Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikeda mamaki yace" Sadik miye haka kana cinkin haiyyacinka kuwa?? Ya da girmanka zaka dinga haka , kana Abu kamar wani saurayi da bai taba aure ba , dan Allah tashi kar hankalin mutane ya dawo kanmu .

Bai ce komai ba, tashi yayi zai tafi , yaji wani iri. Jiri na dibanshi da Sauri ya nemi guri ya zauna.

Niyarshi yana komawa gida ya kira mahaifinshi yazo ya roki mahaifin Aisha ko zai amince ya bashi Aisha .

Sai kuma dabarar kiranshi awaya ta zo mishi

Daukan wayarshi yayi yafara kokarin kiran numbern mahaifinshi , bugu biyu babbanshi ya dauki wayar yace" Sadik lafiya kuwa,?

Cikin tsananin tashin hankali Sadik yace" baba an rabani da Aisha mahaifinta yace bazai bani ita ba , baba dan Allah kazo ka rokeshi yayi hakuri yabani ita.

wallahi a shirye nake na rabu da Rukkaiyya rabuwa ta har abada indai akan Aisha ne .

Da Sauri mahaifiinshi yace "to ganinan zuwa yanzu.

Shiryawa mahaifin Sadik yayi da Sauri ya kira driver ya fada mishi inda zai kaishi.

Bai tsaya ma yima Hajiyan Sadik bayani ba , yadai ce yanazuwa , idan yadawooo zai mata bayani .

Minti goma ya kaishi gidansu Aisha , Inda mahaifin Aisha nata ba Sadik hakuri da kalamai na kwantar da hankali , yakuma ce da bai kira babanshi ba.

Gaisawa sukayi daga bisani suka neni guri suka zauna , nan mahaifin Sadik yace" mallam Rabiu yaro ya kirani yana wasu maganganu naji kamar yace wai kace ba zaka ba da auran yarka ba ko ? Toh ko miye dalili ?.

Gyaran murya mahaifin Aisha yayi yace" gaskiya Alhaji ba komai ne yasa nace najanye wannan auran ba sai dai dan tsoron halin matar danka , wallahi ni ba mutunne mai San rigima ba ko Kadan , shiyasa naga hakura da auren shiyafi.

Caraf Sadik yace " ni wallahi a shirye nake in rabu da Rukkaiyya Akan Aisha in hakan shine mafita .

Shuru mahaifin Aisha yayi yace" A,a baza a yi haka ba bazaiyuyi karabu da matarka ba kan wata , amma gaskiya yakamata kadauki mataki , sannan kuma in harka amincewa zaka rabamusu gida toh na amincewa ka auri Aisha .

cikin Saudi Sadik yace" eh abani nan da sati biyu ma zan gyrara dayan gidana sai ta koma can .

Cikeda gamsuwa mahaifin Aisha yace" toh shikenan na amincewa , amma Ku dakatar da duk wani bidi,a gobe juma a a daura kawai kafin wani Abu ya kara faruwa .

Godiya sossai suka ma mahaifin Aisha daga bisani sukayi sallama .

Gida Yakoma nan yake sanar da su Aisha da mahaifiyarta cewa ya amincewa da auran , amma ga hukuncin da yayayanke .

Murna sossai Aisha tadingayi tashige daki takira Sadik waya.

Cikeda zumudi da farin ciki.

Murna sosai Suka dingayi .

Bayan Sadik ya koma gidane kusan kwana sukayi suna waya cikin farin ciki da kaunar juna .



Washe gari
Da misalin karfe shadaya na rana dubbanin mutane suka shaida Auran Sadik da matarshi Aisha akan Sadaki naira dubu Dari biyu lakadan ba ajalan ba.

Bakin Sadik kamar alawar au duga tsabar murna da farin ciki.

Sanye yake ciki fararen kaya shadda gyznal tasha bakin aiki , kafarshi Sanye da lafiyaiyyen takalmi baki .
daa hula kalar baki da fari hannunshi sanye da tsadadden agogo da zobe .
Da haka aka daura auren bayan anci ansha kowa ya waste .


