Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hannu yana fadin
"Ah,ya mukhtar kai ne?" Baiqi miqa masa nasa hannun ba suka yi musabaha yana fadi tare da tsareshi da wani irin kallo
"Eh,ya kawu da sauren mutanen gidan"
"Duka lafiya alhamdulillahi" ya fada yana sakin hannun mukhtar din sannan ya juya ga sumayya
"Ki nazari a nutse,kada ki ruda kanki,kada ki cuci kanki ki cuceni,gobe in sha Allah zan dawo" ya fada yana juyawa zuwa wajen motarsa,dukkansu ita da mukhtar din suka yi masa rakiyar idanuwa,saidai kowa da abinda ke kai kawo cikin zuciyarsa,ya bude motar ya shiga bayan ya bawa abdallah 'yar madaidaiciyar baqar leda cike da biscuite da choculet ya saukeshi ya tada motar ya wuce.



Busy kuyi haquri da wannan


*mrs muhammad ce*







*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



3⃣8⃣

____________________________
*Bismillahir rahmanir rahim*

*wala taqulanna li shai'in inni faa'ilun zalika gada,illa ay yasha Allah,wazkur rabbaka iza nasit*

_kada kace ni zan aikata wani abu gobe,face sai ubangijinka yaso,ka tuna ubangijinka idan ka manta_

______________________________

        Wani abu ne ya tokare masa wuya yana jin wani irin bacin rai na taso masa,sai yayi qoqarin dannewa ta hanyar daukar abdallah da ya nufo gunsa kai tsaye yana fadin daddy daddy,motsawa sumayya tayi don shigewa cikin gidan cikin hanzari ya sha gabanta
"Me abdur rahman ke zuwa yi gunki?" Idanunta ta dora a kansa kanta tsaye tace
"Alheri"
"Alheri wanne iri?,kada kice min gonata yake son shigowa?"wani irin kallo ta masa
"Yaushe ka fara noma?,dama kana da gona ne?,alheri kuma duka alheri ne babu wani banbanci" ta fada tana rabeshi zata wuceshi ranta a bace,baisan ya riqo gefen hijabinta ba hakan ya sanyata waiwayowa tana dubansa a mamakance
"Me yasa kike cutar da ni haka sumayya me na miki a rayuwa da zafi?" Ya fada zuciyarsa na zafi yayin rauni ya bayyana qarara a fuskarsa
"Cutarwa?,ni nake cutar da kai ma mukhtar!" Ta fada tana nuna qirjinta da yatsa cikin mamaki,sai ta juyo baki daya tana dubansa sosai
"Bance ka cutar da ni ba mukhtar ni da ka saka saki uku ina kwance?,bance ka cutar da ni ba ni da ka yanke min hukunci kan zato da zargi,ka yanken hukunci ba tare da kayi bincike ba?...."
"Wanne bincike sumayya bayan ba labari aka bani ba,na gani da ido na,sannan bincike na likita ya sake tabbatar min da kinsha din wanne bincike kike da buqata nayi bayan wannan" a kaikaice takw dubansa sannan tace
"Ok ko?,to shikenan,yayi kyau hakan ai,amma shawara zan baka ka fita daga dukkan harkoki na,ko da maza dari zaka ganni da su wannan ba damuwarka bane,tunda dai a yanzu ba qarqashin ikonka nake ba,gashin kaina nake ci sai ka shafamin lafiya" tana gama maganar ta juya tayi shigewarta cikin gida ta barshi da abdallah.

     Binta yayi da kallo,taushe sunayya ta koma haka,yaushe bakinta ya bude da magana haka?,saidai batayi laifi ba yana ganin baiken kansa,tabbas ba shakka gaskiya ta fadi yanzun ita din ba huruminsa bace,baisan me ya sanya ya shishshigewa lamarin rayuwarta har haka ba,jiki ba qwari ya koma mota ya dauko siyayyar abdallah ya riqoshi har bakin qofar da zata sadaka da tsakar gidan ya ajjiyeshi ya wuce,cikin mota yana tuqi yana tunanin yadda zai raba kansa da shiga lamuranta,don bisa gaskiyarta take,wani sarawa kansa yayi wanda hakan ya sanyashi yin parking motaraa gefan titi ba shiri,ya dauki a qalla sama da mintuna talatin kafin yaci gaba da tafiya.

