Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaben duka mutumin daka ga dama,quri'arka zata iya zama sanadin jin dadi da walwalar al'ummar qasarka,hakanan zata iya zama silar shigarsu qunci,saidai kar ka manta da wannan,RANAR QIYAMA ZAKA TSAYA GABAN MAHALICCINKA KA BADA HUJJARKA NA DALILIN ZABAR MUTUMIN DAKA ZABA DIN,kada ka manta tsayawa gaban wanda ya halicceka babban lamari ne,mu tsaya mu zabi shugaba na gari,wanda zaton alkhairin da al'umma suke masa ya rinjayi na sharrin,MU ZABI CANCANTA BA JAM'IYYA BA,hakanne kadai zai sanya mu saka qwarya a gurbinta,kada mu yarda wasu su shiga rigar jam'iyya su cucemu,mu duba cancanta da dacewa,mu yiwa kamu alqalanci,kada mu jefa kanmu a fitina da musibar da bamusan ranar qarewarta ba,Allah kasa mu dace ka yi mana jagoranci kada ka barmu da iyawarmu*

*muyi zabe lafiya cikin aminci da kiyayewar mahaliccinmu*








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣6⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*Allah madaukakin sarki yana cewa*

*haqiqa muminai 'yan uwan juna ne kuyi sulhu tsakanin 'yan uwanku*
_____________________________________


           Qarfe uku saura na rana suna zaune bayan motar driva na jansu,tattausan tafin hannunshi na cikin nata,yana zaune gab da ita sabanin daa da kowa ke zama tashi shiyyar,kunya ta sanya ta maida kanta bangareb window tana duban hanya cikin baqin glass din da motar take da shi,yatsunsa ya sanya ya juyo da fuskarta gareshi,ya dage gira daya
"Ina son miki qari kan abinda na fadi miki dazu,zayyano min naji kin haddace?" Wata iriyar kunya ta kamata,ta yaya zata iya maimaita kalaman dazu masu nauyi da girma,kanta ta qwace daga hannunshi ta sake maida kanta ga window murmushi na son kubce mata,ganin haka ya sanyashi janyota jikinsa ya sanya hannu ya matseta
"Maganinki zanyi,naga alama baki fara daukan lacture ko daya ba,yadda nake daban haka nakeson matata ta zama ta daban,you must be ready,qarin karatu guda daya,dole ki koyi zama a jikina,bazan lamunci zama a mabanbantan wurare ba ba,idan baki son haka ki daina zama waje daya da ni" ya fada yana shan mur,baki ta murguda wanda yayi nasaran hangota,cikin zuciyarta tana mita,wuta ce ta dauke mata sanda taji hannayenshi cikin rigarta,ta daga kai ta dubeshi tana narke fuska,idanunshi lumsassu ya zaro mata waje yana mata nuni data daina kallonshi,tilas ta sauke qwayar idanunta,tana ji tana gani haka ta haqura ya dinga yadda yaga dama da ita,sai da yaji tsaiwar motar sannan ya zare hannunshi da jikinshi,hannun nasa ya sanya ya gyara mata rigarta da yafen mayafinta,wanda atamfa ce a jikinta ta dora mayafinta saman ka,kanta na a qasa cike da jin nauyi har ya kammala,bata dago ba sai da taji yace
"Oya,lets go".

        Tayi zaton ganinta a airphort sai ta gansu cikin wani makeken guri wanda yaso yi mata zubi da gida,mutane ke kai kawo,kama daga qananun yara saffa saffa da kuma manya,yana fitowa wasu tarin ma'aikata suka qaraso wajem,cike da girmamawa suka tarbeshi,a mutunce yake gaisawa da su,sannan ya saka hannunshi cikin na sumayyan sanda suke masa rakiya zuwa cikin wani babban gini dake gabansu,ta daga kanta a hankali a naj taci karo da wani rubutu cikin manyan haruffa daga saman gidan wanda aka rubuta MUHAMMAD ALMUSTAPHA ORPHANS HOUSE,cikin ranta take rayawa gidan marayu dama gareshi.

