuce.

Bata kula ko 'yayanta ba kwanciya tayi a gado tadinga rusa kuka , kukan da uwarta da ubanta ma sukayi mutu batayi irinshi ba .

Cikin ranta take aiyyana cewa , wai ace mijinta zai kusanci wata ba itaba , ai tana tunawa takara sa wani irin kuka me tsuma rai ,harda shasheka da majina .

Jin Alamar kuka yasa yaran suka shiga dakin mahaifiyarsu dagudu , dan ganin halin da mahaifiyar tasu take .

Suna shiga suka tarar tanata kuka , da sauri khairat takarasa kusa da ita tace " mama lafiya waye yarasu , ai kuwa saukar mari khairat taji a kuncinta .

Rukkaiyya tace"ubanki ne yarasa ,Ku wuce Ku fita Ku bani guri kafin in ci ubanku , tafada cikin masifa ,da dashashashiyar muryarta da ta dashe tsabar kuka .

Ai bashiri yaran suka fita da gudu sukabar dakin .


Ganin kukan da take zaiyi mata illa yasa tayi shuru ta wanke fuskarta, ta kwanta , kan kace me wani zazzabi me karfi ya rufeta .


A bangaren Aisha kuwa bayan sun shigo daki , mahaifiyar Aisha tace" Aisha Anya kuwa zaki auri mutuminan wallahi da Alama matar
nan tsaf zata kashe mutum akan mijinta .

Aisha tace" haba mama kar ki damu inshallahu babu Abun da ta isa tamun , Aisha tafadi hakane Dan kwantar ma da mahaifiyarta hankali , amma kuma cikin ranta ita kanta ta tsorata da Rukkaiya , amma batabari hakan yayi tasiri akanta ba dan kuwa tabarma Allah lamarinta, idan auren ta da Sadik Alkhairi ne Allah tabbatar in ba Alkhairi bane Allah kawo mata mafi Alkahair.

Itama mahaifiyar Aisha hankali ta yadan kwanta , tabi diyar tata da addu,ar zabin Alkhairi .

Ta kuma cema " Aishan karta fadawa mahaifinta sabida zai iya cewa " a hakura da auran Kawai .

Aisha tace " toh mama amma fa saina fadawa Sadik Dan gaskiya tun wuri yadauki matakin daya dace akan matarnan tashi , ko ba haka ba , dan ni banasan tashin hankali , in ba hakaba zan nunar mishi cewa na hakura dashi kawai koh ? .

Mahaifiyar Aisha tace " eh
Hakane gaskiya kan ki fadamishi tun wuri yayi ma tufkar hanci .


Bayan Sadik ya tashi a aiki bai zarce ko inaba dai gidansu Aisha .


Kiranta yai a waya cewa yang kofar gida , ta shaidamai cewa gatanan zuwa .


Fitowa Aisha tayi rai a bace , ganin hakan yasa Sadik cewa lafiya kuwa My .
Aisha tace ina wuni , Sadik bai ansaba yace ni ba gaisuwarki nakeso ba meyafaru naga kin fito rai a bace bayan ba haka kika saba fito min ba , lafiya?

Aisha tace lafiya amma fa ba lau ba , Sadik ya gyara zama yace toh menene?? .

Aisha tace" matarka ta zo gidanmu , Sadik yace matata kuma , Aisha tace" eh, nan Aisha takwashe komai tafadawa Sadik takara dacewa ni wallahi ma har na karaya naji ma kawai in hakura da auranka wallahi bansan tashin hankali ko kadan.

Ace har matarka tayi kokarin marin mahaifiyata tayaya keke ganin hakan zai yuyu , gaskiya kasan abun yi wallahi .

Cire hular kanshi Sadik yayi yace, toh kinsan me zai faru ki shiga gida kawai sai gobe zan dawo Barin je gida .

Aisha tace" nifa bawai na fada maka bane Dan kaje ku samu Matsala da matarka , na dai fada maka ne ,dan kadauki mataki , gudun kar wani Abu makamancin wanan yakara faruwa , shine kawai ,amma kayi hakuri Dan Allah kuyi magana ta fahimta a tsakaninku kaji .

Sadik yace" toh shikenan amma zan tafi yanzu , sai anjima , kuma idan kin shiga ciki ki fada masu mama da baba cewa gobe inshallahu zan turo a kawo sadakin auranmu , bazan iya bari har sai nan da wata daya ba ni zantafi , Sadik na maganar necikin sauri da gaggawa .

