Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita.

Da sauri wata matar layin takaraso gun Rukkaiyya tace " haba maman kausar meyasa kike hakane , kiduba inda kika tara mutane a layi a nata kallanki, ke ko kunya bakyaji , ni nsan Alhaji Sadik bashi da laifi , Rukkaiyya kece fitinanniya .


Aiko Rukkaiyya tace " munafuka ina ruwanki , ke akasan me kukeyi da naki mijin , munafuka , fita kibarmin gida in banda munafurci ke bakiga abun da yamun bane amma tsabar makirci kina wani Goya mishi baya har kina wani cewa kinsan bai da laifi , to sai kije ki kashe auran ki mana kizo ki aureshi , wayasan ma ko kedin kwartuwarshi ce da kike goya mai baya.

Murmishi matar tace" banyi mamaki da jin haka ba daga gareki ba , dan nasan *MAHAUKACIN KISHIN* da kike yasa kin haukace bazan tsaya biyena mahaukaciya irinki ba , matar da ubanki ma bakuwa wanye lafiya dashi , ga banzar turbar da uwarku ta saku mijinki ma kin yi dashi balle kuma mu makwafta , hummm tir da irin wannan hali naki jaka kawai , kidai ji da abun da yake damunki matar na fadin haka ta fita,.

Da sauri Rukkaiyya tace" dawo mana wallahi da yau sai kinsha mamaki, matar bata dawo ba tayi tafiyarta , cikin bacin rai .


Manafukan gurin hakuri suka dinga ba Rukkaiyya suna zagin Sadik dan sun fuskanci Rukkaiyya matukar zaka zagi mijinta kabashi rashin gaskiya to fa zaki zauna lafiya da ita , itakuma ka tausayamata , dan in dai kace zaka fadamata gaskiya wajan bata rashin gaskiya toh fa ananne zaki mugun samun matsala da ita ba kadanba, hakan yasa yangulma suta zagin Sadik sunacewa bai kyauta ba Rukkaiyya na haka taita tsinemsi tana batashi a gun jama,a Wai zai lalata khairat , *Wa iyazubillah*.

Kausar na gun khairat tanata mata fiffita tana zuba mata ruwa wani dogon nishi taja ta bude idanta .

Sai yanzu mutanen da suka lura da khairat da take kwance a kasa duk fuskarta ta kunbura .

Da sauri wasu sukaje suka dagata ,suka shiga da ita daki , sukace da kausar ta debomata kaya tasa tadansha maganin , haka kausar ta dan kawo mata paracetamol tasha dakyar tasa kaya ta kwanta .

Bayan Sadik ya fitane cema makwafcinshi yayi bari yaje ya hado ma khairat magani .


Daki Rukkaiyya ta shiga tafara shirya kayanta , tana gama bata dauki ko wani yaro ba ta fita sai gidan Anty Sadiya.

Gidan Sadik ya shiga yaje ya duba jikin khairat , lokacin har khairat barcin wahala yayi awun gaba da ita , ya kalli yar Tashi cikeda tausayi ya girgiza kanshi ya dauki keyn mota ya fita, kafin yafita yacema kausar ta daura musu abinci kafin yaje yadawo ,dan wannan karan yace bazai kaisu gidan hajiya ba.

Gidan Hajiyanshi yanufa yake sanar mata da abun da Rukkaiyya tayi , salati Hajiya tafara , tace",toh yanzu ina khairat din ??.

Sadik yace" tana gida a kwance.

Hajiya kam bata komai ba tace " Allah ya kyauta , amma ai da baka saketa ba ka yanke hukunci cikin gaggawa , da kayi hakuri .

Sadik yace kai ina Hajiya bazan iya cigaba da daukan cin mutunci Rukkaiyya ba Hajiya garama kawai da na rabu da ita .

Hajiya tace " toh kayi hakuri kaje ka dawo da ita , Sadik daya fusata yace Hajiya , Hajiya ta amsa tace na am !!yace Hajiya kiyi hakuri bazan iya zuwa ba wallahi kiyi hakuri , Hajiya tace, toh shikenan daga baya in tadan kwana biyu sai kadawo da ita , shuru kawai Sadik yayi bai bada ansa ba yafita .


