Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asar tayi amma basu ci abinciba hakan yasa suka kama barcin yunwa
.kausar ce tashiga kitchen tayi sauri ta dafa musu indomie .bayan tagama ta tashesu suka ci .sunaci hannu baka hanu kwarya kamar tsofaffin mayu abun tausayi . bayan sungama ne suka tambayi kausar yayar tasu yaya kausar ina mama da baba kuma har yanxu yaya kairat bata dawo ba
Kausar tace eh bata dawo ba kutashi kuyi sallah kunji,, to suka ce suka mike suka je sukayi sallah suka dawo suka zauna a daki abin tausayi๐Ÿ˜ญ
Itako da rukkaiya ta na shiga ta ce tayi knocking me gadi ya bude mata
Fan kacecen gida iya tsaruwa gidan ya tsaru dan tsayawa kwatanta gidan bata lokacine . tana shiga anty sadiya ta hango tana hakimce a kujera alhaji madu nayi mata tausa wato mijin nata .ta washe baki tace aa ruki kece karaso mana . rukaiyya tace eh wlhy anty .anty sadiya takalli mijin nata da kanshi yake asunkuye. Tace kai madu bakaga nayi Bakuwa bane bazakatafi ka bani guri ba tafada rai a hade ๐Ÿ˜ก
Yace kiyi hakuri hajiya .alhaji madu yabar gurin sumo sumi kamar munafiki . hummm banban mutum kamar wannan ace ana mai haka nikuwa nace anya haka suka barshi kuwa . hummm zadai muji komiye . rukaiyya tanemi ta zauna tace kai anti kina sha aninki anty ni narasa yanda zanyi da dan iskan mutuminan Wlhy. Anty sadiya tace humm rukaiyya nikaina abun nashi yafara bani mamaki duk cikin dakin mu duk haka muke juya mazaje amma naki yaki juyuwa yanda mukeso . bakuyi waya da hafsa mjinta ya bata motar da yake hawaba . anty tafada .rukaiya ta kurma ihu tace dan Allah anty da gaske kike .Wlhy dagaske nake anty tafada tana murmushi . humm ai ni anty wlhy na rasa wani irin kaurin Kai sadik yake dashi ni ko keke ya kasa kiya balle mota .amma duk da haka baki ga yakasa sakina in ta Mai burga ya sakeni amma ya kasa rukaiya tafada tana dariya ai ni nasan bazai iya ba sabida boka hantaru yace sai a hankali sauran abubuwan zasu biyo baya. Ko yanzu ma sai da mukayi .rukkaiya takwashe komai tafadama antyn tata duk abun da yafaru har rashin lfyr khairat din . anty sadiya ta tabe baki tace uhmm su sukasani shegiyar yarinya ai nafuskanceta ta fi son dangin ubanta bata dauko komai irin namu .gara gara ma kausar da sauki akan khairat da walida shiyasa kamarsu daya da ubansu . suka sa dariya a tare a haka suka sha hirar su sunmma manta da khairat dake kwance a asibiti . daf da sallar magriba rukaiyya tace .uhmm anty barinje in duba yarinyar nan a asibiti . sai in yi gida daganan anty sadiya ta ce toh agaisheta tace zataji . rukaiyya tafito ta nufi hanyar asibitin .lokacin har khairat ta farka tana cin abincin da hajiya ta aiko musu . ita da salma . rukaiya ta shigo cikin takun isa ta tako inda yar tata take tace ya jikin naki . da sauki khairat tace mata .toh Allah kara sauki . salma ta amsa da Ameen . rukaiyya ta bita da shu umin kallo Dan tinda tashigo dakin bata ko kalli inda salma take ba dan ko gaisuwar ta bata ansa ba . da mamaki salma take kallon rukaiyya cikin ranta tana fadin anya wannan matar kanta daya kuwa . sai kace ba itace ta haifi yarinyar nan da cikinta ba .Niko nace kanta daya kawai tsantsar rashin mutunci ne ke damunta dasuka shashi a nono .
Rukaiya ta ce to barin tafi ,nabar kananki a gida khairat a sanyaye tace toh dazu ma naji likita yace zuwa gobe ma zai sallamemu . tace toh Allah kara sauki . natafi khairat tace ki gaidasu kausar . rukaiya a takaice tace zasuji .
Bayan fitar mahaifaiyar tata ne takecewa salma anti salma kinsan miye Wlhy tunda na taso nake ganin irin wannan bala in kullum mamanmu da babanmu cikin fada suke .da zargin juna narasa wani irin rayuwa suke Wlhy . salma tace kiyi hakuri watarana sai labari .
Khairat ta ce to anti salma nagode
A hakan suka dan taba hiransu daga bisani suka kwanta bayan sun yi salla
A bangaren sadik kuwa koda ya bar asibitin gurin aikinshi ya nufa yayi abun daxaiyi ya nufo gida . wani xuciyar na raya mishi ya tafi gurin Aisha ko zai samu sauki .sai kuma yatuna da ciwon dayake kanshi ,zata iya tambayar shi meyasa meshi . haka kawai yaji ba yasan zuwa sabida kar ta tambayeshi . haka ya wuce gida ya tsaya a gun me abinci ya siya abinci .yaci sannan Yakama hangar zuwa gida ko da ya je gidan extra dakin da ke tsakar gidan ya shiga ya dauko kujera da news pappern da ya taho dashi ya fito waje ya zauna
Ya ajiye news paper yafara lalubar numbern budurwar tashi ya kira . haka sukayita hirar su ta masoya gwanin ban sha a wa daga bisani ya yanke kiran sukayi sallama . ya kira kanwarshi salma yana Tambayar jikin yar tasa ko kuma akwai abun da suke bukata in zaizo gobe ya taho musu dashi. da sauki sossai
Babu abun da Mike Bukata salma tace .sukayi sallama
Ya dauko news papern shi yafara karantawa

