Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

qamshin turarensa ya daki hancinta,wani tashin hankali ya ziyarceta,take ta saki kayan hannunta ta buqaci bandaki,nan ta fara kelaya aman da yayi sanadiyyar ficewar ruwan tea din data samu yau ya zauna mata.

       " lafiya sumayya?,meke damunki?,me ya sameki?"haka ya dinga fadi yana riqe da ita,dukkan alamun tashin hankali sun bayyana a fuskarsa wanda hakan yayi matuqar daurewa sumayya kai,mukhtar din tamkar wani bugun jinnu haka ya koma,idan yaso ya dinga gasa mata aya a hannu shi da matarsa,amma wani lokaci sai ya dinga yunqurin juyewa ya koma mata yaya mukhtar dinta sak wanda ta sani a can baya.

       Ganin qamshin turaren ke sake dugunzuma tunaninta ya sanya ta buqaceshi da ya matsa ya barta bata so,haka ya koma baya ya zuba mata ido har ta kammala ta gyara wajen ta dawo bakin gadon ta zauna tana maida numfashi
"Kishirya na kaiki asibiti,ni bansan baki da lafiya ba" duk da yadda take fidda numfashi dai dai amma hakan bai hanata maida masa magana ba
"Bani buqata,me magani zaya yimin?,shin wai damuwa kayi ma da wata sumayya?,na tabbata bakaqi na mutu ba,tunda har zaka iya hanawa a bani abincin gidanka ina a matsayin matar ka" ta qarashe maganar tana sakin kuka don sosai batun ke ci mata qoqon zuciya,ba wai don ta damu da abincin ba,a'ah,ta dauka tafi qarfin komai a gidan mukhtar din,ta dauka ita din mai iya dauka ce ta bayar ma kyauta,sai gashi ita ake hanawa abinci
"Wallahi ni bansan lokacin da akayi hakan ba,waye ya gaya miki ni na hana?"maganarsa ta ratsa kunnenta,sai ta daga ido tana dubansa tana daga kwancen,gani take kawai raina mata wayau zai yi,aljanu gareshi ko farfadiya ce ta kamashi lokacin da ya bawa zainab din umarni?,baqinciki ne ya hanata magana,ganin tayi shiru ba tare da tace komai ba sai kukan ta data ci gaba da yi yasa yace
" duka mubar wannan maganar muje asibitin a dubaki tukun,zanje nayi sallah ma dawo"ya fada yana ficewa.

        Da fari taso taqi yarda,amma jin tsaiwa na niyyar gagararta sanda zata bada faralin sallar magariba yasa ra taushi zuciyarta ta amince,ita kanta zata so taji meke damunta bawai tayita zama da ciwo ba,tunda tunda take bata taba jin irin hakan ba.

        Ba jimawa da idar da sallar sai gashi ya dawo,zuwa lokacin da qyar ta samu ta gama tata sallar aman ya sake tsinke mata,jikinta yayi laushi tubus sai numfashi da take maidawa,yaso taimaka mata wajen fita amma tace bata buqata,haka ta dinga bin bango har suka isa cikin motar.

         Wani private hospital dake cikin unguwar tasu ya kaita,bayan taga likita ya bata takardar gwaji taje lab,minti goma ta karbi sakamakon ta koma dakin ganin likitan ta kai masa
"Alhamdulillah,sai ka godewa Allah,madam na dauke da juna biyu"baki dayansu wuta ce ta dauke musu kada ma sumayya taji labari,sai ta fara girgiza kai hawaye na sauko mata,magana take son yi amma bakinta ya gaza furta komai
" likita don Allah ka daina mana irin wannan wasan sai ka dauki haqqinmu"ta fusgi kalaman da qyar,sau ya dago kai ya dubeta
"Bama yiwa patient wasa cikin abinda ya shafi lalurar da ta kawo su,ki baki yarda bane hajiya,ai muna da na'urar daukan hoto bismillah ga gado can hau in nuna miki" kasa tashi tayi baki daya,ga rashin qwarin jiki ga luguden da maganar tayi mata,mukhtar dake son tabbatar da gaskiyar labarin shi ya taimaka mata har suka isa bakin gadon.

