Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka yi sannan sukayi sallama da baban suka fice,tattambayarta baabaa yayi kan wasu abubuwan tana amsa masa,har alokacin kanta na duqe,ta miqe bayan wasu mintuna ta masa sallama,sai anty ta ajjiye masa kwanon tana masa bayani,qwarai da gaske yaji dadi,domin shi mutum ne da baya raina alkhairi komai qanqantarsa,koda yafi qarfin abu ka bashi shi yana ganin girmansa abun agunsa,dakatar da ita yayi yana fadin
"bari na baki zamzam da bagaruwa ko"
"To" ta fada tana murmushi,antyn yama kwatance cikin dakinsa,cikin sakanni ta shiga ta fito da wata jarka
"Ba ita ba,zamzam din da nayi dawafi da shi" mamaki antyn tayi,don irin wannan zam zam din ba kowa yake bawa shi ba,dashi yaje dawafi da addu'o'i,yakam zama magani cikin ikon Allah ga duk wanda ke jin lalura ya bashi yayi amfani da shi,duk da kasancewarsa tantagaryar dan boko amma akwai ilimin addini mai yawa tattare da shi,jarka ce guda tayi tsawon ta faro qarami ya zuba mata,sannan ya cika mata leda da bagaruwa da dabino,godiya tama baban sosai ta kuma ji dadin kyautar tasa,tare suka fito da antyn
"Anty zan koma"
"Haba daga shigowarki,kodai tsoron kike ji kamar yadda mahmoud ya fada,naga ko mutuniyar taki amira baki gani na,bayan ita tunda muka dawo take maganarki,na tabbata baqi ke suka hanata fitowa da tuni kin ganta,sannan baki shiga kin gaida ummee ba" sam bata so antyn ta debo mata wannan bayanin ba,amma sai ta sadda kai tace
"To,bari na shiga"
"Yauwa,ki gaida ummam khalipan don Allah idan kin koma,nasan itama baqi ke suka hanata leqowa,dukkanmu irin wannan lokacin sai haquri baqi muke ba dauke qafa"
"To zataji" ta furta sanda antyn ke yunqurin amsar husna,nan ma qi tayi,dariya antyn ta dinga
"Shikenan kuje da ita kin samu qanwa,idan tayi kuka ko laila kaya bada ta kawota"
"To anty" tafada tana dariya tare da yin gaba.

        Baki daya falon ya sauya ba kamar waccan karon data shigo shi ba,da alama gyaran azumin ne,komai ya canza a falon,saidai tun kafin ka kai ga qarasowa cikin falon zaka jiyo muryarta,tana tsaye tsakiyar falon hannunta riqe a qugu tana zuba masifa,bisa alamu da 'yanmatan dake zaune a falon take,sun kusa su hudu harda amira dake gefe tana shan ice cream hankalinta kwance kamar ma bata falon
"To bani cike da iskanci,ran kowa sai ya baci wallahi,bazan dauki raini ba,kuma wanda ya fasa karbo greeting cards na 'yammata yana kawowa bai cika ba mu zuba ni da ku,aikin banza kawai" tana gamawa ta juya a fusace tana taku kan tsireren takalminta mai igiya,kowa sanye da suturar al'ada banda ita,wando ne a jikinta irin straight leg din nan,sai riga one shoulder a jikinta,gefe sumayyan ta janye tana dubanta,dariya taji 'yammatan suka saki bayan fitar tata banda amira fake ci gaba da abinda take,daya daga cikinsu tace
"Duk wayon amarya wallahi sai an sha manta"sai a lokacin sumayyan ta maimaita sallamarta,amira ce ta amsa cikin fara'a ta miqe
"amiran umman khalipha kinsan kina raina,sannu ga guri zauna" tana mata nuni da wata kujera dake can gefe babu kowa,qarasawa tayi tana zaman amira ta sake cewa
"Ina kika tsinto wannan uwar qyuyar,daina kallona kina wani saukar da kai ban daukanki zanyi ba nima" ta fada tana dan daga murya da zaro ido da alamu tana jin haushin irin qyuyar husnar,murmushi sumayya ta saki tana dafe kan husna wadda ta kwantar da kanta aqirjinta
"Dole fa ta miki qyuya,kina mata irin haka"
"Allah bata da kirki" gaisawa sukayi ta mata sannu da zuwa sannan ta tambayi ummin
"Ummi na sama,bari na miki kiranta"
"To" ta amsa,satar kallonta 'yammatan suka ci gaba da yi itakam hankalinta na kan husna tana mata wasa a haka amira ta dawo ta tadda su,ba dadewa ummin ta sauko,abinda sumayya ta dan lura da shi shine,ummen irin mutanen nan ne da basu son hayaniya da yawan surutu.

