Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata samu ga diyansa,miqewa tayi cikin farinciki ta fice,fes taje jin ranta,don ta mustapha tana tunanin tasan yadda zata shawo kansa,don ko kadan bata jin zata iya tabbata cikin nijeria tayi rayuwa a cikinta.


Fitarta sukayi kacibus da su amira na niyyar shigowa,babu wanda ta kalla cikinsu tayi gaba abinta,yayin da eesha ta bita da harara kamar idanuwanta zai fado,babu wanda ta tsana a duniyarta sama da su'adah din,tana ganin baki daya ta kanainaye rayuwar mustapha,ta hanashi duban kowacce mace da qima,bayan ita din ba wata uwa take tsinanawa gareshi ba,abinda bata sani ba,abun a jininsa yake,tsaki ta ja wanda ya sanya amira waiwaya ta dubeta,tasan meke kai kawo a zuciyarta,saidai koma mene bata fatan Allah ya ida nufi,don qwaryar sama ke dukan ta qasa,banbancin ita da itan kadan ne.


Bayan sallama da tayi ganinsa shine abu na biyu daya biyo baya bayan shigowarta falon,nutsuwarta yaji na nemam gushewa
"Bafa mukhtar bane,ba kuma zai taba zama mukhtar ba" wannan shine kalaman sa suka dawo mata cikin kwanyarta,sai ta lumshe ido taja dogon numfashi kafin ta ajiye nunfashi ta kuma daidaita nutsuwarta.


Fuskarsa dauke da fara'a yake dubansu
"Mommies dina ne da kuma mai sunan uwar mumunai" ya furta cikin fara'a,su dinma fuskarsu washe take suka samu waje gefe da shi suka zauna,yayin da eesha tafi daura da mustapha,satar kallonshi take,baki daya man din ya sake tafiya da tunaninta,
"Allah ka mallakamin shi" ta fada cikin zuciyarta tana lumshe idanuwa tana ci gaba da satar kallonshi,wanda sam shi baisan ma tana yi ba,abinda ke gabansa kawai shi ya dameshi,gaisuwansun ma bai dago kai ba bare ya gane su waye ya amsa musu baki daya kudin goro,ba haka eesha taso ba,gaida baabaa sukayi baki daya ya amsa cikin fara'a
"Mutan kano,gaki ga mutuniyar dai,bata qyaleki ba,nan ta addabeni sai da na siya musu ticket ta taho" dariya suka dan saka baki dayansu.


A hankali ya miqe yana shafa sumar kanshi,jin maganansu yake kamar a tsakiyan kanshi kasancewar bai son hayaniya,baabaan ya fuskanci me yake son fadi,saboda haka yace
"Shikenan,kana iya tafiya" juyawa yai a hankali ya fice a falon fuska a daure kamar ko yaushe,eesha ji take kamar ta bishi ta rungumeshi,saboda yadda kullum kwanan duniya yake sake tafiya da ita,yayin da sumayya kanta ke qasa tana wasa da yatsunta zuciyarta na bugawa,amira ta bishi da kallo kamar yadda baaba shima ya bishi da kallo,shiru yaci gaba da ratsa falon har ya fice din sannan baabaa ya dauke idanuwansa daga kanshi ya maida kansu,ya dubi amira
"Aishatu ta rakaki amira kuje ku amso min saqo wajen ummenku"
"To abba" ta fada tana miqewa,tasan babanta sosai,hakan ya sanya bata ce sumayya ta taso na,tunda taga haka tasan akwai manufarsa na aikensu su biyu,baki daya taji wani nauyi ya sake kamata bayan fitar tasu,falon yayi shiru ta kasa motsawa sai kanta dake qasa har yanzu
"Mamana,ki saki jiki mana,nima fa babanki ne ko ba haka bane" murmushi tayi
"Haka ne abba" shiru ya sake ratsa falon na wasu sakanni kafin ta sake jin muryarsa
"Mama na,wata alfarma nakeson na roqeki,saidai ina jin nauyin haka" mamaki ya kamata,ita din wace?,wacce alfarma babban mutum kamar baabaa prof din zai nema daga gareta,bayan ita din ba kowa bace,bata kuma mallaki komai ba
"Baabaa,yanzu kace kai abbana ne,kuma na yarda haka ne,me yasa uba zaiji nauyin bawa diyarsa umarni" sosai wani irin qima da darajarta ya qaru a idanuwanshi,ya jima baiga nutsuwa da hankali tattare da yarinya mai makamancin shekaru irin nata ba,nutsuwarta da kaifin hankalinta shine abu na farko daya fara bashi mamaki tattare da ita,tana da wani irin dattako kunya nutsuwa da ganin darajar manya,wanda zaiyi wuya a wannan zamani ka samu mace kamarta da wannan qualities din
"Allah yayi miki albarka maman,haqiqa iyayenki sunyi nasara wajen tarbiyyarki,sun rabauta da diya ta qwarai,mamana.....kinga yayankun nan da ya fice yanzu?" Gabanta ya buga,sai ta kasa daga kai ta kalli baabaan,Allah yasa ba wani sharrin yayi mata wajen baban ba,kai kawai ta kada
"Mamana,zaki taimaka min ki taimaka masa wajen inganta rayuwarsa?" Duburburcewa tunanunta yayi,sam bata gano me baban ke nufi ba,inganta rayuwarsa kamar yaya,ya manta bata da komai ne qarqashin wasu take itama,duk yadda taso ta fassara maganar tsakaninta da qwaqwalwarta ta gaza gano ainihin ma'anar maganar,har rudun hakan ya bayyana saman fuskarta.


