Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zasuci .

Bayan yadawo ya zuba musu sukaci , sunaci sunadan taba hirar du ta masoya .

Bayan sun gama yayi daidai da kiran Sallar isha,i.

Tashi Sadik Yayi ya tafi masallaci , itakuma ta gyara gurin .


Karfe goma suka kwanta , dan wasa Sadik yayi ma Aisha daga bisani suka kwanta , sai dai barcin Sadik Rabi da Rabi , dankuwa bakaramin sha,awa ce ke damunshi ba , dan da ciwon ciki ya ke kwana , batareda sanin kowa ba .

Alhaji madu ne kwance a gado, cikin barci yaji anata fadamishi cewa," _karkaga na taimakeka kayi sakaci da addu,a karike addu,a karike addu,a karike addu,a_.

A figice ya tashi daukeda da salati a bankinshi , zufa ce me karyo mishi , cikin ranshi yana aiyya na cewa , tabbas yayi sakaci da addu,a duk yanda akayi wannan Aljanar ce ta ce take yi mishi magana.

Tashi yayi yayi Alwala Salla raka,a biyu , ya kai kukanshi gun ubangiji .

Bayan ya Idar ya kwanta , barci , cikeda tunani iri _ iri.


Washe gari da safe , Alhaji muktar ya tafi gurin aikinshi , Bayan ya sauke Anti Sadiya a asibiti , kashedi tamishi cewa , bata yarda idan kowa yayi sallama dashi yaje ba in ba haka ba sai ranshi ya matukar baci, amsa mata yayi da toh .

Amma tabbas da dayanda zatayi da ta hanashi fita , amma tasan tunda tamishi kashedi shikenan .

Khairat ce tsaye da Hashim suna hirarsu ta masoya .
Dan soyaiyya mai karfi ce ta kullu tsakaninsu .

Duk Wanda ya kalli khairat tabbas yasan tana cikin farin ciki zamanta a gidan Hajiya , tayi kyau tadanyi kiba , gwanin sha,awa.

Cikin farinciki Hashim ke fadin , wai yaushe zan turo ne ,?? .
Cikin kunya khairat tace," uhmmm Kasan ba ,adade dayin Na baba na ba , kabari in an kwana biyu sai katuro koh ??.

Dan langwabar dakai Hashim yayi yace," toh shikenan amma ba haka naso ba tunda kince haka shikenan .

Hira suka dan taba , sossai daga bisani sukayi sallama.

Ganin Anti Hafsa ta fita yasa Rahama da Maimuna suma suka fita da sauri.

Cikin sauri suke tafiya suka nufi gidan Hajiya Rahmatu

Samun Hajiya sukayi zaune , sukace , kiyi Sauri kitashi mutafi , Antinmu bata gida ta tafi asibiti , in yaso sai mu boye ki a dakin mu , baban MU Na dawo wa sai ki fito .

Da Sauri Hajiya ta yafa dan tsogon gyalenta suka tafi .

Suna isa kofar gidan maimuna tace," barinje in duba ko bala mai gadi yana gun .

Anyi sa, a kuwa koda ta duba yana dakin shi yanata sharar barci.

Da Sauri yace," kushigo a hankali , kuyi Sauri , tafada murya kasa _kasa , Shiga sukayi sumi sumi kamar munafukai , suka shiga dakins.

Maimuna tace," Hajiya wai a akayi kika dawo ne ,?? Ba kintafi kauye ba ?.

Nan Hajiya tabasu labarin duk abun da mallam yafadamata, da kuma dalilin dawowarta

Mamaki sossai sukayi , sukace," ai kuwa inshallahu yau kam sai kun hadu da babanmu , Hajiya tace," Allah yasa ' yayanan , daga bisani suka dan taba hirarsu ta yaushe gamo , cikin farin ciki , bayan suma sun bata labarin irin bakar wahalar da sukasha , Hajiya ta matukar tausaya musu , harda 'yar kwallarta .

A can Asibiti kuwa , Anti Sadiya itama tazo , dan yan uwansu yan dubiya , duk Wanda yazo , sai suce Sadik ne yayi mata mugun dukan dayasa ta kwanciya a asibiti.

Jin hakan kowa sai yayita zagin Sadik suna tsine mishi Albarka .