Rukaiyya kuwa koda ta bar asibitin bata je gida ba yawanta ta wuce kasancewar ba baya bace wajan yawo . sai bayan isha I sannan. Tanufo gida .koda ta dawo tarar da shi tayi a zaune a kan kujera yanata karanta news paper ko kallon Inda take baiyi ba
Tayi kwafa ta fara wake wakenta na habaici .bai ko kalleta ba haka yaci gaba da abun da yake duk da cewar abun da take fada yamai zafi amma yadanne zuciyarshi gudun kar ayi ba dadi . rukaiya ta ji haushi matuka na rashin tanka mata da baiyi ba .haka tayi kwafa ta wuce cikin gida ta tarar yaran nata duk sunyi barci gashi ko haske babu kasancewar ba akawo wutan nepa ba
Ko ta Kansu bata bi ba tashigewarta daki hankalinta a kwance ta hau latsalatsan wayan . .shiko sadik . Mamaki abun yabashi dama ba ta gidan to uban wa ta barwa yaran lallai da yasan bata cikin gidan da ya shiga ya ga halin da yaran nashi suke ciki . yana tsaka da tunani .wani abokin sadik ne kuma makwafcin shi yafito ya Tarar dashi zauna kamar yanda yasaba dan da wuya sadik yayi kwana uku bai fito da daddare ba gudun masifar matar tashi
Duk randa kaga sadik bai fito kofar gida ba to ranar ana shiri da matar tasa wanda fadan yafi shirin yawa . abokin sadik me suna Ibrahim yace alhaji sadik kardai yauma kunkara samun matsalan sadik yace hmm alhaji Ibrahim kabari kawai haka sadik yakwashe komai ya fada mishi haka alhaji Ibrahim yayi shuru yana jimamin wannan lamari nasu shi gaskiya yana mamaki gaskiya akwai lauje cikin Nadi . alhaji Ibrahim ne yace toh Allah ya kyauta . ni barin shiga gida sai allah ya kaimu . allah ya kaimu sadik yace shima daga bisani ya shiga cikin gidan ya kule da ki ya kwanta gwanin ban tausayi

Yana tunanin ko da wace masifa za atashi a gidan nashi ohooo
Da haka har barci yayi awun gaba dashi

*MUJE*ZUWA*


MANAGE THIS AMMA GASKIYA IN BANGA COMMENTS SOSSAI BA BAZANYI TYPING. GOBE BA GASKIYA

*MORE*COMMENT*๐Ÿ˜Ž
*MORE TYPING*โœ๏ธ

*STORY AND WRITTEN BY*โœ๏ธ
*(MUM FU,AD*)