*MUJE ZUWA*

*MORE COMMENTS* 😎😎😎
*MORE TYPING.......*✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️ (MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIMFollow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FefBYiBeHYGCr1haw2GeEQ

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*PAGE 42*

*kuyi hakuri da rashin jina kwana biyu wallahi anyi ma sister na operation ne tana sibiti shiyasa*

*Sorry for the late update*πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘

A bangaren Amarya kuwa Aisha tasha kyau har ta gaji kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki marar misultuwa .

Mutane sai magana suke kan cewa Aisha tayi ganganci Shiga gidan Rukkaiya mai *MAHAUKACUN KISHI*.

Duk wanda yaji cewan Sadik yayi aure sai yata mamaki matuka.

Dan Kuwa mowa cewa yake Aisha tayi matukar na mijin kokarin Shiga gidan Rukkaiyya.

Kakan Aisha kuwa ,wato mahaifin mamanta ya tsaya tsayin daka Dan ganin ya ne nema mata Addu,ar tsari da kuma dafa,I iri_ iri wa Inda idan mutum yayi toh inshallahu Aljani bai isaba balle kuma mutum .

Da kaikayi koma kan mashekiya ,shiyasa Aisha batajin ko dar a jikinta

Dan bata tunani ko shakkar Shiga gidan Rukkaiyya ,San Sadik ya rufemata ido



Rukkaiyya ce kwance a a falon Anti Sadiya tayi shuru tana ta tunanin mijinta.

Sallamar da taji ne yadawo da ita daga dogon tunanin da takeyi .

Kawartace ta shigo , daukeda da salati a bakinta ,kamar wacce akayi ma mutuwa tace " hmmm Rukkauyya tashi tashi zama fa bai sa memu ba .

Ciki rashin fahimta Rukkaiyya tace' bangane ba kike nufi kimun bayani me kike nufi ???

Kawar Rukaiyya cikin zumudi tace" ai yau an daura auren Sasdik .

Cikin zafin nama Rukkaiyya ta mike tace" me kikace wane , Sadik din??? .
Cikeda gulma da tsantsar munafurci , da zumudi tace" humm wallahi Sadik dinki , yau yau ma amaryar zata tare , ba sai gobe ba , wai karkizo ki kara tarwatsamusu taro .

Cikeda tashin hankali Rukaiya tasa hannu akai tace " nashiga uku ,na lalace shikenan Sadik zai San wata mace bayan ni waiyyo " .

Nan tafara kwallama Anti Sadiya kira tana" fadin Anti kizo kizo Dan Allah Anti Sadik dina ya yayi aure!!.

Da sauri Anti Sadiya ta fito a daki tace " ke Rukkaiyya lafiya kuwa , kike kwallamin kira! .

Zama Rukkaiyya tayi a kasa kamar yar bori tama kasa magana ,sai hawaye dayake bin fuskarta
Cikeda Zumudi Kawar Rukkaiyya tace"hummmm Anti wallahi Sadik ne yayi aure.

Anti Sadiya tace" toh sai me mu ai haka mukeso , kuma wallahi sai munyi maganin shi daga shi har tsinanniyar amaryartashi .

Takalli Rukkaiyya tace" toh ke kuma da kike kuka sai me Dallah ki manta tunda an daura auren gobe gobe zamu koma gurin bokan yayi mana aiki yanda ya kamata tunda yace sai anyi auren .

Wani kallo Rukkaiyya tabi Anti Sadiya dashi tace" Anti bazaki gane bane.

Anti. Aure fa!!! Aure fa!!! .
Kennan zaiyyi taraiyya da wata mace bayan ni fa kenan.???

Cikin fushi Anti Sadiya tafara fada tana fadin " ke wacce irin shashace ba bokan yace" komai zai tafi daidai ba ,in baki yardaba kije kiyi duk abun da zakiyi , wallahi na cire hannuna .

Ance miki Nima San kishiyarnan nake ??, to ya za ayi tunda ke aikinki da wanan saloon yazo kinga kuwa dole mubi .

Tun maman nada rai take fama da aikin ki , gashi har yanzu bamuyi nasara ba ,amma ni wallahi inaji a jikina ,wanan Karen akwai nasara tare damu sabida haka ki kwantar da hankalinki. Komai zaiyyi daidai .

Rukkaiyya da takejin jiri , ta tashi tace" toh shikenan , barinje in kwanta , jiki a sanyaye

Tace" ma kawarta sai anjima ki gaida gida.