Aisha tace" kai gobe fa kace me yasa zaka ce gobe ?? Sadik yace kedai kawai in kin shiga ki fada musu hakan .

Aisha tace" toh shikenan , sai goben,.

Nan sukayi sallama Sadik yaja motarshi sai gida .

Yana shiga , yafara kwalama Rukkaiyya kira cikin kakkausar murya yanafadin Rukkaiyya !! Rukkaiyya !!Rukkaiyya.

Yaran suna zaune a falo, kausar tace " ce , ai tana dakinta ta shigo sai kuka take yi , munshiga muna tambayarta, ta wanka ma yaya khairat mari .

Sadik ba cemusu komai ba Kai tsaye ya wuce dakin Rukkaiyya .

Yana shiga yatarar da ita kwance.

Yace" Rukkaiyya ,yafada da kakkausar murya . tana jinshi tayi shuru , a hasale yace ba magana nake miki ba ?? .

Rukkaiyya ta yunkura ta kwadamai wata harara tace" toh wai uban me zakamun ne dan Allah karka dameni.

Sadik dayaga ma kula yace " abun da kikayi kin kyauta kenan , tace " me nayi , cikin tsantsar rashin kunya .

Sadik yace" barikiji bazuwa nayi muyi hayaniya kina fada ina fada ba , nazo ne in miki kashedi , wallahi tallahi in kikara zuwa gidansu Aisha a bakin auranki.

Kuma kinsan Allah sa,arki daya Aisha tace kar in miki magana da yau tabbas a gidanku zaki kwana, kuma kisama ranki cewa , aure kamar anyi angama inshallahu , kiyi hakuri ko kar kiyi yarage naki

Rukkaiyya tace" hummm lallai Sadik wato yarinya tun bata shigo ba har tafara baka umarni kana bi , toh ai shikenan , Kaje Allah ya isa.

Sadik bai cemata komai ba ya fita a dakin , gudun Kar ya biye mata suyi abun da suka sa saba .

Falo yaje ya yace " khairat kin dafa abinci ne tace " ehh , yace," kawo min inci, da sauri ta debo mishi ta kawo mishi yaci .

Bayan Sadik ya fita kuka Rukkaiyya tasa me cin rai .

Washe gari Sadik ya aika kudi naira dubu dari biyu Sadaki Aisha. ,

Nan aka Kai Sadakin inda a lokacin a ka tsaida ranar biki nan da wata uku .

A San samun Sadik yaso a ce bikin a saka nan da wata daya , amma ganin yanayi karfin iyayen Aisha yasa ya amince Nan da wata uku , bayan yayi alkawarin daukar musu nauyin wasu abubuwan .

A bangaren hashim addu,ar zabin Alkhairi yadingayi inda yaji cewa bazai iya rabuwa da khairat ba , yasama ranshi duk yanda Allah ya kaddara shine daidai .

Shiryawa yayi yatafi gidansu khairat , aikawa yayi aje ayi mishi sallama da khairat ,.

Yaro na shiga yace " wai khairat tazo , Rukkaiyya na zaune a kujera , duk Wanda ya kalli Rukkaiyya sai ka rantse da Allah ta yi ciwon watannin ne , duk ta rame , tsakanin jiya zuwa yau .

Cema yaran yayi inji wa,a ? yace" inji wani a waje .

Rukkaiyya tace " dame yazo ?? Yaran yace akan mashin ne Rukkaiyya takwada wata uban harara tace" jekace bazata zo ba daga yau kar ya kara zuwa bashi ba ita , inji ni kace inji maman khairat din, _Niko nace badai haushiba Rukkaiyya_.


Yaro na fita ya shaidawa Hashim Abun da aka fadamai , shuru Hashim yayi yace inji waa , yaran yace" inji mamanta.

Bayan dan lokaci da hashim yaja yana tsaye daga bisani ya ja mashin din shi yakara gaba.


*A gurguje*
Wasa wasa yau saura wata daya bikin Sadik da Aisha inda duka bangare biyun sunata shirye shirye .


Duk Wanda ya kalli Rukkaiyya tabbas sai ya gane cewa tana cikin wani hali , bata da walwala , kullum cikin kuka take , bata hira da yaranta , hasalima duk Wanda yazo gunta duka take mishi , tazama lamar wata zararriya , bata cin ko abincin kirki ,bata zama a gida kullum itace bin gidan bokaye ko za,a samu mafita , amma babu .

Hakan yasa ta hakura , kullum take zuwa gidan Anti Sadiya ko Anty Hafsa .

