Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,muryarta na rawa alamun fara kuka ko da yaushe tace
"Kayi haquri,bada niyya bane?"
"Kika yi me?," ya fada yana sake takowa saura kadan ya hade jikkunansu,tsoro ya hajata daga qafafunta bare taja baya,gani take yau Allah ne yasan me zaya yi mata
"Komai ma" ta fada tana dauke qwallar data ziraro mata ta ido daya ta daya idon tana shirin fitowa itama,hakan yaji tausayinta ya kamashi,a yau din nan fa ita ta fiddashi daga matsalar daya kusa sati biyu ciki,bata cancanci tayi bacin rai a yau din ta sanadinsa ba,bata da kowa a qasar saishi,kwananta kusan ashirin da wani abu tana wuni cikin kewa ita daya qulle a dakin,zaya so a yiwa amiransa haka?,bai manta ba hamza yace ya dauketa tamkar qanwarshi sai a yanzun yaji zai iya hakan.


Ga mamakinta sau taji ya kama fuskarta da hannayenshi biyu ma'ana fuskarta da tsakiyar tafin hannunsa
"Shshshshsh....ya isa,ba laifi kika yi ba,amma indai kika bar daya hawayen ya zuba to zan miki hukunci,maza hadiyeshi" maimakon ya koma din sai ya qarasa silalowa,idonsa ya runtse yana jin ba dadi,baya son kuka ko kadan,sai ya sanya hannunshi a aljihun trouser dinsa ya ciro handkherchief ya goge mata hawayen ta yadda kwalliyarta ba zata baci ba,sannan ya dora shi saman lebanta ya soma rage mata janbakin
"Yayi yawa,kadan ya isa" ya fada yana kallon lips din nata tare da maida handkherchief din aljihunsa,itakam bata ga wani yawa ba da yayi
"Is ok,kada ki sake kuka,ki riqe wayan saboda gida before ki samu wani layin,muje" ya fadi yana dubanta,gaba tayi cikin mamakinshi,wane sabon halayya ne haka?,shi kuma ya take mata baya har suka fice daga dakin ya rufe.


A reception ya tsaya ya karbi muqullin motar sannan suka fice tana gaba yana bayanta.


  A hankali suke takawa suna wucewa zuwa gurin ajiyar motoci,abun mamaki duk inda suka gifta tun daga cikin hotel din sai sun dauki hankali,tsammata ake wasu shaqiqan masoya ne,yanayin shigar kowannensu ya dace da shi,a haka har suka qarasa wajen motar,da kanshi yau zaiyi driving din saboda haka kai tsaye ya wuce mazaunin driver.

         Wani nutststsen tuqi yake yi wanda ke qarawa zuciya da ruhi nutsuwa,bazaiyi qarya ba kam yau wani annushuwa yake ji,hakan kuma yaba tunanin bai rasa nasaba da warwarewar matsalarsa cikin sauqi,shiru kake jin motar,idanunta na bisa titi a fakaice tana qarewa garin kallo,haqiqa yayi matuqar tafiya da ita fiye da uk da ta je,gari ne mai cike da qyale qyale da kayan qawa masu matuqar jan hankali,dan satar kallonta yayin kafin ya maida kanshi bisa titi
"Thanks" taji ya ambata,a hankali ta maida idanunta kanshi wanda titi yake kalla kafin ya dauke kanta,murya qasa tace
"Dame fa?" Shiru ya biyo baya kamar bazai amsa ba,har tayi zaton ma ya bar zancan sai taji ya kuma cewa
"Shukhran alat taujih" sake daga kanta tayi tana dubanshi murmushi na son subuce mata,ta rasa ya akayi yaji larabci haka,wati dazun tayi shuka ne idon makwarwa,ta gode Allah da ba wata magana ta fadi ba,sai ta kauda kanta
"Babu komai,abinda ya kamata ne nayi shi" sosai maganar ta burgeshi,kusan shi daya yake warware matsalolinshi idan sun taso mashi ya riga ya saba,shi yasa wannan karon yake jin tayi mishi wani gagarumin aiki data cancanci a gode mata,ba shakka samun abokin shawara da yin shawara a kuma baka shawarar yana da matuqar muhimmanci kamar yadda ummee ta saba gaya masa
"Ko zaiyiwu na riqeki personal adviser?"
"Aikin kowacce macen gida ce matuqar an lamunce mata hakan" itama ta fada ba tare data dubeshi ba,tana jin qarin mamakinsa cikin ranta,kamar yasha wani abu ne?,wannan ne karon farko tsawon sanayyarta da shi da suka taba zance mai tsahi makamancin hakan,ta nashi bangaren mamakin irin tata baiwa da fasahar yake,yana ganin matan arewa basu da wannan fikirar amma a yanzu yaga guda daya?,haka suke ko kuwa wannan ce kawai?(hmmm,mun wuce haka ma malam almustapha,muje dai zuwa).