Murmushi baaban ya saki,ya yadda har yau ita dinma akwai sauran quruciya tattare da ita,baison rudata,saboda haka yace
"Baki fahimci baaba ko,shikenan,tashi kije kuci gaba da sabgoginku,idan kika fahimci ma'anar maganar ina son ganinki a lokacin,amma fa kada ki zurfafa tunani,kune qawayen amarya,kusha bikinku kinji mamana,Allah yayi miki albarka"
"Amin baabaa,na gode" ta fada tana miqewa,hakanan taji jikinta yayi wani mugun sanyi,rashin jin dadin kasa fahintar maganar baban ce har ya dago haka ko kuwa mene?.



Naso yafi haka but am busy fans.


#mrs muhammad ce








*mrs muhammad ce*👑

📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽
[23/02, 11:51] Beesama Zamani Wrt Grp: ✍ *~KUNDIN QADDARATA~*✍
📖📖📖📖📖


*~NA~*

*~SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA~*

*WATTPAD:HUGUMA*

*_HASKE WRITERS ASSO_*
(HOME OF EXPERT AND PERFECT WRITERS)

7⃣1⃣

*Bismillahir rahmanir rahim*

Allah S W T yana cewa

*"DUK INDA KUKE SAI MUTUWA TA RUSKEKU"*

Allah kasa mu cika da imani

____________________________________

     Qarfe biyar na yammacin ranar baki daya gidan ya sake dinkewa da jama'a saboda shirin fara gabatar da kamun amarya,sumayya na tare da amiran duk inda ta sanya qafarta sai ta janyota,kamar yanzu da suke can uwar dakan anty maamaa suna shiryawa,daga sumayyan sai amira sai humaida da humaira,amiran akewa kwalliya an kusa kammala mata,tayi kyau qwarai da gaske cikin wani irin yadin saqi na fulani mai azqbar kyau da daukan hankali,saqin fulani je wanda aka zamanantar da shi da kayan ado dana qawa,maroon ne sosai da yarfin kwalliyar golden a jiki,walwali kawai take zubawa,ta lura da yadda sumayyan ke yawaita shiru,saka bakinta cikim hirarta yayu qaranci sosai,hannu ta sanya ta tabota,ta daga kai ta dubeta tana murmushi,da hannu ta yi mata alamar lafiya,sai kawai ta girgiza kai ba tare data ce komai ba,duk yadda taso barin zancan da baabaa yayi mata abun yaqi barin kwanyarta,zuciyarta ta nace da son gano ainihin me maganar tashi ke nufi
"An gama min,saura ke" inji amira tana isa bakin mudubi tana duba kwalliyar tata,kai ta kada
"Powder kawai za'a shafa min a jamin jagira sun isa" idanu amira ga watso mata
"Bazaiyiwu ba wallahi,kina babbar qawar amarya?"
"Ki barni ayimin hakan don Allah,naga dai yau aka fara abin nan ko?,gaba a yimin" ta fada tana zama gaban mai kwalliyat,dariya humaida ta saka,yanayi da halayen sumayyan ke qara bata sha'awa,sam bata da rawar kai ko iyayi irin na 'yammata.

