Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saboda yadda taga ya tunzura kamar ta sokeshi da allura.

Qarar wayarsa ce ta sanyashi mai da idanunsa kan wayar,har ra qaraci ringing dinta ta katse bai daga ba,tana katsewa wani kiran ya sake shigowa,sai da ta kusa katsewa sannan ya daga
"Hello" aka fada daga can bangaren,ko bata ga sunan mai kiran ba tasan yaya yahanasu ce,tana jiyo muryarta tar kasancewar tana jikinsa

"Assalamu alaikum"mukhtar ya fada

" sai yanzu kaga damar daga kiran nawa hamshaqi?"ta fada cikin fada

"A'ah ba haka bane...." Ta katseshi da sauri ta hanyar fadin

"Ba wannan nake so naji daga gareka,munyi maganar yarinyar nan fa'iza,naji shiru baka ce komai ba" ransa ya sake baci fiye da dazu,har yanayin fuskarsa ya sake munana fiye da dazun.

"Yaaya,kiyi haquri,inaga gaskiya gwara kawai abar maganar nan,kada in zama silar bata zumuncinku ke da qawarki,domin a gaskiya bani da sha'awar qara aure a yanzu haka,mata ta babu abinda na nema daga gareta na rasa".

" iyeeee,ni muntari kake gayawa haka,kai kuwa ka rasa komai daga matarka,shekararku nawa tare,ko dan yatsa ta taba haifa maka?,hala ma haka sumayyan tace ka fadamin kenan?".

"Babu ruwanta yaya,hasalima bata san da zancan ba banda yanzu,nine kawai bani da ra'ayi".

" muntari ka bini a hankali,idan nayi maka baki fa sai ya kamaka wallahi kai ka sani,aure kuma babu fashi wallahil azim,mu zuba ni da kai da ita kanta qaramar alhakin sumayyar muga wanda zai kai qasa,banza shashasha kawai solobiyo,yarinyar da a haihuwar tumaki ka haifeta zaka tsaya tana juyaka kana tsoronta"qit ta kashe wayar daga fadin hakan.

Tuni sumayyan tayi nisa a duniyar kuka,so tayi ma ya saketa ta zauna qasa ko ta kwanta ko zata fi jin dadin yin kukanta son ranta amma yaqi sakin nata.

Cikin jarumta ta hadiye kukan nata ta dubeshi
"Ya mukhtar,wallahi kaji nima na rantse qarin aure gareka babu fashi matuqar kana qaunata da gaskiya kamar yadda ka fada,wannan kawai ya isheka ishara ka gane kashin kaji kake shirin sake yabamin bayan wanda na goga a baya,saboda haka ya zama dole ka yiwa yaayaa biyayya tunda mazaunin mahaifiya take a gareka" tana gama fadar haka ta miqe daga jikinsa ta shige dakin gadonta.

Cikin kwanakin gaba daya ta daina yi da shi,ta tsame hannu daga sabgarsa ba wai don haka ta so ba,tayi amanna auren da zaiyi ne kadai zai sama mata salama cikin rayuwar aurenta,ta tabbata ba zasu barta ba ko ba dade ko ba jima tunda bata haihu ba.

Kwanaki uku kenan zaman babu dadi,saidai ta tara yaranta suyita sabgarsu amma na ruwanta da shi.

Ranar cikon ta hudun bayan ya dawo daga kasuwa,ya tadda kayan abincinsa ta jera kamar yadda ta saba,tayi shigewarta uwar dakanta babu ita ba alamarta,toilet ya shiga yayi wanka duka tana jinsa bata ko motsa ba balle ta fito,ya gama ya kintsa cikin jallabiya,bai ko kalli abincin ba ya shiga uwar dakan tata,nan ya cimmata saman gado zaune jingine da fuskar gadon,hannunta dauke da qaramin littafin alma'asuraat,ba taka haue bace 'yar gado ce,domin gidansu gidan malamai ne akwai ilimin addini tsantsa wanda hakan ya sanya yara matan gidan basa karatun boko sam sam.