       A mutunce ta gaidata ta amsa mata fuska a sake itama tana son daukar husna,saidai itama husnar ta watsa mata qasa a idanu kamar sauran,tilas ta barta sumayya na mamakin qyuyar yarinyar,bata wani jima ba tayi musu sallama ta fice sabida yadda 'yammatan ke kallonta.

       Anty dije ma tayi mamakin ganinta da husnar,goyata tayi bayan ta bata abinci,ba jimawa kuwa tayi bacci a bayan nata,gab da magariba sukaji sallama a falon,sumayyan ce ta fito goye da husnar tana amsawa,magidanciya ce wadda zata doshi shekara talatin da hudu,fuska a sake sumayya tayi mata sannu da zuwa,leqa bayan sumayyab tayi tana riqe baki cikin fara'a
"Wai lallai raino yayi dadi,ashe kam da gaske tana nan din,ni ina can hankalina na kanki uwar qyuya ashe ke kin haye bayan mutane kina bacci abinki" dariya sumayya ta danyi sai alokacin ta fuskanci mamarta ce,yunqurin saukota tayi tana fadin bari ta bata ita
"A'ah,barta mana idan ba'a matsa miki ba,haba sai kace bare,da nan da gidan baabaa ai duka daya ne,kawai dai idan ta tashine nasam zata taba miki darunta,sai azo a dauketa"
"To" ta amsa tana gyara goyon
"Ina anty dije" ta ambaceta da sunan da suke kiranta a kano sabanin yadda taji mutan gidan na kiranta da umman khalipha
"Yanzun nan ta shiga wanka"
"Sarkin kwalliya wa miji,idan ta fito kice ina gaidata" ta fada da sigar zolaya,bisa alamu sun saba sosai.

      Bata farka ba sai bayan magariba sumayyan ma na shirin tada isha'i,daukota tayi daga kan gadon ta cire mata pampers tare da zuba abinci ta bata,sai da taga ta qoshi sannan ta sabata a kafada ta zura hijabin sallarta wanda ke kusan sharar qasa tace khalipha yazo ya rakata.

        Tarwai gidan da haske kamar kowanne lokaci,saidai yau akwai yawaitar mutane a harabar gidan,sashen anty maamaa ta shiga tacu sa'a ko ta tadda maman husnar,amsarta tayi tana yiwa sumayyan sannu tare da godiya.

       Tunda ta tako daga sashen anty maaman ya zuba mata idanu,haske gidan kadai ya wadatar masa ya gane wace ita,mahmoud da ya gaji da yi masa magana ya dafa kafadarsa wanda hakan ya sanyashi daga kai da sauri yana dubansa
"Mahmoud,sumayya ta nake gani a gidanku" waiwayawa yayi zuwa inda yaga alqasim din na kalla,tabbas sumayya ce ke tahowa
"Wannan sumayyan ce sumayyarka dama?"
"Wallahi itace" alqasim ya fada a rude,dariya mahmoud ya saki
"Ai tazo gidan sauqi,amma fa ba abune mai sauqi ba shawo kanta haka na fuskanta"
"Please mahmoud" alqasim ya fada cikin damuwa yana hade hannayensa ganin sumayyan na gab da su
"Don't mind"mahmoud ya furta yana waiwayawa yadda zata iya ganinsa idan ta qaraso,sam bata lura sa su ba duk da hasken da ya wadatar da gidan tamkar raba,hanakalinta na gefe can inda wasu 'yammata ke zaune suna hira,kusan basu suka dauki hankalinta ba ma yaran dake wasansu kusa da su ne,wanda daya daga cikinsu keta kiran abbanaa da alama labarin abban nasu yake basu,tana ganin sa'o'in abdallah a ciki,cikin ranta ta raya suna cikin farinciki da gata,sabanin abdallah da take fatan zai tashi cikin farinciki saidai baisan dadin uba ba,qwalla ta taru idonta sai tayi hanzarin sadda kai da qara sauri a tafiyarta don ficewa daga gidan,tun jiya ranta a jagule yake,hakanan ta wuni da tunaninsa cikin ranta,wanda ya haddasa mata kasala da mutuwar jiki wunin baki daya,shi ya qara mata qyuyar fitowa waje
"Yi a hankali kada ki fadi" mahmoud ya fada yana dubanta,cak ta tsaya tana dubanshi tare da qaqaro murmushi
"Hala sauri ake a fice daga gidan namu"dariya ma yaso bata saidai bata yin ba sai murmushi saboda damuwar da zuciyarta ta shiga daga tuna mukhtar
" kadai camfani"
"Ko kadan,to daina saurin,ga baqo kinyi,yanata nemanki wata da watanni sai yau Allah ya qaddara haduwarku" a zabure kamar wadda ta yiwa sarki qarya ta daga kai,suka hada idanuwa da alqasim,farinciki yake ji sosai cikin ransa,takowa yayi gefanta yana dubanta
"Zakaran da Allah ya nufa da cara sumayya,mai yiwuwa Allah ya qaddara wani lamari ne mai girma tsakaninmu,shi yasa ya kado hankalina abuja gidansu abokina mahmoud,ashe rabon na ganki ne" ba shakka tana ganin girma da qimar mahmoud,tunda shi ya soma tsaidata,banda haka da tuni ta yankawa alqasim warning cikin daqiqun nan tare da kaucewa.


