Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kayi,zaka gani,ke kuma ku zuba mu gani" sannan ta fice.

         Tabbas ba don har tanzu bai cimma qudirinsa ba akanta da yau babu abinda zai hanata kwana cikin gidan ubanta,gefensa ta zauna ta sanya hannunta cikin nashi sannnan tace
"Sam hakan ba girmanka bane ya mukhtar,tunda nake ban taba gani ka daki wani ba ma bare matarka ta aure,yin hakan ba daidai bane,na roqeka don Allah kada ka sake sai ka fara bani tsoro ai" ta qarasa fada a shagwabe,sai ya dago yana dubanta da murmushi,take kaso saba'in cikin dari na bacin ransa ya zabge ga fadi sai ya dora hannunsa shima saman nata
"Banaso ki fara jin tsoro na sumy ta,idan kika fara tsoro na na zauna da wa?,bazan sake ba,kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi
"Kai ya kamata nace kayi haquri yaya ka yafe mana,yau mun sanyaka cikin bacin rai" kasa magana yayi sai ua rungumeta kawai cikin jikinsa yana jin duminya,yana ganin girma da qimar wannan halitta mau tsananin hankali da biyayya a gareshi,shikam mai zai hana shi faranta nata matuqar yana da iko?,me ya isa ya hanashi sonta a duniya?,babu shi,babu shi ko mene,koda QADDARA ce baijin tana da wannan qarfin ikon,baya fata ma QADDARAR tazo masa ta wannan sigar,gwara ta kowacce siga amma banda wannan,wala'alla ya iya jurewa.

          Sai da suka fara jiyo qaurin girkinta sannan ya saketa ta miqe da hanzari ta fice tana ce masa tana zuwa.





*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)





1⃣7⃣


________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*ma asaba min musibatun fil'ardi wala fi anfusikum illa fi kitabim min qabli an nabra'aha*
_______________________





             Cikin mintuna qalilan ta kammala jallope din taliyar ta rarraba cikin coolers,mukhtar din ta fara kaiwa,tana niyyar juyawa ta fita yace da ita
"Wannan cooler din fa na waye?" Ta dubi cooler din sannan ta dubeshi
"Na fa'ixa ne a ciki"
"Ajjiye a nan" ya fada yana gwada mata inda zata ajjiye din da idonsa,bata kawo komai cikin ranta ba ta ajjiye din ta nufi dakinta.

            Can ta taddasu sun baje suna kallo,duk da cewa kallo daya zaka yiwa yahanasun kasan tabbas har yau ranta a bace yake,ta dire cooler din tana cewa
"Ga abincinku yaya" wani banzan kallo ta watsa mata
"Eh zamu ci ai kuma zamu ambaci sunan Allah,in sha Allahu babu abinda zai samemu,makira,idan ma shiga kika tsakaninmu da fa'iza har take wannan tashan rashin kunyan to ni zanyi maganinku ke da iyan baki daya" kai ta kada ba tare da tace komai ba ta shige uwar dakinta,ta tube kayanta ta sauya na bacci,sai tayi zamanta gefan gado ta janyo RIYADUL JANNAH littafin addu'o'inta da malam ya bata wanda bata rabi da shi ta soma duba wasu shafuka.

          Sumayyan na fita ya dauki cooler din baki daya ya fita da ita waje,wasu almajirai da rabonsu ya rantse ya samu qofar gida zazzaune ya basu,take suka karba suka rabe a tsakaninsu suna zabga godiya banza ta faadi garesu.

             Yana kammala rufe gidan sukayi karo da fa'iza wadda ta dawo daga dakin sumayya ta bankade labulenta ko kallo su ya yahanasu basu isheta ba ta qwallawa sumayya tambayar ina abincinta,tana daga cikin dakin ta gaya mata yana gun yaya mukhtar.

