Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za'aji dadin zama a ciki?,kayan haram ne fa?.......hhhhhh......hmmm kadan ma kenan" ta fada tana jan wani shegen tsaki tare da juyawa ta koma dakinta.

           Cikin mamaki take binta da kallo tare da neman tsari cikim zuciyarta,matar da duk artabun da ake cikin gidan tun safe bata fito ba sai yanzu,watsar da tunanin tayi,me yasa dakinta ya tsone mata ido,koda yaushe bata da magana sai nashi,da bata ce Allah ya sawwaqe ba ta ja bakinta tayi shiru mana,itadai tunda ta riga da tasan cewa tayi addu'a koma meye zaizo ko da QADDARARTA ne sai ya sameta din zaya zo mata da sauqi.

        Tana kammala sallarta kitchen ta wuce ta soma hidimar dora girki saboda yau girkinta ne ita zata karbi mukhtar din,ita kuwa bata wasa da ranakun girkinta,tana kitcehen taga ficewar fa'iza daga gidan.

_kuyi haquri da wannan ina cikin uzururruka_

*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍✍✍✍
✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣2⃣

________________________

*Bismillahir rahmanir rahim*

*qul innal amra kullahu lillah*
_________________________









          Sallamar fadima ce ta ratsa dodon kunnenta,tana daga kitchen din ta amsa mata,kai tsaye ta nufo kitchen din ta leqo,murmushi sumayya tayi qoqarin sannan tace
"Au fadima ce?" Yatsina fuska tayi ta karkace baki tace
"Eh.....nice,ana ta kitchen ne anata fama?" Cikin jin dadin jin fitowar kyakkyawan furuci yau daga bakin wanda ya jibanci mukhtar zuwa gareta tace
"Wallahi kuwa,kin ganmu muna ta fama da sanwa" bisa ga sabanin tunaninta sai taji tace
"A'aha,anan dama aka fi kauri ai,aci a cika mana gida da kashi,sockaway nan da nan ta tumbatsa" sosai maganar ta bata ranta,cin fuskar tana ganin kullum dada gaba yake,me yayi zafi ne haka?,ba aure bane kuma ta bar dan uwansu yayi,tunda a yanzu suna da wadda suke tunanin zata cika muradinsu ai yaci ace sun sakar mata mara tayu fitsari yadda ya kamata,sai ta sake yin wani murmushin idanunta cikin na fatiman
"Ayyah,ai kayi auren ma kayi kashi cikin gidan mijinka ma rahama ce,wasu har yau an rasa wanda zai daukesu ya kaisu gidansa ko kashin ne ma suyi" sarai ta fahimci magana ta yaba mata,a fusace ta qarasa shigowa kitchen din tana tunkarar sumayya kamar zata kai mata shaqa
"Da uban wa kike?"
"Da wanda ya tsargu" ta fada tana bude tukunyar miyarta tana juyawa,wuyanta ta ruqo ta baya,a nutse ta juyo ta sanya hannunta ta zare shi daga wuyan nata tana nunata da yatsa
"Kada ki kuskura fati" sumayyan ta fada kana ta ja tsaki ta juya taci gaba da abinda takeyi.

        Baki ta saki galala tana dubanta,iya tsawon zamanta da su ko kallon banza babu wanda sumayyar ta taba yiwa duk irin budurin da sukeyi tsakiyar kanta,kafin ta kai ga cewa komai fa'iza ta sanyo kai cikin kitchen din tana cewa
"To malama,da kika zo nan kika tsaya kina kalen magana nan aka aikoki?" Ta bude baki tayi da niyyar yin magana fa'izan ta tarbeta
"Kinga miqon saqona sai ki dawo kuyita yinta 'yar ayi jikar na saba" waiwayowa fatiman tayi cikin mamakin kalaman fa'izar
"Wace 'yar ayi jikar na saba din?,babata da ta haifeni ta haifi mijinki muntari ko innar babarmu?"
"Kinga duk wanda kika zaba cikinsu,zaki bani saqon ko kuwa?" Ba yadda ta iya saboda yaya yaha ta jadda da mata saqon,amma ta sake yarda fa'iza ba mutunci gareta ba,tsaf zata iya zagesu su dukan,haka tayi haushin kaza juye kan dami ta zabgawa sumayya harara tare da jan doguwar qwafa
"Yar malamai ba'a haifa ba an shanye mana dan uwa" ta fadi tana shirin ficewa tabi bayan fa'iza,dariya tayi
"Au ashe na isa ma" tana jin maganar kuma ta bata haushi tare da mamakin budewar bakin sumayya amma haka ta haqura tabi bayan fa'izar.