        Bai tsaya ko ina ba sai zabeel park,tunda suka shiga wajen yayi matuqar qayatar da ita,karon farko a rayuwarra data taba shiga wani park,guri ne da family kan iya zuwa,miji da mata da yaransu,koma miji da mata kawai,a hankali suke takawa jere da juna,saidai idanuwanta na wulqawa ko ina tana kalle kalle abinta cikin hikima ba tare daka fuskanci ta matowa gurin ba,wani sashe daban suka nufa wanda ke dauke da wasu rubuce rubuce na SEASON four dubai garden glow,hakan ke nuna lokaci lokaci wajen ke a bude,gurin biyan kudin shiga ya biya aka nasu ticket sannan suka shige.

        Bata taba ganin abubuwan data gani cikin garden din ba,wani irin garden ne da aka baje fasaha wajen yinsa,kowa na harkarshi cikin wajen,kama da yara qananu da matsakaita,maza da mata,masoya gasunan birjik kowa na baje kolin tashi soyayyar,wani guri na musamman suka yi mazauni sanda wayarshi ta fara ruri ya cirota yana qoqarin amsawa yayin da ita kuma taci gaba da bawa idanunta abinci,a hankali idanuwanta suka sauka kan wani family,miji da mata ke sai yaransu uku,mace babba sai mai bi mata namiji sai qaramin shima namiji,a yadda suke raha kana kallonsu kasan banu abinda ya shafi rayuwarsu,sisai yaron suka burgeta kasancewarta mutum mai son yara qwarai,suna ta wasanninsu suna kaiwa suna kawowa wajen iyayensu,ta sake dauke idanunta ta maida kan wasu matasa biyu mace da namiji,namijin ke bawa macen ice cream yana ta faman lallabata ya kasa ya tsare,tayasu dariya tayi ta hanyar sakin murmushi sanda ya dangwala kata shi kan hancinta sanyinsa ya ratsata ta fidda idanuwa,abinda bata sani ba duk abinda take almustaphan na ankare da ita,har ya kammala wayar bata sani ba,maidata aljihu yayi ya hade hannayensa waje guda yana nazarin yadda annuri ke fita daga fuskarta,take ya sake karantar yanayinta na tsantsar son yara,ta sake maida idanunta wajen wasu yara dake daura da su wajen su biyar da wata 'yar matashiya tsakiyarsu da alama ita ta kawosu,wasa sukeyi abinsu na buya,yarinyar dake cikinsu wadda bata wuce shekara uku ba ta taho a guje ba tare data lura da sumayyan ba ta boye bayan kujerar da take zaune tana fadi cikin harshen larabci
"Ki boyeni",murmushi ya qwacewa sumayyan sai ta sake bude doguwar rigarta ta boye yarinyar ga sake lafewa tana sakin dariya irinta quruciya,nemanta suka shiga yi wanda dariyar da take qyalqyalawa ya sanya suka gano inda taje,sai ta cukuikuye sumayya tana dariya tare da kifa kanta acinyarta,daukanta tayi itama tana murmushi sannan ta miqe sanda yaran suka qaraso ta ajjiye musu ita,sake diba sukayi da gudu ta koma ta zauna tana binsu da kallo tana murmushi.