Bata dubeshi ba har ya hauro gadon ya sanya hannu ya karbe littafin ya ajjiye gefe guda,ganin tana shirin yi masa bore ya sanyashi saka qarfinsa ya riqeta gam,cikin salo ya soma rarrashinta da neman sulhu daga gareta,cike da tuburewa ta dubeshi
"Karbar auren nan ne kadai zaya samo maka kaina yaa mukhatar,idan ba haka ba zaka iya tafiyarka muci gaba da zama a haka,ya fiye min akan danginka su dinga ganin na mallakeka,kullum ban da kwanciyar hankali ko nutsuwa a cikinsu" ta qarashe maganar zuciyarta na sake yin rauni,dama can a raunane take,dakiya da haquri yasa take iya sabgoginta kamar bata da damuwa,tun asali mutumce mai zurfin ciki,bugu da qaari zamanta da mukhtar babu wani abun tur da yake mata don haka bata iya fadar matsala ko kai qara ba.

Ya kusan kwashe minti talatin cikin nazari da dogon tunani,har ta fara jan abun rufa zata yi kwanciyarta tana tsammanin yana kan batunsa,ya waiwaya cikin sanyin jiki ya dubeta
"Sumayya,ina sonki kin riga da kin sani,babu kuma abinda na nema na rasa daga garekin,ban dauki rashin haibuwarki a wata matsala ba,saboda na riga da na sani cewa bawa bai isa ya tasara kansa *KUNDIN QADDARARSA* ba,tunda kina gani shine buqatarki kuma shine kwanciyar hakalinki na amince".

Duk da hakan take buqata saboda tasan shine samun salamarta daga hannunsu yaa yahanasu amma sai da wata 'yar banzar faduwar gaba ta ziyarceta,ta hadiye wani abu sannan tace

" shikenan,amma ya kamata gobe kafin ka dawo gida kaje ka sanar da yaayaa yahanasu amincewarka,so nake ta daina zargi ko jin haushina"kallonta ya waiwaya yayi,saboda a yadda tayi maganar shi zai nuna maka akwai ragiwar zallar quruciya a tattare da ita,bai son zuwan saboda haka ya kada kai yace

"Bazan je ba saidai idan zaki shirya muje tare".

Ido ta dan zaro don har ga Allah batasan ya hafuwarsu zata kasance da ita ba,amma sai dabara ta fado mata,kasancewar babu wani nisa sosai tsakanin gidansu da gidan yaya yahanasun bazai wuce naira talatin ba kudin mota

" eh zani,amma saidai ka ajjiiyeni a gida,idan ka dawo kazo ka daukeni mu tafi"baice komai ba ya tire bargon ya shige ciki tare da janyota jikinsa,da sauri ta dubeshi
"Abinci fa kaci ne?" Kai ya girgiza mata
"Na qoshi"
"Amma yaa mukhtar bai......."
"Shshshshsh" yace da ita sai tayi shirun tare da komawa ta lafe ajikinsa,ta sani tunda yace bzaici din ba bazai ci ba,ita kuma bata saba musu da shi ba saboda girman da yake da shi a idanunta.

Cikin dare ta kasa barci,itadai bata san kishi ba tunda bata taba soyayya ba saboda shekarunta sha biyu a sanda aka aurar da ita,tadai auri yaya mukhatar,kuma tanaji a zuciyarta tana sonsa bata so wani abu ya rabeshi,amma tana jin babu dadi duk sanda ta tuna zai kawo wata gidan ta zauna tare da su,ya dinga kulata kamar yadda yake kulata,da tunanin yaqi qare mata sai ta sauko daga saman gadon,ta sadada ta fita ta daura alwala ta kabbara sallah.

Kusan wannan tarbiyyar gidansu ce tun kafin tayi aure,mamarsu tasha gaya musu duk sanda suka kasa barci da kwanciyar banza suyita zaman tunani gwara suyi salla,zasu samu lada kuma daga bisani baccin yazo,a lokacin dariya sumayya take qyalqyalewa da shi saboda tsantsar quruciya,takan ce
"Nikuwa mama mai zai hanani bacci?,bacci fa dadi ne da shi wallahi mama,baki ga da qyar nake iya tashi nayi sallar asuba ba,wataran ma sai kin sanya tsumagiya kin dakeni?" Murmushi kawai uwar takeyi kana tace
"Sumayya kenan quruciya mai dadi ko" sai ta sake yin dariya tace
"Hmmm,mama kenan,nikam babu abinda zai hanani bacci na,ga katifata mai laushi,ga iskar fanka".