       Cikin qwarewa ya shiga nuna masu dan qaramin tayin dake cikinta wanda duka baifi wata biyu da rabi ba,basu iya ganewa amma sun lura da wani dan digo wanda shike alamta yaronsu kenan,wata doguwar ajiyar zuciya ya saki tare da lumshe ido yana jinsa cikin wata sabuwar duniyar,yayin da sumayyan ta fashe da kuka,jikinta baki daya rawa yake,ashe tana daga cikin mata masu haihuwa?,ashe akwai rabon zata ga yaron kanta?,ashe ita ma din watan watarana zata zama uwa?,zata yi raino ta kuma bada tarbiyya?,lallai ubangiji babu wanda ya kaishi iyawa cikin mulki da kyauta,babu ko shakka ubangiji baya bacci,baya mantawa da duk wanda ya ambaceshi ya kuma nemi agajinsa.

        Barinsu likitan yayi suka gama murnarsu,don ya fahimci dukkansu ba'a cikin hayyacinsu suke ba sannan ya sanarwa mukhtar din jikin sumayyan ba qwari,zasu riqeta su sanya mata drip(ruwa)har zuwa safiya ko zata ji karsashi,sannan ya rubuta magungunan da zatayi amfani da su wadanda zasu taimaka mata ita da abinda ke cikinta,sannan ya jadda masa alfanun cina abinci mai kyau da gina jiki da qara kuzari a gareta,karba yayi saida ya tabbatar an gama komai an sanya mata drip din sannan ya fita siyo magungunan.

       Ya jima zaune cikin mota ya kasa tayar da ita,ina zaikai wannan kayan farincikin?,da wa ya kamata ya raba wannan farincikin kada ya masa yawa ya masa illa?,da sauri ya zaro wayarsa daga aljihu ya soma daddanna wasu lambobi kyakkyawan murmushi kwance a kan fuskarsa,jinsa yake cikin wata duniya mai dauke dimbin farincikin da ya jima bai jishi ba,jinsa yau yake wani na daban.

     ****      *****     ****

        Ji take idan ga zauna gu d'aya tamkar wani mummunan abu zai faru ne tare da ita,tana jin qwaqwalwarta ko zuciyarta daya daga ciki zai iya tarwatsewa,tunda take bata taba cin karo da mummunan labari da ya firgita duniyarta ba irin wannan labarin,idanunta basu taba mummunan gani ba irin na wadan nan kwanakin,sumayya kishiyarta da ciki?,ita kuwa tana me?,wanne shirme take?,wanne baccin asarar tayi har mukhtar ya yiwa sumayya ciki duk da uban takatsantsan din da take?,duk da raba tsakaninsu da tayi ya daina sha'awarta?,tabbas idan har ta bari sumayyan ta rigata haihuwa cikin gidan ta dibga babbar asara,hakazalika bata ci sunanta,gidan da take da buri a cikinsa,gidan da take so shi da mamallakin gidan duka su zama qarqashin ikonta shine wata zata riga ta fara ajjiye iri?,tun yanzu ta fara ganin manya manyan sauye sauye ina ga ta haihu?,tun yanzun mukhtar ya ruguza dukkan wani plan data yi cikin gidan,wani kukawa yake bawa sumayyan wanda hakan ke nuni da qiris ya rage sun koma su dinke kamar daa koma sufi daa dinkewa,abinda idan har ya faru ba zata taba gafartawa kanta ba,lallai ko zatayi yawo tsirara sai ta tabbatar ta kawar da duk wata barazana dake shirin tunkaro ta.

      Kamar mahaukaciya haka ta suri wayarta ta soma laluben lambar wayar aminiyarta qawarta,wadda bata aiwatar da komai sai da shawarat,zama tayi dabas gefan gadonta jin wayar ta shiga,cikin qananun sakanni mamallakiyar lambar ta daga,ko ta kan gaisuwar da take jefo mata bata bi ba ta soma zayyano mata abinda ke gudana cikin gidan.

