Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka shige,kwadayin samun yaranshi ya taso masa ya kuma sake nunkuwa fiye da da,don a wannan lokacin haka kawai yaji yafison yara fiye da baya,yana jin dama ace abdallan nasa ne,yaron ya shiga zuciyarshi,amma tana nufin itace mamarshi?,Allah ne ya kiyaye bai kai mata bugu ba randa ta bugeshi kenan,sam bai sani ba,barin jikin sumayya yayi ya nufo almustapha,cak ya dagashi sama murmushi na subucewa daga fuskanshi,sama ya dinga juyashi abdallahn na dariya,yana son ayi masa hakan dalilin da yasa ya kasa manta almustapha kenan,dauke kanta tayi wani farinciki na ratsata ta isa gabansu baba ta duqa,cikin qauna ladabi da girmamawa take gaidasu,cikin kukawa baki daya suke amsawa kafin baba ya dora
"Haduwa tayi wuya mamana,tunda kuka dawo ban ganku ba" kai ta sadda qasa tan murmushi
"Ummee tace kaje jigawa ai sanda muka iso"
"Gaskiya ne kam,ina fatan komai lafiya?,ko da yake alamu sun nuna hakan,saidai muci gaba da binku da addu'a" murmushi taci gaba da yi ba tare data tanka ba,dai dai sanda almustapha ya qaraso ya durqusa gabansun kamar yadda sumayya tayi ya soma gaidasu suna amsawa,ta dan saci kallonshi sanda yake tambayar mama da yaya abubakar,baba ne yace a basu waje da sauri malam yace
"Haba muhtari,waye baqo cikinku,me zan gaya mata me zata gayan,ka daina min haka" dariya baba ya saki ya koma ya zauna,hira suka taba sama sama duk da sumayya ta kasa sakewa,daga bisani ta dauke abdallah ta basu waje,malam din ba sai ta kawo masa komai ba,idan ta aikata hakan ma kamar tayi rashin kunya kenan,don ita kanta ba zata iya qayyade yawan abincin dake gabanshi ba.

        Suna tafe abdallah na kafadarta duk nauyinsa,tana tambayarsa yana rattabo mata labarai kala kala
"Ummu abdallah" taji an ambata daga bayanta,almustapha ne,cikin kunya ta sauke abdallah,ya qaraso ya karbi hannunshi
"Don me zaki fito ki barni ni kadai,wuce sashenki" ya fada yana gyarawa abdallah hannun rigarshi,ba musu ta wuce ta barsu a nan.

        Wajen ummee ya wuce,kasancewar duka yau bai shiga ya gaidata ba,tana cikin baqi ta miqe ta bishi saman,ta samu daya daga cikin kujerun ya zauna,abinda ya burgesu yadda abdallan ya duqa har qasa ya gaida ummen,ji take da ana qwacen d'aa da ta qwace abdallah ta baiwa almustapha,saidai babu komai duka tushiya daya ce,tana fatan wadda ta samar da wannan ta samawa nata dan itama,cikin kulawa da juna suka gaisa sannan yace
"Su'ad fa ta shigo kun gaisa?"
"A'ah,amma wataqila ka ganta,ai ba tafiya zata yi ba yau din,ko zuwa gobe ma duka daya ne zamu gaisa" take ranshi ya baci har fuskarshi ta nuna hakan,dama ya zargi haka saboda baiji baba ya masa maganarta ba,duk yadda akayi shima baisan da zuwanta ba,ko zai lamunci komai amma banda bangaren iyayenshi,sun fiye masa kowa da komai a rayuwarshi,yana da azamar miqewa ta dakatar da shi
"Bance kaje kuyi bacin rai ba har hakan ya kai kunnen babanka gida cike da jama'a" ajiyar zuciya ya sauje,tafi kowa saurin karantarsa abinda yayi niyya kenan yaje ya sameta,ya dan jima wajen ummeen suna tattauna lamuranda suka jima basuyi hira akai ba kafin ya fita daga bangaren.

        Wajensu hamza ya koma,ya taddasu har sun gama ciye ciyensu,wanda duka sumayyan ce ta sa aka kai musu,ba qaramin faranta masa hakan yayi ba,a da aikin ummee ne,ga hidimar baqinta ga na abokanshi,wannan karon kam kafin ummeen ma ta farga har tasa an gama musu komai,musaddqi ke cewa
"Munci mun qoshi,saura a turo mana amarya mu gaisa" wani shegen kallo ya watsa masa,suka tuntsire da dariya baki daua,hamza kam murmushi kawai ya saki yana qarewa almustapha kallo,kusan yafi kowa cikinsu farinciki da samu sauyawar rayuwar abokin nasu,ko makaho ne kai kana kallonshi kasan cewa akwai sauye sauye masu girma tattare da shi.