   *****    *****    *****

    Duk yadda taso abdur rahman ya fahimci abinda take nufi yaqi fahimta,sai ta tattarashi ta janye masa jiki,sau tari takan qi dawowa daga makaranta akan kari,tana kuma dawowar lokacin sallar magariba ne,daga nan kuma suna zama karatu da malam wanda ya sanya musu wasu litattafan addini wanda suke hadda ce wasu abubuwa a ciki,sam ta daina bada wani gaf ko wata dama da zasu kadaice har suyi magana,idan ana tare cikin jama'a zasu yi magana da shi kamar kowa.

      Ta bangare daya kuwa luqman shima ya matsa lamba,tilas ta bashi dama yazo gidan sau daya,a ranar malam ya dawo ya ganshi suka gaisa,saidai malam din baice mata komai ba kamar yadda ta zata,hakanne ya sanya ta saki jiki har ta sake bashi wasu damammakin yazo wai koda hakan zai sanya abdur rahman ya janye daga qudirinsa,saidai duk da hakan babu abinda ya girgiza shi,har mamaki abun ke bata,cikin lokaci qarami ya sanyata ta saki jikinta da shi,mutum ne mai barkwanci da yawan bada labarai,ko bata son magana sai ya sanyata dariya.

       Abinda bata sani ba malam din na sane da komai,bata san da hakan ba sai ranar da aka kai kudin auren abubakar da saka rana wanda baki daya aka tsaida watanni biyu,washegarin ranar malam din yayi kiranta falonsa,bayan ya kammala duka abubuwan da yake ya dubeta
"Am sumayya,nasan cewa kinsan tsarina da al'ada ta gidan nan,sannan alhamdulillah kin san mutuncin mace dakin mijinta,baki da inda yafi nan daraja,dukkan wani abu da ya faru a baya mu ajjiyeshi gefe haka Allah ya tsarama rayuwarki,cikin KUNDIN QADDARARKI yake,babu wanda ya isa ya goge miki ko ya kautar miki da shi"
"Haka ne malam" ta fada kanta na duqe zuciyarta ba bugawa kamar zata bullo,addu'a take kada Allah yasa malam ya bullo mata da zancan da bata da buqatar jinsa a yanzu
"Sumayya,yaron nan abdur rahman yazo guna ya gabatar min da kansa a matsayin manenin aurenki,to amma kasancewarki bazawara a yanzu addini ya baki damar zabawa kanki mijin aure ya sanya nace sai na tambayeki naji mene ne ra'ayinki,kada ki zalunci kanki a yanzu kina da dama,sannan zaman aure zama ne bana yau ko gobe kawai ba,zama ne na har abada". Wani tashin hankali ne ya rikito mata,abubuwan da suka dinga faruwa da ita zamanin tana auren mukhtar tsaf suka dinga dawo mata,a hankali ta bude bakinta muryarta na rawa
"Kayi haquri malam,abdur rahman dan uwa ne ga mukhtar dan wan babansa ne nasan kasan haka malam" murmushi ya saki
"Sumayya,sumayya kenan,wannan duka ba abun damuwa bane tunda dai aure ya halasta a tsakaninku ba haramun bane" tashin hankali ta fada cikin zuciyarta,'yan uwan mukhtar fa sune dai 'yan uwan abdur rahman,ba'a canzawa tuwo suna
"Malam,ina tsoron sake kasancewa da ahalin su mukhtar...." Sai tayi shiru ta kasa qarasawa,shima shirun yayi yana nazarin maganarta,tabbas sumayya yarinya ce mai matuqar zurfin ciki,a iya zamanta na aure bazai iya fadar ranar data kawo matsalarta ba,saidai idan an fahimta a maganta mata.
"Ke kike da zabi a hannunki ai,ba zan miki auren dole ba"
"Malam,ina so abdur rahman ya janye daga qudurinsa,bana son sake shiga ahalinsu" ta fada zuciyarta na raurawa muryarta na rawa
"Shikenan zancansa ya wuce,sai ki fidda miji ina son hada aurenki da na yayanki abubakar idan ta kama har da su halima baki daya"
"Amma malam ba......."
"Sumayya,bana son qorafi ko wata magana,kinsan ba zaiyiwu kici gaba da zama a gida ba,shekara nawa,shekara daya ana gab da cika ta biyu" shuru tayi don tafi kowa sanin waye malam,amma ina mafita meye mafitarta?,
"Sumayyan luqman fa?" Taji ya jefo mata tambayar wadda ta sanya dago kanta ta dubeshi,murmushi ya kuma yi yana dubanta
"Mamaki kike yadda na sanshi?,ya fara zuwa gunki ba da izini ba ya karya doka ta,hakan ya sanya nayi bincike a kansa,na samu gamsassun bayanai a kansa,mutumin kirki ne bakin gwargwado" sai ya dan ja fasali yana dubanta kafin yaci gaba da cewa.