          Qeme me fa'izan ta hanata kudin motar komawar bayan ta bata saqon,juyin duniya tace bata da ai dan uwansu bai bada ba,haka nan ba don taso ba ta shiga wajen sumayyan,a lokacin ta gama aikinta tana kan kujera tana gyaran qumbarta(farce)
"Kudin mota nazo ki bani zan koma gida"a nutse ta daga kai ta dubeta
" da na aikeki ina?"fuska ta hade don kada ta rasa
"Ai na sancewa akwai kudi gurinki"
"Wadanda kika bani ajiya kenan dazu" sosai take shan mamakin yadda sumayyan ta zama,amma babu komai komai ya kusa zuwa qarshe saboda haka ta dan sassauto
"Ba halinki bane sumayya ba fa,ko dari ce ki bani zata kaini gida" shiru ta danyi sannan ta ajjiye rezar hannunta ta shiga uwar dakanta ta dauko dari biyu ta miqa mata,babu godi bare na gode ta amsa ta juya ta fice,da kallo ta bita sannan ta girgiza kai,ashe guri suka samu suketa shanya yadda suka so?,wato sam wani mutumin baisan alkunya ba kenan,sai ka sauya launi kuke iya zama dai dai da shi?,idan banda sun sayawa kai raini ina ita ina fadiman ina ita?wadda a qalla ta bata shekara kusan shekara hudu ko biyar
"Allah ya kyauta ya rufa asiri" ta fada a fili tana ci gaba da abinda take.

          Lafiya lau yau tayi barcinta har ta kammala ranakun girkinta ta miqa mukhtar din ga fa'iza.

         Kasancewar da safe suje miqa girki ga wadda zata karba ya sanya tana kammala komai ta wanke kanta ta wuce gidan kitso nam qarshen layinsu,sai data fara shiga gidan maman nana ta dauki saboda tana son zuwa gida sannan suka wuce.

           Zuwa sha daya na rana aka gama mata kitson ta wuce gidansu.

          A kitchen ta tadda innarta ta dora sanwar rana,gidan babu kowa saboda qannen nata duk weekend na zuwa wata islamiya tun tara na safe sai biyar da rabi na yamma suke dawowa.

         "Ina fatan lafiya kuke dai ko?" Innar ta tambayeta bayan sun gama gaisawa,murmushi ta saki ta kada kai
"Lafiya qalau inna"
"To madalla haka akeson ji,aci gaba dai da haquri,zaman aure ko kai kadai ne sai kayi haquri balle kuma da abokiyar zama,Allah yayi miki albarka"cikin jin dadin addu'arta tace
" amin inna na gode"suka dan fada wata hirar kafin tace
"Wai ni kam inna ina ya abbakar?,ko leqoni fa inna baya yi" ta fada cikin shagwabe fuska
"Hmmm,yayanku ai yanzu bai ga ta zama ba,ya dauko aure" cikim zumudi da murna sumayya tace
"Allah innarmu?,wace a ina take"
"A'ah,sai ki jira shi yazo kuma wannan kyaji daga bakinsa" ta fada innar tana miqewa saboda kasancewar abubakar dan fari a gunta.

          Tana nan har abubakar din ya dawo,nan suka sha hirarsu,sai kusan shida saura ya dauketa kan babur dinsa ya kaita har qofar gida,tayi tayi ya shigo yaqi haka ta haqura.