      Tsawon minti talatin ta dauka kan layin wayar suna qulla saqa a mugun zare,sosai taji dadi da shawarar data baga,shi yasa bata da kamarta,shawara ce mai sauqi wadda babu zuwa gun boka ko malami,hakanan babu barnar kudi,amma fa buqata zata biya,don dama babbar matsalarta yanzun duka jarinta ya karye warwas,saboda ribar da uwar kudin duka sun tafi gun 'yan tsubbu,bata kwana arba'in bata je an mata service ba,tun tana tsoron hadisin data taba tsintar wasu yaran 'yan makarantar islamiya na karantawa na cewa duk wanda yaje gun boka ko dan duba,to sallarsa ta kwana arba'in Allah bazai karbeta har tazo ta dake tama manta da hadisin baki daya bare ta tunoshi ya zame mata birki. (daya daga cikin abinda Allah ke jarabtar masu biye biyen malamai kenan,basu taba tara abun hannunsu,kullum suna kan hanyar rabawa matsubbata da 'yan duba,ko kishiya gareki mai irin wannan biye biyen ki lura da kyau,duk abinda miji zai baku sai ki nemi nata ki rasa,kullum cikin babu da bani bani take,ba zaki taba ganin burbushin abun ba ko a dakinta ko a jikinta ko a jikin yaranta,Allah ka kiyashemu ka tsare mana imaninmu).

       Tana kammala wayar ta saki murmushi ita daya take magana da kanta
"Kissa ai tafi magani,ba shakka quruciyarki ta yimin rana,zan amfana da ita sosai" ta fada tana ficewa a dakin inda kai tsaye ta nufi dakin sumayya.

        Tana kwance saman carfet din dakin nata tayi matashin kai da pillow,duk da ba yadda mukhtar baiyi ta dora kan nata saman cinyansa ba amma ta qiya,yana zaune dirshan gabanta da faranti a tsakiyarsu wanda ke dauke da kankana da tuffa da gwanda,ayaba yake bare mata yana miqa mata tana daga kashingide take amsa tana ci,dubansa take kawai cike da mamaki,yana son dawo mata mukhtar dinta,"Allah yasa ba yaudara bace,ya Allah kasa kada ya juyan baya"haka ta dinga fada cikin ranta tana binsa da kallo wanda shi sam bai ma kula ba,hannu ta sanya ta shafi cikinta wansa daga can qasa ta fara jin dan tudu kadan,lumshe idonta tayi tana jin qauna cakude da farinciki na ratsata,duk kwanan duniya takan shafa cikin sau babu adadi,wani lokaci takan tsaya gaban madubi ta dage rigarta tayita kallon fatar cikinta tana mamaki yau ita ke dauke da juna biyu,idanu ya zuba mata shima yana kallonta farinciki na bibiyar duk wara gaba ta jikinsa,a haka ta bude idanunta karaf cikin nashi,sai kunya taso kamata,murmushi yayi sannan yace
"Bakiyi laifi ba sumayya ki qaunaceshi yadda ya kamata,wallahi Allah a duniya ban taba jin son wani abu a rayuwata ba kamar yadda nakejin son cikin dake jikinki ba,zan iya rasa komai sabida shi,zan iya rabuwa da komai saboda shi,don Allah ki kularmin da kanki da abinda ke cikinki komai runtsi" ko bai fadi ba tasan zancan daga zuciyarsa kai tsaye yake fitowa,ita kanta bata san irin son da takewa cikin ba,kai ta sunkuyar tana murmushi tare da furta
"In sha Allah ya mukhtar".