  
          A nutse suka ci gaba da takawa suna qarewa kyawun wajen da tsarinsa kallo,har yanzu murmushu bai bar fuskarta ba,zuciyarta fes,Allah ya sani tana son yara
"Allah ka bani yara da yawa"ta furta can qasa sosai lebanta na motsawa
"Da wa?" Zuciyarta ta tambayeta,,matuqar yaran takeso saidai tare da mustapha fa kenan,a hankali ta daga kai ta dubi mustapha,sai suka hada idanuwa,tare kowa ya dauke kanshi,kaifin ji gareshi kamar me,yaji sanda tayi addu'ar,shirun minti wajen biyar tsakani taji ya jeho mata tambayar da bata san amsarta ba
"Haihuwa kike so kenan?" Sosai tambayar ta doketa,ya akayi tayi maganar yadda zaya ji,sai ya tsaya cak da tafiyar ya kafeta da idanu ta cikin gilashinsa,bata ce komai ba sai dauke kanta da tayi
"Uhummm,ki amsa mana,kina so ki samu ciki ne ki haihu?" Gani take kamar ma wani nishadi yake yana son qureta,hakan ya sanya ta cire kunya ba tare data dubeshi ba tace
"Kuskure ne?,kai din baka so?,shekarunka nawa a duniya?,ina tsammanin zuwa yanzu zaka yi kwadayin samun diyan kanka" shi din ma ba qaramin dukanshi furucin yayi ba,amma ya sai ya tsinci kansa qaramin murmushi na subuce masa,ya lura qarfin hali tayi ta furta maganar,yana son mutum mai confidence qwarai,zaya so kacici kacicin nasu ya dore saboda haka yace
"Why zan qi hakan,ina so,but bani da matar da zata haifa min.....ko ke zaki iya?" Waiwayowa tayi da hanzari ta dubeshi,sai ta sake kasa ci gaba da jurewa kallon nasa,ta kuma juya baya tana harde da hannayenta a qirji,yayin da,nashi hannayen ke zube a aljihu yana dubanta,yana son qure confidence din da take ji tana da shi,kai ta girgiza bayan ta samo amsar bashi
"A'ah ni a su wa,ban shirya ba,after all ma bazan iya ba" ta fada tana watsa hannuwanta,dariyarshi ya danne don ya hango karaya muraran a kalamanta
"Me zaya hana ne wai?,ai sai an gwada aka san na qwarau,if u can try u can do it" ya fada yana kama qugunta da hannayenshi tare da mannata a jikinsa,har ga Allah yayi da wasa don kuma ya qureta,saidai yaji a jikinsa fiye da yadda ita taji,don ita tsoro ne ya lullubeta,dakiya da taurin zuciya ya hanashi sakinta,sai da yace
"Tunda kika fada dole ki gwada,sai an banbance aya da tsakuwa tukunna" sannan ya saketa,da hanzari tayi baya tana jingina da jikin wasu qarafuna dake tsaye wanda aka yiwa ado saboda yadda qafafunta sukayi sanyi,tsahon mintina qirjinta na bugawa ta rasa ta cewa,batasan sanda ya sayi ice cream din ba ta dai ga yana miqo mata,a sanyaye ta saka hannu ta amsa.

        Basu bar wajen ba sai wajen takwas na dare,duj wata kewa da takura na tsahon satittikan sun baje sunyi nasu guri a park din,don ma baki daya ta kasa ci gaba da sakewa tun maganar da sukayi da shi,kunya nauyi da tsoro sun cikata duk da bai sake dubanta ba bare yace mata wani abu,har suka koma gida yayi wanka yayi shirin bacci tana takure guri daya,tuni yayi luf saman gado,ta qididdige lokutan data saba bashi ja zatonta cewa yayi bacci sannan ta miqe ta shiga toilet tayi wanka ta sauya kayan baccinta,kusan tuni ya haddace sanda take sauya kayan,hakan ya sanya ma yau bacci bai daukeshi ba,tamkar mai jira yaga fitowarta din kuwa sai gata ta fito,a gajiye take don haka a sannu take takawa cikin kayan baccin riga da wando ne,rigar iya cinya wando kuma ya wuce gwiwarta iya qauri,idanunsa ya lumshe yana ajiyar numfashi kadan kadan,kansa ya wani sara mishi,sunan Allah ya ambata tare da addu'ar kada ya zamana ciwon kansa ke shirin tashi,yau yayi surutu ta waya da yawa,ga inda suka je din akwai hayaniya ba laifi,bugu da qari jiya bai samu isashshen bacci ba saboda wannan matsalar,a haka ciwon kan ya dinga sakadarshi har kuaa da asuba kafin ya samu bacci.