Tace" uhmm Nima gidan zan tafi daman dai Nazo fada miki ne , ni nawuce .

Daki Rukkaiyya ta wuce tashiga,Anti Sadiya ma ta bita a baya.




*karfe takwas*
Motocin angwaye suka dira a kodar gidansu Aisha , Dan tafiya da Aisha .

Bayan dan nasihohi da mahaifiyarta tadingayi mata mai ratsa jiki matuka , kuka Aisha ta dingayi sossai , .

Jan kunne sossai mahaifiyarta tayi mata akan zama da abokiyar zamanta .

Takuma fadamata cewa" duk runtsi duk wuya karta taba kai karar kishiyarta gun miji.

Da haka tadinga mata nasiha .

Takai kusan awa daya tana mata fada , tareda da 'yan uwanta , ko wa na tofa Albarkacin Bakinshi.


Fito da Aisha Amarya akayi akasata cikin mota , sai gidan Sadik.

Ango kuwa yama kasa rufe baki dankuwa ba karamin farin ciki take ciki ba marar misultuwa ,.

Dan kuwa Allah Allah yake ya Shiga dakin amaryarshi .

Gidan Sadik akakai Aisha.
Gidan yayi kyau sossai masha Allah , part dinta daban ne , two bedrooms , da tankama tankaman Toilet dinta da kitchen .

Dakinta suka kaita , dakin yasha kyau iya kyau da tsaruwa .

Nan yan uwa suka barta bayan sun mata fada sossai mai ratsa jiki.

Nan naga mum Irfaan takara bata wani hadadden tsumi ta dinga dadaka mata .

Tana bata tafita da Sauri , da alama dai ingatattattun maganin matanta tabata masu kyau kuma wa Inda basu da illa.

Kuka sossai Aisha take , na rabuwa da yan uwanta , bayanda zatayi Dan dole tayi shuru , tana jiran shigowar farin cikinta angwanta .

Karfe Tara da Rabi Sadik yashigo dakin amaryarshi.

Yama kiyarda a bokanshi sumai rakiya Sam .
Dan kuwa yace" shi zai kai kanshi , Ai shi ba Yaro bane da sai abokainai sun rakashi shi zaije da kanshi gun amaryarshi .

Tsiya abokan suka dinga mishi suna fadin shidai kam da alama a hannu Yake gara ma kam yatafi .

Cikin ranshin kuwa shi kadai yasan me yakeji .

Banda kai zuciya nesa dayakeyi toh tabbas da yanzu yafada tarkon shaidan wajan aikata zina .

Dan inbai manta ba rabanshi daya kusanci Rukkaiyya matarshi yaukusan wata shida kenan aikuwa dole yayi azarbabi .


Kwamkwasa kofar dakin Yayi da sallama dauke a bakinshi bayan ya ajiye ledar hannunshi yayi ya matso kusa da amaryarshi fuskarshi daukeda murmushi yace," Alhamdullihi Bini,imati tatimmu salihat .
Allah nagode maka da ni,imar da kaimun na mallakamun wanan Kyakkyarwar mata dakayi .

Cikin wani irin Sallo yace ko zan iya ganin fuskar gimbiyata .

Cikeda kunya Aisha takara rufe fuskarta.

Hannu yasa yabude fuskartata yace" yau kuma ni ake rufewa kyakyawar fusakar matata .????

Humm kawai Aisha ta ce"

nan yace ,sutashi suyi sallah su mika ma Allah godjyarsu akan ni,imar dakuma baiwar da yamusu .

Tashi sukayi suka dauro Alwala yazo yajasu sukayi Salla raka,a biyu .


Bayan sun idar ne yadafa kanta yafara karanto mata wasu addu o,i ,harya kammala .

Tambayoyi yai mata kamar yanda addini ya tanadar , take Aisha tadinga bashi ansarsu .


Rukkaiyya ce kwance akan gado duk abun duniya ya isheta , Barin in ta tuno da rayuwarsu da Sadik .

Cikin ranta tana aiyyana yanzu haka Sadik Nanan tare da wata ko??

Nan ta tuna da lokacin Da suke tariyyar Aure shi da ita , tana cewa" yanzu fa haka zai je yayi ma wata abun dayake mata koh???.