          Muqullinta ta sanya ta bude dakin nata ta sanya kai zata shiga,wani dunqulallen abu ya tokareta,tashi daya taji wani azabbaben bacin rai ya kamata,tsanar dakin ta mamayeta,sai ta koma da baya ta janyo kujera 'yar tsuguno bakin qofar dakin ta zauna,duk da uban tarin gajiyar da ta debo amma sam bata sha'awar shiga dakin.

           Har qarfe goma na dare tana tsakar gudan zaune,a nan tayi magariba tayi isha'i kasancewar mukhtar baya gari yayi tafiya legos sarin kaya.

           Tsakar gidan yayi tsit sai ita daya,fa'iza ta gama kara kainarta ta qule daka tana kyautata zaton ma tayi bacci,gashi babu hasken wutar lantarki don nepa sunyi tsiyar,gidan taje ta rufe sannan ta dawo tsakar gidan,ta jima tsaye a bakin qofar tana nanata addu'a sannan taji salama na saujarwa ruhinta,ta kwashi jakarta ta shiga dakin gabanta na wani irin bugawa,kayanta kawai ta sauya ta haye gado a takure wani tsoro da batasan na meye ba fal ranta.

            Cikin baccinta taji kamar ana tashinta,a firgice ta farka tana ambaton Allah,tamkar ana korota daga dakin haka ta dinga ji,a gaggauce ta fito izuwa tsakar gida jikinta na rawa,sulalewa tayi ta zauna dirshan jikin qofar dakin tana ci gaba da kiran sunan Allah a haka asuba ta risketa,a nan ta daura alwala tayi sallar asubar.

          Qarfe shida da rabi na safiya taji wani irin qwarin gwiwa na shigarta,ta miqe cikin hanzari ta koma cikin dakin,tamkar ana tafasa zuciyarta da tsanar dakin ta nufi uwar dakanta ta dangana da sif dinta,akwatinta ta jawo tamkar ana umartarta ta shiga loda kayanta tsaf sannan ta sauya na jikinta ta rufe akwatin ta janyo shi waje,sakatar gidan ta zare kana ta fice kai tsaye ta nufi bakin titi.

         Ta kusan a qalla awa guda tsaye bakin titin ba tare da ta samu abun hawa ba kasancewar safiya ce babu yawaitar sawaye,sai da ta fara qosawa sa tsaiwar har tana tunanin fara takawa da sawayenta wani mai adaidaita ya nufo inda take,da hanzari ta tsaidashi gudun kada ya wuce ta rasashi,ta gaya masa inda zai kaita shi kuma ya gaya mata abinda zata biya,ba tare da ta tsaya ciniki da shi ba ta hau tare da tura akwatinta ciki shima.

*masu karatu muje zuwa,kada kuce komai kowanne dan adam da irin tasa QADDARAR*





*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍✍✍✍
[9/25, 12:41 AM] ‪+234 908 222 8222‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣3⃣

______________________
*wa iyyamsaskallahu bi durrin fala khashifa lahu illa huw,wa iy yuridka bi khairin fala raadda li fadhlih*
__________________________








           A qofar gidansu mai adidaita sahun ya ajjiyeta,ta biyashi sannan ta ja akwatinta zuwq ciki.

         Ta jima a soron tsaye gabanta na faduwa,tana mtuqar shakkar iyayenta,saidai hakanan taji ana ingizata zuwa barin gidan,wani irin qunci take ji idan tana cikin gidan,numfashi ta ja sannan tayi shahada ta shige.

           Qannanta na tsakar gida suna karyawa jikinsu sanye da unifoarm din islamiyya,innarta kuma na daga cikin rumfarsu,
"Lah sannu da zuwa yaya sumayya" suka fada halima na karbar mata akwatinta tare da shiga da shi cikin rumfar tasu ita kuma tabi bayanta.

           "Lafiya sumayya da safiyarnan?" Innar ta tambayeta cikin fuskar mamaki,gefan kujerar ta samu ta zauna sai kawai ta fashe da kuka ba tare da tace komai ba,baki innan ta sake tana kallonta kafin daga bisani ta yiwa halima nuni da hannu kan ta fita ta basu guri,daga qarshe itama da ta gaji da tambayarta sai ta miqe ta fito tsakar guda ta hau ayyukanta ta barta cikin dakin.