          Dubansa tayi"ina abinci na?"banza ya bawa ajiyarta yayi wucewarsa,sai ta bishi da kallo,bata haqura ba tabi bayansa tana sake tambayarsa,wani wawan birki yaci wanda sai da ya sanyata ja da baya
"Baki daku ba kenan ko?,tare muka hada muka siyo abincin?,ko kinzo da bayi ne daga gidanku?,uban wani ne ya hanaki dafawa kici,ki fice min daga nan tun kafin na hasala na sake kikkifa miki mari" tana qunquni ta juya ta fice ranta qunci fal,ga uwar yunwar dake sakadarta,abinka da mutum mai shegen ci ta riga da ta saba.

            A tsakar gida taci karo da jamila na wanke hannunta,da gayya ta bangajeta tayi taga taga ta fadi,sai ta miqe kuwa ta lailayawa fa'izar ashar abinka da itama tana ji da tata rashin kunyar,ai kuwa fa'izan tayo kanta zata huce bisa kan nata,dai dai sanda yaya yahanasu ta qaraso tayi hanzarin riqeta ta gabza mata mari dama tana ciki da ita ne,tana waiwayowa kuwa ta cakumi wuyan yaya yahanasun take jamila ta shigarwa uwarta nan fada ya kaure tsakanin su ukun.

           Sumayya ce ta fara fitowa,cikin tashin hankali taje dubansu idanunta a waje,dambe da yaya yahanasu?,tab,lallai fa'iza ta kai,dakin mukhtar ta nufa da hanzari tana mamakin me ya hanashi fitowa,ga mamakinta yana tsaye bakin window yana kallonsu,saidai idanun nan sun kada sunyi jazur,a hankali ya juyo ya zuba mata su,itama sai jikinta yayi sanyi,tausayinta ya kamashi,babu shakka wata jarrabawa ce ta fado rayuwarsu,idanunta suka cika taf da qwalla ta tausayin mijin nata,sai kawai ya saki labulen ya taka a hankali ya fita tsakar gidan,wata gigitacciyar tsawa ya sakarwa fa'iza dake tsakiyarsu tana cin na jaki wadda tsawar sai data sanya hanjin sumayya hadewa ya cure guri guda,ta runtse idanunta tana jin ruguginta na ratsa kunnanta.

         Nuni kawai ya yiwa fa'iza da hanyar dakinta yana mata wani irin kallo mai cike da tsana,ba musu ta wuce jikinta na rawa,ya juya ya dubi yaya yahanasu sai kawai ya kamata yayi dakin sumayya da ita.

          Bakin rijiya ta zauna,sai ta kasa daurewa idanunta ya shiga fidda qwalla,wannan wacce iriyar masifa ce lokaci guda,duk wani farinciki da zaman lafiya na gidansu yayi qaura lokaci daya?,tana share hawayen idanunta tana tausayin mukhtar dinta.

           Tana zaune a nan mukhtar din ya fito ya shige dakin fa'iza,a nan ne ta jiyo tashin muryarsa saidai nan din ma bata ji duka abinda yake fadi ba,daga bisani ne ya fito,ta miqe tsaye ta isa gabansa tana kallonsa,tabbas taso ace yau ranar girkinta ne,ta lallashi mukhtar din,saidai sam bata da wannan damar,karyar da kai tayi murya a tausashe tace
"Kayi haquri don Allah yaya mukhtat,komai na duniya mai wucewa ne,jarrabawa ce daga Allah" murmushin qarfin hali ya saki ya shafi gefan fuskarta
"Babu komai my sumy,kije ki kwanta,kuma ban lamunce ki sanya abun cikin ranki ba,ki kwanta kiyi bacci sosai" ya sanya bakinsa yayi kissing  goshinta,sai ya bata kunya har ta dan murmusa,yana tsaye har ta wuce dakinta sannan ya juya nashi.

           Ko da ta isa dakin tuni ta taras da su sun rarrashe kan gadonta,sai yaya yahanasu dake zaune gefan gadon tana huci,abinda take da buqata ta dauka zata fice taji sakin qwafar da yaya yahanasu tayi,ranar kan doguwar kujerar falo ta kwana,saidai tayi qoqari kamar yadda mukhtar ya buqace ta tayi bacci ta qoqarta tayi na 'yan awowi.