Kaii innna bazai yuyuba !!!!!!!. Abun da tafada kenan cikin zafin rai da kunan zuciya

A zabure ta mike .......


Sadik ne da Amaryarshi Aisha zaune yana ciyar da ita daddaden gashasshiyar kazar da yasiyo musu.

Ita kuwa Aisha nata zubamai sangartarciyar shagwaba, tanafadin takoshi.

Hakan da takeyi yayi matukar tafiya da tunanin Sadik take yaji wani irin feeling ya motsa mishi.

Dan taba shafaffen cikinta yayi yace" A,aa banyarda ba wannan cikin bai koshiba .

Cikin sigar shagwaba Aisha tace " uhmm nikam wallahi nakoshi , nikam .

Murmishi Sadik yayi yace" toh. Shikenan tashi muje mu wanke baki mu kwanta tunda kin koshi.

Nima na koshi yafada cikin shagwaba wai zai kwaikwayeta .

Dariya abun yaso ba Aisha tace " toh muje .

Bayan gida suka shiga sukayi brush suka kara dauro alwala daga bisani suka koma dakin dan shirin kwanciya.

Lafiyayyen kayan barci Aisha tasaka , shima yasaka nashi kayan barci.
Jawota jikin shiyayi.

cikeda tsoro Aisha kalleshi tace " Dan Allah sakeni ,tafada da muryar shwagaba.

Kara jawota jikinshi yai suka fada kan gado yana mai da wani wahallen numfashi .

Bum !! Bum!!Bum!!
Knocking din kofarsu a ka kafarayi .

*Toh fan masu karatu*

*MUJE ZUWA*



*IDAN NAGA RUWAN COMMENTS KUJINI ANJIMA IN BAN GANI BA SAI JIBI*


*MORE COMMENTS* 😎😎😎
*MORE TYPING....*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)


*PLS SHARE*

🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN* πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY)*


*____________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*
*PAGE 43*

*Wallahi zan dakatar da rubutun nan haka zan koma rubutun litafin HATSABIBBIYAR MACE kawai ,shi dinma idan naga karancin comments in ajiye in daina , mutum zai shafe sama da awa daya yana typing amma comments din minti biyu zuwa uku ya gagara , wasu ma dan wulakanci ma Sai dai suu turo sticker , ko su sa emoji sign , ko suwani CE tnx, ni ba godiyarku nake bukata plss , comments da dogon sharhi nakeso , in banga comments sama da talatin ba wallahi tallahi zan hakura da rubuta littafin Nima saukina, Na kwanta inyi barci Na , wannan shine karo Na karshe , bari kugani*


Kwankwasa kofar da akayi ne yasa a dan firgice Sadik da Aisha suka tashi .

Cikeda mamaki Sadik yace " waye????.

Cigaba da bubbuga kofar dakin akayi kamar za,a balla kofar .

Cikin zafin nama Sadik yace " waye ne?.

Da murya me karfi , muryar datagama cin kuka , duk muryar ta dashe tace " kabude mana matsiyaci!!!!..

Cikeda mamaki Sadik yake fadin Rukaiyya!!!!.

Aisha kuwa tana manne a jikin Sadik duk tsoro ya kama ta .

Sai yanzu Sadik ya tuna ashe doki yasa yama manta cewa bai rufe babban gate dinsu ba , yana Allah Allah yashiga yafito ya rufe gate din ashe ya manta.

Kara bubbuga kofar takarayi kamar zata balla kofar cikin kuka tace" kabude mun ko narantse da Allah in maka Abun da tunda uwarka ta haifeka ba,a taba maka ba .

Takara da cewa kasan Allah wallahi tallahi idan baka budeba petir ne a hanuna sai na zazzaga Na kunna ashana kowa ma ya mutu .

Kuka Aisha tafarayi tana fadin nashiga uku jeka jeka jeka bude kofar , karta kashemu .

Cikin zafin nama Sadik yaje ya bude kofar.

Shigowa tayi , sanya take , da wata matsatsan wando da wata matsatsiyar Riga , kanta sanye da p_ cap .

Da mamaki sossai sadik ke kallan Rukkaiyya yace"

Ke bakida hankali ne zaki shigo mun gida haka ????.

Bata ce komai ba ta tureshi, ta nufi gun Aisha tazabga mata wani gigitaccen mari .