         Sai yamma sannan malam yayi shirin komawa kasancewar a jirgi yazo a nan kuma zai koma,ba yadda baba baiyi da shi ya bari sai gobe ba amma yawi,yace zasu zo zuwa na musamman,lokacin sumayya na raka abida da nafisa wadanda suma zasu koma
"Amma malam da zaku bar mana shi ya kwana biyu wajenmu?" Murmushi malam ya saki yace
"Gaku nan gashi" ai kuwa yana jin abinda aka fada ya noqe kafada yana narke fuska,dariya malam ya saki shida baba
"Shifa kamar wanda aka haifa tare da gidansu,baison matsawa nan da can,ki baya ga haka ma abdur rahman na tabbata sai ya biyo sahu idan ba'a koma da shi ba,don yana dari dari ya bafa shi gani yake kaman bazai dawo ba" sumayyan tana ji tana gani cike da kewa abdallah ya tafi,taso qwarai ya zauna wajeta yayi wasu kwanaki,tana tsaye tana duban motar data daukesu zata kaisu airphort harda baba,sai da suka fice sannan ta saki ajiyar zuciya,ta baya taji an rungumota,ta dan firgita kadan,sam ta mance hana tsaye gefanta,tun daga sanda yarom ya tafi yaga sauyin yanayin fuskarta,habarshi a saman kafadarta ya rada mata
"Ba ke ba,nima ina buqatan yara,zakiyi himma ki bamu namu da wuri my wife?"tilas murmushi ya kubce mata,kunya ta kuma kamata,ta soma yunqurin raba jikinsu saboda idanun mutane,duk da wajen ba gun wucewar jama'a bane sosai,amma tana iya hango eesha na tahowa da alama hanya ce ta biyo da ita ta wajen,shima sarai ya ganta,ya kuma gane abinda yasa sumayya keson qwacewa,sai ya ma sake hade fuska ya kuma janyota cikin jikin nasa sosai
"baki amsa min ba my life"
"Am ready" da sauri ya juyo da ita suna fuskantar juna
"Really?"kai ta gyada a kunyace,sai ya soma juyi da ita wajen,cikin kunnenta ya rada mata
"ki zama cikin shiri yau"sai ta sinne kanta,ya soma manna mata kisses wanda hakan yaso tsaida bugun zuciyar eesha,qara sauri tayi ta bar wajen zuciyarta na bugawa,tsaki ya ja sanda ta gama wucewan
"stupid....ki kula da yarinyar can,banson wata hulda tsakaninku" inda ta wuce din sumayya tabi da kallo sai ta maida kallonta wajensa,gira ya daga mata kafin ya raba jikinsu,cikinsa ya soma shafawa da hannunshi yana yamutse fuska
"Yunwa" ya furta a hankali,sanoda tun safe rabinshi da abinci,idanu ta zari waje,shaf ta manta
"Am really sorry don Allah,Allah na yi maka abinci tun dazun na zaci kaci na bikin ne" ta fada cikin kwabe fuska,yana son salon maganar nan tata,sai ya sake mata murmushi ba tare da ya shirya ba
"Ban haqura ba" ya fada yan akwaikwayon salon maganar tata,dariya ya bata har sai da farareb haqoranta suka fito,idanu ya zuba nata yana kallon yanayin dariyar tata cikin ban sha'awa da burgewa,sai data gama tsaf sannan yace
"Zan turo a dauka min abincin" ya furta yana takawa kan qafafunshi ya matso dab da ita
"Wuce ciki tukunna" juyawa tayi sai da yaga ta wuce ciki sannan shima ya wuce