Sadik ko baya ma bi ta kanta Dan shi yanata shirye shiryen biki , bai ko damu da Halin da take ciki ba , Dan kuwa a cewarshi ita taso hakan .

Bayanda Sadik ya iya dole ya koya ma rayuwarshi hakura da mace Dan kuwa baya samun biyan bukata a gurin Rukkaiyya .


Sai dai yana iya Bakin kokarinshi wajan kula da yaranshi .


Sadik da kanshi yaje ya dinga hadawa amaryarshi lefe , Inda kai tsaye ya tafi gurin mum irfaan dan hadama amaryarshi lefe , ,dan kuwa kayan mum irfaan akwai sauki sossai ga kayau ga inganci , uwa uwaba bata tsawalla wajan cika kudi a kaya, takalma atamfofi ,jakunkuna, dogayen riguna, laces da sauran kayaiyyakin mata koda mum irfaan tafara curo ma Sadik kayaiyyakin saida Sadik yasha mamaki , yadinga murna yanafadin, basaina je kasuwa siyo kayan lefe ba nan ma ya isa godiya yadinga yi ma mum irfaan, dan kuwa bakaramin dadi yaji ba dan ganin kayan da mum irfaan ta hada mishi , ga kuma saukin kayan, bayan yagama hadawa amaryarshi , nan yafara hadawa uwargidanshi wato Rukkaiyya, itama kaya musu kyan gaske ya siya mata.

Ku tuntubi wannan number domin siyen kaya mai kyau da kuma arha Ku tuntubi wanann number.
08130515037,.

Domin tun tubata Dan yi muku talla zaku iya nemana ta wanan layin 09066386347


Bayan Sadik ya je ya siyo kayan lefenshi , bai zarce dasu ko inaba sai gidan Hajiya.

Nan fa Hajiya takira yan uwanta dan ganin kayan da Sadik yasiyo a gun mum irfaan kowa yaga kayan sai ya matukar yabawa da kyansu tsabar kyan kayansu ga kuma sauki da arha , mutane sai santin kayan sukeyi

Bayan ya bar gidan Hajiya , gida ya wuce Dan kaima Rukkaiyya nata.

Yana zuwa dakin Rukkaiyya yashiga yasameta kwance , baice komai ba ya jiye mata kayaiyyakin yayi , yace" ga kayanki nan nafadar kishiya .

Ball Rukkaiyya tafarayi , da sauri taga wasu takalma da shaddodi da atamfofi dogayen riguna da jakunkuna , da lace da Sauri ta tsagaita ball din da takeyi dasu .

Duk da halin bakin cikin da take ciki bai hanata jin dadin ba ganin kayan mum irfaan da ta yi , tsabar kyan kayan bata san sanda tafara harhadi kayan ba tana kallo, cikin jin dadi .

Sadik yace , ke haushin yatafi kenan , harara ta kwada mishi , baice komai ba yatafi abunshi, yabar Rukkaiyya nata kallo tana santin kayan.

A bangaren Amarya Aisha kuwa ........


*MUJE ZUWA NAGAJI YASIN*πŸ€ͺ

*MORE COMMENTS😎😎😎*
*MORE TYPING...*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️( MUM FU"AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 38*

A bangaren Amarya Aisha kuwa , mahaifin mamanta ya tsaya mata sossai da addu,a yakuma bata wasu addu,oi sossai da za ta dingayi .

Wajen gyaran amarya kuwa Aisha na shan gyara , Dan kuwa wajen gyara ba ,a magana , mum irfaan aka barma ragamar gyaran Aisha Amarya .

Mum irfaan na gyara Aisha kamar me ,da kaya masu inganci da kyau , wajen shan maganin sanyi wato infection Aisha batayi sanya wajan sha ba dan kuwa yana karewa mum irfaan zata kawo mata wani tasha , shiyasa Aisha take jinta ko ina daidai , dan kuwa maganin sanyin mum irfaan sadidan ne yana da matukar kyau .

Bayan mum irfaan tagama hada amarya sossai da ingantaccen maganin sanyin batayi sanyi gurin , hadata da kayan mata masu kyau da inganci .

Dan kuwa tsabar kyan kayan matan mum irfaan Aisha har zuba takeyi tsabar ruwan ni imar dake jikinta .

Bangaren dilka kuwa , ba,a magana Aisha tasha dilka , jikinta sai kyalli da sheki yake kamar zaka taba jini ya fito Dan kuwa bakaramin kyau Aisha tayi ba , .