Cikin hanzari da zafin nama Sadik ya taho ya rike Rukkaiya ya juyo da fuskarta ya wanketa da mari itama .

Bura uba!!! Abun da Rukaiyya tafada kenan .
A zuciye tana huci ta sa hannu ta wanke Sadik da mari .
Kafin kace me ,a zafafe Aisha itama takai ma Rukaiyya mari tace," zan jure duk wani abun da zaki mun , amma bazan taba jurar ki cima mijina mutunci ba .

Takara da cewa"idan har ke bakisan darajarshi ba toni nasani .

Kinasanshi kike daga mai hankali ,bakya bashi kulawar da ta dace, bakya farantamai , kullum ciikin yi mishi bala,i kike , ace mutum mai kwarjini mai nagarta da sanin ya kamata yana fuskantar wananan matsalar , duk wani abun jin dadi da more rayuwa baya samu , toh in hakan !! Ashe dai *MAHAUKACIN KISHIN* da kike nunawa akanshi Na karya , kuma yazama Na banza , tunda bakya bashi farin ciki .

Juyo Aisha tayi ta kallli Sadik tace"mijina !! Tafada cikin wani irin salo tace" inshallahu farin ciki ya dawo gareka kajii!! .

Rike mishi hannun tayi tana kallanshi takara da cewa "farin cikin daka rasa na shekaru goma sha tara, toh inshallahu ni a kwanaki goma sha taran zan gyarasu zan mayar dakai tamkar Wanda bai taba aure ba .

Nan ta kallo Rukaiyya datake dafe da kuncinta sakamakon Marin da tasha a gun Aisha.

Nan Aisha tace," ko da yake mara barka da Wanda bai taba aure ba kadan ne ,sabisa ko saurayi ya fika kwanciyar hankali.

Sabida haka inshallahu nayi maka Alkawarin baka farin ciki Na har Abada .

Kara matsowa kusa da Rukaiyya Aisha tayi tace" duk wanan haukar da kikeyi kiina tunanin ina tsoro ne ???, wallahi hakan da kikayi shi yakaramun San shi a zuciyata.

Wani ihu Rukkaiyya tasa, ta shako Aisha .

Da sauri Sadik ya janye Rukkaiyya .

A zafafe yake magana da karfi yace Rukkaiyya !!!!!! Kifita ki barmin gidana tunkafin ranki ya baci.

Cikin tsantsar rashin mutunci Rukkaiyya tace" bazan fita ba ai nima gidana ne .

Murmishin da yafi kuka ciwo Sadik yayi yace " Rukkaiyya kinsan Allah idan baki fitaba zan miki abun da baza ki taba mantawa ba .

Cikin rashin kunya Rukkaiyya Na harare harare da karkada karkadden jiki tace" kadade bakayi ba , aikin banza kawai .

Bai kara cewa komai ba illa Kamo hannun Aisha da Sadik din yayi ya jawota zuwa kan gado .

Tashi yayi ya kashe wutar dakin , sai bedside lamp kawai yabari .

Aisha binshi kawai take da kallo ,tana mamakin me zaiyyi ????.

Rukkaiyya kuwa ta tsaya Dan ganin ikon Allah.

Kamo Aisha Sadik yayi yafara bata hot kiss a baki .

Wani ihu Rukkaiyya tasa tace" waiyyo nashiga uku.!!!

Sadik a gaban zakuyi iskanci , Na rantse da Allah idan ka kukskura kayimata wani Abu wallahi sai na gutsire abun kowa ya huta .

Tana magana cikin bala,i da tashin hankali, tace"kuma wallahi inanan babu inda zanje har gari yawaye .

Sadik bai ce komai ba , in banda cigaba da bama matar Aisha kyakyawan romance, da Alama ma hankali shi baya jikinshi .

Aisha kuwa ganin Rukaiyya bataso yasa batayi ma Sadik gardamar hakan ba , ta sake mishi jikinta duk da cewa batajin dadin yanda yake mata a Dan tsorace take , kasancewar wannan shine karo Na farko da Na miji yafara Tana jikinta .

Kokarin Miyar ma Sadik da martanin abun dayake mata takeyi , Tana yin hakan ne ba dan komai ba sai dan ta Kular da Rukaiyya .