  ******      ******    *******

         Qarfe tara na safiyar washegari ta fito daga toilet bayan ta wanke bakinta,yana zaune gefan gado yana amsa wayar hamza,kallo daya ta yi masa taga sauyi a idanunshi,sun sauya sun fada kadan ba kamar yadda suka kwanta daren jiya ba,ta daya bangaren hamza ke ce masa
"Muna da baqi fa maan,ka shirya kasan yadda za'ayi"yadan motsa fuskarshi
"Su wafa kenan?"
"Usman,huzaifa,musaddiq,lamin,on their why to dubai tomorrow in sha Allah(abokan asali su shida tun suna universty a america idan kun tuna)" miqewa yayi a hankali ya fice a dakin sannan yace
"Kaifa dan iska ne wallahi hamza,ka girma amma bakasan ka girma ba,sai kasan yadda zakayi don nasan gulma ce zata kawo su ka sanar musu komai ko?" Dariya hamza ya dinga harda qwalla
"Wallahi baka isa ba,ai baqinka ne,congratulating dinka zasu zo suyi sai kace min kuma nasan ya zanyi da su,can ta matse maka" ya fada yana katse kiran,lalubar hamzan ya soma yi,yasan kadan daga iskancinsa yasanyasu suzo mishi daki haka kawai,bugu daya ya daga tunda yana kusa da ita yasan sarai zai kirashin
"Ya akayi?" Inji hamza
"Ya kake ganin za'ayi?"
"Kafi kowa sanin halin guys din nan zuwa daram wllahi"
"Jokes apart don Allah,ka saukesu gidanka,idan yaso sai muzo nan"
"Ka nemi maslaha,tunda kai kafi ganewa zaman hotel,Allah ya sawwaqa"
"Ka rufen baki malam,ka cuci mutane kawai..."ya katse wayar yaja jan tsaki tare da furzar da iska daga bakinshi,hamza bai da mutunci amma sai ya rama zaiji dadi,ya tabbata shi ya gaya musu don bai manta abinda suka dinga masa sanda zai auri abida 'yar africa,juyawa yayi ya koma dakin yana tunanin da me zasu karya,kadan kadan yake jin shima ya soma qosawa da zaman wajen,shekarunshi nawa yana siyan abinci gun saidawa,da a gidane ya tabbata ko coffee zaya samu yasha tunda yaji ta iya dafa shi.

*******    ******    ********

        Washegari bayan fitarsa office ta wayarshi dake hannunta ya tura mata texs ta shirya ga driva nan zai kaita gidan hamza,cikin murna ta hau shiryawa,ko banza yauma zata miqe qafarta,minti talatin kacal ta gama shiryawa cikin african abaya wanda tayi masifar karbarta,ba wani makeup ta yiwa fuskarta ba amma saida duk abinda tayi amfani da shi ya dace da shigarta,hakan shi ya qawata kwalliyarta,dakin ta rufe cikin zumudi sannan suka wuce.

       Gidajene wadanda ke dauke da qawatattun madaidaitan apartment daidai rayuwarku ku babu matsi balle takura,wanda ke nuna na haya ne,falo ne madaidaicin mai kyawun tsari wanda ke dauke dining mai kujeru shida baya ga kujeru set daya,sai dakunan bacci guda biyu kowanne da toilet,sai kitchen daga can daban wanda ke da vantilation,cikin murna da farinciki abida ta tarbeta,wanda ta sauketa da drinks da kayan snacks,abun yayi mata sosai,duk sai taji rayuwar hotel din baki daya bata yi mata ba,bayan sun dan taba hira abida tace
"Ina fata kinzo da shirinki,ogogi na da baqi,kitchen zamu nufa yanzun" baki ta tabe cikin mamaki
"Nikam yace min kawai ja shirya a kawoni wajenku" murmushi abidan tayi
"Almustapha,har yau bai sauya ba miskilancinsa na nan" miqewa sumayya tayi tana dariya
"Muje kawai ki tayani hira,don ke da wannan cikin ai idan ba'a hutashsheki ba ba'a saki wahala ba" miqewa tayi tana gaba sumayya na bin bayanta tace
"Ke!,waya gaya miki?,irin wadan nan mazan namu da suke ganin mata kala kala aisai da miqe tsaye,babu abinda na fasa in gaya miki,daka saki baki saidai ayi babu ke" dariya ta kama sumayya,yayin da maganar ta dan maqale mata a rai.