       Babban office aka bude wanda shine mallakinsa,office din nada girma qwarai,akwai kyau tsari da wadatar tsafta ko da yaushe,sun sani haka yake,ya saba kawo musu ziyarar ba zata,sai a gama waya da shi yau anjima ku ganshi cikin gidan,duka yana haka ne saboda ya tabbatar kowa ya riqe amanar aikin da aka bashi,saman doguwar kujerar cusion suka zauna shi da ita kafin su shiga gaisawa da wadanda ya dorawa nauyi da alhakin kula da gidan,cikin nutsuwa da sanin aiki kowa ke masa bayani kan nashi bangaren da yake riqewa,kusan mintina talatin kafin ya buqaci kewaya fadin gidan.

       Hannunshi tsam cikin nata tafin hannunsu a hade,kunya duka ta kamata,baijin kunyar jama'ar da suke tare?,eanda ta lura wasu sai satar kallonsu suke,a hankali suja fara kewayawa bangaren makarantar yaran inda suke karatu,makaranta ce mai zaman kanta,nursery primary zuwa secondry duka cikin gidan suke,bangaren wajem wasannin yara daga cikinsu,gurin koyon sana'ar manya,da dan madaidaicin asiniti don duba lafiyarsu,duk inda suka zo wucewa suka ci karo da wasu idan manya ne sukan qaraso fuskarsu dauke da madaukakiyar fara'a,abinda zai baka mamaki yadda suke bashi hannu kai tsaye suyi musabaha cikin yanayi na sabo da jan mutum a jiki,idan mata ne sukan duqa cikin girmamawa su gaidashi su wuce suna murna,yara qananu maza da mata da gudu suke qarasowa wajensa,yakan daga su ya sumbacesu,ko ya shafa kansu idan sunyi girman da zaya dagasu,idan yaga wani cikin yanayin da bai masa zai tambayi ba'asi ko dalilin barinsa haka?,bare ma da wuya kaga wani cikinsu cikin mummunan kama,kowa neat yake cikin tsafta da tufafi mai kyau,tun tana satar kallonshi ta gefan idanu har ta koma ta gaban idanuwa,karon farko da taji ya burgeta a rayuwa,wanne irin mutum ne shi mai tausayi haka,sauqin kai jin qai da son yara?,yadda yake mu'amalantarsu abun yayi masifar burgeta,ko banza tana da maraya,tasan ciwon rashin uba,bare wadaj nan da ba'a rasa yaran da ake kira shegu a cikinsu,wanda basu da kowaba duniya,an yardasu tun suna da qananun shekafunsu,basuji ba basu gani ba,ba'a barsu da tabin da aka haifar musu ba na rashin fitowa ta hanyar data dace ba,sai da aka sake cika rayuwarsu da tabo da quncin rashin sakin waye uwa uba kuna dangi a garesu,ba shakka yayi wani abu mai girma arayuwarsa wanda koda shi daya yayi a duniya ya cimma nasara,ma'aiki S A W yana cewa 'nida mai kula da maraya kamar haka muke a aljanna(sai ya kwantanta da yatsansa dan manuni dana tsakiya)' me yafi wannan alkhairi na zama maqoci a aljanna wajen fiyayyen halitta?,ba sai kayi da yawa ba,ko guda daya ka kula da shi kana da wannan garabasar bare kuma kayi serving rayuwar daruruwa,koda baka jin rahama da tausayi cikin zuciyarka kana jinta kamar a qesashe ka dimanci shafa kan maraya kamar yadda ma'aiki ya umarci wani sahabi,Allah ka bamu iko ka bawa masu ikon da qargin cikinmu ikon taimakawa marayan.