Washegari tare suka tashi,shi ya dinga taimakata da ayyukan gidan kamar yadda suka saba yi wadansu lokuta,sunayi yana tsokanarta saboda ya fuskanci tamkar bata da walwala,hatta sallar jiya a idanunsa tayi kasancewar shima bai samu isasshen bacci ba,sai goma ya fita yana gaya mata ta shirya bayan sallar magariba idan ya dawo zasu fita.

Qarfe shida ta kammala girkinta ta tsaftace gidan,ta hada kan yaranta ta zuba musu abinci cikin kwano daya,sannan ta kwashe na mai gidan ta kai falo ta jera sannan ta shiga wanka tana gaya musu saura ta jiyo su suna fada,duk wanda yayi fada ba ruwanta da shi.

Tsaf ta shirya cikin wami swiss lace mai matsakaicin kudi cikin kayan sallarta yake,sanyawarta daya wannan ne na biyu,mukhtar akwai qoqari da zuciyar yiwa iyali,sosai yayi mata kyau,ya sake fidda zallar quruciyarta,tana cikin fesa turare ta jiyo yaran na yi masa sannu da zuwa,bai shigo yau da babur din nashi ba saboda zasu sake fita.

Ta fito sanda yake raba musu alewa suna karba suna godiya kana suka yi mata sallama suka fice,haka ta koya musu,da ya dawo ko bata fada ba zasuyi mata sai gobe su tafi saidai idan ita ta tsaidasu,idanunsa a kanta ya bude mata hannayensa ta tako a hankali cikin kunya ta shige cike ya kulleta gam cikin qirjinsa yana fadin
" kinyi kyau my sumy ta"siririyar dariya ta saki cike da jin dadin yadda yake yaba kwalliyarta.

Wanka ya shiga yayi a gurguje saboda qaratowar lokacin sallah magariba,y hada da alwalarsa ya fice,bayan ya dawo ya shirya cikin shadda ruwan bula mai turuwa(dark blue)wanda yayi shige da lace din jikinta,dariya ta dinga ganin yadda yake waqar(munyi anko da anko)irin ta yara.

Gidan yaya yahanasu taga sun nufa,bugawa qirjinta ya dinga yi,bata so ta masa magana yaga kamar tana qin 'yan uwansa,tunda duk tsiya naka naka ne,sai da ya faka babur dinsa qofar gidan sannan yace da ita
"Idan mun gama da nan gidan mama zamuje ki gaidasu" hakan ne ya dan sake sa mata nutsuwa,"to"kawai tace da shi.

Yana gaba tana biye da shi kamar wadda za'a kama,a tsakar gida suka ci karo da yaron yaya yahanasu wanda bazai wuce shekara goma sha uku ba,ya gaida mukhtar ya amsa yana ce masa
"Jeka qofar gida ka kulamin da machine dina kafin na fito"
"To kawu" ya fada yana ajjiye modar hannunsa saman randa ya fice.

Suna shirin shiga rumfarta tana daga labulen dakin
"Au sai yau kaga damar zuwa kenan......shashan yaro ana maka gata kana noqewa" ta fada tana sakin labulen ta juya zuwa ciki.

Bata lura tare suke ba sai da suka shiga ciki suka zauna,sumayya ta gaisheta ta amsa sama sama,ganin idonta sam bai hana yaya yahanasu yin duk maganganunta ba,ita dai kam kanta ta sunkuyar,daga bisani ta miqe ta basu guri jin musu nason barkewa tsakanin mukhtar da yaya yahanasu kan lissafin abinda suke da buqatar ya bada,kama daga kudin aure kudin zance lefe har zuwa sadaki,yace zaya bada kudin aure da na sadaki amma shikam bazaya iya yin wani lefe ba,kasuwa babu ciniki,nan ta barsu batasan yanda suka kaya ba yadai fito yace ta tashi su tafi.

Ko sallamar da take wa yaya yahanasun bata tanka mata ba har suke wuce,suna kan hanya babu wanda yace da dan uwansa komai har suka qarasa gidansu.

Ciki ya shiga suka gaisa da maman nata kasancewar abba malam mahaifinsu kamar yadda suke ce masa baya nan,'yan qannanta duk suna tsakar gida mukhtar ya raba misu biscuite kamar yadda ya saba,ya miqe zai fice yana cewa zai zaga bayansu gun wani abokinsa idan ya dawo zai kirata su wuce tace tom.