       Qarfe biyar da rabi na yammaci aka soma shirin zuwa dauko amare,dai dai lokacin ya shigo cikin gidan,kwance ya sameta saman gadonshi,idanunta baki daya sun tasa sunyi jajur da su,kanshi ya dauke daga bangarenta,su'ad ta cancanci dukkan wani hukunci daga wajenshi,abubuwan bacin ran data yi masa ba zasu qirgu ba,bai mata yadda baba ya bata lokaci yana musu nasiha ba,da kuma yadda shima yayanka mata warning amma hakan duka bai hanata tsallakewa tayi tafiyarta ba,bugu da qari kuma saboda ta raina mishi iyaye ta dawo cikin gidansu amma babu wanda ya isa ta nemeshi?.ta lura idan batayi da gaske ba wankin hula zai kaiya dare,don wasu takaddu ya diba ya juya yana da nufin sake ficewa,da gudun tsiya ta cimmasa,ta rungumoshi ta baya tana sakin kuka,cikin turanci tace
"Kayi haquri ka yafemin,nasan na bata maka na maka abubuwa marasa dadi,amma duka kai ka janyo da aka hada baki da kai aka dauko mana wata cikin rayuwarmu" dan janyeta yayi daga jikinsa ya waiwayo yana dubanta cikin bacin rai
"Har yau baki hankali ba,duk sanda kika fahimci kinyi kuskure mayi maganar da zamuyi" ya sake juyawa da nufin ficewa,maqalqaleshi tayi bakj daya wanda hakan ya tilasta masa tsayawa,cikin kisaa ta dinga fidda kuka tana bashi haquri,bata da wata mafita data zarve hakan,tasan bazai taba iya shallakewa kukanta ba,kasancewarsa mai yawan tausayi da rashin son kuka,a hankali ya janyeta zuwa gadon suka zube baki daya,hannunshi ya sanya ya goge mata hawayen,har yanzu tana maqalqale a jikinsa,sai da gama goge matan kafin ya dora
"Tun ba yau ba na baki damarki tafi a qirga kan ki gyara,idan baki gyara ba duk abinda ya biyo baya kada kiyi kuka da ni,duk da hakan kika sanya qafa kika shure maganata,mutum nawa kika tadda a nan gidan?,su me ya cisu da suka zauna tare?,me ya gutsiresu gayamin?" Ya fadabyana zuba mata idanu,wani abu ya takoreta,haushin su ummee ya sake kamata,ta tabbatar yana mata kwatance ne da su,tilas ta bude baki a cunkushe tace
"Ba komai"
"So ki iya bakinki ki kyautata kalamanki,kada ki manta wandanda suka sanya baki kan auren su su waye a wajena,iyaye na ne wadanda ba wani abu da matsayinsa yayi dai dai da su ko mene ne shi a duniya" shiru tayi haushi na cikata,tsanar mutanen na sake cikata,itakam wlh bata ga abinda zai sanya ta fasa yi musu abinda tayi niyya ba,amma sai ta kawai ta gyada kai a sanyaye
"Amma almustapha baka daina sona ba har yanzu?,sannan kayi missing dina" murmushi ya subuce masa na gefan baki,kai ya gyada
"Duk yadda kika fada haka ne" qanqameshi tayi tana jin quncin dake ranta na raguwa
"I love u,i love u so much my dear",nan ta narke ta dinga dauka masa alqawuran sauya duk wani abu da baiso,daga qarshe ta masa alqawarin ta bar karatun zata zauna da shi,zata yi dukkan abinda yake so,daya daga cikin abinda ya sake sauko da shi kenan

      Ta jima tana kwatanta yadda zata kirashi ta sanar masa tafiyan nasu,bata son sake shiga dakin balle ta gansu irin na dazu,ba mafita dole ta soma kiran lambar da take kyautata zaton tashi ce,wayar na kusa da shi sai ya miqa hannu ya dauka,capital S ya sanyawa sunan tun wancan lokacin,sai ya daga ya kara kunnenshi ba tare da yace komai ba,sallama tayi ya amsa mata kafin shiru ya biyo baya
" amm,dama.....dama ni da amira ne zamu je gidan amaren ana tafiya"shiru ya danyi kafin ya amsa
"Kice ta wuce ta tafi,ke kuma kizo ina nemanki" ya kashe wayar daga haka,cikin mintuna sumayya ta turo qofan hade da sallama,tayi kyau cikin wani yadin material mint blue mai haske wanda aka yiwa adon baqi,dinkin doguwar riga ne wadda ke da shape na umbrella,ba qaramin kyau shigar tayi mata,ta baro mayafinta a daki bata yafa ba,hakan ya bayyana asirin jelar kitsonta da kuma baqaqen fashion data saka wadanda suka qara haska farar fatarta,duk yadda yaso ya kaucewa kallonta ya kasa har su'ad ta lura da hakan,a nutse ta qaraso tana dauke idanunta daga kansu,wani abu data tabbatar zuwa yanzu kishi ne ya riqe mata wuya,saboda su'ad na jikinsa kamar zata shige cikinsa,kanta na kafadarshi,abinda ya hanata zama kenan tana daga tsayen tace
"Gani"
"Na ganki,u look so beautiful,da da wannan shigan zaki tafi wani gidan amare?,ba inda zaki" duk da hakan bai mata dadi ba amma kishin dake cinta yafi mata zafi kan furucinsa,sai kawai ta juya tana cewa
"Ba damuwa" mamaki ya kama su'ad,taso ace ta masa musu sun fara sa'insa ya bata mata rai kamar yadda nata ran yake a bace,amma sai taga akasin hakan,kishi ya sake maqureta sanda taji su'ad na ambatar wash na gaji yake cewa ta kwanta ra huta,bai son ta qara kuka.