Da kuka Rukkaiyya tashiga gidan Anti Sadiya, Anti Sadiya na kallanta tace kekuma miye haka lafiya , Nan Rukkaiyya takwashe karya da gaskiya tafada mata .

Anti Sadiya tace " wanna yar iskar yarinya , ita kullum itace sanadin fadanku da Sadik duk fada sai sunanta yafito a ciki , toh Allah ya kyauta ai sai kiyi zamanki anan har Allah ya kawo miki wani ,ko kina San komawa gidan tsohon mijinki idan komai ya daidaita ??

, Rukkaiyya tace " tab wallahi Anti ni da gidan Sadik har abada , anti Sadiya tace" toh shikenan .


Bayan kwana biyu khairat taji sauki sossai , tana samun kulawa daga bangaren mahaifinta , itama tana bama kannanta kulawa tamkar mahaifiyarsu .



_________________________

A kwanan a tashi ba wuya yau wata biyar kenan da barin Rukkaiyya daga gidan Sadik , inda Rukkaiyya tana samun zawara bayan tagama idda wasu da iskanci wasu da Santa da aure, duk da mutane sun San halin rashin mutuncinta, shiyasabduk Wanda ya fito da niyyar auranta idan yasamu labarinta da tarihinta da dalilin fitowarta a gidan mijinta , sai ya fasa,.


Mutane biyu ne sukace sunji sun gani zasu iya , amma sudinma ba mutanen kwarai bane.

Babu yanda Rukkaiyya ta iya tace dayan ya turo ,amma zuciyarta ta mutukar karkata da tsohon mijinta , har ga Allah tana matukar San komawa gidanshi amma ya zatayi .


Gashi gidan Anti sadiya ma ba dadi take jiba , kullum cikin fada suke , ga gorin da Anti Sadiya take mata , hakan ne ma ya kara daga ma Rukkaiyya hankali.


Bayan sati daya , a ciki satinan kullum sai Rukkaiyya ta kira Sadik amma ina yaki ya daga wayan duk hankalinta yatashi , kiran duniya tayi ma Sadik amma yaki dagawa .

Bayanda ta iya ta hakura ta yanke shawarar cema dayan bazawarin nata ya futo kawai .

Amma fa ba a San ranta ba ,


A bangaren Sadik kuwa dole ya hakura da mace duk da yana tsananin bukatar mace amma babu yan da ya iya , shiyasa yafara azumi kawai, har yanzu baiga wacce ta kwanta mai ba ,balle ya aure.


Yau saura wata biyu auren Rukkaiyya , duk abun duniya ya isheta kullum sai ta kira Sadik daga karshema ,Sadik din blocking dinta yayi da ta dameshi .

Rukkaiyya duk ta rame ,ga Wanda takeson aura bata taba samun abun da take bukata daga gurinshi , duniya duk ta mata zafi .

Tunanin kiran Hajiyan Sadik tayi da taroketa tasa Sadik ya mayar da ita dakinta .

Nan ta fara kokarin kiran layin Hajiya bugu biyu hajiya ta dauka tace " Rukkaiyya kece! .

Rukkaiyya tafashe da kuka tace eh nice Hajiya , Hajiya dangirman Allah kidubi Allah kidubi Annabi Hajiya kisa Sadik ya maidani dakina Hajiya.

Hajiya kiyi hakuri wallahi tallahi Hajiya na tuba bazan kara ba .

Hajiya da dik tagama jin tausayin Rukkaiyya tace " shikenan Rukkaiyya kiyi hakuri zansan abun yi kinji .

Rukkaiyya tace" toh Hajiya nagode ,tafada cikin sanyi murya , ta kashe wayar , gwani ban tausayi .

Bakaramin damuwa Rukkaiyya take ciki ba dan a halin yanzu ma Anti Sadiya tace" takusan dena bata abinci ,garama ta nemi miji tayi auren.

Haka ta tattara ta koma gidan Anti hafsa itama gidan ba dadi take ji ba.

Ba yanda ta iya haka ta dawo gidan Anti Sadiya dan hakan shine yafi .