       Duk da cewa ba wani kwalliyar azo a gani aka mata ba amma tashi daya ta sauya,tayi wani sihirtaccen kyau mai sanyi wanda babu hayaniya a cikinshi,su kansu sai da suka yaba,biyar da kwata kiran ango saifudden ya shigo wayarta,yake sanar mata sun iso,da yake tare za'a kama su shi da ita,falon anty maamaan suka sauko sannan suka hadu sa sauran qawaye da 'yan uwa suka fito.

       Qyashi da hassada fal ran eesha,duk yadda taso taga ta wuce sumayyan a kwalliya abun yacu tura,ira kadai ta tsone mata duk taton 'yammatan nan,saboda kaf cikinsu bata ga wadda tayi ya kyawunta ba,duk da yake akwai wadanda suka saka suturar da suka fi nata kayan qaawa da tsada,amma ba'a nan take ba wai aj dannewa bodari kai,abinda bata sani ba baki daya sumayyan jinta take a wani mugun takure,karo na farko a rayuwarta data taba shiga makamanciyar wannan,qememe amira ta hanata sanya mayafi sai ratayashi kawai tayi gefan kafadarta guda daya,kayan sunyi masifar amsarta kamar wanda ya saqa su ya saqasu ne musamman saboda ita,takalmin ne kawai ya gagareta tafiya,subaleshi tayi ta nemi plat cikin na amiran ta saka,a ranar tayi adon gashinta wanda yasha gyara aka fito mata da shi cikin daurinta sai sheqi sa walwali yake,ta saje cikin 'yammatan amaryar har ta zama kamar wata fitila ta daban cikinsu.

        Bata gane wautar data tafka ba sai bayan da suka iso gurin taron,wanda a cikin gidan aka shirya kujeru rumfuna da decoration na alfarma da kece raini,saika rantse da Allah wani event center ne mai tsada aka kama,ita ke riqe da amiran amma sai ta kusa faduwa saboda yadda idanuwa suka mata caaa,idanunta ta lumshe tana kiran sunayen Allah,ko ina abokan ango ne gogaggu kuma wayayyu tsaitsaye suna jira a qaraso musu da amaryar,hannun anty huda ta danqa ta sannan ta juya har tana hardewa saboda ido ta juya,su'adah na tsaye gefan huda din,india ta tafi baki daya,sari ne a jikinta wanda ya amsa sunansa,sak irin dinki 'yan qasar hindun ne jikinya skert da 'yar fingilar riga,sai mayafin kayan a jikin skert din ta nannade jikinta,yayin da kanta ke a bude kamar nasu,sai gashin dokin da aka dinkeshi da ainihin nata ya tashi tamkar nata,ta rabashi kafadar hagu da dama kakar yadda 'yan qasar hindun keyi.

     Tana juyawa suka ci karo da anty farida umman husna,bakinta a washe take duban sumayya
"Wai wai,kunyi wuyar gani,ko diyarki baku hadu ba" murmushi sosai kan fuskarta cikin girmamawa ta gaida anty farida sanan ta wuce ummee dake cikin gida bata fito ba ta aikota wajen amiran.

       Wayarta dake hannunta ta dauki vibration sanda amarya ta samu zama a gurbinta ita da angonta,sunan nafisa ta gani,mamaki ya cikata ganin number dinta ce ta nijeria,qarar lasifiqan wajen bazai barta taji ba,hakan ya sanya ta soma takawa don barin wajen tana duban kiran,can baya inda zata iya jin ta ta tsaya ta soma lalubarta saboda kiran ya riga da ya katse
"Am at home sisi" idanu ta fiddo waje
"Da gaske?"
"Suprise wlh naso baki,shigo gidan anty ki shigo dani yau traditional setting na amira ina lissafe dama"
"Wayyo sis,gani nan" ta fada cikin zumudi da murna ta kashe wayar,daidai sanda kida ya soma tashi daga inda ake gabatar da bikin,tsalle ta dan saki kadan farinciki fak ranta
"Yi a hankali gimbiya kada ki fadi ki batan kwalliyar" abinda taji an ambata kenan,da sauri ta waiwayo,alqasim ne tsaye sanye da shadda ya kawo hula gaban goshinsa yana qare mata kallo yana murmushi,daidaita natsuwarta tayi sannan ta juya da niyyar ci gaba da tafiya,saurin shan gabanta yayi,ya wani karyar da kai
"Haba sumayya,ko gaisawa i kya tsaya muyi ko?" shiru tayi tana dubansa ba tare data ce komai ba,ji take kawai zai bata mata lokaci ne,bata da buqatar wani abu a yanzu,tana cewa ta gama da babinsa,tunda tuni ta gaya masa ita din ba budurwa bace bare ya saka ran zata biye masa,idanunta tarufe tare da yin banza da shi,tana jinshi yana magana ci kanka bata ce masa ba.

