Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

NA QUNGIYAR HASKE HARMA WANDA BA NA HASKE BA,SHIN KUNA DA BUQATAR JIN WANI SABON KUNDI WANDA YA TATTARE LABARAI NAU'IN DABAN DABAN WADANDA SUKA SHAFI AL'AMURA NA ZAHIRI DAKE FARUWA CIKIN RAYUWARMU TA YAU DA KULLUM?.......TO MAZA KU GARZAYA KU NEMI LITTAFIN KUNDIN HASKE,WANDA KE QUNSHE DA LABARAI DAKE DAUKE DA NAU'IN RAYUWA IRI DABAN DABAN,LABARAI NE WANDA KE DAUKE DA DIMBIN DARUSSA MASU RATSA ZUKATA,DUMBIN ILIMI MAI JAWO HANKALIN DAN ADAM ZUWA SAKE LURA DA GYARAN RAYUWARSHI,MAZA KA/KI GARZAYA KADA A BAKI LABARI,BA SHAKKA ZA'A CI DA RABONKI MATAUQAR KIKA BARI YA WUCEKI,AKWAI SHI A WATSAPP DA APP DIN WATTPAD BAKI DAYA*


*SADAUKARWAR WANNAN SHAFIN GA:*

*SADIYA ZABURA*
*UMMU RAMLAT*
*MAMAN SAYYID*

*DA MARUBUCIYA*

*AYSHA DAN SABO*

*RABBI YA BAR QAUNA*🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽🤝🏽😍😍😍







       Kyawawan idanuwanshi wanda suka wadatu da gashin idanu kamar yadda girarsa take masu kama da na wanda ke jin bacci suke kan ta,shi daya ne tak sanye cikin qananun kaya sabanin dukka sauran wadanda suke tsaye tare,baki dayansu shadda ce jikinsu dinkin tazarce kaloli daban daban,kusan tare suka janye idanuwansa,gabanta ya shiga faduwa,kasa zaman wajen tayi,batasan ana iya gajin mutum ba,gashi ko mayafi babu a jikinta,sai ta miqe jikinta na rawa gabanta na faduwa ta bar wajen,ta tura qofar ta kulle ta dawo cikin bedroom din anty dijen.

      Gefan gado ta kwanta rub da ciki tana sauke numfashi,maganganun baabaa suka soma dawo mata,har yau ta kasa gane me yake nufi,tana da buqatar qarin bayani,tana buqatar taimako wajen wanu ko zata fahimci me yake nufi,amma ta taimaka masa wajen gyara rayuwarsa kamar yaya kenan,wanu mummunan abu yake mara kyau yakeso ta saka baki?,amma ita a wa?,bata da wannaj power din,ganin qwaqwalwarta na neman daurewa yasa ta kada kai tare da yin watsi da maganar,maimakon ci gaba da tunani sai ta sake daukan wayarta ta lalubi zainab ta kirata,din jiya suna wajen dinner taga misscall dinta baya kuma samu ta bita ba.

        Bayan sun gama gaisawa da mama ta musu Allah ya sanya alkhairi zainab ta karba,nan take gaya mata jiya aka kawo lefe sati uku kuma aka sanya,murmushu sumayya ta saki tana tsokanarta
"Kice mu fara shirin tahowa kano ko?"
"Wallahi yaya,kizo ayi tsare tsare masu kyau"
"Insha Allah,ina huce gajiyar wannan bikin zaki ganni,Allah ya nuna mana da rai da lafiya"
"Amin yaya,ina abdallah na"
"Uhmm,ni kaina bansan ina yake ba,yana gidan biki"
"Ki gaisheshi tunda ya manta da mu" dariya ta danyi
"Zaiji,ki gaidan halimaty,wayarta bata shiga"
"Zata ji" suka katse wayar.

       Tana sauke wayar ta jiyo muryar abdallah yana karadi daga qasa shi da sh hafiz,sauka tayi daga gadon ta sauko qasa,yayi masifar kyau cikin wata arniyar shadda ash wadda batasan inda ya samota ba,hulace kanshi zanna wanda sau faman zuba qyalli take,qafafunshi saye da takalmi sau ciki,abinka da uwa da da,yana ganinta ya tako da gudu ya daneta,murmushu tayi ta zube saman kujera yana faman zuba mata surutu da bata labari.