         Sannu a hankali suka ci gaba da takowa,dubanta yayi kana ua dauke kai yana jawota zuwa jikinsa sosai,kunya kamar qasa ta tsage ta shige,kasa daurewa tayi
"Ammm,akwai mutane fa da suke tare da mu"
"Shshshs,na fiki sani ai ko?,ko wani abu na daban na aikata bayan haka,it seems kin soma gajiya da tafiyar" ya qarasa fada yana tarota sosai,shiru tayi don ta fuskanci ci gaba da bayanin bashi da wani amfani,har zuwa sanda suka qarasa dakin kwanan yaran,don baya shiga sashen 'yammatan,yana baiwa masu kula da su mata ne su dama tambayi matsalarsu,a nan auka ci karo da wata yarinya wadda ta nufoshi da gudu,durqusawa yayi ya dauketa yana sakin murmushi,yana tausayin yaran,yana jinsu a jikinsa,ba shakka rayuwarsu akwai ban tausayi,ka tashi bakasan hatta wadanda sukayi silar kawoka duniya ba,me yafi wannan ciwo?,yana dauke da ita suka ci gaba da takawa wanda ya sanya sakin sumayya daga jikinsa,sam taqi yarda ya sauketa,yarinyar akwai surutu da wayo,tambaya take masa kan me yasa ya dade bai dawo ba?,ko da ya amsa mata sai kuma ta waiwayo ga sumayya tana tambayar wacece wannan,waiwayowa yayi ya kalli sumayya
"Sai ki bata amsa" ya fada yana tsareta da ido,murmushi ta saki wanda ya bayyana fararen haqoranta tana duban yarinyar,maqe kafada tayi
"A'ah uncle kai zaka fada min" gira ya dage murmushi na subuce masa yana duban yarinyar wadda shi ya sanya mata suna randa aka tsintota ya sanya mata amatullah
"Matata ce abokiyar rayuwata,qawata kuma qanwata" ya qarashe fada idanunsa na kan sumayyan,wani abu ne ya tsirga mata daga kai har tafin qafa,janye idanunta tayi tana maimaita kalamanshi
"Mata ta masoyiya?,yaushe na zama masoyiyarsa?" Waiwayawa yayi ya miqawa daya daga cikin masu kula da yaran amatullah sanda suka isa bakin office dinsa yana fadin su jirashi yanzu zai fito madam ta gaji zata huta.

       Shike gaba tana bayanshi,suna qarasa shiga ya waiwayo da hanzari cikin shammata ya hadeta da qofan office din da faffadan qirjinsa,yayin da ya sanya hannunsa ta bayanta yana murzawa qofar muqulli,qugunta ya kama ya riqe da hannu daya,yayin da ya dafe qofar da daya hannun,hucin numfashinsa na sauka saman fuskarta,ya cika mata idanu ya mata wani mugun kwarjini
"Uhumm.....baki yarda bane da nace kedin matata ce kuma masoyiyata?" Ya tambayeta kanshu tsaye,jin tayi shiru yasa ya dora
"If kina doubting kiyi magana" ya sake fada yana dage mata girarshi,qarar wayarshi ya ceceta daga kallon da yake mata,ya dan ka baya yana amsa kiran wanda daga driva ne yake tuna mishi kada su makara har jirgi ya tashi
"Ok" kawai ya fada ya ja da baya,saman teburin ya nufa ya dudduba wasu takardu sannan ya nufi qofa wanda tana tsaye nan tana qoqarin didaita numfashinta,hannunta ya sanya cikin nata kaman yadda suka shigo suka fice bayan ya bar key din jikin qofar yasan akwai mai kullewa,a nan ya samu ma'aikatan,ya yabawa kowa yadda zasuji qwarin gwiwar ci gaba da kula da ayyukansu,sannan ya umarci dalhatu wanda shine shugaba baki daya daya turo mishi bayanan dukkan wata matsala damuwa ko buqatar da suke da shi ta emil dinsa,idan da hali a dauki masa vidiom duk wani mai matsala ko wata buqata koda a rubuce idan zasu iya a masa sending,zai samu lokaci ya duba a nutse in sha Allah,ya bude 'yar jakar dake hannunshi ya musu rabon kudi bawai don ya gaza albashinsu bane,wannan sabonshi ne haka yake duk sanda yazo,wanda wannan na daya daga cikin abinda yasa suke son yazo din da kansa,ya sake jadadda musu muhimmanci amana sannan suka fara tako masa don yi masa rakiya.