*******************

        Cikin kwanakin gaba daya mukhtar ya fita harkar fa'izan duk da cewa daman can ba shiga yake yi ba,saidai duk wani abu da yake haqqinta ne kansa yana sauke mata bakin gwargwado.

           Zaman yaya yahanasu a gidan ya dauki sabon salo,wani irin zama ake a gidan,sosai yaya yahanasun kejin haushin fa'izan gami da ganin baikenta tun farko data daure gindin dan uwanta ya zama miji gareta,sai dai kuma duk da wannan bai hanata jin haushin sumayya ba,gani taje tamkar itace ta shiga tsakaninsu.

          Duk kwanan duniya gari na wayewa da zarar mukhtar din ya sanya qafa ya fice itama fa'izan ke ficewa,ba zata dawo ba sai yaba gab da dawowa koda kuwa ranakun girkinta ne,sai a sannan zata tsiri girkin dare shima tsoron hukuncin mukhtar din ya hau kanta take,ba qaramin horata yayi ba lokacin da ya amshi maqullin locker din abincinsa daga hannunta ba,da rana kuwa saidai kowa tashi ta fishsheshi,shiga su jamila suke kitchen kansu tsaye su girka duk abinda suka ga dama,su din ma ba baya bane wajen iya barnar abinci da ta'adi,sam ko sau daya sumayyan bata taba daga kai ta dubesu ba bare ta gwadawa mukhtar abinda sukeyi cikin gidan,dakinta kam tuni ta sallama musu shi,ta dauke kai baki daya da shi saboda yadda suke abinda suka ga dama cikinsa,wani abun da gayya da gadara suke mata,koda bata tankasu ba sukan bude baki suce "kayan dakin da kudin dan uwansu aka sauya su" sau tari dariya abun yake bata,ta kuma godewa Allah da ya sanya iyayenta masu rufin asiri da zuciyar yiwa iyalinsu ne,suma sun san da haka,babu shakka da Allah kadai ne yasan halin da zata tsinci kanta ciki,hatta da kayan sawarta sai suka fara dauka dai dai da dai dai suna sanyawa idan zasu fita wata unguwa ko biki,ranar da mukhtar ya soma gani ransa ya baci matuqa,bai iya jurewa ba sai da ya kirasu ya musu jan kunne.

            Ganin haka ya sanya mukhtar yace ta debe duk wani abu nata mai amfani ta dawo da shi dakinsa,ya bude ma'ajiyarsa ya adana mata ciki.

            Fa'iza kuwa tsakaninsu da yaya yahanasun da yaran ma baki daya sai harare harare da baqar magana,wanda yawanci ma sunfi yi da jamilan ko sayyada,bata san me mukhtar ya gaya musu ba amma da alama shi ya kawo wannan dan qaramin sauyin da aka samu.

          Cikin wata d'aya kacal mukhtar ya kammala musu gyaran suka tattara suka koma nasu gidan,ko a ranar da zasu tafi din ma sai da ka kusa kwata ta ranar da suka zo din,da zagi suka rabu,ba qaramin qona ran yaya yahanasun abun yayi ba ganin mukhtar din ya gaza daukar kowanne irin mataki,abinda bata sani ba shine ya fita jin takaicin abinda ke faruwar,saidai ya riga da ya tsarama ransa sai sun gama d'aukar darasin rayuwa tukunna.

*********************

           Qarfe takwas na dare ya iso gida tun bayan fitar da yayi da safe sakamakon aiki da suke a shagon sa na kasuwa,sosai yake a gajiye tiqis,saidai yasan cewa abu mafi muhimmanci shine ya adana gajiyarsa,matuqar fa'iza ke da girki babu wani abu da yake iya tsinta ko ya dorar a wunin ranar baki daya,qarin gajiyarsa machine dinsa yau da ya masa tsiya ya baroshi gun bakinike ya tari adaidaita ya iso gida.