        Ganin sha daya tayi ga gidan babu kowa sai ita ya sanyata yin shahada ta yafa mayafinta ta fito,kamar zata nutse haka ta dinga ratsa mutane a darare tana wucewa har ta kai ga cikin gidan bayan ta kira humaida ta gaya mata inda suke,ko ina harabar gidan 'yan uwa da abokan arziqi ke kai kawo,kowa ka ganshi cikin kwalliya da walwala,daga gefe guda ta hango mahmoud da tarin abokansu ciki har da alqasim,suma sun ganta saboda haka ta qara sauri don kada su rusketa.

       Batayi aune ba sukayi karo kanta ya daki qirjinsa,tayi taga taga ta komo ta fada qirjinsa,zuciyarta kamar zata fito saboda tsoro,tayi yunqurin janyewa,ta samu nasara saidai hannunta na cikin nashi hannun yana duban qwayar idanuwanta,sai yanzu ya samu amsar inda ya samu qamshin da ya buwayeshi tun shekaran jiya,wanda har kuka su'adah tayi sabida jin qamshin,don ta tabbatar hadin humra ce ta mata ta musamman ba turaren namiji bane,gaba ta tusashu tana tambayarsa ina ya samu turaren,baki daya zuciyarta ta gama zayyana mata yana neman wata ne,idan banda haka ina zai samo turaren mace a hannunshi?baya ga haka ta lura wannan karon sam baya marmarinta,baya nemanta idan ba ita ta buqata ba,bayan a baya ta sani cewa duk sanda suka hadu har sai ta gaji ta hada kayanta ta gudu yake qyaleta,amma wannan karon sam ba haka bane,yana jinta yayi mata banza ya gama shirin baccinsa ya kwanta tare sa juya mata baya,don bashi da amsar bata,shi kansa yana jin qamshin cikin hancinsa amma baisan inda ya sameshi ba,baijin zai iya bata lokacinsa ya mata wannan bayanin tunda har tana zarginsa,to ta dauki duj hukuncin da take gani zata iya dauka,hakan ya sake hassala zuciyarta,itama ta shiga fushi da shi gadan gadan miqe ta fice ta sauya dakin kwana,bata san cewa ba shi ta yiwa ba kanta ta yiwa,tunda ba yau farau ba da yake kwana shi daya tamkar gauro,idan da sabo ai ya saba.

       So take ya sakar mata hannu ko don idanuwan mutane da ke kai kawo a wajen,uwa uba ga haramci na riqe mata hannu da yayi,tayi yunqurin zame hannun nata amma abu yaci tura yana tsaye qyam yana dubanta,babban goro sai magogin qarfe,ya kusa lullube tsahonta baki daya,dududun nata tsawon bata fi iya qirjinsa ba,ga wani kwarjini daya cika wajen,ganin masu wucewa sun soma ankara ya sanyata cewa
"Ka sakar min hannu" cikin izza da motsa labbansa
"Saikin gayan abinda ke baki tsoro,me ya koroki bayan kowa na kai kawo a nutse amma banda ke?" Daga fararen idanunta tayi ta watsa mishi su,duk da yadda qirjinta ke bugawa,lumshe idonsa yayi ya bude ya janye nashi idanun daga kallonta,bai taba ganin mace mai farin qwayar idanu ba kamar haka ya raya a ransa,tsaki yaja a fili sannan ya saki hannun nata
"Ki kula next time,ban son irin wannan shirmen" ya fada yana duban gefanta,ita ke shirmen ma?,abun ya bata haushi,sai ta banka masa harara ta gefan ido duk da yadda gabanta ke faduwa qasa qasa tace
"Kaima sai ka kula tunda kana da idanu ai ba ni kadai ke da idanuwa ba" batasan tayi kuskure ba saboda kaifin ji da Allah ya hore mishi,ko yaya magana take yana iya jiyota,yana daya daga cikin wadanda Allah ya yiwa baiwar ji,har wani lokaci ba'a iya gulmarsa matuqar yana cikin gidan,har yayi gaba ya juyo a mamakance yana dubanta,karo na farko kenan da wata 'ya ta taba maida masa magana,bakinta ta murguda duk don ta sake bashi haushi tayi gaba abinta,wani abu ya tsaya mishi a rai,ranshi ya baci,yau shi akewa rashin kunya?,abinda yafi tsana kenan a rayuwarsa tun lokacin quruciya,abinda ya fara hadashi kenan da su'adah tun tana qaramarsa,lallai zaiyi maganinta,wace ita da har take jin karanta ya kai tsaiko,babu shakka sai ya hukuntata.