       Gab da zai shiga motar tashi ya hangosu su uku,matasan yammata ne wanda zasu doshi shekara sha shida shida riqe da wata a tsakiyarsu tana dingisawa,sai da suka matso sosai ya kula da jini dake diga a qafarta,cikin tashin hankali ya kirasu suka yo wajensa,benci ya sanya aka dauko suka dorata akai,duk sun rude suna tambayar meta taka suka ce kwalba ce,hankalinshi tashe ya tsugunna da kanshi sanda suke yunqurin aje masa kujera ya dakatar da su,cikin rudewa yake yunqurin kama qafar ya duba inda ta shiga din caraf yaji an riqe qafan,sumayya ce,kusa da shi ta tsugunna ba tare data dubeshi ba,yayin da shi kuma ya biya da kallo yana janye nashi hannun,hakanan kawai taji wani abu ya soketa sanda ya tsugunna gabanta yana qoqarin kama qafar,batasan ta kai wajen ba,daga qafar tayi ta hasko mishi wajen tana duban 'yar budurwar
"Kina budurwa me ya kaiki yawo ba takalmi har ki taka kwalba haka?" Ta tambayeta
"Takalmin nake duba inda na ajjiyeshi ban kula ba she kwalbar na gaba na sai na taka" kai ya daga ya basu umarnin shiga clinic ya gaya musu abinda zasu dauko masa,cikin sakanni suka dawo,ya dauki wani daj qarfe da zai zaqulo kwalbar ya tunkari qafar,da sauri ta sanya hannu zata karba,sai ya sakar mata yana dubanta cikin mamaki,shi ya dinga nuna mata yadda zatayi har ta gama tayi mata dressing,tana cire safar hannun nata bayan ta gama qasa qasa yake dubanta,yana mamakin yadda tayi aikin perfectly,tayi kicin kicin da fuska,baisan me yasa ta hanashi yin aikin ba.


Suna zaune cikin mota murmushi ya subuce masa sanda wani tunani ya fado masa,kai ya kada yana cije lebansa na qasa,ya miqa hannunshi ya damqo nata hannun dake ajjiye saman cinyarta,waiwayowa tayi tana dubanshi,ido daya ya kashe mata,murya can qasa wanda sai ka mugun kasa kunne zaka iya jiyo me yake cewa
"Kada ki yarda ki soma kishina tun yanzu" fuska a hade ya fada,cikin mamaki take dubanshi,sai ta samu kanta da tabe baki
"Na meye zanyi kishinka?"
"Saboda na lura kin fada tarkon sona,ko kina jayayya"mamaki ya sake kamata,yaushe hakan ta faru da zai fadi haka,cikin dakiya tace
" qwarai kuwa"da qarfi ya janyota ta sake matsowa kusa da shi,idanuwansu cikin na juna yana dubanta kamar zai cinyeta danya,daga idanuwanta zuwa jajayen labbanta da suka sha jambaki,ji yake kamar ya cinyesu
"Me yasa kika hanani ta qafarta?"
"Wa kenan?" Ta ambata cikin dakiya,duk da yadda takeson janye idanunta saboda yadda kallon ke aika saqo har cikin qwaqwalwarta,murmushin gefan baki ya saki,he love her style har cikin zuciyarshi hakan ke burgeshi
"Kin qware wajen pretending,uumm?" Ya sake fada yana jifanta da wani salon kallo,so take ta janye idanunta amma ta kasa,har sai da ya samu nasarar jefa kasala da mutuwar jiki tattare da ita
"Idan haka ne,kada ki sake hanani aikina ko ma akan waye" ya fadi yana sakinta
"Dama ba hanaka nayi ba,taimakonka kawai nayi" ta amsa tana gyara zamanta
"Really?,dis is d begining of love,taimako and tausayi,alright?"ya fadi yana daga kafadunsa cikin i dont care manner,shiru tayi maganarsa na mata kaikawo,bata son ya sake kasheta da wannan mayun idanun nashi hakan ya sanya batayi musu shi ba.