           Wuni guda innan na tambayarta amma ta gaza cewa komai,to me zata ce mata ya korota daga gidan,ba matsala bace tsakaninta da mijinta ba ballanta na tace,ba wani abu sukayi ba,to meye dalilinta,sosai hankalin innan ya tashi ganin taqiyin maganar,gashi kuma malam din baya gida sun tafi musabaqa ta jaha da ake gudanarwa daga shi har yayan ta abubakar,amsa daya ta iya bata data tambayeta ina mukhtar din ta sanar masa yayi tafiya,sai kan innar ya sake daurewa,har dare tana zuba ido ko zata ga wani kan sumayyar amma shiru haka suka wayi gari.

            Mamaki innar ta kuma tashi da shi na ganin washegari sumayyan ta sake sarai,walwalarta take kamar babu wani abu da ya shalleta,wannan damuwar da ta zo da ita jiya duka yau babu ita.

           Tunda suka dauko hanya daren jiya yake Allah Allah ya iso gidan nashi don yayi tozali da sumayyar tasa,qarfe uku da minti biyar dan adaidaita sahu ya ajjiyeshu qofar gidan nasa ya sallameshi ya shige gidan bakinsa dauke da sallama fuskarsa qunshe da murmushi don yana da yaqinin samun tarba mai kyau kasancewar ya tafka sa'a cikin ranar girkinta zai dawo din.

           Mamaki ne ya maye gurbin doki murmushi da fara'ar da yakeyi ganin yadda tsakar gidan yake a tarwatse babu cikakkiyar tsafta,sallama ya sakeyi karo na biyu saidai shiru babu amsa,a hankali idanunsa suka sauka kan dakin sumayya,take yaci karo da kwad'on da take kulle dakin duk sanda zata fita,mamakinsa ya sake ninkuwa,ko da can sumayya sanda take da qananun shekaru ainun bata taba fita ba tare da uzininsa ba koda kuwa maqota ne,ya maida kallonsa dakin fa'iza ana sakaye,ya qarasa ya tura ya leqa kansa ciki bata nan,ya tura bandakin ya leqa nan ma bata ciki,jikin bango ya koma ya jingina tare da ajjiye jakar bacco din hannunsa,ba fa'iza ce damuwarsa ba sumayya ce,lambarta ya lalubo ya kira saidai an sanar masa da cewa a kashe take,ya maida wayar cikin aljihunsa yana maida ajiyar zuciya tare da shiga tunani.

          Maganar fa'iza ta katseshi wanda da alama da wasu dake daga waje take maganar,ya zubawa qofar soron idon har ta qaraso,da fari tayi turus,sai kuma ta qaraso tana dubansa
"Au......ashe kai ne.......ashe yanzu zaka dawo.....na dauka sai anjima gashi ban tanada ma komai ba"
"Ina sumayya take?" Ya tambaya ba tare da ya kula da surutun da take zuba masa ba,wani abu ya takore wuyanta,wato ta sumayya ma yake ko,zai gane kuransa ne wlh,baki ta tabe sannan tace
"Ka bani ajiyarta ne?"idanunsa ya ware baki daya har sai da taji tsoro
" ke bana ciki da iskanci,ni kike gayawa haka,zan tattaki ne wallahi naga uban da ya tsaya miki,banza sha sha sha,ina sumayya take nace miki"cikin gunguni tace
"Oho,nidai da asussuba naga ta hada kayanta ta fice bansan inda taje ba".

        Bai qara bi ta kanta ba ya shige dakinsa ya ajjiye kayan hannunsa,da sauri ya sake zaro wayarsa saboda tunawa da yayi waccan satin sumayyan ta saka maaa lambar wayar innar tata ta gaya masa ya abubakar ne ya siya mata waya.

         Bugu biyu zainab ta daga tana fadin
" ya mukhtar ga innar can bari a kai mata"da sauri ya katseta
"A'ah zainab,ina yayarku"
"Gata can a daki a kwance"
"Tun yaushe tazo gidan"
"Tun jiya"
"Ok" ya fada sannan cikin sauri ya ajjiye wayat,kayan jikinsa ya cire sannan ya fito ya nufi tsakar gida,yana jin motsin fa'izan daga kitchen bai bi ta kanta ba ya tara ruwan wanka ya fada bandaki.