       Tunda suka fara tashin kidan ya tashi ya shiga bathroom ya sake wanka,jin kidan yake kamar a tsakiyar kanshi,duk wani abu da zai zama tamkar hayaniya bai qaunarsa,ko qwaqwaran motsi ne ya fiya yawa yanzun zai dameshi,sau tari babban wansi adam kance
"Kai ko mustapha kamar mai aljanu,koyaya motsi yake sai ya dameka" amma hakan bai rasa nasaba da ciwon kan da yake fama da shi tsawon shekaru,wanda idan ya tayar masa baya masa ta dadi.

         Ta baya yabi don bai muradin haduwa da kowa bare a tsaidashi a cikashi da suruti,baki daya yau zucuyarsa a quntace take,saidai ko kai daka sanshi baka isa ka fadi hakan ba,sakamakon yadda ko yaushe haka fuskarsa take a daure koda cikin farinciki yake indai ba girmama farincinkin yayi ba shine zaka ga fuskar ta sake washewa fiye da yadda take da,yatsanshi saqale yake da maqullin motar da yake sha'awar fita cikinta,tun kafin ya shiga wankan ya turawa P.A dinsa ya shirya haduwarsa da mutanen da yace jiya bazai samu damar ganinsu ba qasa da awa daya yana hanya kada su wuce haka,sannan ya turawa driver dinsa shima ya shirya motar da zai fita,kanshi a qasa yake takowa cikin shigarsa ta qa'ida trouser da t.shirt v neck wanda ta fidda structure ta jikinsa sosai,kwata kwata saka manyan kaya bai cikin tsarinshi,duk wanda yasan mustapha cikin duniyarsa yasan ba ma'abocin sanya manyan kaya bane,kana iya gama mu'amalarka kaf da shi baka ganshi da manyan kaya ba,daidai gun da jiya suka zauna wasa ya tuna,yaron ya fado masa,ya tuna shegen wayonsa,wani qaramin murmishi da bai shirya masa ba ya kubce masa,a hankali ya daga kanshi sai ya hangosu,tsaye yake a gabanta yayi kane kane kamar zai hade gaf din dake tsakaninsu,yayin da take tsaye hannayenta harde a qirji tana dubanshi,rashi ya baci,dan salaman da ya samu ta gushe,yana daya daga cikin abinda yasa kenan baison baqin 'yammatan cikin gidansu,yana zaton daga daga cikin 'yan matan family din nasu ne,sauya akalar tafiyar tasa yayi zuwa wajen,sai da yaje dab ya lura alqasim ne
"Itakam haka take,gobe wancan mutumin jibi wannan?" Ya qarasa bayansu,daidai sanda take fadin
"Na riga na gama magana da kai ko?,ba zaka taba samun abinda kake so ba,so don Allah ka qyale rayuwata" ta kammala fadi sannan ta juya a hankali ta soma barin wajen,burinta kawai ta isa ga nafisan gashi ya bata mata rai da lokaci baki daya,binta yayi da kallo har sai data bacewa ganinsa sannan ya juyo yana sakin ajiyar zuciya,sai suka hada idanuwa da mustaphan yana kallonshi,kunya ta kamashi,yana bala'in ganin girman almustapha da mutuncinsa,girmama shi yake qwarai da gaske,ya dan diririce yana fadin
"Barka da fitowa yaya" bai amsa ba ya qara taku zuwa inda yake yana dubanshi,haushi yakeji,hashi ya kamashi,ji yake kamar shi akawa haka
"Kan me ka tsaya mace na gaya maka irin wannan maganar ibrahim?,kai namiji ne ka manta?,so kayi maintaining dignity dinka,akwai mata da yawa a gari ka zabi wata mana,kar ka cusa kanka inda ba'a sonka,ba'a so dole,i hope ka fahimta?,ba ita daya bace mace akwaisu da yawan gaske" kai ya rusuna yana gyadashi alamun gamsuwa,cikin zuciyarshi yana cewa
"Ya mustapha kai baka hango abinda na hango ba,baka hango personalityn dana gani tattare da ita ba,hmmmm ke ka ganin so wani abu mai sauqi ne tunda kullum cikin neman son ake a wajenka"amma a fili sai yace
"na gode,Allah ya qara girma" kai ya jinjina ba tare da yace komai ba ya juya ya bar wajen.