       Dukkan wannan maganganun cikin kunnen zainab suka yisu wadda ta sawo kai don shigowa dakin
" ka nunawa kucciya baka"ta fada sannan ta shigo dakin da sallama tana sake sai saita nutsuwarta,gaban sumayya ya fadi har sai data runtse ido cikin zuciyarta tana fadin
"Allahummakh finihim bima shi'ita(Allah ka isar min da su da abinda kaso)(addu'a ce mai kyau ga wanda yaji tsoron zaluncin wasu mutane)" murmushi taje jifarsu da shi wanda shi kansa mukhtar din sai da yayi mamaki
"Ashe kana gun uwar gidanmu my mukhtar" ta fada tana zama kusa da shi,amsa mata yayi sannan ta dora
"Gwara ai ka kular mana da ita sosai musamman da take dauke da cikar muradinmu,Allah mun gode maka daka nuna mana wannan lokaci" ta fada tana maida hankalinta ga sumayya,hannunta tasa ta riqe nata hannun,ji take kamar ta kama garwashin wuta amma sai ta dake
"Sannu sumayya ya jikin naki?" Da qyar ta bude labbanta tace
"Da sauqi"
"Allah ya inganta ya qara miki lafiya kinji,na godewa Allah da zaki samarwa mukhtar sanyin idaniya,naji dadi qwarai dama ke ya cancanta ki fara samun wannan matsayin,don Allah duk abinda kike da buqata ki sanarmin kada kice zaki yiwa kanki wani abu,kada ki duba duka wasu abubuwa da suka faru a baya,sharrin shaidan ne da kuma zuciya wadda bata da qashi,in sha Allah ba zasu sake faruwa ba,sai yanzu na fahimci kyakkyawar zuciya da kuma haqurin da kike da shi,don Allah mu hada kai mu zauna lafiya kinji?" Duk da bata gama gamsuwa ba amma taji dadin maganganun zainab din,ko babu komai wake son tashin hankali?,ai babu abinda yafi zaman lafiya dadi
"Ba komai maman nafi'u,Allah ya sake hada kanmu"
"Ba amin ba,don wallahi da kai na ya hadu da na kishiya gwara na qare rayuwata kan nawa na ciwo" ta fada a zuciyarta,amma afili sai ta saki murmushi tana fadin amin.

        Sake matsowa tayi ta karbi bare ayabar daga hannun mukhtar din,ita ta dinga barewa sumayyan tana miqa mata,tanayi can qasan zuciyarta na mata suya,amma fuskarta kuwa murmushi da kulawa ne kwance a cikinsu.











*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


3⃣0⃣

___________________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*iy yansur kumullahu fala gaaliba lakum,wa iy yakzulkum faman zal lazi yansur kum min ba'a dih,wa'alal lahi fal yatawakkalil mu'uminin*

*_idan ubangiji ya taimakeku babu wanda ya isa yaci nasara a kanku,idan kuma Allah ya qyaleku(ya fita daga sha'aninku) waye zai taimakeku bayan shi?,ga Allah kawai muminai na qwarai suke dogaro_*

*Ya Allah ka taimakemu cikin dukka lamarun mu*
_________________________________





       Kulawa ta musammanzainab ke bawa sumayya wadda zata kwantar da hankalin dukkan wani mai zargi,ta hanata komai,babu abinda sumayyan keyi cikin gidan banda wanke goma ta tsoma biyar,hatta da ruwan wanka ita ke dafa mata ta ajjiye mata a bandaki,girki kowa saidai kawai taci kuma mukhtar ya kwana dakinta,sau tari zainab din kan yafewa sumayya kwananta a zuwan yaje su kwana tare tafi samun kulawa,ta dauke dukka ayyukan gidan bisa wuyanta,ita kadai tasan me take ji cikin zuciyarta,wani lokaci zuciya kan raya mata ta shaqe sumayyan kawai ta mutu ta huta da ganinta da ganin abinda ke cikinta,saidai mardiyya qawarta kan yawaita ja mata kunne da cewa,matuqar ba zatayi haquri ba to kuwa ba zata cimma nasara ba,hakan shike yawaita taka mata burki tana jira har zuwa lokacin da zata kammala qudirinta.

        Qwarai mukhtar na jin dadin yadda take kula da sumayyan,yana yaba mata sosai,hankalinsa ya kwanta,duk da cewa har ya zuwa yanzu akwai tasirin ragowar sihirinta a jikinsa,a duniya yanzu babu abinda yake so irin cikin jikin sumayyan,shi yasa hakan da takeyi yake sake saka farinta a idonsa,shi din ma ba'a barshi a baya,hidima da tattali yake mata kan jiki kan qarfi,duk da sai data masa tutsun abinda ya dinga mata a baya,saidai abun mamaki yaje bashi,ya sanar mata sam baisan sadda hakan ta dinga faruwa ba,kallon ya raina mata hankali ta dinga masa,hakan da ya lura da shi ya sanya ya karbi lefin kawai ya kuma bata haquri.