      A bangaren anty maamaa ta tadda su,tana zaune tsakiyar yayunta anty farida da anty huda da matan yayyen ta ni'imah da fahariyya,sai qawayenta da cousins dinta irinsu eesha humaida ummu salma da sauransu,a hankali ta qaraso saboda lasalar da take ji cikin jikinta tana karbar saqon harara daga amira,duk da haka murmushi ne kan fuskarta,ta riga da ta sani itace mai laifi,sauran da suka san mekw faruwa dariya suka dunga yi sunsan za'a kwashi daramer,amma sai sumayya ta kashe mata gwiwa da fadin
"Ta zama ta saifullahi,ayya yarinya zata bar gida" ai kuwa sai ta soma qwalla,tana dariya ciki ciki ta qaraso ta zauna gefanta ra mata rada a kunne ma tsawon minti biyu,sau gani sukayi ta saki dariya tana share hawayen,huda ce taja tsaki
"Au qaryar banza,dama fa son aurenta take 'yar banza bansani bane,saifullahin da ake ji da shi kamar a lashe mishi mazaunai" dariya ta kamasu baki daya,dqi dai da dai dai sumayya ta bi ta gaida kowa,batasan matan yaya adam ba sai lokacin ni'imah da fahariyya,fahariyya ita ta fara tahowa ni'imah ta jira maigidan sai jiya suka taho tare da daddare,bata ga fahariyyan ba saboda 'yar jin kaice itama kamar yadda amira ke gaya mata,ni'imah din ce babu ruwanga,hakanan take haquri da halayyar fahariyya na goranta mata da take lokaci lokaci akan rashin haihuwa,saidai zaman nasu babu yabi ba fallasa,rashin mutuncin fahariyyar da sauqi sakamakon cewa adam din tsayayyen namiji ne,bai yarda a wulaqanta masa uwar gida ba,sam basa shiri da su'adah da fahariyya saboda kowacce na jin kanta da jin cewa ta isa saidai daya tabi daya,duk da a zahiri duk cikin yaran gidan babu wanda ke da dukiyat almustapha,wannan ya qara kishin su'ad cikin zuciyar fahariyya,itakam ni'imah 'yar babu ruwa na ce,ta kama mutuncin kanta,don iyayenta ba wasu bane rufin asirin Allah ke garesu,sai a yanzu da tayi dace da miji na qwarai suke samun sauyin rayuwa sanadiyyarsa,duk da haka dama tana da managartan halaye wadanda su suka fusgi adam zuwa gareta,duk da tarin yaran masu kudi dake sonshi a lokacin,ta kasance ta daban a gunsa har a yanzun duk da bata taba haihuwa da shu ba,sakamakon haquri biyayya da tsantsar iya zamantakewa da miji mai tafiyar da hankali.

        Da daidai suka miqe suka fice ya rage saga sumayyan sai anty ni'imah sai humaida,suma sun maqale ne saboda suna kwasar wasu sirrika da lacture da anty ni'iman ke bawa amira,wanda baga fara ba sai bayan da wadancan suka fita,ba amira ba hatta su sumayya sun qaru da ita sosai,a nan suka zauna suka ci gaba da hirarsu,ni'imah ba dai sauqin kai ba,kamar qannenta haka ta daukesu,aqalla zata girme musu da kusan shekaru goma,amma sam hakan bai wani nuna ba sosai sabida tsabar gayu.

      Qarfe bakwai na magariba aka tafi kai amarya,babu wani takura ko neman mota kasancewar kusan kowa ya mallaki motar hawanshi,wanda ya taho daga wani garin ne bai taho da abun hawanshi ba sukayi amfani da motocin gidan baabaa,ga kuma ta familyn saifullahi.

       Ba shakka wannan shi ake kira qwarya tabi qwarya,ba shakka amiran ta shiga gidan da yayi dai dai da ita,gidane na alfarma wanda ke tafiya da tunanin mai tunani,sanda aka fara tafiya amiran ta riqe sumayya gam kan sai ta jira anzo an sayi baki,sun riga da sun gama tsarawa babu batun siyan baki,ko akwai din ma ita batajin zata tsaya,saboda mutum biyu daga cikin abokan saifullahi da suka uzzurawa rayuwarta tun ranar kamu,ta musu qaryar a niger take,saboda haka bata son su hadu bare su takura ta,dabara tayi mata cewar bari taje tayi fitsari daga haka ta arto gida.