Bude ido Rukaiyya tafara kokarin yi , dusu dusu take gani , bata iya cewa komai ba , sai hawaye dake fita a idonta , dasauri suka matso kusa da ita sukace," sannu Rukaiyya ya jikin naki , kasa magana tayi sai binsu kawai da ido takeyi .

Sannu suka dinga mata amma babakin magana .

Doctor suka kira , Nan yazo yadan yi gwaje gwajenshi ,yace," su kwantar da hankalinsu , ba wata damuwa .

Aisha ce kwamce a cinyar ,Sadik kasancewa yau Sadik bai FIta aiki ba , sanye take da Riga da wando , sun matukar ansar jikinta , dan kashe murya Aisha tayi tace," wai ni yaushe yarana zasu dawo ne ,?? Gaskiya inaso su dawo muzauna tare ,Cikin matukar kulawa, Sadik yace," humm Ai ba yanzu ba sai munci amracin mu.

Kunya ce ta kama Aisha da gudu ta tashi ta tafi daki, shima ya bita , a baya , yana dariya .

Wunin ranar Haka Rukkaiya ta ke ido a bude amma ba baki magana , da haka su Anti Sadiya da Anti Hafsa sukace zasu tafi gida , subarta da Anti umma .

Karfe shida na yamma , yayi daidai , da lokacin dawowar Alhaji mukhtar daga gurin aiki , bayan ya biya asibiti dubo jikin Rukaiyya , Anti Hafsa tace," zata bishi sutafi gida kawai , sukayi sallama suka tafi .

Horn Alhaji mukatr yafarayi a kofar gidan shi dagudu , bala mai gadi yazo ya bude gate din kofar .

Wangale gate din yayi Alhaji mukatr ya kunno hancin motarshi cikin gidan .

Jin horn yasa su maimuna sukace ," Hajiya gashi ya dawo tashi mufita addu,ar samun nasara suka farayi , bayan Hajiya tayi duk abun da mallam ya umar ceta tayi , FItA tayi dauke da addu,a a bakinta .

Fitowar Alhaji Mukhtar daga mota yayi daidai da fitowar Hajiya daga dakinsu maimuna.
su maimuna suna biyeda ita a baya .

Gaban Anti HAFSA ne yayi mummunan faduwa ganin Hajiya Ramatu a cikin gidan .

Kan Alhaji muktar ne yai wani irin sarawa , ya kalli Hajiya yace," Hajiya !!!!!! yanunata da yatsa yafada da kakkausar murya .........✍️

*MUJE ZUWA*


_*INA KARA BAKU HAKURI KUYI HAKURI DA RASHIN POSTING DA WURI DAN ALLAH*_


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING....*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*

*PAGE 50*

Da sauri yazo gurinta yace," Hajiya !!! Ina kika shigane kwana biyu , ina kika shiga,??.

Kuka Hajiya tasa tace," muntari kai ka ka wulakantani akan matarka , shiyasa Na tattara nakoma kauye .

Su maimuna da suke gefe , ya kallesu yace," maimuna !!!Rahma !!! yafada da muryar mamaki , yace," meya sameku kuka lalace haka ?? Me yafaru .

Anti Hafsat datake tsaye , zufa ce kawai take karyomata, cikinta Na wani irin bada sauti Kululululu.. , .

Alhaji mukhtar da gaba daya kanshi yagama kullewa yace," ni fa ban fahimci duk abun da kuke nufi ba .

Hajiya tace," kazo mu shiga ciki kazauna ,zanmaka bayanin komai .

Anti Hafsa kuwa, dan tabbatar da cewa dagaske aikinta ya lalace tayi saurin cewa ," kaje inaa!! dawo banyarda kabita ba , in kuma kaje wallahi sai ranka ya baci, Anti Hafsa tafada cikin fada .
Wani wawan mari yakifeta dashi yace," baki da hankali ne? ina mijinki zaki dinga bani umarni ko danki ne nii?? shasha kawai .

Ya kallo Hajiya yace," Hajiya mushiga ciki.
Ganin Hakan yasa Hajiya yin hamdallah cikin ranta , takuma tabbatar da asirin jikin danta ya karye, tace," toh muje .

Anti Hafsa datake tsaye kamar mutum mutumi , hannunta akan fuskarta , zuciyarta nawani irin zafi ,hankalinta a matukar tashe , wasu hawaye masu dumi ne suka zubo mata .