Da zauri Rukaiyya ta nufuso ta ture Aisha gefe ,tafara kuka sossai Tana fadin ," tsinanne matsiyaci ,wallahi Baka is kasan wata mace ba bayan ni narantse da Allah baka isa ka sadu da wata mace ba bayan ni kuma bari kagani .

Nan fa Rukaiyya tafara nuna musu asalin hauka ,dan hawa gadan tayi tafara birkitawa tadinga fasa kayan kan Dress mirror dinta ,tana ihu Tana bala,i .

Sadik Na kokarin Janta amma ina ta fita haiyyacinta kamar wata mahaukaciya , wurgi kawai takeyi da kaya ko ta ina .

Bayan tayi kacaca kaca da dakin , ta koma kan gadan ta zauna , tace" wallahi duk abun da zakayi sai dai kayi inanan , ehee .

Kamo hannun Aisha Sadik yayi da Sauri ya jata zasu fita , da Sauri Rukkaiyya tasha, gabansu tace" La,anannu wallahi babu Inda kuka is a kuje kunanan .

Da sauri ta kulle kofar dakin tasa keyn, ta tusa keyn ta wurga cikin rigarta .

Banda kuka babu abun da Aisha takeyi, dago idi tayi takalli agogon cikin dakin taga har karfe uku saura Takara fashewa da kuka ta kallo Rukkaiyya tace", wallahi Allah ya isa tsakanina dake kin lalatamin komai kin lalatamin darena na farko kin cuceni , kin mayar mum da Daren far in ciki Na daren bakin ciki .
Nasan ke macece kinada 'ya
Amma bazan miki fatan ayi ma yarki abun da kika mun ba dan nima 'yata ce .

Amma inaso kisan wani abu inshallahu sai kinga sakaiyyar Allah cikin gaggawa .

Tana fadin haka tanemi guri ta zauna .

Idan Sadik ya kada yayi, jaa zuciyarshi na wani irin tafasa , gurin Rukkaiyya ya nufo ya kifa mata mari .

Dukkanta yafarayi ko ta Ina yadinga short da ita yana ball da ita har Sai da ta fadi kasa .

Tun Rukkaiyya Na kokarin ramawa har takasa Dan karfi su ba daya ba .

Tun Aisha Na kuka Tana yunkurin hanashi Tana tureshi Tana yabari yabari amma ina takasa , Dan Sadik baya ma jinta dan bakaramin zuciya yayi ba .

Bai bar dukan Rukkaiyya ba sai da yaga jini na fita a jikinta , kuma da alama bata ko numfashi bare kuma motsi.

Daina dukanta yayi , cikin bacin rai yanata hakki .

Zama yayi a kan gado , ya daukko wayarshi , ya lalubo lambar Anti Sadiya ya kira .

Dauka Anti , Safiya tayi tace "toh Allah yasa lafiya kiran Sadik a wanan lokacin ???
Dauka tayi race " Sadik lafiya .

Batareda Sadik ya gaisheta ba yace " kuzo Ku dauki gawar kanwarku a gidana , yana fadin hakan ya kashe wayarshi .

Cikin tsananin tashin hankali Anti Sadiya ta Shiga dakin mijinta dayake ta barci , tafara bubbugashi tace ", kai!! kai !!, tashi tashi ka kaini gidan Rukkaiyya .

Alhaji madu dayake barci yace" to, amma kisa driver ya kaiki mana kuma lafiya ???., zakije gidan ,ba Rukkaiyyan na nan ba ??

Oho bansani ba dallah nace ka kaini kanamun wani banzar tambaya , dallah matsa tashi muje .

Ba driver nakeso ya kaini ba kai nakeso ka kaini

Tana fadin hakan ta daukki waya tafara kokarin kiran layin Anti hafsa bugu biyu ta dauka tace" Anti lafiya kuwa ??kira A wanan lokacin .

Cikin tashin hankali Anti Sadiya tace" Sadik!! Sadik, ya kashe Rukkaiyya , kiyi Sauri kishirya zanzo yanzu in daukeki mutafi gidan ,yakiran yace wai muzo mudauki gawarta .

Cikin tasbin hankali Anti tace" kan uba bashi da hankali ne ?

Yaushe ma Rukkaiyyan

Please Login or Register in order to submit comment