_yauma dai amin uziri_








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)


4⃣0⃣



*Bismillahir rahmanir rahim*

*innal laha la yugayyiru maa bi qaumin hatta yugayyiru ma bi'an fusihim*

_haqiqa Allah baya canzawa mutane(halin ko yanayin da suke ciki)har sai sun canza da kansu_

______________________________

        Ungawa ce mai matuqar kyau da tsari,akwai nauikan mutane daban daban cikinta,saidai akasarin mzauna cikinta din masu hannu da shuni ne da kuma masu rufin asiri ko wadanda suke ma'aikatan gwamnatin tarayya ta basu gida su zauna kamar su anty dije.

       Sai da mansur ya fidda kayanta baki daya ya shigar mata cikin gidan ta masa godiya sosai sannan ya ja motarsa ya shige wani katafare kuma hamshaqin gida dake kallon nasu.

         Dukka yaran gidan na nan kasancewar ranar qarshen mako ce,laila ita ce babba,sai hafiz mai bi mata,sannan khalifa sai nasir sai auta amina minal,a qalla laila zata yi shekaru goma sha hudu,ita ta fara ganin shigowar sumayya falon,ihu ta sanya wanda ya janyo hankalin 'yan uwanta ta nufi sumayya ta rungumeta,haka sauran suka baibayeta wanda ya janyo musu faduwa a qasa dukansu suna dariya,da qyar ta samu suka dagata suka koma saman kujera sannan ta soma tambayarsu anty dijen don bata ji motsinta ba,dining laila ta nuna wa sumayyan tana cewa
"Kinga yaya sumayya can duka abincinki ne,tun dazu mama ke jiranki baku iso ba har ta gaji ta shiga gidan daddy prof,amma bari naje na kirata" ta fada tana yafa dan yalolon mayafinta tayi waje da sauri,khalifa sumayya tasa ya fara nuna mata toilet ta shiga tayi alwala,tana kammala alwalar anty dije na shigowa
"Sai yanzu?,gaskiya kunyi nauyi a hanya kamar wadanda suka hau motar haya inji hajiya bilki" murmushi sumayya tayi tana duban anty dije wadda ta sake gogewa bisa dukkan alamu zaman garin ya karbeta matuqa,ta kuma zama 'yar gayu ita da yaranta baki daya
"Wallahi anty sai da muka biya kasuwa muka karbo wasu kaya sannan har mun dau hanya wani oga ko yallabai ya maida ku zoo road karbo dinki"
"Eh inaga man ne dinkunan su'ad ce,maza yi sallar kizo kici abinci kafin mu zauna hirar yashe gamo" ta fada tana sanya su laila dauke akwatunta zuwa wani daki da aka tanada saboda baqi irinta.