Bayan kwana biyu Hajiya tasamu Sadik da maganar dawo da Rukkaiyya, nan Sadik ya tubure yaki yarda, dakyar dakyar Hajiya tadan shawo kanshi , yace" toh zaiyyi shawara .


Har ga Allah shi kanshi yana matukar San dawo da matarshi ko dan 'ya'yanshi amma halinta yake ji , Sam bata da halin ko kadan .


Tashi Sadik yayi ya tafi gida , yana zuwa yatarar yara suna kallo , duk Wanda ya gansu yasan suna cikin fadin ciki ,dan khairat harwata yar kiba tayi , dama sauran yaran sunyi kyau sunyi kiba , in ka gansu baza kace ba babu uwa A tattre da dasu ba , ko dayake ai gara ba uwar ma ,tunda gashi rashinta ma sunfi samun kwanciyar hankali .

Sadik ne ya zauna yace. Yarana , yaran suka kalloshi sukece na,ama.

Yace kufadanun gaskiya kunaso in dawo da mamanku ??? Nan yaran suka fara kallan kallo .

Kausar tace A,aa baba .
Kahairat tace " eh baba kadawo da ita duk tsiya gara ace muna tare din ,kaga baba idan zaka kara aure bamusan wacce za ka kawo ba , kayi hakuri kawai ka dawo da ita .

Sadik yace " toh shikenan Allah ya miki Albarka suka ansa da Ameen .

Washe gari Sadik ya koma ya sanar mata da cewa ya amince Rukkaiyya ta dawo amma bisa sharadin zadaina duk wani mugun halinta .

Hajiya tace eh zata jamata kunne.


Kara kiran Hajiya Rukkaiyya tayi taji ko ya ake ciki , nan Hajiya ta shida mata cewa Sadik ya yarda ta dawo murna gun Rukkaiyya ba a magana nan Hajiya takara mata nasiha sossai , nan Rukkaiyya tayi shuru kamar nasihar tashiga jikinta .

Kiran Rukkaiyya Sadik yayi a waya bawani dogon magana yace" ki shirya zan aiko da Sadaki kuma za a daura auren a satinan .

Rukkaiyya tace"toh wait har yanzu baka huce bane, naji muryarkw haka.,??

Sadik yace na huce mana kidai shirya din, yana fadin hakan ya kashe wayar.

Rukkaiyya tace"oho tunda zaka mai dani dakina fushinka bazai dameni ba , taja dogon tsaki .



A yaune aka daura auran Rukkaiyya da Sadik a karo na biyu , basuyi wani taro ba mutane kalilan ne suka halacci gun daurin auran .

Ana gama daurawa kowa ya watse.

*Muje zuwa*

*Indai naga bakwa comments sossai sai na Dade banyi typing ba*

*Sannan Ina kara fada nakusa na dai posting a group din dabasa comment*

*MORE COMMENTS*😎😎😎.
*MORE TYPING....*✍️✍️✍

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️ (MUM FU'AD*)

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 35*

Bayan kwana biyu Rukkaiyya ta tare a gidan Sadik .

Wannan karan da murnarta ta tarbi yaranata , suma yaran sunji dadi ganin canji daga mahaifiyarsu.

Yau kusan sati kenan da dawowarta amma Sadik bai sake mata fuska ba hasalima ko hira ba ya yi da ita balle kuma wani abu na aurataiyya yashiga tsakaninsu .

Duk da matsananciyar sha,war dake damunshi , amma ya daure ,dan yayi niyyar matukar ba Rukkaiyya bace takawo mishi kanta toh yayi Alkawarin bazai je ba .


Abun ya matukar fara damun Rukkaiyya, hakan yasa ta yanke shawara zuwa gurinshi taji dalili sauyawarshi , dan bai taba mata irin wannan fushin haka ba duk irin fadan da suke yi .

Dakinshi tashiga ta tarar dashi yana zaune da boxers da kuma singlate kusa dashi taje tafara magana tace" Dan Allah mijina kayi hakuri komai ya wuce, nan fa tafara mishi kalamai masu dadi da sanyaya zuciya , da fada sha,wa yanayin yandatake dole yadaga hankalin duk wani Namiji me cikakkiyar lafiya , tanayi tana tsarashi har Sadik yadan sakko .