        Saye yake da quater zip sweater mai dogon hannu ta kamfanin armani maroon colour saboda sanyin da ya soma busawa sakamakon hadarin da ya hadu dazu bai zub da ruwa ba sai ya bada sanyi wa garin baki daya,wandon jeans baqi,sai high top sneakers,hannayensa saye cikin aljihun wandonsa ya fito zuwa harabar gidan yana duddubawa,kusan al'adarsa ce wannan a lokaci irin wannan,kafin yaje ya kwanta sai ya dudduba ko ina saboda baqin dake gidan,ya tabbatar babu yarinyar data fita yawo balle akai ga zuwan saurayi zance gidan,yace duk mai buqatar hakan ta bari idan ta koma gidansu tayi abinda taga ya mata amma ba cikin gidansu ba,tsarin ya yiwa baabaa prof saboda haka baice komai ba,a irin hakan wasu daga 'yammatan wadanda suke zaton wayewa ce garesu,iliminsu da gogewarsu ta kai wani mizani,sukan fita ciye ciye ko siyayya da samarinsu,wani lokaci sukan kai goma ko tara na dare basu dawo ba,yayin da wasu sukan maida harabar gidan filin baje kolin gayyatar saurayi suyi zance,hakan ne ya sanyashi sanya wannan doka wadda ta yiwa manyan dai dai saboda tsaron tarbiyyar kowacce yarinya har ta koma gidansu,hakanan duk wanda ke kawo ziyara gidan a irin wannan lokaci ya san da dokar,walau mace ko namiji.


Cikin izza da ginshira yake takowa tsakiyar harabar gidan yana qarewa kowacce kusurwa ta gidan kallo da idanunshi,tuni hayaniyar wajen ta soma raguwa kowa ya soma shiga taitayinsa,wasunsu suka shagala da kallonsa,masu gulmarsa qasa qasa nayi.


Kamar ta sanya kuka haka sumayyan keji,yayin da alqasim kuma ya dage wajen ganin komai ya daidaita kafin barinta wajen,idanunsa ya sake wurgawa wani sashen,a can saka masa kamu,maca ce tsaye da hijabinta har qasa da wani saurayi tsaye a gabanta,sai wani saga gefanta,ranshi ya matuqar baci,ya tsani ya sanya doka a karya masa,a ganinshi wannan daya ne daga cikin alamun raini,idanu ya zuba sosai sai ya dinga hango kamar mahmoud ne dayan dake gefe,cikin bacin rai ya soma takawa idanuwansa na wajen,sam mahmoud bai ankara da fitowarsa ba shakka da tuni ya sallameta,ya riga da yasan halinsa sarai mutum ne mai doka da qa'ida,bazai karya dokar wani ba so shima kada a karya tasa shine zaman lafiyar mutum.