      Kamar ta goya nafisa haka taji lokacin data ganta,tayi ado sosai tana rungume da khalid,ta amshi khalid din kai tsaye suka koma wajen da ake kamu,sanda suka je tuni al'amura sun fara nisa,bayan gabatar da abubuwan da suka dace sannan aka kama amira kafin daga bisani a bada damar yiwa amarya da ango liqi,basu suka tashi daga kamun ba sai qarfe takwas na dare,kamu ya qayatar matuqa da gaske,tafiya nafisa tayi bayan sun gaisa da amira sama sama,taso riqeta tace a'ah tayi haquri abban khalid din ya iso,saidai zata zo dinner insha Allah wanda za'ayi ranar alhamis.

       Washegari akayi arabian night wanda aka gabatar da ita itama cikin gidan baabaa prof,gidane gari guda hakan ya sanya basu da damuwar sai sun kama waje,ba qaramin qawata wajen akayi da kayan ado ba,ranar duk wani ahali da ya shafi baabaa prof sanye yake da abaya ta mata,maza kuma doguwar riga ce da hirami,kai ka rantse a ranar baqin larabawa aka yi a unguwar.


 ******* ****** ********     


Washegari tana kwance tana baccin gajiya,kasancewar alhamis ce ranar babu event din da za'a yi sai gobe idan Allah ya kaimu,ji tayi an daka mata duka,tilas ta farka tana mutstsike idanu,amira ce zaune gefanta
"Sannu,ai wallahi bacci bai ganki ba bai kuma kamaki ba,qarfe hudu zamu lunching na maman saifullahi,kuma ba kowa ne zashi ba,bamu da yawa" zama tayi sosai tana hamma hannunta kan bakinta
"Shine zaki dakamin wannan dukan,badon inajin kunyar idanun saifullahi ba sai na rama" dariya ta qyalqyale da ita
"Ato bismillah,ni kinga ina da mai ramamin,ke kuwa nasan ko na dakeki na daki banza,waccan mutumin da na gani a kano babu abinda zaya iya" ta sani sarai da abdur rahman take,bata san meye hadinta dashi ba data saka masa tsama haka da yawa,harara ta jefa mata sannan ya shiga bandaki ta wanke bakinta ta dawo ta amshi katin tana dubawa,komai a tsare yake harda dress code na maza da mata,mata shigan baqi zasuyi maza shigan fari.

        Kusan baki daya kayanta sai data baje su saman gado,ta rasa wanda zata zaba,a haka anty dije ta cimmata,dariya ta dinga yi mata
"Ato wallahi gwara ki qure adaka,don suma dangin saifullahin ba baya bane"sai data gama ruwan idonta sannan ta zabi wani shegen lace a cikin kayan wanda yake baqi ne an masa adon ja mai daukar idanuwa,zuba kayan tayi a jaka don ta nufi gidan baabaa don amira na can na jira,sanda ta isa an gama mata kwalliya,tayi masifar kyau cikin baqar wedding gown,sumayyan zama tayi itama aka soma yi mata tata.

         Wani irin sihirtaccen kyau ke fita daga kwalliyarta hadi da tsumammen qamshi,kunya ta kamata da mamakin kanta,riga da skert ne wanda suka fitar da baki daya qirarta gaba da baya
" wow"abinda amira ta dinga fada kenan tana qarewa sumayya kalo
"Haka baqin kaya ke miki kyau amiran umman khalipha?,ya Allah" kai ta kada
"Ai kam cire kayan nan ya zamemin wajibi,ina zan iya fita cikin jama'a haka amira" ta fada tana yunqurin cire daurin dankwalin da aka bata lokaci ana mata shi,da sauri amiran ta riqe hannunta tayi kicin kicin da fuska
"Allah idan kika cire sai mun bata,ke komai ma bakison ya miki kyau,kina da kyau kina da aji kina da isar da za'a dama dake,kibar yin haka don Allah" yanayin yadda tayi maganar ta bata dariya,sai ta zame hannunta tana hada mata kayayyakinta data yi amfani da su kasancewar yau cikin dakinta ta shirya
"Bari na maida su sashin anty maamaan ko"
"Godiya namescy na" murmushi tayi ta fice a dakin.