        Ita din ma sumayyan ba'a barta a baya ba wajen tattalin kanta da abinda ke cikinta,duk wani abu da tasan zaya kawo tarnaqi ga lafiyar cikinta tana kauce masa,har yau bata bar mamaki ba wai itace yau da ciki bayan shekaru kusan takwas cikin na tara da aurenta,bayan da ta riga ta debe haso?,lallai rabon kwado baya taba hawa saka ko ya hau din ma rabi zaya sauko da shi,babu ranar da zata fito ta fadi bata godewa ubangiji ba.

      Mama mahaufiyarta kuwa kullum cikin kiranta a waya take da turowa a duba mata ita,duk sanda zata aiko da abinda zata kawo mata na kayan qwalama na masu ciki,ita kanta yaya yahanasu da taji labarin laqwas jikinta yayi,sai ta rasa me take ciki farinciki ko baqinciki,amma jikinta yayi sanyi ta kuma taya mukhtar din murna,saidai har yau bata je ta ganta ba,tanq gudun wulaqancin da zata taras a gun zainab,don ta yanka musu gargadi kan zuwa gidan duk sadda suka ga dama.

*.........KAYAN KWALABA*
          _MAFARI_



        Zaune yake gefan gadon dakinsa yana sanya maballan rigarsa a shirin sa na fita kasuwa. Ahankali zainab ra bude qofar dakin ta turo ta a hankali kamar wadda qwai ya fashewa a ciki,kujerar madubu ta janyo ta zauna tana fuskantar mukhtar idanunta a kansa,shi ya soma magana
"Lafiya dai ko?,na lura tun jiya jikinki a sanyaye yake,mu da muke cikin farinciki a kwanakin nan"
"Kake cikin farinciki dai,kuma na kusa datse igiyar farincikin". A zahiri sai ta soma goge qwalla da ta fara sakkowa a idanunta tana kallon mukhtar din
" mukhtar,wannan farincikin da muka samu idan bamuyi wasa ba yana gab da qwacewa daga cikin gidan nan,bansan me yasa take ta qoqarin aikata haka ba,bansan me yake damunta ba"barin sanya takalman da yake qoqarin yi yayi,ya dago ya dubeta idanunsa cike fal da tambaya,har ya gaza boye hakan sai da ya furta
"Kamar yaya fa?,me yake faruwa ne?" Kai ta shiga girgizawa cike kirsa
"A'ah mukhtar,barin maganar nan shi yafi alkhairi,don bansan ya zaka dauketa ba"
"Idan kina tunanin wani abu ne da zai cutar da ni qauna ce ki boyemin kiqi gayan,gaya min zainab" dan shiru tayi a zahiri fuskarta dauke da tashin hankali,yayin da zuciyarta ke cike fal da murna da farinciki tare da fata da addu'ar samu nasara tamkar wata wadda zata aikata abun arziqi,bata kuma magana ba har sai da mukhtar din ya jaddada sake tambayarta,taba goge qwalla tace
"Mukhtar,sumayya ce......sumayya ce naji tana magana da wata baquwa da tayi,bansanta ba,ina tunani ko qawarta ce ko qanwarta ko 'yar uwarsu,wai wallahi sam batayi farinciki da samuwar wannan ciki ba,ina ita ina haihuwa bayan ko shekara ashirim baga gama rufawa ba,dama ita can kawai nunawa take tana son haihuwa amma wlh sam bata qaunarta,bare wai ta lura ba wani kulawa take samu yanzu daga gareka ba,tunda kwanakin baya ka juya mata baya yanzu haka data haihu qila ka sake komawa halayyarka,yanzu haka maganar da nake maka har ta bata shawarar ta sha maganin da zai barar da cikin kawai ta huta".