       Kusan abida 'yar kallo ta zama duk qwarewarta a girki tana daukan style wajen sumayya,kafin wani lokaci komai ya kammala abinka da na'ura,sumayya na zaune gefan gadon abida sanda abidan ta shiga wanka,wayar almustapha dake jakarta ta dauki kidan wani sassanyan ringing,ta ajjiye littafin da take dubawar ta ciro wayar MY SU'AD shine sunan da ya bayyana saman screen din hadi da hotonta,ta jima tana kallon wayar har kiran ya katse,wani kiran ne ya sake shigowa ta sake daga kai ta zubawa wayar ido,batasan me take ji ba a qirjinga saidai tana jin wani abu na neman cushe mata wuya,a haka abida ta fito ta taras da ita
"Ah ah,waya nata ringing fa"
"Bani ake kira ba" ta fada tana dauke kanta daga saitin wayar
"To wayar wane?"
"Wayarshi ce"
"Ki daga to ki gayawa mai kiran bashi kusa ko wani abu mai muhimmanci ne ya....." Sai maganar tata ta katse sanda taje kusa da wayar don daukar bargon da zata tsane jikinta da shi ganin sunan su'ad
"Bar shegiya wallahi kada ki daga" cewar abida cikin tsantsar kishi,dubanta sumayya tayi ganin yadda abidan ya sauya maganarta lokaci daya,bata dubi sumayyan ba ta nufi bakin mudubi abinda ta soma shafa mai,har kiran ya katse babu wanda yace uffan sai daga bisani abidan tace
"Sumayya,Allah ne ya hada jinina dake,wlh kinga baifi sau biyu muka taba haduwa da su'ad ba amma baki daya bansan me yasa jininmu sam baizo daya ba,bana son mutum mai dagawa da jin kai,don Allah kada ki sake komi bari taga wallenki bare ta rainaki,ki zame mata dodo,ki daukaka darajar almustapha a idanuwanga tasan cewa ba kowane ke iya jefar da daimond ya dawo ya tsinceshi ba awajen,ba taba ganin sakaryar mace ko a labari ba irin su'ad wallahi" ajiyar zuciya sumayyan ta saki ta furta
"Na gode,Allah ya bar qauna" daga haka suka rufe chapter din suka shiga wata hirar daban,yayin da wayar tacu gaba da burari aqalla sai data hada miscal goma sha biyar sannan ta haqura ta bi bayansu ta tex wanda bata sake taba wayar ba ma balle taga me ta rubuta din.

        Bayan idar da sallar la'asar baki dayansu suka iso cikin lafiyayyar motar almustapha wadda ta cinyesu baki dayansu,hira da musu ta cika motar baki daya,baka jin komai sai muryoyinsu,yayin da almustapha ke daga zaune yana dariya,ya jima baiyi dariya irin wannan ba,ba shakka aboki wani abu mai muhimmanci ne a rayuwar mutum,musamman idan kayi dace da samun aboki na gari,hamza shine kan gaba suna bayansa,da irin wannan hirar suka shigo falon wanda ya wadata da qamshin turaren wuta wanda sumayya ce ta mata kyautarsa irin wanda tayi da hannunta,sosai yanayin falin ya yiwa almustapha,haka qamshin dake tashi,take ya soma wassafa komaea nashi gidan yana tsara yadda hakan zaya kasance.

       Dukan cinyarsa musaddiq yayi bayan hamza ya wuce dakin abida
"Maann,Allah na qagu naga wacce 'yar afrika ko ince arewar ce tayi nasarar sace ka haka?" Dariya suka sanya baki daya,usman yace
"Ai wallahi tunda maan ya sallama kowa ma ya sallama,nikam dama tuni na miqawa sahar kaina,wallahi na sallama"
"Bare ni da naga zuhra" cewar huzaifa yana latsa waya yana dariya,harara dukka ya watsa musu,yasan baki dayansu hamza ya kwaza musu yadda akai auren
"Ina fata har yau baku manta waye maan ba ko?,kubar ganin kun fara neman aure har yau baku girmi na daddaki bakinku ba wallahi qattin banza" ihu suka sake sanyawa
"Allah ya shiryeka,mata biyu amma har yau basu sanyaka ka girma ba" haka suka dinga fadi,ganin fitowar hamza ya sanya su nutsuwa yana sanar musu gasu nan fitowa,yadda suka nutsu suna jiran ganin fitowar tasu hakanan mustapha ya dinga jin kamar yace kada su fito suyi zamansu.