Karo na biyu ta sake shigowa garin abuja a matsayinta na matar almustapha suruka ga baba prof,sai ta tsinci kanta cikin tsantsar kunya da nauyin ahalin gidan,sanda suka isa alamu na nuna gidan ya soma karbar baki kamar yadda hakan ya zama al'adar gidan duk yayin da wani sha'ani ya tashi,kai tsaye bangaren ummee ta nufacu zuwa,saidai ya sanya hannunshi ya riqe nata hannun ya sauya akalarta zuwa nasu bangaren
"me kika yimin sa zaki nufi wani gun,idan na kammala duka abinda zanyi kina iya zuwa but not now" shiru ta masa tana jin yadda idanuwa sukayi yawa akansu,akwai 'yammata zaune harabar gidan suna sheqar iskar almuru wanda ke busowa kasancewar an kusa sallar magariba,hakanan garin yana dan hade da hadari mai bada iska,sai yanayin ya dinga haifar da wani yanayi cikin zuciyarta,sai ta samu kanta da lafewa a jikinsa har suka shige bangarensu,sai da suka bacewa idanuwansu sannan suka dauke kansh daga wajen,daya daga cikin 'yammatan ta doka hannunta saman tebur
"Kan bala'i,wai ya akayi haka ne ta faru?,wacce iriyar rashin sa'a garemu da aka gaza samun ko daya daga cikinmu ta shiga rayuwar man din can?"
"Rashin sa'a babba ma kuwa,sai nake ganin fuskar yarinyar ma kamar na santa fa"dariya dayar ta saki
"haba sakina,bakiga yanayinta ba,ba lallai bafa ma a qasar nan ta tashi ba itama,kinsan man din nan yake da bala'in aji da daukar kai,dukanmu munsan ra'ayinshi da aqidarsa irin macen da yake buri,da alama kuma ya samu,don wallahi wannan sai taci uban su'ad a komai da komai"da sauri wadda da alama duka abun yafi tsumata tace
"Yes,gaskiyanki shuhuda,u know what?,ina ganin ma fa soyayyar da yake mata akwai banbanci,i never ever seeing him rungume da su'ad,but ku dubu wannan fa,tana jikinsa,dan gararin idanunshi a wanke,na tabbata ya ganmu but ko a jikinsa,kai i love this man wallahi naso ace ni na samu wannan sa'ar,dole eesha ta shiga wani hali" ta fada abun na tsumata,ci gaba sukayi da tattaunawa kowa na fadin albarkacin bakinsa,'yammata ne dabkowacce ke jin ta burunqasa,kowacce tana burin zamantowa suruka cikin gidan,wadda dukkansu sun kwana da sanin cewa a gurinsu babbar sa'a ce ka zama wani ahali na jini cikin gidan,ko yaya sha'ani yake na gidan basa wasa da shi,mutane ne masu son budawa da kuma babbar harka,idan kuwa suka iso gidan suna samun dukkanin yadda suke so,duk da kowaccensu mahaifinta ba baya bane shima,saidai hausawa sunce baba ma da babansa,kafi wani wani ya fika,haka Allah ya qaddari rayuwarmu,yadda da hakan kadai shi zai sama maka rayuwa mai cike da wadatar zucci,da kuma cikakkiyar godiya ga Allah bisa dukkan wani bigire da ya azaka,Allah kasa mu dace,ka bamu wadatar zuci wadda itace babbar wadata itace babban arziqin duniya.


Sannu a hankali suke takowa zuwa bangaren ummi,jifa jifa suna wuce mutane da suka yo sammakon zuwa bikin tun farkon satin,sanye take da abaya baqa mai zubin dinkin buba,ta yane kanta da mayafin rigar,yayin da yake sanye da qananun kaya shirt da trouser baki daya shima baqaqe,zo kaga wani kyau da sukayi,musamman da yake riqe da hannunta saboda yadda ya lura akwai yawaitar 'yan sanya idanu,takanji wani nauyi duk sanda ta tuna yadda ya ritsata awa daya da suka shude a toilet daure da towel tana shirin yin wanka,yana jaddada mata wajibcin yin wankansu tare fuska daure,saidai baki daya yanayin da ya ganta ya sakar masa da jiki,ya zuba masa kasala da wani irin feeling a jikinsa,yayin data yayibi wani towel din ta rufe kanta hakan ya tunzurashi ya dinga takowa inda take har ya qureta a bango
"Yau zaki san kinyi kuskure,me kike boyemin" ya ambata yana dauke towel din dake kanta,gashinta ya bazu zuwa kafadarta,abinda ke sake burgeshi da tafiya da shi kenan,baya ta sake ja taha qoqarin boyewa cikin jacuzzi,cikin sa'a ya samu nasarar danqo ta,idanunta suka fito ganin yana niyyar sanyata cikin bathtube,tsoron dama yake son gani cikin idanunta,wani abu daban take koma masa mai kyau,bai bari ba kuwa sai daya sanyata sannan ya soma rage kayan jikinsa
"Saiki jira na gama nawa wakan sannan kiyi naki tunda baki son muyi tare sannan kuma cikin toilet dina kike ba naki ba"
"Amma ka bari na fita idan ka gama na dawo"
"Is too late" ya fada ko a jikinsa yana tubewa abinsa,idanuwanta ta runtse sanda yake qoqarin cire bixer din da shi kadai ya rage,sai qyarma take,bata taba ganin jiki mai lullube da siffar qarfi haka muraran a gabanta ba,gargasar jikinsa kawai abar kallo ce,karon farko data soma ganinsa a hakan,ko a jikinsa ya kammala wankansa tas sannan ya nade jikinsa da towel ya fice.


