Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna zaune cikin farin ciki da kaunar juna, suna son junansu ,
Maimuna da rahma 'yan mata ne sunyi karatun su ba laifi a halin yanzu suna kan yin degree dinsu a( ATBU ) dukkansu suna 200 level.
Mahaifiyarsu ta basu tarbiya iya gwargwado , dan hajiya hajara mace me mutunci da sanin yakamata , abin duniya bai rufemata ido ba yasa ta shagala ,
Iya kokarin ta tanayi dan ganin yaranta sun samu tarbiyya mai kyau ,
Kullum cikin musu nasiha takeyi akan su zama mutane na gari , kar abun duniyar mahaifinsu yadinga rudansu , yaran suna jin nasihar da mahaifiyarsu take ba laifi , suna iya kokarinsu dan ganin sun kaucewa duk wani abin da zai yi sanadin lalacewar tarbiyarsu , ba laifi yaran sunada tarbiyya sossai , abin duniyar mahaifinsu baisa sun shagala ba ,

Kwatsam alhaji muktar yayi tozali da anty hafsa , agurin wani babban super market sunje siyaiyya , tunda ya ganta yaji duk duniya bai abun da yakeson mallaka kamarta ,
Ashe itace ,sanadin tarwatsewar farin cikin shi
Alhaji muktar yaje ya samu anty hafsa , suka yi magana da ga bisani ,ya karbi numbernta ,
Anty hafsa tayi matukar jin dadi , da tw hado da alhaji muktar, domin zuciyarta ta matukar kamuwa da sanshi , dan tayi alwashin duk yanda zata bi sai ta bi ta aureshi , domin ta ganshi ba laifi , ga kuma uwa uba akwai naira , hakan yasa taji takara sanshi sossai , cikin ranta
Dan ko da alhaji muktar yw bijiro mata da kudirinshi bai sha wani wahala ba , dan bata wani jamishi aji ba dan takamu sossai.

Bayan alhaji muktar ya je gidan su yasameta ,ya fada mata kudirinshi , akan da gaske yake auranta zaiyyi , sannan ya shaida mata yanada mata da 'ya'ya biyu,
Tunda alhaji muktar ya fada anty hafsa cewa yanada mata da yara haknkalinta , ya matukar tashi , dan fuskarta ya nuna alamar haka
Alhaji muktar ne ya dubi yanayinta , yace , yadai fatan hakan bazai sa ki juyamun baya ba , nayi miki alkwarin rike amana,
Anti hafsa tayi murmushin yake tace haba alhaji ai badamuwa wlhy , Allah ya hada kanmu yaba ka ikon adalci a tsakani _niko nace_kamar gaske_
Allah yasani in tace batasan alhaji muktar tayi karya , dan tana matukar sanshi ,
Alhaji muktar yayi farin ciki da jin maganar hafsa , dan yasa a ranshi yasamu matar kwarai .

Anti hafasa kuwa tana shiga gida ta sanarwa da mahaifiyarsu cewan alhaji muktar Nada mata harda yara biyu, hajiya amina bata ji dadin hakan ba , amma ganin' yarta naso hakan yasa tayi na am da abun, dan itama tana so 'yarta tashiga gidan daula ,
amma daniyar cewan sai su mallakeshi tun kafin ta shiga gidan , sannan duk hanyar da zasubi sai sunbi dan ganin sun raba matar alhaji muktar da gidan, domin bazata taba zama da kishiyaba , dan suna gani sunfi karfin su zauna da kishiya ,
hajiya amina ta kai sunan alhaji muktar gun bokansu da yake mata aiki, ta fadi bukatarta ,akan a mallake alhaji muktar, sannan kuma duk yanda za ayi ayi dan ganin matar ta bar gidan , boka yace , ba ta yanda za ayi matar alhaji muktar ta bar gidan sai dai , amma in har aka samu aka mallake alhaji muktar, bakin cikin yanda rayuwar gidan zai kasance hakan zai sa ta bakin ciki har yayi sanadin rayuwarta , hajiya amina da anti hafa sunyi matukar farin ciki da hakan , suka amince da hakan.