      Sai da taci ta qoshi sannan suka baje a falon ana hiran yaushe gamo,kusan haka suka qarar da wunin ranar,ko da malamar lesson din yaran ma tazo guduwa sukayi suka qi zuwa sai tafiya tayi,da dare ma yayi da qyar suka tafi dakinsu don cewa sukayi tare da sumayyan zasu kwana,saida anty dije ta korasu saboda tana son suyi zance,sosai suka sake kuwa don mai gidan ta baya nan sun tafi semina lagos,sosai anty dije ta sake kwantar mata da hankali tare da bata shawarwari ta rufe da fadi cikin sigar tsokana
"Duk da nasan sumayyan tawa zuwa yanzu ta fara girma,hankali ya fara zuwa mata" itama dariya tayi,sai wajen sha daya da rabi sannan ta fita ta barta,to nan din ma lukman bai barta ba da hira sai data ce tana jin bacci sannan yace
"Ki kula min da kanki to na baki amanar kanki my dear kinji"ajiyar zuciya ta saki sannan ta amsa masa ta katse kiran,taso kiran halina taji ya abdallah yake,amma ganin dare yayi nisa ya sanyata ta haqura ta barwa gobe,duk sai taji tana kewar yaron nata.

   ******     ******     ******

      Kwanakin da tayi a garin kwanaki ke da suka yi mata dadi sosai,kullum yaran na nanuqe da ita suna hira,sauqin abun sun gama jarabawa hutu kawai suke jira,wani lokaci da yammaci anty dije kan debe su da motar mai gidan da ya barta a gida ta kaisu park su dan sha iska suyi ciye ciye su dawo,hakan na yiwa sumayya dadi,lallai ko yaya ka motsa daga wani gu zuwa wani gu zaka samu sauyi zuciyarka zata yi dadi.

        Duk wani abu da ya kamata a yiwa amarya anty dije da kanta ta yiwa sumayya,cikin kwana goma ta hadata tsaf.

       Ana ya gobe zasu koma kanon laila na kwance kan cinyar sumayya sumayyan na tsefe mata kitsonta zasu wankin gashi da yamma anty dije ta fito ta dubesu
"zan dan shiga gidan daddy prof zamuyi sallama da su,Allah baiyi da ni za'a yi sunan nan ba"sumayya ta daga kai ta dubi anty dije
" au haihuwa akayi halan?"
"Sai yau zaki tambaya kenan,kwana na nawa ina leqa su amma baki taba karar ki shiga ku gaisa da mutanen ba,direban gidan ya dauko ki daga kano fa,surukar gidan ce ta haihu" murmushi sumayya tayi
"To ai ban sansu bane anty"
"Ni ai na sansu kuma gashi na gaya miki,mutanen akwai tsabar mutunci da karrama mutum,duk yadda Allah ya musu tsabar arziqi amma basu raina na qasansu,mai gidan bakiga yadda ya dauki abban khalifa ba kamar dan cikinsa,su khalifa kuwa ya maidasu tamkar jikokinsa" jinjina kai sumayya keyi sannan tace
"Allah ya saka musu da alkhairi,kice ina musu barka"
"Zasuji tunda ba zaki din ba" inji anty dije ta fice tana mita sumayya ta bita da dariya.

       Basu jima da kammala tsifar ba anty dijen ta dawo hannunya dauke da baqar leda,ta cillar kan cinyar sumayya
"Da baki iya zuwa gaida mutane ba gashinan haj bilkisu tace na kawo miki kiyi fitar biki,ta yaba da zabin leshin ki wai kin iya zabar kala,ashe tare kuka shiga shagon da mansur din". Baki ta saki sanda ta fiddo leshin taga daya daga cikin wadanda suka siya dinne
"Anty kinsan kuwa nawa ne farashinsa duk guda daya?". Dariya anty dijen tayi
"Hmmmmm,bakisan mutan gidan bane sumayya,kinga ku tashi ku shirya ku wuce wankin kan nan kada dare yayi muku hanya"ta furta tana miqewa ta nufi kitchen.

   ******    *******    *******

      Sanda suka isa kwanaki biyu sukayi saura a daura aure don babu wani event da sumayyan ta tsara yi,yaya abubakar ne kawai zaiyi walima bayan an gama daura aure.

       Kusa awa guda kenan da shigowarta gidan amma bata ga wulgawar abdallah ba,tun tana kawaici bata tambaya ba har sai data magantu
"wai nikam ina abdallah ne?" Maimakon maman ta amsa mata sai tace da ita
"Kije malam nason magana da ke" hakanan taji jikinta bai bata ba,ta miqe ta zura hijabinta ta fice.