       A shirye ta tadda anty mamman,kasancewar ita zata yiwa amiran rakiya,wani irin biki suke a tsarin familynsu,suna gayyatar amarya ne da manyan yayyenta da iyayenta,inda zasu kawo musu ita suyi mata nasu bikin ma musamman haka sukeyi,ta ajjiye kayan tana saukowa suka sake kacibus da anty maamaa wadda ke kai kawon hadawa baabaa kunun alkama,haka matan suke,duk rintsi basa wasa da cikin mijinsu
"Amiran umman khalipha zo don Allah ki kulamin da kunun nan in qarasa hadawa babanku hadin salad din nan"aladabce ta asawa ta bita kitchen din,cikin sauri sauri take hada komai saboda lokacin tafiya yayi,sau uku amira na aikowa sumayyan tazo su tafi,antyn bata sani ba,sai ana hudu taji aiken da ake mata ta dubeta
"Jeki amira,na qarasa na biyoku daga baya" murmushi tayi tana noqe kafada
"A'ah anty suje kawai,ma taho".

     Cikin mintuna talatin suka gama,babu abinda jikinta yayi,saboda haka goge hannunta kawai tayi,sannan ta fidda kwalakcarta ta goga a hannayenta,ta sake shafe jikinta da turaren humrarta mai fidda wani sihirtaccen qamshi,wayarta dake ruri anty maman ta daga ta kara a kunnenta sannan tace
"Eh na gama,gani nan" ta dubi sumayya tana maqala kyakkyawar jakarta
"Muje ko amira" ta amsa.