Dakyar ta iya Shiga cikin dakin .

Zama Alhaji mukhtar yayi Hajiya ma ta zauna .

yace,"Hajiya ina jinki meke faruwa ?? , nan ya maida kallanshi gun su maimuna yace," Mamana , fadamun ya akayi naganku cikin wanan yanayi ??.

Rahama ta kalleshi tasa kuka tace," Na,am baba , yace," wai meya same ku duk kuka lalace haka ??.

Kuka sossai maimuna da Rahma sukeyi , Dakyar Maimuna tayi shuru tana shashekar kuka tace," baba munsa cewa duk abun da kake mana ba asan ranka bane kuma baka cikin hankalinka , baba Antimun ta azabtar damu, ta cutar da mu tasa kayi mana wulakancin da har yasa mukayi tunanin cewa kamar ba kai bane .

Nan Hajiya ta tsoma baki a maganar tace" tabbas muntari abun da ni kaina kamun nayi mamaki , hakan yasa Na daina zuwa gidanka , Na tafi kauye dan nema maka magani.
kuka Hajiya tasa tace," ohh Allah sarki Hajaratu Allah ya jikanki yayi miki Rahama matar kirki , hakika Hajara tasha wahala kafin takoma ga mahallincinta .

Nan Hajiya da maimuna da Rahma suka fara bashi labarin abubuwan da duk suka faru , wa inda suka iya tunawa .

Tunda suka fara bada labarin , wata irin zufa ce ke karyoma Anti Hafsa , tashin hankalin da take ciki bazai misultuba .

Alhaji mukhtar kuwa da tunda aka fara magana , kasa cewa komai yayi , sai kaulla da take zubo mishi .

Share hawayen fuskar shi yayi yace," wai da gaske ni ne na aikatawa Hajara ta haka ,?? Hajara matar kirki , gashi har Allah yayi mata rasuwa ,kuka yafashe dashi kamar karamin yaro
sossai yake kuka Mai tsuma zuciya .

Hakuri Hajiya tafara bashi , tace," kayi Hakuri bagashi yanzu sai labari ba .

Can yadago rinannun idanuwanshi ya saukesu akan Hafsa datake sumi sumi dakai , yace," wallahi Hafsa kin ban mamaki , duk yanda akayi tun kafin miyi aure kika asirceni , Shiyasa duk Wanda yayi kokarin hanani nake jin haushin shi Ashe duk kece sila , Hafsa kin cuceni , kinsa Na cutar da yarana , kiduba yanda yarana suka dawo tamkar ba 'ya'yana ba , me Na miki dazaki azabtar da ahalina haka me namiki menamiki Hafsa???


Cikin ma tsananicin kuka Hafsat tace ," dan Allah dan Annabi kayi ......... batareda ta karasa magana ba yagada hannu yace," kimun shuru , babu abun da zaki fadamun , da kinsan Allah da bakimun abun da kikayi ba , Sabida Haka kije nasakeki nasakeki , nasakeki , saki uku , ihu Anti Hafsa tasa ta tsugunna akasa ........

*MUJE ZUWA*

*KUYI MANAGE DA WANAN PLSS*



*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING......*✍️✍️✍️


*STORY AND WRITTEN BY ✍️✍️✍️(MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*πŸ‘‡πŸ»

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*_________________________________*
*PAGE 51*

*_Sorry for the late post nadanyi tafiya ne wallahi_*


Kuka tasa tana fadin haba Alhaji karkayi haka wallahi nayi nadama , kayi hakuri karka yanke hukunci cikin fushi .

Nan ta kallo Hajiya tace," Hajiya dan Allah kisa baki , Hajiya ko da farin ciki fal cikin ranta tace," yoo ke banda abinki kintaba gani anyi saki uku kuma andawo , ai kiyi Hakuri kawai kitafin, tunda ba kofar da zai dawo dake ,toh ko da kofar da zai mai dake ai bazan bari ba, kin manta cin mutuncin da kika mun .

Kuka Anti Hafsa ta kara fashewa dashi .

Alhaji muktar kuwa , yama kasa magana tsabar bacin rai da bakin cikin Hafsa.

Da sallama yaran suka shigo sun dawo daga makaranta .

Cikin rashin fahimta suke Kallan mutanen dake cikin falon, sukace mommy daddy lafiya ??.