      A ladabce ta gaisheshi ya amsa yana tsokanarta abuja ta karbeta,sai ya bata kunya ta sunkui da kai tana murmushi yayin da tausayinta kuma ya darsu a zuciyar malam din
"Sumayya maganar da zamuyi da ke nasan ba zata miki dadi ba,domin raba da da uwa sai Allah,saidai babu yadda muka iya,bayan tafiyarki mukhtar yazo ya karbi yaronsa...." A firgice ta dago ta dubeshi muryarta na rawa idanunta na fidda ruwan hawaye
"Amma malam me yasa zaimin haka,rabamu ken......."kaaa qarasawa tayi tayi qas da kanta
" kiyi haquri sumayya,shi ya fiki a haqqu da shi,sannan ya riga da yace baiso yaron yayi zaman a golanci gidan wani kamar yadda shima yayi,kiyu haquri nasan ba wai ya rabaku bane na har abada saboda yadda yazo mana bada nuna isa ko qarfa qarfa bane,abinda na lura shine bazai iya jurar rashin ganin yaron bane,tunda idan har kika tafi da shi bashi yiwuwa ya dinga binki gidan mijinki da sunan yazk ganin dansa,kiyi haquri babu komai ai kuna tare,na tabbata za'a dinga kai miki shi"malam ya fada cikin tausasawa. Haka malam din ya dinga lallashinta yana bata kalamai har ta samu ta danji sauqin zugin zuciyarta,saidai abinda take ji na game da kewar yaron har yau bai sauya ba.

       Data koma daki taga sauran kayayyakinsa kasa ci gaba da daurewar tayi,ba shakka raba da da uwa ba qaramin abu bane,shi yasa aka ce ko mutuwa tana shakkar idon uwa,yaya wadanda suka rabu da 'ya'yayensu suke ji rabuwa ta har abada?,ashe da sauqi ita tunda yana nan cikin duniyarta kusa da ita amma duk da haka ta gaza daurewa,kuka tayi mai yawan gaske wanda shi ya haifar mata da zazzabin da ciwon kai mai tsanani har ranar da aka daura auren,haka nan aka tattarata aka kaita dakinta tana mai ci gaba da kuka mai qunshe da abubuwa iri daban daban

     **** *9:30 pm*  *****

      Lukman Bashir shine asalin sunansa,haifaffen garin kano cikin qaramar hukumar kano municipal,yayi karatunsa iya N.C.E sai ya fada kasuwanci gadan gadan,mahaifiyarsa hajiya kubra shi kadai tallin tal ta haifa,hakan ya sanya ta dauki so da qauna da kulawa ta dora masa,wannan shine dalilin da ya sanya duk lokacin da yayi aure ta fuskanci yana mutuwar son matar take rabasu don wai ba zata bari a mallake mata yaro ba tana kallo,kasancewar gidansu daya part guda yayi mata da ya tashi ginin gidansa,a haka a haka ta sanya lukman ya rabu da mata kusan hudu kenan duk da cewa yana dacen matan aure masu matuqar haquri da biyayya saidai ita sam bata gani,haquri da biyayyar da sukewa lukman din ita ke jawo musu qauna gunsa,amma ita gani taje tsabar asiri ne matan suke yi,sam matan basu da sukuni,hatta zanin daurawa idan zai musu ita ke karbar kudin ta siyo ta bada adinka musu ita kuwa sai wanda ta zaba zata sanya,hakanan duk cikin matan da yake aurowa mutum daya ce ta haihu da shi don na wani dadewa take bari suyi ba,ita din ma a gidansu ta haife sai da ta yaye hajiyan tasa aka karbota,'ya mace ta haifa wadda ake kira da nuwaira.