         Babu wutar nepa a unguwar tasu hakan shi ya sabba ba duhun da gidan yayi,sai hasken fitila daga dakin sumayya dakin fa'iza da kuma kitchen din gidan.

           Bashi da sha'awar yin tozali da fa'izar ko kadan,saboda haka ya bude dakinsa ya shige da zummar zuwa ya rage kayan jikinsa ya koma bayi ya tanadi ruwan wanka,hular kansa ya cire ya jefata saman gadonsa,ya balle maballan rigarsa ya zareta ya ajjiye sannan ya nufi window dinsa ya yaye labulen don ya bawa iska damar shigowa.

            Kamar wanda aka kira idanunsa suka sauka kan kitchen,fa'iza ya hango,da farko yayi niyyar dauke kansa,saidai wani abu da ya hango shi ya ja hankalinsa,idanu ya zuba sosai don yana son ya tabbatar da abinda idanunsa ke gane masa,baiso yayi hukunci bisa kuskure zato ko tsammani.

            Sakin labulen yayi sannan a hankali ya fita izuwa kitchen din cikin takun sanda,bakin window ya isa sannan ya lafe daga jikin bangon yana kallon komai tar kamar yadda idanunsa suka soma nuna masa daga cikin dakinsa,yana tsaye harta sheqe da dariya sannan tace..............





*mrs muhammad ce*

📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)





1⃣8⃣


______________________
*Bismillahir rahmanir rahim*


*innal laha huwar razzaqu zul quwwatil matin*
______________________



"Mukhtar!,mukhtar!!,hmmmmm" haka ta fadi sannan ta maida murfin food flask din ta rufe tana ci gaba da dariyarta cike da nishadi da jin dadi.


A hankali ya zare jikinsa,cikin tafiya ta sand'a kamar yadda yazo haka ya koma,bakin gado ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa biyu,zuciyarsa na rawa saidai baiso ya bata dama,oh Allah!,tun yaushe?,tun yaushe ya fara turawa kansa wannan qazantar?,me ya samu yaya yahanasu ne har udanunta suka rufe ta kai ga nannade hannu zata jefashi ramin halaka?,me ta gani ne wai gun fa'iza ya burgeta har ta nemi suyi tarayya wajen hada zuriyya.


Sallamarta ta katse masa zaren tunaninsa,ya daga kansa wanda idanunsa suka kada jazur ya dubeta,tayi ado yau cikin shadda koriya sgar,bakin nan ya sha jan jambaki tamkar ya digo,zai iya rantsewa da Allah yau ne karo na farko da zai iya cewa ya ganta tayi wata aba mai suna kwalliya tun bayan qare kwanakinta bakwai na amarci.


Wani kwarkwasa na musamman yau din take masa,wanda dai dai da qwayar zarra bata qara farashin qaunarta cikin zuciyarsa ba face rageta ma da tayi,haushi takaici da baqinciki suka cika shi amma yayi namijin qoqarin dannewa
"Sannu da zuwa yaya mukhtar,yau kam ka jima baka shigo ba,Allah ya sanya lafiya" ta fada tana zama dab da shi tare da kashe masa ido,tausar zuciyarsa yayi don yana son ya ga gudun ruwanta,don idan baka iya kama b'arawo ba shi sai ya kamaka,tsawon zamansu duk iya inda ya kai darensa indai ba a dakin sumayya bane to shi ta shafa bata da damuwa,koda wasa bata taba tambayarsa ba
"Lafiya lau" ya fada yana miqewa tsaye,sai ta dubeshi gabanta na faduwa tana fatan ba asarar aikinta zai mata ba yau ma dai
"Ina zuwa yaya mukhtar gashi na shirya maka abinci?"
"Wanka zan shiga nayi" ya fada bayan yayi kamar bazai amsa mata ba,ta miqe tana fadin bari ta hada masa ruwan wanka sai ya dakatar da ita kan ta jirashi.