Dawowa tayi daga duniyar data tafi sanda taji yana matsa hannunta,tuni sun iso qofar falon ummeen ita yake jira ta cire takalmanta,a nutse ta zaresu sannan suka sanya kai ciki,shi yayi sallama yayin da suka jiyo muryar ummee tana amsawa,kunya da nauyi suka cika sumayyan,kamar ta koma bayanshi ta boye haka ta dinga ji,tana qoqarin zame hannunta dake cikin nashi amma yaqi bata dama,saima rada daya soma yi mata
"I want to show them i care with amanar da suka bani,nasan haka ne so ya kamata suma su gani,sai suyi alqalancin waye ya kasa kula da tashi amanar ko?" Sunne kai tayi ganin idanun ummee na kansu,fuskarta dauke da murmushi da kuma mamaki,don ta taji yara na fadin zuwan nashi bata yarda ba,don an riga da an saba,yawanci sai ana ya gobe daurin aure yake zuwa,wani lokaci ma sai ran daurin auren,awa daya kafin a daura ko minti talatin,musamman idan na yaran 'yan uwa ne,suma sai na kusa saboda tsabar busy,amma yau sai gashi kwanaki shida saura a daura auren,wannan wane irin gagarumin canji ne haka ke tunkarar rayuwar yaron nata,bata gushe ba tana musu barka da isowa fuskarta tamkar gonar auduga,yayin da eesha dake gefe bata daga kai ba tana danne dannen waya har sai da taji muryarshi,karaf idanunta suka fada kansu,zumbur ta miqe tsaye tana rarraba idanu,kada dai ace ta fara samun matsalar idanuwa,wannan yarinyar ya aura?,ko daga bacci ta tashi duk sauyawar da taji da samun cikakkem hutu dake kwance a jikinta ba zata manta ta ba,haka kawai yarinyar ta tsaye mata a rai
"Mutanen UAE" haka ummin ke fada wanda wannan kawai ya isheta amsa,sai ta hau girgiza kai ta shige dakin da ta sauka da gudu,sai sannan hankalin ummen ya kai kai,takun gudunta yaja hankalin almustapha da ya kai sumayya har gaban ummee,kunyarta ta sake burgeshi karo na biyu musamman sanda ta zame daga samn kujera zuwa qasa gaban ummeen,abinda bai taba gani kenan ba wajen su'ad,yana zama kujerar dake daura da ummin yace
"Waccar fa?,sunzi zasu fara haukar nasu kenan ko?"
"Kai kuma kazo zaka fara kenan ba"
"A'a ummi ni ban da case da kowa,just su kiyaye rules din da na sawa zuwansu gidan nan"
"Allah fa ya kawo mu,amiran umman khalipha ya fama da wannan" ta fada tana duban sumayya,alamun qarfi taba ga mai qiba,daga yanayin fuskar almustapha kawai ya isa ya sanar mata akwai gagarumin sauyi daya fara nasar rayuwarsa,yanayinsa baki daya akwai sauyi koda shi din bai san ko ya lura da hakan ba,kunya ta sake kamata tayi qas da kai tana gaidata,ta amsa cike da kulawa da farinciki,shima tashi gaisuwar ya dora ta amsa cikin jin dadi tana tambayarsu ya suka baro dubai
"Sai kuma gaku tun yau?" Ta tambaya cikin mamaki,satar kallonta yayi wanda ummin ta kula da haka
"Eh ummi,akwai wani aiki da nakeson yi,shi ya taso ni dole,tunda naga yayi daidai da date din daurin auren" ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba.




         







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:52] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



8⃣7⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

*SANARWA DA BABBAR MURYA*

*BA NUFIN MU CIN ZARAFIN WANI KO BATAWA WANI BA,SABODA GUDUN RUBUTA MUNANAN AYYUKA CIKIN LITTAFIN AYYUKANMU,WANDA SAI MUN TSAYA GABAN UBANGIJI MUNYI BAYANI RANAR GOBE QIYAMA,AMMA TURA TA KAI BANGO,AN FARA SHIGA SHINGENMU ANA MANA BARNA,BAYAN MUN KAME KANMU DAGA DUKKAN WANI ABU DA ZAI ZAMA SHIGA HURUMUN WANI BATANCI KO CIN ZARAFI A GAREMU*