Nan fa Rukkaiyya tafara amfani da kwarewarta wajan sarrafa mijinta , nan danan hankalin Sadik ya tashi dama kiris yake jira , Nan fa yafara mayar mata da martani cikin wani irin salo.

_nikam na tattara inawa inawa na baro dakin_.


Bayan wasu watanni, Rukkaiyya tadan canza ba laifi , da Dan sauki masifan sai abun da ba a rasa ba , amma fa bawai har zuciyarta ba dan kawai tana tsoron kar Sadik ya kara koranta shiyasa take dan kiyayewa .

Sadik ne akan hanya zai tafi gidan Hajiya , hango Aisha yayi sanye da katon hijabi , gwanin sha,wa farace yar doguwa bata da jiki sossai , bai yi mata magana sanin cewa ba mutunci bane tsaida mace a hanya ba ya dinga binta a mota a hankali har yaga gidansu .

Bayan tashiga ne ya aika yaro yace a je ayi mishi sallama da wacce ta shiga gidan .

Nan yaro yashiga gidan yace wai wacce ta shigo nan yanzu ana sallama da ita.

Aisha da mahaifiyarta dasuke zaune tace " inji wa yaran yace " wai inji wani .


Mahafiyar Aisha tace" jeki ki gani .

Nan Aisha tasa hijab tafita .

Murmushi dauke a fuskar Sadik yace baiwar Allah nine ai nake sallama .

Karasa Aisha tayi tace " toh gani Allah sa lafiya .

Murmishi Sadik yace gaskiya kinmun satane , Aisha tace" nashiga uku sata kuma ni a ina na sanka me kuma na satanmaka .

Sadik yasa dariya yace" zuciyata mana .

Aisha tasa dariya tace hummn ana sace zuciyane ?? Sadik yace sosaima gashi kuwa kinsacemun tawa zuciyar , yakara da cewa , a gurguje dai ni sunana Alhaji Sadik ni haifaffen nan ne gaskiya ina ganiniki naji kinyi mun kuma ina matukar San mallakarki a matsayin mata , kuma da gaske neke .

Sanin cewa ba mutunci bane tsaida mace a hanya shiyasa na biyoki har gidan fatan banyi laifi ba .

Aisha tayi murmishi tace toh bakayi ba Allah tabbatar mana da Alkhairi .

Sadik yace kin amince kenan ? Cikeda kunya Aisha tace " hummm ,Sadik yace humm me ??Aisha tace" na Amice tafada a dan kunyace .

Sadik yayi farin ciki sossai da rashin shan wahala wajan samun soyaiyyar ta dakuma yanayi kunyar Aisha dan ya San mace me kunya.

Yace" sorry na manata ban fada miki ba inada fa da mata dayara biyar .

Aisha tace " ai a hakan??Sadik yace ehh ko kin jante ra ,ayinki ne akan bukatata .

Tace " A, idan Allah ya kaddara kai mijinane ai ko a ta hudu ne sai ka aureni kawai dai ba mecewa kanada mata bale ma yara , jikinka bai nuna hakan ba .

Sadik yayi murmishi yace a haba dai fada dai kike Aisha tae" wallahi da gaske . nan Sadik yace nagode.

Suka Dan kara taba hira daga bisani sukayi sallama , bayan Sadik ya karbi number wayanta .

Aisha na zuwa ta shaidama mahaifiyarta abun da yafaru addu a taimata tace" Alah tabbatar da Alkhairi .

Bayan kwana biyu soyaiyya mai karfi ta kullu tsakanin Sadik da Aisha , suna gudanar da soyaiyyarsu cikeda kulawa da kaunar juna .

Dan har ta kai kunnen manya Inda iyayen Aisha since Indai ya shirya yafito ,Sadik yai na,am da abun .

Nan ya sanarma da Hajiya da mahaifinshi halin da ake ciki ,sunkuma yi matukar farin ciki da hakan .

Amma bai sanarwa da Rukkaiyya ba dan mahaifinshi ya hanashi yace sai komai ya kankama kafin matarshi tasani gudun kar akarayin ta wancan lokacin .

Yakumace ma Sadik dinma kar yafadawa kowa Dan idan mutane sukaji toh fa zai iya komawa kunnen Rukkaiyya.