        Daki ta shiga ta fada kan gado idanunta na mata zafi kamar yadda zuciyarta ke mata,bata tabajin makamancin wannan kishin ba akan duka mazajen data aura har da mukhtar kuwa,sunan Allah ta dinga ambata kadan kadan har ta soma ji zuciyarta na mata sanyi,miqewa tayi ta isa gaban mudubi tana duban kanta,sai ta soma zargin kanta da zafafa kishi?,meye ne a ciki?,su'ad matarsa ce,meye ke bai miki ba kema?ta tambayi kanta,sai ta saki murmushi tana baiwa kanta qwarin gwiwa,ganin lokacin sallar magariba yayi sai ta shiga bayi ta daura akwala,ta dawo ta sake sabunta kwalliyarta ta zura haijabi ta tada sallah,bata bar kan abun sallar ba sai wajen takwas na dare bayan tayi sallar isha'i tare da karatun qur'ani saboda ta sake samun nutsuwar zuciya,ta kuwa sameta,don sakayau take jinta,bata san ya tsarin gidan nasu zai kasance ba,hakan ya sanya batayi gigin dora komai a matsayin abincin dare ba,sai data gama sallar ne ma ta shiga kitchen,cikin qanqanin lokaci ta shirya haddaden salad,ta fere abarba ta markada ta tayi lemon abarba wanda yaji flavour mai dadin qamshi.

       Tana fitowa a kitchen suka kusa karo,yana sanye da shirt da trouser dukkansu baqaqe,sun matuqar yi masa kyau,kallo daya zaka yi masa kasan cewa ya sake wanka ne,kishi na nemon taso mata ta danneshi,ya tsareta da idanu,sai kuma ya sake matsowa dab da ita,ta dan matsa baya ya sake biyota,sai da suka dangana da jikin bango,sunkuyo da kanshu yayi daidai kunnenta ya rada mata wata magana data sanyata saurin kallonshi,sai kuma ta sake yin sauri ta kauda kanta,murmushi ya saki ya kamo fuskarta saitinsa
"Me kike kitchen da daren nan" cikin cool voice tace
"Abincin darenka,amma ban sani ba ko ka qoshi" ba qarakin burgeshi tayi ba,wanu banbarakwai yake jin kansa,abinci direct ba tare da yayi oder kashe kudi ya jira an kawo masa ba
"Thanks" ya furta a sanyaye,idanunta ta watsa masa kafin tace
"Dutyn kowacce mace ne" sai ya dage giranshi yana murmushi
"Oh haka ne?" Da idanu ta amsa masa,sai ya lumshe idanunshi kafin ya bude,wannan idanu nashi na tafiya da shi,sau tari sukan so karya dukkan wata mzantaka tashi lokaci guda,su kuma tafi da nutsuwarshi.

       Yana tsaye yana duban nata suka ji takun sawun takalma,su'ad ce cikin qananun kaya riga da wando wadanda suka dameta sosai,zamewa sumayya ta danyi ta goce,sai ya bita da kallo yana fadin
"Sorry madam,zan ganku ne ke da ita"
"Yes sir" ta fadi cikin wani irin salo da ya sanyashi murmushin dole.