*GAREKU MASU SATAR FASAHA ZANCE KO BARAYIN ZAUNE*

*Ina mai shaidawa duk wani mahaluki da yasan cewa yaci da gumi na,ya dauki wani littafi nawa da na zauna na bata lokacina na rubutashi da hannu na don al'ummar ma'aiki su amfana,MALLAKINA ya kaishi wane waje ya saida yana zuba kudin a aljihunsa cewa NI SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,BAN YAFE BA,KUMA INA ROQON ALLAH YAYI MIN SAKAYYA KAYANA DA AKA DAUKA ANA SAIDAWA*

*GAREKA KO GAREKI BARAUNIYA A OKADA,DUK WANDA YA SANSHI KO YA SANTA YA ISAR MASA/TA*

*ABADAN DAYA SATA KOTA SATA,AKA KAISHI OKADA ANA SAIDAWA AKAN KUDI NAIRA DARI BIYU,NACE ALLAH YA ISA BAN YAFE BA,INA ROQON ALLAH KUMA YA FITAR MIN HAQQI NA MATUQAR BANI NA ZALUNCESU BA SU SUKA ZALUNCENI,TUNDA BAN TABA DAUKAR HAQQIN WANI MALLAKIN WANI NA MAIDA SHI MALLAKINA BA,ALLAH YA BIMIN HAQQINA,INA FATAR ZAKU SADAR DA WANNAN SAQO ZUWA GARESU*

*SANNAN WANNAN LITTAFI DA NAKE RUBUTAWA DAMA SAURAN LITTATTAFAINA,MALLAKINA NE,NA YISHI NE KYAUTA BA NA SAIDAWA BA,A DUK SANDA NAKE DA BUQATAR SAIDAWA ZAN SIYAR DIN,AMMA BAN BAIWA KOWA IZINI YA SIYAR MIN BA,WANDA KUMA YAYI HAKAN NA BARSHI DA FITOWAR RANA DA FADUWARTA,NA BARSHI DA MAI SAMA,MUGA ALFANUN DA ZAI SAMU CIKIN KUDIN DA KA SAMU TA HANYAR SAIDA ABUN SATA*

*WALLAHI WALLAHI ALLAH MU GUJI CIN HAQQIN WANI,BILLAHILLAZAI LA ILAHA ILLA HUWA DUK WANDA KA GANSHI RAN QIYAMA YA QETARE TO BABU HAQQIN WANI A KANSHI,WANNAN ALQAWARI NE NA UBANGIJI,SAI YA FITARWA DA DUK WANI BAWA HAQQINSA KAN DAN UWANSA,KODA DABBA CE TA ZALUNCI 'YAR UWARTA DABBA*

*ALLAH KASA MU DACE*
_____________________________________




        ta fahimci salon magana ce kawai ta qwatar kai,tunda da aiki ne da tuni ya shaidawa baba,amma ko baban baisan da zuwanshi ba,koma meye tana maraba kuma tana fatan alkhairi da samun wannan kyakkyawan canjin,sai ta saki murmushi
"Masha Allah" ta fada tana maida dubanta ga sumayya
"Me zaku ci,ko zaki shiga kitchen ki sama muku ko snacks ne,yau duka ma'aikatan na can baya suna aikace aikace suma"
"Am ok ummee" almustapha ya fadi,farinciki ya mamayetq,ta tabbata tunda ya fadi hakan hakanne,sai ta waiwaya ta dubi sumayya
"To kefa amira?"
"Nima ummee na......"
"Qarya take,ba abinda naga taci tunda muka taho" almustapha ya katseta yana tsareta da ido,murmushi ya subucewa ummee,salon da bata taba gani wajen almustaphan ba yau sai gashi da shi
"Maza shiga ki samu wani abu kici,halan shi kin sama masa wani abun yaci ke baki ci komai ha ko?" Cikin kunya tana murmushi ta miqe kanta a qasa tayi kitchen din,yayin da ya bita da kallo yana yabawa salon kunyarta,yanayin yadda take ganin girma da darajar mahaifansa,tunanin yadda cikin qan qanin lokaci kan ya gama shiryawa ta hada misi wani hadadden patatoe salad ya fado masa,ya jima baici hadin salad da ya masa dadi irin wannan na,murmushi ua dan qwace masa,yanayim takun ta na burgeshi,ya dauke kai sanda ta kai ga shigewa kitchen din,sai suka hada ido da

Please Login or Register in order to submit comment