"Mahmoud" ya ambaci sunanshi bayan isowarshi gun,wani abu taji ya caketa tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin qafarta da taji muryar mukhtar gab da ita,kuma a bayanta,kamar mai ciwon wuya haka ta dinga waiwayawa a hankali har ta kammala juyawa baki daya,tsaye yake harde da hannayensa yana yiwa mahmoud da alqasim magaba cikin bacin rai,idanuwansa na kansu,wanda sam bata iya jin abinda yake gaya musu illa bakinsa da take gani yana motsawa,muryar ce taci gaba da yi mata amsa kuwwa cikin kunnuwanta,a hankali ya dinga juye mata zuwa mukhtar dinta,sannu sannu jikinta ya soma rawa tamkar wadda aka tsoma cikin ruwan sanyi,bata ankare ba taga yana qoqarin juyawa ya bar gurin,batasan lokacin da ta daga murya cikin qaraji daya sabbaba har wadanda ke daura da su jin sautinta ta ambaci
"Mukhtar!" Cak ya tsaya tare da waiwayowa yana dubanta,kallonsa take tana takowa zuwa gurinsa a hankali,tsayawa kawai yayi yana dubanta,tun dazun haushi ya tsaye masa a wuya,tunda ya tsaya gun ya lura da yadda ta zuba masa udanuwa,abinda ya tsana kenan cikin kafatanin halayen 'yammatan wannan qarnin,kallon tsiyawa d'a namiji,babu wata kunya tattare da su
"Mukhtar kai ne?,kaine mukhtar!,dama kana nan,dama baka mutu ba?" Cikin bacin rai da yi mata kallon mai tabin hankali ya dubi mahmoud
"After All ma ashe da mai lalurar tabin hankali kuke tsaye?,sai kuzo kusan yadda zaku fidda ta tun kafin ta soma yiwa mutane barna"
"Mukhtar nice fa,sumayyarka ce mukhtar,nike da tabin hankali?" Har yanzu bai gasgata mai hankali bace,amma sai ya nutsu tsaf ya dubeta,babu alamu na hauka tattare da ita,ayyanawa yayi kawai tsabar rainin wayo ne da son samun guri,wanda ba tun yau ba ya gama haddace kissa ta son samun guri na 'yammata masu cusa kai kala daban daban,wani tsaki ya ja,sannan cikin dakakkiyar muryarsa wadda ta sake taimakawa wajen sawwara mata surarsa zuwa ta mukhtar yace
"Ban ciki da hauka da gidadanci kinji ko,ki kama kanki tun bai gudu ya barki ba,kama hanyarki ki koma inda kika fito" ya juya yana yunqurin barin wajen,a zabure ta bishi har ta samu nasarar riqo dantsensa,cikin tsananin bacin rai ya juyo yana dubanta cikin ido,wani kallo ya jefe ta da shi wanda tabbas da cikin hayyacinta take tuni ta sake shi saidai sam ko a jikinta
"Sake tafiya zakayi ka barni?"
"Sakeni!" Ya daka mata tsawa
"Bazan sake ka ba" itama ta fada cikin tsawa da bacin rau,take zuciya tanzuroshi,marinta yaso yi amma yaga rashin dacewar hakan,maiyiwuwa akwai tabin qwaqwalwar da batasan tana da shi ba,yaga kuma alama matuqar yaci gaba da tsaiwa zata iya ma rungumeshi kaban wadan nan yaran ta zubda masa mutunci,saboda haka sai ya fincike hannunshi tare da tunkudata yayi gaba,wani irin zafi yake ji da haushinta,baya tayi cikin rashin qwarin jiki,sun tsammaci zata turje ta tsaya sai kawai suka ga ta sulale ta zube baki daya,cikin firgici da tashin hankali mahmoud ya soma qwalawa amira kira don babu damar taba ta wadda fitowarta kenan shan iska batasan ma meke faruwa ba,ganin sumayyan kwance ya daga hankalinta ta koma ciki a sukwane,nan sukayi kacibus da anty farida mamar husna ta kamo hannunta suka yo wajen.


Ba amira da anty farida ba,hatta mahmoud da alqasim hankalinsu tashi yayi,kowa mamaki yake,meke faruwa ne haka,abu kamar dramer cikin sakanni qalilan,tana ta faman kiran mukhtar shi kuma wannan ALMUSTPHA ne abinda suke tunani kenan,cikin hanzari anty farida ta soma yunqurin dagata da taimakon amira,idan ka dubi fuskar wasu dai daikun 'yammatan dake gun jimami da tausayi ne bisa fuskrsu,addu'a suke mata kan Allah yasa ba qoshin wahalar da suka afka bane itama ta afka cikinsa,yayin da wasu dadi ya rufesu kamar su taka rawa,ko banza basu zama su kadai ba cikin wadanda suka rasa wannan damar.