Gaisawa sosai sukayi da mamanta ta tambayi lafiyarta da ta gidanta ta amsa mata da komai lafiya.

Shiru ne ya biyo baya,tunanin abinda ya faru dazun gidan yaya yahanasu yayi nasarar wafce tunaninta ba tare da ta shirya ba,haka maman ta tadda ta,ta ajjiye kwanon dambun data je debo mata
"Lafiya dai ko sumayya" murmushin yaqe tayi ta janyo kwanon dambun tana budewa sannan tace
"Mama aure yaya mukhtar zai qara" maganar ta dan taba maman,tsakanin da d'a da mahaifi,tausayinta ta dinga ji yana ratsata,babu shakka abu ne mai wuya zama da kishiya a wannan zamanin,abu ne da har yau yaqi dadi a cikin gidajen aurenmu,ga yarinyar tata gwanar haquri da shegen zurfin ciki ce,amma duk da haka ta sani ba duka aka taru aka zama daya ba,duk abinda zata gaya mata a yanzu shi zai zame mata madubin dubawarta.

Murmushi maman tayi sannan tace
"Babu komai,ai namiji mijin mace hudu ne,Allah ne ya halasta masa,abinda nake son gaya miki kawai shine kada ki soma cewa zaki tada hankalinki ko ki daga hankalin mijinki,ki zauna da ita tsakani da Allah,ki sauke duk wani haqqi nata dake wuyanki,sumayya kada ki sake kice zaki cuceta,idan kika cuceta sumayya ni mahaifiyarki ban yafe miki ba".

Kai ta gyada" in sha Allahu mama zanyi duk abinda kika ce,da ikon Allah bazan zama mai sabawa maganarki ba"a hankali maman ta dinga hilatarta tana kwantar mata da hankali har ta kusa cinye dambun baki daya.



*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍🏽 *~KUNDIN QADDARATA~*✍🏽
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

_bismilla hir rahmanir rahim_


*inna ma'al usri yusrah,fa inna ma'al usri yusrah*

______________________



0⃣3⃣




    Suna cikin hirar mukhatr ya turo qaninta mubarak yayi kiranta ta fito zasu tafi,nan mama ta hada mata su kuka kubaiwa daddawa barkono har da tsakin masara saboda dambu ko dan malele,tana hada mata kayan tana dada kwantar mata da hankali tare da jaddada mata kada ta sake ta tashi hankalin mijinta ko ita kanta,ko tace zata yi wani rashin kyautawa ga daya daga cikin 'yan uwan mukhtar,haihuwa kuwa lokaci ne,idan Allah yaso ma sai taga sanadiyyar shigowar wata ita ma ta samu nata rabon,ta dora da cewa
"Bare ma duka duka nawa kike sumayya,mu a da can Allah na tuba ba sai kiyi shekara goma da aure baki haihu ba babu wanda ya damu da ke,haka kema baki damu kanki ba,ci da zuci ne kawai yanzu irin na yaran zamani" maganar sai ta bama sumayya dariya da kunya,har ta sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta.

       Suna shirin kwanciya bacci lokacin yana zaune gefan gadonsu yana shan ruwan baqin shayi,ita kuma tana taje kanta,ta cikin madubin yake qare mata kallo yadda kullum take sake zama cikakkiyar mace,tamkar ba zata masa magana ba amma abun nata cinta a zuciya,saboda daga shigowarsu gida zuwa shirin kwanciya da sukeyi yanzu yaya yahanasu ta kira shi ya kusa sau biyar,duk da bata kusa amma ta fahimci taqaddamar me suke,maganar lefe ne da yace ba zaya yi ba,ta dan cije lebanta sannan tace
"Ya mukhtar"
"Ya akayi sumy?" Ya fadi yana saurarenta.

    Sai data jawo dressing chair gabansa ta zauna sannan ya dubeshi,cikin nutsuwar nan tata hadi da kaifin hankali da zurfin tunani
"Ya mukhtar kayi haquri idan na maka shishshigi,sai nake ganin baka kyauta ba",cikin rashin fahimta ya tambayeta
" da akayi me fa?"ta danyi jim kamar ba zata yi magana ba sannan tace
"A ganina bai kamata ka dinga sa'insa da yaya yahanasu ba,ko banza ta girmeka,bugu da qari ita ta zame maka tamkar mahaifiyarka ka manta?,ita ta raineka har ka kawo girmanka,ka san cewa dai ba zata taba yin abinda zai cutar da kai ba,a ganina auren nan saboda qaruwarka ne take buqatar kayi,ko babu komai idan fa'iza ta haihu sai an fara cewa danka kafin a ce dan yaya yahanasu ko?" Ta dan sarara da maganar tana hadiye wani abu mai daci wanda bata san meue sanadiyyar tasowarsa ba daga qirjinta.