Kai tsaye dakin sumayya ya shiga,tana kwance saman doguwar kujera hannunta riqe da wayarta tana kallon wani film 'DAN KUKA,dariyarta take mai sanyi a hankali cikin nutsuwa,ya jima tsaye kanta yana dubanta cike da qauna da burgewa har sai da ya sanya hannunsa ya zare wayar sannan ta miqe a firgice tana ambaton
"Bismillahi,hasbunallahu wa ni'imal wakil" sai suka hada idanu,ta shagwabe fuska cikin muryar shagwaba tace
"Kai yaya mukhtar wallahi ka tsoratani" girarsa qwaya daya ya dage mata
"Eh amma naji dadi da kika ambaci sunan Allah yayin da kika tsorata din,haka akeso" murmushi ta danyi,duban screen din wayar yayi ya tsayar da film din,cikin shagwaba shima yace
"Wato yau ko ki nemeni ko my sumy?,hala ma kin daina damuwa da ni,kina nan kina kallonki kina ta dariya abinki bayan bakiji shigowar sahibinki ba ko?"idanu ta zaro tare da dafe baki sannan daga bisani ta hade hannayanta guri guda alamar roqo
" ka yimin afuwa don Allah,wallahi kewarka ce ta dameni shi yasa ma kaga ina rage lokaci da kallon,ai kasan yaya kallo ba damuna yayi ba ko?"ta qarasa maganar da sigar yarinta,idanu yasa yana kallonta sosai,babu shakka yana daya daga abinda ke sake rura qaunarta cikin zuciyarsa wannan shagwaba da quruciya tata,murmushi ya sakar mata
"Na miki sumayya ta,ai baki laifi a gurina" ya fada yana miqa mata wayar tate da cewa
"Zan shiga wanka"
"A fito lafiya ranka ya dade"
"Allah yasa my sumayyata" ya fada sannan ya juya ya fice yana murmushi.


Kai tsaye sif dinsa ya wuce ya fidda jallabiya ya saka tana ta faman zuba masa surutu,ko daya bai kula ta ba sai sabgarsa ma da yake,har ya kammala ya zauna.


Cikin hanzari ta jawo abincin gabansa tana fadin bari ta zuba masa,idanu ya zuba mata harta kammala ta dago ta dubeshi suka hada idanu,signa ta masa sannan tace
"Gashi ya mukhtar sai ci ko"
"Qwarai kuwa" ya fada yana janyo abincin gabansa,fatanta daya kawai taga ya sanya koda loma guda bakinsa ne,hakan ya sanya ta bata dukka lokacinta yau ko girkin rana batayi ba cikin gidan ta tsara masa abincin da tasan yafi so.


Kamar ta sume don dadi sanda taga ya kai loma guda bakinsa sai kuma ya dakata ya ajjiye cokalin ba tare da yaci din ba,ya dubeta ya sakar mata wani murmushi
"Yau tare da ke nake sha'awar muci abincin,matso bismillah" tamkar an sanya guduma an doki qirjinta haka taji amma tayi hanzarin mazewa ta girgiza kai
"Haba ai ba girmanka bane,baka ne kai kadai" idanu ya zaro
"Au bakison samun matsayi kenan irin na sumayya bayan naga shi kike ta fafutukar samu maza matso,na saba tare muke cin abinci da ita duk ran girkinta" sai ta wani kamme ido a dole sai ta ja ra'ayinsa
"Haba muntari wannan ai ba tarbiyya bace,miji na diba kema na diba,kaci kawai ni a qoshe ma nake" kafada ya daga alamun rashin damwa daman ya san da kwanan hakan
"To shikenan,ba damuww,bari na kira sumayyan ta tayani ci" kamar ta tashi ta riqo shi haja taji amma don kada ta bada kanta sai ta dake.