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

*MA HAUKACIN KISHI*

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

*MALLAKIN*๐Ÿ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabir
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*



*PAGE 04*



Da safe sadik yana tashi yayi wanka yanufi asibit dan ganin lafiyar diyar tashi ko takan iyalan nashi bai bi ba ya fita abinshi gudun kar yashiga gidan asamu matsala .,, dan bakaramin aikin ta bane ta nemeshi da masifa.
ko da yaje asibitin jikin nata yayi sauki sossai . sunata hira da salma
Yace khairat ya jikin naki da sauki sossai baba khairat ta fada murya a sanyaye
Yace toh Allah yakara sauki kina shan magungunan ko , tace eh inasha ,
Salma tace baban khairat ina kwana ya jikin naka kaima . ahh ai ni da sauki ,dan karamin ciwone fa .salma tace toh Allah kara sauki.
Ya amsa da ameen
Sai a lokaccine khairat ta lura da ciwon dake kan mahaifin nata tace baba meyasa me ka .
Yace bigewa nayi . tace bigewa kuma eh yafada a takaice.
Cikin ran khairat kuwa bata gamasu da maganar da mahaifin nata yafada ba ,tasan cewa Abun da iyayen nata suka sabane sukayi
Bazai wuce mamanta ce tafasa mishi kai ba ,
Sabida wannan bashine karo nafarko da suka fara ma junansu lahani ba , sadik yace barinje inga likitan
, sukace toh

Office din likitan sadik ya shiga doctor ya rubuta musu sallama . suka tattara komai nasu suka nufi gida
A hanya salma tace baban kairat nii kam kasaukeni in karasa gida kawai . sadik yace aa salma baza ki raka khairat din gida ba . aa gida kawai zan wuce . sadik yace toh shikenan . barinje in saukeki sai mu wuce .salma tace la daka barima zankarasa wlhy . aa bari dai in kaiki .
Toh" salma tace . suka tafi suna isa ya sauketa yace kigaida hajiya ,baran samu damar shigowaba sauri nake ,salma tace toh shikenan .kairat allah kara sauki . a sanyaye kairat tace ameen nagode anty salma ki gai da gida toh gida zaiji

Sukayi sallama sadik yakamo hanyar zuwa gida koda ya iso gidan bai karasa ciki ba khairat ce ta shiga jiki a sanyaye da rashin karfin jiki
Sadik kuwa gun aikinshi ya nufa
Bayan ya isa gun aikine yazauna yayi shuru
yana tunani iriri cikin ranshi . abokin aikinshine mesuna idris ne ya shigo yana sallama amma sadik bai amsaba kasan cewar yayi nisa cikin tunanin da yake . idris yadan buga tebur din kadan yace alhaji sadik tunanin me kake ne ina tayi maka magana baka jiba .
,,Afirgice ,sadik yadago kai iya kallonshi . yace bakomai kawai dai ina tunanin rayuwa . idris yace toh Allah dai ya rufa asiri. Sadik yace amin .
Daga bisani suka ci gaba da aiki suna dan taba hira .

Da sallama khairat tashigo dakin ta tarar da mamanta tana tafaman waya tana shewa