Abuwan da mum fu,ad na hadama Aisha wajan hada dilka sune.
Kurkur jaa da yellow , amma na gwangwami original
Sai Ajino , sugar , nescafe , lemon tsami , kwai danye , amma banda york din ciki wato kwaiduwan iya ruwan kwan ake bukata , sai madarar ruwa ,madarar turare , lallen gargajiya , da lallen sajen , sai kuma garin dilka da turaren , dilkan, Wanda za a turare jiki bayan gama dilkan dakuma turaren tsuguno .

Duk Wanda yaga Aisha sai ya yaba Dan bakaramin kyau Aisha tayi ba , shi kanshi sai da Sadik ya yaba da kyan da amaryarshi tayi , godiya yadinga yi ma mum fu'ad dan kuwa bakaramin dadi Sadik yaji ba ganin kyan da Amaryarshi tayi .


Bayan kayan mata da mum irfaan ta hada mata mum fu'ad bata bar Aisha haka ba dan ganin ta gyarama Sadik Amarya , nanfa tadinga harhadamata abubuwan karin ni ima wa inda ta hada da kanta , ta dinga dirkawa Aisha tana sha , Aisha ko har ta gaji da shaye shayen magunguna .

Kaya Sadik ya je ya siyo ma su khairat , da zasu sa na fitar biki , duk da yasan cewa Rukkaiyya zaiyyi wuya tayi wani taro , yadai siyo musu ne kawai .

Aikuwa Sadik na fita Rukkaiyya ta karbi kayan a gun yaran ta yaiyyagasu ta watsar a shara ,kaya musu kyauda tsada , takuma cema yaran duk Wanda ya sake yafadawa , babansu sai ta ci ubanshi ta mai tsinannen duka.



Wasa wasa yau biki saura sati biyu , Inda naga members din group din mum fu'ad fans club sunje gidan Rukkaiyya sunata mata dannan kirji , amma fa na gulma cikin ransu kuwa sunata taya Sadik murna ne.

Aikuwa Rukkaiyya tace"toh munafukai ba kun iya munafurci ba , ba harda Ku a murna dan Sadik zai karo min kishiyaba , dallah kutashi kubarmin gida tukafin ranku ya baci.


Da sauri su ka tattare cikin borin kunya da sanyin jiki suka baro gidan .

gidansu Aisha suka tattara suka tafi dan ganin Kyan da tayi domin suyi tsaigumi .

Suna zuwa sukaga Aisha kamar ba yar Nigeria ba tsabar kyan da tayi , bayan sun dan ba Aisha shawarwarin zama da miji da kuma kishiyarta suka tafi abinsu .


A bangaren gidan Anti Hafsa kuwa , yaranta sun dawo daga hutu, Nusaiba da faruk , ba laifi yaran basa nuna ma su Maimuna tsana ko tsangwama , suna sansu sossai , dan , wani lokaci ma har zuwa dakinsu Maimuna suke suta hira .

Zuwansu Nusaiba hutu yasa su Maimuna farin ciki dankuwa ko ba komai yanzu suna dan cin abinci akai akai, dan watarana Nusaiba dakanta zata shiga kitchen ta debo musu abinci dayawa suci da su Maimuna har sai ta tabbatar sun koshi , wani lokaci a boye take debowa wani lokaci da sanin mahaifiyarsu .

Duk yanda Anti Hafsa tayi Dan ganin ta zasa ma yaran tsanar su maimuna hakan baiyi tasiri ba , Dan kuwa jini daya bawasa ba , hakan kuwa na matukar bata mata rai .

Wataran taita cema yaran ai su Maimuna Yan aiki ne sudaina rabarsu amma hakan baya taba tasiri domin kuwa tun suna kanana suke sansu .

Domin sansu a jininsu yake , har aka kaisu school din kwana wato boarding school .

Su farhan da fariha su kam dai bawani san su maimuna suke ba , dan Hafsa bata taba bari su rabesu , a cewarta sakacin datayi kenan har Nusaiba da Faruk suke sansu , dan kuwa zunsha wahala dasu shiyasa.

kullum nuna musu zallar kiyaiyyar da take musu take .

Shiyasa yaran basu taso da sansu ba .



Yau saura sati daya bikin Sadik inda ya kawo ma Rukkaiyya invitation card din aure yace"gashi ya Ciro invitation card din yace ki rabama yan uwa da abokan arziki .

Sanan inaso ki fadamun me dame kike bukata na hidimar biki .

Wani

Please Login or Register in order to submit comment