       Wani abu ya dinga motsa masa sanda suka fito,abida na kan gaba dauke da try sumayya na bayanta dauke da wani try din me snacks a ciki,sai yake ganin duk cikin shigarta ta yau kamar ta musamman tayi,ganin abida ta nufi gaban hamza ta dire itama ya sanyata isa gabanshi ta dire
"Amma wannan tsabagen son kaine,mazanku kurum kuka sani?" Cewar musaddiq idanunshi na kan sumayya wadda ta saki murmushi idonta a qasa,baki daya wanu nauyi take ji bata saba shiga cikin maza haka ba,idanun almustaphan shima na kanta,can qasan murmushin nata yake hango damuwa kadan kadan,almustaphan ne ya sanya qafarshi ya tura plate din gabansa
"Gashinan malam sai ka saurara haka ko?" Ya fada cikin dakewa,dariya ya tuntsire da ita,kusan halinsu daya da hamza,yaci alwashin yau sai ya wana almustapha ya manna masa hauka,dama an dade ba'a hadu ba
"Amma dai da ka barta ta kawo da kanta a matsayinmu na baqinsu" ya fada sanda suka gama gaisawa suka koma kitchen don shirya musu abincin saman tebur,wani banzan kallo ya watsa masa
"Tunda tare muka hada muka biya sadakin ko?" Ya fada cikin subul da baka,dariya suka sake kwashewa da ita,lamin ke nuna shi da yatsa,hamza na danne dariyarshi ya sauka qasa ya soma zuba musu kunun aya da sumayya ta hada mai sanyi da yasha madara da flavour cikin cups yana miqawa kowa,ya zuba na qarshe ya miqawa almustapha,sai yaqi masa ya zuba ma hamzan ido yana aika masa da gargadi
"Karbi mana malam ka sanya min ido haka?" Wannan maganan ita ta ja hankalin sauran,musaddiw yace
"Wai man har yau kana kan bakanka baka shan irin wadan nan abubuwan,ina cewa komai ya sauya tunda now u r married baka da case"
"Keepquite malam,ni na gaya ma haka?" Ya fada yana amsar cup din daga hannun hamzan don baison suyi masa dogon sharhin nan nasu,ya kai bakinsa ya kurba,sosai abun yayi masa dadi,ya lumshe ido yana jerowa hamza Allah ya isa cikin zuciyarsa,ya tabbatar yau ya jefashi a masifa ne kawai,usman ne da yake shi ya dan biyo almustapha kadan
"Kai maaaan,wallahi ko cikin larabawa ka samu yarinyar nan ka more,idan zaka saki jiki ka kwashi gara tun lokaci bai qure maka ba ato"
"Gaya masa dai mutumina,komai fa yaji wallahi,gaba da baya duka babu makusa" wanu abu yaji ya soki zuciyarshi,ranshi ya baci wanda ko a wasa bai taba zaton zai baci ba,dukkaninsu suka lura da hakan saidai basu fasa dariyarsu ba
"Koma ciki!" Almustaphan ya fada cikin dakakken sauti da daga murya sanda take fitowa daga kitchen dan kawo kayan abincin saman dining,sosai maganar ta ratsata,sai ta koma da abincin ta samu wajen cikin kitchen din tayi zamanta,sai a sannan suka lura da sauyawar yanayinsa,hakan ya sanya suka rage tsokanar suna yiwa juna magana da ido tare da danne dariyarsu, don duk basu dauki abun zaiyi tasiri haka ba.