         Tamkar guduma zainab ta sanya ta daki qahon zuciyarsa haka yaji,take maganar da yaya yahansu ta ta sha gaya masa shekarun baya suka bijiro mada suka cakudu da wannan sabon batun
" kai idan zaka farka gwara ka farka,matarka fa ba son haihuwa take ba,bata ma sha'awarta,tunda kuke ka taba gani ta sha wani magani don ta haihu ko ta taba maka maganar kuje asibiti a dubaku?,ina kyautata zatan ma ita tasha maganin da zata hana kanta haihuwa,banda haka yarinyar dake da quruciya mai zai hanata haihuwa a irin wannan lokacin?". Wani fushi da bacin rai mai tsanani ya sauko masa,sai kawai ya miqe,burinsa kawai yaje ya samu sumayya yanzun nan,da sauri ta riqeshi don ba yanzu take da muradin nakiyar ta fashe ba
" a'ah mukhtar ina kuma zaka?"
"Sakeni zainab,sakeni naje na sameta" wani mugun marairaicewa tayi sannan tace
"Shi yasa fa naqi gaya maka tun jiyan,yanzu me zakaje ka yiwa yarinyar mutane kana cikin fushi haka?,idan baka iya kama barawo ba sai shi barawo ya kamaka,zauna muyi magana akwai mafita" babu musu ya koma ya zauna yana maida numfashi
"Mukhtar,kada ka damu,ni mai qaunarka,ina son abinda kake so,idan baka manta ba nike kulawa da sumayya...to kada ka damu,zan sanya ido sosai a kanta,sannan zan hana duk wani abu faruwa har Allah yasa ta haihu lafiya na maka alqawari" hakanan yaji kalamanta sun kwanta masa a rai,sai ya sauke ajiyar zuciya
"Na gode zainab,don Allah na roqeki ki kula da ita,a duniya yanzu babu abinda nakeso sama da cikin nan don Allah" wani shegen kishi ya takore mata,cabdi,a haka zata bari sumayya ta fara haihuwa,ai ba zaya yiwu ba,a fili tace masa
"Na maka alqawari tare ma zamu dinga wuni insha Allahu kada ka damu" jikinsa a sanyaye ya gama shirin zuciyarsa na bugawa,mamaki da haushin sumayya ne fal cikin zuciyarsa,da kamar ya wuce abinsa ba tare da ya mata sallama ba zainab din ce ta tursasashi kan sai ya shiga din,koda ya shiga sumayyan sai taga yanayinsa ya sauya sosai,ba kamar yadda ya saba mata ba,gabanta ne ya dinga faduwa tana fatan ba halayensa na baya bane zasu dawo,don ko kusa bata da buqatar wannan yanayin.

       Har ya juya zai fita sai ya sake waiwayowa ya dubeta
"Ki kularmin da cikina,din bazan iya jurewa ko yafiya gareki ba ga duk wani abun qi da zaya samu cikin nan ba" dai ya juya ya fita,kanta ne ya daure sosai,me yake nufi kenan,ta jima tana qoqarin lalubo amsar,daga qarshe abinda qwaqwalwarta ta bata shine tsabar son cikin da mukhtar din keyi ne haka ta barwa ranta taci gaba da sabgoginta.

      ****     ****     ****

    Bata gushe ba tana ci gaba da cusawa mukhtar tunani kala kala kan zub da ciki sumayya ke qoqarin yi,amma ta nuna masa tana bala'in takatsantsan akan faruwar hakan,sosai ya shiga damuwa da tashin hankali,mamakin sumayyan yake yi,da ya matsanta kan sai ya mata magana yana son daukar mataki,bazai iya jura ba idan wani abun ya samu cikin sai ta masa alqawarin zata nuna masa da idanunsa zai gani saboda hukunci da hujja yafi.