,,yaran na zaune suna kallo
Oyoyo yaya kairat suka nufi gunta suka rungumeta kindawo ya jikin naki suka fada a tare kausar ce tace kai Ku saketa mana bakwa ganin bata da lfy ne
Maman tasu ce tace ya jikin naki bayan tagama wayar
,,Da sauki kairat tace . toh allah ya kara sauki tafada tana cuno baki . yar yarinya dake kisama kanki damuwa .in kikakashe kanki kin huta . ko dayike ubankine yaja miki ta tabe baki
Khairat tace mama Dan Allah akwai ruwan wanka inyi jikina duk yamun tasmin wlhy
Kausar ce tayi saurin cewa eh na jona a heather bari yayi sai in juyemiki . kairat tace toh nagode
rukaiyya ce tayi kwafa tace uhmm ni fita zanyi in kungama kudaurama muku abinci . kausar tace mama inazaki !. rukaiya tace gidan ubanki zani kausar tayi shuru kairat da sauran kanan suka ce sai kindawo .,suna kallo uwar tasu ta dauki dan ficicin gyalenta ta yafa tafita
Khairat ce tace kausar meyasa yau bakuje school ba . khausar tace . toh ba wanda zai shirya mu. Ni kuma ba Iya shiryasu zanyi dakyar ma nasamu na dafa mana abun kร ryawa . kairat tace shikennan
Barinje in juye ruwan wankan. Inyi wankan .kausar tace la yaya kairat kibarshi kawai barin juye miki . toh kkairat tace .
Yauwa ,, kausar me yasami baba a kai .ne nasan halin nasu sukayi koh , kairat ta fada . kausar tace uhmm Wlhy kuwa yaya kairat , nan kausar ta kashe komai tafadawa yayar tata khairat tace toh Allah ya kyauta ,kausar ta amsa da ameen
Khairat tace barije inyi wankan
,
Bayan tagana wankan ne ta fito ta shirya. Sai ga sallamar wani yaro yana fadin wai ana sallama da khairat gaban kairat ne yafadi tace ni kuma kaje kace waye . yaron Yakoma yace wai ance waye kai . saurayin mutumin yayi murmushi yace kace Hashim ,ne . yaron Yakoma gida yace wai Hashim ne . khairat tace Hashim ,!! to kace ina zauwa . yace toh . powder kairat tadan shafa sannan tadanshafa lipstick
Saurayi '' ne kyakkyawa ba laifi.black beauty . yana jingine a jikin mashine dinshi rober rober ta karaso da salllama tace ina wuni . lfy kalau ya kike ya gida
Khairat tace lfy kalau . meke tafe dakai . Hashim yace dama maganar gaskiya gurin ki nazo tun ranar da na ganki naji kin kwanta mun arai Kuma Wlhy ba da wasa Nazo ba da gaske nake
Amma bansan miye ra a yinki a kaina ba .
Nan Hashim yadan bata takaitaccen tarihinshi
Daga bisani yadaura da cewar ki bani numbernki dan mudinga waya
Khairat tace ba waya a hannuna wlhy
Hashim yace ba waya hannunki.kuma , Meyasa ,,khairat tace eh ta lalacene tafada a takaice ,
Toh shikenan badamu wa allah ya wuce mana gaba .amma gaskiya ni da gaske auranki zanyi .kuma banaso abun ya dau lokaci Gaskiya ,, danni a shirye nake Hashim yafada yana murmushi .,, har ga Allah khairat taji dadin Abun da sadik yace ,dan gaskiya ba abun da take buri kamar tayi aure ,,ko dan ta DAINA ganin bakin cikin nan ,, kuma bata taba sha awa ko tunanin zaman aure irin na iyayenta ba'' .amma wani gefe na zuciyarta tana tunanin Barin kannanta , tausayin kannan nata ya Kama ta , .eehmm sadik yayi gyaran murya .khairat ta dawo daga tunanin da take .
Yace in kingama tunanin ina jiran amsa
Dan a gaskiya a matse nake inji amsarki dan gaskiya inaso in mallakeki matsayin matata