Alhaji muktar yana zaune a office yaji yana matukar san ganin hafsa , bayan yaje gunta ne yake shaida mata cewan yana so ayi abun cikin gaggawa da ya matsu ya ganta a dakinshi kuma yana a cikin wata daya a gama komai ,
Anti hafsa taji dadin hakan, kuma hakan alamace ta cewan aikin boka na aiki , haka ta a mince da hakan.
Tana komaqa gida tasanra da mahaifiyarta yanda sukayi , duk sukayi farin ciki da hakan .

Alhaji muktar ne yaje gida , dan yau yake da niyyar. Tunkarar matarshi , akan maganar aurenshi ,

*MUJE ZUWA*😎😎

*KUYI MANAGE DA WANNA DAN BANGA RUWAN COMMENTS BA SHIYASA BANMUKU DA YAWA BA, AMMA IN NAGA COMMENTS SOSSAI ZANYI LONG PAGE A NEXT PAGE I INSHALLAHU*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️✍️
*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU,AD)*

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 14*
Alhaji ,muktar ne ya shigo gida , batareda da fargaban fadawa matarshi maganar auren ba , dan yasan cewan matarshi bata da matsala ,

Yana shiga gidan yatarar da matarshi da yaranshi suna kallo , suna dan taba hirarsu jifa jifa ,gwanin sha awa,
Sa nu da zuwa suka mishi , ya amsa , yanemi guri ,ya zauna ya kalli yaran nashi yace maimuna ,rahama, kudan bamu guri , zamuyi magana da mahaifiyarku , yaran suka amsa da toh suka tashi suka nufi dakinsu ,

Alhaji muktar ne ya kalli hajiya hajara ,da take zaune tana jiran jin wacce maganane mai mahimmaci haka , yace hajiya kunsan duk abun da Allah ya kaddarawa bawa babu makawa sai ya faru ko , hajiya hajara tace kawarai kuwa ,

Ya cigaba da cewa , wlhy hajiya hajara baki rageni da komai ba , bata inda kika gaza wajan kyan hali da kuma bani kulawa , sannan ko a ina ina yabonki domin Ke macece me mutunci da sanin ya kamata
Hajiya hajara tace , haba alhaji dan allah wa inan maganganu naka sun isheni haka ,kafadi abun da zaka fada , yanda kake ta tsarani ya isa haka , tafada dauke da murmishi a fuskarta ,