       Hausawa suka ce alhaki kwikuyo ne,a irin haka ne Allah ya hada lukman da KARIMA gogaggiya mai idanu a tsakiyar kaa wadda ita ta haifa masa yara uku dukka mata zaitun marwa da radiya,da fari kariman lumbu lumbu ta yiwa hajiyan har ta saki jiki da ita,sannan daga bisani ta sanya gaba daya daga lukman din har hajiyan aka sanya su qarqashin ikonta,daga lukman din har hajiyan umarni suke karba daga wajenta,babu wanda ya isa ya tsallake abinda ta shimfida masa,sai a bayan idonta su yita takaici da jimami amma a gaban idonta ko tari ba wanda ya isa yayi,mutane da yawa sunyi murna sunyi shewa da wannan sauyi domin ya zamewa hajiya kubra izina.

       Tun bayan da ya auri karima bai kuma gigin qara wani auren ba sai a yanzu da yake KUNDIN QADDARArsa na rubuce da auren sumayya,sanda yake gaya mata zai qara aure a tsorace yake,ita kanta tayi matuqar mamaki,a fusace ta shiga dakinta ta kira wayar malaminta ta sanar masa,wayar tace ya kashe zaiyi bincike nan da awa guda zai nemeta,ya kuwa nemetan ya sanar mata wannan aure ba makawa sai an yishi saboda yarinyar nada addu'a hakazalika 'yar gidan malamai ce,wannan kalma ta sake tunzura karima ta sanya aka sake sabunta aiki mai kyau akan hajiya da lukman don kada sumayyan ta samu kafar rusa mata shirinta wanda ta riga ta qudurceshi cikin ranta,haqura tayi saidai duk wani harkar biki kama daga lefe da sauransu ita tayi su,komai sai data ninka kudinsa sannan kuma ta zuba abinda ranta yaga dama,sauqin daya gidansu sumayyan gida ne na dattako babu wanda ya damu dabtsada ko yawan abinda aka zuba cikin lefen.


         Qarfe tara da rabi na daren bayan an kaita gun hajiya an gabatar da ita yayin da ita kuwa hajiyan ke fadin tabi karima wanda ya baiwa kowa mamaki sannan aka dawo da ita dakinta wanda falo ne guda daya makeke sai dakunan bacci na kowacce mace da bandaki a cikinsa,sai dakin yara da mai gida kitchen da bandaki duk cikin babban falon,cikin falon dai ya kira sumayya don dama ita karima na zaune a falon tun kan a kawo sumayyan har kowa ya watse
"To sumayya wannan itace uwar gida na uwar 'ya'ya na,idan kika bita kamar kin bini ne,na auroki ne ba don bana sonta ba,bana so kuma ki raina min ita,hatta hajiya farincikinta shine farincikin karima da fatan kin gane" kanta ta cira a hankali tana dubansu baki daya,cikin zuciyarta ta furta
"Ikon Allah,yau kuma da wacce kalar Allah ya hadani?".
Miqewa kariman tayi cikin izza tana yatsina
" idan ka gama ka sameni a daki,kada ka wuce minti biyar"
"To....to to" ya amsa cikin inda inda tare da binta da kallo har ta wuce dakinta,da sauri ya dubi sumayya
"Amarya ta muje na rakaki daki kinji" ya fada cikin kwantar da murya,ba musu ta miqe tayi gaba mamaki na kasheta,wai dama haka lukman din yake?me yake shirin faruwa ne?.

      Bakin gado ya zaunar da ita yana duba agogo don kada yayi laifi
"Zauna bari naje,in Allah ya yarda zanyi qoqarin dawowa,ga kaxarki nan idan kina jin yunwa kici kafin na dawo" ya fada yana juyawa ya fice da sauri,binsa tayi dakallo baki daya qimarsa da mutuncinsa da take dan gani a da suna ficewa fit daga ranta,hawaye suka soma fita daga kuncinta data tuna rayuwar gidan mukhtar makamanciyar wannan,saidai sam da alamu bata kai qazancewar wannan ba,ita kuma nata salon QADDARAR kenan?. Juyawa tayi ta kwanta tana faman zubar da hawaye.