     Tuni hakimar ta hakimce saman kujera qafa daya kan daya,kusa da su'ad din ya zauna sannan ya kama hannun sumayya dake qoqarin zama waje daban ya janyota wanda hakan har yayi sikar fadawarta jikinshi,da sauri ta tashi tana daure fuska ta zauna kusa da shi kamar yadda ya buqata,hannun kowacce ya sanya cikin nashi,wanda hakan yayi tasiri a jikinsu da zuciyarsu baki daya
"Dukkaninku kowacce cikinku tasan cewa ita matata ce,sadaki na biya na kawo kowacce cikin gida na qarqashin kulawata da sunan matata ko?,.....to ba dogon zance zanyi ba,ku zaina lpy bana son fitina ko tashin hankali ko hayaniya duk kun sani,ba wanda zan saurarawa matuqar ya nemi tada fitina ko hargitsa zaman lafiya,saboda haka ku kiyaye" cikin dabara sumayya ta janye nata hannun kana qasa qasa tace
"In sha Allah" don ita bata ga meye abun tashin hankali ba imdai da su'ad ne,tashin hankalin da ba yau ta soma fuskantarshi ba,abu daya ta snai wannan karon babu mau fiddata daga gidan,koda QADDARARTA kuwa zata yaqeta da addu'a wadda take fatan ta sauya mata ita da iko da kuma izinin ubangiji
"Ina da magana" su'ad ta fada qunci na cika mata zuciyarta,din gani take ajinta ya fado raga raga matuqar ma qawayenta suka samu labarin ita aka yiwa kishiya
"Ya za'ayi da rabon kwana?,sannan girki kowa mai aikinshi ta masa,kuma ban lamunce mutum ya ganka ba cikin ranata" kafada ya dage gami da girarshi
"Wannan tsakaninku ne,kawai abinda na sani shine,da rana ina da ikon yin mu'amala da kowa,sannan zanyi magana da duk wanda naso,da darene zaki kwana da ni,zancan kwana kuma bibbiyu kaman naga ana yi,idan ma ba haka akeyi ba abarshi hakan" sai ya dubi sumayya
"Can i have my dinner?" Bata ce komai ba ta miqe tsam ta wuce kitchen,su'ad ta rakata da harara kafin ta maida idonta ga almustapha
"Kada kace min aninci gida zaka ci,kuma abincim waccan?"fuska ya bata yana dubanta
" bana son kowaccenku ta dinga min zanca 'yar uwarta,mind your own business" ya dauke kanahi daga gareta,rabe baki tayi har tau halin yana nan sannan ta narke fuska tana dubanshi
"Me zan ci as dinner ne dear,yunwa nake ji" yana sauya tashar dake kan t.vn zuwa wata yace
"Akwai komai a kitchen ko?,ki samawa kanki wani abu mana" idanu ta zaro kamar wadda aka sheqawa mari
"Habba dear,so kake nayi baqi,kamar wata baqauya,kawai zanyi order nan da few minute nasan za'a kawo min" ta furta tana latsa wayarta tana neman lambar gidan abincin da suka saba order idan suka zo garin.

      A nutse ta fito da komai,ta iso gabanshi ta soma shiryawa,kishi ya cika su'ad,ta rasa me zata yi ta bata ranta,ta lura kamar ma bata gabanta,bazai yiwu wata 'yar nujeria 'yar arewa wadda bata san kanta ba ta dinga bata ranta a  banza ba ba tare data rama ba
"Dear..." Ta fada a shagwabe,waiwayowa yayi ya dubeta ba tare da ya amsa ba
"Amma yau kwana na ne ko?"
"Like how?"
"Eh,haka za'ayi,ban qoshi ba dear...." Ta fada tana sakin murmushi
"But its better a fara rabawan daga gobe ko?,tunda bansan da zuwankin ba bare mu tsara haka" fuska ta bata wanda sumayyan ta lura da haka,sai ta saki murmushi tana duban almustapha,ido daya ta kashe masa cikin tausasa murya tace
"Baqonka fa annabinka,babu komai na bar matan,nima na huta ko?,jibi sai mu hadu" haka kawai yaji ranshi ya baci kamar yadda ran sj'ad din ya baci,duk da taji dadin bar matan data yi amma sai ta tsuke fuska ta hau daddanna waya,harara ya jefeta da ita ya janyo plate din salad din wanda ada yake zumudin ci amma manarta ta sanya kaso hamsin cikin dari na shauqin salad din nashi ya tafi,ganin tana niyyar miqewa ya sanyashi cewa su'ad
"Daukomin cumputer na a daki" a kasalance ta miqe,daya daga cikin abinda ta tsana ya aiketa tana zaune tana hutawa,qafa ya sanyawa sumayya dake niyyan barin wajen,ai kuwa ta fado samansa baki daya,ruqon tsauri yayi mata wanda ya sanyata jin zafi,ta saki qaramar qara
"Wa ya baki iznin yin kyauta da kwananki ba tare da yardata ba?sabida kin tsaneni" idanu ta qwalalo sannan a shagwabe tace
"Gani nayi ta fini buqatar ka"
"Ok,ke kin gaji dani kenan?"
"A..a'ah...ba haka bane bafa"
"Kin gudu ne baki tsira ba,zaki biya bashin da sai kin gwammace bakimin kyauta da kwanana ba,oya miqe kiyi feeding dina" ya fada yana sakinta,boyayyen murmushi ta saki,itakam bai dameta ba hakan,saboda tana son ta shiryawa wannan zamanne sosai,sai ta sanya su'ad ta banvance tsakanin aya da tsakuwa,zata gane matan areea ba kanwar lasa bane kamar yadda take hasashe.