           Sai da ya rama sallar azahar dake kansa sannan ya shirya cikin wani yadin kufta ruwan toka(ash),ya feshe jikinsa da turare,yayi kyau matuqa,take zatinsa da kwarjininsa suka fito,yana sanya takalminsa sau ciki irin na maza fa'iza ta shigo dakin hannunta dauke da plate data ciko da jallope din taliya wadda keta zuba qauri saboda uwar wutar da ta babbaka mata saboda saurin da take ta kawo masa yaci tun kafin yaje ya maido da sumayya gidan plan dinta ya rushe.

       "A'ah,mutari ina zaka daga dawowarka,ga abinci na maka ai ko shi ka tsaya kaci" kallo daya yayi mata ita da taliyar tata yaci gaba da sanya takalmansa yana daga duqen ya jefeta da
"Bani da buqata" gabanta ya fadi ganin asara qiri qiri na shirin riskarta,kwana uku tayi tana tattalin kayan tarkacen da ta dafa taliyar da shi sai gashi cikin mintinan da basu gaza biyar yana son janyo mata asara.

        Matsowa tayi kusa da shi cikin marairaicewa da tausasa murya irin wadda bai taba riska daga gareta ba ta soma hilatarsa,da sauri ya ja baya tare da jan matsiyacin tsaki ganin tana gab da shafa masa maiqon abincin,maqullin babur dinsa ha zara ya fice ya barta tsaye a nan dafe da kai.

            Tana kwance cikin falon yaro yayi sallama ya shigo
"Wai mukhtar ke magana a qofar gida" inji yaron,zumbur ta miqe zaune saboda wata muvuwar faduwar gaba data tsinci kanta a ciki,da sauri ta qule uwar daka sanda taji muryar inna na sanya hijabinta tare da cewa yaron ya shigo.

           Ta window ta dinga leqensa sanda yake tsugunne gaban innan kansa qasa yana gaidata,sosai ya mata kyau,mukhtar akwai bala'in kwarjini da kyawun siga,sonsa da qaunarsa ke dambarwa cikin zuciyarta,gefe guda kuma  wani mashahurin tsoro fargaba da qin son komawa cikin gidansa ke kai kawo cikin wani irin qarfi cikin qirjinta,sai ta koma gefan gado ta zauna jiki sanyaye tana fidda qwalla.

          Tana jin shigowarsu cikin falon shi da innar,ta sa baki tayi kiranta,sai data kirata kusan sau hudu sannan ta samu ta fito,kanta a qasa tana digar qwalla,gefe ta samu ta takure kanta a qasa ta gaidashi,ya amsa yana dubanta,har yanzu mamakin da ya daureshi tun farko shi yaqi sakinsa,me ya samu sumayyar?,me yayi mata ta baro gidansa ba tare da saninsa ba?.

"Ka ganta nan,nima hakanan na ganta da sassafe bansan me ya faru ba,kuma juyin duniya meke faruwa taqi cewa komai,to gaka nan dai gata" inna ta fada tana dubansu
"Wlh nima inna dawowata ta ras bata nan,amma ki sake tambayarta inna ko wani abu nayi mata"waiwayawa tayi cikin daurewar fuska dake nuna ba'a son wargi tace
" ke sumayya......dubeni da kyau banason rashin mutunci da iskancim banza,ki gaya mana me mijnki yayi miki?"cikin muryar kuka tace
"Babu inna,babu abinda yayimin wallahi" cikin hargowa da bacin rai innar ta sake cewa
"Babu abinda yayi miki don iskanci shine zaki debo qafa ki taho gida,to ki tashi tun muna shaida juna tun kafin mahaifinki ya dawo sawunki a likkafa ki tattara kayanki kibi mijinki" wani irin kuja ta fashe da shi tamkar ana cire ranta ba tare da ta iya cewa komai ba,juyin duniya inna tayi mata ta tashi ta bishi taqi,har duka ta kai mata amma a banza,ganin hakan ya sanya mukhtar tarar innar yace
"Inna,ki barta,barta kawai,idan malam din ya dawo ko zuwa gobe ne sai na dawo" bacin rai tsantsa ne cikin ran innan haka mukhtar din ya fita.