A hankali ta ja numfashi tana ambaton sunan Allah,idanunta ta bude,jinta take kamar wadda ta tashi daga bacci,idanuwanta ta sake lumshewa take abun ya sake fado mata,kalamansa da muryarsa suka fara yi mata amsa kuwwa cikin kunne,take idanuwanta suka tara hawaye masu dumin gaske suka soma bin gefen kunnenta,sake rintse idanuwanta tayi,kamanninsa suka fara dawo mata ganin farko data yi masa kafin idanuwanta su rudeta,da sauri ta bude idanuwanab tana girgiza kai,tabbas ba mukhtar bane,babu kamannin mukhtar ma tattare da shi idan ka dauke murya,me ya shiga kanta ta aikata haka sai kace wadda jinnu suka juyawa tunani?.


Saitin fuskarta taga an turo screen din waya,idanuwanta ta bude kan screen din,shine,shine wanda ta gani dazun,sanye yake da qananun kaya kyakkyawar fuskarshi qunshe da murmushi,hotonsa ya cika fuskar wayar baki daya,a yanzun ta sake tabbatarwa bata ga kama tsakaninsa da mukhtar dinta ba,sai ta waiwaya don taga wanda ke haska mata hoton,amira ce zaune gefanta,idanuwa suka hada sai ta janye wayar tata ta kasheta tana duban sumayya
"Wannan yaya nane,mama da baabaanmu daya,ummee ita ta haifemu,sunanshi MUSTAPHA ko ALMUSTAPHA duk daya ne,anty dije ta bani labarin waye mukhtar a gunki,matuqar suna kama da mukhtar kuma yayi miki na miki alqawarin zaki zama mallakinsa,duk da nasan babban aiki na daukawa kaina saboda sanin waye YAYA MAN,amma abinda yayi miki ya bata min rai,ina jin tamkar ni aka yiwa,ko don saboda wannan indai kina sonshi amiran umman khalipha na miki alqawarin aurensa".













*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

6⃣1⃣



*Bismillahir rahmanir rahim*


*SHIN ko kunsan RUWAN DAN WUTA,RUWAN MUGUNYA NE(KAMAR RUWAN CIWO QURJI)TAFASASHSHE MAI AZABAR ZAFI DA TURURI,A DUK LOKACIN DA YA BUQACI SHAN WANI ABUN SHA SABODA TSANANIN QISHIRWAR DA YAKE JI SHI ZA'A BASHI YA SHA,YAYIN DA YAKE SHA DIN SABODA TSABAR ZAFI DA TAFASA HAKA ZAI DINGA YAYYANKA DA TSITSTSINKA MASA HANJINSA,YANA ZAGWANYEWA*