     Gabansa ta tanqwashe qafa cikin wani irin salo da ita kanta bata san tana yi ba ta soma zuba masa cikin plate,baki daya ya raja'a a kallonta har baisan da isowar su'ad ba wadda ganinsu haka take jin kamar ta sanya bakin bindiga ta harbe sumayya,baisan me yasa take daukan hankalinshi haka ba,komai tayi daban yake ganinshi da na saura,hannu ya sanya ya amshi cumputer din ya budeta,kan ta gaka zuba kasa salad zuwa lemo ya soma danne dannenshu,tura plate din tayi gabanshi
"Bismillah"bai dubeta ba yace
"u seen what am doing,so feed me" ya fadi yana bude bakinshi"
"Amma rana ta ce nike da right da zanyi feeding dinka ba ita ba" tayi hanzari katse sumayya,sai kawai sumayyan ta tura spoon din bakinshi ba tare data dubeta ba,tamkar ma wani qwarin gwiwa taji ta qara mata,sai da ya hadiye na bkinshi sannan yace
"Ki bari idan kin girka naki sai kiyi feeding dina,ba adalci ta hada ke kuma ki bani,gwara ra qarasa ladan" kusan da biyu ya fadi hakan,tun ba yau ba yasha fama da ita kan ko ruwan coffe ta hada mishi amma bata taba gwadawa ba,kanta ta dauke don ita din ma tasan bazata taba yarda ta shiga kitchen da sunan yi masa abinci ba,sam ba zata iya ba,ai ranan tana jin qila sai ta kwanta asibiti an qara mata ruwa,ina zata iya shaqan qaurin abinci warin gas da zafinshi.


*YA UBANGIJIN ANNABI MUHAMMADU KA ZABA MANA SHUWAGABANNI NA GARI,YA ALLAH KANA GANINSU,KA SANSU,KASAN FILI DA BOYENSU,ZAHIRI DA BADININSU,ALLAH IDAN AKWAI MUMMUNAN NUFI DA QUDURI BOYE CIKIN ZUCIYARSU KAN BAYINKA,ALLAH KA KARYASU KARYUWAR DA BAZASU TABA DORUWA BA HAR ABADA KO WANE SHI YA ALLAH,ALLAH KAI KACE MU ROQEKA ZAKA AMSA MANA,ALLAH KAYI MANA WANNAN GATAN,KADA LAIFUKANMU SU SANYA KA SALLADA MANA SHUGABA AZZULUMI MARA IMANI,ALLAH KAYI MANA GATA ALFARMAR SHUGABA MASOYINKA DAN GATANKA ANNABI MUHAMMAD S A W*

*BANDA NI CIKIN RIKICIN ZABE,MU JEFA QURI'ARMU CIKIN NUTSUWA DA BIN DOKA,ALLAH YASA MU DACE,SAI ALLAH YA KAIMU RAN LAHADI KUMA IDAN MUN SAMU DAMA*

SUBHANAKALLAHUMMA WABI HAMDIKA,ASH HADU AN LA'ILAHA ILLA ANTA,ASTAGFIRUKA WA'ATUBU ILAIKA






*mrs muhammad ce*👑✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



9⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah S W T yana cewa*

*HAQIQA DAN ADAM MAI YAWAN ZALUNCI NE MAI KUMA BIJIREWA*
______________________________________



Sai da ta kammala bashi sannan ta tattare dukkan kwanukan dake wajen tayi kitchen da su,ta tsaya ta daurayesu ta maidasu muhallinsu,daga kitchen din ta lallaba ta shige dakinta,fin bata son komawa cikinsu,bata ga ma amfanin komawar ba baki daya,sai data shiga toilet ta sake wanka,ta sauya kayan bacci sanda ta nufi gadonta.