          Sake qara sautin kukan nata tayi can qasan zuciyarta na mata zafi,ta rasa dalilin da ya sanya ta yiwa mijin nata haka,can qarqashin zuciyarta itama son binsa take,son kebancewa take da shi,tana da buqatarsa,tana buqatar jin duminsa amma tsanar gidan ya taso ta danne komai.

        Tun innan na jin haushinta da jin haushin kukan nata har abun ya fara bata tsoro,addu'a ta soma cikin zuciyarta tana fata ba abinda take tunani bane ya afkawa sumayyan.

             Tunda ya koma gidan ya qulle kansa cikin dakinsa,fa'iza ta sake dawowa da niyyar bashi taliyar,nacin duniya yaqi bude qofar,da taga haka kuma ta lura bai dawo da sumayyan ba sai ta watsar da shi tayi komawarta daki tare da kwafar da taliyar cikin kwandon shara tunda burinta dai ya cika,dama ba wai damuwa tayi da yunwar cikinsa ba,aikinta dake cikin taliyar take yiwa kuma komai ya tafi dai dai.

          Tun a daren da malam din ya dawo ta zayyane masa komai,shiru yayi cikin dogon nazari,innar tayi niyyar taso masa sumayyan ya dakatar da ita yace ta barta zuwa safiya sa hadu.

           Qarfe bakwai da rabi na safe ta shigo dakin malam din sanye da hijabi,ga mamakinta sai ta tadda su tare da mukhtar,gabansu kayan kari ne wanda malam din ya gama karyawa kasancewar da wuri yake karyawa ya kuma takura mukhtar wanda shayi kadai ya iya sha.

          "Sumayya,me ya hadaki da mai gidanki wanda har ya sanyaki fitowa daga gidanki ba tare da izinin mai gidanki ba?bayan ba haka muka baki tarbiyya ba" Shiru tayi qwalla na taruwa cikin idanunta ta daga kai ta dubi abba malam din,inna da zuciya ta hasalota tace
"Tsabar rashin mutunci ne da sakarci kawai ba komai ba" da sauri malam din ya dakatar da inna ta hanyar daga mata hannu sannan ya sake duban sumayyan
"Uhmmmm,ina jinki" ya fada yana zuba mata idanunsa,motsa bakinta ta shiga yi sai ya fahimci tamkar bata son yin magana ne saboda haka ya bata qwarin gwiwa
"Kada ki ji tsoron komai kada ki kuma damu,ki gayamin ko ma mene,mu iyayenki ne baki da kamar mu,baki da wanda zaki gayawa damuwarki sama da mu kinji ko?"kai ta gyada sannan ta bude bakinta qwalla na ziraro mata
" Abba.......bana son gidan,haushin gidan da d'akina nake ji,tsoron dakin ma nake ji,bana iya bacci,wani abu kullum sai ya fito ta bango yana kiran suna na......"shiru ne ya ratsa dakin,kowa da tunaninsa,tausayinta ke yawo cikin ransu.

          Bayan dogon nazari da abba malam yayi sannan ya magantu
"Kin tabbata kina addu'o'inki kuwa?" Shiru ta danyi sannan cikin karyewar murya tace
"Eh inayi amma wani lokaci ina mantawa bana yi" kai ya jinjina
"Shikenan babu komai,wani lokaci kuna sakaci da addu'a har shaidanu ke samun damar rabarku su cutar da ku,ba komai ki shirya kibi mai gidanki zan baki qarin wasu addu'o'in ki hada da na gunki,ki tabbata kin dage da yi babu fashi,insha Allah babu abinda zai sameki".