Hummm"" khairat tace . cikin ranta Kuwa cewa tayi allah yasa hakan dan in bata manta samari har uku suna zuwa nema auranta sai sufasa bayan. Sunyi bincike akanta .hakan yasa tayi shuru tana tunani .,, Hashim ne yace yanaga kinyi shuru , . cike da jin kunya kairat tace toh Allah ya zabamana Abun Dayafi zama alkhairi
Hashim yace ameen ina godiya da amnicewa da kikayi .
Khairat tace ni Barin shiga . hashim yace da wuri haka . eh Wlhy bana dan jin Dadi ne yau Wlhy shiyasa cike da kulawa hashim yace toh Allah ya kara sauki,, ameen tace daga bisani sukayi sallama tashiga gida shima ya tada machine din shi ya tafi
Yafara tafiya ne wani mutum da yake kallon lokacin da Hashim yazo gun khairat ya tare shi yace sannu bawan allah Hashim yace yauwa sannu lafiya !!
Mutumin yace lfy kalau kawai dai inason baka shawarane. Hashim yayi shuru ya ce shawara kuma to ina jinka .mutumin yace naga kaje gurin yarinyar gidan can koh . Hashim yace eh akwai matsala ne . mutumin yace babba ma kuwa dan Wlhy gidan ba tarbiya kullum ranar daidaine ne iyeyenta basa fito su doku a titi suna zage zage , sannan uwarta ga *MAUHAUKACIN KISHI* Dan Wlhy tafi karfin ubanta ,
Sabida haka in baka yardaba zaka iya xuwa kayi bincike akai
Jikin Hashim a sanyaye dan tunda mutumin yafara magana Hashim yaketa hada zufa .
Ya yi shuru kamar me nazarin wani Abu . daga bisani yace toh nagode . mutimin yace yoo ai badamuwa daman gani nayi mutum me mutunci kamarka da nutsuwa bai kamata ka hada zuri a da su ba dan Wlhy ba dangin arziki bane
Hashim yace barinje sai anjima na gode Hashim ya ja machine dinshi ya tafi jiki a sanyaye da tunani iri iri cikin ranshi
Koda kairat ta shiga gida farin ciki fam cikin ranta ko ba komai ta dai kusa tabarma masiffafun iyayen nata gidan
Kausar ce tace yaya kairat waye yaxo ,, kairat takwashe komai tafadawa kanwar tata .
Kausar tace kai alhamdulillah. Allah yasa dai shi kar yafasa . , ameen khairat tace da haka suka shiga kitchen sukafara shirye shiryen yin abincin Rana ,,sauran kannan nasu suna fallo suna kallo

''A bangaren rukkaiya kuwa koda ta fita bata wuce ko ina ba sai gidan anty hafsa dan ganin sabuwar motar da mijinnata ya siya mata ,, gidane kato na alfarma ,tashiga gidan kai tsaye,,. 'yan mata tagani su biyu kowacce tana ta faman aiki
Daya tana sharan gida daya tana wanki
Daganinsu kasan sun jigata dan duk me tausayi in ya kallesu sai ya tausaya musu
Duk sun fita haiyyacin su gawasu kaya da sukasa . kamar tsofaffin almajirai
Ko kallansu batayi ba . 'yan matan sukace sannu da zuwa .anty rukkaiya ina wuni . , ko kallo basu isheta ba balle su samu damar da zata ansa musu gaisuwar su
Kai tsaye ta kutsa cikin dakin
Hafsat na zaune ta hakimce akan kujera tana latsa waya . yaranta ne su biyu mace da na miji suna zaune suna wasa dagani Kasan hutu ya ratsa su
Aa,, rukkaiya sannun dazuwa hafsat tafada
Yauwa sannu anty hafsa . rukaiya ta fada ta nemi guri ta zauna ,, tace "anty hafsa nazo ganin abin alkhairi ne nazo murna ,jiya naje gidan anty takefadamun wai baban junior ya baki motar da yake hawa .
Hummm Wlhy kuwa ruki yagadama yabani ai ina tambayarshi jikinshi na rawa ya mika min key din motar da takardun
Hummm anty hafsat dama nice
Wai baki ji abun da yafaru nidashi bane agun anty sadiya rukaiya tafada. Uhmm takirani tafadamun ,ai kin bani haushi ne wlhy shiyasa ma ko kiranki banyi a waye ba , toh anty yazanyi duk *(MAHAUKACIN KISHIN*) danake nuna masa abun yaki ,kuma Allah yasani inasanshi ,shiyasa bana san rabuwa dashi
Muyi fada muyi dambe amma
har yanzu muna tare
Badan son da nake mishi ba da yanzu nabar mishi gidan shi ,rukaiyya tafada , lallai toh ai shikenan ai .bagara kin rabu dashi ba kije ki auri mutumin da zaki dinga juyashi San ranki amma kinki tunda haka kika zaba ai shikenanan anty hafsa tafada
Yauwa,"anty ina shigo naga wa incan yaran suna ta uban aiki .naga duk sun fita haiyyacin su kai anty gaskiya kina wuta!! Rukaiya ta fada tana kyalkyakewa da dariya . wai ubansu baya ganinsu a haka ne . mssttt anty hafsa taja tsaki toh sai me yana ganinsu mana ,,toh ko shi baifi karfin in maidashi haka ba ehee
Kai anty hafsa baki da dama wlhy ,rukaiya tafada tana dariya keta da mugunta