      Biki ya tashi lafiya,ummee da kanta ta yi ma sumayyan godiya tare da godiyar kayan humra data yi mata wanda su aka jerawa amiran ma,kunya ce ta kama sumayyan,duka duka me tayi,su basu duba tarin karamcinsu wanda ya kai ga cancantarsu kan yi musu komai.

       Tun a daren ta kashe wayarta kwata kwata,don ta tabbatar cewa gobe kamar da qasa sai amira ta nemeta,jikinta ya gaji tubus irin gajiyar da bata taba yin irinta ba,lallai biki ba wasa bane,tunda ta kwanta bata tashi ba sai da gari ya waye,ta makara sallar asuba,don sai shida da rabi ta yita,tana gamawa ta koma ta sake kwanciya,ba ita ta farka ba sai sha biyu saura na rana,yunwa ta sadakarta,a guje tayi kicin ta tadda anty dije na soya miya qamshinta ya cika gidan baki daya,ba magana ta mata nuni da kayan break dinta dake ajjiye gefe,tana kaiwa baki daya yiwa antyn sannu da aiki
"Ai ke zanwa sannu,yaran nan sunso tadaki badon ma hanasu ba,shi yasa da abbansu zai fita na hadasu da shi ya kaisu wajen inna(kakarshi)"
"Kai kina ji da ni anty na" ta fada tana jan kujera don ta ji dadin cin abincin sosai
"Ba dole ba,kece fa babbar diya" suka sanya dariya baki daya sannan suka ci gaba da hira suna tattauna wasu daga lamuran da suka faru yayin bikin,antyn na juye miyar cikin warmer tace
"Ai ke kam bakiga hutu ba,saura sati uku a shiga wani bikin"
"Wallahi anty shi yasa nakeso nayi kamar kwana uku haka ina bacci,don so nake next week na wuce kano" hararata antyn tayi
"Dama na sani ai,ke kam garin nan kamar yana mintsininki,gidan fa baki daya baya dadi wallahi idan kika tafi,hatta da abbansu ya dinga mitar kin dade,amma wani lokaci sai na rayawa a raina dole fa mu saba tunda wataran zaki aure,idan kika tafi kuma ya zamuyi" shiru sumayyan tayi taci gaba da kurbar tea,saboda anty dijen ta kawo zancan da bata qauna cikin hirar tasu,sai data gama sha ta sure cup din tana goge hannunta sannan tace
"Anty,wata tambaya ce da ni"
"Uhmmm,Allah yasa na sani" shiru ya danyi tana tsara yadda zata jefa mata tambayar kafin tace
"Wai idan wata ko wani yazo ya cewa budurwa ki taimaka ki gyara rayuwar wane,wai me hakan yake nufi?" Waiwayowa tayi ta kalleta har sai da gaban sumayya ya fadi,Allah yasa ba wani mummunan abu bane,kamar antyn ta tambayeta wa ya fadawa wani hakan sai kuma ta fasa,taci gaba da aikinta tana bata amsa
"Maganar na da ma'ana bangare biyu,nq farko idan har aka fadi haka ga wani ko wata makusanciya ta mutum ana nufin ta dinga bashi shawara da hanashi aikata wasu abubuwa,ko kuma wani abu na son faruwa da shi ana son ka taimaka kada ya fada cikin wannan abun,sannan ma'anar na iya daukan AURE ko SOYAYYA,abun nufi.......shi wanda ya gaya miki maganar yana ganin kamar kina da wasu qualities da wani namiji ke buqata,wanda wannan qualities din zau taimaka masa wajen gyaruwa ko ingantuwar rayuwarsa,babu kuma hanyar da zaki gyara ko ki inganta rayuwar tasa sai ta hanyar AURENSA ko yin SOYAYYA da shi,to sai a baka maganar a dunqule" tunda ta dauko maganar gaban sumayyan ke faduwa
"Da gaske baba na nufin kenan ta auri almustapha?,abinda baabaa ke son fadi mata kenan" kai ta shiga girgizawa cikin zuciyarta ta soma furta
"La haula wala quwwata illa billah,Allah ka sani ina ganin qima da darajar wannan bawa naka,ya Allah ka fidda masa wannan tunanin daga zuciyarsa a kaina,ka jefa masa tunanin wata,Allah kada ka bashi iko ya tambayi abinda bazan iya masa ba"
"Ke sumayya meye haka?" Inji anty dije ganin yadda take kada kai tana mus mus da baki,murmushin yaqe na musamman ta qaqalo sannan tace
"Ba komai,kawai ina mamakin yadda muka kasa fassarar maganar,wani ne ya gayawa wata" ta fada tana miqewa tsaye sannan ta fice daga kitchen din,da kallo anty dije ta bita,cikin zuciyarta tana addu'a,Allah ubangiji ya sanya sumayyan tayi gamo da miji ne dan gaske,wanda zata huce takaicinta,babu shakka zata so za kuma tayi burin sumayyan tayi auren da zata huta ta sanadiyyarta,juyawa tayi taci gaba da aikinta tana addu'a cikin ranta.