Alhaji muktar yayi gyaran murya yace hajiya hajara ,aure nake san in Kara , kuma maganar gaskiya nan da wata daya nakesan yin auren .
Ya fadamata , a inda suka hadu , sannan ya kara da cewar' ai 'yargidan alhaji Muhammadu ma dala ce
Tunda ya anbato sunan alhaji Muhammadu mai dala gabanta yayi mugun faduwa , amma ta danne dan kar ya gane hakan , tace 'yar wacce matar ce a cikinsu , alhaji muktar yace 'yar uwar gidanshi ce ai ,
Hajiya hajara takara jin gabanta ya fadi , jin yace 'yar hajiya amina .
In bata manta ba tabbas , ta ji labarin hajiya amina , da 'ya'yanta ,basu sa mutunci ko kadan , amma tayi saurin danne zuciyarta ,
Ta kalli alhaji muktar tace to dama akan maganar nan kake ta wani tsara ni , haba alhaji , shekarata ashirin da uku dakai baka taba cewa zakayi aureba sai yanzu da kake burin yi , ai kar ma kayi tunanin bazan goya maka baya ba
aikamun hallacci sossai , sabida da haka ina tayaka ,murna allah yatabbatar manaa abun da yafi zama alkhairi
Amma in badamuwa inaso in dan baka shawara , allaji mukatar ya kalleta cikin , sauri yace shawarar me hajiya , hajiya hajara tace kafin kayi aure inaso kayi bincike sossai akan amaryara tawa , dan allah ya sani banaso ka kawo wacce zatayi sanadin tar watsa farin ciki mu , inaso kayi bincike sossai ,
Alhaji muktar cikin rashin jin dadin maganar matar tashi yace , toh kina tunanin zan auri wacce zatayi , sanadin lalacewar farin ciki mu ne kome ?
Hajiya hajara takalleshi tace , haba alhaji wlhy ba haka nake nufi ba , shawara kawai na baka , amma in hakan yabata ma rai kayi hakuri mijina
Alhaji muktar yace shikennan ya wuce , zanyi abincikena kamar yanda addini ta koyarmana , hajiya hajara tace toh hakan ma yayi allah wuce mana gaba ya , amsa da ameen, ya ce gone sai he ya sanarwa da mahaifiyarshi maganar auren ,hajiya hajara ta ce allah kaimu , daga bisani alhaji muktar ya shiga dakinshi ,
Bayan ya shigane hajiya hajara ta nufi dakin 'ya'yanta dan sanar musu da maganar auren mahaifinsu
Tana shiga tasamu yaran suna hira gwanin sha awa , cikin ranta , tace ,allah karkasa wanna auren yayi sanadin tarwatsewar farin cikin iyalina , dan harga allah tana ji ajikinta kamar wannan da mijinta zaiyyi babu alkhairi a ciki, amma zata dinga kokarin addu ,ar zabin alkhairi .
Yaran ne suka kalleta sukace mommah lafiya kuwa , tace lfy kl yarana, kawai akwai maganar da nakeso muyi da kune,
Duk suka gyara zama sukace wani magana ,mommah , hajiya hajara ta kallesu ta ce dazu da mahifinku ya shigo shine yake mun maganar cewa zai kara aure ,kuma cikin wata daya yakeso a gama komai .

Ga mamaki yaran Ke kallon mommah tasu , sukace ,aurefa kikace mommah , hajiya hajara takallesu tace kwarai kuwa , takara da cewar amma ni allah yasani 'yar da zai aurane gaskiya ina tsoronta, sabida nasamu labarin hallaiyarau da ta mahaifiyarta , wlhy basu da hali , ina tsoro kar tazo ta ta tarwatsa mana Farin cikin mu ,
hajiya hajara tace kunsan wa zai aura ?? Yaran suka girgiza kai ,alamar aa, tace toh yar gidan hajiya amina zai aura matar alhaji Muhammadu mai dala, rahama tace , tab wacce a cikinsu rukaiyya ko hafsa ?
Hajiya hajara tace toh wlhy ban tambayeshi sunanta ba , amma ko wacece ai zamuji .
Rahama tace wlhy mommah, yaran basun da hali , ana yawan maganarsu , ko a makaranta sai kinji a na maganar rashin kirkinsu , basu ba har mahaifiyarsu.

Naji labarin yayarsu da take aure baki yanda take juya mijinta ba wlhy, dan naji ance tunkafin suyi aure ta mallakeshi sai abun da datace yake mata, tun a waje Kennan , kuma dasu kayi auren ma wai sai abun da tace yake, abun tausayi
Rahama tace ni tunani na ma mommah kar fa su zo su mallake babanmu mu shiga uku , dan allah mommah kisan abun yi