       Har bacci ya soma fusgarta taji yana ambaton sunanta sama sama,ta bude idanunta tana dubansa,murmushi yake yana kallonta shima tare da duba bakin qofar dakin kamar wani ya biyoshi,ganin ta tashi ta zauna ya sanyashi maida qofar dakin ya murza key,kamar wanda ke sauri jirgi zai tashi ya barshi yake magana
"Tashi maza ki dauro alwala,ina fatan dai kinci abincin ko?.....kinyi sallar isha'i?.....dauro alwala sumayya babu lokaci...."ya fadi yana satar kallon qofar dakin
Cikin mamaki take dubanshi duk ya wani firgice,lokaci kada ya qure kamar yaya take tambayar kanta
" don Allah tashi mana sumayya kada ta....."bai qarasa fada ba aka fara dukan qofar kamar za'a ballata
"Innalillahi wa inna aihi raji'un" ya fada yana dafe kansa.
"Zaka bude ko sai na sassaba maka,maci amana" inji mai buga qofar,jiki ba qwari ya nufi qofar ya bude mai bugun ta fado dakin tana raba idanuwa,kubra ce sai data qarewa dakin kallo ta fuskanci babu abinda ya faru sannan ta kalleshi
"Ni zaka ci amana ka karya alqawarin daka yimun?,to wallahi ko kwana a dakin baka yi butulu kawai,maye,tunda ni ban isar maka ba,wuce muje nace ka tsaya ka kafeni da idanuwa" sai ya waiwaya yana duban sumayyan har sai data ingiza qeyarsa sannan ya fice yana waiwaye.

     Kan sumayya ta dawo da kallonta"da sauran quruciyarki amma kin zabi nakasta rayuwarki,idan don kwanciyar aure kika zo gidan nan to kinyi babban kuskure don yadda kika zo haka zaki koma,don babu wasu 'ya'ya da za'a haifa a gidan nan sai nawa yaran,itama wadda aka haifa din don uwarta ta rigani zuwa ne,wlh da ni na rugata zuwa da bata isa ta haifeta ba,keda lukman kuwa saidai kallo"
"Ke lukman ya dama,kuma ta Allah ba taki ba,ni an bani ilimin yarda da QADDARA mai kyau ko akasinta,hikinar ubangiji kuma yawa gareta,hakanan sanin gaibu sai Allah,duk kuma nisan jifa wataran qasa zai fado,mai yiwuwa ma idan ya tashi fadowar ya dawo tsakiyar kan wanda yayi jifan"
"Ke ki iya bakinki wallahi idan baso kike kiyi kwanan gidanku ba"
"Idan kinso kina iya karbe aron numfashin ma da kika bani idan yaso nayi kwanan kabari baki daya" sumayya ta fada hankalinta kwance,don ya zuwa yanzu tana jin ta gama daukar haquri da rainin wayon kishiya,bata cuce su ba don me su zasu dinga cutar da ita,tabbaa dafi da gubar zainab har yau bata bar illata zuciya da gangar jikinta ba,don kusan ita ta zama silar data sake cillota wannan muhalli da take ganin wata rayuwa miji ke biyayya wa mata. Mamaki ya cika kariman don ta jima rabon da a mayar mata da magana haka,sai zuciyarta ta tuna mata daga inda sumayya ta fito,take gumi ya fara tsatstsafo mata,tabbas sai ta sake shiri a kanta,qwafa taja sannan ta juya tana fadin
"Da karimatu kike zancan lallai bakisan wace ni ba"bata yi nauyin bakin maida mata amsa ba don kada ma ta fita bata ji ba
"hakanan bakisan wace sumayya ba,ki zuba ido kisha kallo". Bayan fitarta muqulli sumayya ta sanyawa qofarta ta shiga toilet ta daura alwala,sam bata ji wata damuwa na barinta da angonta yayi ita daya a dakin ba,kaya ta fiddo ta sauya wadanda zata sake a cikinsu sannan ta sanya hijabi ta tada sallah,kyawawan nafiloli ta raya daren sosai da su kafin bacci ya rinjayi idanuwanta.

*asuba ta gari amaryar lukman*

*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

4⃣1⃣



*Bimillahir rahmanir rahim*

*wattaqu yauman turja'una fihi ilallah,summa tuwaffa kullu nafsin ma kasabat wa hum la yuzlamun*

*_KUJI TSORON WATA RANA DA AKE KOMAR DA KU

Please Login or Register in order to submit comment