Daga bakin qofar dakinsa ya coge ya kirata don kada ma ta samu damar sauya masa abincin,cikin mintuna qalilan sumayyan ta shigo dakin,kallonta yayi cikin salo na burgewa
"Yayarki ta qi tayani cin abinci shi yasa na gayyatoki ki tayani" sai ta danyi jim duk da murmushin da ta sanyawa fuskarta,ta sani cewa suna hada kwanon cin abinci ne kadai idan ranar girkinta ce.



Matsowa yayi da kwanon da sauri gabanta don kada ma ta musanta masa
"Oya,matso mana" da sauri fa'iza tayi tsallen albarka ta dira gabansu,ta sanya hannu ta rufe abincin,cikin daurw fuska tace
"Nifa gaskiya bana son haka,wannan ai bai kamata ba,ni ina shiga sha'aninku ranar kwananta ne,to nima ban lamunta ba girki kai daya na yiwa shi kuma kai zakaci" kallonta yake a nutse tsaf riqe da habarsa kamar yadda sumayyan ke kallonta,murmushi ya aje cikin nutsuwa
"Ikon Allah,to aikam nima ban yarda ba cikin biyu dole ki zabi daya,ko ki tayani ci ko my sumy ta tayani" ya fada yana sareta da idanunsa.


Take gumi ya yanko mata,ta fuskanci idan batayi da gaske ba wankin hula zai iya kaita dare,kafin ta kai ga cewa komai nepa suka kawo wuta,haske ya wadaci dakin,ba bata lokaci fuskar fa'iza ta bayyana,wadda tuni gumi ya yiwa jikinta sharkaf,ganin yadda suke kallon gumin ya sanya ta fara nade tabarmar kunya da hauka,wadda ta sake tonawa kanta asiri tsaf a gun mukhtar din ba tare da ta sani ba
"Lallai muntari,to me kake nufi?,kana nufin baka yarda da ni ba kenan?,ko kama nufin wani abu na zuba maka a ciki?"
"Ni bance kin zuba wani abu ba,amma tunda kika fada din akwai qamshin gaskiya cikin lamarin" miqewa tsaye tayi zata nade tabarmar kunya da hauka
"Lallai ma muntari,sharrin da zakamin kenan,sharrin d'a namijin da ake fada kenan yau yazo kaina,eh lallai ba shakka" tsawa ya daka mata ganin zata masa hauka ya miqe tsaye.


Kallon fuskarsa tayi ta tabbatar babu rahama a cikinta,take tsoro ya dirar mata abu ya hadu kuma da rashin gaskiya,sai taja da baya ganin yadda yayi dab da ita har tana jin hucin numfashinsa,tana niyyar guduwa ya damqi hannunta har da taji azaba har tsakiyar kanta
"Fa'iza!" Ya kira sunanta a matuqar kausashe,hantar cikinta ta kada tamkar zata saki fitsari a wandonta
"Basai na bata lokacina nayi doguwar magana da ke ba,wallahi wallahi duk ranar da kika sake yunqurin zuba min wani abu mai kama da sihiri ko surkulle sai kin raina kanki,ki kuma tabbatar daga ranar sunanki SAKAKKIYA!"


ba qaramin dukan qirjinta kalmar tayi ba,sam bata koda sha'awar jin wata kalma makamanciyar haka daga bakin muntarin,don ko kusa bata marmarin komawa gidansu wanda yake mata daidai da gidan kurkuku,gidan da talauci yunea babu masifa da rashin tarbiyya ya yiwa katutu.


Sakar mata hannu yayi cikin rawar jiki ta juya zata fice don baya da abun cewa,yanayinsa kadai ya tsoratata,balle ko shakka bata yi tasan cewa ya ganta ne muntarin,tsawa ya kuma daka mata ya bata umarnin ta dawo ta kwashe abincinta tasan yadda zatayi da shi baya da buqatar sa,haka ta kwashe kwanukan jiki na rawa ta fice.