maimuna tace aikam wlhy , ai munyi makaranta da autarsu saffiya Muhammad mai dala , wlhy in tana bamu labarinsu , abun mamaki basu da kirki ko kadan ,
Kuma ace ita za a kawomana a matsayin matar Babanmu , gaskiya mommah kiyi ma baba magana wlhy ba mutanen arziki bane ,
Dan naji harcewa akayi basa tausayin ubansu ,dan basuki ya mutu su ci gado ba , tsabar jarabar san kudi
Ga uwarsu da mugunta ga *MAHAUKACIN KISHINE* da ita wlhy kuma yaran duk sun gajeta
Hajiya hajara kuwa kanta yayi matukar daurewa ,sossai a kan maganar da taji yaranta sun fada , amma zatasa ayi mata bincike sossai akansu ,
Hajiya amina tace toh Ku a ina kuka ji maganar nan , sukace mommah maganar duniya ,ai bata buya ,
Amma gaskiya in tace hankalinta bai tashiba tayi karya ,
Tace toh kunsan me zamuyita addu a zamuyita yi , akan allah yasa yayi bincike sossai akai , dan in yayi bincike yagane to zai iya yuyuwa ya fasa auren , amma ni bazanje mai da maganar ba , dan zai iya cewa ina kishine
Maimuna tace , aikuwa mommah matukar zaiyi bincike sossai toh tabbas sai ansamu mai fadamishi cewan ba mutanen arxiki bane

*MUJE ZUWA*😎

*MORE COMMENTS* 😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY*✍️✍️✍️
*(MUM FU,AD*)

*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*


*PAGE 15*
Rahama ce tace to mama ko hajiyan baba za a fadawa tayi mishi magana akan yabar auranan
Hajiya hajara tayi murmishin da yafi kuka ciwo tace hummm maimunatu na Kennan wlhy baza ta taba goya mun bayaba , kinsan yanda muke da ita ba kaunta take ba . yanzu dai munar maganar lokacin sallah yayi .

Haka hajiya hajara ta ta shi tace ma yaran sutashi suyi sallar magriba lokaci yayi

Bayan ta shiga dakinta ne tayi sallar ta idar ne
ta dinga tunanin yanda zata bullowa al amarin
Da farko tayi tunanin ta dauki shawarar maimumatu na samun mahaifiyar alhaji muktar akan ta hanashi auren , amma kuma sai ta tuna cewar, matar ba wani Santa take ba , dan tasan tabbas zata goyama danta baya yayi aurenne ko dan ta kuntata mata ,
Amma sai kawai ta yanke shawara gara ta hakura da maganar kawai zata cigaba da fadawa allah , tana kai kukanta gun ubangiji , shi zai mata maganin komai ,allah yasan zuciyarta bata taba nufin kowa da sharri ba shiyasa , take addu ar in har amaryar da zai auro, zata zo ne da niyar tarwatsewar farin cikinsu ,allah ya mayar mata mugun nufinta kanta ,

Washe gari ,da safe alhaji muktar yanufa gidan mahaifiyarshi , dan shaida mata maganar auren , dan sai ya fara zuwa gidanta kafin yanufi office .

Yana shiga ya tarar da mahaifiyarshi zaune ta na kallo , Yana shiga ya dukusa ya gaisheta , ta amsa , tace , yau hajaran taga dama ta barka anfito da safe ne , alhaji muktar yace hajiya ai dama ba ita ce take hanani xuwa ba , aikine yakemun yawa wlhy , amma kiyi hakuri , tace yooo dama ai hakurin nake , alhaji muktar yace" hajiya dama. Nazo muyi wata magana mai muhimmacci ne dake , hajiya ,tace ina jinka ,

Alhaji muktar yayi gyaran murya yace , dama aure nakesan karawa , kuma inaso cikin wata daya ace amgama komai.
Hajiya ta washe baki tace aaa alhamdulillah , allah ya karbi addu ata , gaskiya naji dadin wannan maganar ,toh allah Sanya alkhairi , a ina sirikar tawa take , alhaji muktar yace , ai 'yar gidan alhaji Muhammadu mai dala ce ,
Hajiya ta ce yar waye a cikin matan nashi , alhaji muktar yace yar uwar gidan shi ce , hajiya tace kana nufin yar gidan hajiya amina kenan , yace ehh ita ,
Hajiya tace toh allah ya sanya alkhairi , yace ameen , amman hajara ce tazomin da wata magana wai tace inyi bincike sossai a kanta ,
Hajiya tace kaji zanca. banza itadai kawai tace tana kishi in banda haka , miye nawani cewa kayi bincike ai dama a mysulunce bincike na dakyau , amma akace kar a zurfafa bincike shine , shine take wani cewa ayi bincike, dan iyayi da bakin hali ,
Hajiya tace tashi kaje allah ya maka albarka ,allah Sanya alhairi ,