Duk wannan abun Rukkaiyya bata San komai ba gameda neman auran da mijinta yakeyi .

Anti Sadiya ce takirata a waya tace tazo tasamu .

Cikeda fariin ciki Rukkaiyya tace "toh ganinan zuwa ,shiryawa tayi ta tafi tace ma yaran Idan babbansu yadawo suce basusan Inda taje ba idan ta dawo zata San me zata fada mishi, sukace toh .

Gidan Anti Sadiya taje , nan Anti Sadiya take shaidamata ansamu wani hatsabibin boka da yake aiki dakyau .

Cikin farin ciki Rukkaiyya tace" toh yaushe zamuje ,kunga Ku gara Ku bakuda matsala nice nakeda matsaloli sossai , wallahi .

Anti Sadiya tace" eh bari Hafsa tazo idan tazo sai mu tafi , Rukkaiyya tace " toh shikenan .

Jim kadan sai ga Anti Hafsa, da sauri suka shirya suka tafi gun boka .

Nan boka yayi bige bigenshi ya gano cewa matukar ba aure Sadik yayi ba Rukkaiyya bazata taba iya juya shi ba .

Amma idan akayi auran to fa har amaryarshi sai ta mallaka.

Rukkaiyya tashin hankali tashiga , tace" ina bazata iyaba indai sai mijinta sai yayi aure , ta hakura da juyashin .

Boka yace" toh shikenan ,

Haka suka dawo gida cikin jin haushin rashin nasarar da basuyi ba .


Yau saura wata data Sadik yakai Sadik kuma yanaso yana kaiwa ayi maganar aure cikin gaggawa , hakan yasa ya yanke shawarar fadama Rukkaiyya maganar auran shi da Aisha , bayan ya nemi shawarar mahaifinshi .

Mahaifinshi yace" eh zai iya fadamata dan gudun kar tace ba a mata adalci ba kuma gudun bakin mutane kar suce bakayi adalci ba , kafadamata din zamuyita addu,a .

Zaune Rukkaiyya take akan kujera da yaranta suna kallo .

Shigowa Sadik yayi yace" kai kubamu guri zamuyi magana , yaran suka amsa da toh , suka tashi suka tafi dakinsu .


Sadik ne yace Uhmmm Rukkaiyya kinajina , Rukkaiyya ta tattaro ilahirin Nutsuwarta tace " eh inaji menene??

Nan Sadik yace" zankara Aurene .

Gaban Rukkaiyya yafadi jikake ras ai kuwa ta kunduma ihu tafara zage zage tun sunayi a daki har suka fito tsakar gida.



*TOH MASU KARATU WANNAN KENAN ,KUNJI WAYE RUKKAIYYA WAYE KUMA SADIK*


*KUBIYONI DAN JIN CIGABAN LABARIN*

*TAKU HAR KULLUM MUM FU'AD CE*

*MORE CIMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING....*✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 36*

*GODIYA TA MUSAMMAN GAREKU MASU YAWAN YIN COMMENTS INA MATUKAR JIN DADIN YANDA KUKE DOGON SHARHI AKAN LITTAFIN NAN , SI WA INDA BASA COMMENT KUNCI DARAJAR WA INAN MUTANENπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺπŸ€ͺ DA BAZAN DINGA POSTING SOSSAI BA*πŸ‘‡πŸ‘‡πŸ‘‡

*MAMAN HAJJA*
*AISHATU YUSUF (MAMAN AFFAN)*
*AISHA MUHAMMAD*
*MUM TASNEEM*
*MAMAN NANA*
*UMMU AJMAL*

*INA MATUAKAR JIN DADIN YANDA BAKWA GAJIYA DA MUN COMMENT A DUK PAGE DIN DANAYI POSTING. SABIDA HAKA INA MIKA SAKON GAISUWATA GAREKU ALLAH YASAKA DA ALKHAIRI , DA DUK WANI WANDA YAKE KARATUN LITTAFIN MAHAUKACI KISHI , LUV U ALL*

Duk wata hanyar da Rukkaiyya tabi dan ganin aurenan bai yuyuba abun yaki .

Duk inda akayi mata kwatacen shahararren boka sai taje amma duk magana daya ake fadamata nacewa , sai dai ta hakura ayi auran .