     Ko bata qarasa ba ya fahimci kan me take magana,saboda haka ya bata fuska
"Kinga sumayya,babu ruwanki da wannan maganar ki fita a cikinta,lefe ne nace bazanyi ba suyi mata,ai bani nace ina son auren ba ko?,ina zaman zamana haka kawai ina lallaba rayuwata sai su baro min aikin da bani na saka su ba?".

       Kai take gyadawa idonta cikin nasa wanda tuni ya tara qwalla shirin zubowa kawai take
" na gode ya mukhatar,ina ka taba gani an auri budurwa ba'a yi mata lefe ba?bayan haka kuma ka riga da ka san cewa matuqar bakayi lefe ba to sumayya ce ta hanaka,duk wanda yaga laifina ko ya zageni ya mukhtar kai ka jawomin"sai ta tashi daga saman kujerar ta haye gado ta lulluba har saman kanta kaana ta fashe da kuka.

     Har cikin ransa ya dinga jin shigar kukan nata,ya runtse ido yana jin bata can can ci haka ba,da me zata ji cikin abu ukun,sai ya sanya hannayeshi ya dagota baki daya zuwa jikinsa yana goge mata hawayen tare da fadin
"Ya isa sumayya,ya isa,me kike so ayi?,gaya min" sai da taja hanci kadan sannan tace
"Kayi lefe kamar yadda yaya yahanasu ta buqata"
"Shikenan an gama,sunci darajarki" sai ta saki dan qaramin murmushi sannan tace
"Na gode".

       Washegari yana cikin karyawa kafin ya fita wayarsa ta soma ringing,sumayya ta dauko ta miqa masa da yake tana kan t.v stand tana chargy,daga yanayin maganarsa kawai ya tabbatar mata yaya yahanasu ce,kuma zancan jiya ne bai wuce ba,a gimtse ya amsa cewa zaiyi laifen,amma fa sam shi ba kudi zai bada ba,zaiyi iyakacin abinda zai iya ya kawo musu,daga haka ya kashe wayan ma baki daya,tana gefe tana saurarensu kanta sunkuye tana wasa da yatsun hannunta,ya kammala ta masa rakiya kamar yadda ta saba,dawowa yayi da baya ya rungumeta sannan ya sumbaci goshinta
" Allah yayi miki albarka"ya fada yana sakinta
"Amin ya mukhtar" ta fada cikin farinciki,saboda tuni maman ta ta gaya mata albarkar miji na bin mace,hakanan fushinsa ko  yardarsa na tare da ta ubangiji.

     Cike da farinciki ta koma cikin gidan saboda albarkar da ya sa mata ta faranta mata,taci gaba da kintsa ragowar ayyukan da suka rage mata,bata jima da kammalawa ba ta zauna tana hutawa wayarta ta dauki qara,da sauri ta daga ganin sunan abbanta na yawo bisa screen din wayar.

     Cikin girmamawa ta gaidashi ya amsa mata yana tambayarta gida da kuma mukhtar tace ai yama fita.

"Mamanki ta gaya min mukhtar zai qara aure"
"Eh abba malam"
"To ina fata ba zaki watsa mana qasa a ido ba,ba za kiyi watsi da tarbiyyar da muka baki ba"
"In sha Allahu malam"
"To Allah ubangiji ya albarkaceki ya albarkaci aurenki" daga haka ya dora mata da nasiha cikin hikima da ilimi,cike da fadar Allah da ma'aikinsa,hakan ba qaramin sake kwantar mata da hankali yayi ba,ya qare nasihar tasa da fadin
"Babu wani abu da kike buqata?"
"Eh babu malam" ta fadi hakan saboda babu abinda mukhtar ya gaza da shi,don hatta kudin kashewa yakan qimanta ya bata,ya danganta da yanayin samun da yayi a kasuwa.