           Ga mamakinsu sai ta fashe da kuka kamar wadda ake zarar ranta
" Allah abba malam bazan iya komawa ba,tsoro nake ji abba,don Allah ku qyaleni"idanu suka zuba mata baki daya,bayan wani lokaci malam ya maida kansa ga mukhtar ya dafashi
"Kayi haquri mukhtari,ka bar min sumayyah anan,bayan kwana uku kacal kazo ka dauketa,kayi haquri kuma kada ka damu,ba zata wuce kwana ukun ba" kansa a qasa cikim girmamawa yace
"To malam,na gode" ya miqe ya fice suka bishi da kallo.

     Inna ce ta soma cewa cikin laushin murya
"Meye hikimar yin hakan din malam?"
"Zaki gani habiba,ku shiga ciki ke da ita sai ki dawo ki dauko kin jakar fatar can ta cikim uwar dakina"
"To" ta amsa sannan ta miqe ta kama hannun sumayya dake ci gaba da kuka suka koma ciki.






*mrs muhammad ce*👑


📚📚📚📚✍✍✍✍
[9/25, 12:42 AM] ‪+234 908 222 8222‬: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)



1⃣4⃣


________________________

*A hasiban nasi ay yaquluu amanna wa hum la yuftanun?*
_____________________

*Sadaukarwa ne ga*

*MAMAN HANIF NOVELS GROUP*👌🏽






      Qarfe goma na dare tana saman gadon innar tata,juyi kawai takeyi tare da tuhuma da kuma bincikar kanta kan abinda ta aikata,batasan dalili ba batasan me yasa ba amma ji ta dinga yi kamar ana ingizata barin gidan,wata qauna da kewar mukhtar din suka kamata,halima ce ta shigo dauke da wayar innarsu
"Yaya sumayya,yaya mukhtar ne" ta fada tana miqa mata wayar,da sauri ta miqe ta amsa wayar sannan ta kara a kunnenta halima ta juya ta fita,kasa cewa komai tayi har sai da yace
"Sumayyah!" Muryarsa a tausashe
"Na'am" ta amsa muryarta na rawa
"Sumayya......me yasa kike son ki gujemin bayan kinsan zuciyata ba zata juri haka ba?,sumayya ko cikin mafarki banson mu rabu bare a gaske,a zahiri kuma  idanu biyu" tuni ta fara tara qwalla a idanunta,zuciyarta na sake karyewa
"Ya mukhtar ban sani ba,nima bansan dalili ba da ya sanya na tsani dakina ba,bansan dalili ba na tsani dakina ma baki daya ba,kayi haquri ya mukhtar........kaji?" Shiru yayi yana mamako,babu shakka gaskiya take gaya masa har cikin zuciyarta,ya riga da yasan sumayyan sosai,koma mene yana jin ya haqura ya bada kwana ukun kamar yadda malam yace yaci gaba da addu'a kamin zuwan kwanakin,ajiyar zuciya ya sauke sannan yace
"Shikenan....babu komai kada ki damu kinji,muyi addu'a mu jira kwanakin ukun kamar yadda malam yace"
"To" ta fada,sai ya kawar da zancan ya soko wani don son faranta mata rai da kawar da zancan
"Yanzu me zan samu my sumy,nayi kewarki sosai,na dawo da kewar taki kuma tarar kin min yaji" ya qarashe cikin sigar shagwaba,dariya sosai ya bata har ta dinga jiyo sautinta ta cikin wayar wanda hakan ya masa dadi sosai,kewarsa taji ya kamata kamar ta bude idanu ta ganta gabanshi,nan ya janyeta da hira har sai da ya qarar da dukka kudin dake cikin wayarsa sannan ya haqura.

      Cikin kwanakin duk wani hadi da malam din ya sani na kariya daga shaidanu ya hada ma sumayyan,suratul baqara itace ruwan shanta,ayatush shifa,da ayoyin karya sihiri,hadin ganyan magarya,man habbatus sauda shi take shafawa saboda yana kore duk wani shaidani da zai iya kusantarka,sai turaruka daban daban,azkar na safiya da maraice da wasu qarin addu'o'in kan wanda takeyi

         Ita kanta cikin jiki da zuciyarta take jin salama da farinciki,dokin ganin mukhtar da son komawarta dakinta take.

         Ranar kwana na

Please Login or Register in order to submit comment