Hajiya tayi saurin cewa , ina lafiya kunga kuje ku yi abun da ke gabanku.
Cikin matukar mamaki suka ce, toh wacece kee!!! .

Hajiya tace," Uwar ubanku , baku sanni ba koh ?? suka daga kai Alamar ehh , Hajiya tace," toh nice nan na tsuguna nahaifi ubanku .

Kallo Mahaifiyarsu sukayi ido jajawur , Kanta a kasa, sukace," mommy kikace mana maman daddy ta dade da rasuwa , yanzu kuma ita tace," itace maman daddy .

Sallati Hajiya tafarayi tana fadin, Hafsatu , ni kikayi ma fatan mutuwa Ehh lallai Hafsatu , muntari ,muntari kajita koh , lallai ma .

Kasa daga kai Anti Hafsa tayi balle har ta kallesu ta iya bada ansa.

Alhaji muktar ne ya kallosu yace," bata mutu ba , tanada rai mahaifiyarku ce ta rabani da ita , amma yanzu gata tadawo gareni .

Nan Alhjai muktar yadan basu kadan daga cikin zaman da yayi da Hajara mahaifiyar su Maimuna da kuma abubuwan da Hafsat ta aikata .

Kuka sossai yaran sukeyi , daga bisani sukayi shuru , cikin ransu suna jinjina irin rashin imani irin na mahaifiyarsu .

Cikin Fushi Alhaji Muktar ke fadin , kee!!.Hafsa , nabaki minti talatin maza maza ki barmun gida.

kuma ,yayana zasu zauna taredani , bazaki dauki ko daya ba , gudun karki koya musu mugun halinki na gado, zan nema musu uwa me mutunci, wacce zata basu kyakkyawar tarbiyya .

Hakuri tafara bashi tana kuka, amma ko kallanta baiyyi ba .

kallan Yaran Alhaji mukhtar yayi yace," kuyi Hakuri nasan Cewa ," zakuji ba dadi barin mahaifiyaku gidanan , amma bazan taba iya zama da mahaifiyar ku a gidanan ba , ta cutar dani , ta zalinceni , tasa na cutar da matata matar mutunci , tasa nayi nesa da mahaifiyata tsawan shekaru , tasa na wahalar da 'ya'yan cikina , taya kuma zan iya zama da mata irin wanan , tsawan shekaru , goma sha bakwai bana cikin haiyyacina, sai abun da mahaifiyarku tafada , duk abun data sani shi nakeyi mai kyau ko maras kyau, Sabida Haka , dole in rabu da ita .
Gaba dayansu kuka suke yi babu me ba ma wani hakuri.

Tashi Anti HAFSA tayi tashiga daki tadan hada kayanta , tafito , ta tafi.

Kuka sossai yaran sukeyi na tafiyar mahaifiyarsu , amma tabbas sun San cewa," mahaifiyarsu bata kyauta , bata cancanci duk wani na miji yaci gaba da zama da mace irin wanan ba .
Babu yanda suka iya haba suna gani ta tafi.

Da
A banagaren Sadik kuwa , bayan yafito daga gida ,gidan Hajiya ya nufa.

Bayan ya isa, ya tarar da Hajiya zaune tana lazumi .

Nan ya tsuguna dan gaisheta yace," Hajiya ina kwana .

batare da ta amsa gaisuwar shi ba tace," ka je ka koma ka kara gaida Rukaiyya??.

Sunkuyar dakai Sadik yayi yace," A,a gaskiya , cikin bacin rai Hajiya tace, " akan me ??.

Shuru Sadik yayi baice komai ba .
Cikin fushi Hajiya kefadin ," Sadik wai meyasa kake hakane??, miye damuwarka ?? ,wacce irin zuciya ce dakai haka , bakada hankali ne ?? Matar nan fa matar kace, kuma uwar 'ya'yanka , ko ba komai ai kaje kaduba lafiyarta, ko kana mantawa cewa kaine ummul aba isin kwanciyarta a asibitin ne?? , kasan Allah banasan naji ka ce komai , kana fita, yanzu kaje gida ka daukko matar ka , ka biyo tanan mutafi asibitin , banasan inji ka ce komai maza maza ina jiranka .

Sadik zaiyyi Magana , Hajiya ta daka mai tsawa tace," banasan inji komai maza maza ka tafi.