       Hamza shi ya qarasa shirya komai,yayin da suka shiga wata hirar,shi dinma dannewa ya dinga yi yana sin tabbatarwa kansa ba wani abu bane ya faru,har sanda suka zauna kan dining hamza yayi serving kowa sannan suka fara kaiwa baka,take kuma sai aka koma santi,suka soma tambayar inda suka siyo abincin,shikam yasan ba taste din abincin abida bane,duk ita gwanar girki ce,sai ya ciro waya yasanya handsfree ya kirata yana tambayarta inda suka siyo abinci,dariya ta qyalqyale da ita
"Dear ba wani gidan abinci,girkin sumayya ne,taga nayi nauyi ne ta amsar min aikin"
"To masha Allah" ya fada yana katse kiran ya dubesu yana kai wata lomar bakinsa
"To kunji girkin amaryar musty ne" take kowa ya soma yaba girkin,lomar da yayi ta tsaye masa a wuya,sau kawai ya dauki ruwa ya kora ya miqe tana duban hamza fuska a dinke
"Tashi ka kiramin ita mu wuce" dubansa yayi yana qoqarin hadiye abinci
"A'ah man,bamu tattauna komai bafa,dududu ko awa bamuyi ba agidan nan"
"Zaka kira min ita ko sai na shiga dakin da kaina" dariya suke qasa qasa,lamin ne ya dake ya soma masa bayani ba wani abu suke nufi da matarshi ba tsokanarshi kawai suke,hannu ya saka ya daki teburin
"Ce muku nayi wannan ne ya bani haushi,shut up da Allah"yau sunga bala'i sai suka sanya masa ido,miqewa hamza yayi ya isa kafadarshi ya dafa shi ya soma masa magana wanda basa jin me yake ceww,ajiyar numfashi yayi ya juya ya dubesu,sau ya saki qaramin murmushi
"kunci bashi wlh zakusan kunyi da musty,amma kiramin ita mu wuce din kawai na riga da na tashi,after eight zamu hadu a masauki ba case"dariya suka saki baki daya,cikin minti biyi sumayyan ta fito
"amarya ki gaida gida"suka ce mata ta amsa da to tabi bayanshi.

      Tuqinsa yake a hankali saidai har yau abinda ke tokare a zuciyarshi bai baje ba,sau biyu yana satar kallonta,har yanzu mode din damuwa yake iya gani kan fuskarta,ya lura da wayarshu dake ta haske a jakarta amma baice komai ba kamar yadda bata ce masa ba,a zaman kuramen suka isa gida.

       A waje yayi magariba da isha'i,sanda ya dawo da zummar yin wanka sai ya sameta nannade saman doguwar kujera,ko t.vn ma da ya kunna kafin ya fita a kashe take,hakanan yaji ya fasa fita,wayoyinsa biyun da suke gunsa ya kashe ya shiga yayi wanka ya dawo ya sanya pyjamas masu taushi farare qal bayan ya wadata jikinsa da turarensa kamar ko yaushe,tana kwancen bata motsa ba,jikinta duka na arufe sai kanta dake a waje,qwayayen dakin ya kashe ya kunna na bacci duk da a sannan dududu qarfe tara na dare,gadonsa ya haye yaja lallausan bargonsa ya rufa iya qirjinsa bayan ya zauna sosai saman gadon yana karanto addu'o'i,sai yaje yayi bacci da wuri tun kafin abinda ya sha ya soma taso masa.

       Wayar dake saman kanta ta soma haske,hannu ta sanya ta duba,miscal ne da qarin saqonni,tsaki ta ja kamar ta maidata ba tare data gaya masa ba sai taga hakan bai dace ba,mai kiran zatayi tsammanin ya ganu ne bai kula ba,kuma ko banza matarshi ce,motsa bakinta tayi murya can qasa a tausashe kamar maijin bacci tace
"ana kiranka akwai kima sms"
"Tun yaushe?"
"Rana"
"Waye?" Dan jim tayi sannan tace
"Su'ad na gani" shiru yayi yana ci gaba da addu'arsa har sai daya kammala sannan yace
"Me saqon yace?" Kai ta girgiza tana daga kwancen
"Ban duba ba"
"Me yasa?"
"Ba saqona bane,ba kuma hurumina bane" amsar tayi masa,wannan itace cikakkiyar amana
"Ok,karantomin naji" shiru tayi don bata da muradin karantawar har ranta,sai da ya sake maimaitawa,janyo wayar tayi ta bude,a hankali ta isa ma'ajiyar saqonni wanda tunda wayar ke gurinta ko gefan bata je ba,ta dannan saqon daya fara shigowa da fari ta soma karanta masa,idanu ya lumshe muryarta da tayi low tayi sanyi na ratsashi,har ta qare kusan bai fahimci me ta karanta din ba,sai da yaji shiru alamun ta gama karanta saqonnin sannan ya farga,gyara zamanshi yayi tare

Please Login or Register in order to submit comment