        A sanyaye ta zauna bakin gado maganar na sake y mata yawo,indai haka ne ba shakka dole ta qauracewa haduwar ta da baabaa,kai ya zame mata jazaman tafiya kano,kuma bata jin zata dawo nan kusa idan ta tafi din,zata yita qirqiro dalilai ne wadanda zasu zaunar da ita a can.

       A daddafe ta haqura ta kai ranar alhamis kamar yadda ta gayawa anty dije,sannan ta shirya tafiya,wanda ya rage sauran kwanaki goma sha hudu bikin,anty dije ta bata saqonni gun mama sannan tace suma nan da kwana bakwai suna tafe,wannan karon saboda tsabar zaquwa ta tafi bata iya jira abban laila ya dawo daga kaduna da yaje ba ya hadata da driver,motar haya ta hawo ta tafi,ba yadda anty dije bata yi ba amma ta kasa daurewa ta jira.

        Tana hanya taji kira,lambar amira ce,tun kafin ta daga ta saki murmushi
"Amaryar saifullahi bada kanki a sare" kamar wadda ke shirin sakin kuka ta soma mata qorafin kota nemeta ko?,sun hada baki da saifullahi sun sace mata wayarta,shi din ma ya rufe gidan ba shiga ba fita wai sai sun huta,ya kuma hanata wayarshi sai yau ya bata wayan,dariya ta dinga mata din yasan da wannan plan din,sai da ta gama qorafinta sannan suka gaisa tace yaushe zata zo don Allah
"Kin ganni hanyar kano,wani bikin ya sake kira na,bikin zainab dita"
"Wayyo,dama a kusa da namu ne,naci burin zuwa fa namecy" dariya tayi
"saidai ki tara ana halima idan Allah ya kawo"haka nan suka gama hirarsu ta baiwa saifullahin suka gaisa sannan sukayi sallama.

   Kamar ko yaushe sunyi murna da zuwanta,mama nata tsokanar abdallah wai ya qara qiba
"Amma dai zaka koma ko?" Wuya ya maqale a kafadarsa
"Nan yafi dadi,can kullum kuna rufe a gida" dariya suka saki don abdallahn badai son yawo da wasa ba,hararshi sumayya tayi
"Nima babu inda zaka bini,rigimammen kawai" ko a jikinsa dariyarsa ma ya sanya abinsa,washe gari yaya yahansu tazo ta daukeshi ma sukayi tafiyarsu,sai ranar kamun zainab tace zata dawo da shi.

       Tunda tazo babu zama suna ta shirye shirye ba kama hannun yaro,ita da anty salma qanwar mama da anty amina matan yaya abubakar,sunyi waya abdur rahman bai nan amma zai dawo da shi za'a yi daurin auren shi yasa take hidimarta hankali kwance ba wani damuwa ko takura,cikin ikon Allah da baiwarsa komai yana tafiya daidai,sumayya taga yadda ake komai cikin tsari saboda haka ta dage ta tsarawa 'yar uwarta komai yadda zai qawatar ya kuma burge,kudi sosai tasa yaya abubakar ya bata bayan wanda anty dije da uncle farouq suka bata,dinkuna sosai ta yiwa mama,atamfofi masu tsada da kyau,harda mayafai da takalma duk da yaya abubakar yayi musu amma tace wannan nata ne,sannan ta siyawa malam gezna ta asalin wadda zai sanya ranar daurin aure,takalmi mai kyau harda agogo da turare da sabon rawani fari qal,kasancewar malam din ba baya bane wajen tsafta shi yasa kusan kayansa galibi farare ne,aka yi masa dinkin babbar riga 'yar ciki da wando,ita kam dama bata da matsalar sutura sai anko kawai data yi,sai abdallah data masa shaddar daurin aure duk da dumbin kayan da yake da su,saura kwana tara biki kuwa saiga anty dije da iyalinta,nan aka shiga hidima sosai.