"To shikenan,haka ake so,inaga zan duba wajen sati na gaba ko wajejen satin sama,zan aiko abubakar(yayanta ne shine na fari a gidansu,amma baiyi aure ba karatu yake)zaizo. A fidda kayan gadonki da kujerunki a sauya miki wasu" farinciki ya cikata,duk da cewa wadan nan natan ma babu abinda sukayi,don sanda sukayi shekara hudu da aure mukhtar ya fitar da na aurenta na ainihi ya sauya mata su.

"Na gode,na gode qwarai malam Allah ya saka da alkhairi,ya qara lafiya da nisan kwana mai amfani,Allah ya qara budi da rufin asiri"
"Amin ya Allah,amma abinda zaki biyani da shi kawai kici gaba da zaman aure cikin gidanki"
"Da yardar Allah malam" ta amsa masa daga haka sukayi sallama.

     Sosai malam yake aon sumayya,don tun tana mitsitsiyarta halayyarta daban take,tana da tarin haquri kawaici da zurfin ciki,shi yasa duk cikin yaransa yafi sonta,duk da cewar dukan yaran nasa maman sumayyan ce ta haifesu,ko a lokacin da suka aura mata mukhtar ma ce mata kawai yayi ga miji yayi mata kuma aure zaiyi mata,bata ce komai ba don ba wayo gareta ba,duk da haka dama kunya gareta,gudu tayi ma ta bar gurin sanda malam din ke gaya mata,ita ce yarinya mace ta farko a gurinsa sai qannenta su hudu.

    Mukhtar zamu iya cewa rako wani abokinsa yayi gurin malam din kasancewar malam din yana bada karatu tsakanin sallar magariba da isha'i wa matasa da dattijan unguwa,gani daya ya yiwa sumayya yaji tayi masa kasancewarsa mutum wanda sam baya da sha'awar auren macen da tayi zurfi a karatu,tunda yayi universty shima yaga irin qazamar rayuwar da mafi yawancin 'yammatan keyi duk da ba duka aka taru aka zama daya ba.

     To sara ne yazo kan gaba shima malam ba mai son yaransa suyi bokon bane,saboda haka yana bincike kan mukhtar ya tabbatar da nagartar halayyarsa ya basu auren sumayyan.

     Da fari 'yan uwansa sun so su turje kan mai zai sa ya auri yarinyar da rainonta kawai zaiyi,musamman yaya yahanasu wadda ita ta riqe mukhtar din,saboda bai wuce shekara biyar a duniya ba Allah ya yiwa mahaifiyarsu rasuwa wanda dama tun mukhtar na da watanni a duniya mahaifinsu ya rasu,to amma daga bisani suka haqura kasancewar sun lura mukhtar din bashi da niyyar fasa aurensa.

     Da fari sun karbi sumayyan a matsayin 'ya kuma qanwa,amma daga lokacin da suka lura da gatan da mukhtar ke mata hassada ta soma aiki,duk da ba zaka kirashi mai kudi ba amma mai arziqi ne,iyalansa sunfi qarfin yin kukan rashin wani abu cikin gidansa,shekara uku tayi ta cika shekara sha shida,a lokacin ta zama mace saboda Allah ya mata halitta da jiki mai kyau,sai suka juya akalar hassadarsu kuma zuwa sa mata idon yaushe zata samu ciki?,yaushe zata haihu?,wanda har yau suna bisa wannan bigire basu sauka daga kai ba

Wannan kenan.....

      Sati hudu suka sanya lokacin aurensu,sunata budirinsu suna shirye shiryensu ango ko oho,kayan lefe ne yace zaiyi kuma bai fasa yi din ba.

     A falonta ta tadda shi yana amsa waya bayan ta gama soya masa wainar fulawa da yace yana sha'awa har tana ta masa dariya qai qwalama ce kawai ta dameshi,mai ya hadashi da abincin mata,ya sauke wayar daga kunnensa yana janyo plate din tare da budewa yana fadin
"Yauwa amaryata kuma uwargida na" qeya ta juya masa tana turo baki
"Um_um,barni a uwar gidan dai,amaren na nan tafe" cikin sigar tsokana ya dan talle mata qeyar data turo masa
"Ka jini da yarinyar nan wai itama ta iya kishi?" Duk da tasan wasa yake sai ta juyo tana dubansa zuciyarta na raunana amma ta dake
"Don me bazanyi kishinka ba ya mukhtar?" Bai so maganar tayi tsayi don bata masa rai maganar take balle ita saboda haka yace
"Haka ne" a taqaice sannan ya hau qirqiro santin waina duk da cewa a zahiri tayi dadin,biye masa tayi tana masa dariya tare da kara masa filo a bayansa.