*Subhanallah,muji tsoron azabar Allah 'yan uwa*

____________________________________



Shuru amiran tayi tana duban sumayya cike da qwarin gwiwa da kuma yaqini cikin zancanta,itama dubanta sumayyan keyi kafin ta saki murmushi sannan ya kada kai
"Ni nayi kuskure amira,ni na yi masa kallon mukhtar dina bayan bashi bane kamanceceniyar iya murya ce kawai,koma waye zaiyi zaton ba lafiya tunda baisan farkon lamarin ba,amira,bana jin so ko qaunar ko wanne namiji bare na yi sha'awar zaman aure da shi,banqi a ce nabi mukhtar ba muyi zamanmu cikin rahamar ubangiji,abunda kawai nake tausayawa abdallah na" ta fadi cikin karyewar murya da rauni,duk da qoqarin kaucewa hakan da takeyi,tausayinta ya sake kama amira
"Da gaske amiran umman khalipha kin taba aure kuma ma har da boy?" Ta tambaya cikin zumudi,kai ta gyada mata tana murmushi
"Zanso naga boy din nan,na tabbata zaiyi kyau kamar mamarsa" wannan karon har dariya taso sara,saboda ta tabo gudan jininta,yaron da shima tun kafin ya shaqi iskar duniya ya fara fuskantar gwagwarmaya da matsalar rayuwa,koda ya shigo cikin duniyar ma ba'a barshi ya huta ba sai da aka so saida rayuwarsa,zainab ta fado mata,ko yanzu tana wacce duniya,baki daya sai taji son aure ya sake fita daga zuciyarta,itakam yanzu me zata ci da aure
"Amma zanso amira ki amincewa qudirina,na tabbata cewa rayuwar yaya man zata sauya zuwa yanayin da muke masa fata da hange,zan iya cewa ANTY SU'AD bata da wani amfani a rayuwanshi" cewar amira tana duban sumayya,kai ta shiga girgizawa
"Duk mai qaunata amira ba zai sake min sha'awar aure ba a yanzu,nikam me zanci da aure,auren ma na mai mata"
"Me kike cewa ne?,amira zanso sanin wace ke,na tabbatar akwai wani abu a rayuwarki ba wai mukhtar bane zalla" miqewa tayi a hankali ta zauna tana duban amiran
"Babu lokaci,duba kiga goma na dare"
"Ko zan kwana anan nasan babu damuwa,ina son ki ban labarinki don Allah,naji anty dije na fadin wasu abubuwa da ban gane ma kansu ba"murmushi tayi
"Me zakici da labarina banda kayan sanya hawaye a ciki,babu komai a labarina face wuya da naci game da kishiyoyi da abokan zama na" idanuwa amiran ta zaro
"Kina nufin bama aure daya kika yi ba amiran umman khalipha?,ina cewa zamuyi sa'anni dake fa?" Dariya tayi wannan karon
"Hala mass com kika karanta ko,ina ce miki dare yayi amma baki damu ba?"
Dariya itama ta saki tare da miqewa ba don taso ba
"Zan tafi,amma zan dawo ki bani labarinki"
"Sai kinzo,sai da safe na gode"
"Nice da godiya kuma kiyi haquri da abinda ya faru"
"Babu komai QADDARA CE!" ta ambata wani abu na taba ranta,juyawa amiran tayi ta fice tana murmushi


****** ******* *******


Sukuku haka ta wuni washegari,duk da ba wani abu take ji na ciwo a jikinta ba amma baki daya bata da kuzari kamar wadda aka zarewa laka,da yammaci tana kwance a falon,babu kowa gidan daga ita sai anty dije,su laila sun tafi gidan kakarsu,itama rashin qwarin jiki ne ya hanata zuwa taji muryar amira tana sallama,miqewa tayi daga kwanciyar tana amsawa tare da maida daurin dankwalinta da ya zame,sai taga ashe su biyu ne ita da anty maamaa,miqewa tayi fuskarta qunshe da fara'a tana musu sannu da zuwa,kitchen ta juya ta dauko lemo saman tray ruwa da kofuna ta ajjiye musu sannan ta haura sama don kiran anty dije.


Tare suka sauko,fuskarta dauke da fara'a itama take musu lale da zuwa,ta zauna suka gaisa sannan sumayya ta gaida antyn kafin ta waiwaya ga amira suka gaisa
"Zuwa nayi dubiya,jiya muna cikin gida ashe haka abu ya faru,sam ban sani ba sai dazu da mahmoud ya shigo yake gayan,sai kuma farida itama ta sanarmin su suka kawota gida"
"Wallahi kuwa,abin sai addu'a,damuwar dake ranta ce ta mata tasiri har ta haifar da hakan"
"Allah ya kiyaye gaba,baki daya ma banga mustaphan ba yau,yana ta shirye shiryen komawa,inason tambayarsa ya akai hakan ta faru,banji dadi ba sam bai kyauta ba,ai ba'a haka.....sannu sumayya ya jikin?" A kunyace kanta na qasa tana murza yatsun hannunta,tana jin tamkar ta jawowa kanta wani babban abun kunya ne,kada ma wasu su tsammaci saboda shi ta suma tace
"Na warke ai anty"
"Allah ya sawwaqe ya qara afuwa"
"Amin anty dije ta amsa,amiran ce ta dubi sumayya
"muje ina son in ganki"tana dariya,sai ta miqe tayi gaba amiran ta biyo bayanta.


Bakin gado suke zaube baki dayansu amiran ta kalleta
"ina alqawarina?"
"Labarina bazai yiwu ba yanzu amira,ki bari na sake samun sauqi ko?"shiru ta danyi tana kada kai
"To shikenan,Allah ya qara baki lafiya"
"Amin" ta fada tana murmushi,jefi jefi amiran ta dinga sako mata hita,wata ta 'yan uwa wata ta qawayenta wata ta gidansu duk don ta sake sakin jiki,yawanci duka bata sansu ba,amma abun yana burgeta,saidai tayi murmushi kawai,a nan ta fahimci su'ad itace matar mustapha.