      Kan hanyarsa yake ta dawowa daga airphort bayan ya kai anty dije da yaranta sun tashi zuwa kano,tun daga nesa yaga kamar motar baabaa prof a tsaye,hakan ya sanya ya rage gudun motar ya qaraso a hankali ya faka tashi motar bayan tasu sannan ya bude ya fito.

      Baabaan ne tsaye gaban motar,kana dubanta kasan matsala ta basu,qarfen nasara da bashi da tabbas,motar kwata kwata shekararta guda,ba yadda mustapha baiyi kan a canzata ba kamar yadda ya saba sauya masa motocin hawanshi amma yace a sauya sauran amma ita banda ita,yana jin dadin motar,da ita yake zuwa gidan gonan sulensa duk qarshen sati,duk randa zai tafin baya tafiya da wasu motocin face wadda ita kadai zai hau,kuma daga shi sai druvansa,yana jin dadin zama gidan gonar,ya zazzaga yaga gidan gonar sosai,yanajin nishadi da farincikin yadda dukiyar sulensa ke habaka,fatanshi Allah nuna masa ranar da zaiga sulenshi,a irin haka ne yau motar ta tsaya musu a hanya.

       A aladabce uncle farouq ya qaraso
"Subhanallah,baba kada dai ace qarfen nasara ya muku tsiya?" Cikin murmushi mai dauke da dattako yace
"Wallahi kuwa,to ya za'ayi,yau da gobe ai sai Allah,babu wani abu dake matabbaci"
"Gaskiya ne" inji uncle farouq yana fidda waya daga aljihunshi yana fadin
"Bari a kira gida to a turo wata ko baabaa,tamu motar ba lallai ka iya shiga irinta ba" murmushi ya kuma subucewa baban,har ya sanyashi ya juya ya sake kallon motar duk da ya santa,motace mai lafiya wadda bata da wani aibu ko makusa,ko kai waye zaka iya hawanta,amma ya sani cewa irin motocin da mustapha ke ajjiye masa yana hawa shi ya sanya farouq din tunanin yafi qarfin wannan
"Haba faruqu,saidai kawai idan rawar hawa motar take kake min,amma ni din waye da bazan hau wannan motar ba" ya fada yana dariya,bakinsa ya rufe shima yana dariya
"Afuwa baabaa" ya fada yana bude masa gaban motar,kafin ya shiga ya waiwaya ya dubi drivan nashi
"Kada ka tsawaita tsaiwa a nan,ka kira bakaniken nan,idan bakaniken ya iso ka bashi muqullan ka taho gida" a ladabce yace
"Yallabai man yace kada a sake barinka ka hau motar da baniken hanya ya tabata ranka ya dade" murmushi ya saki
"Qyale wannan,idan na biye masa ma a jirgin sama zan dinga yawo,ni waye da bakaniken hanya bazai taban mota ba,shi yasa na hana a kira gida agaya musu motarmu ta tsaya nasan zai iya jin zancan ya damu mutane da batub sauyan motoci,bayan ni din duka kwana nawa ya rage mana a duniya,kayi yadda nace kawai"
"To ranka ya dade" inji drivan,baban ya juya ya shiga motar faruqun ya rufe ya zagaya shima ya shiga ya tadata suka fara tafiya.

       "Asalina daga qauye na fito faruqu,kiwon dabbobi  na dinga yi ni da aminina,da can ko jaki bani da shi na hawa bare a kai ga mota,din me zan dinga manta asalina,ita duniya gaba dayanta yadda ka dauketa haka take zuwa maka,mafi daraja cikin mutane shine wanda a zahiri ya isan amma yake daukan kanshi ba'a bakin komai ba,girman kai rawanin tsiya ne,wanda ke zaton ya isa kuma sai Allah ya qasqantar da shi a duk inda baiyi zato ba" kai uncke farouq ke gayadawa cike da gamsuwa,tsohon dattijon qwarai ne,yana bala'in son zama da shi saboda dole ka dauki darasin rayuwa,idan ya shiga cikin wasu baka isa kace shine wannan professor din ba,kuma tsohon jakadan nijeria a qasar amurka.