       Tuni maman ta rigata yin gaba saboda hill shoes din dake qafarta wanda ya sake sauya yanayin tafiyarta,sannu a hankali take takawa,sai ka dauka wani salon tafiya ce ta daban,koko tsabar yanga ce da iyayi ga wanda baisan takalmin ne ya takurata ba,baqar rantsatstsiyar mota ce wadda har sheqi take da daukan ido saboda tsabar sabunta da kyau,ita daya ta rage tsaye a wajen,da alamu dukka an tafi,baya anty mamaan ta bude ta shiga,yayi kyau cikin farin qal din trouser da lallausar short sleeve t.shirt baqa mai adon fari a jiki,wadda ta fidda sirrin hannunshi na tarin gargasa wadda ta kwanta har saman tafin hannunshi,da wani sashi na murdadden dantsensa wanda kana gani kasan ya saba daga qarfe,daya daga cikin abinda ya sanya kenan bai fiya saka kaya masu gajeran hannu ba,black hight top snickers ne a qafarsa,tsintsiyar hannunshi daure da agogon fata na kamfanin gucci mai matuqar tsada da kyau,yadda jikinsa ke fidda wani sihirtaccen qamshin wani turare da mawuyacine ka gane wani iri ne haka motar ki fidda sanyayyan qamshin freshner,komai nasa mai kyau tsafta da aji ne,jin yana niyyar tayarwa ya sanya tace
"Tsaya,akwai mutum daya" a kasalance ya kashe motar,ka kadan baison tuqi da kanshi idan ba kamawa tayi ba kamar irin hakan,qarasowa tayi tana niyyar bude bayan anty maamaa tace
"Koma gaba amira" don tasan halinshi sarai,ya tsani ya dauko mutane su shiga baya baki dayansu,yana alaqanta hakan da sai driver,jin an ambaci sunan amira ya sanyashi juyowa,daidai sanda take daidaita zamanta gaban motar suka hada idanu,idanuwanta suka fada cikin nashi,tashin farko kowanne ya janye idanunshi,qirjinta na bugawa,qamshin turarenshi na ratsa qofofin hancinta,idanunta ta ragewa girma tana duban gaban motar,tana ji kamar ta zura da gudu ta bar motar,wani dabaibayi taji na daureta,kwarjininsa ya mata yawa,tana jin zamanta a bigiren bai dace ba,a kasalance ta sanya hannu zata rufe murfin motar taji kamar muryar laila na kiran sunanta,itace tafe riqe da hannun abdallah da yayi kyau cikin baqaqen suit na yara,sai baqin sau ciki na yara da baqar safa baki daya,suka qaraso bakin motar inda take zaune
"Anty,mami tace na kawo miki shi,kuka ya soma yaqi zama" dubanshi tayi cikin sigar lallashi
"Abdallah,ina cewa na gaya maka tun dazun bazanje da kai ba,ka koma gida ka zauna da su laila,yanzu zan dawo bazan jima ba" qafafunshi ya sa bubbugawa yana sakin kuka sosai kamar wanda ake yanka yana fadin
"Allah ni sai naje" ranta ya baci ganin yadda yake tsala kuka kamar tayi mishi wata uwa,sake lallaminshi tayi baiji na,maimakon haka ma sai ya buge hannun laila ya taho inda take ya shigo sit din da take,abinda bai taba yi ba kenan,yana qarasowa kuwa ta daga hannu ta kai masa mari,ta kuwa sameshi gefan fuskarshi,kafin anty maama ta furta maganar daga bude baki zata yi wata tsawa ta karade motar,tuni laila ta ja baya a tsorace,hannunshi ya miqo inda suke ya janyo abdallah wanda ke sakin kuka cikim jim zafin marin ya dorashi kan cinyarshi yana shafa inda ta mareshin
"U r very stupid,how dare you zaki mari qaramin yaro har haka?,saboda bakisan ciwonshi ba?,bakisan ciwon haihuwa ba?,idan baki iya riqeshi mai ya sanya ba zaki sa a maidashi wajen mamarshi ba,fice min a mota!" ya fada cikin bacin rai da zafin rai,bata ankara ba taji hawaye sun soma layi bisa kuncinta,ji take kamar mukhtar ke mata fadan,me ya fusata ta ta mari abdallah itama bata sani ba,hannunta ta sanya kan mabudin motar ta tura da niyyar fita anty maamaa ta dakatar da ita
"A'ah zauna,kuyi haquri mutapha,baki kyauta ba amiran umman khalipha,saurin hannu wa yaro bai kamata ba,ki kiyaye gaba"
"To maamaa" ta fada ba don taso ba ta koma ta zauna,so tayi ta qyaleta ta fita,wani nauyi taji zuciyarta tayi,tana jin hucin numfashinsu su biyun.

      Luf abdallah yayi kan cinyar mustapha wanda ya zaunar da shi suna facing juna ya rungumeshi cikin jikinshi yana ci gaba da shafa inda tayi marin,ci gaba da kallonshi abdallahn yayi,a hankali ya furta
"Abba!" Sannan ya sake narkewa cikin jikinshi,wani nauyi zuciyarta ta sake yi,sai ta kasa daurewa ta sanya kanta a tsakiyar qafafunta,tausayin abdallahn yasake qara yawan hawayen dake fita a idanunta.

        Bubbuga bayan abdallahn yaci gaba dayi kadan kadan har sai da yaji alamun ya huce,hannun ya sanya gefanshi ya ciro gorar ruwan da ya dauko da niyyar sha ya bude mishi ya saka mai a baki,sai da yasha sosai sannan ya rufe ya maidata gurbinta,ya sake zaro wayarsa ya latso wasu lambobi ya kara a kunnenshi yayi magana a taqaice
"Eh,ka sameni gidan,ka tambaya adress din" ya katse kiran ya ajjiye,tada motar yayi sannan ya ya jata a sukwane abdallah na kwance jikinsa.

        Shiru ne ya ratsa motar ba wanda ya sake magana,sumayya na kife har yanzu kan cinyarta tana qoqarin control din hawayenta,ambaton sunayen Allah ta dinga yi daya bayan daya har ta samu hawayen suka tsaya saidai bata iya dagowa ba har suka isa wajem,anty maamaa ce ta soma fita,tuni tayi gaba saboda suna isowa taji ana nemanta ta lasifiqar dake cikin wajen taron.

       A hankali ta daga kanta ta gyara yafen mayafin dake kanta sannan ta bude murfin motar ta fice,ta gefan ido yake dubanta har ta bace a wajen,gajeran tsaki ya ja,yana jin bazai iya ci

Please Login or Register in order to submit comment