*kuyi haquri da wannan*






*mrs muhammad ce*


📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖

*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

1⃣9⃣

_________________________
*Bismillahir rahmamir rahim*

*ala bi zikrillahi tad'ma innul quluub*
______________________

Mamaki fal zuciyar sumayya,kanta ya daure tamau,ta kasa furta ma komai sai kallon mukhtar da takeyi,ta tabbata ba qarya ya yiwa fa'iza ba domin ba halinsa bane,amma halayyar fa'iza har ta kai haka?.

"Ina naki abincin?" Mukhtar ya tambayeta,ta katse tunaninta ta dago ta dubeshi
"Ya d'aki"
"Ki dauko,ban amince kema. a yau kici ba,ki zuba a leda ki saka a shara a zubar,shiga kitchen ki samar mana abinda zamu ci koda indomie ce sai ki hada mana da qwai" ya fada yana kashingida gami da lumshe idanunsa,tsam ta miqe ta fice don aiwatar da abinda ya umarceta.

************************

Cikin kwanakin ta dage sosai da addu'ar neman tsari,ta san tabbas shartin mutum girma gareshi,zuwa yanzu ta kuma sallama kaidin fa'iza,ta fahimci irinsu matan da suka dauki kishi ko a mutu ko ayi rai,irinsu wadanda zash iya aikata komai saboda kishi,sosai take takatsantsan kan duk wani motsi da kai kawo nata a gidan,ba ruwanta da sabgar fa'izan bare wani abu ya shiga tsakaninsu,koda fa'izan zata shekara tana takalar tashin hankali bata bi ta kanta,don ta riga ta tabbatar cewa akwai banbancin gida da kowaccensu ta fito,bai kyautu ta biye mata su zamana kamar wadanda suka fito daga gurbi guda ba.

********************

Tun da asubahin ranar suka dinga jiyo kakarin amai a tsakar gidan nasu,sumayya ta dubi mukhtar dake gefanta wanda basu jima da kammala sallar asubahin ba kasancewar sun makara basu tashi da wuri ba
"Ya mukhtar,kamar kakarin amai nake ji fa a tsakar gida" shi din ma taji amma sam bai da muradin fita,tamkar bazai tanka ba sai ya daure yace
"Eh nima naji" yaci gaba da jan carbinsa,ganin yayi shiru ya sanya ta sake cewa
"Ya mukhtar ka duba mana,inajin kamar fa'iza ce fa" shiru ya sake mata ganin hakan ya sanya itama ta tsuke bakinta tayi shiru tana ci gaba da sauraran kakarin wanda yake fita tamkar da kayan cikinta,ya kammala azkar dinsa ya haye gado abinsa ya kashingida.

Zuciyar musulunci ya sanyata ta kasa daurewa,sai ta miqe ta fidda hijabin jikinga ta nufi qofa,sanya baki yayi ya kirata tare da tambayarta ina zata
"Zanje na duba ne,bai kyautu da mutane cikin gidan ba kuma aqi fita a dubata ba,bamu san meke damunta ba" kai ya girgiza
"Dawo tausa nake so kimin"
"Kayi haquri naje na dubata din minti biyu kawai zan dawo sai na maka tausar"
"Idan ban isa da ke ba shikenan kina iya hakan" ya fada yana maida kansa ya kwantar kan pillow,sai jikinta yayi sanyi bata son saba masa ko kadan,saboda haka ta juyo a sanyaye tahaye gadon.

A tausashe take masa tausar tana leqen fuskarsa ganin yaqi kulata,har ta soma tara qwalla bata iya jure fushinsa,sai taji kawai ya birkitota ya danneta da rabin jikinsa yana dariya qasa qasa
"Raguwa kawai sarkin kuka" ya fada yana lakuce mata hanci,dariya ta saki ya shiga mata cakulkuli daga haka suja shige duniyar ma'aurata wanda hakan shi ya hanasu fitowa da wuri.

Qarfe goma ya gama shirinsa zaya fita,a tsakar gida daga

Please Login or Register in order to submit comment