      Danja ta tsaidasu uncle farouq yaci burki da sauri saboda yana dan gudu,wanda hakan ya sanya katinan dake zube gaban motarshi suka zubo,jiya ya karbosu shi yasa aka yiwa malam su na daurin auren zainab ya baiwa anty dije ta tafar mai da su ragowar ya ajjiye wajansa zai bawa kawunshi
"Bismillahi" malam ya fada yana cewa
"Kaima ashe kana dan taba irin tuqin almustapha kenan ko?" Ya fada yana murmushu tare da duqawa yana kwaso katinan sa sukw zube din.

       Caraf idanunshi suka kai kan sunan dake jikin katin wanda ke qunahe sa sanarwar daurin auren SULAIMAN AMINU DAHIRU GOMBE,sake maimata sunan yayi,sunann da ya kasance sak irin na tsohon amininshi sule,tsohon aminin da kullum zuciya ke begen ganawarsu,maimaita sunan ya dinga yi tare da kallon rubutun da aka tsarashi kalar golden,tamkar zai gano masa da zargin da zuciyarshu ta fara yi,uncle farouq ya lura da hakan sai yace
"Bikin qanwar mai sunan mama ne,wato 'yar yayar khadija" wawiyar ajiyar zuciya ya sauke ya maida dubanshi ga farouq
"A ina suke faruqu"
"A kano suke"
"Kano?,meys asalin mai gidan" kai ya girgiza cikin kokwanto
"Bamu taba zancan gaskiya da ita ba,amma dai a kano na sansu,wani abu ne baabaa?" Kai ya kada yana maida katinan mazaunansu
"Sunan ne kawai ya yimin kama da na wani tsohon aminina wanda har yau nake neman bayan ya bata tsahon shekaru"
"Ayyah,Allah ya bayyana shi"
"Amin amin faruqu". Bai bar babaan ba sai daya dangana da shi har cikin gidan sannan baabaan ya sauka yaba masa godiya,kunya duk ta kama faruqun,a rayuwa babu wani abu da zaiwa baban da har zai masa godiya,bayan babu wani nau'in karamci da kyautatawa da baban bai masa ba tun daga sanda ya sanshi har zuwa yau.

      Tunda ya koma gidan baki daya ya kasa sukuni,katinan da sunan sun tsaye masa a rai,daren ranar kasa cikakken bacci yayi,yayi salloli sosai kafin ya samu bacci yayi awon gaba da shi,da asuba da ya tashi da abun ya tashi cikin ransa,har gari yayi haske,sai kawai ya tsinci kanshi da jawo kiran wayar uncke farouq ya buqaci adress din gidan mamallakin sunan da ya gani jikin katin,babu haufi ya tura masa don baya shakka cikin nagartan baabaan,yasan cewa koma mene alkhairi ne IN SHA ALLAH.

        Waya kawai ya sake dagawa,ya lalubi lambar mahmoud ya buqaci ganinsa,ba bata lokaci ya iso kasancewar yana cikin gidan,sanar masa yayi ya laluba idan akwai jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano ya yankar masa ticket guda hudu,shi daya mahmoud din daya mus'ab wanda yazo biki bai koma thailand ba,da kuma drivansu,bai wani mamaki ba saboda yasan lokaci zuwa lokaci baaban nasu nayin tafiya kota ziyara ko duba gidajen gonar wannan babban aminin nashi da tunda suka taso suke jin sunanshi suka kuma haddaceshi,tare da riqe girma da matsayinsa wajen babansu,lokaci lokaci sukan yi bita da tilawarsa,saidai har kawo yanzu idanuwa basu taba ganinshi ba,cikin sa'a aka samu jirgin azaman wanda zai tashi ne da la'asar qarfe hudu na yamma,ba haka baban yaso ba amma haka ya karba.

        Qarfe hudun jirgin ya lula da su sararin subhana zuwa kanon dabo,wanda cikin mintuna suka isa cikin yarjewa da ikon ubangiji tare da sahalewar ci gaban zamani irin na yanzu,kano tamkar gida take

Please Login or Register in order to submit comment