Hakan yasa ta yanke hukunci neman gidansu Aisha tayi musu rashin mutunci , haka yasa tadinga kokarin wajan nemo gidansu Aisha, har aka samu wacce tasani , hakan yayi matukar sanya Rukkaiyya farinciki matuka , dan ba karamin wahala tasha ba kafin a gano gidan , dan dabara tayi Ta bigi cikin wata a dangin su Sadik harta fadamata.

Washe gari Rukkaiyya ta shirya bata zarce ko inaba sai gidansu Aisha, bata fadama kowa inda zataje ba , Sadik na fita itama ta fita.

Gidan Anti Sadiya ta fara nufa dagacan sukayi gidan Anti Hafsa, suka nufi gidan su Aisha.

Dan tunda Rukkaiyya ta gano gidansu Aisha takirasu akan suzo ta gano gidansu Aisha , nan sukace sunanan zuwa zasuje su musu rashin mutunci .


Shiga gidansu Aisha sukayi cikin takun kasaita da tsantsar rashin mutunci , dukkaninsu daukeda bakin glass a idanuwansu , suna taunar cingum , suna karema gidan kallo suna zub da yawu , suna hura hanci hadeda toshewa kamar sunga sabon kashi .


Mahaifiyar Aisha datake zaune tana tsintar wake tace" Bayan Allah lafiya ?? .

Anti Hafsa tayi caraf tace" kinga Alamar lafiya a tattare damu ?? .

Wai Inbanda San abun duniya da tsaurin ido irin na talaka , kidubemu ki kallemu da kyau mun miki kama da wa inda zaki so ki hada ' yarki kishi damu ???.

Mahaifiyar Aisha tace" eh gaskiya Alama ta nuna hakan , dan kuwa rashin mutunci da rashin tarbiya ya baiyyana karara a fuskarku naga alamar hakan , duk yanda akayi baku fito gidan tarbiya ba .

Da Sauri Anti Sadiya tayi caraf tace " ke matsiyaciya karki kuskura kiyi gangancin barin diyarki ta shigo gidan yar uwarmu in ba hakaba zakiyi kuka da idanki wallahi .

Mahaifiyar Aisha , duk da ta tsorata da kalaman su amma hakan baisa taji Shakar fadamusu magana ba tace" kunsan Allah hakan da kukayi shine ya bani kwarin gwaiwar barin yata ta auri Sadik duk da cewa , bakuda da mutunci da tarbiya hakan bazaisa naji na karaya wajan barin yata ta auri Sadik ba, dan Baku isa kuyi mata abun da Allah bai mataba .

Da Sauri Rukkaiyya ta yunkuro zata wanketa da mari .

Aisha da take daki tana kallansu tana jin duk abun da suke fada tazo da Sauri ta rike hannun Rukkaiyya ta sauke kasa

Tace" kee ba bakida hankali ne , zan jure komai amma banda cin mutunci mahaifiyata , in banda sakarci , kizo har gidanmu kuma kiyi kokarin Marin mahaifiyata kuma a gabana , wallahi tallahi kinyi karya , idan kin saba zuwa gidan mutane ki ci musu mutunci toh nikam karyarki tasha karya wallahi ,dabba wawiya kije ki gama koyan karatun zama da miji da mutunta juna dakuma sanin yakamata da sanin darajar mutane bawai kizo kina dabbanci a gidan mutane ba .

sannan hakan da kikayi wallahi tallahi bazaisa in ji na fasa auran mijinki ba , bakinyi hakan bane domin in janye kudirina akan auran mijinki , toh barikiji , wutar sanshi ma kika kara ruramin a cikin zuciyata wallahi , kuma a inda nakeji , zan zauna a gidan Sadik ko da taburma za a kaini .

Aisha tana magana cikin zafin rai da kunan zuciya da Bacin rai , da rashin tsoro da jajircewan da ita kanta batasan tanada shi ba .

Aiko Rukkaiyya ji Aisha ta ambaci San mijinta yasa zuciyarta kamar ta fashe , tace" toh wallahi tallahi in kika shigo gidana sai dai uwarki ta haifi wata

Please Login or Register in order to submit comment