    Sai da yaci kusan rabi sannan tace da shi
"Nikam yaya mukhtar banga kana shiri ba" cikin son samun qarin bayani yace
"Wanne irin shiri?,name?"
"Banga wani sauyi ba agidan nan?"
"Kamar wanne iri fa" ya sake tambayarta
"Gani nayi kace na kwashe shirgin dake cikin dakin shirgin can nan amarya zata zauna,nace maka ka hada mata da naka dakin itama ta samu falle biyu ka qiya,to a barshi a hakan,amma ya kamata ace daga dakin nata zuwa tsakar gida ko shafen farar qasa ka yi masa don ya haska ko,tunda nawa dakin ba'a jima da yi masa fenti mai tsada ba fes yake kamar yau akayi".

    Banza yayi da ita kamar bai ji ba har sai da ta qosa tace masa
" kana jina kuwa ya mukhtar?"
"Ina jinki kuma bazan yi ba,ke wallahil azim kika sake yimin magana makamanciyar haka sai ranki ya baci,idan zata zo ta zauna haka ta zauna,idan ba zata zauna ba ta qara gaba dama ba ni na gayyatota ba,haba,dame kike so naji?".sai ya miqe a fusace ya fice zuwa dakinsa ya barta da sauran wainarta.

     Jikinta ne yayi sanyi,tayi da na sanin yi masa maganar,sai data bashi kusan awa guda sannan ta gyara gurin ta shirya zuwa shigar barci tabi bayansa don ta lallashe shi.

     Bata sake masa maganar ba kuwa,sai ranar asabar ranar 'yan yaranta duka suna gida saboda ba ranar karatu bace,ta aika nana tayi mata kiran wani dan saurayi dake maqotansu,tace ya duba mata don Allah farar qasa kwano nawa zai isa dakin zuwa tsakar gidansu ya gaya mata yadda yake zaton zata isa,cikin kudin da take adanawa ta qirgo ta bashi har da kudin mota,cikin minti talatin ya dawo,tasa ya jiqa mata sannan ya tafi ta masa godiya ta bashi dari tace yasha ruwa.

      Yaranta ta kalla wadanda sun kai su takwas,akwai bilkisu,fatima,hauwa'u,khadija,aisha,ummi,asma'u sai nana ta gurinta
" maza kowa yaje gida ya cire kayan jikinsa ya saka marasa kyau zamuyi fenti"cikin zumudi kuwa har suna rige rige suka fice suna murna.

     Kafin su dawo itama har ta sauya nata kayan,saiga yaran kuwa,nan suka zage suka dinga shafen farar qasar,abinka da ba aikinsu bane tun safe har bayan la'asar,nan ta musu girki suka ci,idan sun huta su dora.

    Cikin haka sai ga maman nana ta shigo,salati ta saka tare da kama habarta ganin sumayya saman tsani,duk sunyi face face da farar qasa
"Ni salma,ai nayi zaton qarya nana take da tace fenti zakuyi ashe da gaske take",dariya ta qyalqyale da ita tana saukowa daga kan tsanin
" to ya zanyi maman naana,ya mukhtar yaqi yarda yayi fenti,shi yasa na siyo da kaina mukeyi ni da 'ya'ya na"(da yake ita kadai ta gayawa zancan,saboda yadda take mata tamkar mamanta,tafi shaquwa da ita fiye da sauran iyayen yaran.

    kai maman naana ta dafe tana cewa
"Lallai sumayya quruciya na damunki,yanzu kishiya kike yiwa fenti da kudinki da jikinki,Allah ya shiryeku" ta fada tana dariya
"To sauko hakanan na kira muku jamilu(babban danta) ya qarasa muku,tunda kun rantse sai kunyi" murmushi tayi tana kakkabe jikinta tare da fadin
"Ai kuwa mun gode" da kanta maman naanan ta leqa ga nemo jamilun,cikin 'yan qananun mintina ya qarasa musu inda basu qarasa din ba.

"Magana ba zata yiwu

Please Login or Register in order to submit comment