A gugurguce""" lokaci na ta tafiya , alhaji muktar yayi bincike akan hafsa , duk wanda ya tambaya akan halin hafsa da mahaifiyarta da 'yan uwanta kowa baya bada shaida mai kyau , akansu ,
amma ina baya ji baya gani ,yace shi yaji ya gani yanasanta a haka, domin idonshi ya rufe matuka akan hafsa , dan bakaramin aiki boka yayi akan alhaji muktar ba shiyasa, alhaji muktar yace yaji yagani kowani irin hali ne dasu ya yarda zai zauna da ita , baya ganin ko wani iri aibu a tareda ita .

A bangaren hajiya hajara kuwa , ta ammata bincike sossai akan hafasa da yan uwanta da mahaifiyarta, amma amsa dayace , cewan basu da halo kwata kwata ,
Akwai wata kawar hajiya hajara da tazo ta sameta take bata labarin halinsu , da danginta , takecemata , tabbas ta shiga uku zatayi kishi da dangin masifa , tace , tabbas , aka auro miki hafsa kashinki ya buce dan wlhy wa inan *MAHAUKACIN KISHI* ne da su , sabida haka shawara daya zanbaki addu a zaku dage sossai da neman taimako , dan wlhy har na tausayamiki ,
Hajiya hajara tace badamuwa ni na fawwalawa allah lamarina , allah ya fisu bi iznillah ...

*MUJE ZUWA*πŸ’ƒ

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️✍️* *(MUM FU, AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 16*
A gurguce
Duk yanda hajiya hajara tayi dan ganin auranan ba ayishi ba , amma ina allah ya kaddara sai anyi auran , shiyasa ta fawwalawa allah lamarinta dan , haka allah ya kaddara ,

A Yaune dubannin jama a suka shaida daurin auren alhaji muktar tafida , tareda hafsat Muhammadu mai dala ,
Alhaji muktar ba laifi ya narkawa hafsa kudi sossai dan yin hidimar bikin , dan ko nawa ya tambaya haka zai cire ya bata .

Bayan an daura aurene ankai amarya gidanta. Alhaji muktar ys tarasu yanayi musu nasiha mai ratsa jiki, hajiya hajara ce ta ce , amarya dan allah roko daya zan miki ki zauna dani zuciya daya , duk abun da namiki wanda ba daidai ba dan allah ki fito kifadamun , nima nayi miki alkawarin hakan , yara kuma dama yara nakine , kinada damar da zaki musu duk abun da yadace , sannan ga amar mijinmu kirike mana shi hannu bibbiyu dan allah ,
Hafsa kuwa cikin ranta wani bakin ciki taje ji a ranta kamar ta kashe hajiya hajara ,dan wani mugun haushinta takeji , cikin ranta tana aiyyana cewar zata dandana kudarta, daga ita har 'ya'yanta , amma a filli cewa tayi laa bakomai inshallah , nagode
Da haka alhaji muktar yakara yi musu wa a xi sossai , daga bisani sukayi sallama kowa ya watse , hajiya hajara tace toh asuba ta gari ango da amarya dukkaninsu sukasa dariya