Shiru tayi saman gadon ita daya,juyi ta dinga yi daga wannan bangare zuwa wanacan,baki daya dakin yayi mata girma da fadi,ta manta yaushe rabon ta xa kwana ciki daya ita daya kamar haka?,qwan wutar lantarkin dakin da aka kunna shi ya sanyata yin firgigit ta daga kai,almustapha ne tsaye bakin qofa harde da hannahenshi,sanye yake da kayan bacci ruwan hoda kalar da su'ad tafi so kenan,sun masa kyau sun haska kalar fatarshi,idanunshi a kanta ya dinga takowa a hankali har ya qaraso inda take,shigowanshin bai sanyata tashi zaune ba,tana daga kwancen take kallonshi irin kallon qasan idanun nan,wani abu ke sukan zuciyarta.


Kai tsaye gadon ya hauro bai bata lokaci ba ya danneta ya aza mata nauyinshi,murya qasa qasa yace
"Baki damu da ni ba ballantana ki tsaya muyi sallama ba ko?" Qoqarin tureshi take ta miqe saidai ta kasa,cikin nishi tace
"Ba haka bane,bacci nake ji shi yasa" dagowa yayi yana duban fuskarta yayin da taqi yarda ita din ta kalleshi
"Uhummm,yaushe kika fara qarya?,ko dama can maqarayaciyar ce,idan bacci kike ji me ya hanaki yi yanzun?"
"Akwai abinda na tsaya yi ne" dagata yayi yana 'yar qaramar dariya
"Gaskiya ne,coffee nazo ki hadamin in sha kafin na kwanta" ya ambata yaba gyara wuyan rigar baccibsa wadda ke da V shape,dagowa tayi ta dubeshi
"Amman ita yafi cancanta ta dafa makan,tunda gunta kake" ta fada tana qoqarin hadiye kishin dake taso mata,eh tabbas ya sani ita zata dafa din,amma shi kansa yasan wasa ne ma,ta yaya su'ad din zata iya wani dafa mishi coffe koda ta iya bayan yasha wanka ta harde saman gado tana jiranshi?,hasalima ita ta bashi daman ya kira masu aikin gidan su dafa mishi
"Bazan samu ba kenan?" Kai ta kada tana yunqurin sauka daga kan gadon,binta yayi da kallo,kayan duk da na bacci ne amma sun amsheta sosai,ta sake kyau a idanunshi,saukowan shima yayi ya biyo bayanta,ta dora hannun saman hijabinta da niyyar sanyawa ta fice ya riqe hannun nata,dagowa tayi suka hada idanu
"Muje na rakaki kitchen din,a haka nake son ganinki" ba musu ta saki ya sanyata a gaba suka fice.


Cikin kitchen din yana tsaye jingine da freezer hannunsa harde a qirjinsa,duka motsinta da kaikawonta idanunshi na kanta,komanta a nutse a tsaftace abun burgewa,ta gama komai ta zuba cikin dogon cup wanda yake da riqe zafi ta miqa masa,hannu biyu ya sanya ya amsa yana murmushi,tun kafin yasha din kwadayi ya kamashi,qamshin ya cika masa ciki,baisan yau wanne kalar coffe tayi masa,ganyayyakin da yaga tana hadawa dabanne
"Thank you" ya furta a tausashe,har cikin zuciyarta lafazin ya sauka,sai ta samu kanta da maida masa martanin murmushinsa
"Albarka nake son ka sanyamin" ta fada a kunyace,murmushinsa ya fadada
"Qwarai albarka tafi lafazina na thank you,Allah yayi miki albarka" ya maimaita har sau uku tana amsawa da amin,gaba ya sake sanyata suka fice,sai dayaga ta shige corridor dinta sannan ya juya ya haura sama da tea din hannunshin,don a bedroom dinta na qasa tayi kwanciyarta bata ma yi sha'awar hawa na saman ba.

***** ****** ***** ****


Misalin sha daya da rabi ne na safiyar washegari,yana tsaye

Please Login or Register in order to submit comment