PLSS KUYI HAKURI DA WANNAN

*AMMA INBANGA RUWAN COMMENT BA BA ZAKU JINIBA ANJIMA*๐Ÿ™„๐Ÿ™„๐Ÿ™„
*MORE COMMENTS*๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž๐Ÿ˜Ž
*MORE TYPING*โœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธโœ๏ธ
*STORY &WRITTEN BY*
*(MUM FU,AD*)


๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”๐Ÿ’”

*MA HAUKACIN KISHI*

๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ

*MALLAKIN*๐Ÿ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU,AD)*

*FREE BOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

Wattpad , zaynerb Muhammad kabir
*____________________________________*

*๐ŸŒˆ๐Ÿ‡ฐAINUWA ๐Ÿ‡ผRITER'Sโœ๐Ÿผ*
*๐Ÿ‡ฆSSOCIATION๐Ÿค๐Ÿป*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*๐Ÿ‘‡๐Ÿป

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*




*PAGE 05*



'Yan matan ne suka shigo cikin dakin a wahale suka ce anty mun gama dan girman Allah kitaimaka kibamu abinci muci yunwa mukeji wlhy dan Allah , suka fada suna kwalla abin tausayi
Dalla matsamun anan tsofaffin mayu ,cemuku akayi bazan bayarba ,sai kuje ga dumamen tuwan dukukayi shekaran jiya kuje Ku dauka kuci
Daya a cikin su tace anty ai tuwan yayi tsami ,ya lalace , hafsa tace kan uba samun guri bawa da bacin rana dan bura ubanku kar allah yasa kuci in kunci kun raina ubanku , kuma wlhy nama fasa Baku gara in ba ma karnuka su ci ,, rukaiyya tace hmmm lallai samun guri kam tsabar rashin godiyar allah kuce baza kuci ba toh ai shikenan ,
Bar 'yan bura uba ina daidai dasu dalla kutashi kubani guri kan in ci ubanku yanzunan. ,,hafsa ta fada a fusace da sauri suka tashi sukabar gurin suna kuka abin tausayi
Dakinsu suka nufa suka nemi guri suka zauna in kaga dakin kamar ba dakin 'yanmata ba katifa ce kawai yar karama sai taburma sai kayansu a kunshe a cikin zannuwa ,dukansu sukayi shuru suna tunani ga yunwa ga gajiyar aiki hakan yasa duk suka galabaita daya a cikin su ne tace , maimuna ko muje gurin me gadi ne ya arama kudi muje mu siyo Abun da zamuci kar yunwa ta galabaitar damu ,dayar tace rahama kinfasan yana binmu kudi , nasan ma bazai bamuba sabida yana binmu bashi ,
Maimuna tace toh ko zamu fita ne ko allah zai sa musamu abinda zamuci
Rahama tace oo nikam maimuna rayuwar nan Abun tsoro ne kidubemu kigani kiduba rayuwar mu tadaa bantaba tunani zamu kasance a haka ba
Kiduba kiga baba ,Yama manta damu kwatakwata a rayuwa ,tafada tasa kuka me cin rai daban tausayi ,
Maimuna ta rungume yayaryata suna kuka a tare tace anty rahama kiyi hakuri watarana sai labari ,amma kinsan ba haka akabar baba ba sabida in kika duba yanda baba yakeji damu adaa zaki Tabbatar ba yin kanshi bane amma zamuyita addu a allah ya karkato da hankalinshi garemu , baki ga ko hajiya kaka ba ta riga ta sallama ma anty shi
Mudai mucigaba da addu a kawai itace kawai mafita
Dahaka suka tashi suka fita kamar almajirai dan Neman abin da zasuci
Abangaren sadik kuwa bayan ya tashi a aiki bai zarce ko ina ba sai gidan hajiya , acan yasamu ya ci abinci daga bisani ya sukayi sallama da hajiya ya wuce gida .
Ko da yaje gida kai tsaye

Please Login or Register in order to submit comment