Suna zaune anty dije ta leqo tace anty zata tafu,miqewa tayi tana cewa
"Nima tafiya zanyi,zamu je unguwa ne yau duka 'yammatan,sai na dawo"
"Allah ya tsare,na gode ki gaida ummee"
"Zataji kuwa,don batasan abinda ya faru ba,da yau ya man ya shiga uku wallahi,inaga ma sai na guntsa mata batun" ta fada tana dariya gami da ficewa,sumayyan nason ce mata kada tayi amma tuni tayi gaba abinta.


Kiran wayar bdur rahaman ita ta qarasa tayata hira har sha biyu na dare sunata hira,yana ta bata labarin yadda shirye shirye suka kankama na bude islamic clinic dinshi,yana so ya soko mata maganar yadda yayi missing dinta da kuma yadda yake son ganinta saidai yana tsoron kada damar da ya samu ya rasata,sam bata gaya masa zata zo kano ba har sukayi sallama.


******* ******* ********


A hankali ya dinga takowa cikin tafiyar sa ta qasaita har cikin falon baabaa prof din,sanye da short sleev polo t.shirt jaa da touches na baqi,straight leg trouser sai safa a qafarnshi,hannunsa soke a aljihun wandonsa,wanda ya zame masa al'ada idan ya sanya qananun kaya,idan ba waya hannunshi to zaka samu hannayen cikin aljihu ko harde a qirji.


Sallamarsa ce ta sanya baabaan dago kai yana dubansa,mai hali bai sauya halinsa,wasu daga al'adar turawa har yau sunqi barin mustaphan,ko da yake ta yaya zasu barshin bayan har yau shima bai bar cikinsu ba,sam baison manyan kaya,da wuya ka ganshi da su,cikin girmamawa ya qaraso ya duqa gaban baabaan yana gaida shi,amsawa shima yayi saidai fuskanshi sam babu walwala sabanin yadda ya saba ganinsa
"Yaushe ne zaka koma" hannayensa soke cikin juna ya amsa kamar wanda baison yin maganar
"Cikin wannan satin in sha Allah"
"Allah ya lamunce"
"Amin ya Allah". Shiru ne ya dan ratsa tsakaninsu,shi mustpha na sauraron me baaban zai gaya mishi tunda shi ya aikata takanas sashensa aka kira shi,yayin da shi kuma baaban yayi banza da shi,yana so yau ya qure miskilancinsa,yaci gaba da bude shafukan jaridar dake hannunsa,sam baka rabashi da duba jaridu,duk da bai cikin sabgogi da al'amuran gwamnati a bayyane amma a badini gangar jiki da zuciyarsa na tare da su.


Har ya kammala karatun jaridarsa baiji yace komai ba,hasalima da ya daga kansa sai yaga ya jingina bayansa da jikin kujera gami da miqe qafafunsa idanuwansa a lumshe,ajjiye jaridar yayi yana sauke ajiyar zuciya,glass dinsa ya zare shima ya ajjiye gefe yana dubansa
"wato ba zaka iya tambayar dalilin da ya sanya na kiraka ba kenan"miqewa yayi ya zauna sosai yana duban baaban
"nayi zaton baka kammala abinda kake bane,banson kuma katse ka"shuru yai ya jinjina kai,duk cikin 'ya'yansa bai haifi kamar mustapha ba har yau ta kowanni fanni ya tsrerema 'yan uwansa maza da mata
"me ya kaika ture yarinyar mutane har ta suma"
"Yarinyar mutane har ta suma?" Abinda ya dinga maimaitawa ciki kwanyarsa kenan,sam ya mance wace ce,wa baabaa ke fadi ya ambata cikin zuciyarsa
"Yarinya baquwa 'yar gidan alhj farouq" har ga Allah bai fuskanci kan wa baba ke magana ba,don shi baki daya ya mance lamarin,baaban ya kalla kamar yanason qarin bayani kan abinda yake cewa,baabaan yasan irin kallo,indai mustaphan yayi ba shakka yana buqatar qarin bayani
"Tashi kaje,ka kyauta ka kuma yi abinda ya dace,nima zanyi

Please Login or Register in order to submit comment