Hajiya hajara dakin yaranta tashiga ya samesu suna chart , takallesu tace ,maimuna rahama ,kubani hankalinku , Kunga dai yanda allah yake lamarinshi allah yakaddara dai wannan aure sai anyishi ,
Toh maimuna rahma dangirma allah dan allah ina rokonku. Kuyi biyayya ga matar mahaifinku kamar yanda zaku mu dan allah , kar inji kar ina gani , duk abun da tace kuyi kuyi , karwani raini yashiga tsakanin Ku da ita , ba ruwanku da ita , kunsan hali kunsan ni bana san tashin hankali ko kadan dan allah dan annabi ina kara rokonku yarana kuyi hakuri ,

Yaran ne sukace , haba mommah kamar bakisan tarbiyyar da kika bamu ba Wlhy ba damuwa , munmiki alkawarin bazamu taba watsa miki kasa a ido ba , mommah ,
Cikeda farin ciki hajiya hajara tace toh Allah muku albarka , sai da safe , suka amsa da ameen ,tace , gobe kutashi da wuri dan a shiryama antinku breakfast mai kyau , suka ce toh sai da safe
Bayan hajiya hajara tafita ne maimuna tace , rahama gaskiya mommah zuciyarta Nada kyau allah karkaba da ikon da anty zata cutar mana da ita , dan wlhy ni a karya , rahama tace humm ameen fa anti maimuna, dahaka su kwanta abinsu

*MUJE ZUEW*

*PLSS KU MANAGE DA WANNAN SHORT PAGE DIN , DA BABU GARA BA DADI*

*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING*✍️✍️✍️✍️

*STORY AND WRITTEN BY* *(MUM FU,AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IaEiILApyqN6ePQRzOPT7k
🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 17*
Washe gari da safe su maimuna da rahama suka hada abin karyawa , chips da kwai sukayi , suka yi farfesu kaji , sai sukayi kunun gyda da kuma tea , suka jera akan dining ,

Hafsat ce tafito tana shan kanshi tana taunar cingum kamar magajiyar karuwai .
Ta sa riga da wondo , sun mugun matseta , tafito tana murguda baki , ta nufi gurin dining din ta bude kulolin abincin ta duba tagani, ai kuwa tana gani ta wani yamutsa fuska kamar taga sabon kashi , ta kwallama rahama da maimuna ihu , tace kuna ina kufito , da sauri sukafito , hajiya hajara ma tayi saurin fitowa tace antynsu rahma lafiya kuwa , su rahama ma suka karaso da sauri sukace anty gamu

Aikuwa hafsa ta wanke maimuna da rahama da mari ji kake tassss, tasss tace , dan ubanku baku da tarbiyar da za ku gaisheni ne kun wani zo kuntsayamun akai , cike da mamaki suke kallonta , da mahaifiyarsu , marin da taimusu yayi daidai da fitowar alhaji mukhtar daga daki , ya karaso yace lafiya , kuwa hafsa?

hafsa ta ce da alama baka ba yarannan tarbiyya mai kyau ba ko ince uwarsu bata basu tarbiya mai kyau ba , tunda har zasu iya fitowa basu gaisheni ba ,sannan kuma tsabar dabbanci sukaje suka yi abun da bance su girka ba, ai da sai suzo su tambayeni abun da zanci sai su girkamun ,

Alhaji mukhtar yace eh gaskiya basu kyauta ba kiyi hakuri baza su kara ba Dan Allah .
Ya kallesu yace Ku dan ubanku Baku da hankaline da baza Ku gaisheta ba , kuma kunje kundafa abincin da bashi take da ra ayin ci ba , dallah Ku tsuggunna kubata hakuri ,kafin ranku ya baci, yafada a zafafe
Yaran suka kalli mommah tasu , alama tayi musu da ido akan su durkusa su bata hakuri , dukkansu suka durkusa suka ce anti kiyi hakuri , hafsa bata ko kallesu ba tace kutashi kubani guri, har sun tashi ta kwallamusu kira tace, kai suka juyo ,

Please Login or Register in order to submit comment