Dole Haka Sadik ya koma gida dan daukko Aisha .

Dawowarshi gida ya matukar ba Aisha mamaki , cikin rashin fahimta Aisha tace," lafiya kuwa,? naga kadawo gida a irin wanan yanayi??.

Murya a sanyaye Sadik yace", kishirya muje asibiti gun Rukaiyya .

Mamaki karara a fuskar Aisha tace," asibiti kuma da nii ??.
Yace ", Eh umarnin Hajiya ne , kishirya ina waje kisameni a moto , yana fadin Haka yafita .

Daki tashiga ta shirya daga bisani tafito suka tafi .

Gidan Hajiya ya koma , yayi mata horn , da Sauri Hajiya ta fito suka tafi .

Cikin ladabi da kunya Aisha ta gaishe da Hajiya tace," ina wuni ," cikin sakin fuska Hajiya tace," lafiya kalau Aishatu yakike ya gida ??.

Cikin kunya Aisha tace," uhm lafiya kalau Hajiya.

Hajiya tace," kiyi hakuri na tasoki batareda kin shirya ba koh?.

Aisha tace," laa Hajiya badamuwa wallahi ai a shiryema nake, dama kuma inaso inje .

Hajiya tace, " toh shikenan ,Allah shi Albarka , da murmishi Aisha ta amsa da Ameen .

Suka nufi Asibtin.


Anti Hafsa kuwa bayan fitanta Asibiti ta nufa , bayan ta je Abibtin Anti Sadiya kadai tasamu a asibitin.

Rukaiyya kuwa na kishin gide a kan gado , tayi matukar rama sossai , tana dan magana amma kasa kasa in ba ka kawo kunnanka ba ballai kaji ba , ta rame sossai kamar me shekara goma tana jinya , duk Wanda ya ganta yasan ce wa ta gala baita matuka, kamanin fuskarta duk sun canza .

Cikin matsananicin tashin Hankali , Anti Sadiya kefadin ,kee!! Hafsat lafiya naganki haka ??. Ko wanine ya rasu,.??

Kuka Anti Hafsa tasa tace," ba gara ma mutuwa ba Alhaji muktar yasakeni , kuma saki uku , tana fadin haka tafashe da matsanancin kuka .

Cikin rashin fahimta Anti Sadiya tace" yasakeki ?? .

Kada kai Anti Hafsa tayi tace," ehh .

Anti Sadiya kuwa cikin ranta farin ciki sossai tayi , tasan ko ba komai ita daya ce me aure cikinsu , a fili kuwa cewa tayi toh sai kiyi Hakuri , dama ai kinsan hakan zata faru , sai kidawo muci gaba da zama .

Mamaki sossai Anti Hafsa tayi da ganin ko inkula da Anti Sadiya tayi akan halin da ta tsinci kanta , Hawayen fuskarta ta share tace," Anti yanaga ko kinuna da muwa da hakan .

Wani kallo Anti Hafsat ta bita dashi tace," ha,a toh ya kikeso in miki ???, ko so kike in je in CE Alhaji muktar dole sai ya maidake dakinshi ?? ,
yazan miki bakiji na ce kizo muci gaba da zama a gida naba ?.

Anti Hafsa kuwa bata kara ce wa komai ba tayi , shuru , cikin sanyi murya tace," toh kiyi Hakuri ,dan tasan Anti Sadiya ba mutunci ne da itaba sai ta iya ce wa tafasa , baza ta zauna a Gidan ba .
shuru Anti Sadiya tayi batareda ta ce komai ba.

Da sallama su Hajiya suka shigo dakin .

Wani kallan rainin hankali , su Anti Sadiya suka bisu dashi .

Tashi Anti Sadiya tayi daga kan kujerar da take ta kallo Aisha tace," lafiya kika kara zuwa nan , wai ke meyasa bakida zuciya bakida hankali ne?? Ke wacce irin jaka kuma kidahumace , bamun fada miki cewa idan kika kara zuwa nan sai mum miki tsinanen duka ba .

Wani mari Anti Sadiya ta wanke Aisha dashi cikin zafin nama, Anti Hafsa ma ta kife Aisha da Mari, kuka Aisha tasa ta rike fuskarta .

Sadik da Hajiya ko mamaki ma abun yabasu.
Hajiya tace," Hafsa Sadiya me tayi muku haka zaku mareta ,?? Bayan duk cin mtuncin nan da zagin da kukayi mata be isaba sai kun hada da mari kuma?.