*KUNDIN QADDARA*

*_BAQAR RANA_*



Tun da safe ta hada mata shayi kamar yadda ta sabarwa kanta,duka yana cikin qudurinta da tsarinta. Ranar kusan da wuri mukhtar ya fita,tana kwancan har ya fita din ko abin kari ma bata masa ba saboda mugun qudirinta data qulla aiwatarwa a yau din nan ko farkawa bata nuna tayi ba,hakan ya sanya data shiga da shayin ta zauna tana jan sumayyan da hira,bata bar dakin ba sai data tabbata ta kammala shan shayin,sannu a hankali ta soma hamma,zainab din ta dubeta fuskarta qunshe da murmushi wanda ke dauke da manufofi uku,manufar cimma nasara da manufar mugunta,sai kuma dadi daya kamata saboda tafuskanci magungunanta zasu soma aiki lokaci guda yadda take so
"Kwanta ki huta qanwata na fuskanci kamar bacci kike ji"
"Wallahi kuwa,duk jikina ya mutu" ta fada tana jan pillow ya yada kai saboda nauyi da taji kanta ya soma yi sakamakon bacci mai nuyi daya lullube idanunta. Leqa fuskarta tayi ta tabbata ta soma baccin sannan ta sake sakin murmushi,a nutse ta nufi drower din gefan gadon sumayyan ta fiddo magungunan da suke soke cikin rigar mamanta,magunguna ne har saches uku dukka na zub da ciki ne,saches daya aka balla guda gudu wanda ita tayi amfani da shi ta zubawa sumayyan cikin ruwan shayin data kammala sha yanzu,sai wata 'yar qalamar kwalba da wani saches din wanda duka maganin dake bugarwa ne da saka bacci wanda yawanci 'yan shaye shaye aka sani suna ta'ammali da shi. Dorasu duka tayi kan drower din sannan ta fice.


Kitchen ta shiga ta samo kofi cikin kayan sumayyan ta zuba ruwa ta dawo kusa da magungunan ta ajjuye,ta bude kwabar kayanta ta ciro hijabi ta ajjiye saman kanta sannam ta nufi ma'ajiyar takalmanta ta ciro ta sanya mata daya daga ciki a qafafunta,sai data qare mata kallo ta tabbatar komai ya kammala sannan ta saki dariya ta fice zuwa dakinta.


Tazarar mintina goma ta bada kamar yadda aka ce mata magungunan zasu fara aiki amma maganin baccin zai sa ba zasu tashi aikinsu gadan gadan ba sai bayan minti ashirin,dakin ta sake nufa ta leqata sai ta tarar har yanzu baccin take amma tana motsawa akai a kai,jinjina kai tayi ta sake komawa dakinta.


Kai tsaye ta dauki wayarta ta laluba lambar mukhtar,bugu uku ya daga tare da yin sallama,bata bi ta kan amsawa ba ta soma magana cikin yanayi na matuqar rudewa qwarai da gaske
"Wayyo Allah mukhtar mun shiga uku,mukhtar na kasa riqe amanar da ka bani" cikin wani mugun tashin hankali ya miqe tsaye daga inda yake zaune sannan ya fara tambayarta
"Lafiya zainab yi magana mene ne?"
"Kasan ka barni a daki ina kwance ina bacci,to ina tashi naga lokaci ya ja,sai na tuna sumayya na barta bata ci komai ba,da sauri na shiga kitchen na hada mata abun kari na nufi dakinta,ina shiga naga babu kowa na duba gidan baki daya ban ganta ba,ina falo ina taraddi ina ma shirin kiran wayarka ko kasam zata fita?,kawai sai gata ta dawo dauke da wata baqar leda ita da wannan 'yar uwar tata,da nayi mata magana ma kallon banza ta yimin tayi tsaki ta wuce daki,sai ma qyaleta sabida nasan masu ciki da fushi,sai daga baya na sake leqata sai na tarar tana shan wani magani,na mata zancan abinci tace ta qoshi bata buqata taci a waje,na qyaleta na dawo ina hidimar gida,bayan wajen minti talatin sai na fara jiyo ihunta tana wayyo cikina wayyo bayana inzo in taimaketa" sai ta fashe da kuka kamar gaske,ya gaji da dogon jawabi kawai jira yake azo gurin
"Ki gayan me ya faru?"
"Jini ma gani daga jikinta mukhtar yana fita wanda ke nuna kamar bari tayi"
"Me!" Ya fada da madaukakin sauti,kafin ta kai ga amsawar ta soma jiyo kumar sumayyan na kiran sunata,dadi ya kamata komai yazo a daidai kenan?,sai ta sake dububurcewa
"Tana kirana mukhtar don Allah kayi sauri kazo mu kaita asibiti kada mu rasa cikin nan" sai ta katse kiran kawai cikin gaggawa ta nufi dakin sumayya.


Murququsu ta cimmata tana yi da malelekuwa daga saman gadon har qasan carfet din dakin,tun

Please Login or Register in order to submit comment