Sadik da rashin yayi matukar baci yace," Hajiya abun da nakesan fada miki kenan kika ki saurarata , jiya fa munzo , suka mata irin wanan cin mutuncin , yanzuma kinga sun maimaita , nan ya kallo su yace," Na rantse da Allah duk wacce ta kara yunkurin taba mun mata ,wallahi kun daki igiyar auran 'yar uwarku , kuma abun bazai tsaya a nan ba har sai na dauki kaukkwaran mataki akai tunda ku bakuda mutunci .

Cikin masifa Anti Hafsa ke fadin ka dade baka dauka ba oh kai har kanada bakin dazakayi magana , kamanta abun da kayi ma 'yar uwarmu, ance maka mudinma kyaleka mukayi , kajira warke warta kagani , kana wani ikirarin ce wa zaka saki Rukaiyya , to kasaketan mana seme?? Daman wallahi ko baka saketa ba zama da kai ya kare , babu kai babu ita tunda kai bakada mutunci , kai badan mutunci bane baka gaji arziki ba .

Hajiya kam kasa cewa komai tayi , kanta ya matukar daurewa , tace," Sadik kar inji kace komai mutafi , murabu dasu, Kallan Sadiya tayi tace," Sadiya nagode , har ki kalli tsabar idona ki farfadi magana San ranki , kin kyauta nagode .

Anti Sadiya ta galla harara tace," ba duk tarbiyar da kika bashi bace haka , da kin nutsu kin bashi tarbiya ai da ba haka ba , ke nifa bari kuji daga ke har dan naki wallahi na tsaneku , ni da kin isama da kinsa wanan dan naki yasaken mun 'yar uwa .

Kallan Sadik tayi tace," kai in ka haifu cikin wanan , tanuna Hajiyan Sadik da yatsa , tace," kasaki Rukaiyya .

A wanan karan ran Hajiya yayi mugun baci,
hakan yasata ta kalli Sadik tace," a wanan Karen bazan hanaka ba kadauki duk hukuncin dakaga yadace , tana fadin haka ta rike hanun Aisha da take gefe tana kuka, tace," mutafi , Aisha tabita suka fita.

Da karfi Anti Sadiya tace," Allah raka taki gona umma tagai da asha, dan naki yadauki matakin daya dace din in ya isa.

Ran Sadik yayi matukar baci, idanshi yayi jaa, dan kuwa bakaramin bata mishi rai kalaman Anti Sadiya yayi ba , cikin fushi yace," ni kuwa na haifu cikin uwata , sabida haka na saki matata Rukaiyya saki na har abada.

Yana fadin haka yafita a dakin .

Cikin ran Anti Sadiya farin ciki sossai kamar ta zuba ruwa a kasa tasha tsabar murna , dankuwa tayi haka ne daman da ganganka , dan so take dukkanin 'yan uwanta su fito gidan mazanjensu , itakuwa tanan a gidan mijinta sai abun da ta ce, dan haka dolema ta bazama gurin neman wani kasun gumin bokan da zai kara mata aiki .

Rukaiyya datake kwance takejin abun da suke fada, tayi wani razananan ihu jin ansaketa.......✍️✍️

*MUJE ZUWA MASU KARATU*

*IDAN NAGA COMMENTS KUJINI GOBE IDAN BAN GA COMMENTS BA WALLAHI SAI JIBI KO GATA KO BAYAN KWANA HUDU, IN YI BARCI NA IN HUTA , πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚*.


*MORE COMMENTS*😎😎😎
*MORE TYPING........✍️✍️✍️✍️✍*


*STORY AND WRITTEN BY✍️✍️✍️( MUM FU'AD*)


*PLSS SHARE*πŸ‘πŸ‘πŸ‘


🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺

πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

*MAHAUKACIN KISHI*
🌺🌺🌺🌺🌺🌺

*MALLAKIN*πŸ‘‰zaynerb Muhammad kabir *(MUM FU'AD*)

*FREEBOOK*

*(TRUE LIFE STORY*)

*_________________________________*

*πŸŒˆπŸ‡°AINUWA πŸ‡ΌRITER'S✍🏼*
*πŸ‡¦SSOCIATION🀝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na

Please Login or Register in order to submit comment